Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻```

Mun tsaya

Sai ta ce, “Kaka ina ruwanta da ni, ni fa ban kula kowa ba tunda nazo.” Shatima ya dubeta fuskarshi babu walwala, “Kije gida na gode kawai.” Mamanta ta ce, “Ai ita sakarya ce, shegen kishi ta dora ma ranta.” Hajiyarshi ta ce, “Nafisa ai dole kuwa ki koyi hakuri da danne kishi tun da Allah Yasa ba ke kadai ce za ki zauna ba.” Fuu! Ta fice ta nufi gida.

Su Amna suna dawowa suka soma shirin.. tafiya. Shatima ya ce, “Ni dai ba ni ki ka zo dubawa ba.” Ta ce, “Waye ne nazo dubawa?”
Ya ce, “Kin zo danna waya ne da zama a waccan kujerar.” Ta ce, “To ina zan zauna?” Ya nuna bakin gadonshi.
“Ga guri nan.”Ai tafiya zamu yi, tunda ka ji sauki. Haka
ma ya yi min dadi.” Ta fada cikin yake. “Ban gaji da ganinki ba.” Ya fada yana kallonta. Ta ce, “To kayi ta kallona na minti biyu.” Anty tayi dariya ta fita. Kaka ta ce, “Ikon Allah! Yaran yanzu ba kara.” Amna ta ce, “Kaka ban ce komai ba.” duk suka sa dariya, sannan suka fice. Rakiya gurin mota har da Hajiya.
Zuwa washegari Shatima yayi sarai. Da safe iyayen sun zo duba shi, don Mustapha ne ya kwana. Ganin jikin nashi, shi ne ya ba su damar saka shi tsakiya suna tambayarshi wannan damuwa da Likita ya ce za su nesanta shi da ita.
Shatima ya yi shiru. Hajiya ta ce, “Haba Shatima, kana son saka mu a cikin damuwa ko?” Yayi murya irin ta yaron da ke gaban iyayensa irin ‘yan gatan nan.Ya ce, “Ku bar shi kawai, ko na fada ba lallai ne ku amince ba.” Alhaji ya ce, “In kaga ba a amince ba to abin ya shafi addini ko mutuncinmu.”


Shatima yayi shiru don dai ya dan kara ja musu aji. Alhaji ya ce, “Kayi magana mana Babana.” Shatima ya ce, “Wata yarinya ce ni ke son in cike ta hudu da ita su Hajiya suka ce a’a, kuma ni gara in fasa auran duk ukun nan in aureta ita daya. Yanda ni ke ji kamar zan rasa raina…”
“Kai yi mana shiru!” Hajiya ta katse shi. “Na ce ban yarda ba da karin wani aure.” Shatima ya koma ya kwanta a hankali, bai ce komai ba.Alhaji ya dubi Hajiya, “Wai kin manta da
zancan Likita ne?” Ya sake matsowa kusa da Shatima. “Babana ‘yar gidan wane ne?”
Shatima ya ce, “Alhaji marainiya ce, ubanta ya mutu. Na yi ma Allah alkawarin kula da ita, aurenta shi ne zai fi bani damar lura da ita, domin zata kasance kusa da ni, in ko na barta na ce zan ke taimaka mata, kila wani lokaci yazo wani yanayi na daukaka ko akasin haka ya sani in manta da ita. Wannan ce damuwata, in har zan samu yardarku zan zama a cikin farin ciki mai dorewa.”
Hajiya ta ce, “Ka san Allah…” Alhaji ya daga mata hannu tare da cewa “Kiyi min shiru.” Ya kalle shi, “Yaushe ka ke son aje zancen auren?”
Ya ce, “In an sallame ni gobe ko zuwa jibi ne sai aje. ” Ya ce, “Shi kenan ka Kaddara cewa ka aureta an gama.” Ya kalli Hajiya, “Na haramta miki sake ďauko zancan nan in dai na isa.”
Kwafa tayi sannan tasa kai ta fice daga dakin. Alhaji ya ce, “Kar ka damu, zata sauko da zaran na lallasheta. Zan sanar da Babanka Musa sai aje gidan iyayen yarinyar, sun san dai da kurewar lokacin ko?”
Ya ce, “Sun sani.” Ya ce, “To ba ka da sauran damuwa in dai wannan ce. Yanzun dai zan wuce da Hajiya gida, ku ci gaba da zama da Mustapha in ta huce zata dawo.”
