Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskar maman
deeny sannan tace halima aka gani a motar
shi sannan gawar halima budurwar aka samu a cikin motarsa nan ta
kara fashewa da kuka. maman aliyu ce ke rarashin
ta tace kiyi hakuri yanzu tashi mu tafi gidan br
fadila din dakyar aka samu tayi shiru ita dai abun
ya mata yawa ba maryam ba zaharadeen din ta
tasa mayafi suka fita suka tsaida nafen sai gidan
br fadila. sunyi sa'a tana gida kuwa da yake ba
wani aiki suna isa ta tare su hannun bibiyu tasa mai
aiki ta kawo musu abinci da ruwa da lemo haka
kuwa aka kawo musu abinci aka girke a gaban su
ga lemoka kala kala. su duk hankalin su ba'a akan
abince yake ba su brfadila suke su ta fito su mata
bayani kawai. can after 5mnt sai gata ta fito daga
daki fuskar ta cike da murmushi tace a su maman
deeny manya ba'a ko ganin ku yanzu yaushe rabo
mu hadu. maman deeny kuwa murmushi ta nema
ta rasa duk batada sukuni. tace ai kune manya
bakwa ko neman mu. kallo daya brfadila tawa
maman deeny ta fahimci ba lafiya ba. taga duk ta
wani canza. tace maman deeny lafiya kuwa. haba
sai hawaye kamar jira suke dama nan ta kwashe
labarin duka ta fada wa barrist fadila sannan tace
yanzu haka sunce gobe gobe za'a shiga kotu
saboda baban halima ya kai kara. brfadila wani a
jiyar zuciya ta saki sannan tace tabdi babbar
magana. tace yanzu bari in shirya inje mu gana da
deeny inji kan lamarin ankama deeny ai bamuga ta
zama ba. maman deeny ta dan share hawaye
sannan ta kalla brfadila tace yanzu saiki fada mana
abunda zamu kawo dan allah ki ceci yaran nan
nasan bazai iya kisan kai ba kuma shike daukar
dawai niyar mu yanzu in bashi ya zamu yi gashi
maryam din ma bamu san inda tayi ba. cikin sauri
fadila ta dago kai ta dafe kirji tace maryam ta bata.
maman aliyu ce ta bata amsa tace kwarai kuwa tun
jiya data fita islamiya bata dawo ba har yanzu.
maman deeny kuka take sosai. fadila ta kalle su
cike da tausayawa ta taso daga kujerar ta ta dawo
kusa da maman deeny ta rike hannun maman
deeny sannan tace. ki kwantar da hankalin ki
isha'alahu zamuyi nasara kuma kibar maganar kudi
deeny ai dana ne sannan ta kara dacewa in allah
yayarda deeny zai fito ki bar komai a hannun na
yanzu zanje na sama deeny. maman deeny da
maman aliyu godiya suke kamar me sun rasa kalan
godiyar da zasu mata ma. tace ba komai muje
driver ya kai ku idan ya dawo sannan na shirya sai
mu wuce da shi station wajan deeny…………
08096831009




→BANI NA KASHE TABA← PART8
na bigboy isah
salama tayi ya amsa kanshi a kasa yanata faman
zubarda hawaye duk wanda yaga deeny a wannan
halin dole ya tausaya masa sbd tsananin duka da
yasha. takare mai kallo sannan ta sama waje ta
zauna tace sannu deeny da kyar ya dago kai ya
kalle ta yace yauwa sannu sannan tace sunana br
fadila nice lauyan ka mai kare ka ina san sannan
wasu bayanai game da abunda ake zargin ka da shi
da fatan ka shirya?. shidai kawai ido ya zura mata
sannan ya daga kai alamun eh. nan sukayi yan
maganganun su tana tambayar sa yana bata amsa.
daga karshe tace zamuyi nasara isha allahu kafin
nan ina so in sanar da kai cewa karka yi magana
biyu a kotu dan hakan zai iya jawo mana matsala
yace toh sukayi sallama ta tashi ta fice.
