Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

motsa idonta a hankali -a hankali ta bude tana kallon Iya, tayi saurin dafe kanta tana rumtse ido! Da sauri Mai koko ta rike hannun tana yi mata sannu, da k'yar tace." Iya bani ruwa insha wayyo kaina!!!! Iya ta mike da sauri ta d'ebo mata ruwa. Ta tashe ta zaune tare da karata a jikinta ta fara bata ruwan. Kad'an tasha ta kauda kanta.
Mai koko tace." LADIDI ina kikaje waye yayi miki wannan dukan. "? Kamar da dutse take magana. ta kara maimaita maganar tata. Ladidi batasan ma tanayi ba
hannunta ta tab'a tare da fad'in ." magana nake miki fa." Da k'arfi tace." Iya me kika CE." Itama Iya sai ta bud'e murya sosai tace." Cewa nayi waye ya doke ki haka har ya kumbura miki fuska tare da zubar miki da jini."?
Kuka ta fashe dashi tace." Wani d'an burni ne ya doke ni babu abunda nayi masa kawai don na zo wucewa Iya Allah kuwa sai narama bazan barshi ba."
Cike da takaici da jin zafi tace." Ai nima bazan barshi ba,sai nabi miki hakkin ki, domin bazai shigo garinmu yaci albarkaci na kuma ya doke ki har da zubar miki da jini kowa daga ya tashi muguntarsa sai yace ke,to sai nabi miki hakkin ki, ko dame yake tak'ama kuwa.". Kuka sosai Ladidi take, hankali Mai koko ya kara tashi, tunda taga Ladidi na kuka tabbas tana jin jiki.

*********

K'arfe biyar shaura kwata sun shirya tsaf! suna tsatsaye a harabar gidan suna jiran futowar general, kana kallon fuskokinsu kasan suna cikin damuwa, mussaman Hajiya Asiya.
General ya futo cikin sauri yana d'aura agogo hannunshi, duk ya bisu da kallo, yace." Ina Hakkim d'in yake." Yusuf ya sunkyar da kanshi yace." Bai futo ba." Cikin b'acin rai! General yace." Maza jeka kira shi,Hakkim yana so mu sanya k'afar wando guda dashi wallahi." Salim yace." Dady kayi hakuri
" ko kallonsa baiyi ba ya shiga mota Mama da Salima suka bude suka shiga. Minti biyar tsakani sai gasu nan sun futo Hakkim sai cin magani yake, Dady yayi k'wafa yana girgiza Kai cikin zuciyarsa yace." Zakaci malafar ubanka ne yaro."
Yace." Ka shiga kayi driving domin babu wani direba da zan d'auka. " zuciyarsa babu dad'i ya shiga motar gami da kunna ta, suka futa daga gidan.

********
Hankali Mai koko bai k'ara tashi ba sai da taga tana yiwa Ladidi magana tana shiru tamkar bata ji ba,sai ta d'aga murya sosai sannan take amsa mata, tace." Oh! ni 'yarnan Allah yasa wannan mugun mutumin bai lahanta miki kunne ba." Jira kawai take D'alha ya dawo domin tafad'a masa hankalin ta yayi mugun tashi, duk da ta gaggasa mata jiki tare da shafe mata jiki da Robb hakan bai hana ta cize baki ba,daga an tab'ata zata kurma ihu!! Jikinta duk ciwo yake.
D'alha ya dawo a gajiye ya Tatar da wannan tashin hankalin ,Iya ta kwashe komai ta fada masa hankali sa ya tashi shima ya kwatanta kiran Ladidi shiru sai da ya d'aga murya sannan taji shi, nan ya k'ara tambayar ta abunda ya faru, tana kuka ta warware masa komai.
Shikam bai yadda ba yafi yadda da cewar wani abun tayi masa shine shi kuma ya mata wannan dukan, tunanin mafuta kawai yake, d'an jarinsa bai taka kara ya k'arya ba shi zai rusa dole ya kaita asibitin burni a duba mata kunnuwan ta, tun kafin Abu yayi tsanani, dama asibitoci suna kuka dasu mutanan k'auye cewa basa tashi zuwa asibiti sai sunga cuta tayi tsanani, shikam baya fatan haka.

