Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa ko kaɗan ma ba su da wani ƙiba, wannan kyakykyawar iska aka yi zai iya awon gaba da su.

Juyowa ta yi ta ci gaba da cin abincinta, tana mamakin yawan abincin da aka ajiye ba masu ci.

Wannan kam almubazzaranci ne. Wataƙila don ba su san wahalar noma ba ne shi ya sa suke haka.

Tattaro sauran sayyayyen dankali da ƙwan da ya rage akan farantin ta yi, ta haɗe waje guda ta dunƙule ta kai baki, tana tauna daɗi na shigarta.

Bakinta cike, ta ce,

"U'uhum! Garin daɗi na nesa, wani ya zo Jinjin bai ga moto ba. Su Inno ana can ana gwagwarmaya da ɗumame."

Ta kurɓi ruwan shayin.

Ba ta bar wajen ba, sai da ta tabbatar da cikinta ya gama cika gaba da baya.

Juyi kawai ta ke yi a kujerar falon, tun tana iya zama har ta gaji ta kwanta, gashi kwanciyar ma duk ya isheta.

Wannan wani irin gida ne haka? Ba fita ba aikin komai, duk jikin mutum ya yi ta ciwo. Sai aikin zuba ma kwalba ido kana ganin masu jajayen kunnuwa na ta gwalaɓen magana.

Tsaki ta ja, Lubna da ke zaune kan kujera tana danne-danne a waya ta ɗago ta kalleta ta sake mai da kai ga waya.

Ba tare da ta ɗago ba, ta ce'

"Ke! Ki ɗauko min ruwa a firij."

Waiga-waige ta shiga yi, ba ta ga kowa ba. Kenan ma da ita, ita ce Ke!

Lallai wannan rainin hankalinta ya wuce inda take tsammani.

Juyawa ta yi ta bata baya.

"Wai ba ki ji me na ce ba ne?"

Ta yi tambayar.

Shiru ba amsa.

"Zainab! Wani salon iskanci ne haka? Ina yi miki magana, kin yi banza da ni."

Jin ta ƙira sunanta yasa ta juyowa tana faɗin,

"Ji nayi kin ce ke! A iya sanina Inno da Baffa Zenabe Abu suka raɗamin wanda wasu ke ƙirana da, Abuwa, Abulle. A garin Jinjin kuma Zenabu, kinga ko ai ba lallai in san da ni ki ke yi ba."

Kallon mamaki ta bita da shi. Lallai yarinyar nan bata da kunya.

"Idan ba da ke nake yi ba, da wa nake yi? Za ki tashi ko sai na ɓaɓɓallaki."

Kallon sama da ƙasa ta yi mata, ta ƙare mata kallo tsaf!

'Wai ɓallawa? Allah na tuba ai ko dusa nake ci wuce nan. Yasin damƙa ɗaya na yi miki sai kin gane kurenki. Renon dawa ce ni.'

A fili kuma ta ce,

"Zan karɓo miki da gudu ma."

Ta miƙe ta bar falon.

****

Inna Talle da 'yan uwanta sun yi cigiyar Hamusu har sun fara gajiya ba labarinshi.

Yau kwana biyar kenan da tafiyarshi.

Tun tana kukan fili har ta dawo na zuci.

An shaida mata ya tafi garin Jinjin, lokacin da ta sa a yi mata cigiya a tasha.

Duk wanda ta ji zai je garin Jinjin, saƙonta baya wuce a sanar ma Hamusu ya dawo gida.

Duk wanda ya dawo, ce mata yake bai ganshi ba.

Sosai ta tashi hankalinta, lokaci guda duk ta zabge ta fita hayyacinta.

Ganin halin da take ciki ne, yasa Wani ƙaninta Garbati ya tafi da ita garinsu Ɗan kurma.

Ƙauye ne sosai, ga ƙauyanci har ya fi na Mai Ludaya.

Tafiyar awa goma za ka yi daga Mai Ludaya, zuwa Ɗan kurma.

Su Inno shirye-shirye ake ta yi, ba ji ba gani. Haka ma gidan Mai Unguwa ana ta shirin tarbar sabuwar amarya.

Yayin da galibin 'ya'ya da jikokin Mai Unguwa ke ji kamar su kamashi da ranshi su jefashi cikin tukunya, su gangama mai wuta ya mutu ko su cakuɗa mishi abincinshi da shinkafar ɓera ya mutu kowa ma ya huta.

A fadar Mai Unguwa ma, tawagar ta kasu biyu.

Tawagar da ta fi rinjaye, suna tawagar ƙin auren Abulle da Mai Unguwan, tawagar amincewa kuwa! Ba su fi a ƙirga ba.

***

A hankali take tafiya a kan simintin bature, gudun kaiwa kasa irin na ɗazu, har ta isa ƙofar ɗakin.

Buga ƙofar ta shiga yi.

Daga ciki aka tambaya da waye?

"Nice Abulle."

Tasowa ya yi ya buɗe ƙofar.

"Yaya ne?"

Ya tambayeta.

"Cewa aka yi in karɓo ruwan sha a wajenka."

Kallon rashin fahimta ya yi mata,

"Ruwa a wajena kuma? Duk gidan nan ace ba ruwa sai an aiko ki wajena? Waye a aikoki?"

Taɓe baki ta yi itama, tana tunanin kinibibi irin na waccar mai kama da takardar. Ace duk ruwan gidan ya gagareta sha, a na wajen Afirij!

"Uhmmm! Nima shi nagani. Akwai ruwa a gidan amma wai in karɓo mata a wajenka."

Tsaki ya yi, ya ce

"Wai waye ne?"

"Labano mana?"

"Labano kuma? Waye haka?"

Ya yi tambayar cikin rashin fahimta.

Kallon rashin fahimta itama ta yi mishi.

"Labano ta gidan nan mana. Ko akwai wata ne."

Dariya ne ya kufce mishi, da ya gane ashe Lubna take nufi.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*


*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*


_Ummyn Yusrah_

_Ku yi haƙuri da jina shiru, zazzaɓi ya riƙe ni. Amma sauƙi sosai, masu yi mini addu ar samun sauƙi ina godiya._

_Masu yi min magana ba amsa a private ko cikin group ba amsa ku yi hakuri don Allah, na ɗan yi fama da matsalar network ne._


_Afwan! Sunan garin su Inna Talle Kurmawa ba ɗan kurma ba._

_23_

Dariya yake ta ƙyaƙyatawa, ita kuwa ta gama ƙuluwa, haushi duk ya cikata. Ba abin da ta tsana kamar a tasata gaba ai ta doka dariya ba dalili.

Juyawa ta yi cikin fushi zata tafi, da sauri ya biyota yana ƙiranta.

"Zainab!"

Tsayawa ta yi kafin ta juyo, fuskarta a haɗe.

"Meye?"

"Yi haƙuri! Da fari ban fahimci wa kike nufi ba."
Keɓe baki ta yi, irin kai ka sani ɗin nan.

"Je ki, ki ce mata zan kawo mata kin ji."

Juyawa ta yi ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta bashi amsa ba.

Ganin ta shigo ba ruwa a hannunta yasa ta tambaya.
"Ina ruwan da nace ki ɗauko min?"
"Ya ce in je zai kawo."
Kallon rashin fahimta ta yi mata.
"Shi wa?"
"A firij!"

Tsaki ta ja sannan ta ce,
"Kin taɓa ganin Fridge ya yi ƙafa ne? Ko kuma ya yi baki da har zai ce miki jeki zan kawo?"

Kallonta ta yi, ta ce

"Dama A Firij ɗin kurma ne? Naga kullum yana magan..."

Kafin ta ƙarasa maganar sai gashi ya shigo, yana faɗin.

"Aunty Labano ga ruwan."

"Yauwa, gashi nan ma kin ji yana magana." Cewar Abulle

Yamutsa fuska ta yi,
"Meye kuma wani Labano?"

"Ba ki san Labano ba?"
Ya tambayeta lokacin da ya ke zama kan kujerar.

"Ban sani ba."
"Sabon sunanki ne da Zainab ta raɗa miki yau." Tsaki ta ja cikin jin haushi.
Harara ta galla ma Abulle, tana faɗin,

"Wannan bata da saiti, don iskanci sunan nawa ne zata ƙira da sunan wani ƙasa." Dariya shikam ya sake kwashewa da shi.

"Ke kin cika masifa wallahi, yarinyar da bata iya ba, don ta kuskure ai gyara za a yi mata ba wai a yi mata masifa ba."

"Koma dai meye ku kuka sani. Dallah ni bani ruwana."

Ta faɗa tana faucewa.

'Kya ji da shi dai masifatu, Allah yaso gobe ma zan bar muku gidan ki ci kanki. Cewar Abulle ta juya ta fita.

"Wai gurinka ta je karɓar ruwan ne?"
"Dama ba wajena kika aikota ba?"
"Duk ruwan da ke gidan nan in kasa sha sa sha sai na wajenka? A Fridge fa nace ta ɗauki min."
"To, ai wajen a Firij ɗin ta je karɓo miki."
"Ban gane ba?"
"Suna na ne fa A Firij ɗin wai."

Dariya ta sa, shima ya tayata, kowa yana ƙiran sabon sunan kowa.

Bakin get ta nufa wajen Ɗayyabu mai gadi.

Yana hangota ya wangale baki yana dariya don yasan yau, zai sha labarin Mai Ludaya har ya ƙoshi.

"Abulle! Abulle! Abulle mutan Mai Ludaya. Sai kuma gaki a Jinjin."

Ya faɗa yana tura mata farar kujerar roba.

Bayan ta zauna ya ce,

"Yaya kika ji Jinjin ɗin?"
"Ba daɗi."
Zaro ido ya yi,
"Ba daɗi kuma? Birni ne fa!"

"To, ina daɗi anan don Allah? An jibge mutum waje guda kamar kayan wanki, daga barci sai kafa ma kwalba ido."

Dariya ya yi,
"Wato dai kin fi gane ki yi ta jeka ka dawo ko?"
"Iy mana! Zama waje ɗaya ai haɗari ne."
"Gaskiya kam, musamman ma ga wanda bai saba ba."
"A, to. Ni waje ma nake son leƙawa."
"A yi haka kuwa? Ke da kike baƙuwa idan na barki kika fita ai ba kanta."
"Yasin ba nisan zan ba, yanzu zan dawo."
"To, ai rana ya yi, ki bari zuwa anjima yanzu za a yi sallar azahar ne."
"Dan Allah Baba Ɗayyabu ka bari na leƙa, yanzu zan dawo."

Jin ta girmamashi yasa ya ce,

"To, iyakarki bakin layin nan, yanzu ki dawo."
"Yauware, Na gode."

Ƙaramin ƙofar da ke jikin jet ɗin ya buɗe mata, har waje ya fito ya nuna mata hanyar ƙarshen layin, tana zuwa kuma ta juyo ta dawo.

Godiya ta yi, ta ɗau hanya.

Sunkuyawa ta yi, ta tsinci duwatsu, tana tafe tana ciccilasu sama.

Ta zo wucewa wajen wani masallaci dake jikin wani gida taga wani mai saida gauta, a tsugunne. Har ta wuce sai kuma ta dawo.

"Malam nawa kahin gautar?"

"Hansin da ta dari."

Ta nuna ɗaya tiren da ba mai ita,

"Su kuma wa innan ɗin fa?"

"Duk kuɗinsu ɗaya, mai ita ya zaga makewayi ne, yanzu zai fito amma."

"Ni na naira Ahirin nake so."

Ta kwanto a bakin zaninta.

"To, kawo mana sai in ɗiba miki, da gani ai kema tamu ce daga gida kike."

Dariya ta yi, ta ce

"Kai ma ɗan Mai Ludaya ɗin ne?"

"A'a, a Bugawa nake."