***** alhj sunusi kuwa wani kwararan lauya ya
nema ana ce dashi barristr bashir ya biya shi kudi
har 500,000naira da yake shi ya kasan ce mai kudi
ne kudin sa kuwa sanadin wani yayan shi ya,same
su wani compny da yayan ya bar mishi sunan
yayan nashi alhaji bashir matar shi daya saratu. da
daya allah ya basu sunan yaran nasu yazeed yaran
nasu yana jida kudin uban sa shi kuma uban ya
sakar mai duk dukiyar sa a cewar shi shi zai gaje
shi ay hajj saratu taita fada idan taga yanda alhj ke
sakar wa dan nashi kudi.
*******
wata babbar kotu nagani a cike makil da yan kallo
da wanda aka bukaci ganin su. kotu tayi shiru.
alkali kawai ake jira ba'a jima ba saiga shi ya shigo
ai kuwa duk jama'a gaba daya aka mike alkali ya
nufi set din sa ya zauna .an fito da zaharadeen
cikin ankwa duk wanda ya kalle sa saiya tausaya
mai alkali yace assalamu alaikum warahmatul lahi
wabarakatuho.
duk jama'a suka amsa sannan alkali yaci "court
clerk call the
case" Court yafara bayaninsa "In the case of
murder between zaharadeen kabir and alhj sunusi.
yaci gaba da bayanin sa muna bukatar lauyoyi su
gabatar muna da kansu. ya koma ya zauna. my
name is barrister bashir lauyan mai kara shima ya
koma ya,zauna.fadilat ta mike my name is barrister
fadila mai kare wanda ake tuguma. sai duk kotu
tayi tsit har yan wajan ma kowa yayi shiru. babu
wanda bai hallara a wajan ba.maman deeny.amina
maman aliyu.alhj sunusi da matar sa. da wanda
yaga gawar da duk sauran jama'a dai duk sun
halara har da baban yazeed da maman sa duk…………08096831009








→BANI NA KASHE TABA←PART 9
na bigboy isah
br bashir ya nema alfarma ga kotu domin ya fara
tambayoyin sa. kotu tamai izini. sannan yaje gaban
deeny. yace zanso sanin cikeken sunan ka. ya
dago kai yace. sunana zaharadeen kabir. br bashir
yace. miye hadinka da halima. deeny yace budurwa
tace. duk jama'a suka dago kai suka kurawa deeny
ido.kai ka kashe halima?.deeny yace BANI NA
KASHE TABA. br yace an tabbatar da anga gawar
halima a motar ka muna da sheda ba daya ba ma.
yace haka ne. br yayi ajiyar zuciya. sannan yace to
waya kashe ta?. deeny yace nima ban sani
ba.bashir yace zaka iya fada mana dalilin ka na
cewa bakai ka kashe taba kuma bayan antabatar
kai kazo har gida ka dauke ta?. deeny ya fara bada
labari. ranar washe garin ranar da dare mu kayi
waya da halima take cemin dan allah gobe inzo mu
tafi yawan shakatawa ita kafin hutun su ya kare
tana so ta dan ga gari. da har naki amincewa nace
ni ba inda zani yawan shakatawa ay na masu
kudine muda muke nema ina mukaga samun damar
zuwa wani shakatawa. ai kuwa nan ta fashe da
kukan shagwaba wai ita wllh sai yazo ya dauke
ta.dai dai nan hjj hauwa ta shigo dakin halima ta
isketa da dan kukan ta hada hawaye. da sauri ta
karasa tace halima lafiya kuwa.tace momy lafiya
lau ba komai. hjj hauwa tace ban yarda ba sai kin
fada min. alokaci shi deeny kuwa yana saurarn su.