******
Gudu yake shararawa General ya buga masa tsawa! tare da fad'in." Ka jamu a hankali ka kaimu ko muma za ka gwada mana zafin zuciyar ne, sai faman gudu kake damu a mota kamar Wanda zai bar gari."
Hakkim ya rage gudun da yake, yana jin wani daci a zuciyarsa wai yau shi Dady yakewa tsawa kan wata bare yarinyar da bai sani ba, kwata-kwata ya kasa fahimtar shi, fad'a sosai General ya dinga yi masa har suka Isa Kano bakinsa baiyi shiru ba, Hakkim duk ya koma kalar tausayi saboda abunda bai saba ne, Yusuf ne dinga bawa Dady Hakuri,shima Yusuf din ya samu rabonsa, sai yaja bakinsa yayi shiru cikin zuciyarsa yake cewa" da alama allurar soja ce ta motsawa Dady.








*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿21*




Sai bayan sallahr magariba suka isa K'auyan D'an kunkuru, Dady ya futo daga mota yana hamdala ga Allah, gurin yake bi da kallo sosai yayi kyau ya k'ayatu haske fitila ko ina,nan ya jagoran ce su suka shiga ciki domin su samu nutsuwa suyi sallah, in yaso ko meye sai ya biyo baya.
Sallolinsu sukayi suka ci abinci, Dady ya kalli agogon dake manne a bangon farlon takwas da rabi na dare, ya kalli Hakkim da fuska a turb'une yace.'" Yanzu dai ka huta sai ka tashi ka fara laluben inda yarinyar mutane take domin inyi abunda ya kawo ni garin."
Ya d'ago kanshi dake sunkuya yace." Dady dare yayi yanzu ga hanya babu kyau ga yanayi na damuna gari duk ya jike kayi hakuri sai Gabe."
Tsawa! Ya buga masa tare da fad'in." Bana son wata banzar magana ka tashi ka fara laluben yarinyar nan da halin da take ciki."

Mik'ewa yayi da sauri Yusuf ya mike shima suka futa tare.
Dady yace." Ai ka jawowa kanka tunda kai kace me kunnen k'ashi ne."
Cikin d'ari-d'ari Hajiya Asiya tace." Ayi hakuri Yallab'ai." Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da girgiza k'afarsa guda.


Tsaye suke a harabar gurin suna shawarwarin me za suyi. Hakkim ya nufi gurin masu gadi jikinsa duk yayi sanyi fad'an Dady ta soma damunshi, Sam! bai saba ba.
Suna ganinshi ne suka nutsu nan ya k'arasa gami da mik'a musu hannu suka gaisa a mutunce. Sai ya rasa me zai ce.
D'aya daga cikinsu yace." Akwai abunda za'ayi ne Oga."? Girgiza kai yayi alamun a'a yace." Tambayar ku kawai zanyi."
Sukace Allah yasa mun sani.
"Wata yarinya siririya nake tambaya zaku ganta fara 'yar fulani k'azama yarinyar bata da kintsi tana tafiya kamar mahaukaciya ko kun santa."
Shuru sukayi na minti biyu daga bisani suka had'a baki gurin fad'in." Gaskiya ba mu gane yarinyar ba domin kasan yaran K'auyan nan suna da yawa kuma dai duk haka d'abin ansu yake na rashin kintsi."
Yusuf yace." Ko d'azu ma ta wuce ta nan wajejen k'arfe goma na Safiya, ko gilmawarta baku gani ba." ?
Nan suka ce Sam basu gane taba.
Cike da jin haushin su Hakkim ya futa waje yana kalle-kalle Yusuf yace." Bari in d'auko mota mu nausa ciki ko za'a dace."
Shiru yayi masa kawai ya soka hannuwansa duk biyun cikin aljuhu.

