Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Maza Ku futo muje Allah ya kiyaye gaba."

Mai koko ta zura mata hijabinta tana goge mata fuska suka futa


To gurin shiga motar ma Ladidi ki tayi ta dinga turjewa wai bata yarda ba gurin yankan kai za'a kaisu a siyar musu da kai.


Da k'yar Dady ya rarrashe ta ta shiga motar. Hakkim kamar ya Dora hannu aka Dan takaicin ta.







*Comment vote and share*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_






*🅿24*




Cikin gari suka futa General yace." Zamu samu pravite hospital anan kurkusa sai mu tsaya kawai ba sai mun je babban asibiti na Murtala ba."

D'alha yace." Za'a samu Alhaji." Yace." Sai mu tsaya anan kawai a duba ta."


Cikin birget suka samu hospital.Hakkim ya kashe mota duk suka futo suka shiga ciki.


Idan da kud'in ka babu wahala da kaskantar da kai da zakayi,D'alha yayi mamakin yanda ma'aikatan asubitin suke karrama Alhaji sai rawar jiki suke.nan ka yanki kati likita na ofis General yace." Da Ladidi tazo su shiga tare. Mak'ale kafad'a tayi tana b'uya bayan Mai koko, murmushi yayi yace." Zo muje ciki dactor ya duba ki kinji ko." Ladidi ta zumb'uro baki gaba. Yace." Dawa-dawa kike so mu shiga tare." ? Shiru tayi masa. Haushi yasa D'alha ya buga mata tsawa tare da fad'in." Idan baki sake ta wallahi sai Nazo nan na gaura miki mari."

Mai koko tace." Kaga D'alha rabu da ita don Allah.Ina dalili nifa wannan asibitin be kwanta min a rai ba,asibiti ko ina sanyi hatta k'afar ka in ka aje ta a kasa sanyi ga wasu abubuwa a bango naji fa ana cewa wasu asubitin duk barna suke aikata wa. Gwara muje na Murtala kawai."

Takaici ya hana D'alha cewa komai. General yace." Iya wannan hospital din ana biyan kudi sab'anin sa dana gwamnati kenan kinga ai baza mu bi wannan dogon layin ba, kiyi hakuri mu shiga tare dake babu abunda za'ayi mata."
Mai koko ta kalli Ladidi tana yi mata magana k'asa-k'asa sannan ta sake ta suka mike General yayu gaba suka bishi a baya. D'alha ya nemi guri ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.

Hakkim kuwa takaici ya hanashi cewa komai yarasa me yasa Dady ya damu da al'amarin yarinyar nan wallahi. Shiko Yusuf Dariya yakewa Ladidi ganin yanda take ta kalle-kalle kauyacinta kawai take.
Dactor suka gaisa da General cikin mutum ci yana tsokanar Ladidi bata San ma yanayi ba domin tana can tana kallon tv mak'ale a bango na wani India film na fad'a, amma ba fassarar hausa bace. Dariya ta kyalkyale dashi tace." Iya kalli wannan film din ki gani don Allah, na fada miki afton nan Dan bala'in ne hinefa singam da nake fada miki,hahahahahaha."


General da Dactor suka saki baki suna kallon mara lafiya tayi tsalle gaban tv tana kallo tamkar zata rikito da ita daga sama.

Wannan karon kunya ce ta kama Iya ganin abunda Ladidi take babu kamun kai,kokari kawai take tayi tsalle ta tab'o tv in da jarumi Ajay devgan yake ragargaza 'yan gidan boss da bundigar sa,Ihu!! Kawai ta kurmawa tana buga tsalle.
Sosai dariya take cin General yana k'okarin dannewa sai da ta subuce. Ganin yana dariya yasa Dactor ya fara yi shima Suna kallon juna.
Iya tana k'okarin kamo ta tana fuzgewa duk kunya ta ishe ta gashi tun farko dama bata iya sarrafa Ladidi. Dactor ne da ya gaji da abunda take ga jama'a a na jiran shi a waje yasa ya buga mata tsawa! Tare da fad'in." Ki nutsu yanzu ko in sa a zo a zuk'i jinin ki kuma inyi miki allura goma.''
Firgigit ta dawo nutsuwar ta jin zan can Allura sai taji kallon ya fuce mata daga rai mugun tsoran dactor ya shiga zuciyar ta simi-simi ta dawo kusa da Iya tana zare ido.!