Suna tafiya ya dauki wayarshi ya kira Munnir ya ce yana gurin aiki. Shatima ji yake kamar a sallame shi yaje yayi aikin da zai saka Munnir. Haka dai ya hakura har karfe biyar, Munnir ya taso. Ya ce “Don Allah yana son yaje gidan su Salma ya bata wayarshi zasu yi magana.”
Munnir bai so ba amma ba ya son ya bata masa rai, tunda duk sun ji labarin abin da Likitan ya ce a kansa, ya tafi.
Yana zuwa kofar gidan Yayanta yana fitowa. Suka gaisa, ya ce “Ina Alhajin yau?” Munnir ya ce, “Shi ne ya aiko ni, ina yarinyar nan?’
Yaya Auwal ya ce, “Umma Salma tana ciki, bari in kira ta.” Duk zatonshi Munnir ne mijin da Shatima ya ce zai kawo mata, har yana fada mata.
“Kin gane abokin nan nashi? Ina jin shi ne zai aure ki. amma kije ki gani.” Tare suka fito, ta gaishe shi tare da tambayar Alhajin. Ya ce “Shi ne ma ya ce in nazo in kira shi za kuyi magana.”
Ya soma kiran layin Shatima. Shi ko Yaya Auwal yana can gefe yana lura da su saboda tsaro. Shatima ya daga wayar Munnir ya mika mata tare da fadin. “Gashi.” Ta amsa tayi sallama. Shatima ya amsa. Ya ce, “Salma.” tace”Na’am! Yaya.”
Ya ce “Ina Yayanki Auwal?” Ta ce, “Gashi can tsallaken titi.” Ya ce “Kira shi ki ba shi wayar.” Ta kalli gurin da Auwal yake suka hada ido.
Ta yafito shi da hannu alamun yazo. Ya zo, ta ce “Yaya zai maka magana.” Auwal ya ansa tare da cewa “Alhajin ne?”
Bayan sun gaisa ya ce, “Salma ta ce min haya ku ke yi ko?” Ya ce, “Eh haya ne Alhaji.” Shatima ya ce, “Ina wanda gidan ke hannunsa?” Ya ce, “Makocinmu ne.”
Shatima ya ce, “Ina son ya samo muku wani gidan hayar za ku tashi a wannan gidan, ko ba ya nemowa?’ Auwal ya ce, “Yana yi.” Shatima ya ce, “To ina son duk yanda za’ayi gobe a samu gidan da zaku koma saboda za a zo neman auran Salma.
Ka amshi lambata a hannun wannan abokin nawa, koda wayar wani ne ka kira ni ka fada min.
Auwal ya ce, “To Alhaji, Allah Ya saka da alkairi.” Shatima ya ce, “Ba komai, ba Salma to.” Ya kalli Munnir ya ce, “Ka bani lambarsa.”
Ta amsa ya ce “Sai ma na fada ma Yayanki ne zaku canza gidan haya kin ji ko?” Ta ce, “To
Yaya.” Naji muryarka kana yin mura ne? Ya ce, “A’a na gaji ne, abubuwa sun yi min yawa ba ki ganni ba, zan zo.”
Ta ce, “To Yaya amma yaushe ne za ka zo
din?” Ya ce, “Ko jibi haka, kada ki damu ba
Munnir wayar ta ce to sai anjima.” Ta mika ma Munnir tare da fadin “Gashi Yaya.” Ta dan durkusa ta bashi. Suna tsaye ya tafi, Auwal ya ce, “Muje ciki muyi magana da su Inna.”
Auwal ya fada musu abin da Shatima ya ce.. Inna ta ce, “Kai ku tsaya! Ni fa ina tsoran wannan al’amari, kar fa garin son abin duniya mu sa kanmu uku! Yanzu in tsakani da Allah za’ayi ga inda aka ganta ba za a zo neman auranta nan ba?” Yaya
Auwal ya ce, “Inna babu kyau munanan zato, mu
fa ya ce mu nemo gidan hayar zai biya. Kuma manyan mutane ne za su zo kin ga ai mu ma ba za mu so su same mu a kaskance ba.” Yaya Hadiza ta ce “Inna yanzun dai a bar wannan zance a nemi índa za’a samu gida tunda dama kudinmu ya kare tun wancan watan. Masu gidan suna ta yi mana rashin mutunci.
Salma ta ce, “Allah ne ya kawo mana mafita dama muna ta ya ya za a yi a samu dubu sha biyu da za a baiwa masu gida?
Suka ce, “Haka ne kam!” Auwal ya ce “Ina ga ba zan yiwa Maigidan nan maganar wani gidan ba, gara in je in sa samu Bala dillali. Hadiza ta ce, abin da zance kenan, ba za’a rasa gida a hannunshi ba.”
Ya mike “Ina zuwa ma dai ku gani, da zafi zafi a kan bigi karfe.
Cikin sa’a Bala ya ce masa “Akwai gida guda
biyu, daya na zaman mutum uku, daya kuma na zaman mutum biyu. Daki nawa za ku kama?” Auwal ya ce, “Daki biyu ma ya ishe mu.” Bala ya ce, “To me zai hana ku kama gidan can na kusa da ku, gidan dan kurma wanda ya saida
Auwal ya ce Matsalar dai biya mana za’ayi
kila kudin ya yi yawa ko?” Ya ce, “Dari ne da goma sai mu da za’a sallama.” Auwal ya ce, “A dai yi mana sauki mu gani.” Ya ce, “To magana daya dubu tamanin ne, sai mu kuma a sallame mu.”
“To duk yanda aka yi zan same ka gobe.” Bala ya ce, “In kuma na wancan ku ke so daki biyu dubu talatin da biyar ne. Auwal ya ce zan fada masa duka. Haka kuwa sai washegari da misalin karfe goma Yaya Auwal ya kira lambar da ke jikin katin da Munnir ya bashi..
Shatima ya daga, ya ce Ni ne Auwal lambar Alhaji ce? Shatima ya gane ya ce, “Ni ne.” Ya kalli Mustapha da ke hada kayan su don Likita ya fita yanzun bayan ya sallame su.
Ya ce, “Kaje waje. Bayan fitarsa Shatima ya ci gaba da magana. “Auwal ka samu gidan?” Ya ce “An samu alheji.” Ya fada mishi farashin su. Ya ce, “To ku kama naku kadai din zan ba abokina dubu dari ya kawo muku anjima, in da dan wani gyara sai kuyi.”
Auwal ya shiga godiya, Shatima ya kashe.” Nafisa tana isowa asibitin suna fitowa. Ta ce, “An sallame ku ne? Suka ce “Eh.” Don haka tare suka juya.
Da suka isa gida Hajiya ta ce “Kar ya hau samanshi, a bude masa falon Babansu saboda mutane za suke zuwa duba shi.
Ya yi Transfer din dubu dari a cikin account din Munnir. Ya ce, “Ya cire ya kaima su Salma. Da ya taso aiki kuma ya ciro yazo ya yi sallama da Salma ya bata..Ranar kuwa suka biya kudin gidan aka ba su mukullin. Ranar suka share, washegari da safe, suka dan yi saye-sayen labule da ‘yar ledar kasa suka tafi suka gyara suka shiga.
A daren ranar Alhaji da dan’uwansa Alhaji Musa Baban su Nafisa, suka zo gurin Shatima suka ce, “Batun wannan yarinya za a je gurin iyayenta.
Shatima ya ce,. “Su bari sai washegari. Da yammacin washegari kuwa Shatima yayi fes cikin kananan kaya, in ka ganshi dole ya birge ka ya dauki makullin mota ya fita.
Hajiya ta ce, “Ina zaka?” Ya ce, “Zan dan zaga gari ne, na gaji da zaman gida.” Ta ce, “To sai ka dawo.”
Kai tsaye gidan su Salma ya dosa, cikin
zuciyarshi yana son in ya zo gidan su nada
ya tambayi inda suka koma.
Cikin sa’a ma yana fitowa sai ya ji Auwal yayi masa sallama. Ya waiwaya ya bashi hannu suka gaisa, ya ce “Ai ina can naga wucewar motarka.” Shatima ya ce, “Ina ne gidan naku?” Auwal ya ce, “Baya ne kadan.” Ya ce, “To shiga muje. Ya ji dadin ganin gidan har ciki ya shiga. Su Inna da sauran ‘yan’uwansu da basu wuce ba suna ta godiya. Ya samu Salma tana wanke wanke ta saki tazo ta tsugunna ta gaida shi. Ya ce, “Salma nan yayi?” Ta ce, “Kai! Sosai
ma.” Cikin mamaki tayi maganar. Ya dubi Inna, “Gurin wa za a zo neman auran na Salma, saboda anjima za sú zo?”
Inna ta ce, “Gurin kanin Babansu ne a can Kofar kaura ya ke, in an ji lokacin da za su zo sai a je a dauko su da aminin Babansu nan makotan da muka taso.”
Shatima ya ce, “Yau za su zo karfe takwas na dare Sannan kuma Inna bikin yau saura kwana ashirin da biyar.” Inna ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce “In sun zo iyayen namu za ku ji komai.” Ta ce. “To shi kenan, Allah Ya kawo su. Shi kuma Kawun nasu za a je a zo da shi.”
Da zai tafi ya ce Salma ta zo, a zauren gidan suka tsaya. Ya kalleta yana murmushi.
“Kin shirya aure nan da kwana ishirin da biyar?” Ta dan juyar da fuskarta cikin kunya ta kalli bango. Ya ce, “Kiyi magana.” Ta ce. “Zan yi mana.” Ya ce “To juyo ki kalle ni.”_____
*🏚️RANA DAYA 🏚️*


CHAPTER 14


*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*


```🧕🏻🧕🏻Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551🍉🍉🥥🥥```

```Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551```

```Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi🙈🙈```

```Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai```

```🗣️🗣️🗣️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi🥥🍉```

```Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari🙈🙈 akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan🍉🥥```
```Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida🐓🐓🐓 Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata```

```Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551```

```Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻```


Mun tsaya

Shatima ya ce, “Yau za su zo karfe takwas na dare Sannan kuma Inna bikin yau saura kwana ashirin da biyar.” Inna ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce “In sun zo iyayen namu za ku ji komai.” Ta ce. “To shi kenan, Allah Ya kawo su. Shi kuma Kawun nasu za a je a zo da shi.”
Da zai tafi ya ce Salma ta zo, a zauren gidan suka tsaya. Ya kalleta yana murmushi.
“Kin shirya aure nan da kwana ishirin da biyar?” Ta dan juyar da fuskarta cikin kunya ta kalli bango. Ya ce, “Kiyi magana.” Ta ce. “Zan yi mana.” Ya ce “To juyo ki kalle ni.”

Ta juyo ta dube shi. Ya ce, “Kina sona?” Ta
zaro ido cikin tsananin mamaki. Ta murtsuke idanunta wai ta ga ko mafarki take yi. Ta sake kallonshi a gabanta. Ta cce “Nasan kana tsokanata ne, ni ban fi
yar wanke-wanken gidanka ba.” Ya ce, “Ni fa
na tambaye ki ne kawai, kina sona?”
Ta durkusa kasa, “Don Allah kada ka cutar dani, wallahi na dauke ka na musamman a rayuwata, na soma tsoron ka.” Hawaye suka zubo mata.
Ya tsugunna shima, “Ba ki sona dai a takaice kenan ba za ki aure ni ba?” Ta dago ido, suka kalli juna hawaye suna sauka a kan kumatunta.
“Ni ina sonki, kuma zan aure ki, kuma za ki


yi karatunki har ma ki cika burinki na zama ‘yar
Jarida. Ki ci gaba da daukana na musamman a
rayuwarki, koda ba ki sona.” Ya mike tsaye. “Sai dai ke ce ta hudu da zan aure ku rana daya.” Ta mike tsaye, “Don Allah ka fada min wani zancen daban ba da wadannan zantukan na. zolaya ba.”
Yayi murmushi, “Na tafi zan sake zuwa.” Nan ya bar ta tsaye tana al’ajabi. Ta jingina da bango, ba zan fada ma kowa wannan zancen ba, don na san ba gaskiya yake fada min ba.
Ta share idanunta ta nufi cikin gidan ta ci gaba da harkokinta, tana jin su suna tattauna zancen dauko kanin Babansu. Ta ce a ranta ‘Ni dai zan ga ikon Allah!’
Daga nan gidan Anty Momiyo ya nufa, ta kai shi dakin da a kwatunan suke. Yayi murna da ganin su don sun birge shi. Ya ce, “Yanzun nawa ne cikona da Allah kai su yau, zuwa jibi a kai ma kowa kayanta.”
