Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

naked ba, bazan auri matar da batada kunya da kuma k'arancin ilimin addini ba kamar ki. You disgust me Nazeefah, idan har kinsan ciwon kanki kinsan ina ke maki ciwo baza kibari wannan aure ya auku tsakani na dake ba saboda I'll never learn to respect and regard you as a woman than a wife because kin riga kin zubar da darajar ki da k'ima da kuma mutunci a idanu na. Just to tell you how worthless you're, akuya ma tafiki daraja a idanu na" yana kaiwa nan ya tsaya don jin ko zata fad'i wani abu amman ko uffan ta kasa cewa. Hawaye ke bin k'uncinta kawai, tunda tasan kanta ba a ta6a humiliating nata haka ba, don ya fad'a mata wannan munanan kalamun ne dama ya ma Daddy k'arya yace yana son nuna mata wank abu? Ashe don yaci mata mutunci a gaban abokinsa ne? Don yasata ta tsani kanta? Bata san mey ya hanata miyar masa da magana ba a lokacin saboda sanin kowa ne Nazeefah nada baki ba'a ta6a ta tayi shiru se gashi a lokacin data fi buk'atan bakinta ya bud'u yak'i yin hakan. Toh mey zata ce masa bayan wannan munanan kalamun daya kwatanta ta dasu? Yes he might be right, there is amount of truth acikin duk abinda ya fad'a but just because Daddy yace ya basa ita doesn't mean he has the right to hurt her feelings like this. Ai ko macen da take sana'ar karuwanci ma bata so akira ta da mazinaciya.

Ganin bata da niyyan cewa komi banda hawayen da take tayi Afzal ya cigaba "They say a word is enough for the wise I hope this is message enough for you, you can go back in, greet your mother when you do sai anjima." Yana kaiwa nan ya zagaya to the driver's side ya tada motar tare da kad'a mata k'ura. Tsaye Nazeefah tayi wajen wane gunki se aikin kuka take, sauk'a har k'asa tayi a wajen tana kukan cire rai.

Wacce irin rayuwa ce wannan?

 


RANA D'AYA
#RD
 Love... King Miemiebee👄✨
[12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣

💦💦 🍃🍃🍃
*RANA D'AYA!*
💦💦 🍃🍃🍃
April, 2018

_Written by Miemiebee👄_


*PAGE 0⃣6⃣*



    "Nifa ka sani acikin duhu, wai meke faruwa ne?" Sultan ya tambayi Afzal dake tuk'i cike da rashin hak'uri da neman k'arin bayani. Shiru Afzal ya masa yana me sa hankali sosai akan tuk'in da yakeyi.

  "Triple A?" ya kuma kiransa kusan sau goma kenan tun zamar su cikin motar.

  "Bansan yaushe ka kurmance ba wallahi, referring to abubuwan da kaji na fad'a mata ai yaci kasan auranta mahaifinta yakeson inyi."

   "Nazeefan fah?" Sultan ya tambaya cike da d'umbun mamaki.

  "Ask me again" ya fad'a tare da basa d'aya daga cikin mugayen kallonsa sannan ya maida kallonsa kan hanya.

  "How?? Triple A kabani labari please."

  "Idiot ai labarin nakeson baka yasa nace ka taho."

   "Asshole" ya fad'a tare da kai masa punch a hannu "Am all ears" nan Afzal yashiga zazzage masa dukannim abubuwan da suka gabata tun daga yinin jiya, a haka har suka iso layin dake kusa da gidansu Amal.

   "Tsaya maza mey kuma zamuyi anan? Mey ya kawomu unguwan nan? Kode kayi 6atan kai ne?" Sultan ya tambaya nan take.

  "Nop" ya amsa tare da popping P d'in "Ina yarinyan dana fad'a maka na bugeta accidentally jiya?"

  "Yes" ya amsa tare da gyad'a kansa "Dr ya buk'aci a mayar da ita yau a sake treating k'afan so am here to fetch her" ya fayyace mar.

  "Toh shine se kai ne zaka kaita? Ai tunda ka riga ka biya kud'in komai se ka bawa mamanta transport fee tana kaita."

   "No Sultan I cursed this upon them, ganganci na ya kaini kad'eta I have to take full responsibility."

  "Toh Mr good samaritan jeka ina jiranka" ya amsa shi cike da gatsine. K'aramin mirror dake gaban driver seat Afzal yaja yana duban fuskansa tare da sake daidaita hulansa sannan ya fice. Shi de Sultan baice komi ba illa binsa da kallo da yake.

