Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[12/5, 4:58 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 1*


Abakin k'ofar wani gida ginin k'asa na hango wata matashiyar budurwa tsaye da saurayinta ya parker motarsa jeep, saurayin sanye yake da k'ananan tufafi kansa yasha askin samarin zamani kallo d'aya zakayi masa ka gane d'an hamshaki'n mai kud'i ne.
Saurayin mai suna Ridwan ya jingina jikinsa akan motarsa sai kallon soyayya yake jifar budurwarsa dashi , murmushi ya sakar mata yace"Raihana ki sani ina sonki ina k'aunarki tabbas soyayyarki ta riga tayimin mugun kamu azuciya, aduniya babu abinda nafi muradi sama dake masoyiyata".
murmushi Raihana tayi tace"soyayyarka tayimin dashe acikin zuciyata ka sani har abada babu mai iya rushe ginin da kayi cikin rayuwata,na riga na baka ragamar rayuwata da amanar zuciya da gangar jikina".
"karki damu azamantakewar soyayyarmu babu cuta bale cutarwa, nayi miki alk'awarin idan mukayi aure zan baki farin ciki na har abada".
"dako nafi kowace mace sa'ar samun masoyin gaskiya".
Ridwan ya kalleta cikin shauk'in so da k'aunarta yace"nima nafi kowane namiji sa'ar samun mace k'yak'k'yawa d'iyar mutunci,yanzu dai ki gayamin abinda kike buk'ata in siyo miki idan zan dawo wata rana".
Raihana tayi rau rau da idanunta ta shagwab'e fuska kamar zatayi kuka tace"tun yanzu zaka wuce gida habibi?".
Langwab'e kansa yayi cikin alamar lallashi da tarairaiya yace"eh yanzu zan tafi kiyi hak'uri zan dawo kinji banason ganin b'acin ranki".Bud'e gaban motarsa yayi ya d'auko babbar leda ya mik'a mata ta amsa .
Zaro kud'i yayi cikin aljihunsa ya bata kud'i dubu talatin ta amshe babu kunya kamar ba budurwa ba, cikin fara'a ta sakar masa murmushi tace"nagode habibi".
Ridwan ya girgiza mata kai yace"ki daina yimin godiya kinfi k'arfin komai awurina".
"uhmmmm godiya nake".
"ki rik'e godiyarki nizan wuce aiki companyn mahaifina".
"ubangiji ya kaika lafiya".
"Amin my Raihana".Yana rufe bakinsa ya shige cikin motarsa ya tadda motar ya fice daga bakin k'ofar gidansu Raihana.
Raihana tana tsaye tana kallonsa har saida ya b'acewa ganinta, sannan ta juya ta shiga cikin gida hannunta rik'e da ledar daya kawo mata.
Tana tafiya tana rangaji har ta iso tsakiyar filin gidan ta iske Rayyanatu zaune saman k'aramar kujera tana wankin kayan Raihana dana Inna Zulai, Raihana ta isowa wurin Rayyanatu ta tofar da miyau tace"aikin kenan haka zaki tabbata babu aure tunda kin dauk'i girman kai kin sanya arayuwarki, kece kullum Inna take sawa aiki kamar jaka bazaki tab'a wayewa ba har abada kanki yana cikin duhu! ".
Rayyanatu taji zafin kalamanta har cikin zuciyarta cikin takaici ta d'ago idanunta ta kalli Raihana tace"naji ni jaka ce babu komai tunda yayar mahaifiyata nakeyiwa biyayya keda yake itace ta zuk'unna ta haifeki baki mayarda ita abakin komai ba, sannan wayewa kuma da kike magana idan ta wuce misali ubangiji ya kareni da irin wayewar zamani".
Raihana ta hasala sosai domin maganar Rayyana tayi mata rad'ad'i da zafi azuciya cikin masifa da hargowa tace"keeeee lallai wannan yarinyar kin rainani ki kalli tsabar idanuna kicemin ban mayarda Innata abakin komai ba, hmmmmm zaki gane kurenki wata rana idan kika kai hak'urina bango saina fasa miki baki ".
"duk abinda nace miki ai ke kika fara tsokanata sannan babba jan girmansa yakeyi awurin k'arami,karki manta duk tsoho baiji kunyar hawa jaki ba jaki bazaiji kunyar kayarda tsoho ba".
"eh tabbas Rayyana kin zama 'yar iskar yarinya amma zan nuna miki ko gaba da gabanta".
"babu abinda zaki nunamin in banda tara samari a k'ofar gida idan shege yazo yau gobe d'an iska zaizo jibi b'arawo zaki jawo ,kin mayarda bakin k'ofar gidan nan kamar tacin kasuwa ki gyara rayuwarki kafin lokaci ya k'ure miki".

Raihana ta fashe da dariya sannan ta tsagaita tace"kice hassada kikeyimin saboda inada farin jinin da za'a soni shiyasa idan akace ana sallama dani kike jin bak'in ciki kamar zuciyarki ta fashe,kona tara samari na isa ne shiyasa nake tara samari idan fitsari banza ne kaza tayi mana mu gani".

Rayyanatu taji rad'ad'i da zafin soka mata magana da Raihana tayi bata sake cewa k'ala ba, saboda tasan idan ta biye mata itace da wahala cigaba da wankin tayi tana shanyawa saman igiyar shanya tufafi.

Jin hayaniyarsu yasa Inna Zulai ta fito daga cikin d'aki ta iso wurin Raihana tana k'are mata kallo, cikin alamar mamaki tace"lafiya nake jin kamar ana fad'a keda waye Raihana? ".

Raihana ta zumb'ura baki kamar zatayi kuka tace"nida wannan 'yar hassadar ce mana".

"wa cece 'yar hassada kuma ban gane inda maganarki ta dosa ba?".

Cikin sagarci da shagwab'a ta bud'i baki tace"Rayyanatu mana".

Cikin harzuk'a da tsantsar Rayyanatu dake kwance cikin k'wayar idanun Inna Zulai tace"mi tayi miki ne?".

Gaban Rayyanatu sai bugawa yakeyi fat fat fat zuciyarta ta tsinke saboda tasan halin Inna Zulai akan d'iyarta Raihana, zata iya yiwa kowa rashin mutunci muddin akan Raihana ne,kashe kunnenta tayi domin taji irin k'azafin da za'a k'ulla mata".

"daga kawai na shigo cikin gida zan nufi d'aki shikenan Rayyanatu taga ganina ta dinga zagina tana cemin karuwa, wai ban mayarda uwata abakin komai ba sannan banda b'arayi da 'yan iska babu wad'anda nake tarawa a k'ofar gida sai su".

Tsantsar takaici da bak'in ciki ne kwance afuskar Inna Zulai wani irin tururin d'aci da zogi zuciyarta keyi cikin k'unar rai ta dakawa Rayyanatu rikitaccen tsawa tace"Rayyana!Abinda zaki kalli Raihana ki gaya mata kenan saboda bakida mutunci da sanin ya kamata!? ".

Jikin Rayyanatu ya dauk'i kad'uwa da mazari bak'in cikin k'azafin da Raihana tayi mata ne shimfid'e afuskarta, nan da nan hawaye suka shatata afuskarta bakinta yana rawa tace"wa.....llahi Allah In....na ba...nce ma...ta karuwa ba...".

"Rufemin bakinki! Tambayarki nakeyi ba kuka nace kiyimin ba shegiya munafukar yarinya!".

"bance mata ka..... ".

Kafin ta k'arasa maganarta Inna Zulai ta kwasheta da gigitattun maruka biyu masu zafi wanda asanadiyar haka, saida ji da ganin Rayyanatu suka d'auke na wucin gadi ta fita daga cikin hayyacinta ta duk'e k'asa dafe da kuncinta tana zubar da hawayen takaici da rashin iyaye.

Kuka takeyi mai k'unshe da tsantsar damuwa da k'uncin rayuwa.