Iya tace." Ke kam anyi mara wayo wallahi ke da baki da lafiya kike tsalle-tsalle."
Da sauri tace." Nifa lafiya na lau ni dai kice kar ayi min allura bana so."

General yace." Ai dama ba allura za'ayi miki ba, dawo nan kusa dani dactor ya duba ki kaman matsalar kunnen ki,sai ya baki magani bazan bari yayi miki allura ba."
A d'arare taje ta zauna inda yake nuna mata sai harara Dactor take yi, bai lura ba yana can yana aikin sa. Ya d'ago kansa a nutse yace Alhaji meye Matsalar ta ne." Iya da ba'a tambaya ta fara zayya no masa abunda ya faru."
A hankali ya ambaci sunan Ladidi Wanda ya gani jikin kati wato Amina sai yaga bata dago kai ta kalle shi ba, da Ladidi ya kira ta da k'arfi sai ta dago kanta tana kallonsa. Mik'ewa yayi hannunsa rike da wani Abu,ganin yana zuwa inda suke ne yasa ta tsora ta ga wani Abu a hannunsa. Kafin General ya ankara ta buga tsalle, wajan kofar futa suka tsince ta tana kici-kicin budewa ta futa.

General ya mike da sauri yana kiranta ko sauraron sa ba tayi ba Allah ya bata sa'a ta bude tayi waje da gudu.!
Su Hakkim na zaune reception suka ga futowar ta kamar walkiya tayi kofar futa. D'alha gyangyad'i yake bai ganta ba, kasan cewar jiya baccinsa ragagge ne.
General suka gani ya futo hankali a tashe yake fadin "Tana ina ne." Kofa ya kalla yaga gilmawar ta ta futa, ya bugawa Hakkim tsawa tare da fad'in" Maza tashi kaje ka dauko ta.wato kana kallo ta futa baka yi wani Abu akai ba ko."?

Hakkim ya mike da sauri ya futa yana kunshe dariya yaji dad'i da Ladidi ta nunawa Dady wacece ita.

General ya jin gina da hango yana sauke ajiyar zuciya gefe guda kuma yana mamakin halin yarinyar kamar aljana, yanzu ya fara sarewa da lamarinta.


Hakkim na futa ya hango ta bakin get tana rigima da masu gadi, dole sai sun barta ta futa su kuma sun hanata saboda ganin yanda ta futo daga ciki tana fella guda sai kace me tab'in hankali. Kuma sunga lokacin da suka zo cikin mota sosai asibiti yake da tsaro. A hankali ya Isa inda suke dama tun kafin ya k'arasa yayi shiri ya tattate hannun rigarsa, yana isa ya sunkuce ta, sosai ya rike tamau! Ya had'e k'afafun ta da hannaye ta ya sab'a a kafad'arsa. Ladidi ta dinga ihu! Tana zandare masa a baya Hakkim ya rik'e hannuwan balle ta doke shi, sai ta kafa kanta a wuyansa ta gartsa masa cizo. Ko a jikinsa, bai sauke ta ba sai ya kaita har ofis din dactoe.
Iya tace."Sannu na yaba da k'okarin ka samari da baka d'auko ta ba wallahi futa waje zatayi k'arshe mu rasa inda take, Maza danne ta likita ya duba ta." Hakkim ya b'ata fuska bai mata komai ba ya fara k'okarin futa sai suka ci karo da General da D'alha suna k'okarin shigowa, Dady yace." Koma muje ka riketa a duba kunnen nata. Babu yadda ya iya ya koma ya zauna kan wata kujera Ya jawo Ladidi tana turjewa ya rike tamau! A jikinsa Dactor yazo da Abu a hannunsa ya kunna hasken sa, ya kafa kunnen Ladidi yana dubawa.

