Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ba ma, da tunda suka daukosa daga asibiti zai ce su saukesa a tasha.

Sai dai rashin kuɗin moto da ba ya da shi a yanzu, shi zai taka masa burki, domin a cikin jakar kayansa ya sanya kuɗin, tunda kuma lamarin ya faru bai bi ta kansu ba, ta ransa kawai ya ke yi.

Yanzu koda ya sami lafiya ma, dole sai ya nemi kuɗin moto. Ga shi duk jarinsa ya haɗa cikin jakar, tunowa da ya yi da gidan Alhaji Sama'ila ya sa ya ɗan ji sanyi, amma da kunya ya koma a yanzu ya ce musu ga tsautsayin da ya afka masa, tunda sun sallamesa. Wataƙila ma su ce ƙarya ya yi musu dama.

Haka ya yi ta saƙe-saƙe, har likita ya fito, ya kamasa ya miƙe, ya saƙalo hannunsa ta wuya, ƙafa ɗayar a ƙasa, ɗayar kuma ya ɗangaleta, domin bai isa taka ta ba, tsananin raɗaɗi da azabar zafi ta ke yi masa.

Badiyya da ke tsaye jikin motar ce ta yi saurin buɗe musu ƙofar baya, ya zaunar da shi, sannan ya zaga ya shiga, ta yi musu fatan alkairi ta koma ciki suma su ka tafi.

Sosai ya azabtu wajen Malam Ɗahe mai ɗori, karaya ce a cinya, kuma ta yi tsami sosai. Gida suka nufa, bayan an gama da su.

"Yaya! Don Allah, tsawon wani lokaci zan yi kafin a kwance mun wannan ɗaurin?" Hamusu ya tambayi Kamal, ganin zai fita daga ɗakin.

Juyowa ya yi, ya ce,
"Malam dai ya ce, wata huɗu, ko uku, idan har jikinka na da kyau. Zai riƙa turo yaronsa yana duba ka."

Hawaye ne ya wanke masa fuska lokaci guda, yaraf! Ya koma ya kwanta.

"Ka yi haƙuri Khamis! In Sha Allah kamar yau ne, za ka sami lafiya, ka koma garinku. Kada ka sanya ma kanka damuwa, ka sake janyo wata cutar." Yana kaiwa nan ya fice.

"Wata huɗu ko uku?"
Ya tambayi kansa. Ya dora da cewa,

"Inna! Ƙaddara ta yi sanadin rashin haɗuwarmu a lokacin da na so. Wani hali kike a yanzu? Wa ke yi miki jagora akan dukkanin lamuranki? Wayyo Allah na!!"

Ya faɗa cikin ɗaga murya.

***

Kallo ɗaya za ka yi ma Inno ka san ta faɗa sosai, duk da ba ta nuna damuwarta a fili, damuwar a cikin ranta ta ke, ba ta kuma samun kanta cikin yanayi na rashin jin daɗi ba, sai da ta ga jama'a na ta tafiya gidajensu, kasantuwar an yi addu'ar kwana uku.

Lubna kam, har yanzu tana cikin jimami haka ma Afreen, sai dai shi ta wajensa da sauƙi.

"Hajiya kuma yanzu tafiyar za ku yi?"
Inno ta tambayi Mommy da ke ta shirya kayansu a jaka.

"Za mu tafi Inno, amma In Sha Allah za mu riƙa zuwa akai - akai wannan lokacin, babu jinkiri irin na baya."
"Allah yasa!"
"Amin. Akwai dai sauran kayan abinci nan da yawa ko?"
"Eh, kinsan sun ce a maida na wajen Mai Unguwan nan."
"Ya kamata, tunda ba auren aka yi ba, ba amfanin a ci gaba da yi musu amfani da wani abunsu, duk wasu kaya ma da yake na su, ya kamata a mayar musu."
"Shi ke nan! Hakan za a yi." Inno ta amsa a sanyaye.

Har waje aka rako su, ana yi musu fatan Allah ya kai su lafiya ya tsare hanya.

"Wai ina Lubnar ta tsaya ne? Mun fito da ita fa, ta kuma komawa ciki, ko so take mu yi dare ne? Kai Muntari! Je ka ce ta fito mu tafi."

Da gudu Muntari ya koma cikin gidan.

A tsakar gida ya tarar da ita, ta durƙushe sai rabzar kuka take yi.

