Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

hali taganshi tace." Babban yaya waye ya zubar maka da jini? Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Sai ta kara rurucewa da kuka. Yusuf ya rasa ma abunyi yace." Yanzu dai muje hospital ayi maka dressing d'in ciwon nan,in yaso ko ma meye sai ya faru, ni wallahi kaina ya kulle ma." Salima tace." Ya Yusuf fada sukayi ne." ? D'aga mata kai yayi ya nufi bedroom domin dauko masa kaya, to duk irin tambayoyin da Salima take masa yak'i tanka mata, yana durkushe sai sakin ajiyar zuciya yake ta b'acin rai! Da cin alwashi kan Ladidi. Wata razananniyar tsawa! ya buga mata tare da fad'in "Tashi ki bani gurin idan na fada miki waye me zakiyi, ne kin dame ni." Salima ta mike da sauri taja gefe cike da tsoro take kallonsa ganin yanda duk hallitunsa suka sauya.







*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿17*



Yusuf ne ya katse masa tunanin da take. Yace."Ka tashi ka saka muje hospital, ko sai na taimaka maka ne."? Da k'arfi ya fuzge! kayan da ya ke mik'o masa, ya mik'e da kuzari ya fara sanyawa zuciyarsa nayi masa zafi da radadin gami da takaicin abunda Ladidi tayi shuka masa. Yusuf yayi gaba yana fad'in." Bari in matso da mota kusa." Ko kallonsa baiyi ya fara d'ingisawa Salima tabi bayansa simi-simi.

Cikin gari suka futa suka nemi wani pravite hospital, nan akai masa dressing sosai suka had'a masa magunguna masu kyau da tsada, Wanda in yayi amfani dasu insha'Allah zai samu sassauci. Hanyar su ta dawowa suka tsaya suka siyi abubuwan da basu dashi, Salima ta kalli Yusuf a tsorace tace." Ya Yusuf nifa ina jin kwana biyu ko uku zanyi in koma gida wallahi tsoro nake ji." Yusuf ya fashe da dariya har da dukan kan mota yace." Nima ai munyi d'aya dake gaskiya tafiya zamuyi tsakanin jiya da yau mun sha fargaba mu da muka zo Hutu mun b'ige da jinya, ga tashin hankalin wannan yarinyar." Hakkim ya ja tsaki! yace." Wallahi babu inda zaku je,ni kadai na shirya tafiya ta,saboda gulma da munafurci kuka ce dole sai kunzo, mussaman ke." Ya fada yana kallon Salima da ta sunkuyar da kanta ya cigaba da cewa "har da kuka sai kinzo saboda haka dole ku zauna sai sanda naga damar tafiya sannan." Yusuf yace." Ni indai tani ne babu matsala Salima ce abun ji." Aikuwa ta marairaice fuska, Yusuf ya dinga mata dariya yana tsokanar ta da daddare zata ga Ladidi a kusa da ita tazo taya ta kwana aikuwa duk ta gigice. da wannan suka Isa, Hakkim ya futo daga mota yana kalle-kalle wai ko zai ga Ladidi,duk suka shige suka barshi a gurin, daga bisani ya bi bayansu yana d'in gisa k'afafu.



*********

Ladidi kuwa tunda ta samu ta d'auki fansar abunda Dan burni yayi mata sai kawai ta manta dashi da al'amuran shi ta cigaba da sabgarta.

Tafe take fakam-fakam da allo a hannunta ta cire d'ankwalin ta taci Uwar d'ammara dashi, tana sane ta cire ko wani zai tsokane ta ta samu na duka, bayan haka kuma tana so ta b'akantawa Kawun ta D'alha rai tunda ta lura baya so ya ga tana yawo babu d'ankwali, shi kanshi hijab dinta na hannuta, karo suka ci da Iliya dai-dai wani lungu,

Tun daga nesa yake k'unshe dariya, har ya k'araso daf da ita, taki kaucewa tamkar zasu bangaji juna, Iliya ya sha kunu ya d'an kauce mata tazo ta wuce, shima kamar zai wuce sai ya tsaya ya mik'a hannusa ya daki! kanta sosai yace.' Woooo k'waryar malo dama a namiji aka hallice ki domin kin fi kyau da maza!yana gama fad'ar haka ya runtuma da gudu yana dariya, aikuwa a sittin! Ta bishi da wani irin mugun gudu kamar zata tashi sama, yana gudu yana waiwayen ta,ganin ta kusa cimma sa yasa ya kara k'aimi!wani irin tsalle me had'e da gudu ta buga sai gata a gabansa,ba tayi wata-wata ba ta zura k'afarta k'arkashin tasa ta tad'o shi ya fad'i wanwar a gurin, ya yunk'ura zai mik'e, da sauri ta d'ebi k'asar gurin ta watsa masa a fuska, aikuwa ya saka ihu! Yana rintse idonsa, kamar walkiya ta bar gurin. Iliya ya dinga lalube yana ihu gami da mutsika idanunwansa k'asa sai gurin-gurin take masa a ciki ruwa ne kawai yake shatata da k'yar ya mike ya fara tafiya, aikuwa ya jishi cikin kwata tsumbul, yayi zaman 'yan bori, ya dinga salati yana neman d'auki.


*********
Yau kwanan so biyar a garin d'an kunkuru Hakkim ya warke tsaf, kullum cikin zuba ido yake yaga ko Ladidi zata kara dawo wa, shiru safe da yamma sai sun futa ganin gari cikin mota, ya dinga kalle-kalle kenan ko zai ganta babu alamunta, cikin zuciyarsa shi kadai yasan irin tanadin da yayi mata, Labarin abunda ya faru kuwa har su Dady sun sani domin Salima ta fada musu komai, Dady ya kira shi a waya tare masa fad'a kan ya kula kar ya k'ara dukan yarinyar kowa a garin shi kam baya son tashin hankali, amma ya Dade da sanin halin dashi mafad'aci ne sosai idan aka tab'o shi, tun yana yaro haka yake,amma fa in baka tab'o shi ba zaka jima dashi kuna mu'amula domin yana da saukin kai. Duk wannan gargad'in da Dady yayi masa yaji ne kawai amma yanda yaci alwashi kan yarinyar yana gani in bai dauki fansa a kanta ba ma kamar ya aikata zunubi ne.



**********
Yau Juma'a tun sassafe Mai koko ta tsaya kan Ladidi sai da taga tayi Wanka tas sannan ta k'yaleta ta shiga sabgogina, tana zaune tsakar gida, sanye da atamfa nicham jajazur da ita,ta sallahr ta ce ta bara,dinkin riga da zani ne da d'ankwali, tayi kwaliyya rabazau a fuskarta da d'ige-d'ige inda ta labta Jan jan baki a leb'anta da kan hancin ta saman idonta da girar ta, Mai koko ta k'araso gurin da Murmushi a fuskarta tace." Ko kefa Jikar Mai koko Ladidiya matar gwamna da shugaban k'asa,Ladidiya matar sarakai da Alhazai Ladidi matar masu mulki, kinyi kyau sosai, ki dinga tsafta kina wanka ki nutsu kinga kin fara girma wai baki ga kirjin ki bane har kin fara k'irgan dangi."? ta k'arashe maganar tana 'yar dariya.
K'irjinta ta kalla jin abunda Iya tace zumb'ura baki tayi ta cigaba da goga jar hodar ta,a fuska.Mai koko tace." Hodar ta isa haka ai kar tayi miki yawa." Aje abun shafar tayi tace." Dandali zamu je yau akwai gad'a kuma kin san nice shugaba." Mai koko tace." To babu laifi, amma idan kin je don Allah ki nutsu kar ki shirme banda fad'a da maza ki kama kanki kinji ko." Tab'e baki tayi tace." Nifa Iya kin san duk wanda ya takale ni mace ko namiji babba ko yaro sai na rama ehee." Iya tace." To naji ai duk Wanda bai kula ki ba babu ruwan ki dashi." Gyad'a Kai tayi ta mike tsaye tana warware wani mayafin ta me kama da abun tata, sai uban k'yalli yake wani har yana zuba a k'asa, k'okarin d'aura k'ugunta take dashi, Mai koko tace." A'a ke da zaki yafa kuma kyayi d'amara dashi." " Ni dai k'yale ni nafi son haka." Tafad'a tana zura silifas dinta sabo dal dashi,da alama yau zata fara sawa. Mai koko tace." To sai an dawo kar kiyi dare." Uffan bata ce ba takama hanyar futa fakam-fakam zanin jikinta sai harde ta yake, tana futa waje ta kwance shi ta jashi sama sosai duk k'waurin ta a waje, ta fi jin dadin tafiya a haka.
Har ta nufi hanyar Dandali sai ta fasa ta nufi hanyar titi.