"Taɓ! Ban taɓa ji ba."

"Nima ban taɓa jin naku ba."

Ya faɗa lokacin da yake miƙa mata.

Sai da ta ƙirga, ta ce

"Ƙwara fa huɗu ne?"

"Iy!"

"Taɓ! Can kam sai dai mu je mu tsinko, nan kuma ɗan wannan wai Ahirin hu um!"

Ta faɗa tana tafiya.

Tana barin wajen sai ga Hamusu ya fito daga magewayi.
"Ai kawai mu yi alwala kawai mu yi sallah sai mu wuce."

Cewar Hamusu.

"Kawai ba."

Abokin tafiyar tashi ya bashi amsa.


A yi haƙuri da kura-kuran ciki, ban bibiyaba.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_

_24_

Tana tafe tana cin gautarta har ta isa bakin hanya, sai da ta tsaya ta kalli motoci da babura masu wucewa sannan ta juyo. Ci gaba da wurga duwatsunta sama ta yi tana cafkewa.

Wani gini ta hango da aka fara ba a gama ba aka mai dashi wajen zuba shara. Hango kwalayen sabulai da robobin mai da kwalaben turaruka da ta yi kan bolan yasa ta nufi wajen. Leda ta nema babba ta karkaɗe, Allah ya taimaketa bai yage sosai ba, ta hau tsintar kwalayen sabulu mai hoton mata da robobin mai da kwalaben turaren da basu fashe ba. A ranta tana hango yanda zata jeresu a cikin kwabet ɗinta.

Ta tsinci na tsinta ta bar na bari, ta ɗauko ta nufo hanyar gida.

"Lahhhh! Mai gauta har yanzu kana nan?"
Ta faɗa lokacin da ta zo giftawa wajenshi a ƙofar wani gida.

"Iy, wallahi. Mai gidan nan ne ya ce mu zo mu zubar mai da hyara, ɗan uwana ya shiga ciki zai ɗauko."

"Lahhhh! Aiko zan jirashi ko zan sam wasu kwalayen."

"Yanzu zai fito kuwa."

Suna tsaye sai ga Ɗayyabu da saurinshi.

"Abulle! Zo yanzu Alhaji ya dawo sallah yake tambayar ina kike na ce kin fita sai faɗa yake, me ya sa na barki ki ka fita."

"Allah sarki Baba Ɗayyabu! Yanzu fa zan dawo. So nake a fito da sharar gidan nan sai in ƙara wasu. Kagama wanda na samu a wancan jujin."
Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe ledar shirgin.

"Taho mu tafi, ki zubar da wannan sharar don ba yarda za a yi ki shiga da shi gida ba."

"Abunfa jeren ɗaki ne."

Ta faɗa tana zaro ido.

"Mu je, nan ai su basu amfani da shi. Ana gamawa da shi sai bola."

Ya faɗa lokacin da ya tasa ƙeyarta.

"Hu umm! Nikam ina so, zan ajiye a wajenka, gobe idan zan tafi sai in ɗau abuna. Har Sarai ma zan ɗibar ma wasu itama ta jera a ɗakinta tunda ta kusa aure itama."

"Oh! Mutanenmu akwai son jere. Har yanzu dai ba a barta ba?"

"Tana nan, ku ai nan sai dai ku aje ƙaton kwalba da kujeru muko cika ɗaki ake da jere mai kyau."

"Ci gaba ai aka samu."

Ta taɓe baki

"Amma dai anjima zaka barni na dawo na sake ɗiban wasu ko?"

Zaro ido ya yi,

"Rufamin asiri, so kike Alhaji ya sallame ni a aiki."

"A'a."

"To, ki haƙura da wanda kika samu."

Suna shiga ta ɓoye a cikin wani ɗan lungu da ke gefen ɗakin Ɗayyabu, ta nufi cikin gida.

Duk a falo ta samesu zaune kan kujera.

"A'a! Ɗiyata har kin fara gane gari ne kika fita yawo?"

Alhaji ya faɗa yana miƙo mata hannu.

Zama ta yi a ƙasa can nesa ta ce,

"Gajiya na yi da zaman shine na fita."

"Nan ai ɓata za ki yi, zuwa yamma yayanki zai fita da ke sai kiga gari ko?"

Da murna ta ce,

"To, Baffa!"

"Ɗan gidan wanene angon ne? Na manta ban tambayi Ilu ba."

Sunkuyar da kainta ƙasa ta yi, ta kamo bakin mayafinta rufe rabin fuskarta sannan ta ɗago fuskar ta buɗe ido ɗaya ta ce,

"Mai Unguwar yankinmu ne."

Ta ƙarashe faɗa cikin jin kunya, ta duƙar da kai.

Dariya suka sanya, Hajiya Sabuwa ta ce,

"Da alama ana ji da maigidan nan! Wannan irin jin kunya haka?"

Ta kaɗa kai ba tare da ta sake dagowa ba.

Alhaji ya sake tambayarta.
"Wani yaro ne ɗaya daga cikin gidan? Ko cikin jikokin gidan ne?"

Ɗagowa ta yi, fuskarta na nuna alamar rashin jin daɗin tambayar, har da 'yar ƙaramar harararta.

"Mai Unguwa fa nace Baffa!"
Gyara zama ya yi sosai don bai fahimci wani Mai Unguwar take nufi ba.

"Mai Unguwar Yankin mai Ludaya ƙarama kike nufi kokuma yaronshi da ake cema Mai Unguwa?"

Kaɗa kai ta yi ba tare da ta bashi amsa ba.

"Ban fahimta ba, ki buɗe baki ki yi min bayani."

"Baba Mai Unguwa Rabi..."

Bata kai ga karasawa ba, ta miƙe a guje ta yi ɗaki.

Hannu ya shiga tafawa yana salati yana sanar da Ubangiji.

Su kuma yaran sai dariyar Abullen suke yi.

"Alhaji lafiya kake ta jero salati?"
Hajiya Sabuwa ta tambayeshi

"Ina fa lafiya?"
"Me ya faru?"
"Ban taɓa sanin cewar Ilu baya da hankali ba sai yanzu. Kin san wa zai aura ma yarinyar nan kuwa?"

Girgizar kai ta yi, kafin ta amsa

"A'a."

Tsaki ya ja cikin ɓacin rai kafin ya ce,

"Tsoho ne fa da ya kusa ba shekaru ɗari baya."

Kirji ta buga ta ce,
"Mun shiga uku! Shi ko Ilu me ya yi mishi daɗi haka da zai ɗau 'yar jaririyar 'ya ya ba wannan tsoho?"

"Rashin tunani da rashin hankali mana."
"Gaskiya Alhaji gara tun wuri asan abun yi. Ni kam da haƙura aka yi da auren nan ta yi zamanta anan, a sama mata makaranta."
"Hakan ma za a yi, ba sai sun ga ƙafarta a goben bama."
"A, to. Ai wannan abu da cutarwa. Duka-duka Zainab ɗin nawa take da har za a yi mata aure?"
"Kin san mutanenmu ai, yanzu idan kin je can ma za ki samu ana ƙorafin girmanta."


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_


_25_

"Lallai akwai su da yi ma yaro auren wuri."
   "Ai ba auren wurin ne ma damuwa ba, da ya zaɓa mata tsaranta ai ba damuwa. Amma a ce  ya ɗauki yarinya ya danƙata hannu tsoho ai abun bai yi ba."
   "Kuma fa kaga ita yarinyar kamar tana son shi, ji wani sunne kai da take ta yi ita a dole kunyar nan."
    "Koma menene ita dai ta sani na riga na gama magana."

Ya kalli Afreen ya ce,
"Anjima ka kaita taga gari, kasan su basu saba zama waje ɗaya ba, tanan za a ɗauke hankalinta."

"To, Daddy! Amma ka faɗa ma Labano ta daina kyararta."