"Aunty, Hajiyar Jinjin ta ce ki fito ku tafi ke ake jira."
"Anti! Ki zo ku ta fi ke ake jira." Ya sake maimaita a karo na biyu.

Jajayen idanunta da ke ta sauƙar da ruwan hawaye, tamkar indararo ta ɗago ta kallesa.

A hankali ta ce,
"Je ka ce su tafi, ba za ni ba."

Kallon ta ya yi, sannan ya fita a guje.

"Ina take?"
Inno ta tambayesa.

"Cewa ta yi wai su tafi ba za ta ba."

Kallon juna su ka shiga yi,

"Kamar ya ya mu je ba za ta ba?"Afreen ya tambaya.

"Haka ta ce." Muntari ya amsa mishi.

"Me ta ke yi?" Ya sake tambayar Muntari.

"Kuke ta ke ta yi, tana tsakar gida ma."

Duk suka sauka daga kan mashin ɗin suka yi cikin gidan, tare da sauran mutanen da su ka yi musu rajiya, anan suka sameta durkushe sai zabga kuka ta ke yi.

Har gabanta Daddy ya ƙaraso, ya ɗagota.
"Mamana me ke faruwa ne?"

Kai ta ɗago ta kallesa,
"Daddy! Don Allah ku tafi ku barni anan. Ku barni in koyi zama da mutane, in koyi sanin daraja da kima ta ɗan Adam, ku tafi ku barni in gyara hallayata da ɗabi'ata, ko nima zan iya rayuwa cikin mutane, in daina keɓe kaina waje ɗaya a kodayaushe, na roƙeku Daddy kada ku ce a'a, don Allah. Mommy! Zainab ta yi gaskiya, ban san komai ba game da zamantakewa cikin mutane, ku amince mun don Allah."

Ta ƙarasa maganar tana durƙusawa kan gwiwoyinta; Ta haɗe hannayenta waje ɗaya alamar roƙo a garesu.

Matsanancin tausayinta ya rufe illahirin mutanen da ke wajen. Kukan da ya ƙwace ma Inno ne ya sa ta juya da sauri ta nufi ɗakinta, don ta san da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.

Zai so zamanta shi ma, kamar yadda ta ce za ta gyara rayuwarta, shi ma yana fatan rabuwa da tasa mummunar ɗabi'ar saurin fushi da rashin yi ma mutane uzuri. Ɗagota ya yi, ya rungumeta a jikinsa, ya shiga shafa kanta a hankali.

Saitin kunnenta ya kai bakinsa,
"Za ki iya zama a nan?"
Kai ta ɗaga
"Za ki iya rayuwa a cikin garin nan?"
Ta sake kaɗa kai.
"Share idanunki, ki yi min alƙawarin kin daina wannan kukan daga yau, ki kuma saki ranki, zan barki anan na wani lokaci."

Ɗagowa ta yi, ta matse idanunta, hawaye ya gangaro, ta sanya bayan hannunta ta goge, ta kalli Daddyn tana kuka mai haɗe da dariya a lokaci ɗaya.

"Kalla!"Ya faɗa, yana taɓa kumatunta.
"Ga wani hawayen na fitowa, da alama ba ki shirya zama ba."

Da sauri, ta sanya hannayenta biyu, ta goge fuskar tana faɗin,
"Na daina Daddy! Na daina, ka ga ma na goge ko?"

Murmushi ya yi, ya kaɗa mata kai, ta rungumesa tana faɗin,

"Na gode Daddy! Na gode sosai."

Kallon Hajiya da Afreen da ke kallonsu tun ɗazu ya yi, suna jira su ji hukuncin da Daddyn zai yanke, da ma sauran jama'ar da ke wajen.

Mommy da ke ta addu'ar, Allah ya sa ya amince ya bar ta,ya ga ta marairaice kamar za ta yi kuka, domin tana son ɗiyar tata ta zauna, ta koyi rayuwa cikin mutane, ta rage saurin fushi da ƙyamar mutane.

Gira Alhaji ya ɗaga mata, alamar tambaya. Murmushin da ta yi masa ya fahimci ta amince, domin shi ma yana tantamar kada ta yi masa turjiya, don yana so ya barta ɗin ko da na sati biyu ne, ta ɗan ɗebe ma su Ilu kewar rashin 'yarsu da suka yi.

Kallon Ilu ya yi,
"Ga diyarku, mu za mu wuce, kada dare ya yi mana."