**********


Cikin kyakyawan shiri suka futo duk su ukun Salima sai washe baki take yau zata koma gida, shima Yusuf murna yake saboda yayi kewar sweetyn shi kullum suna mak'ale a waye tana masa mita.
Shi ko gogon naku cikin b'acin rai yake,gashi har sun gama hutun su zasu koma bai ga al'janar yarinyar nan, balle ya dauki fansar abunda tayi masa,motsi kad'an zai buga musu tsawa kamar wani ubansu Yusuf har ya gaji ya fara mayar masa da martani,sai da suka kusa yin fada da juna, yana huci ya bude mota ya shiga suka shiga suma,da gudu ya figeta suka futa daga gidan, kasancewar hanyar babu kyau kafin a futa titi yasa tayar su tayi faci, cikin jin haushi Yusuf yace." Gashi nan garin zagin zuciya ka satar mana da taya sai ka futa ka d'aura mana wata." Yace." Sai dai in kai ka futa ka d'aura wallahi." Sanin halinsa na taurin kai yasa ya bude motar ya futa. Yana dubawa yaga babu wata spire yace." Babu wata fa." Gabansa ne ya fad'i jin abunda Yusuf yace futowa yayi yana tunanin yaya za'ayi, Yusuf yace
" Dole a futa bakin titi a siyo wata bari inje da kaina. ". Daga masa kai kurum yayi, Yusuf ya kama hanya tafi.

Bayan tafiyar Yusuf da kamar minti goma Ladidi ta bayyana a gurin.







*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿18*



Kanshi a k'asa ya dinga jin alamun tafiya, a nutse ya d'ago kanshi, suka had'a ido da ita ta kusa k'arasowa inda yake tsaye, wannan karon ma bai gane taba saboda kwalliyar da tayiwa fuskarta, kauda kansa kurum yayi, ita kam Ladidi ta gane shi sosai, wuce shi tayi, sai kuma ta dawo da baya, ta d'an tsaya nesa dashi, tace." Kai d'an burni." Da sauri ya d'ago kansa jin muryar yarinyar da yake nema ruwa a jallo. aikuwa k'wayar idonta ya kalla ya gane itace, fuskarsa ta rikid'e tayi murtuk kam bai tab'a dariya ba tunda Allah ya hallice shi, kanta yayi da sauri! tana tsaye tana jiran isowarsa tana dariya kamar mahaukaciya, tana ganin ya kusa k'arasowa gurin ta sunkuya ta d'ibi k'asar gurin ta watsa masa a fuska tana shek'a dariya fad'i take" Zo ka kamani ka gani in zaka iya, hahahahaha." Hakkim yaji shigar yashi idonsa sosai bai damu ba, cikin wata irin zuciya ya kai hannunsa zai mare ta ta sunkuya tana dariya,ya mari iska! cikin rashin imani! Ya kwarfo k'afafunta duk biyun, ta zube a gurin,yunk'urin mik'ewa take ranta a b'ace yayi saurin take mata k'afa guda ya dinga murzata da takalmin shi sawu ciki, ihu!! Ta kurma tafa d'ura masa ashar! ya daki! Bakinta da gwiwar hannusa, kafin kwace kwabo bakin ya fashe, hannunsa guda ya sa ya d'ago ta, ta rike hannunsa tana cizo,ko a jikinsa, ya shak'e mata wuya sosai! Suka fara kallon-kallon ita dashi, idonta yayi bala'in ja na azaba! Shims nasa idon sunyi jajazur! Ko da yake dama tunda suka futo haka nasa yake, a zafafe! Yace." Ke dan ubanki ya sunanki."? Cikin shak'ewar nuffashi tace." Ba dai Ubana wallahi meye ruwanka da sanin sunana,kuma zaka san ni ka Mara." Yace." Sai dai uban wa.". Ko nuffasa bata bari yayi ba tace." Sai dai ubanka." Murmushi yayi kana ganinsa kasan zaiyi mugunta, sakin ta yayi ta fad'i gurin tana mai da nuffashi, ta zabura zata mike yq maida kafarsa kan tata, blet din jikin shi ya Ciro, ya fara lafta mata, Ladidi ta fara ihu tana neman d'auki. Salima na cikin mota tana kukan tashin hankali tana jin tsoran kar yayan ta yayi kisan kai! Dukan Ladidi yake ko ta ina tana ihu! Wanda babu hawaye, da wuya tayi wuya sai ta fara sharb'en kuka tana cigaba da zaginsa,Salima ta bude mota a tsorace tazo ta rike shi tana bashi hakuri ya bangaje ta tafad'i a gurin,ya cigaba da laftar Ladidi har sai da yaga bakin ta yayi shiru, duk da haka bai saurara mata ba sai da yaga ta daina nuffashi sannan ya k'yaleta! Ya maida belt d'insa gami da matsawa gefe guda yana mai da nuffashi.

