Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sosa inda yake mata zafi take tana kuka,, baki na rawa Mai koko tace"ina ne yake miki zafi" ? Aminoni ta nuna mata k'irjinta da gefen hannun ta,aikuwa tana dubawa taga gurin yayi jajazur har ya soma tashi, cikin gida ta shige da sauri tana salati,,,,, zuwa yanzu mazan dake waje sunji abunda yake faruwa nan suka shigo suna aikin raba fad'a inda Ladidi ta dunga Kai musu duka tana zaginsu duk girman su kuwa, da yake duk sun san halinta,suka k'yaleta k'okarin su fuzge Iliya da tayi masa rik'on tsauri,, Iliya da ya samu ta sake shi sai yayi waje yana maida nuffashi,, ita ko Ladidi gefe ta koma tana haki! Bakin ta bai mutu ba, tana ta zagin Iliya da masu roban fad'a,, futa sukayi suna mamakin rashin kunyar ta,, bakin kofar ta tsare tana kallon Iliya tace"Wallahi baza a siyar maka da kokon ba, don haka kasan inda dare yayi maka,, bai ce mata komai ba d'auki kofunsa ya tafi,,, cikin takaicin na bata lokacin sa da yayi gashi gidansu duk sun fi son kokon Iya saboda ta iya ga gard'i da tsabta fari tass dashi yana k'amshin citta da kaninfari.

Mai koko ta dawo hannunta dauke da wata roba ta kad'o omo a ciki tazo tana shafawa Aminoni a jiki tana mata sannu, Aminoni kad'a kai kurum take tayiwa Ladidi Allah ya isa babu a dadi domin babu damar ta fada a fili,, rigar Ladidi ta sanya mata, ta dauki kwanon kokon ta zubo mata wani,, har waje ta rakata tana mata sannu,, mutanan dake waje ta tsaya tana bawa hakuri, sannan ta koma ciki, ko takan Ladidi bata bi ba, ta cigaba da sallamr mutane,, haka suka hak'ura da hukuncin da Ladidi tayi musu na farko ya koma k'arshe na k'arshe ya koma baya



**********


Hajiya Asiya na zaune kan kujera tana jiran isowar su,, tayi kwalliya tsab da ita ta shiryawa shalelen ta daining shi kadai kawai ake jira,,, tana jin shigowar mota gidan ta furta Kalmar "Alhamdulilahi, idonta a kofa har suka shigo,, da sauri ya cire hannunsa daga na Salima ya rungumeta yana fad'in" Mamana I miss you!!" Shafa kansa tayi tana murmushi tace"Nima haka my Son nayi kewar ka, sati biyu kacal sai suka zama kamar shekara a gurina" lumshe idonsa yayi yana jin d'umin mahaifiyar sa mai so da kaunar sa,, G.Abbas yace"Idan ya koma can da zama kuma yaya zakiyi gwara ma ki sawa zuciyar ki sauk'i" Hakkim ya zauna hannusa rik'e da nata yana kallon Dady din yace"Wallahi Dady saboda Mama zan iya hak'ura nifa da man bai wani dame ni ba,gwara in zauna a k'asata" Dady yace"Aikin gama ya Riga ya gama tunda kaje ka saka hannu lokaci kawai ake jira"" Hajiya Asiya tace"Tashi muje kaci abunci na mussaman" cike da farin ciki suka nufi gurin cin abunci dukan su..