Yusuf ya futo da mota ya shiga suka kama nausa cikin karkarar ba tare da sun san ina zasu je ba.
Ganin mota tana shigowa ne yasa matasa da suke zaune Suna shan rake tsakiyar su futalar aci bal-bal ce sai hayaki take suna ta hira da shewa duk suka bi motar da kallo.
Yusuf yace." Ina ganin mu tsaya mu tambayi matasan can."
Parking yayi suka futo a tare matasan suka bisu da kallo. Cikin nutsuwa suka k'arasa kusa dasu duk suka basu hannu sukayi musabaha.
Yusuf yace." Muna tambaya ne." Sukaje Allah yasa mun sani."
Shiru yayi domin ya rasa da yaya zaiyi kwatan Ladidi.
Hakkim yaja tsaki yace.' Ka fara magana kuma kayi shiru, muna tambayar wata ibilishiyar yarinya a garin nan, ita ba mutum ba ita ba'ajana ba siririya tamkar tsolan rake, zaku ganta k'azama tana da manyan idanu."
Shiru sukayi na minti biyu daga bisani sukace ."Gaskiya bamu gane taba, sai da Ku k'ara shiga cikin k'auyen ko za'a dace."
Ko gama sauraransu baiyi ba yayi gaba ya bud'e mota ya shiga Yusuf ya biyo bayanshi shima duk ya sare da al'amarin. Har ya kunna mota zasu tafi, d'aya daga cikinsu ya taso da sauri yana fad'in." Ku tsaya Ku tsaya."
Hakkim yace." Dallah ja mota mu tafi ya Wani taso yana mu tsaya mybe ma yayi mana shirme."
Yusuf ya share shi kawai ya kashe mota, saurayin ya k'araso yana fad'in." Ina kyautata zaton yarinyar da kuke magana akanta baza ta wuce Ladidi ba, domin duk siffofin daka fada ita take dasu."
Yana daga cikin mota tace." Shigo ka kaimu gidansu."
Da sauri yaja baya cike da tsoro, chaiiiii! Akan me zai shiga motarsu ya sani ko 'yan yankan kai ne, Karin abun damuwar ma Ladidi suke nema, tabbas yasan abun babbane.
Ina-inda ya fara da k'yar yace." Yanzu dare yayi zani gurin iyalina,amma bari in yi muku kwatance."
Yusuf yace." Ok muna jinka."

"Idan kuka mike wannan hanyar zata kaiku har *Dausara* sai ku tsaya dai-dai majalisar Yahaya kuce ina ne gidan Iya Mai koko insha Allahu za a nuna muku nan ne gidansu Ladidi."
Yusuf ya zura hannu a aljuhu ya Ciro gudar dubu daya ya mik'a masa, yana godiya,
Da sauri ya karb'a yana zabga masa godiya
Motar yaja suka k'ara gaba.





******



D'alha da Yahaya na zaune a kan dakali suna hira Duk 'yan majalisar sun tashi, nan D'alha ya samu damar fad'awa mak'ocinsa Yahaya abunda ya faru da Ladidi
Sosai Yahaya ya jimanta al'amarin yace." Yanzu kana nufin jarin ka zaka rusa kan yarinyar nan D'alha ka k'yaleta kawai tunda tana ji kad'an kad'an sai nake ganin kamar wahalar da kanka zakayi kan hakan.'
Ajiyar zuciya D'alha ya sauke yace." Wallahi Yahaya ina mutukar tausayin rayuwar Ladidi marainiya ce bata da uwa babu uba sam bata san su ba bata da gatan kowa sai ni sai Ubangiji kaga kuwa dole in tsaya kan lafiyarta domin nasan amana ce a hannuna."
Yahaya yace." Da ina da wasu kudi a aje dana ranta maka gaskiya bana so ka taba jarinka."
"To yaya za'ayi insha Allahu zai farfad'o."