Wani farin ciki ne ya ziyarci Ilu na irin karamcin da ya yi masa,

"Amma Yaya! Kana ganin za ta iya rayuwa anan kuwa? Babu wasu ababe na more rayuwa da ta saba da su, kada kuma ta taƙura."

Karaf ta cafke,
"Zan iya Baba."
"To, ai shi ke nan. Inno ta sami mai yi mata wanke - wanke da shara."

Dariya duk suka yi.

Sakin Daddyn ta yi, ta je ta shige jikin Mommy ta ƙanƙameta tamkar mai shirin komawa ciki, ta ce,

"Na gode sosai Mommy!"

Murmushi ta yi mata,
"Ba komai, Allah ya yi miki albarka, ki kuma kula da kan ki, ki kare kima da darajarki ta 'ya mace, kamar yadda na ke umurtarki da shi kodayaushe."

"Zan yi Mommy! Zan yi In Sha Allah."

Afreen da ke tsaye a gefen Mommy ne ya dafa bayanta ya ce,

"A sake mun Mommy haka, kada a ɓallata don an yi sabuwar Mommy a barni in shiga uku."

Sake Mommyn ta yi, ta juyo ta rungumesa tana kuka, ta ce,

"Almisyu ɗan'uwa!"

Hawaye ne ya sako daga idonsa ya ce,

"Ai rili mis u mai sista."

Da gudu Muntari ya isa wajen Inno, ya sanar mata, sai ga ta da saurinta ta fito tana goge ido, zuciyarta fal! Farin ciki, ta yi musu godiya sosai tare da alƙawarin kula musu da 'yar su, yadda ya kamata idan Allah ya yarda.

"Za ku saki juna mu tafi ko kuwa?" Mommy ta ce, ganin Lubna da Afreen ba su da niyyar barin juna.

Sakinta ya yi, ya juya.

Har ƙofar gida suka raka su, aka sauƙe ma Lubna kayanta, nan aka sake neman yafiyar juna, suka hau sai hanyar Jinjin.
Sai da suka ɓace ma ganinsu, sannan suka shige gida.

Dis is jos da biginin!

Rayuwa daga Jinjin zuwa Mai Ludaya.
Ko ya Rayuwar za ta kasance?
Ya rayuwar Hamusu a Jinjin?
Ya Inna Talle a Kurmawa?
Ina labarin Mai Unguwa?

Ku dakaceni cikin littafi na biyu mai suna *RAYUWAR LUBNA*
(Cigaban Abulle)
Nan ba da daɗewa ba.

Godiya ta musamman ga:
Badiyya Adam
Yayana Almu
Abu Hisham
Ummu Mahmoud
Da ɗaukacin masu bibiyar wannan labarin.

Sannunku da jimurin bibiyar wannan labari, duk da tsaiko da aka yi ta samu, hakan bai sa kun nuna gajiyawarku ba. Na gode sosai Allah ya saka da alkairi

Kura - kuran da ke ciki, Allah ya yafemin.

*ALHAMDULILLAH!*

16/12/2019

_Ummyn Yusrah_*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

*K'arshe*

_50_

Kowa ya tuba don wuya, ba lada.
Inna Talle dai tun tana iya tsayuwa, har ƙafarta ta gaza ɗaukarta ta nemi waje ta zauna, daga zaunen ma gyangyaɗi take hakan ya sa ta ja tsufanta ta yi ɗaki don sanya haƙarƙarinta a makwanci, har lokacin ba wanda ya dawo.

****

Tun daga yi mata sallah, zuwa kai ta makwancinta, zuwa yanzu da suke zaune ƙofar gida karɓar gaisuwa, gani ya ke, al'amarin tamkar almara, gani ya ke ba ta mutu ba. Idanu kawai ya zuba ma saitin ƙofar gidan, tamkar za ta fito, su zauna ta yi masa hirar shirmen nan nata. Addu'ar da ya ke, Allah ya sa ya farka daga wannan mummunar mafarkin da ya ke tun ɗazu.

Ga shi nan dai zaune kamar mutum-mutumi, abu ne mawuyaci ka iya gane halin da ya ke ciki. Baya ga fitar numfashi da kiftawar idanunsa, babu wani abu da ke motsawa a jikinsa.

"Haba Afreen! Kada ka bari tunani ya shige ka..."

Daddy da ya matso kusa da Afreen ne ya yi masa magana, ganin hawayen da ya ziraro daga idanunsa zuwa kan fuskarsa ne ya sa ya katse maganar.

