Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaiku Jinjin sifeshiyal hosfitan ko ruwa ne sai su ɗaura mata su bata magani ko zata ɗan ji ƙarfin jikinta."

"Mami! Ɗakina kuma? Kada ta je ta..."

"Zan ɗaura miki mari. Riƙeta ku je. Kai ƙaramin Asabe ta je ta tsaftace can ɗakin."

Haka ta kamata tana yatsina fuska suka tafi.

***

Inna Talle ta cigaba da magana.

"Ya shiga tashin hankali mara iyaka, haka na yi ta bashi baki ina bashi haƙuri kan cewar idan Allah ya nufa Abulle matarshi ce sai ƙaddara ta bashi ita, idan kuma ba matarshi bace ya yi haƙuri tun can haka Allah ya nufa, ya yi addu'ar zaɓi na gari. Ganin yadda nima na shiga damuwa a 'yan tsakanin nan ne yasa ya daina tunƙarata da zancen, ganin haka yasa nima na kwantar da hankali na."

Shiru ya sake ratsa tsakani.

Inno kan na tsugunne kan ƙafafunta da suka gama yi mata tsami, ta kasa magana sai sauraro kawai.

"Lokacin da Abulle ta fara zaga gidajen sallamar tafiya gidan aure lokacin ne muka tabbatar da ta fita rabonmu. Ranar ya zo ya ce mun sun haɗu da Abulle ta faɗa mishi maganganu marasa daɗi, ya kuma samu labarin tafiyarta Rangwangwan a ranar tunda ya fita ban ƙara jin motsin shi ba har yau, duk wanda na tambaya sai ya ce ya ganshi da kaya a leda ya ce za shi garin Dagal aike wajen kawunshi. Ashe tafiyar kenan..."

Kuka ya ci ƙarfinta.

"Shi ɗaya ke gareni, shike tallafamin saboda lalurata ta rashin ido, yau anwayi gari na rasashi, kukuma taku ɗiyar tana tare da ku..."

Ta sake rushewa da kuka.


Hamusu ya yi hijira a soyayya.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

      _Ummyn Yusrah_

_Gwiwoyina a ƙasa, hannayena bisa kunnuwana ina neman afwa._

_17_

"Inna Talle ki yi haƙuri! Bansan komai game da wannan lamari ba, kwanaki dai Muntari ya faɗamin Abulle sun tafi faɗa a dandali ita da Indo, tun a lokacin na sa aka ƙirata na haneta da hakan. Ta kuma yi min bayanin dalilin faɗan cewar shi Hamusun yana zuwa gurinta, tun daga lokacin ban kuma bi ta kan zancen ba. Ko auren nan da za a yi mata da amincewar ta ba wai dole za a yi mata ba."

Sharce majina Inna Talle ta yi daga hancinta, bakin zaninta ta sa ta goggoge hancin kafin ta ce,

"Allah ya sauwaƙe wahala, tsohuwa taga kwananta ya yi kusa. Ba nema tsakanin Indo da Hamusu, shi ɗin dai wakili ne kawai. Wanda aka cuta, ai shi ake ba haƙuri.
Haƙuri kam ai ya zama dole."

"Wakili? Na wa kenan Inna?"

"Ɗan gidan kawunshi Saluhu dake Dagal ne ya ganta yake kamu, to shine fa shi Hamusun ke isar mata da saƙo idan ya je garin. Ya yi ƙoƙarin ya sanar ma ita Abullen amma ta ƙi sauraronshi."

Haɓa Inno ta kama cike da mamaki da saurin yanke hukunci irin na Abullen.

"Amma ko Abulle ta yi wauta! Ban san dalilinta na ƙin tsayawa ta saurari jawabin Hamusun ba."

"Mai hankali ai shi kan ba kaza ruwa da damina."

"Karuwa ai bata kiwon kaza. Ki yi haƙuri za mu magantu da mahaifin nata idan ya dawo, da yardar Allah kuma za mu tayaki cigiyarshi. Ko ba Abulle ai Hamusu ɗa ne a wajenmu."

Sandarta ta fara lalube, tana ɗauka ta muƙe tana faɗin,

"Uhmmm! Allah ya jishshemu alheri."

"Amun.
Inno ta amsa.

Har ƙofar gida ta yi ma Inna Talle jagora, anan ta ƙira ɗan rakiyar nata ya zo suka tafi, itama ta koma ta cigaba da aikinta.


Ba dare bayan dawowar Malam Ilu, ya yi mata banganjiya da tambayar yadda ta baro mutanen Jinjin da Yayanshi, ta sanar da shi duk suna lafiya, amma basu gamu da Yayan ba ya tafi aiki. Ta faɗa mishi irin sha tara ta arziƙin da Hajiya ta yi mata.

Godiya ya yi gami da yaba ma matar Yayan nashi na halin ƙwarai da son kyautata ma jama'a.

"Ohh! Niko Malam ka ji wani batu kuma?"

Ta faɗa tana kama haɓa.

Kallonta ya yi, ya ce,

"Batu akan me fa?"

"Batun ɓatan Hamusu ɗan gidan Inna Talle jikan Yawale mai Gurguzu."

"I, wallahi, duk gari ya ɗauka. Ko ina ka gifta zancen ake."

"Allah sarki! Na tausaya ma halin da Inna ke ciki. Ɗazu bayan dawowata har ta ɗan ɗau lokaci ma anan muna magana kan Abulle da shi Hamusun."

"Allah sarki! Abun ai akwai al ajabi, yaro dare ɗaya ya ɓace ɓat! Kamar wanda aka yi ma kurciya? Wannan abu da mamaki."

"Wallahi kuwa, ta sanar mun da komai, ashe shi Hamusun ba neman 'yar gidan Mai Unguwa yake ba, ɗan gidan kawunshi yake zuwa ma aike wurinta, da Abulle tagansu tare shine fa ta hau dokin zuciya, ya yi ƙoƙarin sanar da ita gaskiyar magana ta ƙi bashi haɗin kai. Da ya bita ta ƙi sauraronshi shine ya gudu wai ba zai iya ganin auren Abulle da wani ba."

"Ka ji shirmen banza! Duk tarin matan garin nan na Mai Ludaya ba zai zaɓi wata ba sai Abuwa? Wannan ai shashanci ne, dama can ya yi niyyar shiga bariki ne kawai. Ba wai rashin auren nata ba. Bana ma son sake jin zancen daga bakinki, tun wuri ki haƙa rami anan ki birne shi, kafin gari ya ɗauka."

"To, amma Malam maihaifiyar shi yaron fa? Tana cikin wani..."

"Dakata don Allah!"
Ya faɗa yana daga mata hannu.

"Na faɗa miki ki yi gum da bakinki, ki tayata da addu'a Allah ya bayyanashi kawai. Domin matuƙar zancen nan ya baza gari to, ina mai tabbatar miki fita ma sai ya gagaremu, ki barmu dai mu ji da wanda ake yi mana yanzun muka toshe kunnuwanmu."

Cikin marairaice fuska ta ce,

"Shi ke nan. Allah ya bayyana shi, ya yi mishi zaɓi da mafi alkairi."

"Faƙat! Amin."

Ya kaɗe 'yar shararshi ya fice daga gidan.


****

_Fadar Mai Unguwa_

"Sarkin fada! Yanzu ya kake ganin za a tsara lamarin bikin nan? So nake a yi biki na kece raini."

Kallon Mai Unguwa ya yi, da yake ta mamula gole a bakinshi.

"Ranka shi daɗe! Ai kasa a je cikin garin Jinjin a lafto shinkafa a zo a dafa a bi gida-gida ana rabashi, matuƙar akayi hakan to fa ina mai tabbatar maka da cewar wannan biki zai kafa tarihi matuƙa a cikin garin nan da kewayenshi."

Wangale baki ya yi, irin a dole yana dariya ɗin nan, ga haƙoran gaba, sama da ƙasa guda huɗu duk babu.

"Sarkin fada shi yasa nake son zama da kai. Ga ka ƙarami sai iya tsari wallahi."

"Ai Ranka shi daɗe, na fi kowa san kasance a zaman fadar nan."

Murmushi Mai Unguwa ya yi, ya ce,

"Zama waje uku suna da amfani. Zama a makaranta, zama a mahauta, da zama a fada. Zama a makaranta ko ba ka yi karatu ba, idan ak yi abun addini ka ji. A mahauta in an fiɗa, ko fince ka yi. A fada kuwa za ka ƙaru da maganar tsofaffi don nan ne matattarar magana."

"Gaskiya ne! Ina ƙaruwa kam sosai a fadar nan."

Nan suka ci gaba da tattaunawa.



_Ummyn Yusrah_


*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

    _UMMYN YUSRAH_

_18_

Leda biyu na ruwa Abulle ta sha da kuma allurai biyu bayan dogun artabu da akasha wajen sa mata ruwan da tsira mata alluran.

Ba kunya ba tsoron Allah ta zage ta yi ta zabga kururuwa tamkar wacce za a zare ma rai.

Sai wajen ƙarfe ɗaya saura na dare aka sallemesu. Shima dalilin matsawar da Lubna ta yi ma likitan, don ba zata iya kwana a asibitin ba.

Itama Abulle tunda ruwa ya ratsata, jijiyoyin jikinta ya saki, ta ji ta ƙagu su koma gida, don ta gaji da kwanciya a gado mai tafiya. Ko yaya aka ɗan muskuta sai kaga gadon ya matsa.

Kamar ba ita ce ɗazu aka sha gwagwarmaya wajen sanya ruwan ba.

Gari ya yi shiru, kai ka ce ba wani ɗan adam da ya wuni yana zirga-zirga a wajen.

Tituna ma ɗai-ɗaikun ababen hawa ne ke giftawa.

Ba ka jin motsin komai sai kukan kwaɗi da wasu ƙwarin.

Ƙofofin gidaje ma a rufe, haka ma shaguna, sai dai a wasu ƙofofin gidajen da yake mallakin gidan almajirai, zaka iya hangosu shimfiɗe kan tabarma suna ta sheƙa barci. Wasu kuma a ƙofar shagunan mutane.

Tunda suka fara tafiya waje ɗaya ne kawai suka ga mai shayi, da wasu tsirarun mutane da basu wuce uku ba.

Dare kenan! Mahutar bawa.

Kowa ya bar gida-gida ya barshi.

Hakan ce ta kasance.

Hamusu ma yana ɗaya daga cikin mutanen da ke ƙawance  a ƙofar wani shago, a tsakiyar bencin da aka tokare ƙofar shagon bayan an rufeshi da kwaɗo.

***
Tun ranar da suka yi sa'insa da Abulle ya tattara kayanshi ya bar mahaifarshi, ya fita neman kuɗi don huce takaicin abunda Abulle ta yi mishi.

Yana da yaƙinin kuɗi ta bi, shi yasa ta amince da auren Mai Unguwa. Inda yana da su da yanzu suna tare.

Ya shigo cikin garin Jinjin ba tare da yasan kowa ba, hasalima karo na farko kenan a tarihin rayuwarshi da ya taɓa zuwa.

Sosai yaga bambanci da garinsu. Kowa a nan harƙar gabanshi yake yi, idan zaka wuni baka sami ɗigon ruwa ka jiƙa maƙoshinka ba, ba mai baka, basu damu da kai ɗin baƙo ba ne, ya saba gani a garinsu idan aka yi baƙo an rinƙa ina asaka da shi kenan.

Kwananshi biyu yana garari a cikin tasha, ganin 'yan kuɗaɗenshi na shirin gangarawa su barshi, yasa ya nemi mafita daga wajen wani da suke kwana kullum a tsakiyar motocin da ake ajesu idan dare ya yi.