Bayan ya gama cin abunci part d'insa ya nufa a gajiye ya fad'a toilet yayi Wanka ya futo daure da towol a jikinsa, ko mai bai shafa ba,ya zauna gefan gado yana latse-latse a wayar sa,, kira ne ya shigo yana dubawa yaga babban abokinsa Yusuf d'aga wayar yayi tare da fad'in "Ya akaiyi ne yaro"? D'ayan b'angaran Yusuf yace" Ganin kan hanya nasan dai yanzu all ready kana gida" Hakkim yace"Ina gida hutawa kuma zanyi karkazo ka dame ni da surutun ka na ala tsine" Yusuf na k'okarin kashe wayar yace"Idan nazo kar ka bude min kofa" Kitty!ya kashe wayarsa, Hakkim yasa Dariya yana fad'in"Lallai wannan bai da mutumci ni ya kashewa waya, anyway zai zo ya same ni""" mik'ewa yayi ya d'auko boxer da singlet Cikin kayansa ya saka ya fesa turare ya koma ya zauna inda ya tashi, latse-latse ya cigaba dayi da wayarsa.. Bugun kofa Yusuf yake yana jinsa ya share shi,, kiran wayarsa yayi ya kashe,wato ya rama kenan, Yusuf ya fi minti goma a tsaye sannan yaje ya bude masa kofa,, ya shigo cikin jin haushi yace"Wallahi mugun Dan wulakanci ne kai fa" kai tsaye yace"Waye yace ka kashe min waya, abunda na tsana a rayuwa ta" Yusuf yace"An kashe d'in, dallah kai kowa sai ka gwadawa iko da mulki to ni baka isa ba""Dariya Hakkim yake masa ya bashi hannu suka tafa,, Yusuf ya zauna yana fad'in"To yane akwai labari ne"? Tab'e baki yayi yace"Ni da na dawo ni za'a bawa labari ai" Gyara zama yayi yace"Aiko akwai labari fa""""" kallonsa yayi yana kanne masa ido,, doka ya kai masa yana fad'in"Bana son iskanci fa" Sosai Hakkim yake dariya yana fad'in "Ai nasan zance gizo baya wuce na k'oki labarin ka kullum akan abu d'aya ne,, kan wannan bak'yauyiyar budurwar taka da komai bata Iya shafawa ba"" Yusuf ya b'ata fuska yana fad'in"Bana son iya shege gwara ni ina da budurwa kai kuwa fa,ka tsaya tsoron mata dube ka don Allah gemai-geman da kai to wai in kayi auran ya zakayi da ita"" ? Ya k'arashe maganar yana dariya ta shak'iyan ci,, a kufule Hakkim yace"Uwar ka zanyi da ita d'an iska" dariya Yusuf yake har da kwanciya yace"Kullum sai sweet heart d'ina ta tambaye ka,,wai kazo ta baka kanwar ta" Duka ya kaima sa,, da sauri ya goce yana cigaba da masa dariya"" cikin jin haushi yace"Idan kaje kafad'a mata ni nafi k'arfin k'azamar kanwar ta"" Yusuf yace"Aikuwa zan fada mata wallahi,, kullum in muna hira ko a wayane ina bata labarin ka da yanda kake tsoron mace sai tai ta mamaki ita tana ganin kamar k'arya nake, a wannan zamanin akwai namiji me tsoron mace kuwa,nace ta kwantar da hankalin ta zan kawo mata kai har gida"" hararasa yayi yace"Taje tayi ta mamaki, kuma Wallahi idan baka daina bata labari na,, na rantse maka da Allah har a d'aura auranku bazan jebe".

Yusuf ya mike zaune yana fad'in "Na daina ni da da nake so gobe ma ka rakani gurin ta""" tab'e baki yayi yana fad'in"Sai dai ka bari sai na dawo domin zan tafi Hutu ne"?

"Ina zakaje Hutu kaji d'an iska"" Hakkim yayi wani k'ayattacen murmushi yana fad'in "Kano zani Dady yayi gidan gona wani k'auye shine nake ta zumud'i""" Yusuf yace"A'a kace zamu huta yaushe zamu tafi"? Kallonsa yayi yana fad'in "Zakaje ne"? Gyad'a kai yayi yace" K'warai kuwa""" kashewa sukayi suna dariya yace"Gobe nake so mu tafi"" Yusuf yace "Yayi Allah ya kaimu".




*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/28, 10:16 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________



_*DEDIGATED*_
*TO*
_RAHAMA ALIYU_



_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*Ayi hakuri errow⚠⚠*






*🅿11*



Cikin kyakyawan shiri ya futo daga part dinsa , kai tsaye part d'in Mama ya nufa cikin nutsuwa yayi sallama, Mama da mai aikin ta Jummai suna tsaye suna shirya daining ta amsa fuska a sake take fad'in "Har ka shirya kenan"? K'araso wa yayi inda suke, da murmushi a fuskarsa yace" Tuntuni na shirya yanzu ma Yusuf nake jira,banason tafiyar rana" Mama tace"Yusuf ma zashi ne"? Zama yayi kan daya daga cikin kujerun cin abunci yana fad'in"Jiya daga ji ina zancan yace shima zashi" Salima dake zaune can falo tace"Babban yaya nima zani don Allah" hararata yayi yace"Babu inda zani dake" Mama tace."Kai kuwa kaje da ita mana dama sunyi Hutu". Yace. "Mama kin san ko kwana zamuyi kuwa"? Girgiza kai tayi tana fad'in" Sai ka fad'a". "Sati biyu zamuyi fa" Mama tace"To meye a ciki ka tafi da ita kawai" shiru yayi baya son musu da Maman shi, Gen.Abbas ne yake saukowa daga bene yana sanye da jallabiyya ruwan toka hannunsa rike da Jarida ta Daily trus, idonsa farin galashi ne, zama yayi suna gaisawa Mama ta fara had'a musu Kalaci, bayan sun kammala Hakkim yace."Dady na fa shirya" Gen. Yace. Na gani ai daga dawo wa zaka k'ara tafiya jiya munyi waya da masu aikin komai ya kammala, mybe yau zasu bar gurin amma dai na fada musu su zauna sai kazo". Yace. "Dady yanzu ma Yusuf nake jira tare zamu tafi". Salima ce ta futo cikin shiri sai murna take hannuta rike da trolly d'inta ya loda uban kaya, Dady yace." Ke kuma fa"? Narai-narai tayi da ido, Mama tayi saurin cewa"Tare zasu tafi" ."Shine ta lodo kaya Cikin jaka kamar wacce zata bar gari" tsuro-tsuru tayi, Hakkim ya buga mata tsawa! Tare da fad'in"Maza je ki rage kayan nan idan ba haka ba wallahi inki zuwa dake". Da gudu ta koma dakinta

********
Ihun!! Ladidi ne ya cika gidan,inda har daga waje ma ana jinta, sai zageye tsargidan take tana buga tsalle Mai koko na bin ta sai ta kamata,hannuta rike da sabuwar reza cikin takardar ta,fad'i take" Baki tsaya ba ko Ladidi ki daina wahalar dani, gwara ki tsaya a aske miki gashin kema kya huta da wannan azababbiyar kwarkwatar da ta dame ki". Ladidi tace"Wallahi ba zaki min aski ba,haka kurum sai kice sai kin aske min gashi ne,ina ruwanki da kwarkwatata ki bar min kayata mana, Mai koko tayi kanta da sauri zata damk'e ta, ta buga wani uban tsalle! Sai gata ta tsallake rijiya da baya!! A gigice Mai koko take salati, babu shiri taje ta aje rezar tana fad'in"Kinga na aje rezar futo daga bayan rijiyar Ladidi"mak'e kafad'a tayi tana fad'in"Wato in futo ki kamani,wallahi na gadama sai in fada rijayar ma" Sanin rashin hankali da gab'unta na Ladidi yasa Mai koko ta fara rarrashin ta da dadad'an kalamai, tace."Kinga d'azu munyi magana da Mairo mai dashi cewar zata bani d'auka ta uku shine nace da ta bani zan shiga kasuwar burni na siyo miki kayan kallo" Ladidi tasa dariya tana fad'in"Nagane wayo zakiyi min, ni sai na fad'a a rijayar ma" tayi taga-taga!! Kamar zata fad'a!Mai koko ta rafka salati zaninta na k'okarin fad'uwa tayi waje da sauri ko ina zata oho"! Dariya Ladidi take mata, ta buga tsalle ta futo daga bayan rijiyar, can wani guri da ya rushe Cikin gidan taje ta b'oya dake tunda gurin ya rushe babu mai zuwa gurin,Mai koko ta dawo ciki tare da wasu mutane biyu ita a nufinta su taya ta bawa Ladidi hakuri, wayam! Babu ita a gurin, Wani irin salati Mai koko ta kurma tayi bakin rijiyar gadan-gadan tana fad'in"Shikkenan ta fad'a cikin rijiya dama nasan Halin ladidi kome tace zatayi sai tayi, kuka ta farayi tana kara zura kanta cikin rijiyar, sai akayi sa'a tarwad'ar dake cikin rijiyar suka dunga motsi a ciki, kuka sosai Mai koko take tana fyace majina tace"Kunyi tsaye meye amfanin ku, kuzo Ku shiga Ku d'auko ta,Idan ma mutuwa zatayi ta mutu a gabana"

Kallon juna sukayi suka kama hanya futa suna fad'in"A'a Mai koko bari dai mu garzaya mu kira miki sarkin ruwa, wannan yarinyar me k'wamk'wamai watak'ila ma su suka jata ta fad'a ciki, haka kawai mu shiga su kama mu, domin ita suna iya sakin ta, tunda tasu CE"Mai koko ta saki baki har suka fuce. Suna futa d'aya yace."Allah yasa ma su kaita bakin ruwa su d'auke kayan su kowa ya huta da masifa".

Mai koko ta lek'a rijayar tana fad'in"Mai yasa zakiyi min haka Aminatu mai yasa zakiyi min ke kad'ai nake kallo a matsayin Aminu shine zaki fad'a rijiya Haba Ladidiya kiyi hakuri da halina da halin Kawun ki, majina ta fyace! da gefen zaninta sai zura kanta take cikin rijar tana sambatu! Ladidi ta lek'o daga kanta ta wata 'yar kafa sai dariya take yiwa Mai koko ganin yadda take kuka tana fyace majina dariya har sai da ta kwanta.

Kafin kace kwabo labari ya bazu a cikin unguwar Ladidi ta fad'a rijiya wasu suyi jaje wasu suyi ko murna suke cewar an rage mugun iri, D'alha na gurin sana'ar sa labari ya riske shi, babu shiri ya tawo gida ko kayan sana'ar bai d'auko ba, Mai koko kuwa ganin kamar tana son fad'awa cikin rijiyar yasa mak'otan ta suka nufi gudansu da ita sai sambatu take, hakan ya bawa Ladidi damar futowa daga mab'oyar ta tayi waje a guje! Kanta ko d'ankwali babu,wani abun mamaki da al'ajabi idan ka kalli gashin nata sai ya baka tsoro domin Duk ya dunk'ule ya cure guri guda yayi wata muguwar dauda ga tsakin kwarkwata da amosani man burjiki! Wani gurin sal-sal babu d'igon Gashi wani gurin da akwai, ita kanta idan tana sosawa ciro gashin take da hannunta ta yar. *Ni kaina sai da nace Ladidi da kin sani kin bari anyi miki aski domin shine mafuta a gare ki*
Can hanyar titi ta nufa tana fafara gudu kamar mahaukaciya, ko da wasa babu wanda ya ga gilmawar ta.


Sarkin ruwa tare da jama'ar gari suka shiga cikin gidan, jin ance ga Sarkin ruwa nan yazo yasa Mai koko futowa daga gidan da take da sauri duk tayi wujuga-wujuga, suka had'u da D'alha sai gumi yake zabgawa babu wanda yace da Dan uwa sa komai suka afka cikin gidan, To duk iya lalube Sarkin ruwa yayi amma bai ga Ladidi ba kusan awarsa guda a cikin ruwa ya futo yana fad'in"Da Ladidi tana cikin rijiyar nan to ko da na ganta domin na baje basira ta sak'o da loko, kogo da kogona babu inda ban duba bata ciki". Guri yayi Tsitt!! D'ai-d'ai jama'a suka fara futa suna surutu cewar "dama tuntuni suna zargin yarinyar " yar ruwa ce to gwara da suka d'auke kayansu kowa ya huta.

***********
Tafiya suke suna hira irin ta abokai sai dariya suke ma junansu Salima na bayan mota da waya a hannunta tana chat fa friends d'inta, sam bata jin abunda suke cewa to suma k'asa-k'asa suke hirar su, har suka shigo Kano suka d'auki hanyar K'auyan d'an kunkuru Yusuf yace"Har na fara jin wata iska me dad'i wallahi" Dariya Hakkim yayi yace." Sai ma ka shiga garin sosai zakaji dad'insa shiru babu hayaniya sai manya bishiyu masu bada iska mai dad'i".

Wani dank'areran get nake hangowa tunda nesa nan naga Hakkim ya nufa da mota, wasu mutane dake tsaye bakin gurin suka bud'e masa get d'in ya shiga da motar ciki, sai da yayi tafiya sosai sannan ya samu guri yayi parking Yusuf ya futo daga motar yana fad'in"Wow kaga guri sai kace a k'asar waje Yaro" ? Murmushi Hakkim yayi ya kashe motar futowa yayi yana mik'a ta gajiya gurin kawai yake bi da kallo cike da sha'awa irin bokokin nan na k'asar waje hudu ne sai part biyu da gurin kiwo an kewaye shi na kaji daban na kifi daban na talo talo daban ko wanne an kewaye shi, gefan hannunsa kuma wasu manya-manya lambu ne a kewaye da raga k'ofar da mutum zai shiga tana can baya, da sauri yaja hannun Yusuf suka nufi gurin shiga Salima na binsu a baya tana tsalle da dariya fad'i take"Zanci d'ata in more abuna dama a abuja babu sai mutum ya sha wahala kafin ya samu. Suna shiga kowa ya kama gabansa domin kashe kwarkwatar idonsa , Hakkim ya nutsa sosai ciki, yaji motsi saman bishiya d'aga kai yayi da sauri, wata halitta ya gani ita ba mutum ba ita ba aljana ba, gabansa ya fad'i, dake namijin duniya ne sai ya dake yana hirji cikin zuciyarsa cikin jarumta yace"Ke wacece ke mutum ko aljana"? Ladidi ta tsura masa ido tana kallonsa,a zuciyar ta tace"Dube shi kyakyawa d'an burni yasa fararan kaya gaskiya yayi kyau"!! Buga mata tsawa! yayi a karo na biyu ya sake fad'in"Mutum ko aljan nace kun tsura min ido babu kyawun gani kuna kallo" Soso kanta tayi ta ciro kwarkwata har biyu, ta kalle shi ya kalle ta daga saman bishiyan ta sako masa kwarkwartar ta fad'o jikinsa, abunka da fararan kaya, aikuwa nan take suka nuna kwarkwata ga tanan tana bin gefen kafad'ar shi har guda biyu, tsalle! Ya buga ganin k'awaro baki na bin jikinsa ya bugeta cike da k'yamkyami ya tsartar da miyau! Ya d'ago kansa a fusace! Ganinta yayi mak'ale jikin bishiyar tana k'okarin sakkowa kamar me sufa, dura k'asa tayi yayi sauri matsawa baya gaban shi na bugawa! Amma idan ka kalli fuskarsa baza ka gane razanar sa ba,, cikin minti biyu ya gama k'are mata kallo, k'anjamammiyar yarinya mai k'irar muciya kanta wani gurin da gashi wani garin babu fuskarta a rame sai uban dogon hanci irin na aljani ga hannuta da k'afar ta k'ananu duk jijiya" hirji yake Cikin zuciyar sa, yace."Ke aljana ce ko mutum"? Kai tsaye tace"Aljana ce" Cikin tsawa yace"Bar nan yanzu don ubanki ko na zane ki, dagani ke ba aljana bace ibilishiya ce,me ya kawo nan har da hawa kan bishiya" ? "kar ka k'ara zagina" tafad'a idonta a kansa, a zabure! Yace"Ubanki uwarki kajini da shegiyar yarinya k'azama zo ki fuce daga gurin nan ko in karya miki k'afafu" ya k'arashe maganar yana zuwa kanta, wani tsalle ta buga! Ta d'ane jikin bishiyar mangwaro can kololowa, cikin mamaki ya d'aga kai yana kallonta, itama shi take kallo tace." Idan ka isa kazo ka Kore ni, bayan ma gonar ta kakana ce kuka sace mana" Hakkim ya saki baki galala! Yana kallonta ,wasu mangwaro ta Ciro sun gaji da nuna ta mulmulasu sukayi ruwa tafasa da bakin ta ta saita shi, ta jefo masa a jiki kafin kace me yayi fallatsi ya b'ata masa duk gaban rigar sa da fuskar sa.








*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/29, 6:51 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________



*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*



_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*Ayi hak'uri da errow⚠*


_Yau pege d'in babu yawa saboda ina fama da zazzab'i, ina b'ukatar addu'ar ku😓👏🏻_





*🅿12*




Cikin tsantsar b'acin rai! Ya d'aga kansa sama yana kallonta, tana k'okarin saukowa sai dariya take k'yalk'yala masa, tana dura k'asa ya cafki hannunta wanda yaji tamkar ya rik'e bushashan ice dan tauri, k'okarin fuzge hannunta take tana zabga masa harara tamkar idonta zai fad'o k'asa!. A fusace! ya kai mata wani wawan mari! ta kauce da sauri! amma duk da haka sai da ya samu gefan fuskar ta, zagi ta hau d'ura masa tana tsalle, kamar zata kai masa duka take fad'in "Sakar min hannuna ni ba " yar iska bace". Hakkim ya buge mata baki da d'aya hannun nasa, kafin kace kwabo jini ya fara zuba, ihu! ta kurma wanda yasa su Yusuf suka runtumo da gudu gurin. Hakkim na tsaye hannunsa tam! da na Ladidi sai buge-buge take tana kwanciya a k'asa dole sai ta k'wace daga hannunsa, wawan hauri ya kai mata da k'afar shi guda, ta k'ara k'wala k'ara tana kuza masa ashariya! Yusuf ya k'araso gurin, hankali a tashe yake fad'in"Wai meye yake faruwa ne? wannan yarinyar fa, daga ina".? Bak'in ciki da b'acin ya hana shi cewa uffan,sai cije baki yake yana dukanta da k'afar sa, Salima ta k'araso gurin jikinta a sanyaye take fad'in"Broth waye ya b'ata maka jiki da wannan k'azantar " Yusuf ya Kai dubansa gurin shi sam bai lura ba, hankalin sa na kan Ladidi, har hanzu hannuta na rike a nashi yana dukanta da k'afafunsa ita kuma bakin ta bai bar zaginsa ba, tana deb'o k'asar gurin tana watsa masa a jiki. Yusuf ya fara k'okarin kwace daga hannunsa, ya fuzge da k'arfin yayi wani mugun boll da ita ta gangara can gurin k'ofar futa kanta ya bugu da wani dutse, da sauri ta mike tamkar ba ita akai wa wannan dukan ba, wani mugun tsalle tayi sai gata a gabansa, dama ya tsammaci zuwan ta, k'afar sa ya sanya ya tad'eta! Ta fad'in a gurin a sume!! Yusuf ya saka salati yana fad'in"Shikkenan kaga ka kashe yarinyar mutane ko, innalilahi wa'inna ilahi raji'un"!! Salima ta fashe da kuka tayi kan Ladidi tana tattab'a jikinta, Yusuf ya futa daga gurin da sauri, gabansa sai fad'uwa yake, ashe k'addara ce ta kawo shi, shi ko Hakkim ko a jikinsa, karkad'e rigar sa yayi cike da bak'in ciki da b'acin rai! Yake k'okarin barin gurin,Salima ta rik'e hannunsa tana kuka take fad'in"Broth ina zakaje LA tsaya ka duba wannan yarinyar ko suma tayi don girman Allah, ni kam Wallahi da nasan haka zata faru da ban biyo ka ba" . Fuzge hannunsa yayi cikin b'acin rai! Yace"Yanzu ma kina iya komawa gida babu Wanda ya rike miki k'afafu ga hanya nan" yana gama fad'in maganar shi ya futa daga gurin. Karo suka ci da Yusuf ya tawo da sauri hannunsa rike da robar ruwa na faro, ko kallonsa bai yi ba yayi fucewar sa.







*COMMENT VOTE AND SHARE*
[9/30, 10:08 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




*NA*
_BINTA UMAR ABBALE_
~*®BINTUBATULA👄*~



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

_*LOODING:*_
_*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________


_Alhmdullahi jiki yayi sauk'i_

*Gaskiya naji dad'i sosai da kularwar ku akaina nagode masu kirana a waya kuna yimin ya jiki da fatan samu lafiya,masu min sannu ta pravite wanda na sani da wanda ban sani ba nagode sosai da sosai ina muku fatan alkairi*




*Jan kunne⚠*

_Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin book d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ ki siyar min da littafi ba da sanina ba, Wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan haka, hattara dai!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje yaci gumin sa, kane mi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka_




*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*




_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿13*




Cikin sauri Yusuf ya k'araso gurin da Ladidi take kwance, ya bud'e ruwan,ya fara zuba mata a fuskar ta furgice! ta mik'e zaune ta k'wala k'ara! Waige-waige take tana neman Hakkim a gurin, Salima ta rik'e hannunta tana son tayi mata magana. Fuzge hannunta tayi da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in" Yana ina."? Duk suka mik'e suna kallonta, Yusuf yace." Ke yarinya me ya shigo dake gurin nan?,da har kika jawo wa kanki suma." Banza kallo tayi masa ta murgud'a bakinta, bata ce masa komai ba, ta bar gurin bagazan-bagazan! kallo suka bita dashi, Yusuf ya kalli Salima yace." Anya kuwa yarinyar nan me lafiya ce"? Salima ta k'unshe dariya tace." Lafiyan ta lau. Kamar ka manta da a k'auye kake dole kaga haka." Yusuf ya girgiza kai yace." Ni abunda ya bani mamaki da ita shine yadda ta shigo gurin nan wallahi". "Gaskiya nima nayi mamaki." Salima tafad'a yayin da suke k'okarin futa dafa gurin.

********
Ta inda ta shiga gurin tanan ta haura ta futa Hakkim na kallonta tun futowar ta har lokacin da take haure katangar yana gani, zuciyar sa yana mamakin ibilicin yarinyar, yau d'in nan zai sanya a kewaye katangar gurin, da waya mai k'ayoyi, duk saboda ita dole kuma a zuba masu gadi a gurin. tuni ya cire kayan da ta b'ata masa ya watsar dasu harabar gurin, domin mugun k'yamk'yami ne dashi, idan ya tuno halittar yarinyar sai yaji zuciyarsa tana wani irin tashi! sosai zuciyar sa take masa zafi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya tab'ai masa irin abunda yarinyar tayi masa dole ne ya d'auki mataki akanta mutukar ya kara ganin k'afarta a gidan, karya ta zaiyi kawai kowa ya huta. Su Yusuf suka k'araso gurinshi ya sha kunnu domin baya son ma yayi masa maganar, Simi-simi Salima ta shiga ciki, Yusuf ya samu kujera ya zauna yana kallon Hakkim d'in, da yake k'ara yin kicin-kicin da fuska, yace." Zauna zamuyi magana da kai". A fusace! Ya juyo yana fad'in"Ubana ne kai zaka bani umarni". Yusuf ya kalleshi , da alama zuciyar sa har yanzu batayi sanyi ba. Yace." A'a ba ubanka bane". "To ka fad'i duk abunda zaka fad'a kunne na yana ji". Ya k'arashe maganar yana juya masa baya. Yusuf ya mik'e ya k'arasa inda yake, kafad'arsa ya dafa cikin taushin murya yace." Aboki wai me ya faru tsakanin ka da yarinyar nan? Wallahi hankalina ya tashi sosai domin ta dad'e kafin ta farfad'o,haka kurum daga zuwanmu guri zakayi kisan kai saboda zafin zuciya". Hakkim ya juyo yana fuskantar sa, cikin kaushin murya ya fara fad'a masa abunda ya faru. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." Gaskiya kam yarinyar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On LADIDI KWADAGA
avatar
north

1 year ago

Reply

dadi

Please Login or Register in order to submit comment