Shiru ya yi na ɗan lokaci ya ci gaba.

"Haƙuri da juriya shi ya kama ce ka, ka yi mata addu'a Afreen! Shi ta fi buƙata, ba kuka ba."

"Me ya sa Daddy? Me ya sa tun a can ba ku sanar mana ba? Me ya sa kuka yi mana bazata? Ka fi kowa sanin wani hali Aunty Lubna za ta iya shiga a wannan lokacin. Na tabbatar idan ni na daure a matsayina na Namiji, ka sani ita ba lallai ta iya jurewa hakan ba. Da tun a can kuka sanar mana da komai, na san za ku taushe ta kafin mu zo..."

Kuka ne ya ƙwace masa.

Rungumosa ya yi jikinsa ya shiga bubbuga bayansa, yana magana.

"Gudun faruwar hakan ya sa muka ƙi sanar da ku, domin mun san shaƙuwar da ke tsakaninku zai iya jefa ku cikin wani hali. Ka yi ƙoƙarin riƙe kanka, ka ga taron mutanen nan duk kai su ke kallo. Ka shiga ciki ka duba wani hali su ke ciki."

Ɗago kan da zai yi, su ka yi ido biyu da Sarkin fada da ke ta galla masa harara, shi a dole yana taya Mai Unguwa kishi, gani ya ke kamar saurayinta ne.

"Zan shiga, ba yanzu ba. Daddy waye wancan da ya kima rawani, tamkar kullin kayan wanki?"
Ya tambaya yana kallon saitin da tawagar mai Unguwa ke zaune.

"Sarkin fada ne, wancan ɗayan kuma shi ne Mai Unguwa." Daddy ya ba shi amsa.

"Banza girman kato, ƙaramin mai hankali ya fishi. Idan ba zalunci ba, kamar wannan a ce shi za a ba Zainab? Ga shi ma Ubangiji ya karɓi abarsa. Shi ma Baba Ilun ko makancewa ya yi ne Ohho!"

Cewar Afreen da shi ma ke ta aike musu da saƙon harara, ga kuma wani kululun takaici da ya gama tokare masa maƙoshi, ji ya ke, kamar ya tashi ya je ya shaƙo wuyan tsoho mai budurwar zuciyar nan, domin shi ne sila. Da bai ballo zancen aure ba, da yanzu tana raye.

"Ranka shi daɗe! Anya ba za mu bar wajen nan ba? Sai ƙus-ƙus ake yi, kuma da alama duk kai su ke kallo, gani su ke duk kai ne sanadin komai, da ba a daga zancen aure ba da hakan bai faru ba."

Cewar Sarkin fada, da ya dawo da fuskarsa ga mai unguwa, bayan sake aika ma Afreen da wani mugun harara. Kansu na haɗe ya ke maganar cikin murya ƙasa-ƙasa.

"Allah ko? Gara mu zo mu tafi, nima duk a tsarge nake, ga kuma masassarar nan da ta dameni sosai."

"Mu yi musu sallama kawai mu wuce, tun kafin a fara aiko mana da makaman ƙare dangi ta ido. Ka ga wancan matashin da ke saiti na? Wannan da gani taƙadari ne, ina ga kuma saurayinta ne. Ja'iri mai kama da ƙosai."

"Na hangosa, sai saƙonni ya ke aikon ta ido. Sallamesu sai mu wuce."

Sallama su ka yi, bayan Sarkin fada ya sanar da su cewar, masassara ta dami mai unguwa sakamakon faruwar wannan al'amari.

*****

"Kinga ni ko? Na ce ki sassauta kukan nan kada ya ja miki zazzaɓi, amma tamkar zugaki na ke, dubi yadda kike ta ɓarin sanyi, kamar wacce aka izama shokin."

"Hajiya a bi ta a hankali, kin san irin wannan sabo na kwana kaɗan ya fi shiga jiki, ga kuma mutuwa ta farat ɗaya, dole abun ya dameta."
Inno da ke jan carbi ta yi magana ganin yadda Mommy ke yi ma Lubna da ke kuɗunɗune faɗa.

"Sai a ka ce ta yi ta kuka? Ashe ba za ta sanya ma ranta haƙuri ba? Duk wata shaƙuwa da suka yi, ya kai shaƙuwar da kuka yi ke da kika haifeta? Yanzu ina za a samu asibiti nan kusa?"