Gauta yake kasawa a tire ya yi ta yawo kan tituna yana sayarwa.

Shine sana ar da Hamusu ya fara yi.

Yau kwananshi biyu kenan da fara sana ar, sai dai yanzu ya bar cikin tasha ya dawo kwana ƙofar wani shago.

Har ya fara tunanin canza sana ar, domin yau ba ƙaramin galabaita ya yi da zafin rana ba.

Sai dai kuma ba ya da wani ishashshen jarin da zai kama wani sana ar.

Juyi kawai yake yi, sam! Barci ya ƙi ya ɗaukeshi sai ma wasiƙar jakin da yake ta karanta.

"Allah sarki Inna ta! Ko yanzu a wani hali kike? Ki yi haƙuri na tafi na barki ba tare da izininki ba, na tafi na barki ba tare da tunanin lalular makanta da kike fama da shi ba. Ban yi hakan domin in sanya ki a damuwa ba, sai don sama wa zuciyata mafita, Inna ba zan iya zama cikin Mai ludaya a ɗaura wa macen da nake so aure da wani ba, zuciyata ba zata gaza ganin hakan ba Inna! Ki fahimceni, zan dawo gareki nan ba da daɗewa ba, zan dawo, zan dawo..."

Maganar da yake yi kenan a hankali cikin sautin kuka, zuciyarshi kuma na ƙuna.

***
Barci sosai Abulle ta sha akan lafiyyayen gadon da ya sha shimfiɗi, ba kamar gadonta da aka yi shi da yayi aka ɗinkeshi da buhu ba.

"Ke wai ba za ki tashi ba ne?"

Lubna ta faɗa tana ɗaka mata duka a sangalalin ƙafafunta.

Tashi ta yi tana miƙa, tana hararar Lubnan da gefen ido, don ba ta so tashi yanzu ba.

"Lafiya kika tsareni da ido? Ko baki gama warwarewa ba ne?"

'Wannan baiwar Allah akwai buhun masifa! Inaga da ita ke da gidan ma ko wuni ɗaya ba zan yi ba.'

Ta faɗa a zuciyarta, a fili kuma ta ce,

"Ras nake! Allah na tuba ma ai inaga na fiki lafiya."

Ta ƙarashe maganar tana sauƙa daga kan gadon.

Zaro ido Lubna ta yi,

"Me kika ce?"

Ta tambayeta.

"Cewa na yi, ai yanzu ko garin nan aka ce in zagaye da gudu zan iya."

Tsaki ta yi, ta koma ta kwanta a cikin kujerar da ke cikin ɗakin.

"Ina kuma za ki je? Banɗaki za ki shiga, akwai sabon  burosh da makilin na ajiye miki."

'Buroshi? Makel? Su kuma suwaye hakan?'

Ta tambayi zuciyarta yayin da ta nufi ƙofar banɗakin.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Na_
_Ummyn Yusrah_

_Hhhhhh! Sosai Abulle ta ce in miƙo gaisuwarta ga masoyanta, musamman,_
_Abu Hisham_
_Yayana Almu_
_Kamala Minna_
_Beauty Queen_
_Mai Dambu_
_Heenart Nijar_
_Queen Beelart_

_19_

Duk dube-dubenta ta yi bata fahimci komai ba, don banɗakin cike yake da shirgi.

Taɓe baki ta yi, ta ce,

"Shima banɗaki sai an yi mishi jere tsabar samun waje. Wannan kwalayen idan na samu na jeresu a kan sif ɗina ba ƙaramin kyauwu za su yi ba."

Ta ƙarashe maganar tana murmushi.

"Ce miki a kayi ana magana a toilet ne kam."

Daga can ta ji Lubna na mata magani.

"Ohho miki kuma! Ni na san wani tulat ne."

Ta faɗa a hankali, sannan ta ɗauro alwala ta fito.

"Kawai ki goge baki ki yi alwala shine ki ka zauna surutu?"