Haske mota suka hango tun daga nesa yana haske su. Yahaya yace." Baki mukayi daga burni kenan.'?
D'alha yace." Da'alama dai."
Ido suka zubawa motar har ta k'araso inda suke.
Yusuf yayi parking suka futo a tare. Suna isa kusa dasu suka mik'a musu hannu suka gaisa, Hakkim yace." Da Allah muna neman majalisar Yahaya ne."
D'alha yace." Gatanan ga Yahaya nan yana jin ka."
Yace." Gidan Iya mai koko muke nema."
Da hannu Yahaya ya nuna musu kofar gidan.
Hamdala Yusuf yayi yana jin farin ciki, yace." Nan wata yarinya Ladidi take."
Yahaya yace." K'warai kuwa ince ko lafiya."?
Hakkim ya juya ya da niyyar shiga mota a cikin zuciyarsa yace." Tunda anga gidan kome me sauki ne, gwara inje in kwanta in huta ko na samu Dady ya k'yaleni."
Bayani Yusuf ya tsaya yana musu Hakkim ya kunna Mota da k'arfi yake masa hon!!! Yusuf yace." Kuyi hakuri Insha Allahu gobe zamu zo da safe kome ye sai ayi." Yana gama maganar yaje ya bud'e mota ya shiga, Yusuf ya fige ta suka bar gurin.
Cikin takaici yace." Duk wannan abun bazai kai maka ba, don ma ka samu ina taimaka maka na tabbata da kai kadai ne sai dai ka kwana a kauyen nan kana tambaya baka samu ba, shine kake k'okarin tafiya ka barni. "
Shiru yayi masa yana draving, Yusuf ya dunga masa mita hat suka Isa masaukinsu.








*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿22*





Motar su na barin gurin. D'alha ya mik'a da niyar shiga gida yana mik'awa Yahaya hannu sukayi sallama kowa ya shiga gida.

Cikin bacci taji kamar murya D'alha yana tashin ta, ta mike zauna tana gyara d'aurin dankwalinta. Hasken Fitilar kwai ta karo tace." Lafiya kake tashina bacci na yayi nisa wallahi."

D'alha ya zauna gefen katifar da take zaune yace." Wasu mutane ne suka zo yanzu, wai suna Neman Ladidi."

Bude ido tayi sosai gabanta na fad'uwa tace." Wace Ladidi kuma,wacce yinin yau bata futa ba balle ace tayi Wani Abu."

Kwantar da hankalin ki Iya suma basu ce tayi komai ba, sun dai ga gidan sun ce gobe zasu dawo da safe."
Iya tayi jigum! Tana kallon Ladidi dake shararar baccinta tace." Kaganta nan ta sha wahala kafin bacci ya d'auke ta, motsi kad'an sai tace kunnenta."

D'alha yace." Da'alama ai kunnen ba k'aramin bugu akayi masa ba."

Iya ta share hawaye cike da tausayin jikar tata tace." Ko waye wannan ba k'aramin azzalimi bane wallahi. "

Shiru D'alha yayi domin baya so ya tanka maganar yasan laifin Ladidin ne.

Mik'ewa yayi yana mata sallama, har zai futa ta tsayar dashi tana cewa." Kace gobe babu koko ko."?

"Eh kin san zamu futa da safe sosai domin mu kama layi,sai dai hanzari ba gudu ba, mutanan da zasu zo."

Iya tace." Hakane kuma dole mu jirasu domin muji da abunda zasu dashi."


******
Lokacin dasu Hakkim suka koma gida babu kowa a farlo sai General kawai duk sun je sun kwanta, yana zaune yana jiran dawowar su


Ko zama bai bari sunyi ba yace." Kun samu inda take.?
Yusuf yace." Eh Dady mun samu saboda dare yasa muka ce mu bari gobe da safe sai mu koma."
Dady ya mike tsaye yana kallonsu yace." Allah ya kaimu gobe nima dani za'aje domin inga inda yarinyar take."

Shiru sukayi kai a kasa sai da ya wuce tukkuna suka dago Kansu, Hakkim ya zube. Cikin kujera yana shafa kansa yayi wata muguwar gajiyq

Yusuf kuwa tv ya kuna ya zauna yana fadin ." duk yanda kake ganin ga gaji ni nafi ka gajiya wallahi."
Hakkim yayi masa shiru yana lumshe ido, mik'ewa yayi ya nufi firji domin d'auko Lemo ko ya samu ya samu sassauci a zuciyarsa.