Alokacin ne Inna Zulai ta nunata da yatsa cikin kakkausar murya tace"gobe ki sake zaginta kiga irin hukuncin da zanyi miki sai yafi wannan muni arayuwa, keee dan ubanki idan ba hassada ba yadda kike kifin rijiya gaki da bak'in jini haka kikeson 'yata ta kasance, ki kiyayeni banida k'yau lamarina babu sauk'i bana d'aukar raini da walak'ancin kowa ".

Raihana tana kallon yadda mahaifiyarta ke tozarta 'yar uwarta amma ko ajikinta saima wani irin farin ciki da dad'i dake kwaranya cikin zuciyarta, murmushi ne kwance afuskarta tana hararar Rayyanatu cikin tsamgwama da *RASHIN SO*.

Zasu shige d'aki kenan saiga Baba Iliyasu ya shigo cikin tsakiyar gidan bakinsa d'auke da sallama, daga Inna Zulai har Raihana babu wadda ta amsa mishi sallamar, k'arasowa wurinsu yayi ya kallesu cikin nazari da tuhuma yace"Zulai mi kukeyi ne kukayi tsaye cirko cirko?".

Inna Zulai ta yamutsa fuskarta cikin rashin ladabi tace"babu abinda mukeyi illa Rayyanatu ce tayimin rashin kunya shine na hukuntata".

Baba Iliyasu ya mayarda kallonsa wurin Rayyanatu dake durk'ushe dafe da kuncinta tanata rusar kukan damuwa da tsantsar takaici, cikin mutuwar jiki da tausayawa ya isa wurinta ya mik'ar da ita tsaye cikin d'aci da zogin zuciya yace"yi shiru kiyi hak'uri ki daina kinji banason ganin hawayenki 'yata".

Rayyanatu ta sassauta kukanta tana gyad'a kanta alamar gamsuwa da maganarsa, sake kallonta yayi yace"yi tafiyarki d'aki ki kwanta ki huta".

Inna Zulai tayi charap tace"taje ina? To babu ita babu hutu har saita kammala duka ayyukan gidan nan fa ".

"to ai ba ita kad'aice budurwa acikin gidan nan ba ki saka Raihana ta k'arasa wasu ayyukan gida mana, ita kuma sai abarta ta huta shine adalci kinji Zulai ".

"Rayyana dai zatayi duka aikin gidan nan d'iyar k'anwata ce ba d'iyarka ba saboda haka babu ruwanka".

"ohhh to saboda tana d'iyar k'anwarki shine zaki dinga cutar yarinya kina cin amanarta, kiji tsoron Allah ki chanza rayuwarki wallahi ina guje miki ranar da zakiyi nadamar da batada amfani".

Ganin suna hayaniya yasa su Raihana suka zare jikinsu da wayo wayo kowaccesu ta shiga cikin d'akin da take rayuwa cikinsa, su Inna Zulai basu ankara da sun fice ba saboda dukansu suna cikeda haushin juna.

Inna Zulai ta rik'e k'ugu cikin son fitina tace"kaga Iliyasu nifa banason mutum ya dinga saka bakinsa acikin abinda bai shafeshi ba, wannan ai salon sa ido ne miye ya shafeka? Inace Rayyana d'iyata ce har lahira to miya dauk'i bakinka ya sanya cikin wannan lamari ".

"kedai na fahimci bak'ya son gaskiya dole kuma in gaya miki gaskiya komai d'acinta saboda bazan bari ina ji ina gani ba ki halaka yarinya marainiyar Allah ".

Mtssss Inna Zulai taja tsoki tace"gaskiya ka sani bale ka gayamini ita ni banida lokacinka saboda haka je kayi tayi da wanda yake tsararka ".Tana kai k'arshen maganarta taja k'afafunta ta shige cikin d'akin da Raihana ta shiga tabar Baba Iliyasu tsaye yana mamakin rashin son gaskiya irin nata.

Ajiyar numfashi yayi yace"Allah ubangiji ya shiryeki Zulai yasa ki dawo akan hanyar gaskiya".Yana k'arasa maganarsa ya nufi cikin d'akinsa wanda yake kusaga na Inna Zulai.

Baba Iliyasu yana shiga cikin d'akinsa ya cire tufafinsa ya nufi famfo ya d'ebi ruwa abokiti, direct ya fad'a toilet yayi wanka sannan ya fito daga cikin toilet d'in hannunsa rik'e da bokitin awaje ya aje bucket d'in, sannan ya fad'a cikin d'akin manshafi ya shafa ajikinsa sai ya ciro riga da wando shadda wad'anda d'an amininsa ya bashi k'yauta, bayan ya gama shiryawa ya jawo k'ofar d'akin ya rufe ya nufi cikin d'akin Inna Zulai.
Azaune ya taraddasu suna cin tsire da korawa da ruwan lemu jin takun tafiyar mutum yasa Inna Zulai ta waigo tareda yi masa walak'antaccen kallo sannan ta kauda fuskarta, ita Raihana ko d'ago kanta batayi ba bale ta kallesa, tsaye Baba Iliyasu yayi yana jijjiga kansa cikin katsewa da lamarin Zulai sassauta muryarsa yayi yace"Zulai ina abincina tun d'azu nake jiranki ki kawomini a d'akina? ".Batare data sake waigowa ba tace"ban girka ba! ".Cikin rashin girmamawa da rashin mutunci...........



_Shin labarin yayi muku dad'i ko baiyi ba? Ku cigaba da bina sannu ahankali domin jin yadda rayuwar Rayyanatu zata kasance._

_More comment more typing._


~Mugirat Musa ce.~😘
[12/5, 5:06 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 2*


Baba Iliyasu tsaye yayi yana jinjina rashin mutunci irin na Inna Zulai, sannan ya saukar da nannauyar ajiyar zuciya yace"saboda mi?"."Saboda niba baiwarka bace Iliyasu kullum kullum baka tashi aiko da kayan cefane sai marece tayi, shiyasa ni bazan iya yin bak'ar wahala ba wata rana ma d'anyen icce kake aikowa dashi ayi girki bayan nasha gaya maka ka daina siyomin itace d'anyu, amma sai kayi banza da maganata saboda baka mayardani abakin komai ba cikin gidanka".
"ya isa kice dai bakiyi niyar yin dahuwa ba babu wani k'auli da ba'adi da zaki kawo mini, sai naga bake kikeyin girkin ba kullum Rayyanatu ce kike sakawa aikin komai, saboda haka daga yau na gaya miki kada ak'ara kuskuren rashin yin abinci idan ke kinada masu kawo miki keda 'yarki mu bamuda masu bamu abinci ".
Inna Zulai ta wurga masa harara tace"k'warai kuwa munada masu kawo mana ko mutum yayi bak'in ciki da hassada babu abinda ya shafemu! Daga yau idan ka siyo cefanenka kaba Rayyana ta dafa maka inhar kanason kaci abinci".

Baba Iliyasu ya musk'uta yace"zan bata saboda ita nake aure bake ba, ke kuma Raihana kiji tsoron Allah duk abinda kikeyi kisan Allah yana ganinki kada ki kuskura ki biyewa hud'ubar Innarki da rud'in shaid'an domin wata rana zasu iya jefaki cikin wahala! ".Yana k'arasa maganarsa yaja k'afafunsa ya nufi k'ofar d'akin Rayyanatu ke barci.

Yana isa yayi knocking d'in k'ofar ta taso ta bud'e idanunta ya fad'a cikin nasa ta d'uka cikin girmamawa tace"Baba barka da rana"."Barka dai Rayyana".
Rayyanatu ta mik'e tsaye tace"akwai abinda kuke buk'ata ne yanzu in fito inyi muku? ".
"a'a bana buk'atar komai".Hannunsa ya saka cikin aljihunsa ya ciro d'ari biyar ya mik'awa Rayyanatu ta amsa tace"mi za'a siyo maka Baba?".
Baba Iliyasu ya kalleta cikin tsantsar tausayi yace"ba komai zaki siyomin ba ki sayi abinci kici nasan kina jin yunwa kuma gashi Innarki bata girka komai ba".
Hawaye suka cicciko cikin idanunta tausayin Baba Iliyasu ne ya d'arsu cikin zuciyarta cikin sanyin murya tace"nagode Baba ubangiji Allah ya k'ara rufa asiri duniya da lahira".
Hak'ik'a yaji dad'in addu'arta matuk'a har cikin zuciya da sassan jikinsa farin ciki ne kwance afuskarsa yace"Amin Rayyanatu ki cigaba da hak'uri komai na duniya yanada farko yanada k'arshe, nasan bak'ya jin dad'in zama cikin gidan nan ko kad'an saboda irin musgunawa da tozartar da rayuwarki da Zulai takeyi, da sannu komai zai wuce kamar bai tab'a faruwa kinji".
Hawayen da take b'oyo suka zubo afuskarta ta nisa tace"babu komai Baba duk abinda yake faruwa dani na d'aukesa amatsayin k'addara ce, sannan cikin tsanani akwai sauk'i komai zai zama tarihi".
"naji dad'i da kika fahimci cewa babu abinda yake dawwama aduniya nina fita zuwa kasuwa saina dawo".
"Allah ya kiyaye hanya".Tace.
"Amin d'iyar albarka".
Sanya kai Baba Iliyasu yayi ya fice daga cikin gidan yayinda yabar Rayyanatu tana shirin fita ta siyo taliya ta dafa, saboda yunwa tana matuk'ar nuk'urk'usarta har cikin hanjinta, hijabi kawai ta jawo ta sanya sannan ta fice daga cikin gidan tareda nufar shagon Tanimu mai saida kayayyakin miya.
____________________

Rayyanatu bata zarce ko'ina ba sai bakin shagon Tanimu ta siyo taliya da maggi star da racco,gishiri,tarugu,albasa da mangyad'a komai ya sanya mata cikin bak'ar leda ta nufo hanyar gida.
Tana isa tsakiyar gidan har yanzu su Inna Zulai suna cikin d'aki basu fito ba suna shagalinsu, cire hijabi Rayyanatu tayi ta azashi saman tabarma sannan ta d'auko tukunya k'arama ta fara kichaniyar dafa taliyar, aza tukunya saman murhu tayi bayan ta k'yasta ashana wuta ta kama ci bal bal bal, jajjagen kayan miya tayi bayan ta tafasa mangyad'a ta kawo jajjagen ta sanya domin ya soyu, yana soyuwa ta zuba ruwa cikin tukunya ta zauna tana jiran har ruwan su tafasa.
Su Inna Zulai suna cikin d'aki suna jiyo k'amshin girkinta alokacin ne suka had'iye miyau mak'wat cikin mak'oshinsu, lumshe idanu kawai sukeyi suna shak'ar k'amshin jajjagen kayan miya, Raihana ta kalli mahaifiyarta tace"Inna kina jin k'amshin girki acikin gidan nan".
"ina ji mana kamar Rayyana ce ke dahuwar abinci".
Raihana ta yamutsa fuskarta tace"itace ba kama bace Inna".
Inna Zulai ta rik'e baki cikin haushi da takaici tace"kenan Iliyasu kud'in cefane ya bata lallai yau cikin gidan nan zamu kwashi 'yan kallo dani dashi, ita kuma mu bari idan ta gama wahalar girkawa muje mu d'ibi namu rabo tunda ba ubanta bane ya kawosa! ".
"ai koda masifa da bala'i sai munci girkin nan tunda shegiyar yarinya ce! ".
"shakuruminki Raihana ci kam mun gama idan ta nemi tayimin rashin kunya sai in koreta tabar gidan nan, ta tafi duk gidan ubanda zataje babu abinda ya shafeni ".
Raihana tayi murmushi cikin jin dad'in maganar Innarta tace"da kin k'yauta Inna saboda maganin shege sai d'an banza".

"hmmmmm akwaiki da iya zance Raihana sarauniyar masu farin jini".
Kusan atare suka fashe da dariya suna k'yak'yatawa saboda jin dad'in duniya.

Ruwan suna tafasa tuni Rayyanatu ta zuba rabin taliyar tana zubawa tasa murfi ta rufe tukunyar, tana jiran abincin ya dahu babu dad'ewa taliyar ta dahu ta mik'e tsaye domin ta d'auko kula ta juye taliyar ciki direct cikin d'aki ta shiga.
Tana shiga cikin d'aki Inna Zulai itada Raihana suka fito daga cikin d'akin da suke zaune rik'e da babban plate ahannun Raihana, basu tsaya b'ata lokaci ba suka juye abincin cikin plate basu bar mata komai cikin tukunyar ba da zafinsa da komai suka fara ci suna sud'ar hannu sai sankad'a k'atanyar loma sukeyi da uwa da d'iyarta. 😂

Rayyanatu ta fito d'auke da kula ahannunta tana isowa wurin tukunyar idanunta ya sauka akansu Inna Zulai da suke cin taliyar data dafa, bud'e murfin tukunyar tayi taga wayam babu komai cikin tukunya tsaye tayi tana matuk'ar mamakin rashin tausayi irin nasu Raihana, tana kallonsu suka cinye taliyar tass cikinta sai k'ugin yunwa yakeyi yana kuka k'uk'uk'uk'u zad tausayi.

Suna kammala cinye taliyar Inna Zulai tace"Raihana je ki d'ebomin ruwa insha inji sanyi araina".
Raihana ta mik'e tsaye tana murmushin mugunta tana kallon Rayyanatu da tayi tsaye jugum tace"to Innata bari in d'ebo miki ruwan".Tana k'arasa maganarta ta nufi wurin famfo domin ta d'ebo ruwan akofi.

Alokacin ne Inna ta lura da tsayuwar mutum kusa gareta hararar Rayyana tayi tace"keeee!Lafiya kikayimin tsaye akai ko bashi kike biyata ne? ".

Jikin Rayyanatu ya d'auki mazari da k'yarrrma saboda tana mugun matuk'ar tsoron Inna Zulai azuciyarta, cikin tsinkewar zuciya fargaba da tsantsar tsoro ne shimfid'e afuskarta tace"Inna abincin dana dafa nazo d'auka ba wurinki nazo ba".

"mara kunyar banza ina kika ajiye abincin!? ".

Rayyanatu tayi rau rau da idanunta tace "cikin tukunyar nan yake".

Inna Zulai ta nisa cikin zafin rai da tafasar zuciya tace"afffff zancen banza abincin kam mun riga mun cinye saidai ki dauk'i ta annabawa tunda ba ubanki bane ya baki kud'i kika siyo taliyar ba, idan banda kina makira azuza Iliyasu ya iskoki har cikin d'aki ya baki kud'i shine don tsabar kutungwila kije ki siyo taliya batare da sanina ba! ".

Rayyanatu ta noce kanta ak'asa cikin zullumi tace"kiyi hak'uri hakan bazai sake far........ ".Kafin ta k'arasa maganarta Inna Zulai ta katse mata hanzari.

Cikin suk'uwa tace"yimin shiru munafukar Allah hak'urin munafurci zaki bani bayan kin nunamin ba nice na haifeki ba,dani mahaifiyarki ce da baza kiyimin haka ba saboda haka ki b'acemin da gani! ".
Sai alokacin Raihana ta iso da ruwa ahannunta farin ciki shimfid'e afuskarta tace"Inna ga ruwan".

"yauwa d'iyar k'warai Allah ubangiji ya nunamin lokacin aurenki ".Inna Zulai ta fad'a tareda amsar ruwan ahannun Raihana tasha.

Bayan tasha ruwan ta mik'awa Raihana kofi tace"ga kofin".Rayyanatu tuni ta shige cikin d'aki sufsufsuf kamar b'arauniya kafin Inna Zulai ta gano bata fice daga wurin ba.

Raihana tana amsar kofi saiga yaro ya shigo cikin tsakiyar gidan yana isowa wurinsu ya gaidasu, suka amsa masa agadarance sannan ya dubi Raihana yace"Anti Raihana wai ana miki sallama awaje".

Kallon yaron tayi tace"waye yake mini sallama?".

"malam Mubasshir".Inji yaron.

Cikin tsananin takaici wanda ya bayyana k'arara afuskarta tace"je kace masa bani zuwa".
Inna Zulai tana jin abinda Raihana ta fad'a har yaron ya juya zai wuce ta k'wala masa kira tace"kai kace masa tana zuwa yanzu ".

Yaron ya juyo yace"to Inna".Sannan ya sanya kai yayi ficewarsa daga cikin gidan.
Inna Zulai ta mayarda hankalinta wurin Raihana dake tsaye ta b'ata rai tareda kicin kicin da fuska kamar zatayi kuka, saukar da numfashi tayi tace"ki daure kije wurinsa kinji 'yata walak'anci babu k'yawo".

Zumb'ura baki tayi tace"haba Inna kinsan fa ko naje wurinsa babu abinda yake bani saidai ya dameni da yawan surutu akwai aukin cewa ina sonki Raihana bazan iya rayuwa idan babu ke ba, alhalin kuwa duk k'arya ne babu wani son dayake mini tunda marowaci ne".

Inna Zulai ta fashe da dariya tace"aiko kinje wurinsa bashi zaisa ki auresa ba keda kikeda samari buhu buhu ina ke ina wani matsiyaci Mubasshir, aike matar manya ce sai mai kud'in gaske irinsu Ridwan zaki aura".

Raihana tayi tsalle tana murmushin dake k'ayatar da fuskarta tace"ashe kinada tunani da hangen nesa Inna kin fahimci banason in auri talaka arayuwata".

"ina ke ina talaka keda talaka ai kun raba hanya kinyi gabas yayi yamma, yoohhh bazan tab'a bari ki auri talaka ba ai saboda nima inason akirani da surukar mai kud'i ".

"da gaske Inna kinaso? ".

"inaso mana aiko Annabi (S. A. W) ya nemi tsari da talauci bale mu 'ya'yan bani Adam, wuce ki gyara fuskarki ki tafi wurinsa kada yace kin walak'anta shi".

"To Inna".Inji Raihana cikin sanyin murya ta shige cikin d'aki domin tayi kwalliya ta chanza tufafinta.

Duk maganganun da sukeyi Rayyanatu tana cikin d'aki tana jinsu yayinda take shan gari da sugar, girgiza kai kawai takeyi tana Allah yayi wadaran da iyaye irin Inna Zulai ita da kanta takeyiwa d'iyarta hud'ubar tsiya ta azata bisa hanyar shaid'an .

Raihana tana shiga cikin d'aki ta jawo kayan kwalliyarta ta fara yin kwalliya sannan ta d'auko doguwar rigarta ta sanya ajikinta, turare ta fesa sannan ta fito daga cikin d'akin ta iso har wurin da Inna Zulai ke zaune tace"zan wuce".

Inna Zulai ta d'ago idanunta ta kalleta tace"wow!Kinyi matuk'ar k'yawo Raihana sai kin dawo".

Murmushin jin dad'i tayi tace"to Innata"".Tana rufe bakinta ta nufi hanyar fita daga cikin gidan tana rangaji da yauk'i kamar d'iyar gwamna, tana isa waje ta iske Mubasshir zaune saman teburin dake bakin k'ofar gidansu wani irin kallo ta jefeshi dashi mai tattare da raini da tsantsar tsana tace"ance kana kirana lafiya dai mi akayi?"............
[12/5, 9:30 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 3*



Mubasshir yayi murmushi cikin walwala yace"bako gaisuwa saiki fara tambayata lafiya nazo wurinki, ai k'ya bari har mu gaisa tukun kafin kiyi mini tambayoyi".Raihana ta firfito idanunta awaje cikin walak'anci tace"idan ban bari ba fa?".Mubasshir ya saki ajiyar zuciya yace"a'aaaa ba fad'a bane malama Raihana ubangiji ya sanyayi zuciyarki".
"Amin ya rabbi".
Mubasshir ya musk'uta tareda gyaran murya yace"dama abinda yasa nazo wurinki domin in k'ara jaddada miki ina kan

Please Login or Register in order to submit comment