  Sallama yayi a hankali alokacin da yake sa kai cikin gidan. Amal ya tarar zaune akan benchin jiya da wani novel na English rik'e a hannunta ta zurfafa ciki tana karantawa. Sanye take da wata atamfa riga da skirt wanda ta mugun amshe kalan skin nata, kanta kuwa ba d'ankwali hakan ya bawa Afzal daman ganin silky gashinta dake nan kaman na bak'ak'en 'yan India. Kamashi tayi a tsakan kanta tare na nannad'e jelar wanda a sanadin haka Afzal be samu daman gano k'arshen ba. Kallonta ya tsaya yi musamman yadda ta miqar da k'afan nata me targad'e wane wacce ke jiran koda kuda ne ya ta6a ta hau bala'i da k'orafi.

  "Uhm uhm" yayi gyaran murya wanda hakan yasa Amal tsaida duk wani abinda takeyi ta d'ago kanta domin ganin wanene. Wani irin d'an banzan tsinkewa zuciyarta tayi ganin Afzal tsaye akanta da ratan da befi meters biyu zuwa uku tsakaninsu ba. Da sauri ta dukar da kanta a lokacin da idanunsu suka had'e tana me neman mayafi don lullu6e jikinta sede ba halin yin hakan dan k'afarta. Yadda zama ke bata wuya haka zalika miqewa don haka kawai ta shiga kare k'irjinta dukda cewa bawai ya bayyano waje bane. Shiko Afzal ganin ta soma yin wasu abubuwan yayi saurin juya mata baya totally dan kuwa bega abun gani ba achan da take ta wani faman tarewa.

  A hankali ta d'ago kanta taga gabad'aya ma baya ya juya mata aiko take ta murgud'a mai baki "Tafi nono fari" ta fad'i can k'asa-k'asa sannan ya k'wolla ma kira.

   "Mamiiii!" Dan k'ara irin na muryarta seda Afzal ya toshe kunnensa.

   "Ki fito kinyi bak'o and please ki taho min da hijabi na."

  "Toh" Mami ta amsa daga ciki, bada dad'ewa ba se gata nan ta fito, ganin mutum kaman Afzal ne yasata sakan murmushi. "A'ah Afzal ko?"

  Se anan ya kewayo nan ta tabbatar shi d'inne "Sannu da zuwa Baba na ina yini?" Ta gaishesa tana mik'a wa Amal hijabin data fito mata dashin.

   "Yauwa Mami ina yini? Ya gajiya?" Ya amsa cike da girmamawa.

  "Lafiya k'alau ya kayi tsaye haka? Ka k'ariso ciki mana. Ke Baby haka akeyi ne seki bar bak'o tsaye bazaki ce masa ya k'ariso ba?" Mami ta tambayi Amal data had'e gira gu d'aya.

  "Yo ba nace ya shigo ba yayi tsaye wajen" ta fad'a cike da rashin kunya. Baki Afzal ya bud'e cike da mamaki yana kallonta wato acikin had'uwa biyu da sukayi ya karance Amal is such a big liar, gashi comfortably take yin k'arya kuma bata d'auki hakan a bakin komai ba.

  "Toh gaisuwa fa? Kin gaishe shi?"

"Abinda na farayi kenan daya shigo" ta kuma amsawa. Shide Afzal bece komai ba. "Bari in d'auko ma taburma mana ka zauna Afzal ko ruwa ne kasha."

  "A'a Mami karki damu daga gida nake nazo d'aukan Amal ne ayi dressing k'afan nata kaman yadda Dr ya buk'ata" Kafin Mami tace za tayi magana Amal har ta tsoma baki ta soma k'orafi "Ni wallahi ban komawa asibitin chan in kanayi wa Allah ka koma inda ka fito nagode da kulawarka amman ban sake taka k'ofan asibitin chan." Har anan Afzal bece komi ba saboda yasan abinda ya tanadar mata.

  "Yau ina ganin ikon Allah!" Mami ta tsaya kallonta tare da dafe k'irji "Ke da hankalinki? Yanzu ya dace ki fad'awa mutumin da ke nema maki lafiya wannan kalamu? Wallahi karki bari raina ya 6aci in basa hak'uri yayi tafiyansa yaso k'afan naki yayi tsami ya ru6e in kaiki nan gun wanzan a gintile kowa ya huta." Dariya sosai comment na Mami yabawa Afzal don haka ya shiga gyaran murya don had'iye dariyar sede still seda curves na murmishi suka nuna a fuskansa. Wani kallo Amal ta watsa masa tare da fad'in wasu kalamun chan k'asa-k'asan muryarta yadda ita kad'ai tasan abinda tace.

  "Maza tashi karki 6ata min lokaci!" Seda ta gama tsiyarta sannan ta amince Mami ta taimaka mata ta miqar da ita.

  "Toh Allah ya kare Afzal kaikuma Allah ya biya."

  "Ameen Mami" daga fad'in haka ya fice Amal na k'ingishi tana mara mai baya har suka isa gun da motarsa ke. Kasancewar motar tinted ce Amal bata samu daman gane cewa da akwai mutum acikin motar ba shi kuwa Afzal shiru yayi mata daya ga tana nufan k'ofan gaba. Tsaye yayi yana jiran na aukuwa ya faru. Tana bud'e k'ofan kawai setaga bak'on fuska na kallonta, kunya tajiyo sosai yanzu Afzal yasan da mutum cikin motan yamata shiru har ta bud'e? Yamar kyau.

  "Ina yini?" Ta gaishe sa cike da kunya tana ja baya a hankali se kace ba ita ba.

  "Lafiya 'yan mata kin 6ata ne?" Sultan ya tambaya danko besan itace yarinyan da Afzal ke nufi ba.

   "Ban san da mutum aciki bane am sorry." K'ofan ta miyar mishi tare da d'ago kai tana kallon Afzal dake ta faman kallonta shima dariya ya ciko mar dam a baki amman ya dage ya danne. Ba tare da yace mata komai ba ya bud'e motan ya shiga wanda itama tayi hakan. Bayan ya kunna motan Sultan da kansa ya d'aure ya juya ya dubi Amal sannan ya kalli Afzal sam be kawo a ransa cewa budurwa ce Afzal ya buge ba cause yadda Afzal ya basa labarin k'iriniyar yarinyar seyayi picturing nata to be 13-14 years.

  "Itace yarinyar?" Ya tambaya not believing it.

  "Wai ba" Afzal ya amsa sa in an I don't care tone tare da yin reverse suka hau kan hanya. "Kana bani labari" cewar Sultan after a while "Amman Triple A bakada mutunci."

  "Da nayi meh?" Ya tambayesa yana me miyar da hankalinsa sosai game da tuk'in da yake a yayinda Amal dake baya ta ware kunnuwanta domin jin abinda wannan mara mutuncin yayi da har abokinsa ke mamaki haka.
 
  "Kaji kalan kalamun daka fad'awa yarinyan chan mana Nazeefah" ta6e baki Amal tayi, dama tasan za'ayi haka a yayinda ta cigaba da kasa kunne.

  "She needs to be told the truth" Afzal ya miyar masa ba tare da ya nuna damuwa ba.

  "Toh kai kasan ka k'yamaceta haka meyasa ka amince da k'udurin auren nata?"
   Aure de? Amal ta nanata a ranta, lallai ta tausayawa 'yar da zata auri wannan mutumi me uban ji da kai haka, ai kuwa gashi tun ba'a je ko ina ba abokin shi yace baida mutunci be kyauta ba, ko mey ya gaya wa yarinyan se Allah. Shiru tayi tana me cigaba da sauraran hiran nasu.

   "To make Abba happy" ya amsa sa simply.

   "Hmm fire on the mountain sunan wani abu, Afzal da Nazeefah a k'ark'ashin rumfa d'aya ai akwai show" jin Afzal be amsa shi ba ya cigaba "Triple A tell me something mana kode dama kanada interest akan yarinyar ne?"

   "Interest?" Afzal ya nanata cike da mamaki yanzu upon all people Sultan ne ze fad'a masa wannan batu? Lallai amman be kyauta ba, ai wannan zagi ne.

  "Dan Allah ka miyar da kallonka kan hanya kafin kaje ka zubda mu" yace da Afzal daya tsaya yana kallonsa da alama ya manta akan hanya yake domin ko niyyan kau da kansa ba beyi ba.

   "This is an insult to my face Sultan, ai ko Nazeefah ce autan mata I'll never learn to love her, she simply disgusts me."

   "Hmmm nide nayi shiru amm-"

   "Shut up Sultan" yace dashi tare da katse sa. Shirun da Sultan beyi ba kenan ya cigaba da neman tsokan Afzal har sanda suka isa asibitin amman ko uffan Afzal be ce dashi ba, hasali manna mishi yayi. Dukansu uku suka kuguma suka fita inda suka nufi cikin asibitun tun daga harabar Amal ta soma kauce-kauce ita bata so Afzal yayi hak'uri ya maidata gida, ita kad'ai tasan azabar dataji jiya sede ko kallonta beyi ba bale yasan tanayi. Bayan sun gaisa da likitan ya kewayo da fatan ganin Amal se de ya ganta chan tsaye bakin k'ofa ta maraice fuska. Murmushin mugunta ya saki sannan ya dawo da kallonsa akan likitan tare da yin gyaran murya, "Dr ya naga kaman jiya baku ja k'afar yarinyan can kaman yadda ya kamata ba?"

"Ba'a ja ba kuma Alanguburo? Meyasa kace haka?"

"Toh gashi k'afan nata yayi tsami ya kumbura-"

"Wallah bai kumbura ba" Amal da ta kasa kunne tana sauraronsu tayi saurin katsesa "Wallahi be yi tsami ba Dr don Allah karka sauraresa" ta fad'a cike da tashin hankali. Shareta Afzal yayi ya cigaba, "Gashi na kawota yau ina son ku jashi sosai please, a ja sosai saboda kar a samu complications nan gaba."

"Toh Alanguburo in shaa Allah ina yarinyan ne? Ke shigo mana" yace da Amal yana maida kallonsa a gareta. Ja da baya ta farayi da niyyan ta gudu.

"Don't even think of running ga nurses da securities kota ina sasu zanyi su kama ki" Afzal ya fad'a cikin tattausar muryar data mugun razana Amal da tuni tasa kuka. Wai don meyasa yake mata haka? Kode don rashin kunyan da take mar ne yayi tunanin ramawa ta nan? Tayi tunanin haka a ranta. Ai kuwa ya zama dole ta basa hak'uri yanzu dukda cewa yin hakan bawai yana nufin bazata kuma mar rashin kunyan bane idan yayi mata abinda be gameta ba.

"Afzal- no" tayi saurin kad'a kanta "Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri wallahi bazan sake ba."

"Yaya?" Ya nanata a yayinda dariya me k'arfi ya ku6uce mar bashi kad'ai ba harta Sultan. "Ni ne Yaya? Guy kanajin yarinyan nan?" ya juya tare da tambayan Sultan nan suka kuma fashewa da wata dariyar barin ma Afzal da yake sark'ewa. Amal ji take kamar ta bisu da mari, ba abinda ta tsana kaman a tsaya ana yi mata dariya amman ya ta iya?

"Wallahi a kullum kai Yaya na ne ai ko ido ma ma'auni ne" tayi saurin bashi amsa a rud'e.

"Kinga karki kaini inda Allah be kaini ba" ya fad'a yana composing kansa, "I don't have any sibling so am nobody's Yaya."

"Wallahi a'a kai Yaya na ne kuma ai bazaka so a cutar maka da k'anwarka ba ko? Dan Allah ka fad'awa likitan nan karya ja min k'afa da zafi."

"Nak'i" ya fad'a a takaice.

"Dan Allah Ya Afzal kayi hak'uri bazan sake maka rashin kunya."

"Wancan kuma ke ya dama ki shigo suyi miki abinda ya kamata na maidaki gida I have things to attend to."

"Dan Allah I'm sorry" ta fad'a tana kad'a kai.

"Doctor ka turo nurses su jawota jiki she's wasting my time."

"A'a don Allah zan shigo da kaina."

"Then make it quick" ya fad'a tare da galla mata wata mumunar kallo. "Kina fa 6ata min lokaci" ya kuma fad'i ganin bata motsa ba.

"Zan shigo zan shigo" ta fad'a a kid'ime sede fiye da minti biyu ta kasa takowa ciki.

"Ina nurses d'inne kam wai?" Afzal ya tambaya yana kewaya.

"A'a dan Allah zan shigo, wallahi zan shigo." Da hakan ta k'ariso ciki tana k'ingishi. "Please kace musu kar su ja min k'afan Ya Afzal."

"Nak'i" ya sake nanata mata ko d'igon tausayi babu a tattare dashi.

"Bazan sake maka rashin kunya ba wallahi na tuba."

"Guy pardon her please" fad'in Sultan dake tsaye daga gefe guda sede sanin taurin kai da zuciya irin na abokinsa yasan ba lallai bane ya jisa balle ya sassauta wa yarinyan.

  "Make me" ya ce dashi tare da basa one of his nasty looks. "Ba ruwanka you better stay out of this, nurses take her in ku ja min k'afan nata sosai don idan yayi tsami ina tabbatar muku da cewa zanyi suing asibitin nan naku duk ku rasa aikinku kuma" ya razanasu. Haka nurses suka taho suka ja Amal se ihu take tana had'a Afzal da Allah amman yayi tamkar bada shi yake ba, idan ba hakan yayi mata ba bazata daina mai rashin kunyar ba. Bayan long draman da aka sha tsakanin Dr, nurses da Amal aka samu akayi retreating ciwon aka sa mata sabon bandage suka kuma jashi sosai kaman yadda Afzal ya buk'ata. Fuskan nan duk jirwayen majina da hawaye gabad'aya ta fita daga hayyacinta.

  Dariya sosai Sultan ya saki lokacinda shi da Afzal suka shiga d'akin suka tarar da ita zaune bakin gado tana aikin share hawaye. Shima Afzal d'in dariyar ce ta k'eto mar amman kaman yadda ya saba bonewa hakan yayi.

   "Lets go" yace da ita, da mamaki yaga ta mik'e ba gardama ba suratai. Lallai plan nasa yayi working.

   "Triple A yaci ace an saya mata koda ice cream ne ta d'anji sanyi a ranta da wannan muguntar da kasa nurses sukayi mata" cewar Sultan lokacin da suka wuce ta downtown. D'ago ido Afzal yayi yana hangenta ta mirror yadda tayi tsit a motan kaman ba ita aciki.

   "A saya miki kinaso?" Ya tambayeta da gan-gan yana wani murmusawa ta gefe. Idanunta takai inda nasa suke sannan ta kad'a kai a hankali "Karku damu nagode" ta fad'a a nitse ba Afzal kad'ai ba har Sultan yasha mamaki. Wani murmushin ya kuma sakewa sannan ya miyar da kallonsa kan hanyan. U turn yayi suka koma baya inda ya tsaya ya sai mata ice cream d'in.

   Bayan ya kaita gida ya mik'a mata, jira yake ta amsa ta bud'e ta kwa6ar a k'asa tunda de wanka ta biya kud'in sabulu gashi ya kawota gida se kuwa yaga tana kad'a kai "Nagode ni zan wuce gida" ta sanar dashi kanta a sunkuye.

    "Haba 'yan mata, yi hak'uri ki kar6a kinji?" Cewan Sultan cike da dabara. Ba ta kuma yin musu ba tasa hannu ta amsa tare da masu godiya sannan ta bud'e k'ofar.

  "Sekuma gobe ko?" Cewar Afzal da gan-gan domin jin me zatace.

  "Eh Allah kaimu" ta amsa calmly. Killer smile nasa ya saki ashede plan d'in yayi working, frankly ko shi be d'au ze iya yin abinda yasa akayi mata ba, but he had to it is the only way da zesa ta dena masa rashin kunya.

   Tun daga ranan Afzal ya cigaba da d'awainiyar Amal kamar yadda yayi alk'awari. Mostly daga office bayan yaci lunch seya biyo ya d'auketa, wani sa'in sukan taho tare da Sultan mostly kuma shi kad'ai yake zuwa. Amal kuwa tun rana me kaman na ranan bata sake yiwa Afzal rashin kunya ba, cike da girmamawa da ladabi take gaishe sa duk sanda yazo, bata kuma fasa kiransa da Ya Afzal d'in ba, har abin ya zame mata jiki. Shima Afzal kullum daga clinic se sun tsaya a downtown sun sai mata ice cream. Ranan daya kaita dressing na k'arshe bayan ya kawota gida Amal tayita insisting cewa ya shigo ciki suyi final sallama da Mami tunda basu samu daman yin hakan ba d'azu kasancewar Mami bata gida daya taho. Sam baida niyyan shiga ciki again sede kuma yaga Amal nada point idan ba wani ikon Allahn ba kam ai ba abinda ze sake kawosa gidansu, yaci ace sunyi ban kwana da Mami.

  "Kaji Ya Afzal kashigo ku gaisa da Mami please" ta kuma cewa ganin be ko motsa acikin motar ba. "Pleaseeee Ya Afzal." Juyowa yayi yana k'are mata kallo seji yake a jikinsa Amal is upto no good, dama chan bawai ya yarda da wannan d'abi'un da take portraying bane ace for the past 6 days ko rashin kunya bata mishi sema ladabi da biyayya.

  "Amal?" Ya kira sunanta yana k'are mata kallo.

  "Na'am" ta amsa tare da sunkuyar da kanta tana wasa da ledan ice cream daya siya mata.

  "Wani abin kike shirin yi ko? Kinsan I don't trust you not even a single bit."

  "Haba Yaya har mey yayi zafi haka? Mey zanyi maka? Allah ba komai kawai inason kuyi bankwana ne da Mami kaga ai idan ba wani ikon Allahn ba bazaku k'ara had'uwa ba."

  Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauk'e "Let's go" nan ya kashe motan suka fice. Bayan sun k'arisa ciki Amal ta shimfid'a mai taburma tare da yima Mami da Papi sallama, bayan sun fito ta nuna musu ice cream da Afzal ya sai mata. Godiya sosai sukayi mishi sannan suka gaisa, da wayo ta saci jiki ta fice ba tare da sunyi realizing ba.

Pins da k'usosin da ta tanada ta ciro sannan ta k'arisa gun motan nasa, tayan baya ta sace dana gaba sannan ta gwada bud'e motar haushi taji datayi confirming a kulle ne if not da tayi niyyan kwa6ar mar da ice cream d'in acikin motar ne next time se taga idan ze sake sa mugayen likitocin asibiti su ja mata k'afa kai bama ita kad'ai ba koda wata ta daban. Seda ta ga tayoyin sun soma tsotsewa sannan ta kama hanyan gidansu Azee inda suka hau shan ice cream suna hira. Afzal kuwa bayan sun gama gaisawa dasu Mami sun d'an ta6a hira kad'an yace ze tafi, har wajen gida suka rakasa sannan suka koma ciki. Yana wasa da makullin motansa yana tafiya har ya isa inda yayi parking motan nashi, sam hankalinsa be kai ga patched tires guda biyun ba seda ya shiga yasa key ya shiga neman yin reverse yaji mota yak'i baya balle yayi gaba. Tirk'ashi, accelerator yata dannawa amman ina mota yak'i motsawa hakan yasa ya fito don duban inda matsalar take to his ultimate surprise yaga tire biyu duk a pache. Da farko yayi tunanin ko 'ya'yan unguwa ne suka mai d'anyen aikin nan amman tuna yadda Amal ta dage sam seya shiga sun gaisa da Mami yasa ya soma zarginta.

   Tabbas yarinyan nan bata da kunya, upon duk d'awainiyyan dayayi ta mata da abinda zata saqa masa kenan? Lallai kuwa she's messing with fire. Ji yake kaman ya shiga gidansu ya nunawa Mami da Papinta abinda 'yarsu tayi mar amman tuna ba lallai ne su hukunta ta kaman yadda yakeso ba yasa ya fasa, yafison ya hukuntata da kansa, hukuncin da ko akan layi ta gansa seta canza hanya. Murmusawa yayi ya ciro wayansa daga aljihu tare da kiran mechanic nasa. Within 20 minutes ya iso sede ba pachi kad'ai Amal tayi ba, tiren gaban entirely yasamu matsala wanda idan ba ikon Allah ba se an canza shi gabad'aya. Anan de mechanic yamasa concluding cewa mota bazata gyaru a yau ba. Wayan Sultan ya kira don yazo ya d'aukeshi sede switched off yakeji. Be damu ba yashiga neman driver'n Daddy nan ma network yak'i barinsa. Abu fa kaman wasa se trying yake amman network yak'i bari call ya shiga chan kawai service ya d'auke gabad'aya. Babban magana! Ji Afzal yake kaman ya k'urma ihu bayan nan yaje ya nemo duk inda Amal take a fad'in unguwansun nan ya nad'a mata na jaki.

  Abu kaman wasa network yak'i dawowa gashi se ci yamma keyi, bayan d'an gyaran da mechanic yayi yakuma cire important parts na motan gudun kar 6arayi suyi gaba dasu dake motan ma se an barta ta kwana anan ya buk'aci Afzal daya bisa cikin keke napep daya taho sesu sauk'eshi a
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment