Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ba tayi maka dai-dai ba,amma kai ma bai kamata kayi mata irin wannan dukan ba,saboda yadda na lura da ita kamar irin yaran nan masu lalurar k'wak'walwa kasan k'auye ko d'ansu na cuta basa mai da hankali sai abu yayi tsanani, sannan zaka gansu sun nufi asibiti hankali a tashe." Zuciyarsa ce fara sanyi ya zauna kan kujera guda Yusuf ma ya zauna kusa dashi, yace." Ka bari kawai Yaro wallahi zuciyata a lokacin ji nake tamkar na kashe ta na huta da b'akin ciki." "Kayi hakuri don Allah ka rage zafin zuciya." Yusuf yafad'a yana dukan kafad'unsa.


Salima ya k'walawa kira, tana can ta shagala da kallon yadda aka tsara falo da kayan jin dad'i da more rayuwa, har ta kunna kallo tanayi taji kiran big broth amsawa tayi ta mik'e da sauri, tana zuwa yace." Ki shiga kchin kiyi mana abunci." "Angama big broth" tafad'a cike da bin umarni, kai tsaye kichin d'in ta nufa, gashinan komai akwai na amfani nan take ta fara aikinta.



**********

To can gidan su Ladidiya kuwa Mai koko ta saddak'ar ta fawwala wa Allah cewar Ladidi ta mutu cikin rijiyar don haka mutane sun cika gidan ana yi mata ta'aziyya, Jama'a sun kewaye ta, tana zaune da carbi a hannu ga idonta yayi jajazur! taci kuka ta k'oshi, D'alha na waje da mutane zazzaune kan tabarma, sam yak'i yadda cewar Ladidiya ta mutu cikin rijiya k'wak'walwar sa tafi tunanin yarinyar tana can gurin gantalin ta, shiyasa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zurga-zurga yake a gurin. Duk Wanda yazo gurin sai ya hau yi masa gaisuwa, ko kallon su baya yi

*********
Tafiya take fakam-fakam!! sak'e-sak'e kawai take a zuciyarta da tunanin d'aukar fansa kan, d'an burni,sunan da ta sama sa kenan, wallahi bai dake ta a banza,sai ta rama duk hanyar da zata bi ta sani, leb'anta ta tab'a da hannunta, cire hannuta tayi tana girgiza kai! a fili tace."Wallahi he na rama idan ubanka ne shugaban k'asa he na rama, nima sai na fasa maka baki,hummm!! Zaka san ka tab'o Ladidi jikar Mai koko, bana barin takwana kuma bana manta ranar d'aukar fansa." Da tafiyar ta ya gane i tace jiki na rawa ya k'wala mata kira,"Ladidi" da sauri ta juyo tana waigen idan taji ana kiranta. Kakanta ne D'an fulani, yake tawo wa inda take, yana can gurin kiwo labari ya same shi na mutuwar ta,shine ya tawo cikin tashin hankali! Abun mamaki kuma sai gashi ya ganta a hanya, yana k'arasowa inda take ya damk'i hannuta, bai ce mata komai ba suka fara tafiya, zub'uro baki tayi tace." Ni ka sake ni ka rik'e min hannu da k'arfi ai gida zani ba wani guri ba." D'an Fulani yayi mata shiru, shi dai k'okarin shi kawai yaga ya danganata da gida,hankalin kowa ya kwanta. Tun daga nesa jama'ar dake gurin suka hango tawowar su, sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, da suka tabbatar da cewar itace sai kowa ya fara zura silafas d'insa yana guduwa, D'alha ya juya yaga wayam! babu kowa a gurin, girgiza kai kurum yayi yana jin wani d'aci cikin zuciyarsa wato Ladidi ta zama abun tsoro kenan? D'an Fulani ya d'amk'ata a hannunsa yana fad'in"Gatanan can wajejan titi na gano ta tana tafiya ita kad'ai." D'alha ya sauke ajiyar zuciya yace."Alhamdullahi, dama ni jiki na bani yarinyar nan tana raye,amma jama'ar gari suna ta fad'in ta mutu a cikin ruwa,Allah nagode maka daka bayyana mana ita ko hankalin Mai koko ya kwanta." Sai sanan Ladidi ta tuna da abunda ya faru d'azu tsakaninta da Mai koko, dariya ta kece dashi,hahahaha! D'alha ya gaura mata mari! Yana fad'in"Rufe miki don buhun ubanki, shashasha, shakatafe, naga ranar da zakiyi hankali dai" D'an Fulani kuwa a'lamarin Ladidi ya fara bashi tsoro,don haka yace."D'alha mu shiga cikin gidan sai mu San abun yi." Kai tsaye cikin gidan suka shiga.