Yusuf ya k'araso gurin hankali a tashe, Ladidi kawai yake bi da kallo cikin tsantsar tashin hankali ya jefar da tayar yayi kanta yana salati. Salima ya kalla bakinsa sai motsi yake, ita kam kuka kawai take, Hakkim kuwa tayar ya d'auka ya fara sanyawa babu abunda ya dame shi. Suna can durk'ushe kan Ladidi sukaji karar mota a Kansu,da sauri suka mike Hakkim ya kunna mota yana k'okarin tafiya ya barsu, jiki a sanyaye suka bude motar suka shiga cike da tausayin Ladidi da bata san a wace duniyar take ciki ba.


Sai da suka hau titi sosai Yusuf ya samu bakin magana yace." Yanzu sai da ka aikata abunda kayi niyya kan yarinyar nan, wato duk irin maganar da Dady yayi maka baka d'auka ba ko."? Hakkim yayi masa banza fuskarsa a had'e take har yanzu, wani gefen kuma ya dan samu sassauci tunda ya hukunta yarinyar yana ganin gaba idan ance mata gashi a guri baza ta zo gurin ba. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." To wallahi ka sani kamar Dady yaji wannan labarin, kome zakayi sai na fada masa." D'aga kafad'u yayi alamun bai dame shi ba.


Cikin b'acin rai suka isa Abuja. Mai gadi ya bude musu get yana musu bar ka zuwa, Yusuf ne kawai ya amsa, Hakkim ya shige da mota ya gyara parking, futowa yayi ya nufi part d'insa, Yusuf da Salima suka nufi cikin gidan.



Mama na zaune a falo tana kallo taji sallamar su ta dago kanta cike da walwala da farin ciki ta amsa, Salima ta tawo da gudu gurinta, rungume ta tayi ta fashe da kuka! Mama ta kalli ya Yusuf ta ganshi duk a furgice tace." Yusuf me ya faru ina Abdul yake." ?Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kan kujera yana goge gomin dake tsatstsafo masa, yace." Lafiya ba lafiya ba Mama." Salati Mama tasa tace." To ai sai kayi min bayani. Salima ta bude baki zatayi magana Mama tace." A'a bake na tambaya ba." Shiru tayi tana ajiyar zuciya. Yusuf ya warware wa Mama duk abunda ya faru tunda ranar da sukaje har yau da zasu dawo.

Mama ta dinga salati tana sallallami, tace."Wai wannan zuciya ta Abdul ina zata kaishi yanzu idan ya kashe musu yarinya fa." ? Yusuf yace." Wallahi Mama na tsorata da al'amarin domin ni gani nake ma kamar ta mutu." Salima tace." Wallahi nima haka." Mama ta mik'e tsaye da sauri! Jikinta sai rawa yake wayar ta ta d'auko ta kira mijinta yana dagawa tace." Kazo gida babu lafiya." Ba ta jira abunda zai ce ba ta kashe wayar. Tace." Yusuf je ka kira min shi yanzu.'

Yusuf ya mike da jiki a sanyaye ya nufi part d'insa.