sai halima tayi sauri ta katse call din ta kamo wani
video fassara tace momy fin ne nake kallo shine
abun ya bani tausayi nake hawaye. momy dariya
tayi tare da cewa allah ya shirye ki. sannan ta
kama hanya ta fita. tana fita daga dakin. halima ta
sake kiran deeny duka daya ya daga wayar kamar
dama jira yake. yana dagawa yace kin gama
kukan. tace pls dan allah kayi hakuri kazo mu fita
gobe. yace kwantar da hankalin ki gimbiyata zanzo
isha'alahu ai kuwa dan murna hada tsale sannan
tace gobe karfe 10 ka shirya ko anguwar mu
sannan baban na ya fita nasan yada zanwa momy
ta barni in fita kaji yace to.allah ya kaimu haka taita
jin dadi. har allah allah take gari ya waye. ai kuwa
gari na waye wa ta yi sallah ta fito farllo sukayi
breek sannan momy ta dakowa dady jakar sa zai
fita dan har ya makara yanzu karfe 9:30 suka raka
shi har mota halima ce rike da jakar sai da ya shiga
mota sannan ta durkusa ta mika mai ya amsa yace
baby allah ya miki albarka tace amin sannan ya
juya yawa maman baby bye bye driver yaja shi
suka fice yana su kuma suka koma farllo suna
kallo ita kuma halima duk tabi ta damu ta rasa
wace karya zatayi ga waya a hannun ta sai
jujuyawa take. hjj hauwa ta fahimce ta tace ke me
yake damunki ne naga duk kin changer fuska.
halima tace momy mun dan sama sabani ne da
deeny wai shine yace inje yana kofa zai
bani.hakuri. momy tayi murmushi tace kude yaran
nan bakwa gajiya da rikici ko shiyasa naga jiya kina
hawaye. ta sadda kanta kasa. momy tace hmm
shiyasa naga bai shigo ba kenan yasan yau ba a
shirye kuke ba ay saiki tashi ki fita. halima
a,zuciyar ta cike da farin ciki a fuska ko kamar
bata so. ta tashi ta shiga dakin ta tayi yar kulleyar
ta sannan ta chanza kaya. wata atamfa ta saka mai
kyau green & water riga da siket sun mata cip cip
sun kara fito da kyan ta ta dau gyalan ta fari ta yafa
sannan taje jikin mirror ta kalla kanta tayi
murmushi sannan ta fice a dakin …………
mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy
on-line 17.04 12:52






→BANI NA KASHE TA BA← PART 10
na bigboy isah
ta fito tace momy na tafi momy tace to a dawo
lafiya kuma kice ina gaida shi tunda shi yau bazai
shigo ya gaida mu ba. tace ameen momy zai ji.
ta fita da murnan ta ta nufi inda yake a mota ta bude
motar ta shiga sannan tayi ajiyar zuciya tace to sai
motafi ko ina zamu fara zuwa. wani kalan kallo ya
mata mai cike da so da kauna. yace saida kika
wahalar dani na zo sai jira nake kinki fitowa. ta
mararai raice tace haba sweethr kasan irin faman
da nasha kafin in samu a barni na fito kuwa sai da
nayi karya fa. gaba daya suka kwashe da dariya.
sannan yaja motar yayi gaba suna tafiya suna ta
zuba hirar su ta soyayya tana tamai shagwaba kala
kala tace wannan yatsaya ya saya tace wancan
haka dai suke ta tafiya suna soyayyar su abun
gwanin ban sha'awa. sune har wajan la'asar yace
tabari tunda ga masalaci a kusa kuma ankira sallah
to tabari yayi sallah tunda kinga ko sallahr azahar
banyi ba. tace to nifa nima ay banyi ba. yace ai ku
mata ne kun saba dama idan ana biki sallar huni
guda duk kuke hadawa lol. ta jefo mai bisket din
hannun sa ya kare da hannun sa kuma ya fita da
gudu yana dariya itama dariyar take. ita kadai a
mota shi kuma ya nufi masalaci ya dauki buta ya
zuba ruwa ya nufi ban daki.
kotu dai tayi tsit deeny kadai ake ji sai zuba labari
yake nima ina gefe ina sauraran sa.
yace bayan na gama sallah ne na nufi mota ina
zuwa na iske halima a kwance ni a tunani na barci
take haka nayi murmushi nace yarinya ai gobe
bazaki kara cewa a taho yawan shakatawa ba
gakinan duk kin gaji har kinyi barcin dole. ni kuwa
nace deeny ka kashe yarinya kace barci take ko
lol. yaci gaba da jan motar shi bai tsaya ko inaba
sai gidan su halima yana zuwa ya tsaya a kofa
yakama dan babuga ta yana cewa my luv tashi
mun iso my heart ki tashi ko duk gajiyar ce haka.