Hajiya ta ce,
"Waye kuma Labano?"
Dariya yake yana nuna Lubna da hannu
"Wai Lubnan ce ta dawo Labano? Wannan suna daga ina kuma?"

"Daga wajen Zainab, wannan ai kafin ta saitu sai ansha fama. Daddy wai kai ma haka ka yi ne farkon zuwanka Jinjin?"

Filon dake kan kujera ya ɗauka ya jifeshi da shi yana faɗin,

"Ka ci gidanku! Kana raina mana 'yan gari ko? Can zan kai ku ku yi wata ɗaya ku saba da 'yan uwa."

Afreen har da murnarshi

"Eh, wallahi Daddy ina son zuwa ƙauye."

Labano kuwa yamutsa fuska ta yi, ta turo baki tana faɗin

"Daddy har wata ɗaya? Ni dai ba za ni ba. Sai dai ko Afirij."

Duk suka sa dariya, Hajiya ta kalli Alhaji

"Ni ko Lubna za a ba Mai Unguwar tunda ta girmi Zainab ɗin?"

Kwaɓe fuska ta yi, kamar zata yi kuka, ta ce

"Mommy!"

Sai kuma ta miƙe ta nufi hanyar ɗaki.

Afreen da ke ta kwasar dariya harda kwanciya kan kujera ya ce,

"Labano ta Mai Unguwa! Kuma fa za su dace sosai Mommy."

Juyowa ta yi, ta jefomishi remote ɗin tibin da ke hannunta.

"Wayyo Allah matar Mai Unguwa zata yi min illah."

Ya sake ƙular da ita, Daddy ya ce

"Ya isheka, zo abunki 'yar Daddy ba mai yi miki wannan aikin ina raye."

Da gudu ta shige ɗaki abunta.

"Sai ki je ki rarrasheta, kin santa ai idan ta kumbura sai an nemi allurar da za a soka mata ta sace."

"Ai Lubna ban san wace irin yarinya ba ce, bata son mutane ko kaɗan ga ta da ƙin 'yan ƙauye, ko don ba ta zuwa ne yasa hakan?"

"Zata daina ne, yanzu duk lokacin da aka yi hutu zan riƙa kai su akai-akai."

"Gaskiya ya kamata kam."

Ta kalli Afreen da tun ɗazu ke kwasar dariya ta ce,

"Kai kuma abun na ya samu ko? Ba a taɓa ganin dauriyarka sai ta ɓaci. Tashi ka je ka shirya idan zaku fita ku sauƙeni gidan Suwaiba in dubata da jaririyarta."

Ciki ya shige ya bar su suna ci gaba da tattaunawa.

Sai ƙarfe uku aka gama abincin rana, lokacin duk yunya ya addabi Abulle, tun tana shan ruwa yana riƙe mata ciki har ya dawo da ta sha jimawa sai banɗaki.

****

"Daga ɗauko shara ka je ka zauna, wata yarinya ta yi ta jiran zuwanka zai ta tsinci kwalin sabulu ta yi jere baka fito ba."

"Bari kawai Ɗalliti, na yi zaton sharan kaɗan ne ashe da yawa, na yi tunanin in ce ka shigo sai naga gara ka zauna ko za mu sami masu saye kada mu ɓata lokaci a waje ɗaya mu zo kuma bamu sami komai ba."

"Gaskiya! Kuma ka yi farar dabara don ina nan mutane biyu ma sun zo sun saya."

"Kaga ai da yanzu ciniki ya wuceemu, don ma naga layin nan ba ba irin layin masu sayen gauta bane."

"Yo, Hamisu gautar abinci ne da mutane zasu yi ta jidarshi? Ina jibi idan na tafi gida in zan dawo zan nimo wasu 'yan kuɗaɗen in sake jarraba wani sana ar."

"Allah ya kai mu. Barin kai wannan ɗin idan na dawo sai ka shiga kaima ka ɗebo."

"To, ba damuwa."

Ya tura baron zuwa wajen da ake tara shara.

"Na yi tunanin fa kai zaka zaga da gautarnan, ni sai in ƙarasa kwashe sharar kawai."

Hamisu ya faɗa ma abokinshi lokacin da ya dawo daga kai shara.

"Allah ko? To inaga kuma za a yi fa! Kada mu taru mu zauna waje ɗaya."

Ya faɗa lokacin da ya ɗaura tirenshi a kai, ya miƙo hannunshi Hamisu ya ɗoramishi nashi tiren.

Har ya yi gaba ya juyo ya ce,

"Idan ka gama kawai mu haɗu wajen Goshi mai abinci."

"To, ba damuwa."

*Ummyn Yusrah*

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_Ina taya Haziƙan Marubuta murnar kammala littafinsu, mai suna TA FI BAGARUWA IYA JIMA. Zeety, Ummyn Yusra, Beauty Queen. Allah ya kara hazaƙa ya ƙaro kaifin ƙwaƙwalwa._

_Ruƙaiya Haroun (Maman Nour) ina tayaki murnar kammala littafinki mai suna RUƊANIN RAYUWA (Ƙalubalenmu a yau) Allah ya kara hazaƙa da fikra._

_26_

Bayan sun ci abinci, sun yi sallar la asar ne, Abulle ta je ta tsalo wanka. Kwalliya sosai ta yi cikin atamfarta riga da zani da ɗankwali mai kalar koriya da ruwan ɗorawa.

Ta shafe fuskarta da fauda, ta ɗauko ƙwalli ta yi ɗigo uku a saman goshinta, biyu a ƙasa ɗaya a sama. Haka ta yi a gefen kumatunta na hagu da dama da kuma ƙasan haɓarta.

Ta sanya jan jambaki a leɓenta ta sa kwalli a cikin idanunta. Sabon silifas ɗinta mai soso ta sa ta sanya hijabinta, sai gata ta fito cas! Kamar ranar sallah.

Ta fi minti goma tana kallon madubi, tana ƙare ma kanta kallo, domin ita kanta ta san yau ta yi kyau! Idan ta juya furkarta gefe ta yi fari da idonta, sai ta sake juyawa ɗaya gefen ta sake fari da idanun. Tana yi kuma tana murmusawa.

"Na shiga uku! Wannan wani irin hauka ne? Kin gama ƙwaɓa fuskarki wai ke kin yi ado, kuma kina nufin a haka za ki bimu? Gara ma ki koma banɗaki ki je ki wanke fuskar nan wallahi idan ba haka ba sai dai ki zauna." Lubna ta faɗa lokacin da ta fito daga wanka.

Kallo ta yi mata, irin mai nuna amar kin taƙura min ɗin nan, 'Ba ke aka ce ki fita da ni ba, kama albarkacin Hajiya ne ta ce ki shirya ku je gidan barkar haihuwa.'

"Afirij zan bi ai! Ke kuma Hajiya za ki bi."

Ɗagowa ta yi daga shafa man da ta fara, ta yi mata kallo na sakan biyu, kafin ta ce,

"Owo! Shine baza ki goge fuskar ba kenan? Ki barshi to don Allah, zamu ga wa za ki bi. Mara kunya kawai. Ana magana kina ba mutane amsa."

Cike da haushi ta nufi bayan gidan ta wanke fuskarta. Tana fitowa ta nufi hanyar fita.

"Zo nan."

Lubna ta ce da ita, har ta kara gaba sai kuma ta juyo ta dawo.

Kaya ta miƙo mata ta ce,

"Ki cire na jikinki, ki sa wannan."

Murmushin takaici ta yi, zuciyarta na faɗin

'A rashin sani, baƙo ya sha ruwan wanka. Ki bi a hankali, idan na bauɗe sai kin raina kanki Labano, sai kin san Abullen Inno ba baya bane.'

Karɓar kayan ta yi, ta cire nata ta sa. Doguwar riga ne, da ɗan mayafinshi. Ta rasa yadda zata yi da mayafin, don santsi ne da shi, kawai sai ta tattaro ta ɗaure a wuya. Ta yi waje.

****

"Kai! Na aikatu sosai yau, amma na fanshe gumina fa."

Hamisu ya faɗa lokacin da suke zaune a ƙarƙashin biya.

"Gaskiya kam! Nima da na gama zagawa, na je gurin Goshi na ci abinci na jima sosai a wajen kafin ka zo."

"Bari ka gani Ɗalliti!"

Ya faɗa yana ciro kuɗin da ke cikin aljihun rigarshi.

"Ka gansu."

Ya nuna mishi ɗari biyar-biyar guda uku.

"Dubu ɗaya da ɗari biyar ya bani, da abinci mai yawa. Ya kuma ce duk bayan kwana biyu in rinƙa zuwa ina zubar da shara da share musu harabar gidan sabida furannin da ke zuba." Ya kare maganar yana kunce wani baƙin leda da ya taho da shi.

"Ga naka abincin, ni na ci na ƙoshi a can."

"Kai mutumina!"
Cewar Ɗalliti, lokacin da yake miƙa ma Hamisu hannu suka tafa, fuskarshi cike da annuri ya ci gaba da faɗin.

"Ka ce dai mun shiga wannan layin a sa a?"
"Ba laifi, mun taki babbar sa a. Ya kasuwar taka?"
"Ba laifi, na ɗan taɓa ciniki."
"Mun gode Allah!"
Janyo ledar abincin ya yi, ya wurga wani ƙaton yankin nama a bakinshi, sannan ya ce,
"Niko Hamisu me zai hana mu kama ɗaki a gidan Malam Bukar, zai fi mana sauƙi da kwanan ƙofar shagunan mutane ko cikin rumfar kasuwa ko? Kaga kullum Da u, cikin kai mana hari suke, sai ka yi nisa cikin barci wani ƙaton ya mirginaka ya kwashe abunda da wuni kana nema."

Ajiyar zuciya Hamisu ya yi, da godiya ga Allah da ya haɗashi da abokin ƙwarai, mai son ci gabanshi. Bai da ƙyashi ko hassada.

"Kuma fa ka kawo shawara mai kyau wallahi. Amma kana ga zamu iya biyan kuɗin?"

"In Allah ya yarda zamu iya. Dubu huɗu ne fa a wata guda, kasan ɗakunan ba wani fasali ne da su ba."

Dariya Hamisu ya yi, ya ce,
"Allah na tuba! Wa ke duba wani fasali Ɗanliti? In dai asiri ya rufu ai shi ke nan."

"Haka ne kuma."

Ya faɗa yana ciro kuɗi daga cikin ramin zariyar wandonshi.

"Ga dubu biyu nan, ka kawo na wajenka mu haɗa sai ya bimu bashin ɗari biyar ko?"

"Kawo dubu guda a wajenka ka gani."

Ya karɓa, ya haɗa da na aikinshi, ya ciro wata tsohuwar dubu ɗaya a ramin zariyar shi shima ya haɗa.

"Kaga sun cika dubu uku da ɗari biyar, ka adana dubun kaga tafiya ce jibi a gabanka, ba lallai ka sake samun wasu kuɗaɗen kamar wannan a gobe ba."

"Ikon Allah! To, ai na gama shirye-shiryena, na sai musu omo, sabulu, manshafawa, da farin magi. Burodi kawai dama ya rage in saya."

"To, ka gani ai. Ko mu hakura har ka je ka dawo?"

"A a! Daga yanzu ai duk aikin da ya samu yi za mu yi. Kaga tanan zamu riƙa samun wasu kuɗaɗen."

"Allah ya taimakemu, yanzu ina muka dosa?"

" 'Yan kura za mu, mu yi haya kagani mu ɗebi ruwa mu shigar unguwannin da suke da ƙarancin ruwa ka gani."

"Hhhhhh! 'Yan Garuwa kenan?"

"Ƙwarai!"

Ya faɗa yana wanke hannunshi da guntun fiya watan da ya sha.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_27_

Kai tsaye fallo ta dawo ta zauna,

Please Login or Register in order to submit comment