Anty Momiyo ta ce, “Ai ba don ciwonka ba yau muka tsara za a kai kayan amma jibin ma ya yi. Ya ce, “Nawa ne ciko na?”
Ta ce, “Hajiyar ku ta biya kudin ukunnan, tace ba za ta bada na karshen nan ba, shatima ya ce Au! Ta sai min ne? gaskiya ta min komai. To. ki cire kudin na Salma din, sai ki bata canji. Ta ce, Ta ce tuni na cire har ma nayi maka karambani.”
Ta janyo wata Ghana most go wasu lesuka ne masu shegen kyau, ta ce “Ka gan su guda goma sha biyu ne kowacce guda uku.
Ya ce, “Ai da kin bani kudina don na ba Hajiya kudin komai.” Ta ce, “Duk dai ba zai ki ba.” Ya ce, “Bari ma in je in samu Hajiyar muji ya za ayi?” Ta ce, “To muje da akwatunan mana. Ka dibi wasu nima in diba a mota ta muje ya ce “To.”
Yasha mamaki da Hajiya ta fito da kayan da aka siya. Sai dai ta ce ita na mutum uku ne, sai, yasan yanda zai yi da dayar.
Ya ce, To bari in bada kudi itama sai a kawo mata.” Hajiya ta ce, “Sam! Je kasuwa ka siya. Yayi shiru yana kallon kayan.
Anty Momiyo ta ce, “Kana zuwa kasuwa za ka hada komai.” Ya ce, “Anty ku ne ku ka san kayanku. To ke don Allah in ba ki ki sai mata tace yawanci kayan nan ba ‘yan nan ba ne ba, lallai a samu irinsu ba. Amma ka kawo sai a duba.”
Hajiya tana jin su kala bata ce ba. ya ce, “Zan yi miki Transfer cire mata kukan ta kija mata cikin akwatin ta kada kuma ta ce ban da ita marainiyar Allah. Take ya tura mata kudi don ta sai ma Salma kayan lefeb
Lefen Amna a ka soma kawai kafin ranar sai da ya sanar da ita zuwan su Hajiya kuma sai da
ta sa kayan Amna sun fi na kowa a cewarta babban goro sai magogin karfe. Suma sun samu sauka ta musamman sannan sun dauko tukuici mai tsoka.
Washegari aka kai na Nafisa. Nan ma sun yi bajintar tukwici. Na Aliya ma an kai, suma sun ba da daidai karfinsu. Aka dawo ana ta tsegunguma.
Salma kuwa cewa yayi a bari zai kai mata, don ya ji lokacin da Hajiyarshi ta kira Baba Alhaji Musa tana tambayar shi game da Salma, bayan sun dawo kai sadaki da kudin gaisuwa. Wai nawa suka bada?
Ya ce, “Dubu hamsin suka ce kudin gaisuwa ashirin.” Ta ce,”Wai an binciki asalin yarinyar?” Ya ce, “Shi ya ce ya bincika.” Ta ce, “Yasan ‘yar matsiyata ce shi yasa baya so aje gidan, ai za a kai lefe, za’a zo min da labari.” Shi kuma yana falon bata san ya shigo ba, don haka sai ya juya.
Ranar da za’a kai na gidan su Salma ya ce su bar shi shi ne zai kai. Hajiya ta ce, ai ko dole a kai. Ya ce, “Hajiya kiyi hakuri zan kai mata da kaina.”
Alhaji yace, “Wannan fa al’ada ce, don haka ki har shi kawai.” ya kai da kanshi. Bayan ya kai ya baro gidan, Inna ta ce “Kai Hadiza! Ku lura da lamarin nan da kyau. Ba shi da dangi ne zai kawo lefe da kansa! ni fa ina tsoron in’kai ‘yata mahallaka da kaina?”
Hadiza ta ce, “Ni dai ban tsorata ba, ai ba boyayyu ba ne. mu dai yanzun mu san ya ya zamu yi da wannan kudin, a sai mata gado da ‘yan kujeru.”
Salma dai bata magana, domin har yau gani take ba’a ne duk da kayan da aka kawo masu tsada na lefe, da kudin dinki Naira dubu dari. Sun yanke a cire ishirin tayi dinki, tamanin a
hada da saba’in a sai mata kayan daki da na aiki,
tun dai daga wannan ranar har yau Salma bata
kuma sa shi a idonta ba.