Ihu!!!!! Take kurmawa tun k'arfin ta,tana haure-haure da hannuwata da k'afafun ta tare da ya kushin Hakkim ko ta Ina.ganin hakane yasa D'alha zuwa gurin ya rike hannunwan nata tamau! Dactor ya cigaba da aikinsa.







*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_






*🅿25*






Hakkim zuciyar sa zafi take masa yana jin kamar ya saki Ladidi ta fad'i kasa saboda yanda take ta faman duk k'irjinsa duk ta ya kushe masa fatar hannunsa ga majinarta da miyau duk sun b'ata masa jikinsa, lokaci guda yaji zuciyarsa na tashi kyamkyamin Ladidi yake sosai.ya dinga kauda fuskarsa har dactor ya gama dube-duben sa ya matsa daga gurin.

Da sauri ya sake ta ta fad'i kasan gurin ya mik'e da sauri yana duba jikinsa. Saboda fargabar da suke ciki babu Wanda ya damu da fad'uwarta a gurin itama bata damuba ta mik'e zumbur tana sharb'e hawayen fuskar ta.


General ya k'araso kusa da ita cikin taushin harshe yace." Yi hakuri kinji Aminatu kinga ni ai na fada miki ba allura za ai miki ba kin tashi hankalin ki da namu kiyi shiru ki fada min me kike so in siya miki."
Ya k'arashe maganar sa lokacin da suke zama kujerar dake fuskantar ta dactor.

Tsabar takaici da b'acin rai yasa Hakkim kasa cewa komai ya bude kofa ya futa a fusace.!!

Dactor ya gama rubuce-rubucen sa ya d'ago yana kallon General yace." Alhaji gaskiya ta samu matsala daga kunnen ta na hagu, Wanda ya dumd'e ba taji sosai ta bangaran sa,amma insha Allahu in an bi doka zai dawo dai-dai yanzu zan dorata kan magani kuma kullum za'a dunga kawo ta ana mata wankin kunnen tsahon sati uku, insha Allahu idan akayi haka za'a samu maslaha."

General ya d'aga kansa cike da takaici yake Neman Hakkim a gurin sai ga babu shi girgiza kai yayi ya maida kallonsa gurin Dactor yace." Babu damuwa dactor INA so ka tsaya min kan yarinyar nan domin bana so ta rasa wani Abu me muhimmamci a rayuwar ta mussaman ma kunne domin jikin dan Adam yana da muhimamci duk abunda ake buk'ata zan biya insha Allahu a kula min da ita."

Dactor yace." Insha Allahu za muyi iya iyawar mu Matsalar daga yarinyar ne Allah yasa ta bamu hadin kai."


General yace." Insha Allahu babu Matsala." Dactor ya mik'e tsaye yace." Muje pharmacy zan had'a mata magani gobe misalin takwas na safe sai a kawo ta domi fara yi mata wankin kunne."

Duk suka mik'e suka futa a reception suka zauna Dactor shi da wata nurse suka nufi dakin magana.

General ya dinga laluben inda Hakkim yake bai ganshi ba Yusuf ya kalla da fuska a daure yace." Ina Hakkim yake.?


Kai a sunkuye Yusuf yace." Ya tafi sanjo kaya."

Cike da mamaki General yace." Kamar yaya ya tafi sanjo kaya wato yana nufin mu tsaya jiran shi ya tafi da mota sai sanda ya ga damar dawowa ko me.?
K'asa da kai Yusuf yayi cike da girmamawa.

General yace." Ya kyauta ai."

Suna zaune Dactor ya dawo hannunsa rike da Leda me tambari da sunan hospital din nasu cike da mugunguna nasha dana digawa a kunne dactor ya mik'awa General yana fad'a masa yanda za'ayi amfani dasu.

Nan General ya karb'i numbar account ni dactor din domin ya turo musu da hakkin su sukayi sallama suka futa.


Hakkim ne ya shigo asibitin cikin mota General ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Kayiwa kanka k'iyamun laili wallahi da ka bari mun bi motar haya sai na b'ata maka rai."

Shiru yayi yana sunkuyar da kai kasa ya sanjo kaya yanzu yana sanye da wata lafiyyyare shadda geznar sai maiko take brown ce babu hula kanshi sai sumar shi tasha gyara da alamu sai da ya sake sabon Wanka kafin ya dawo.


General da kansa ya budewa Ladidi kofar ta shiga su Iya da D'alha suka shiga sannan ya shiga, Yusuf ya zauna kusa da Hakkim ya ja motar Dady na d'agawa Dactor hannu.

General ya zurfafa a tunanin yaya za'ayi wannan bayin Allah su yarda da shawarar da ya yanke kan Ladidi, zuciyarsa a dake ya kalli Mai koko da tayi tsumu! Cikin hijabi tana shan Ac mota sai zare ido take yace." Iya akwai shawarar da na yanke kan Aminatu. "

Mai koko ta kalle shi tace." To Alaji ai babu komai ka fada min naji ai kana da kirki kai kam ko ajikin masu kud'in samun kamar ka sai an tona lallai albasa batayi halin ruwa ba wancan yaron naka me zuciyar kafurai da rashin imani."
Tafad'a tana hararar Hakkim dake driving


Takaici kamar ya kashe D'alha Ji Iya da wata magana don Allah ya juyo yana kifta mata ido Iya ko ganewa ba tayi ba ta cigaba da surutun ta daga ni tana cike da jin haushin Hakkim din.


Sai da General ya Bari ta gama surutun nata sannan yace." Dama cewa nayi me zai hana Aminatu ta dawo hannuna saboda shan maganin ta kan k'aida idan yaso idan lokacin da dactor din ya d'iba ya cika sai ta dawo gurin ki ko yaya kike CE."

General ya karashe maganar a tausashe domin ya lura tsohuwar yar taratsatsi ce.


Mai koko ta kalli General baki na rawa tace." Me kake cewa Alhaji."!!!!!!?







*Inga ruwan comment da dogon sharhi kan book din nan idan ba haka ba tammm! Zan mai dashi........ Ba sai na fada ba kun San sauran ehe, ko ta ina ina ga ruwan comment na zuba Lol😄*







*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHIMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿26*






General yace." Iya cewa nayi ki bar min Aminatu a hannuna domin tafi jin dadin karb'ar magani cikin nutsuwa kinga lalurar tata tana buk'atar hakan ,zamu zauna da ita a gidana na nan garin tsawon lokacin da dactor din ya fad'a insha Allahu komai zai yi dai-dai."

Girgiza kai Mai koko tayi tace." Ayyo! yanzu na fahimci inda ka dosa Alaji, ni kam ban amunce ba domin bazan iya baku ladidi ba ta zauna tare da wanda yayi yunk'urin nakasta ta."

General yace." Maganar ki haka take Iya amma wannan karon ina me tabbatar miki da cewar idan Hakkim ya kuskura hannunsa ya sauka kan Aminatu da sunan duka to babu shakka zan dauki k'wak'warar mataki kansa."

Girgiza kai Iya tayi tace." Oh!-oh! Ni kam ban yarda ba Alaji kawai ka bamu magani ai naga lokacin da likita ya ke nuna maka yanda za'ayi amfani dashi sai in dinga bata."

Shiru motor tayi kowa na tunani a zuciyarsa hak'ika General bai ji dadin rashin amincewar Iya ba.

D'alha ya juyu a nutse yana kallon General yace." Allah kada ranka ya b'aci kan hakan hak'ika nasan zuciyarka daya ka fad'i haka za mu baka Ladidi kamar yanda ka buk'ata tunda ba nisa zakuyi da ita ba kuna cikin garin nan sai in dinga kawo Iya tana ganinta kullum ina ganin haka yayi ko."?

General yace." Haka yayi samari naji dad'i kuma daka fahimce ni sosai da sosai." Iya ta kalli D'alha cike da takaici gani tayi fuskarsa a murtuke sai tayi shiru bata kara cewa komai ba sam bata son b'acin ransa kasamcewar shi kadai ne da ita a halin yanzu.

Cike da mamaki suka ga motar ta tsaya gidan gonar dasu ke hira a kwanaki, da sauri Iya tace." Alaji nan ne gidan naka. " ? Da murmushi a fuskarsa yace." Eh nan ne amma ba'anan muke da zama ba ni da iyalina muna abuja, kwanaki na siyi gurin nan nayi gidan gona domin mu dinga zuwa hutu ni da iyalina."

Caraf! Ladidi tace." Dama bana fada miki ba Nace gonarmu ce suka sace, mana shine daga zuwa zan tsinko mangwaro ya kamani yayi ta duka ni da gonarmu Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na rama."

Hakkim tun sanda ta fara magana yake kallonta ta mirror yana jin wani kuttun bakin cikin da takaici ji yake kamar ya tsayar da mota ya futar da yarinyar waje, amma babu hali yin haka. Yanzu tunanin da yake yaya za'ayi ya bar garin domin dai bazai iya had'a guri da ita yana jin zai iya kasheta saboda yanda yake jin zafinta a cikin zuciyarsa.

Dariya General yayi jin abunda Ladidi take fada ya kalli D'alha dake sunkuyar da kai cike da kunya yace." Hakane abunda ta fad'a 'yan samari."? D'alha ya sunkuyar da kansa kasa sosai yace." Hakane Alhaji mun siyar da gurin ne ni da mahaifina kafin rasuwar sa shekaru goma sha biyu da suka wuce,sai dai ba duka ne gurinmu ba." General yace." Ayya! Allah ya jikansa da rahama, ya kyauta makwancin mazan jiya hak'ika nasan babbar matsala ce tasa ya daga gonarsa ya siyar haka." D'alha yace." Hakane Alhaji. " General yace." Ku futo mu shiga ciki ai duk Iyalina na ciki sai Ku gaisa."

Futowa sukayi dukaninsu, banda Hakkim shi tunda yayi parking gurin da aka tanada domin aje mota yayi fucewarsa ya barsu cikin motar. Kai tsaye sharararn farlo suka nufa dukansu, Iya sai kalle-kalle take na k'auyanci ita ko Ladidi dama ba wannan ne zuwanta na farko ba.

Hajiya Asiya na hakimce kan kujera da romot control a hannunta tana neman tashar kallo, Salima ta Dora kanta a cinyarta suna hira, suka ji sallama.

Hajiya Asiya ta amsa a nutse tana yi musu sannu da zuwa, Salima ta mike da sauri tana kallon Ladidi cikin tsoro.
General yace." Bisimilh Ku zauna mana." D'alha ya zauna yana satar kallon farlo. Iya ma haka suka zauna guri guda da Ladidin ta.

Cike da farin ciki Hajiya Asiya tace." Alhaji da alama waccan CE yarinyar."? Yace." Itace Momy kin ganta k'arama ko." Tace." Wallahi kuwa, zo nan kinji mu gaisa." Tafad'a tana mik'awa Ladidi hannu." Kin zuwa tayi sai da D'alha ya buga mata tsawa sannan ta tashi tana zumb'ura baki.

Mama tace. " kayi mata a hankali mana." Ladidi ta k'arasa kusa da ita, da sauri Salima ta mike ta bar gurin jikinta na b'ari! Kusa da Dady dinta ta koma tana zare ido! Ya kalleta yana fadin." Ga 'yar uwa na kawo miki zata zauna damu sati uku ta karb'i magani Dan uwanki yayi mata lahani ke shaida CE kin gani da idon ki."

Hajiya Asiya tace." Alhaji ban fahimci abunda kake nufi ba." Nan General ya warware mata duk abunda ya faru da abunda dector yace . salati kawai takeyi tana duba kunnen Ladidi tace." Oh ni Asiya yaro na nema ya jawo mana masifa." Mai koko ta kalla tace." Kuyi hakuri don Allah tsautsayi ne." Mai koko tace." A'a babu komai ai ya wuce. Sai dai ga Ladidi nan amana Ku kula da ita domin marainiya CE, zan dinga zuwa kullum ina dubata"

Hajiya Asiya tace." Ai kar ki damu Iya insha Allah za kula da ita yanda ya kamata Allah ya bawa zuciyoyinku hakuri dai."

D'alha yace." Ai magana ta wuce mu zamu tafi gida."

Mik'ewa sukayi suna shirin tafiya. Abun mamaki sai naga Ladidi ko a jikinta ta nemi guri ta zauna gami da tsurawa TV ido fuskarta d'auke da murmushi sai motsu-mutsun dad'i take, TV din D'alha ya kalla sai yaga jarumi Salman khan da kayan 'yan sanda a jikinsa yana suburbud'an 'yan gidan boss! D'auke kansa yayi cike da takaici.

Iya ta kalleta tare da fad'in."Ladidi mun tafi babu rakiya ne."? Inaa!! Ladidi na can ta na kallo tama manta dasu a gurin.








*COMMENT*
*VOTE AND*
*SHARE*











*16/October/2009*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿27*






General yace." Iya Aminatu ta samu kallo ai ba zata saurare ku ba." Murmushi Mai koko tayi tace." Aikam gashinan naga alama Humm Ladidi da son kallon talabijin ai sai addu'a." Dariya sukayi dukaninsu Hajiya Asiya ta mike domin tayi musu rakiya, tare suka futa harabar gidan Wanda yayi dai-dai da shigowar Salim cikin mota yana k'okarin gyara parking General yace." Ya bari tukkuna ga bak'i nan ya mai dasu gida, cike da mamaki Salim yake kallonsu suka gaisa sama-sama ganin kallon da yakewa su D'alha na rashin sani yasa ya fara yi masa bayaninsu, sai ya saki fuskarsa sosai suka shiga mota General na daga musu hannu suka futa daga gidan.

Salima kuwa da aka futa aka barta ita da Ladidi cike da tsoro take kallonta, sai taga Ladidi kwata-kwata hankalinta baya kanta tana can tana kallo abunta. Muryar ta na rawa tace." Ya sunan ki na gaskiya."? Ladidi ta juyo fuskarta d'auke da murmushi tace." Amina kefa."? Tace." Salima sunana." Dariya Ladidi tasa tace." Sunan 'yan gayu 'yan burni da dad'i Wallahi. " Salima tasa dariya wanda yayi dai-dai da shigowar su General yace." Yawwa Salima kuje da ita ki nuna mata komai tayi wanka sosai sai kuzo muje cikin gari a siya mata kayan kwalliya irin naki domin so nake Aminatu ta dawo 'yar burni.'

Ladidi ta buga tsalle ta koma kusa da General tana washe baki tace." Ni so nima wallahi baba daga yanzu ka zama Ubana zan zauna daku ina sha'awar Ku." Tausayin ta yaji sosai yace." Muma muna sonki Aminatu zan nemi alfarma gurin Kawun ki ya bani aronki in sanya ki a makaranta.". Murna sosai ta dinga yi, Hajiya Asiya taji tausayin ta da so da kaunarta. Nan Salima ta jata d'akinta suka shiga toilet ta nuna mata komai. Dake Ladidi akwai saurin fahimta bata sha wahalar hada ruwan Wanka ba tayi tsaf ta wanke bakin ta da miskilin kamar yarda Salima ta nuna mata ta futo daure da towol Wanda ta aje mata.

Salima ta kalleta tana b'oye dariya ganin yanda kanta yake babu gashi duk yayi cibiri-birici gashi nan ya fara futowa ta wanke shi tas! Tace." Yanzu in muka shiga cikin gari za siya miki man gashi me kyau daka gani kina da kufan gashi ganin ya fara daga farko sinkif dashi." Ladidi ta zauna kusa da ita tace." Kwarkwata ce ta dame ni shine Kawuna yasa aka aske min amma duk cikin k'awayena babu wacce ta fini gashi."
Salima tace." Aikuwa naga alama gashinan ai.yanzu ungo wannan kayan ki sanya a jikin ki sai kizo muje farlo." Ladidi ta kalli kayan da Salima ta mik'a mata, ta sanya hannu ta karb'a da fuskarta da murmushi tace." Ina son mai sona nagode sosai wallahi ina son babanku."
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On LADIDI KWADAGA
avatar
north

1 year ago

Reply

dadi

Please Login or Register in order to submit comment