Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

min."

"Kika sake cewa na karya miki k'afa sena go6e wannan fitsararren bakin naki try me and see" ya fad'a threateningly.

"Azzalumi" ta furta can k'asa-k'asa yadda baze ji taba sede shegen nisan kunne ne dashi tsab ya jiyota.

  "Kema 'yar gudun hijira kawai" ya mayar mata. Harara ta watsa mishi tana cigaba da zum6uro bakinta, kallo ya k'are mata sannan daga bisani ya jata da hannu tare da d'agata a sama cak ya wulla ta into a bride like style sannan ya shiga takawa da ita. Cikin motar ya sata sannan ya rufe har a yanzun tana mai ihu.

"Wayyo 6arawo ze gudu da ni!" ta fad'a tana bubbuga glass na windon. So take ta bud'e k'ofar ta fita amman don k'auyenci irin nata bata iya ba. Yana shiga motan ya kunna ignition d'in har nan bata bar ihun ba yanzu kuma ba na ze gudu da ita take ba na cafanin Mami ne da suka zube, akan ya tsaya ta tattara sauran abubuwan da basu sha k'asa sosai ba saidai be ko saurara mata ba. Ganin hayaniyan nata bana k'arewa bane yayi pulling headphones nasa ya cika da loud music ya sanya yadda bazata kuma daminshi ba. Don kanta tayi shiru ganin ba mahalicci se Allah, har anan kuwa k'afan nata nakan yi mata zok'i. A hankali AC'n dake tashi acikin motan ya soma shiganta wani sanyin da bazata iya tuna when last ta ji irinsa ba ta soma ji probably tun da suka je competiton Kano da take ss2.

   Afzal be sake ce mata komai ba seda suka isa asibitin inda yayi parking a harabar asibitin sannan ya fita ya bud'e mata k'ofar yana jiran ta fito itama.
   "Ko ka manta ka karya min k'afa ne kake jiran in fita da kaina d'in?" Tayi inquiring cike da rashin kunya.

  "Bance karki sake fad'in na karya miki k'afa ba?" Can k'asa-k'asa tace, "Ka fad'a amman ai gaskiya ne."

   "Kuma bana son gungunin nan bana son raini" ya fad'a a cikin tattausar murya. Ita dariya ma ya bata wa yaga Babanta da har zaice ga abinda yakeso da kuma abinda bayi so. Dariyan ta saki tana me mai kallon bakwai saura kwata cike da fitsara. Har maqora ta kai sa besan sanda ya fincikota daga cikin motar ba a fusace. Wani irin mumunar ihu ta k'urma bisa zogin da k'afan nata mai ciwo yayi mata bayan da ta taka mistakenly. Zubewa tayi take a gun a k'asa tana me raira kuka a yayinda ta rik'e gun idon sahun nata tana ihu. Ganin fa tana iya tara mishi jama'a ya jata da hannu d'aya putting her in a bride-like style kaman na d'azu ya shiga takawa da ita.

   "Ka sauk'eni nikam bana so ka sauk'e ni nace mugu kawai shin baka san haramun ne ba ta6a wanda ba muharramin ka ba? Ka sauk'e ni!" Maida kallonsa yayi a gareta, "In sauk'eki?" ya tambayeta looking directly into her brown eyes a yayinda manly k'amshin jikinsa ya cika mata hanci, yau taji k'amshin da yafi turaren wutan Mami dad'i.

  "Eh" ta fad'a tana me kawar da kanta a hankali, bata san me ba amman bata iya kallon cikin idanunsa na tsawon lokaci. Nodding kansa yayi sannan daga bisani ya janye hannayensa da suke riqe da ita, ai ba shiri ta zagaye hannayenta a wuyansa don maintaining balance nata da kuma hana kanta daga fad'uwa a k'asa to injure herself some more. Hak'i ta shiga yi na sosai sabida yadda zuciyarta ta mugun tsinke bata d'au rashin imanin nasa ya kai ga har zata ce ya saketa ya kuma yi hakan ba. Mak'irin murmushin da ya 6ullo da one-sided dimple nasa ya saki ganin wannan funny reaction natan ashede ba da gaske take ba "Dan Allah ka tare ni kar na fad'i" tayi rasping cike da tsoro ganin tana neman zamewa shikuwa baida niyyan preventing aukuwan hakan.

   "In tare ki? Ina cewa kikayi in sake ki? Sai ki sakeni nima" ya fad'a in an I don't care tone.

   "Zan fad'i ne please ka tare ni."

  "Kin san da hakan kikace in sake ki?"

  "Toh kai ma kasan zaka sakenin ka d'auke ni tun farko?" Har anan bata bari sun sake had'a ido ba.

  "Kina magana ne?"

   "A'a nayi shiru" ta furta a hankali. Mugun kallo ya watsa mata sannan ya rik'eta firmly suka k'arisa cikin asibitin inda akayi mata duk wasu gwaje gwajen da suka kamata aka gano spraining ankle (targade kafan) nata tayi a garin fad'uwan da tayi shiyasa ta kasa taka k'afan amman ba karyewa kaman yadda take ta kururuwa ba. Miqar da k'afan nata akayi inda tayita ihu wane wacce ke labor room. Shi de Afzal dake tsaye bakin k'ofa yana tsananin mamakin wacce irin roguwar yarinya ce wannan.

   Bayan fitowan Dr ya basa prescription na drugs nata inda ya nufi gun cashier don biyan kudi sede hakan ya gagara kasancewan besan sunanta ba kuma a k'aidan asibitin bayan ko wani payment se anyi entering sunan patient da magunan da aka biya a record book. Excusing kan sa yayi ya wuce d'akin nata inda yayi knocking kamin nan yasa kai. Zaune bisa kan gadon d'akin ya tsince ta, ta zura wa k'afan nata da aka nad'e mata shi da bandage ido tana ta shessheqa. Tausayi da dariya duka ta bashi at a time, yana iya cewa tun da ya san kan sa be ta6a ganin drama queen kalan ta ba.

   Ba'a dauki tsawon lokaci ba kafin k'amshin turarensa na Caron designs ya bugi hancinta kai tayi saurin d'agawa don ganin waye, ganin shi ne kuwa ta dukar da kan nata sannan ta shiga share hawayenta a hankali. Cike da k'asaita ya k'arisa gefen ta ya zauna daga baya kamin tace wani cikin ze sake mata idan ya matso kusa da ita.

   Ganin ya kusan minti biyu zaune wajen batayi yunk'urin mai magana ba yayi deciding to go first, "What is your name?" ya tambayeta amman tamkar da gunki yake magana haka ta mar ko kallonsa batayi ba. "Hey dake nake magana fa" ya fad'a bayan wani lokaci. "Tell me your name in samu inyi settling bills naki" ai kaman me jiran ya kuma cewa wani abu kawai ta sa mai kuka, abinda yafi tsana kenan, ihun nan nata.

  "Oh! Help me God'" ya furta tare da dafe kansa "Ke wai shikenan bakida sana'ar data fi ta kuka? Kukan me kuma kike min yanzu? Ni na ja miki k'afan ne? Seki je ki samu Dr'n kimar wannan kukan and not me" ya fada dalla dalla yadda zata gane.

  "Mugu amman ai kai ka kawo ni seda na ce maka ka kaini gun Mami na kak'i Allah ze saqa min." Dariya ne ya k'eto mar dukda cewa ta kwatantasa da mugun, muryansa ya gyara don 6atar da dariyar there's no way ze bar 'yar yarinya haka ta gane mar dariya.

  "Whatever tell me your name, will you?"

  "I won't okay? Stop asking me to and just take me home I don't want your drugs keep it" ta sanar dashi cike da tsiwa. Baki hangame ya bud'e yana kallonta da mamaki bil adadin. Na farko sam be kawo a ransa ma ta ta6a zuwa boko ba bale ta iya speaking fluent English haka. Na biyu taya zata kalli duk girmanshin nan ta mai masifa kaman wani d'anta ko shakkansa bata yi? Yau yana ganin wacce ta fisa taurin kai, ya lura idan yace shima ze nuna mata nasa taurin kan toh ba shakka baza su amfana da komi ba illa ma raina shi da zatayi don haka ya yayyafa wa zuciyarsa ruwan sanyi ya sauk'e duk wani tak'ama da jin kai nasa, fatansa kawai su rabu.

   Numfasawa yayi don bata hak'uri amman ya kasa gashi har yanzun bata bar kukan da take ba.