******
Da safe da k'yar Iya ta taimakwa Ladidi tayi wanka domin jikin nata ya kara d'aukar zafi mussaman gefen wuyanta wanda da k'yar take iya motsa shi, har dan kumbura yayi.
Tana zaune cikin wani leshi wanda ya gaji da kodewa yayi haske sosai dinki riga da zani ne da d'ankwali Iya ma ta shirya tsaf hijab dinta na aje a gefe D'alha ya shigo ya tarar dasu suna karyawa iya na lallaba ta tasha koko, tana kin sha, saboda zafi da take ji gurin hadiyar abu shiyasa ma ko kosai ba ta Ciba.

Iya tace." Har yanzu basu zo ba ko." Daga kai D'alha yayi Yace. " gashi yanzu k'arfe takwas ba."

Tace." To ai sai muta fi domin ba zamu tsaya su katse mana abunda mukayi NIyya ba."
Yace." Hakane kuwa hankali na ya kara tashi da yanda naga yarinyar ta tashi da jiki yau." Iya tace." Yanzu da k'yar take hadiyar koko dan taki cin k'osai ma."
Kallonta D'alha yake cike da tausayi..... Sallama suka ji daga waje D'alha ya mike da sauri ya futa


*****
Gaban shi ne ya fad'i ganin hamshakin mutum jingine da mota, fuskokin su Hakkim yake karewa kallo yana so ya fahimci ko sune mutanan na jiya.

A hankali ya k'arasa kusa dasu ya dan rankwafa gami da fadin." Barka da zuwa ranka ya Dade."

General ya mik'a masa hannu fuskar sa a sake yace." Barka kadai samari fatan mun same Ku lafiya. "

D'alha yace." Lafiya lau Alhaji." Hannu ya mik'awa su Hakkim sukayi musabaha ga juna yace." Hala kune bakinmu na jiya da daddare ko."?
Yusuf yace." Mune wallahi."
D'alha yace." To bari in shiga gida in sanar da mahaifiyata dama yanzu muke shirin futa."

General yace." Babu laifi samari." D'alha ya shiga gida cikin sauri.

Gogon ku na tsaye jikin mota ya harde hannuwansa a k'irji jira kawai su shiga gidan ya kara yin ido hudu da marakaunyar yarinyar nan yaga tayi ladaf ko kuwa.
Minti biyar D'alha yayi ya dawo da sauri yace." Bisimillah Alhaji ku shigo daga ciki."

Bayan sa suka bi. Yaran unguwar dake tsaye na kallonsu suka biyo su yuuuuuuu! D'alha ya buga musu tsawa, suka koma gefe,wasu na cewa Ladidi ce taje ta jawo futuna.
Mai koko na zaune gefan tabarma ta lullub'e jikinta da mayafi. Sukayi sallama suka shiga gurin zama ta nuna musu tana musu Barka da zuwa cike da mamakinsu
Suka zauna babu kyankyamin komai domin gidan tsaf yake tun safe tayi shara da wanke wanke ko ina tas iskar Safiya na kadawa

Gaisawa suke cike da mutumchi, General yace." Ina fata nan ne gidan su wata yarinya Ladidi."
Mai koko tace." K'warai kuwa nan Alhaji ina fatan ba wani abun tayi muku ba."
Cike fa tausayi yake kallonta yace." Mine dai mukayi mata laif............ Kafin ya gama maganar shi Ladidi ta bayyana a gurin, ta tsaya tsakinyar ta barmar idonta kan Hakkim! suka kurawa juna ido. Ihu!!! Ta kurma tana nuna shi da hannunta tace." Iya!!! Gashinan shine ya dinga dukana kamar zai kashe ni wallahi Iya shine, Allah ya kawo shi gidanmu mu dauki fansa domin bazan barshi ba."











*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿23*





Cike da mamaki General yake kallon Ladidi. dake tsaye Kansu D'alha mata tsawa ta matsa daka kan mutane amma kamar kara ingizata ake tanayi kamar zata kaiwa Hakkim duka.


General ya kalli Yusuf da alamun tambaya.

Yusuf yace." Itace yarinyar Dady."


Sosai General yayi mamakin kankantar ta ya kalli Hakkim cike da takaici yace." Meye abun duka jikin wannan k'aramar yarinyar."?


Sunkuyar da kansa kasa yayi. Yana jin tsoron kar dady ya tsinkashi a gaban mutane.


Ladidi ta ruga kicin da gudu! Duk suka bita da kallo. D'alha kamar yasan abunda zatayi ya mike da sauri zai bita.sai gata ta futo hannunta rike da doguwar muciyar da Iya take dama koko tayi kan Hakkim da gudu.



Hakkim yasan gurinsa ta nufo sai ya shirya tsaff ta d'aga muciyar da k'arfi zata maka masa.ya rike ta da sauri yw fuzgota sai gata ta fad'o jikinsa,cike da mugunta ya wurgar da ita gurin kanta ya bugu da bango ihu!! Ta kurma tana fadin." Wayyo kaina."!! D'alha yazo ya daga ta cike da jin haushi ya kwarfa mata mari yana fad'in." Ashe rashin lafiyar naki na k'arya ne."

General yace." Yi mata a hankali samari." D'alha yace."Alhaji baka San halin yarinyar nan ba ne."


General yace." Koma meye dai ni ta burge ni tunda take k'okarin k'watar 'yan cinta ga Wanda ya cuce ta, saboda rashin imani kamar Hakkim da shekarunsa da komai ya zage k'arfin shi kan yarinya k'arama kamar wannan."



Mai koko tace." Alhaji bamu game me kake nufi ba."?

General yace." Wannan da yake zaune shine ya sumar muku da ita jiya nine kuma mahaifinsa Nazo domin in nemi afuwar Ku."

Iya ta mike tsaye da sauri ta gyara d'aurin zaninta tace." Ko dana ji ahwo!!! Shiyasa naga yana sinne kai tamkar b'arawo a hannun mata,wato dama kaine kake k'okarin kurman tamin da jikita. ? Babu shakka Ladidi ta kurmance sai munyi sha'ra'a dakai."


Wani mugun haushin Matar yaji a zuciyarsa yace." Da zata kurman ce ma ai da kowa ya huta da alak'ak'ai."

Ladidi ta taso da sauri tana rike Iya tana kuka take fad'in." Iya kar ki barshi nima bazan barshi ba."


General yace." Innalillahi wa'inna ilahi rajinu. Ashe abun yayi tsanani haka,shiyasa zuciya ta kasa amunta nace dole sai Nazo naga halin da take ciki. Tabbas dole ki dauki hukunci Iya amma ki zauna muyi mgn dake ta fahimta. "


Mai koko ta koma ta zauna tana maida nuffashi Ladidi ta jawo jikinta ta rungume ta tana rarrashin ta.


Haushi duk ya tuk'e D'alha ya kalli General a nutse yace." Alhaji ka kwantar da hankalin ka don Allah ni nasan duk abunda ya faru da dalili haka kurum shi bazai kamata ya doke ta ba."



General yace." Haka kake gani samari inace gashinan a gabanka ya wurgar da ita da mugunta ta buga kanta a hango ko baka gani bane."?


D'alha yace." Nagaji Alhaji ai kana ganin abunda tayi masa ko."?


Shiru General yayi yana girgiza kansa.


D'alha ya bugawa ladidi tsawa tare da fad'in" yimana shiru shashasha kawai kin bude baki kina kukan banza da wofi."


Iya tace." K'yaleta tayi kukan ta to kaji."!!!!.


General yace."ina me bawa zuciyoyin Ku hakuri sosai domin narasa dame zan fara a halin yanzu amma kafin wani hukunci ya biyo baya ina rokon Ku da muje mu kai yarinyar nan asibiti a duba ta, domin hankalina ya tashi da jin maganar da kikayi."



D'alha yace." Dama yanzu zamu tafi asibitin cikin gari."


Mik'ewa General yayi yace."
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On LADIDI KWADAGA
avatar
north

1 year ago

Reply

dadi

Please Login or Register in order to submit comment