"Babu kam! Asibitin ɗaya ne, kuma ba ma'aikata. Akwai saiwa ai, idan za ta iya sha sai a kawo mata, a yi haƙuri a bi ta a hankali."

Da ƙyar aka samu ta sha maganin, ta koma ta kwanta.

***

"Ni fa ina ga kamar ƙafar nan akwai karaya, ba za a kai sa wajen Malam Ɗahe ya duba ba kuwa? Kwanansa biyu fa kenan da dawowa gida, bayan ya kwana ɗaya a asibiti. Ƙafar za ta yi masa tsami."

Cewar Badiyya da ke kallon Kamal, lokacin da suka shigo duba Hamusu, a ɗaya daga cikin ɗakunan dake gidan wanda suka yi masa masauƙi.

"Na yi tunanin hakan, na ga har yanzu ba ya taka ƙafar. Barin shirya sai in kai sa."

Ficewa su ka yi, ya ta fi shiryawa.

Hamusu da tun lokacin da aka ambaci karaya, ya ji damuwa ta ziyarcesa, fatansa kawai Allah ya sa buguwa ne ba karayar da suka ambata ba. Domin ko kwana biyu baya fatan ya kara a cikin garin nan, ba don rashin tafiyarsa ba ma, da tunda suka daukosa daga asibiti zai ce su saukesa a tasha.

Sai dai rashin kuɗin moto da ba ya da shi a yanzu, shi zai taka masa burki, domin a cikin jakar kayansa ya sanya kuɗin, tunda kuma lamarin ya faru bai bi ta kansu ba, ta ransa kawai ya ke yi.

Yanzu koda ya sami lafiya ma, dole sai ya nemi kuɗin moto. Ga shi duk jarinsa ya haɗa cikin jakar, tunowa da ya yi da gidan Alhaji Sama'ila ya sa ya ɗan ji sanyi, amma da kunya ya koma a yanzu ya ce musu ga tsautsayin da ya afka masa, tunda sun sallamesa. Wataƙila ma su ce ƙarya ya yi musu dama.

Haka ya yi ta saƙe-saƙe, har likita ya fito, ya kamasa ya miƙe, ya saƙalo hannunsa ta wuya, ƙafa ɗayar a ƙasa, ɗayar kuma ya ɗangaleta, domin bai isa taka ta ba, tsananin raɗaɗi da azabar zafi ta ke yi masa.

Badiyya da ke tsaye jikin motar ce ta yi saurin buɗe musu ƙofar baya, ya zaunar da shi, sannan ya zaga ya shiga, ta yi musu fatan alkairi ta koma ciki suma su ka tafi.

Sosai ya azabtu wajen Malam Ɗahe mai ɗori, karaya ce a cinya, kuma ta yi tsami sosai. Gida suka nufa, bayan an gama da su.

"Yaya! Don Allah, tsawon wani lokaci zan yi kafin a kwance mun wannan ɗaurin?" Hamusu ya tambayi Kamal, ganin zai fita daga ɗakin.

Juyowa ya yi, ya ce,
"Malam dai ya ce, wata huɗu, ko uku, idan har jikinka na da kyau. Zai riƙa turo yaronsa yana duba ka."

Hawaye ne ya wanke masa fuska lokaci guda, yaraf! Ya koma ya kwanta.

"Ka yi haƙuri Khamis! In Sha Allah kamar yau ne, za ka sami lafiya, ka koma garinku. Kada ka sanya ma kanka damuwa, ka sake janyo wata cutar." Yana kaiwa nan ya fice.

"Wata huɗu ko uku?"
Ya tambayi kansa. Ya dora da cewa,

"Inna! Ƙaddara ta yi sanadin rashin haɗuwarmu a lokacin da na so. Wani hali kike a yanzu? Wa ke yi miki jagora akan dukkanin lamuranki? Wayyo Allah na!!"

Ya faɗa cikin ɗaga murya.

***

Kallo ɗaya za ka yi ma Inno ka san ta faɗa sosai, duk da ba ta nuna damuwarta a fili, damuwar a cikin ranta ta ke, ba ta kuma samun kanta cikin yanayi na rashin jin daɗi ba, sai da ta ga jama'a na ta tafiya gidajensu, kasantuwar an yi addu'ar kwana uku.

Lubna kam, har yanzu tana cikin jimami haka ma Afreen, sai dai shi ta wajensa da sauƙi.

"Hajiya kuma yanzu tafiyar za ku yi?"
Inno ta tambayi Mommy da ke ta shirya kayansu a jaka.

"Za mu tafi Inno, amma In Sha Allah za mu riƙa zuwa akai - akai wannan lokacin, babu jinkiri irin na baya."
"Allah yasa!"
"Amin. Akwai dai sauran kayan abinci nan da yawa ko?"
"Eh, kinsan sun ce a maida na wajen Mai Unguwan nan."
"Ya kamata, tunda ba auren aka yi ba, ba amfanin a ci gaba da yi musu amfani da wani abunsu, duk wasu kaya ma da yake na su, ya kamata a mayar musu."
"Shi ke nan! Hakan za a yi." Inno ta amsa a sanyaye.

Har waje aka rako su, ana yi musu fatan Allah ya kai su lafiya ya tsare hanya.

"Wai ina Lubnar ta tsaya ne? Mun fito da ita fa, ta kuma komawa ciki, ko so take mu yi dare ne? Kai Muntari! Je ka ce ta fito mu tafi."

Da gudu Muntari ya koma cikin gidan.

A tsakar gida ya tarar da ita, ta durƙushe sai rabzar kuka take yi.

"Aunty, Hajiyar Jinjin ta ce ki fito ku tafi ke ake jira."
"Anti! Ki zo ku ta fi ke ake jira." Ya sake maimaita a karo na biyu.

Jajayen idanunta da ke ta sauƙar da ruwan hawaye, tamkar indararo ta ɗago ta kallesa.

A hankali ta ce,
"Je ka ce su tafi, ba za ni ba."

Kallon ta ya yi, sannan ya fita a guje.

"Ina take?"
Inno ta tambayesa.

"Cewa ta yi wai su tafi ba za ta ba."

Kallon juna su ka shiga yi,

"Kamar ya ya mu je ba za ta ba?"Afreen ya tambaya.

"Haka ta ce." Muntari ya amsa mishi.

"Me ta ke yi?" Ya sake tambayar Muntari.

"Kuke ta ke ta yi, tana tsakar gida ma."

Duk suka sauka daga kan mashin ɗin suka yi cikin gidan, tare da sauran mutanen da su ka yi musu rajiya, anan suka sameta durkushe sai zabga kuka ta ke yi.

Har gabanta Daddy ya ƙaraso, ya ɗagota.
"Mamana me ke faruwa ne?"

Kai ta ɗago ta kallesa,
"Daddy! Don Allah ku tafi ku barni anan. Ku barni in koyi zama da mutane, in koyi sanin daraja da kima ta ɗan Adam, ku tafi ku barni in gyara hallayata da ɗabi'ata, ko nima zan iya rayuwa cikin mutane, in daina keɓe kaina waje ɗaya a kodayaushe, na roƙeku Daddy kada ku ce a'a, don Allah. Mommy! Zainab ta yi gaskiya, ban san komai ba game da zamantakewa cikin mutane, ku amince mun don Allah."

Ta ƙarasa maganar tana durƙusawa kan gwiwoyinta; Ta haɗe hannayenta waje ɗaya alamar roƙo a garesu.

Matsanancin tausayinta ya rufe illahirin mutanen da ke wajen. Kukan da ya ƙwace ma Inno ne ya sa ta juya da sauri ta nufi ɗakinta, don ta san da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.

Zai so zamanta shi ma, kamar yadda ta ce za ta gyara rayuwarta, shi ma yana fatan rabuwa da tasa mummunar ɗabi'ar saurin fushi da rashin yi ma mutane uzuri. Ɗagota ya yi, ya rungumeta a jikinsa, ya shiga shafa kanta a hankali.

Saitin kunnenta ya kai bakinsa,
"Za ki iya zama a nan?"
Kai ta ɗaga
"Za ki iya rayuwa a cikin garin nan?"
Ta sake kaɗa kai.
"Share idanunki, ki yi min alƙawarin kin daina wannan kukan daga yau, ki kuma saki ranki, zan barki anan na wani lokaci."

Ɗagowa ta yi, ta matse idanunta, hawaye ya gangaro, ta sanya bayan hannunta ta goge, ta kalli Daddyn tana kuka mai haɗe da dariya a lokaci ɗaya.

"Kalla!"Ya faɗa, yana taɓa kumatunta.
"Ga wani hawayen na fitowa, da alama ba ki shirya zama ba."

Da sauri, ta sanya hannayenta biyu, ta goge fuskar tana faɗin,
"Na daina Daddy! Na daina, ka ga ma na goge ko?"

Murmushi ya yi, ya kaɗa mata kai, ta rungumesa tana faɗin,

"Na gode Daddy! Na gode sosai."

Kallon Hajiya da Afreen da ke kallonsu tun ɗazu ya yi, suna jira su ji hukuncin da Daddyn zai yanke, da ma sauran jama'ar da ke wajen.

Mommy da ke ta addu'ar, Allah ya sa ya amince ya bar ta,ya ga ta marairaice kamar za ta yi kuka, domin tana son ɗiyar tata ta zauna, ta koyi rayuwa cikin mutane, ta rage saurin fushi da ƙyamar mutane.

Gira Alhaji ya ɗaga mata, alamar tambaya. Murmushin da ta yi masa ya fahimci ta amince, domin shi ma yana tantamar kada ta yi masa turjiya, don yana so ya barta ɗin ko da na sati biyu ne, ta ɗan ɗebe ma su Ilu kewar rashin 'yarsu da suka yi.

Kallon Ilu ya yi,
"Ga diyarku, mu za mu wuce, kada dare ya yi mana."

Wani farin ciki ne ya ziyarci Ilu na irin karamcin da ya yi masa,

"Amma Yaya! Kana ganin za ta iya rayuwa anan kuwa? Babu wasu ababe na more rayuwa da ta saba da su, kada kuma ta taƙura."

Karaf ta cafke,
"Zan iya Baba."
"To, ai shi ke nan. Inno ta sami mai yi mata wanke - wanke da shara."

Dariya duk suka yi.

Sakin Daddyn ta yi, ta je ta shige jikin Mommy ta ƙanƙameta tamkar mai shirin komawa ciki, ta ce,

"Na gode sosai Mommy!"

Murmushi ta yi mata,
"Ba komai, Allah ya yi miki albarka, ki kuma kula da kan ki, ki kare kima da darajarki ta 'ya mace, kamar yadda na ke umurtarki da shi kodayaushe."

"Zan yi Mommy! Zan yi In Sha Allah."

Afreen da ke tsaye a gefen Mommy ne ya dafa bayanta ya ce,

"A sake mun Mommy haka, kada a ɓallata don an yi sabuwar Mommy a barni in shiga uku."

Sake Mommyn ta yi, ta juyo ta rungumesa tana kuka, ta ce,

"Almisyu ɗan'uwa!"

Hawaye ne ya sako daga idonsa ya ce,

"Ai rili mis u mai sista."

Da gudu Muntari ya isa wajen Inno, ya sanar mata, sai ga ta da saurinta ta fito tana goge ido, zuciyarta fal! Farin ciki, ta yi musu godiya sosai tare da alƙawarin kula musu da 'yar su, yadda ya kamata idan Allah ya yarda.

"Za ku saki juna mu tafi ko kuwa?" Mommy ta ce, ganin Lubna da Afreen ba su da niyyar barin juna.

Sakinta ya yi, ya juya.

Har ƙofar gida suka raka su, aka sauƙe ma Lubna kayanta, nan aka sake neman yafiyar juna, suka hau sai hanyar Jinjin.
Sai da suka ɓace ma ganinsu, sannan suka shige gida.

Dis is jos da biginin!

Rayuwa daga Jinjin zuwa Mai Ludaya.
Ko ya Rayuwar za ta kasance?
Ya rayuwar Hamusu a Jinjin?
Ya Inna Talle a Kurmawa?
Ina labarin Mai Unguwa?

Ku dakaceni cikin littafi na biyu mai suna *RAYUWAR LUBNA*
(Cigaban Abulle)
Nan ba da daɗewa ba.

Godiya ta musamman ga:
Badiyya Adam
Yayana Almu
Abu Hisham
Ummu Mahmoud
Da ɗaukacin masu bibiyar wannan labarin.

Sannunku da jimurin bibiyar wannan labari, duk da tsaiko da aka yi ta samu, hakan bai sa kun nuna gajiyawarku ba. Na gode sosai Allah ya saka da alkairi

Kura - kuran da ke ciki, Allah ya yafemin.

*ALHAMDULILLAH!*

16/12/2019

_Ummyn Yusrah_

/n An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na

Please Login or Register in order to submit comment