*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_





*🅿19*




Lokacin da Yusuf ya shiga d'akin samun sa yayi zaune gefen gado d'aure da towol a jikinsa da alama daga Wanka ya futo, yana zaune yana danne-danne a waya babu abunda ya dame shi. Cikin takaici Yusuf yace." Sai kazo Mama na kira,wato kai kanan kana danne-danne a waya babu abunda ya dame ka ko." Dago kansa yayi yana kallonsa yace." E babu abunda ya dame ni, d'in, so kake in tada hankalina kamar yanda ka tada naka ko me."? Yusuf yace." Zakayi bayani ne wallahi ni kaga tafiya ta, idan kaga dama kaje kiran da ake maka." Tsaki! Yaja ya d'auke kansa Yusuf ya futa cike da jin haushin sa.

K'ananun kaya ya sanya a jikinsa Wanda suka masa kyau sosai ya fesa turare, me sanyin kamshi wayarshi ya d'auka tare da eirpix d'insa ya futa.


Mama na tsaye a farlo tana kai kawo hankalinta duk ya tashi, yayi sallama ya shiga, Salima ce kawai ta amsa masa yana kallon fuskar Maman shi yasan tana cikin tashin hankali da damuwa, k'okarin zama yake ta dakatar dashi ta hanyar fad'in." Kar ka zauna domin zama bai kama ka ba."


Tsayawa yayi yana sunkuyar da kai kasa, tace." Ka kyauta Abdul nace ka kyauta da abunda kayi." Shuru farlon yayi, tace." Kullum ina gargadin ka da ka rage zafin zuciyar nan taka kana mai da abun wasa, duk naji abunda kaje ka aikata a garin mutane ka sumar da yarinyar mutane har sau biyu kan abunda bai taka kara ya karya ba ko."? Dago kansa yayi yana kallon Maman yace." Mama kin San abunda yarinyar nan tayi min kuwa? Nasan Yusuf ne zai ce miki babu abunda tayi min domin ya kareta, idan da tsautsayi lokacin da ta fasa kwalabe na taka da narasa k'afafu me za kuce ko kuma in kwanta jinya me tsayi kinga ta cuce nu, wallahi Mama ibilicin yarinyar nan ya wuce tunanin me tunani shiyasa na hora ta yadda gaba baza ta kara yiwa wani Abu makamancin nawa ba." Mama tace." Kaine kake ganin haka, Abdul kasan halin mahaifin ku dai ba kai kadai abun zai tsaya ba har dani, babban abunda ya tada min hankali yanda Yusuf yace ka hana ya tsaya ya ceci rayuwar ta kayi mata dukan mutuwa tana kwance bata san inda kanta yake ba." Sunkuyar da kansa tayi har yanzu baya nadamar abunda ya aikata ga Ladidi. General. Ne yayi sallama ya shigo cikin sauri, duk ya gansu a tsaye, hankalin sa ya kara tashi, wata irin tsawa! ya buga musu har da Maman yace." Ku fada min abunda yake faruwa kinyi cirko!Cirko".! Jiki a sanyaye Mama tace." Gashinan a tsaye ya janyo mana tashin hankali nan ta warware masa duk abunda ya faru. Wani irin bahagon mari! Ya kaiwa Hakkim jikinsa na tsuma! Yace." Abunda ka je kayi kenan shiya dama ka takura dole Kaine zaka fara zuwa."? Hakkim ya dafe kuncinsa ransa a mugun b'ace! Yau shi mahaifinsa ya Mara kan wata "yar iskar yarinya 'yar kauyen k'auyau! Nan take yaji wata muguwar tsanar Ladidi cikin zuciyarsa.
General ya cigaba da cewa." Duk irin jan kunnen da nayi maka kan yarinyar ashe baka ji ba, kanan da muguwar zuciyar ka, OK shikkenan ka sani mutukar yarinyar mutane ta mutu ko ta nakasa ta dalilin ka babu shakka! Zan barka da Matsalar ka ne domin ni ba abunda ya shafe ni bane ko me hukuma zatayi maka tayi maka, ni zan bada tawa gudumawar." Salim ne ya shigo ya tarar da tashin hankali Mama na kuka Salima na kuka gogan na tsaye idonsa yayi jazur General sai surfa masa bala'i yake, nan Salim ya tambayi abunda yake faruwa Yusuf ne ya warware masa komai. Shima ya kad'u sosai kuma ya rausayawa Dan uwansa saboda yasan b'acin ran mahaifin su bashi da kyau mugun mafada ci ne. General ya kalli Mama cike da bada umarni yace." Ku shirya muna yin sallahr La'asar zamu dauki hanyar Kano dole ne muje mu ga halin da yarinyar ke ciki, duk inda take za binciko min ita." Mama tace." To Allah ya kaimu." Sama ya hau ya barsu suna tunanin abunda zai faru a gaba addu'a kawai suke Allah yasa yarinyar bata mutu ba.
Hakkim yq mike ba tare da ya kalli kowa ba ya zura takalmin shi ya futa ransa a dugunzu me, ya lura da Dady ya dauki serious kan al'amarin, wato Sam!shi ba'a duba irin b'arnar da yarinyar tayi masa abun ya kai har da duka abunda bai tab'a faruwa ba tsakanin shi da mahaifinsa tunani yake wane irin hukunci ya kamata ya yanke kan yarinyar.


********
Ladidi kwance cikin jini gefen kunne ta ya fashe yana digar da jini gashi ya kumbura leb'anta ya kumbura had'e da saman idon ta,duk hallitun fuskar ta sun jirkita tana kwance bata san in da take ba, hanya ce da ba kowa ne yake bi ba sai masu kiwo sune suka bi tare da dabbobinsu shiyasa har yanzu babu Wanda ya kawo mata dauki.


D'an Fulani ne ya shigo gurin tare da d'anshi Mati da dabbobin su, sai da suka zo dabda ita sannan suka fahimci mutum ne a kwance ,Mati yayi saurin birkitoto kawai sai yaga Ladidi d'iyar yayarsa Amina, me rasuwa, cike da tsoro ya kira mahaifin nasa yana fad'in "Baffa zo ka ga Ladidiyar Mai koko ce.......








*COMMENT VOTE AND SHARE*
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚*
*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀*




~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*



*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```

*LOADING:*
*{LADIDI K'WADAGA🌚}*




_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_

_______________________
```We are here to educate motivate and entertain our reades```
_______________________




*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_





*DEDIGATED*
*TO*
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~





_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_






*🅿20*





Da sauri d'an Fulani ya k'araso gurin, hankalinsa a tashe yace." Maza d'auke ta muje gida nasan ana can ana neman ta." Mati ya sab'ata a kafad'a bata san inda kanta yake ba, suka nufi gida.
Mai koko na aikace-aikacen ta na gida kawai taga an shigo da Ladidi a kafad'a, da sauri ya yar da tsintsiyar hannunta tana salati, Mati ya shimfid'eta a tabarma da sauri ya nufi gidin rijiya ya jawo ruwa cikin wata roba ba tare da b'ata lokaci ba yazo ya kwara mata a fuskar.
Minti biyar tsakani ta saki wata wawar ajiyar zuciya, nuffashin ta ya dawo amma kuma bata bude ido ba.
Mai koko ta dinga share hawaye cike da tausayin ta tace." A'ina kuka ganta kuma waye ya fasa mata baki har ya zubar mata da jini."? Dan Fulani yace." Inda kika ganta muma haka muka ganta kwance hanyar titi bata san inda kanta yake ba. Amma nafi tunanin wani tayiwa rashin kunya ya gwada mata rashin imani."
"Shiyasa kullum nake gargad'inta da rage haikewa manya domin nasan watarana dole ta had'u da wanda zai hukuntata."
tafad'a tana goge hawayen ta da gefan zanin ta.
D'an Fulani yace." Ai tun farko an fada miki abunda za'ayi mata a huta kink'iji, ni kinga tafiya na Dade da sanin duk lalatar da yarinyar take kece kike daure mata gindi,ni babu abunda zance sai dai ince Allah shi kyauta."
Yana gama maganar shi ya kad'a kansa ya futa, Mati ya rufa masa baya
Mai koko tabisu da kallo cike da takaici ya share hawaye tace." Duk dan kunga marainiya ce shiyasa kuke mata haka, wallahi idona idon wanda yayi wa jikata wannan b'arnar sai na rotsa masa kansa shima."
Ta fada cike da jin haushi da takaici, Ladidi ta fara
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On LADIDI KWADAGA
avatar
north

1 year ago

Reply

dadi

Please Login or Register in order to submit comment