   "Okay I'm sorry" ya furta murya chan ciki-ciki bayan ya d'auki tsawon lokaci. "Nasan duk laifi nane kike nan but-"

   "Amal... Amal Abdallah" ta sanar dashi cikin hawaye ta hanyan katse sa ba tare da ta d'ago kai ta kallesa ba. Kallonta yayi na 'yan seconds sannan ya miqe yaje yayi settling bills d'in ya dawo ya tarar da ita still yadda ya barta.



     *~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~*~
  So guys how was the chapter? Our very own first chapter. Was it a hit? Did you enjoy it? Are you craving for another update already?

RANA D'AYA
#RD
   Love... Miemiebee👄✨
[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣

💦💦 🍃🍃🍃
*RANA D'AYA!*
💦💦 🍃🍃🍃

_Written by Miemiebee👄_


*PAGE 0⃣2⃣*




    Seda ya d'auki tsawon lokacin da ya wuce tsammanin mutum sannan yace, "Ga magunan naki, ina kyautata zaton kin iya karatu za kuma ki iya gane dosage d-" bata basa dama ya k'arisa fad'in abinda yake da niyya ba ta katse shi "Mallam ba seka zageni ba am not an illiterate."

   "Serve you well" ya fad'a ba tare da nuna damuwa ba "Then kina iya tashi in kaiki gida."

  "Nagode kar ka damu I can bring myself home" taga alaman d'an rainin wayo ne shi to ya kwantar da bokatin hankalinsa, kar yace don ya ganta a haka zey raina mata wayo dan kuwa ita ba jahila bace saboda tayi karatun ta na secondary ba kuma a kowani gajan government school ba. No private school ne me kyau wanda ake kira da Ruby springfield college wanda ya kasance one of the best schools in Maiduguri.

  "What gibberish are you saying?" Ya tambayeta a takaice. "See kar ki 6ata min lokaci, kar kiga don tun d'azun ina danne zuciya na ina binki a hankali ki d'au hakan ba a bakin komi ba. Ina da muhimman abubuwa a gaba na wanda sukafi tsayuwa anan ina rok'anki to take you home, now get up" ya buk'aceta cike da tsiwa sede ko motsawa Amal batayi ba. "Are you deaf?"

   "I said to leave me alone!" Ta buga mai tsawan itama "Ka kama ka jawo min asara ina zaman zama na zaka wani kama kace min in tashi ka kaini gida? Me kakeson in cewa Mami bayan duk cafanin dana yo mata ka ta6ar6arar min dasu kabarni da babu? Don Allah ka barni kayi tafiyanka."

   "In ke baki san abunda ya kamata ba toh ni na sani a cewarki bazan biya ki asaran dana janyo miki bane? I'm aware of all that and zan mayar miki da komi kawai ni ki tashi in kaiki gida na bawa iyayenki hak'uri na fita hak'k'inki, I have other important things to attend to" ya sanar da ita. Kaman wacce bazata motsa ba se kuma ta shiga miqewa a hankali wanda a garin hakan ta kusa fad'i kasancewar k'afar nata da ta kasa takashi. Da sauri Afzal ya tarota, ganin bey saketa ba har yanzun kuma baida niyyan yin hakan ta shiga jan hannunta sai dai ta kasa.

   "Don't fight it" yace da ita "Muje" bata sake yunk'urin k'watan kanta ba har suka kai haraban asibitin inda yayi parking motarsa. Sanyata yayi a kujeran gaba sannan ya zagaya ya shiga shima tare da tada motar. A circular road inda ya kad'etan suka koma inda ya buk'ace ta da ta rubuta masa list na abubuwan datayi rashin nasu. Ba gardama ta amshi paper da biron ta lisafo komi harda kud'ad'e da amount nasu. Abu d'ad'd'aiku ne be samu ba wanda yamata alk'awarin bata kud'in idan ya kaita gida. A farko yaso su jesu kasuwan domin ta siyo amman tuna besan kan kasuwan ba sabida bai ta6a shiga ba seya fasa. A karo na biyu kuwa yayi tunanin ko zasu shiga su biyu tayi leading nasu but referring to her wounded leg yaga wuya kawai hakan zai bata so se yayi sticking to first decision d'in kawai: na miyar mata da kud'in. Kwatancen gidansu ya buk'ace ta da tayi mar wanda tayi ba tare da gardama ba. Chan cikin Jiddari suka shige. Tunda Afzal yake be ta6a shiga kwamacalan unguwa ba kaman wannan se yau, yasan war haka motansa ya fita daga kamanninsa ya dawo wani abun na daban saboda potholes da kwatamin daya rink'a shiga. Sun kai wani junction ta buk'ace sa daya tsaya.