*Tofaa ko ya zata kasance idan jama'ar gidan sukaga Ladidi Wanda suka dauka ta mutu cikin rijiya,ko yaya Mai koko zatayi in taga Ladidi? To Ku cigaba da bina dai cikin labarin domin in warware muku*






*COMMENT VOTE AND SHARE*
[10/2, 5:54 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________





*ALHAMDULLAHI*

*HAUWA S ZARI'A*
_Maman Usuwan_

*Ina taya ki murnar kammala littafin ki HAKA ALLAH YA NUFA _KADDARA TACE_ ALLAH YA KARA BASIRA YASA SAKON KI YA ISA INDA KIKE SO*
____________________


*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*




*🅿14*





Suna k'okarin shiga da ita cikin gidan tana turjewa D'alha ya kwad'e mata k'eya yana fad'in "Zaki wuce muje ko kuwa,? Kin tayar wa da mutane hankali, gidan buhun ubanki zaki je ne" Ihu! Ta kurma, wanda yasa Mai koko da sauran jama'ar gidan mik'ewa tsaye da sauri sukayo waje suna salati! Kafin su rufe bakinsu, sai ga Ladidi an shigo da ita tana turjewa! Mai koko ta bude baki zatayi magana D'alha ya katse ta hanyar cewa." Don Allah kar Ku tsorata da ganin ta, dama na fada muku tana raye bata mutu ba, ga shi a can bakin titi d'an Fulani ya gano ta,wanda shima labari ne ya riske har inda yake kiwo cewar ta mutu." Mai koko ta k'araso gurin da jiki a sanyaye zuwa yanzu itama ta fara tsorata da al'amarin Ladidi, da muryar ta wacce tasha kuka ta gaji tace. " Ladidiya dama baki fad'a rijiya ba, me yasa kika yi min haka Ladidi"? Turo baki tayi tace." Nifa ban fad'a rijiya ba, kinga gurin dana b'uyar miki fa" Mai koko tabi hannuta da kallo, cike da mamaki da al'ajabi Matan da suke tsatstsaye a gurin, duk suka tsure sai zare ido suke burin su kawai su bar gidan, Mai koko tace." Me yasa to duk aka duba ba a ganki ba"? Shiru tayi mata, D'alha ya dubi matan dake tsatstsaye, yace." Ko wacce tana iya tafiya" aikuwa kafin kace kwabo duk sun zura takalman su, suna bangazar juna suka futa daga gidan, ko wacce cikin ta ya d'uri ruwa. D'an Fulani yace." Ku zauna zamuyi magana ta fahimta" Mai koko taja hannun Ladidi suka zauna kan tabarma. D'alha suka zauna gan benci, D'an Fulani ya kalli Mai koko a nutse yace." Al'amarin yarinyar nan ya soma bani tsoro saboda haka na yanke wata shawara." Mai koko tace." Ai kana da iko akanta tunda kai ka haifi mahaifiyar ta." Yace." NA yanke shawarar cewa gobe insha Allahu zan kawo malamin ruk'iya zai yi mata idan da makarai a jikinta sai a sulhun ta dasu"

Shiru tayi na minti biyu, ta d'ago kai tana kallonsa, tace." Ba wai nak'i taka bane, gaskiya ka janye maganar ruk'iyar nan,domin su wad'annan mutane ba a haka dasu, idan kuma basu suka rab'e ta b,kaga sai a jawo mata su da hujja, abar maganar ruk'iya mu cigaba da yi mata addu'a" Dan Fulani da D'alha suka kalli juna, girgiza kai kurum D'alha yake yasan dama Mai koko baza ta yarda ba, shi ko D'an Fulani saboda tsabar haushi da takaici bai sake cewa komai ba. Ya mik'e yana musu sallama, sama-sama Mai koko ta amsa masa, D'alha ya mik'e domin ya raka shi. Mai koko ta dinga rarrashin Ladidi, da lallab'ata tamkar ba wacce tayi mata laifi ba, tace." Tashi ga ruwan zafi can muje kiyi Wanka ko"? Mak'ale kafad'a tayi. Tace." Akwai miyar kifi nan a fulas na aje miki sai ki siyo buredi" Mik'ewa tayi zaune tana Sosa kai tace." Amma ni zanyi wanka na gaskiya" tace." E amma zan cud'a miki baya." Mik'ewa tayi tana tube kayan jikinta ita kuma ta nufi kicin din, bakin rijiya ta tsuguna tana wasa da ruwan Wanka, Mai koko ta k'araso da abun sabulu a hannuta tace."Ladidi waye ya fasa miki leb'e haka? Ko garin tsalle-tsallen ki ne"? Hannuta tasa ta shafo gurin, girgiza kai tayi tace." Wani d'an burni ne, kawai babu abunda nayi masa don zalin ci." "A'a Ladidi nasan halin ki fa"? Iya tafad'a tana murza sabulu jikin soso. " Kawai don na shiga gonarmu shine ya doke ni" "Wace gona kuke da ita Ladidi'? Iya. Ta fada cike da mamaki! " Ranan da zamu wuce Kawu ya nuna min gonar tun kafin a gina gurin yace."Tasu ce da babana." "To yanzu na gane inda kika dosa" Iya tafad'a tana durzar jikinta da soso, ta cigaba da cewa " Ladidi kin cika futuna me ya kai ki gurin nan, yanzu bs gonar su bace, domin sun siyar da ita dalilin haihuwar ki, ranar bakiji Kawun ki yana fad'in wani mai kud'i ya siya har da tasu Malam Tanimu da Manu ba" girgiza kai tayi tace." Ni babu ruwana ko sun siyar ko basu siyar ba, in naga dama zanje ne" Mai koko tace." To sai ki kiyaye domin mutanan burni ba dai-dai suke da na k'auye ba." Zumb'ura baki tayi tace." Aiko sai na rama abunda yayi min ko shugaban k'asa ne ya haife shi." Mai koko dai shiru tayi domin bata so ta tsanan ta mata kar ta sake guduwa.



Kawu D'alha kuwa akwai abunda ya k'udura a ransa kan Ladidi. Sai da ya tabbatar da sunyi bacci sannan ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mai koko ya nufa, dama duk ranar da tayi ibilincin ta. To in ta kwanta bacci bata motsawa sai gari ya waye, Mai koko ma bacci take sosai ansha fargaba an gaji, reza ya futo da ita daga cikin aljinunsa ya kwance d'aurin d'ankwalin Ladidi a nutse a shafa sabulu da ruwa ya soma yi mata aski babu abunda ya dame shi. Har D'alha ya gama aske mata kai bata motsa ba, ya mayar mata da dankwalin ta ya daure mata kanta kamar yanda tayi, ya sunkuya ya tattare gashin da zube k'asa ya zuba cikin leda shara ya zuba yasa omo ya wanke hannunsa tass!!! . Ladidi bacci tayi sosai da sosai sam bata san inda kanta yake ba, sai wajan shiga da rabi na safe ta tashi lokacin Mai koko ta Dade da tashi tana can tana hidimar huta huta domin ta d'ora ruwan kuka. D'ankwalin ta take laluba kan shinfid'ar ta d'auka zata d'aura akanta tana tab'awa taji sumul tamkar gwiwa hannuwa biyu tasa tana shafawa, Ihu!! Ta kurma tana fad'in "Wayyo!! Mai koko wani ya aske min kai na" Mai koko ta aje icen dake hannunta da sauri ta nufi dakin. Tana shiga taga Ladidi ta d'ora hannu aka tana kurma ihu! Ga kanta sumul! Babu k'wallin gashi ko d'aya, cikin mamaki tace."Ladidi waye yayi miki k'wal kwabo hak..... Kafin ta k'arasa muryar D'alha ta katse ta inda yake cewa." Iya nine nayi mata aski saboda in cika rantsuwa bayan haka kuma da wahalar da ta bamu jiya, shiyasa na yanke wannan hukuncin a kanta."






*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_






*🅿15*






Mai koko tace." To kinji inda maganar take, don haka sai kiyi hak'uri kinji da kunnen ki,wanda ya aske miki kanki." D'alha ya kalle ta cikin taikaci ya buga mata tsawa tare da fad'in."Rufe min baki ko inzo k'ara fasa miki shi,shashasha kawai!! Gum! tayi da bakin ta dama kukan babu hawaye sai dai ihu! Sai dai kana kallon idonta kasan tana cikin b'acin rai! Yarinya 'yar shekara goma sha biyu ta san d'aukar fansa, abunda take ta raya wa kenan cikin zuciyar ta Kawunta da d'an burni sai ta rama abunda sukayi mata. Mai koko ta kalleta ganin yadda take ta sauke ajiyar zuciya yasa ta sassauta murya tace." Yanzu ke kanki zaki ji dad'i kuma iska zata shiga kanki sosai kinga kin rabu da kwarkwata har abada,domin wani sabon gashi ne zai futo miki." Banza tayi mata. Kawu D'alha ya futa ya barsu a d'akin, Mai koko dai da taga tak'i kulata sai ta futa ta k'yaleta tana addu'ar kat Allah yasa ta b'ullo da wani abun kuma. Aikuwa futowa tayi babu d'ankwali a kanta nufi gidin rijiya, 'yan siyan koko suka bita da kallo, tuni wasu daga cikinsu suka fara futa waje cikin tsoro ganin kan Ladidi a cikin rana sai k'yalli yake, Mai koko tace." Ya kuke futa kuma kowa ya tsaya a sallame shi." Wani Yaro yace." Iya wacece wacan kamar Ladidiya ko." Iya ta kalli inda Yaron yake nunawa Ladidi ta gani da buta a hannu tana durzar bakin ta da dakakkaken gawayi kanta sai k'yalli yake cikin hasken ranar da ya fara futowa, cikin takaici tace." Ladidi ke ko kika futo babu Dan kwali ko kunyar k'awayen ki baza kyaji, ki koma ki dauro dan kwalin ki." Kuskure bakinta tayi tace." Daga yau na bar d'aura d'ankwali wallahi haka zan dinga yawo da kai na, kuma duk yaron da ya tsokane ni, inci Ubansa." Jiki a sanyaye Mai koko ta juya ta cigaba da abunda take cikin zuciyar ta take fad'in"Ba a rabu da bukar ba an haifi Habu,dama ni nasan wata futunar zata k'ara b'ullo da ita."
Tana gama Alwalar ta bar gurin. Wani tsohon buhu ta kwance nan kayan ta na sawa suke ta ciro wata doguwar riga irin ta kanti duk taji jiki dan wani gurin ma d'inkin ya soma zarewa gashi ta tattare sosai ta d'angale mata duk k'waurinta a waje ta saka, ta zura hijabin da take sallah ta tayar da sallah.Bayan ta idar ta tub'e hijab d'in ta aje shi kan gado, haka ta futo babu d'ankwali kai tsaye hanyar futa ta nufa, tunda ta doso gurin suka fara matsawa kowa na k'okarin ya bata hanya kar ta make shi, ball tayi da kofin Alawiyya dake bisa layi, Iya ta juyo da sauri tana fad'in." Kar Ku har gitsa layin fa.' Ladidi ta gani tana k'okarin futa,da sauri tace." Ina zakije a haka sai da nace ki d'aure kanki ke ku kunya ba kya ji." Ko kallonta ba tayi ba ta fuce abunta,girgiza kai kurum tayi ta cigaba da aikin ta tan addu'ar Allah yasa Kawunta na waje ya koro ta, aikuwa D'alha na tsaye da kayan sana'arshi suna gaisawa da mak'ocin su Yahaya,suka had'a ido dashi, sam bata tsorata ba. Ta fara k'okarin wuce shi,tsawa ya buga mata yana fad'in"Koma ki d'auro d'an kwallinki" Ido jazur! Ta koma ta cikin gidan, D'alha yayi sallama da Yahaya ya kama hanya ya tafi, lab'ewa tayi bayan k'yaure sai da ta tabbatar da yayi nisa sannan ta futo, tana ganin Yahaya yana gyara kwatar gidansa, ta galla masa harara, yana sunkuye bai sai abunda take ba, sai saukar Abu yaji a jikinsa, da sauri ya dago yana karkad'ewa sai ga tarkacan da ya kwaso daga kwata suna fad'owa k'asa, bayan rigarsa duk ya b'aci da kwata, waige-waige yake yana neman yaron da yayi masa wannan sha'ani, ido hud'u sukayi da ita, zabura! Yayi ya matsa gefe guda baki na rawa yace." Lad..ladid..katsaye shi tayi ta hanyar fad'in" Jiya har da kai gurin cewa na mutu har kuna shimfid'a tabarma da zama, to ban mutu, kuma duk sai na kashe Ku." Cikin Yahaya ya bada sautin kulululu!! Bakin sa sai motsi yake, zare masa manyan idonta tayi, ganin yanda yake gumi! ne yasa ta k'yalk'ale da dariya "hahahahahaaaa! fyallawa tayi da gudu ta barshi tsaye a gurin,saura kad'an ya saki futsari.
Cikin mutuwar jiki ya zauna kan dakalin gidansa yana sauke ajiyar zuciya,sai zare ido yake.


Babu inda tayiwa tsinke sai gidan gonar su Hakkim, tana isa ta tarar da an kewaye katangar da waya mai fasa k'afafu dan wani gurin ma har da k'ananun k'walabe, b'uya tayi wani gurin tana tunanin ya za'ayi ta shiga gurin. Can taji motsi an bude kofa, lek'awa tayi kad'an , d'an burni ta hango ya futo daga ciki jikinsa sanye da singlet da wando iya gwiwa 3quetar, suna magana da wani me wanki takalmi, tsura masa Ido tayi tana girgiza kai, a fili tace." Wannan girman jikin naka da wannan k'wanjin naka da wannan murd'ewar taka, duk baza su hanani in d'auki fansa akanka ba, hummm! Ko Kaine Singam gurin k'arfi sai na rama fasa min bakina da kayi." Tana kallonshi suka gama magana da me gyaran takalman ya koma ciki ba tare da kulle k'aramar kofar ba. Da sauri ta futo daga gurin b'uyan ta, kamar walkiya tazo ta shige ciki, Mai gadi nacan na fama da redi'o a hannu, wata bukka ta shiga ta b'uya Kansan kujerun hutawar dake ciki, tana kallonshi ya futo daga wani d'aki hannunsa ruk'e da takalma biyu ya kara futa waje, wuf! Ta futo daga farko inda take, ta afka inda taga ya futo, Sam had'uwar falon ba ya gabanta burinta kawai ta d'auki fansa, ba ta tsaya kalle kalle ba ta afka wani d'aki da tagani a bude, tana shiga ta fara zare ido motsin ruwa taji a band'aki, da sauri ta matse jikinta ta b'uya bayan gado. dama kar ku manta Ladidi bata da k'iba siririya ce sosai, Yusuf ya futo daga toilet yana goge jikinsa da towol, sauri sauri ya sanya kayansa. Ya tsaya gaban mirror yana shafa mai ajikinsa, Hakkim ya shigo d'akin hannunsa rike da takalman su an wanke su tas sai kyalli suke, Yusuf yace." Ka dame ni na tashi na shirya gashinan dai na shirya sai kayi sauri kaima." Zube takalman yayi a gefe guda, toilet ya nufa yana fad'in" Yanda kake da nauyin bacci idan ba haka nayi maka ba ai baza ka tashi ba." Yusuf yace.'' Son bacci da nauyin bacci har na kai ka." Shiru yayi masa ya shiga toilet din, shi kuma yana gama abunda yake ya futa farlor, Ladidi duk tana jinsu, tasan Hakkim ne ya shiga band'aki, futowa tayi daga inda take, ta zauna gefan gadon gami da tsurawa kofar band'ankin ido tana dakon futowar sa. Jikinsa d'aure da guntun towol ya futo cin yoyinsa duk a waje domin babu gajeran wando,a jikinsa dama da k'yar towol d'in ya ratsa masa jiki, yana futowa idonsa ya sauka a nata, tana zaune ta d'ora kafa d'aya kan d'aya, kanta sai k'yalli yake, sam! Bai gane ta ba, domin duk hattun ta sun sauya. Da k'arfi! Yace." Auzibillahi minashaid'anirrajim"!!!! Nan take ya fara karantun ayatul kursiyo, har yanzu idonsa na kallonta itama ta k'ura masa ido k'urrrr!!









*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿16*



Cikin abunda bai fi second guda ba ya ganta a tsaye kan allon gado,kafin yace me ta buga wani tsallen ta sauka kan dressing mirror, tuni kayan shafa suka fara fad'owa k'asa suna fashewa,ta sanya k'afarta guda ta fara ball da sauran suna fad'owa kan 'yan uwansu, d'aya k'afarta tasa ta baya ta daki! mirror d'in ya tarwatse! Dura k'asa tayi ta tsaya gami da rik'e k'ugu! tana kallon sa. Hakkim kuwa jikinsa duk ya jik'e da gumi! Tamkar ba daga wanka ya futo ba, zuwa yanzu yasan mutum yake tare dashi ba aljan ba,saboda lokacin da take ball da kayan shafar sa ya kalli k'afarta,sosai ya tsorata da ibilicin wannan hallitan mace ko namiji domin dai ya kasa gane wani jinsi ne, k'aramin towol d'in dake rataye a wuyansa ya ciro ya goge gumin goshin sa, ya jefar dashi k'asa,rai a b'ace ya durfafi inda take. Tana tsaye turmin danya tana sauraron isowar sa, sam ya manta da kwalaben da ta fasha,kwalba ta caki k'afarsa me mugun tsini kafin kace kwabo jini ya fara zuba yana bin tayal cije baki yayi cikin azaba! Ladidi ta kwashe da dariya "Hahahahaha" tana nuna shi da hannu,d'ago kansa yayi yana kallonta,shan kunu tayi tace." Ni ce wannan yarinyar ta jiya daka doka na fad'a maka dama sai na rama,ko shugaban k'asa ne ubanka. Hehehhaaha." Ta k'arasa maganar tana mahaukaciyar dariya. Cikin tsananin fushi ya cire d'aya k'afar tashi da niyar d'amk'ota, k'afar ta caki! Wata kwalbar turare me tsini! K'ara! ya saki yayi taga-taga zai fad'i, da sauri ya dafe towol d'in jikinsa da yake barazanar fad'uwa k'asa, saboda sanin halin da yake ciki shi kadai ne a jikinsa, gwiwar sa ya sanya a gurin ya sanya hannunwa ya dafe k'asa sai cije baki yake, idonsa ya kad'a yayi ja, jini kuwa duk ya b'ata gurin. Kan gadon ta hau tayi tsaye tana kallonsa, Tace." Naji dad'i na rama abunda kayi min gaba ma sai ka k'ara dukana kaga abunda zanyi maka." Tana gama maganar ta ta dura k'asa, bude kofa tayi ta futa daga d'akin, Salima da Yusuf na tsaye harabar gurin suna jiran futowarsa kawai sai suka ganta ta futo,bagaz-bagan! ta wuce fuuuuu! tamkar zata tashi sama! Cike da tsoro Yusuf ya shiga ciki,Salima kuwa kin shiga tayi,domin ba k"aramin tsorata tayi ba, ita kam da tasan wannan masifar zata gani da bata biyo su, ba k'afafunta sai rawa suke ta nemi guri ta zauna,cikin zuciyarta take cewa gaskiya gurin nan akwai aljanu insha wata k'ila Dady bai sa anyi saukar alk'urani me girma a gidan ba. Cikin jarumta ya mik'e tsaye da sauri ya bi bayanta,yana jin in ya kama yarinyar nan to sai dai idan uwarta ta haifi wata domin har in bai kashe ta ba to sai yayi mata muguwar illah a rayuwarta, wani irin suka da azaba! Tafin k'afafun shi suke yana jin shigar kwalbar jikin jikinshi bai damu ba, bud'e kofa yayi a fusace! Suka ci karo da Yusuf ya shigo a razane! ganin fuskar Hakkim d'in babu rahama ko kad'an, yasa ya duburburce yace." Yaro wai meke faruwa ne,waye ya futa yanzu mace ko namiji? naga yaro ya futa yanzu, ina cikin rud'u fa,anya gurin nan babu aljanu kuwa." Shiru yayi masa cikin k'arfin hali ya nufi kofa da niyyar futa. Yusuf ya bishi da kallo yana kallo yadda yake Jan k'afa ga jini duk ya b'ata gurin, da sauri ya bishi ya dafa kafad'ar shi,yana fad'in." Wai ina zaka ne cikin wannan halin."? A hasale yace." K'yaleni malam." Yusuf yaje ya rufe kofar futa da key ya zura a aljihun sa, yace." Babu inda zakaje sai ka fada min abunda yake faruwa, yanzu fa na futo daga d'akin lafiya Lou amma dubi wani abun al'ajabi. " yace." Zo ka bude min kofa." Yusuf yace." Bazan bude ba wallahi." Wani uban naushi! ya kaiwa kofar da hannuwansa yana fad'in." Yusuf wallahi suma tallahi idan idona ya k'ara ganin yarinyar nan, to ina me tabbatar maka da cewar sai dai uwarta ta haifi wata,wallahi duk shad'aicin ta,sai naci ubanta sai na ragargaza ta, ni zatayi hakaaaaa."!!!!!! Salima na daga waje ta ji ihun Dan uwanta a tsorace ta fara buga kofar tana kuka, Yusuf ya bud'e mata ta shigo yayi saurin mai da kofar ya rufe, cikin mawuyacin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On LADIDI KWADAGA
avatar
north

1 year ago

Reply

dadi

Please Login or Register in order to submit comment