Domin ko da ya kawo kayan lefe bata nan taje cefane, gashi har yau saura kwana goma biki cif-cif!
Tun sassafe ranar Amna ta kira Shatima tana ce masa yau ‘yan gidansu za suje jere can Kaduna. Ya ce, “Ai tuni na ba da makullai ko?” Ta ce, “To honey ai ba wanda yasan gidan ka manta?” Ya ce “Au! Haka ne, to su biyo ta gidanmu sai su dauki kananina Mustapha.” Ya sauko kasa ya shiga gurin Hajiya ya sanar da ita. Ta ce, “To ai ba dan rakiya za’a basu ba, ka dau har da abinci.”
Nan tayi waya in da ake yo musu abincin sha’ani, tasa ayi abinci na alfarma da kaji. Lokacin da suka iso daukar Mustapha har abin sha da na cin an shirya, suka kwasa suka wuce.
Shatima ya ce musu za su ga plat guda hudu duk wanda suke so su zaбa. Na ciki suka zaba wai saboda tsoro. Mustapha dai yasha mamaki, domin sabon aiki yaga an tsiro ma gidan an canja fenti, sannan ga wallpaper irin na zamani an zuba a bangon tun ma kafin kayan su iso guri tsaf.
An zuba kaya fadin su ma kauyanci ne, kayan kicin kuwa irin masu amfani da lantarki abin sai wanda ya gani. Dakuna guda uku kowanne an saka mishi gado na alfarma.
Daidai da kayan bayi abin ba da labari. Hajiya ta ce, “Ni nasan za’ayi haka. Ai harkar manya ba karya.”
Duk a ranar daí Ango yayi niyyar kai ma duk Amaran nashi da ke nan Zaria kudin walima shi da abokanshi. Abu daya ke damunshi yanda bai samu ya fayyace ma sauran Amaren cewa sun cika su hudu ba.
Nafisa ita ce yake da yakini a kan cewa ta sani domin ta kira shi bai daga ba, sai tayi masa message cewa ya daga wayarta suyi magana, tana son tabbatar da abin da taji Babansu yana fada ma Mama.
Ya ki dagawa sam! Ya sani sarai tana zaman jiranshi.
Gidan su Aliya suka soma zuwa shi da Munnir da wani abokinsu Usman. Cikin sa’a kawarta Aisha tazo ganin lefe, sai suka fito tare. An gaggaisa sannan ya bata dubu talatin ya ce, kudin walima, sannan suka bata katina na daurin aure, sai na dinner din da zasu yi bayan an kai Amarya.
Aliya tayi ta masa godiyar kudi har sai da ya ce, ta bari don Allah. Bayan barin su gurin ne abokan suke yabon halin Aliyan, suka ce daga gani tana da hankali kuma zai ji dadin zama da ita.
Gidan su Nafisa suka tafi. Gabanshi yana ta faduwa. A harabar gidan suka tsaya. Ya kira ta a waya, har sau hudu amma bata daga ba.
Yaje ya kwankwasa kofar falon. Momi ce ta bude. Ya ce, “Kira min Nafisa.” Ta ce, “To.” Sannan ta gaishe shi ta juya.
Sun kusa minti hamsin har ran Shatiman ya soma baci, bata fito ba tana can Mama tana fama da ita a kan ta fito ta ki, sai da taga ran Maman ya baci sannan ta tashi ta dauki dan mayafin doguwar rigar da ke jikinta, ta saka takalmi mara tudu ta fita.
Har ya ce su shiga mota su tafi sai ga ta ta fito kamar tana tafiya a kan kwai. Duk da cewa dare ne, kallo daya za ka gane ba walwala a tare da ita.
Ta gaida su gaba daya a tare, Shatima bai amsa ba illa kallonta da yake yi tare da tunanin me ma zai ce mata? Munnir da Usman suka koma cikin mota.
Ya cc, “Kudin walima da kati na zo ba ki.” Tayi shiru tana kallonshi. Yaje motar ya ce, “Ku bani katunanta.” Ya mika mata ta ce, “Ka bar shi, ni ba zan yi wata gayyata ba.”Ya ciro kudin ya cc, “To ga kudin walimar ko itama ba za ki yi ba?” Ta ce, “Eh ba zan yi ba.” cikin bacin rai ya ce, “Ok.” Ya wuce ya shiga mota ya ce, “Ku muje.”

Please Login or Register in order to submit comment