   "Ina ne gidan naku?" Abinda ya fara tambayarta kenan.

   "Mota baya iya shiga layin zan k'arisa daga nan nagode."

"Acewarki kawo ki kawai nayi saboda inada ra'ayin hakan? Am here to apologize to your parents and tsaya ba sekin karya min handle na mota ba" ya buk'ace ta ganin tun d'azun take k'ok'arin bud'ewa amman ta kasa. Fitowa yayi ya zagaya sannan ya bud'e mata k'ofar tare da miqa mata hannunsa.  A cewarta gabad'aya nufi yake da ta sanya nata aciki saboda ya taimaka ya fito da ita daga motan sede wani hanzari ba gudu ba tana gwada yunk'urin sa hannunta cikin nasa kawai taga yaja hannun nasa baya da sauri yana me kad'a mata kai "Tray d'in zaki miqa min" ya sanar da ita. Wani irin kunya kaman ta tone k'asa tasa kanta aciki ta jiyo amman wallahi seta rama ba shakka da gangan ya mata hakan don ya kunyatar da ita. "Kar ka damu ina da hannu I can manage" ta fad'a rai a murtik'e tare da murgud'a mai baki. Murmusawa yayi yaja gefe tare da crossing arms nasa a faffad'ar k'irjinsa yana me kallonta. Yasani sarai bazata iya fitowa ba harta sai ya taimaka mata toh why don't he enjoy the moment?

   Amal tafi minti biyu tana k'ok'arin fitowa amman ta gagara, ko kad'an k'afan nata baison nauyi ai kawai ta rushe da kuka har anan Afzal be motsa ba seda yabari ta sha wahala ta shiga neman taimako da kanta. Ganin ba mahalicci se Allah ta kewayo da kallonta a garesa, dagangan shiko ya shiga duban lokaci a agogon dake d'aure a hannunsa pretending as if beda masaniya game da abinda takeyi tun d'azu.

   "Bawan Allah don Allah ka taimaka min bazan iya fita ba." Dariya ne ya k'eto mar sosai amman ya dage ya danne tare da matsowa kusa da ita. "So kin iya magana da ladabi haka dama?" Ya tambayeta yana me k'are mata kallo.

  "Ni ba abinda na buk'ata ba kenan" ta amsa tana me kawar da kanta haka kawai bata jin dad'in had'a ido dashi, "Ni ka taimaka min in samu in fita daga wannan motar nakan please!"

  "Ohh! Rashin kunya kuma zakiyi min? Kinsan kad'an ne daga cin aiki na in barki har sekinyi tsami cikin motan nan ko? Don't you dare me young lady."

   "A'a kayi hak'uri don Allah." Cike da rashin mutunci ya taimaka mata ta samu ta fito daga motan suka shiga takawa zuwa gidan nasu wanda baida nisa daga inda Afzal yayi parking. Sede duk wani angle da suka wuce se sun zama topic and side of attraction. Surutu babu wanda basu ji ba amman duk haka suka manna musu har suka k'arisa gidansu Amal d'in.

Gida ne dai-dai da d'an talaka bawan Allah wanda za'a iya cewa be rasa ci da sha ba da kuma tufafi. D'akuna biyu ne gabad'aya a gidan a jere seda toilet d'aya daga other end d'in sekuma kitchen a opposite nashi, suna da famfo a tsakar gidan wanda ba sai anje ibo ruwa daga waje ba. Dai-dai Mami ta fito daga kitchen kenan su Amal suke k'arisowa tsakar gidan da Afzal riqe da ita, ai ba shiri tayi baya ta b'oye kanta cikin kitchen d'in tana me leqensu ta window. Salati kawai ta shiga yi ganin yadda mutumin dake sanye da suits ya riqo mata 'ya a cewarta gabad'aya wani masifa Amal taje ta kwaso musu sanin sharpness na bakin 'yar nata kaman razor. Tun farko dama bata goyi bayan zuwa aiken nan ba don de ba yadda ta iya ne Amal tafi k'arfinta gashi Papi (kakan Amal) da take d'an jin maganansa ma bai gida balle ya mata. Yau ina zata sa kanta Amal ta ibo musu abinda yafi k'arfinsu. Tunani kala-kala ba wanda ba tayi ba. Tunda suka shigo Afzal ke bin gidan da kallo, tabbas talakawa ne amman hakan be maida su k'azamai ba. Ko leather d'aya  be gani a k'asa ba ko ina an share tsaf ga kuma k'amshin turaren wutan dake tashi. Suna k'arisowa dai-dai tsakar gidan suka tsaya, se anan ya saketa tare da jan baya kad'an hakan ya bawa Amal daman sauk'e nauyayyiyar ajiyar zuciya.

"Ina Mamin naki?" Ya tambayeta ai take zuciyan Mami yawani har6a shikenan nata ya k'are yau ga Papi bayi nan yayi tafiya.

"Dake fa nake" Afzal ya kuma fad'i jin bata bashi amsa ba. Tsaida kewaye-kewayen da takeyi don neman Mami tayi tana me dawo da kallonta a garesa "Gani nayi tare muka shigo gidan taya kake tsammanin zan san inda take?" Ta tambayesa cike da rashin kunya. Cike da d'ambun mamaki Afzal ya tsaya yana kallonta shin wannan wacce irin fitsararriyar yarinya ce? Ace ko kunyan idonsa batayi ta rage wani abun? Sai dai ya daina mamakin hakan tuna 'yan qauye da masifaffen rashin kunya ga kuma shaidan dayayi mata na 'yar gudun hijira, tama daina basa mamakin. On the other side kuwa cikin Mami ya gama d'iban ruwa ji take kaman ta cafko Amal ta nad'a mata na jaki upon all the trouble data janyo masu still tana da bakin yima wannan security (as yadda ta ma Afzal shaida ganin sa sanye da suits) rashin kunya? Lallai kuwa tayi hak'uri ta rufa musu asiri.

"Mami!" Amal ta k'walla wa mahaifiyar nata kira, shiru kukeji ba amsa. "Mami don Allah ki fito daga b'uyan nan ni bance miki bala'i na kawo ba wannan mutumin gefe nan ne yazo baki hak'uri ya kad'e miki 'ya" ta sanar a fili. Se anan Mami tad'an ji sukuni but even still ta kasa fitowa gani take kamar k'arya Amal keyi saboda sau dayawa takan yi mata hakan, ta d'ibo bala'i daga waje sannan ta fake tazo tace alkhairi ta kawo.

"Mami wallahi zan k'ariso in janyo ki daga kitchen d'innan" tafad'a tana kallon setin windon da Mami ke leqe daga gun ai tuni ta miyar da fuskarta ciki, ashe de Amal ta ganta. Numfasa tayi sannan ta fito alokacin kuwa Afzal ji yake idan be saki wannan dariyan daya k'eto mar ba ze iya mutuwa. Wannan wacce erin matsoraciyar uwa ce? Ai kam dole Amal tayi rashin kunya haka daga ganin mahaifiyar natan batayi kalan me tsiwa ba bale har ace zatayi discipline Amal.

Da k'yar d'in k'yar ya samu ya maida dariyan ciki ahaka ma seda yayi kad'an a waje wanda a sanadin haka Amal ta juya ta galla mai harara sede be ganta ba dake hankalinsa gabad'aya ya duk'ufa akan Mami yana mey mamakin yadda akayi basu kama sekace ba mahaifiyarta ba. Ashe bashi kad'ai ne bayi kama da Umminsa ba (mahaifiyar shi.)

"Sannu da zuwa bawan Allah" Mami ta fad'a tana nufo su cike da tsoro da fargaba.

"Yauwa Mami" Afzal ya amsa. "Ina yini?" Ya gaisheta cike da ladabi had'e da durk'usawa kad'an. Ai gaisuwan da Mami bata amsa ba kenan ta shiga basa hak'uri.

"Don Allah idan wani abun Baby tayi ma kayi hak'uri bawan Allah wallahi banida abun da zan iya baka banda hak'uri" tace ba alaman kwanciyan hankali a tattare da ita. Ido Amal ta juya cike da takaicin abinda Mami keyi gaban wannan maras mutuncin bawan Allah'n, taya zata tsaya tana basa hak'uri while shi ya kamata yayi hakan?

Afzal ya bud'e baki zeyi magana kenan Amal ta riga sa "Wai ni Mami yaushe nace miki nayi mar laifi? Dubi fa, dubi k'afa nafa" tayi maganan tana miqar da k'afanta a hankula so Mami could see "Karya min k'afa yayi."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Baby!" Mami tayi exclaiming tare da yin kan 'yar nata tana me zaunar da ita a hankali bisa wani benchin dake kusa tana mata sannu in the process.

"Look Mami ni ban karya wa 'yarki k'afa ba don't listen to her" Cewar Afzal.

"Wallahi ya karya" Amal tayi saurin fad'i tana katse Mami "Idan ba karya min k'afa yayi ba toh seya fad'i dalilin daya sa ban iya taka k'afan."

"Yi shiru Baby na sannu ai ko baki fad'a ba gashi kumburin k'afarki ta nuna kin karye saidai kariya nawa ne?"

"Kaman biyu ne inji likitan" ta fad'a bayan tasan sarai k'arya take. Se wani zum6uro baki take cike da shagwa6a a yayinda Mami ke ta mata sannu tana shafa k'afan a hankali.
Shi de Afzal ya rasa nayi, ya rasa menene yayi yau Allah ya had'a sa da dramatic people kallan wad'annan, ace ba babba ba yaro? Hmm shide gado ba gwaninta ba. Da kalan uwa me d'aura wa k'arya gindi haka ai ko hannu Amal ta d'aga ta zagi mutum a kan layi baza'a ga laifin ta ba tunda gashi ba tare da bincike ba mahaifiyar nata ta hau ta zauna akan k'aryan da 'yar nata ta shirya na cewa an karya mata k'afa.

"Sannu ko Baby bari Papinki ya dawo a yanka miki d'aya daga cikin kajin kiwon nan. A kariya biyun har kika iya kike taka k'afan? Sannu." Har anan bata yi ta kan Afzal dake tsaye duk mamaki yabi ya mamayesa ba.

"Mami?" Ya kirata ganin wannan draman nasu bana k'arewa bane gashi kuma yana da k'arancin lokaci.

"Tsaya tukuna bawan Allah in gama da 'yar tawa ita kad'ai Allah ya bani-"

"Mami!" ya katse ta cike da rashin hak'uri, shi kansa besan lokacinda ya fusata har ya kira ta da tsiwa haka ba. Da mamaki both Mami da Amal suka juyo suna kallonsa, a yayinda zuciyan Amal ke raya mata itama ta miyar masa da masifan.

   "Kinga na farko ni ban karya wa 'yarki k'afa ba I admit I wasn't watching the road attentively na gauce akan hannuna na yo kanta na kuma bugeta and am dearly sorry" ya fayyace mata. "Amman ban karya mata k'afa ba" ya k'arisa.

"Baka karya mata k'afa bafa kace? Ban gane ba, yo ko nufi kake kawai don ado likitan ya d'aure mata k'afar da bandeji?" Ta tambaya cike da mamaki tana kallon kumburarren k'afan Amal tare da kewayo da kallonta a gareshi, ba shakka akwai rainin hankali anan.

"Ni ba abinda nake nufi ba kenan amman de kam ban karya wa 'yarki k'afa ba, targad'e ne ta samu tun achan kuma Dr'n ya sanar da ita hakan bansan dalilin da yasa tace miki kariya ne ba."

"Hakane Baby?" Ta tambaya tana maido da kallonta akan Amal dake faman raba ido.

"Mami har sekin tambayeta ne? Da girma na ne zan tsaya ina miki wasa da hankali? Kuma idan da har banida niyyan admitting laifin da nayi do you think zan bar duk abinda nakeyi in nemi har gidanku domin in baku hak'uri akan hak'urin dana ba ita Amal d'in? Har kuma in kaita asibiti, think please" Daga yadda yake magana za a san ransa ya soma 6aci kuma bako k'arya acikin duk
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment