Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma, setin kofuna da jug ɗayan kuma setin tukwane.

Tana cikin jeresu a cikin wani buhu ne, Afreen ya shigo, hankali a tashe.

"Mommy wai da gaske Zainab tafiya zata yi?"

Ɗagowa ta yi, fuskarta da alamar rashin jin daɗin tafiyar nata, ta ce

"Hummm! Haka Daddynku ya ce."

"Mommy to me ya sa?"

"Ka sanshi ai, da maida ƙaramin abu ya zama babba. Yanzu haka ya yi ma maganar Babanku rashin fahimta ne, ya hau dokin zuciya."

Zama ya yi a bakin gado,

"Daddy Ho! Me Baban ya ce ne Mommy?"

Nan ta labarta masa yadda aka yi.
Matsowa ya yi kusa da ita, ya riƙo hannunta yana faɗin,

"Mommy don Allah ki roƙe sa ya barta, idan ta koma tsohon nan zasu aura mata, kinga kuma da ƙuruciyarta za a cutar da ita. Don Allah Mommy!"

Ya ƙarasa maganar tamkar mai shirin yin kuka.

"Afreen! Da da yadda zan yi in hana da na yi, sai dai babu, Alhaji ya riga a tirje, sai dai mu yi haƙuri. Idan yaso ko gobe ne sai mu shirya mu tafi, daga can mu rokesu ko Allah zai sa su yarda."

"Allah yasa."

****

Manyan buhunan biyu aka sauƙe da kwandon kayan miyu, tumatur biyu, tattasai biyu, attaruhu ɗaya, da ƙaramin buhun albasa, da jarkar manja a ƙofar gidan Ilu.

Ana gama sauƙewa, sarkin fadar Mai Unguwa ya biya masu amalanken kuɗinsu suka juya. Ilu da ya yi mutuwan tsaye don mamaki ne yasa ya yi saurin ƙarasawa wajen, ganin Sarkin fadan na neman ɗan aika zuwa cikin gidan.

Yana isowa, Sarkin fada ya fara,
"Ranka shi daɗe! Kaga uban Abu, sirikin babban mutum. Kaga zuriya masu rabo da babbar sa a! Mai Unguwa aiko ni, ya ce ga shinkafa a yi ta dafa ma jama'ar garin Mai Ludaya da maƙwaftanta kowa ya shaida, bikin da ba a taɓa yin irinsa ba, ba kuma za a taɓa yi ba."

Gaba ɗaya Ilu ya rasa bakin magana, domin bai san me zai ce ba a yanzun. Yana buƙatar kaɗaicewa don samun damar tunanon mafita.

Yaƙe ya yi, wanda ya fi kuka ciwo.

Hannu ya sa a aljihu ya ciro naira dubi, gudan ɗari biyar, sai gudan ɗari biyu, sai gudan ɗari, sauran duk gudan goma ne da ishirin, sai hamsin.

"Gashi ka zo yau ban fita ba balle in ba da na goro, ga wannan ba yawa, a yi haƙuri. Tukwuici na musamman na zuwa da izinin Allah."

Karɓa ya yi ya jujjuya su alamar sun yi kaɗan, kafin ya cusa magoginsa a baki ya goge haƙorarsa ya furzar da tukar kafin ya ce,

"To, ai shi ke nan, tunda dai mai yawar na hanya, ai ba damuwa. Idan an shiga a gaida gimbiyar."

"Zata ji."

Cikin zaƙuwa ya amsa masa, don ya zaƙu ya tafi.

Yana tafiya ya nemo majiya karfi suka tayashi kwansar kaya.

Kafin ka ce me, zance ya zaga gari, irin kayan abincin da Mai Unguwa ya tura gidansu Abulle.

_Ummyn Yusrah_

[11/22, 9:13 PM] Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_An sami kuskuren lamba a shafin da ya gabata. 36 ne aka sa 37._

_37_

Fitowa ta yi daga maɓoyarta, wanda ta ɓoye lokacin da ta hango motar Afreen ya shigo layin. Waige-waige ta shiga yi, daga bisani ta juya ta cigaba da zuba sauri tamkar mai shirin tashi sama.

Wani nannauyar ajiyar zuciya ta yi, lokacin da ta iso bakin titi. Kallon yadda ababen hawa ke kai kawo kawai take yi, ta rasa ta ina zata fara tsaran abun hawa, ga jikinta dake ta kaɗawa tamkar mazari

****
Mommy! Yanzu ina take?"
Kallonsa ta yi,
"Tana falo ai, can na barta."
"Shigowata banganta ba, wataƙila ko don ban kula bane. Barin dubata."
Ya miƙe ya fita.

Kai tsaye falon ya nufa, bai ganta ba, ya nufi ɗaki, bata ciki, sai jakarta da ke ajiye a tsakar ɗakin.

Tunaninsa ne ya bashi, tana banɗaki, me yiwa ta na wanka ne. Hakan ya sanya ya koma ɗakin Mommyn suka ci gaba da tattaunawa yanda zasu yi don ganin an fasa auren Abullen idan sun je goben.

***
Duk kayan da aka shigo da shi, ɗaki ɗaya aka tarasu.

Cikin sanyin jiki Ilu ke yin komai.
Ganin mutane sun fara taruwa a gidan ne, ya buƙaci da su keɓe a ɗakinsa da Inno don jin yadda suka yi.

"Malam me ya faru ne? Duk naga jikinka ya yi sanyi. Ba dai wani abin ne ya sami mutanen Jinjin ɗin ba?"

Inno ta tambayesa lokacin da ta shigo ɗakin ta ganshi zaune ya taƙure, fuskarsa kuma na bayyanar da alamar damuwa.

"Bari kawai! Yaya ya ce Abulle ba za ta dawo ba, yanzu haka makaranta zai sa ta."

"Malam! Auren fa?"

"Na yi masa maganar, sai dai ya ƙi ya saurareni, ya kuma karɓi uzurina."

Ƙirjinta ta buga da hannayenta duka biyun tana mai kallon sa.

"Yaya kam,  nema yake ya ja mana  abun magana a gari."

"Na ma rasa ta cewa nikam."

"Yanzu Malam meye abun yi?"

Cikin yanayin damuwa ya ce,
" Ni kaina ban san ta ina zan fara ba. Ga kuma kaya da Mai Unguwa ya turo da shi, a yi amfani da shi wajen shagalin buki. Ban san ta ina zan fara sanar da shi zancen Yaya ba! Ban san da wani ido zan kalli jama'ar garin nan ba. Ta dalili hakan duk wani kima da daraja ta zuri'armu zai iya shafa."

Don numfashi ta ja,

"To, Malam! Ko dai komawa za ka yi ne ka gwada ƙiran ita Hajiyar ta lallaɓa Yayan ya barta ta dawo?"

Miƙewa ya yi, yana zura takalmarsa a ƙafa, yana faɗin,

"Haka ma za a yi, barin je yanzu. Ku cigaba da shirye-shirye kada ki nuna wani alama da mutane za su gane akwai matsala."

"To, a dawo lafiya. Allah yasa a dace."
"Amun."
Yamsa ya fita, itama ta koma suka ci gaba da aikinsu.

***

Ko kaɗan baya jin daɗin tallar yau, badon kuɗin mota da yake son tarawa a yau gobe ya wuce gida ba, da ba  abinda zai sa ya fito.

A haka yake yake bin tituna, idan ya ga lungu ya shiga, sai dai cikin da sauƙi.

Gidan Alhajin da ya zubar ma shara ne ya faɗomasa. Cikin azama ya ɗau hanyar Unguwar zuciyarsa cike da fatan samun nasara.

****

"Ina Zainab ɗin?"

Mommy ta tambayi Afreen lokacin da ta fito, ta gansa zaune a falo.

"Ban sameta a falo ba, na leƙa ɗakinta bata ciki, ina tunanin wanka ta shiga."

Ya bata amsa

"Wani irin wanka ne haka har yanzu? Alhaji ya fara magana, ta shirya kafin Tukur ya maida shi wajen aiki ya zo ya kaita, ya dawo."

Ta yi maganar tana tafiya ɗakin don ganin irin wankar da Zainab ke yi, wanda ya hanata fitowa har yanzu.

Shima ɗakin Lubna ya nufa, kwance ya sameta, tana daddana waya.

Bayan ya shiga ne, ya zauna kan kujerar.

"Yau dai mutumiyarki zata tafi ki huta."
Ya faɗa yana dariya,

Ɗagowa ta yi, tana yi masa kallon rashin fahimta.

"Wace mutumiyata kuma?"
"Zainab!"

"Tafiya kuma? Daddy ai ya ce zata yi karatu anan ko? Ba ɗazu ka fita duba makarantar da za a sata ba?"

Ta jero masa tambayoyin, kallonta ya yi, ya ce,

"Kinsan Daddy ai! Abu kaɗan ke harzuƙasa."

"Me aka yi to?"

Nan ya faɗamata abinda Mommy ta faɗamasa.

Karo na farko kenan da ta ji batason tafiyar Abulle, zata je ta roƙi Daddy ko zai yi haƙuri, ya je ya ba Mai Unguwa haƙuri ya haƙura da auren zuwa wani lokaci.

_Ummyn Yusrah_
[11/22, 9:14 PM] Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_38_

"Ina kuma zaki je, kin barni a zaune?"

Ya tambayeta, lokacin da yaga ta ɗau hanyar fita daga ɗakin ba tare da ta yi masa magana ba.

"Zan sami Daddy ne."
Abinda ta ce kenan, ta yi gaba ba tare da ta jira taji me zai ce ba.

Keɓe baki ya yi, ya ɗage kafaɗunsa  fili ya ce,
"A dawo lafiya. Shalelen Daddy."

Yana shirin miƙewa ne Mommy ta shigo,

"Zainab fa bata ɗaki, na duba banɗaki ma bata nan."

Cikin mamaki ya ce,
"Bata ciki kuma? Ni dana ga bata ɗakin na yi zaton banɗaki ta shiga."

"Bata nan kam, zo ka duba ko tana kicin. Barin sanar ma Daddynku tana shiryawa."

Ta juya, shima ya fice zuwa kicin.

***
Yana tsaye, ya kara waya a kunnensa, yana sarma Tukur da ya ƙirasa yana sanar masa ya iso, ne ta shigo.

Sauƙe wayar ya yi, ya kalleta
"Mamana yaya aka yi?"
Ƙarasawa kusa da shi ta yi, ta riƙo hannayensa duk biyun, ta ce

"Daddy! Don Allah kada ka bar Zainab ta..."

Cire hannunsa ɗaya ya yi daga nata, ya ɗaga mata alamar ta dakata yasa ta katse zanceta ba tare da ta kai aya ba.

"Idan dai kan wannan zancen kika zo, to na riga na rufe shafinsa. Idan kuma da makasudin zuwan naki, ki sanar da ni, zan koma wajen aiki ne."

Girgiza kan da ta yi, ya yi daidai da gangarowar hawaye daga idanunta.

"Kuka kuma Mamana? Indai zaki bita maza ki shirya ku tafi, idan an yi bikin sai ku dawo."

Yana kaiwa nan ya yi waje, don baiso ta matsamasa ya santa da naci.

Cikin sanyi jiki ta bar falon zuwa wajen su Mommy da ke ta neman Abulle.

Duk wani saƙo da lungu na gidan sun bincika ba ita ba dalilinta. Har Ɗayyabu suka tambaya ko ta fita, ya sanar da su bata fita ba, ɗazu dai sun jima da ita anan daga bisani ta tashi ta koma ciki.

Abu wasa-wasa, sai gashi yana neman zamewa gaske.

Suna tsaye cirko-cirko tamkar zakarun da suka ƙoshi suna neman abokan gwabzawa ne a harabar gidan, cikin tashin hankali, ƙira ya shigo wayar Mommy.

Sunan da ta gani ne, yasa gabanta ya yi mummunar bugawa.

Sau biyu tana tsinkewa taƙi ɗagawa, tunaninta idan ta ɗaga ya tambayeta 'yarsa ta ce masa me?

Bata shirya wannan amsar ba a yanzu, domin batasan wani irin ruɗani zasu shiga ba, domin a yanzu ma tasan cikinta suke, tunda har taga ƙanin mijin nata ya ƙirata.

****

Ya yi tsaki ya fi a ƙirga. Gashi dai wayar na ƙara, amma anƙi ɗagawa, tunaninsa kada dai itama Hajiyar irin amsar Yayan nashi take son sanar da shi. Tunda ga alama ya nuna, ya ƙirata ta ƙi ɗagawa.

Saƙowa ya yi, daga kan bishiyar, ya zube a ƙasa, ya jingina da jikin itacen bishiyar.

Zuciyarsa ce ke rayamasa, anya ba zai gudu ya bar garin ba? Ya gudu ya je ina? Ita Innon kuma yaya zata yi idan ta ji labarin ya gudu. Gaskiya bai yi mata adalci ba, a ce babu shi babu Abulle, amma kuma fa yana tunanin irin badaƙalar da za a kwasa a garin, gara kawai ya gudu, idan ƙura ta lafa ya dawo. Idan yaso Inna za ji da su.

Yana gama tunanin ne ya miƙe, ya ƙara cusa ƙafarsa cikin ƙwaftarsa tamkar mai shirin zuwa kiwon shanu."

Ya yanki jeji, ya hau tafiya.

*****
"Garbati! Ina fatan ka tura Salele ya tafi duba ɗan nan? Duk hankali na yana garesa."

Inna Talle ta tambaya, lokacin da ta dogaro sandarta ta fito daga cikin ɗakin da aka yi mata masauƙi.

"A'a! Yaya, keda ba ki da lafiya kuma sai fi fito? Da dai kin zauna waje ɗaya ne, kinga jikin naki duk ba ƙwari"

Dalu da ta taho da sauri ta riƙe Innar ce take magana.

" Indai ba Hamusu na gani a gabana ba ai zama bai ganni ba. Gara kawai in fita in nemo ɗana da kaina, tunda naga ku baku damu da batar nasa ba. Da ɗanku ne ya bata, cikinku ba mai zama a gidan nan."

"Yaya ki yi haƙuri, ana iya bakin ƙoƙari wajen nemosa, za a gansa nan bada daɗewa ba."

"Zaki sake ni, ko sai na dokeki da sandar nan? Kuna nan zaune ku ci ku sha hankali ƙwance ne zaki ce ana ƙoƙari? Ina shi mijin naku? Kai Garbati! Ka zo ka maidani Mai Ludaya kokuwa?"

"Ki yi haƙuri, ya tafi kai Salele can Mai Ludayan, daga can zai wuce Jinjin ɗin."

"Au! Sun tafi?"

"Eh, sun tafi."
"To ai shi ke nan, yanzu kam zan ɗan sami nutsuwa. Allah yasa a dace."

"Amin Yaya, mu je ki kwanta."

"Ke ni barni! Kwanciya kamar wata ruwa. Barni a waje sha iska."

"To, mu je ga tabarma can sai..."

"Wannan ai iskanci ne! Hatsin ne aka bar yara suke wasa da shi?"

Garbati ya fara sababi lokacin da ya shigo gidan.

Da sauri Delu ta fara bubbuga hannunta a baki, alamar ya yi shiru.

Ai kamar ta ƙara tunzurasa

"Lallai Delu baki da mutunci! Ina magana kina yi min nuni da in yi shiru? Wato ga sakarai ko?"

Ya nufota kamar zai kai mata duka.

"Wa nake ji kamar Muryar Garbati?"

Da sauri Delu ta ce,
"Iy! Shi ne."
"Har sun dawo ne?"

"Eh, da yake fitar wuri suka yi, zuwa mai Ludayan shi yasa suka dawo da wuri."

Sai yanzu ya fahimci kan me ake zancen.

"Eh, Yaya na dawo, da yake mun fita da wuri."

"To sannu da dawowa."

Ya juya, yana tunanin nacin Yayar tasa.

_Ilu mai amalanke Allah ya tsare hanya_

_Ummyn Yusrah_

[11/23, 3:07 PM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_39_

Ta daɗe sosai a titin, tana tunanin yadda za ta yi ta tsare abin hawa, daga bisani ta sanya hannu ta tsare mai mashin, ganin da ta yi mutane da yawa haka suke yi. Domin a tsayuwar da ta yi mutane da yawa sun tsare kuma sun tafi.

Da ƙyar ta iya tuna sunan tashar da mai mashin ɗin zai kai ta.

Ganin da ya yi mata, wata kala ya sa ya cajeta murtala biyar. Ba ta damu ba, babban burinta kawai ta ganta cikin motar da zai kaita gida.

Suna barin wajen, Hamusu yana yankowa, ya nufi gidan Alhaji Shitu domin aiwatar da aikinsa.

Ya yi sa a kuwa akwai aiki, don haka ajiye tirensa ya yi, ya sunkuya aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

****

"Lahhhh! Alƙur'an na yi mantuwa cikin jakata."

Abulle ta faɗa lokacin da suka yi nisa da tafiya.

Bai kulata ba, sai ma wuta da ya ƙara ma mashin ɗin.

"Malam don Allah ka maidani, na yi mantuwa ne." Ta faɗa ganin da ta yi, bai da alamar tsayawa.

Masifa ya hauta da shi,
"Idan na kai ki sai kin ƙaramin kuɗi, haka kuke, tsabar son abin duniya irin na iyayenku, sai suyi ta turoku birni yin aiki, don ku tara musu abin duniya, ko duba irin rayuwar da za ku faɗa ciki basu yi, abin duniyar kawai shi ne burinsu. Ke da gani ma gudowa kika yi daga gidan aikin naki ba a sani ba."

Takaici ne ya kamata, meye nashi a ciki idan ma hasashen nasa haka ne?

"Nawa zan ƙara maka to?" Ta tambayesa don ba ta son jan wani zance.

"Mu je tukunna in ga inda zan ajiyeki, sai mu fara sabon ciniki."

"Wajen da ka ɗaukoni, wajen za ka ajiye ni."

"Yauwa, Ko ke fa! Gara dai ki koma, idan ya so, sai a mai dake gaban iyayeki a mutunce ai ya fi."

"Yau na ga ikon Allah! Ni fa ba aikatau na zo yi ba."
Ta ba shi amsa.

"Ƙarya kike!"
Ya faɗa har yana wani zabura akan mashin ɗin.
"Idan ba aikatau ba, to menene? Ko aure za a yi miki, kika gudu?"

'Sai ka yi kuma, ni ba danginka ba, ka wani daddage. Da zan iya gane unguwar ma sauƙa zan yi in hau wani, don dai kawai kai ka ɗaukoni shi ya sa.' Ta faɗa a zuciyarta.

Har suka isa inda ya ɗauketa, ba ta kuma ce masa komai ba. Haka ya yi ta zuba tamkar injin markaɗe har suka iso wajen da ya ɗauketa.

Yana sauƙeta ta ba shi murtala shida. Mita ya shiga yi, daga bisani ya ja mashin ɗin ya yi gaba.

****
Ɗayyabu ne ya turo ƙofar gidan ya shigo duk jikinsa ba ƙwari.

"Ya ya, ka sameta kuwa?"
Afreen ya tambayesa cikin zaƙuwa.

"Wallahi na duba, har bakin hanya ko mai kama da ita bangani ba."

Shiru ne ya gifta na wani lokaci, kowa saƙar zuci yake.

"Mommy ko za a faɗa ma Daddy?"
Lubna ta faɗa hankalinta a tashe.

Kallonta Mommyn ta yi,
"Kada mu yi gaggawar sanar da shi, yanzu Afreen da Ɗayyabu za su fita su sake dubata ko Allah zai sa a dace."

"Allah yasa a ganta, In Allah ya yadda ba za ta ɓace ba."

"Allah yasa Mommy!" Ta faɗa tana kwantar da kanta a kafaɗar Mommyn

"Ɗayyabu kuma ka ce baka ji fitarta ba?"
Hajiya ta sake tambayarsa.

"Gaskiya banga fitarta ba, ina zaune a nan tun safe, sai kuma banɗaki da na shiga, bayan nan ban je ko ina ba."

Ya bata amsa.

"Ku je da Afreen ku sake dubata to."

Afreen kam ya ma kasa magana, gaba ɗaya jin lamarin yake kamar almara.

Lokacin da take faɗamasa ko ba a sani ba sai ta gudu, ya ɗauka kawai faɗa take, ashe zancen gaskiya ne.

Lallai kowa ya raina mai labari, in kaga mai gudu shi ne.

****

Har ya ɗau hanyar fita daga gari, sai kuma zuciyarsa ta yi ta tunatar masa da rashin adalcin da yake shirin aikatawa.

Gara yakoma ya sake ƙiran Hajiyar, wataƙila ta ɗauka sai ya yi mata bayani.

****

"Kai Afreen! Ka ko ji abinda nake cewa kuwa?"

Mommy ta taɓa shi, kafin ya dawo daga dogon hanyar da zuciyarsa ta ɗauka, na tunani.

"Na'am!"

Kallonsa ta yi,
"Na ce ka ji me na ce kuwa? Ku je da Ɗayyabu ku sake dubo..."

Ƙiran da ya shigo wayarta ne ya yi silar katsewar maganar da take.

Ba yadda ta iya, dole yanzu ta ɗaga wayar tasa.

Sai da ta tattaro duk wata natsuwarta kafin ta ɗaga, gudun kada ya fahimci wani abun daga gareta. A daidai lokacin da suke jimamin ɓatan 'yarsa.

Bayan gaisuwa ba tare da ya jira komai ba, ya fara wassafomata bayani da yadda suka yi da Yayan nasa, da kuma yadda lamarin zai shafi Ahalinsu.

Sosai ta fahimce shi, ta kuma basa haƙuri, ta sanar da shi cewar, za ta dawo yau, yanzu haka ma shiryawa take.

Daɗi ne ya rufesa, nan ya shiga yi mata godiya, da fatan isowarta lafiya ya datse ƙiran, ya nufi cikin gari, yana mai farin ciki.

"Ku je ko? Allah yasa a d..."
Turo ƙofa da shigowar Abulle ne ya yi sanadin tsaida maganar tata, ba tare da ta kai aya ba.

Duk suka juya, ganin Abullen ce ya sa suka ɗunguma gareta, har suna rige-rigen isa gareta.

Wani irin razana da faɗuwar gaba ne ya ziyarceta a lokacin da ta buɗo ƙofar ta yi tozali da mutanen gidan, tsaye cirko-cirko a harabar gidan.

Ba don sun ganta ba, da juyawa za ta yi ta gudu, ta yafe ɗaukar hotunan da ya dawo da ita.

_Ummyn Yusrah_
[11/25, 8:20 AM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

   _Ummyn Yusrah_

_Ashe haka Abulle ta yi kasuwa? Ina tayata murna, ta ce a yi ma duk mai bibiyarta godiya, a kuma ƙara haƙuri da ita na rashin ganinta a kan lokaci._

_Maman Nour, Beauty Queen, Abu Hisham, Yayana. Taku gaisuwa da godiyar daban ce, har kullum Abulle ba za ta taɓa gajiyawa wajen miƙo saƙon godiyarta gareku ba, koda kuwa za ta cinye shafin nan ne, sai dai za ta taƙaita saboda masoyanta. Amma tabbas tana tare da ku a kodayaushe, tana kuma jin daɗin kwament ɗinku. Mun gode ni da ita. Saura in ji ance kalan dangi.😏 sins shis ma kozin sista ehe!_

_40_

Har wajen da take suka ƙaraso, suna tambayarta ina ta je. Ba ta basu amsa ba, sai da Mommy ta sake tambayarta,
"Zainab ina kika je? Duk kin tashi hankalinmu."

Hawayen da ke shirin gangarowa kan ƙuncinta ta goge, ta ce
"Gida zan tafi."

Duk suka kalleta, Afreen ya ce,
"Gida? Kin san hanya ne? Kina da kuɗin mota ne?"

Kai ta gyaɗa, Mommy ta riƙota,
"Zo mu je, yanzu Tukur zai zo ya kaiki dama. Alhaji ya mayar wajen aiki, ki yi sauri ki shirya maza kafin ya iso."

Da murna ta shiga ɗaki, jakar kayanta ta ɗauko, ta dawo falo wajen su Mommy da ke tattaunawa ita da Afreen. Lubna kam sai ido, don ko da Abulle ta dawo ma ba ta tanka mata ba.

Mommy ta kalleta ta ce,
"Yau sai gida ko?"

Dariya ta yi, ta gyaɗa kai.
"Muma goben muna hanya In Sha Allahu, idan an je a gaida mutanen gidan."
"To!" ta ce, don ɗokima ba zai iya barinta ta yi dogon magana ba.

"Afreen duba Tukur ɗin, idan ya iso yazo ya fita da kayan su tafi ka da su yi dare a hanya."

Jiki a sanyaye ya fita, ba jimawa ya dawo,
"Ta fito, ya iso, motar tana bakin get."

Da sauri ta suri jakarta.
Afreen ya ce,
"Ohh! Wannan saurin fa? Kamar kin gaji da mu?"
Dariya ta yi, Mommy ta ba ta saƙon kuɗin da Daddy ya bada, ta yi mata addu'a da fatan alkairi, itama ta yi godiya suka fita.

Suna tsaye a jikin mota ya kalleta ya ce,
"I miss You!"
"Almisyu?" Ta tambayesa,
"Yeah! I really miss you."

Kallon rashin fahimta ta yi masa, ganin hakan ya sa ya fahimci ba ta gane abinda yake nufi ba.

"Cewa na yi, idan kika tafi zanyi kewarki sosai."

Murmushi ta yi,
"To, ka zo mu tafi mana."
"Na so hakan, sai dai ina da uzuri. Amma zamu zo da su Mommy gobe ko jibi aure."

Jin an ambaci aure, ya sa yanayinta ya canza, ƙirjinta ya shiga bugawa. Haka kawai ta ji sam ba ta son auren nan, tana son komawa Mai Ludaya ne don ta ga Hamusu da mutanen cikinta ba don ayi aurenta da Mai Unguwa ba.

Kallonta ya yi cikin kulawa, ya ɗaga mata gira ya ce,
"Ya aka yi? Ko a fasa tafiyar ne?"

Kai ta girgiza ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ma hawayen da take gogewa.

"Kukan fa? Barin je in faɗa ma Mommy a fasa tafiyar kawai."

Ya juya zai tafi, da sauri ta riƙo rigarsa ta ce,

"Don Allah Yaya Afreen ka yi haƙuri! Na daina."

Juyowa ya yi,
"To, me ya sa ki kuka?"
"Nima ban sani ba, kawai dai bana jin daɗi ne."
"To, ki daina kuka, ki yi ta karanta Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Za ki ji daidai."

Kai ta gyaɗa ta ce,
"Na gode."

Hira suka ci gaba da yi, har Tukur ya fito da kaya ya sa a but, ya shiga gaban motar.

Suna sallama da Afreen ne Lubna ta fito, jikinta ya yi sanyi, duk ta ji ba daɗi, haka kawai ta ji ba ta son tafiyar Abulle.

Kusa da su ta iso tana faɗin,
"Da gaske tafiya za ki yi?"

Kallonta ta yi, ta keɓe baki, zuciyarta na faɗin
'Ji wani kinibibi! Ko meye damuwarta da tafiyata?'

A fili kuma ta ce,
"Eh, zan koma ƙauyenmu inda nafi wayo, inda aka san kimata da darajata."

Duk sai ta ji ba daɗi, da kalaman Abullen.
Hannayenta duka biyu ta riƙo, tana murmushi ta ce,
"Ki yi haƙuri."
"Allah ya kara mana duka."
"Me fa?"
"Haƙurin."
Duk suka sa dariya

Lubna ta ce,
"Zamu zo, jibi. Me za a ajiye ma..."
"Tsareta kuka yi ashe? Sai ta rasa mashin ko?"

Mommy ta katse Lubna, daga maganar da take yi lokacin da ta fito.

Juyowa suka yi su duka, za su yi magana, Mommy ta ce,
"Shiga ku tafi, so suke ki rasa mashin ɗin da zai ƙarasa dake ko?"

Jin zancen rasa mashin ya sa ta daka tsalle ta shige cikin motar.

Duk suka sa mata dariya, Afreen ya rufe ƙofar ya leƙo ta taga, ya ce,

"Allah ya kai ku lafiya, sai mun zo."
"Amin."

Ta amsa ya matsa ya rufo ƙofar. Motarsu ta ɗaga. Hannu suke ɗaga mata, itama haka har tana leƙowa ta taga. Sai da motar ta ɓace ma ganinsu kafin suka juya cikin gida zukatansu cike da kewa da rashin jin daɗin tafiyarta .

_Ummyn Yusrah_
[11/25, 2:25 PM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

   _Ummyn Yusrah_

_Tsangayawa kuma ga naku. Tsangayar Marubuta da ke Fuskanr littafi (Facebook). Ina godiya, ga kyautar shafi gareku musamman Umman Maryam. Na gode._

_41_

Koda Malam Ilu ya isa gida bai iya shiga ba, don a cike yake da mata, sai kai kawo ake, ga wasu manyan tukwanen girki da aka ɗaurasu kan murhu.

A zauren gidan ya tsaya, ya tura aka yi ƙiran Inno.

Da sauri ta nufo wajen har tana tuntuɓe, don tunda ya fita hankalinta ke tashe.

"Malam ya ya kuka yi?"
Ta faɗa lokacin da ta iso, idanunta akan fuskarsa.

Kallonta ya yi, lokaci ɗaya duk ta canza, hakan kuma ba zai rasa nasaba da zancen rashin dawowar Abulle da ya yi mata ɗazu ba. Da shima ya tafi da taraddadi.

"Malam an dace kuwa?" Ta sake tambayarsa.

Dogon numfashi ya ja.
"Eh, mun yi magana da Hajiyar tana hanya."

Itama numfashin ta ja, na jin daɗi,
"Alhamdulillah! Yanzu hankali ya kwanta."
"Suma goben za su iso, a gyara musu ɗakin da Muntari yake kwana ko?"
"To, Allah ya kai mu, ita kuma Allah ya dawo da ita lafiya."
"Amin, barin fita."
"To, a dawo lafiya."

Ya fita, itama ta koma bakin aiki.

****

Gudu kawai yake shararawa, domin yana sauƙeta zai juyo, rediyo ne ke ta aiki, Abulle kuma ta afka kogin tunanin yadda za ta je ta sami Hamusunta har barci ya ɗauketa.

"Hajiya Zainabu! Mun iso."
Tukur direba ya faɗa lokacin da suka iso tashar garin Guwal, anan ne ake hawa mashin ɗin da zai kai mutum Mai Ludaya, don mota ba ta shiga.

Miƙa ta yi, fuskarta na bayyanar da farin ciki. Gari ɗaya za ta wuce yanzu ta isa garinsu.

Tafiyar kwana uku,

Please Login or Register in order to submit comment