Turo baki ta yi da yatsina fuska, haɗe da hararar ta ta gefe don ta tsani masifa, da alama wannan mai farar fuska kamar shinkafar ba za su zauna inuwa ɗaya da ita ba.

"Yo, naga dai alwalar haɗe take da wanke baki, kuma duk na yi. Sallah zan yi yanzu."

"Kina nufin ba ki yi burosh ɗin ba?"

Yadda ta zaburo kai ka ce ashariya Abullen ta yi mata

"Magana ta gaskiya ma ni ban sansu ba."

Ta bata amsa tana sanya hijabin da ta gani kan sallayar ta tada iƙama.

Shiru ta yi ganin ta fara sallah, zuciyarta cike da tunanin wai ba tasan man goge baki ba. To su da me suke wanke bakin?

"Ina kwana?"

Shine kalmar da ya katse mata tunanin.

Kallonta ta yi, tana naɗe hijabin.

"Ba dai kin idar da sallar ba ne?"

Itama kallon ta ta yi,

"Na idar mana."

"Malam raka a biyu fa za ki yi, ba ɗaya ba."

Kallon rashin fahimta ta yi mata.

"To, ai biyun na yi."

"A hakan? Kafin kiftawar ido da buɗewa har kin dungura kin tashi! Da aiki. Wannan shi ake ƙira 'yar mubi ba yawa sai lada."

Yatsina fuska ta yi,

'Koma 'yar waye ke kika sani.'

Ƙofa ta nufa da niyyar fita, tambayar da ta jefo mata yasa ta tsayawa.

"Na ce ina za ki je."

Ta sake maimaita mata tambayar.

"Zuwa gaida masu gidan, in kuma ci abinci."

"Ba ki goge bakin ba ne za ki ci abinci?"

Cikin jin haushi yasa ta ce,

"Wani burushi da makel da kike faɗa ma ni ban sansu ba."

Fuska cike da mamaki da kuma don darawa da sunan da ta ƙira abun goge bakin ta ce,

"To, da me kuke wanke bakin a can?"

"Gawayi da gihiri muke dangwala a jikin soson buhu mu yi ta gogawa a haƙoran. Nan gidan ko ban ga alamar murhu ba balle in samu."

Bata ce komai ba ta miƙe ta nufi banɗakin, sai da ta kai ƙofa sannan ta sa hannu ta yafutota.

Makilin ɗin ta matsa a jikin burunshin ta miƙa mata,

"Ki dirje duk wani lungu da saƙo na cikin bakinki har kan harshenki."

Tana gamawa ta fice ta bar Abulle a banɗakin.

"Wannan akwai shegen iyayi, in da ita ke da gidan inaga ko wuni guda ba zan yi ba za ta korani gi..."

"Wai waya faɗa miki ana magana a banɗaki."

Shiru ta yi, ba amsa.

Ta ɗau tsawon lokaci tana tunanin yadda za ta zura wannan abun cikin bakinta, tsoro ma take kada kifiyoyin robar su caccake mata dadashi.

Lakatar man goge haƙoran ta yi, wani yaji-yaji, zaƙi-zaƙi ne ya gauraye mata baki.

Tas ta shanye makilin ɗin kan burushin ta sake ɗauko, gudar makilin ɗin ta rinƙa matsowa tana sha tana jan yaji, idan ta ja sai ta ji iska mai sanyi yana hura mata cikin baki.

"Mazauni kika samu a ciki ne kam?"

Lubna ta watso mata tambaya daga can.

Zabura ta yi,

"Gani zuwa."

Da sauri ta zura magogin cikin bakinta.

Ta dai yi yadda ya samu ta ɗauraye bakin ta sake tatso man ta lashe kafin ta fito.

"Au! Duk wannan zaman naki ba wanka kike yi ba?"

"Wanka kuma da sassafen nan kamar wacce ta yi fitsarin kwance? Jiya ma ai na yi wanka kafin mu taho nan."

"Ikon Allah! Kenan acan ba kullum kuke wanka ba?"

'Wanka kullum! Wa yaga ƙwaɗi.'

A fili kuma ta ce,

"Ina muka ga ruwan da za mu yi wanka kullum."

"Uhmmm! Je ki."

Ta fice, don dama ta gaji da yawan tambayoyin nan kamar a gaban alƙali.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

           _Ummyn Yusrah_

    _20_

Ta jima zaune a falon ba kowa sai  Lantana mai aiki da ke share-share da goge-goge da kuma tibi da ke ta aiki shi ɗayanshi.

Gajiya da zaman ta yi, ga kuma yunwa da ya dameta.

"Baba! Don Allah an gama abun karyawa ne?"

Ta tambayi Lantana dake goge tibi.

"Abinci a yanzu ƙarfe takwas da rabi? Ai da sauran lokaci 'yannan, da yake yau duk suna gida sai ƙarfe goma ko sha ɗaya za su fito karyawa. Ki koma ki kwanta ko ki je ɗakin girki ki samu wani abun ki ɗan taɓa."

Langwabar da kai ta yi, ta kwantar kan hannun kujerar tana faɗin,

"Na shiga uku! Wallahi zan iya mutuwa da yunwa idan na kai wannan lokacin."

Kallo Lantana ta bita da shi, ta ce,

"Ki shiga ki sami Saude mai girki ta baki ko ruwan shayi mana."

To, kawai ta ce, ta miƙe jiki ba ƙarfi.

"Sannu da aiki Inna!"

Juyowa ta yi ta kalli mai yi mata sannun.

"A'a! Baƙuwarmu har kin tashi ne?"

"Uhmmm! Ina kwana."

"Lafiya, yaya jikinki?"

"Da sauƙi. Dan Allah akwai abinci? Yunwa nake ji."

Ta faɗa kamar zata yi kuka.

"Wai! Gashi yanzu nake ɗaurawa. Ko in haɗa miki shayi ne?"

"Eh."

Ta amsa da sauri.

Tana tsaye a wajen ta haɗa mata a wani ƙaramin kofi ta miƙo mata.

Karɓa ta yi tana godiya a fili, a zuciyarta kuma haushi ne ya gama rufeta.

'Wannan ne wai abunda zai riƙe ni har wani lokaci? Alƙur'an fitsari ɗaya zan yi in zubar da shi.'

Kafa kai ta yi ta kurɓe.

'Da wannan gara ruwa ma wallahi, ban ji komai ba nikam.'

"Ga kofin na gode."

Ta fito tana tunano ɗumamen tuwon dawa da kokon Inno! Da yanzu a gida take da ta manta da ta karya, da yanzu a gidansu ne miyar tuwon rana ne a kan wuta.

Amma anan wai yanzu ne ma ake ɗaura girkin safe, ba za ta iya ba.

Gara ma goben ta yi ta koma gida, kafin yunwa ya mata illah.

Falon ta koma ta zauna ta fara kallo, sai dai sam bata jin daɗin kallon.

Ɗaki ta nufa, ta tarar da Lubna har ta yi barci.

Tsaki ta ja a hankali, a zuci kuma ta ce.

'Barcin asara.'

Ganin ba abunda za ta yi yasa ta koma kan kujerar cikin ɗakin ta kwanta, hannunta riƙe da ciki.

Juyi kawai take na rashin sabo da kwanciyar, ga kuma uwar yunwa.

Ji take kamar ta ƙwala ihu ko duk mutanen gidan zasu tashi.

Idan ba iskanci ba, ace duk barcin da aka yi da dare bai ishe mutum ba, sai ya sake komawa.

Ba ta fatan ma tayi dogon zama a irin wannan wajen da yunwa zai yi ajalinta.

Turo ƙofar ɗakin aka yi, Hajiya ce ta sha ado kamar zata gidan biki.

Jin buɗe ƙofar yasa Abulle ɗagowa.

"A'a! Ashe ɗiyar tawa ta tashi? Yaya jikin naki?"

"Na jima da tashi, na ji sauƙi. Ina kwana?"

"Lafiya, yaya ƙarfin jikin naki?"

"Da sauƙi." Ta bata amsa a fili.

A zuci kuma ta ce,

'Ina wani ƙarfin jiki, ban sanya ma ciki komai ba.'

"Allah ya ƙara sauƙi."

"Amin."

Har ta juya zata fita, ta juyo ta ce,

"Ki tashi Auntynki ku zo ku ci abinci, ga Babanki ma ki zo ku gaisa, jiya mun je asibiti da shi kina barci."

"To."

Ta bata amsa, ta je har gaban gadon ta miƙa hannu ta bubbuga ƙafafunta.

Idanuwanta ta buɗe, ganin ta tashi yasa ta faɗa mata saƙon Hajiya.

"Na ji ta. Ki je sai na yi wanka."

'Sannu kifi.'

Ta miƙe tabar ɗakin.

Fitowarta ma ba kowa a falon.

Tunani take ina shi mai gidan yake da zata gaisheshi? Ita ba ko ina ta sani a cikin gidan ba.

Kicin ta shiga ta tambayi su Lantana, ita ta fito ta nuna mata wani ƙofa da zai kaita har ɓangaren Alhajin.

Dogon lungune da ya sha sumuntin bature, (Tayis) samɓal ta miƙe ta fara tafiya tana kalle-kalle zuciyarta fal tunanin irin kayan more rayuwa da ke gidan, su kuma suna can cikin karmami.

Ba tayi aune ba, sai ji ta yi santsi ya kwasheta ya timata da kasa, take ta baje a wajen ta yi zaman 'yan biri, sakamakon goge wajen da aka yi bai gama bushewa ba.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_

_21_

Rintse idanunta ta yi, har da ɗan guntun hawaye,ta shiga shashshafa kunkuminta da ta buge a da jikin garu.

Sai da ta ɗau tsawon mintuna goma a zaune kafin ta shiga yin rarrafe zuwa wajen su Hajiyar.

Bata yarda ta miƙe ba, sai da ta isa wani babban ƙofa sannan ta tashi tsaye,

'Aljannar duniya! Gida a cikin gida.'

Shine abunda ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta kutsa kai cikin babban falon, sallama ta yi gami da kalle-kalle.

"Shigo mana Zainab."

Hajiya dake zaune kan daya daga cikin kujerun falon ta faɗa bayan ta  amsa sallamar.

A hankali take tafiya don gudun sake afkawa gidan jiya.

Tana jefa ƙafarta kan tattausan kafet ɗin da ke baje tsakiyar kujerun ta yi saurin janyewa, don laushin ya yi yawa, tsore take kada ta kuma jefa kafar ya lume da ita.

Da sauri ta tsugunna a wajen, tana faɗin,

"Ina kwana Baffa!"

"Lafiya lau, ɗiyata ashe ta jirma. Taso a ƙasa ki hau kujera ki zauna."

Yaƙe ta yi, ta ce,

"A'a! Nan ma ya yi."

"Ki saki jikinki, nan ma gidanku ne, maza taso."

Kamar ta kurma ihu haka ta ke ji, gani take kamar lumewa ƙasa za ta yi idan ta sake hawa kan wannan abu mai gashin.

Ƙara matsowa ta yi, ba tare da ta hau kan kafet ɗin ba.

"Ke dai Zainab akwai ƙauyanci! Ace mutum da gidansu ya riƙa abu kamar wani baƙo."

Cewar Hajiya.

Dariya Alhajin ya yi, ya ce,

"Za ta ware ne ai, sai a hankali. Yaya jikin naki?Kin ci abinci dai ko?"

"A'a, yanzu zamu ci."

"To, maza a je a karya, kafin a zo a bani labarin Mai Ludaya."

Da sauri ta miƙe, ta fita.

Tana fitowa ta gurfana ta hau rarrafe.

"Ke! Meye haka?"

Taji tambaya daga sama, ba tare da ta ji tahowar mai tambayar ba, da yake kanta na sunkuye a ƙasa.

Ganin Afreen yasa ta magana.

"Sulewa na yi ɗazu."

Dariya ya saka, ya ce,

"Sai ki riƙa tafiya kina kula." Ya wuce ya barta.

'Ji mugu! Ba ma sannu zai min ba sai wani in kula! Kulo.'

Ta ci gaba da rarrafawa har ta baro wajen, ta iso babban falo.

Tana zuwa ƙofar wajen ta miƙe, ta shiga.

Wajen da suka ci abinci jiya ta wuce ta tarar an ajiye musu komai na karyawa, sai dai ba kowa a wajen.

Daga zamanta zuwa yanzu ta yi tsaki ya fi a ƙirga.

Ga dai kwanukan abinci, amma ba masu cin.

Ga yunwa, ga takaicin rashin zuwan masu gidan.

Ganin ta ɗau lokaci tana jiransu ba su zo ba, yasa ta fara kokuwa da kula. Duk wani dabara da za ta yi don ya buɗu ta yi, amma ya ƙi buɗewa.

Ganin haka yasa ta haƙura ta koma ta cigaba da zaman jira.

A tare suka fito daga gefen Baffan suna kwasar dariya.

Kallonsu Abulle ta yi, take ta ji wani takaici ya ƙara rufeta.

Ji ta yi kamar ta je ta shaƙesu.

Har suka iso wajen suna dariya.

"Ba ki ci abincin ba?"

Afreen ya tambayeta.

Kallon takaici ta yi mishi,

'Banci ba ɗan rainin hankali, da uwar kai kamar Umarun kiyashi.'

A fili kuma ta ce,

"Uhmmm!"

"Me yasa?"

A kufule ta ce,

"Ban iya buɗe kwanukan ba."

Buɗe mata ya yi, ya bata faranti ta ɗibi dankali da ƙwan.

'Ikon Allah! Wannan uwar mai ai sai yasa mutum ya yi lisu.'

Jida tayi yanda zai isheta, ya haɗa mata shayi ya miƙo mata da biredi.

Godiya ta yi mishi.

Ta kalli Lubna da tun zamanta a wajen take danne-dannen waya.

'Albasa dai ba tai halin ruwa ba. A haka dai za a ƙare.'

Ledan burodin ta buɗe ta yagoshi, ta dunƙule ta dauko kofin da ya haɗa mata shayin ta danna a ciki.

Hannu ta sa ta kwaso jiƙaƙƙen burodin, ta hangame baki za ta tura, hakan ya yi daidai da sauƙe kofin shayin da Lubna ta yi daga bakinta.

Kamar ance ɗaga kanki! Sai ko ta yi ido biyu da kwamacalan Abulle.

Furzo da ruwan shayin ta yi, tana faɗin.

"A uzu billahi! Wannan wani irin azanta ne don Allah."

Ta miƙe da shirin barin wajen.

"Sista ba dai kin ƙoshi ba?"

Afreen ya tambayeta.

Juyowa ta yi tana faɗin,

"So kake in yi amai ne? Dubi wani gwale fa da yarinyar nan ke yi."

Ta juya ta bar wajen.

Gallamata harara Abulle ta yi.

'Har da wani korar A'uzun ta, irin ga sheɗaniyar nan. Idan kin ga dama har yauma ta nannaɗe kada ki kuma cin abinci. Har wani Sitta ko sittin ne kai ka ji wajen.'

Ta ci gaba da ba cikinta hakkinshi.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*


_Ummyn Yusrah_


_22_

Afreen ruwan shayi kawai ya haɗa ya sha da wainar ƙai ya miƙe ya bar wajen.

Kallo ta bishi da shi mai cike da mamaki, har yaushe wannan ɗan ruwan shayin zai ɗauki mutum? Ga abinci nan a wadace ba za su sake su ci ba sai a dangwala a tashi. Shi ya

Please Login or Register in order to submit comment