yayi yayi yaga ko motsi taki yi. nan fa duk ya rikice
ya shiga gida ya kira mai gadi wai yazo ya tada mai
ita ta shiga gida. ni duk a sannan ban fahimci
halima mutuwa tayi ba inji deeny. mai gadi yazo
yace ban gane in taya ka tadata ba mai ya faru.
deeny yace nidai nayi nayi taki tashi kuma daga yin
barci. mai gadi ya matsa kusa da ita ya kama
hannun ta ya daga ya sake shi yaji hannun ya dawo
kamar dai yadda gawa take. shima duk bai gamsu
ba tukun ya bude idan halima yaga fari fat ai kuwa
dama tsoho ne da gudu ya ban kade deeny ya nufi
cikin gida.deeny har zai bishi sai yaji mai gadi na
cewa hajiya ya kashe miki yarinya…………
mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy
on-line 18.04 18:45
→BANI NA KASHE TABA← PART 11
na bigboy isah
deeny da gudu yayi baya duk jikin sa na rawa ya
fizgi mota yayi ciki gudu yake ba kaf kaftawa yace
ban tsaya ba nabi wani barji a tunani na duk wajan
daji ne ba mutane. yace haka na je na tsaya da
mota na juya ina ta kallan halima ina kuka a zuciya
ina cewa wai yanzu halima ta ta mutu kenan. nan
hawaye suka fara zarya a fuskata na fito na dauki
halima. wai ni a nufina binne ta zanyi idan na koma
gida koma me za'ayi sai ayi. ina tafiya inata sake
sake na dan yi nisa da mota ta nan na ajiye halima
inata kuka ina jijigata ina cewa ki tashi ki tashi.
shiru nine har magariba ina wajan nan fa na gaji sai
kawai na fara haka rami da yake wajan ba tauri nayi
rami mai dan tsawo nan kuma sai na tsaya ina
tunani toh in binne ta anan ko kuma in maida ta gida
a mata sallah a sa mata lukafani. inata saka
wancan kunce wancan. sai ji nayi ance waye nan
ban ankara ba sai ganin kibiya nayi a gaba na ta
caki kasa ina juyawa naga wani saurayi ne ya
durfafo ni hannun shi rike da kwari da gwafa. ashe
wai nan garkar rogwan sune wai yana ce ni
barawan rogo ne lol. da gudu na bar waje nayi
wajan motata sai na danyi gudu kadan sai na tsaya
a zuciyata nace gwara in tsaya in cemai yar uwata
ce ta mutu shine zan binne ta. wata zuciyar kuma
tace wannan da yake fada a kan rogo baya ko
tsayawa a mai bayani toh ina zai tsaya sauraro
na.yana cikin hakan sai ganin mutum yayi a guje ya
nufo shi yana barwo aradu barawo ne. ni kuma sai
nake cewa ka tsaya ka saurare ni. haba ba sai ji
nayi ya sako wata ki biyar ba badan na guce ba da
sai ta same ni. da gudu na fada mota naja ta da
gudu ya biyo ni. yana har bi yana jifa har dai na
samu na tsere. can naje bakin titi na ajiye motar
sannan na taho a kasa sai dai ina fargaba amma a
haka nace kai gwara inje duk abunda zai same ni
ya same ni amma sai na dako halimata na nufi
garkar na dan bi a hankali na leka nayi zatan yana
nan. amma sai naga wayam tun a nesa naji gabani
yana faduwa da na hangi wajan da na ajiye halimata
ba komai a hajan tun a nesa na dora hannuwa a kai
ina isa wajan kuma na iske ba komai a wajan sai
dai ga dan ramin da nayi nan. haka nata ratsa daji
ina neman saurayin nan ko sama ko kasa na
nemeshi na rasa. bana jin kukan komai a wajan sai
kukan tsintsaye da na dabobi da yake dare ne
rananr dai haka nata yawo ina kuka kamar
mahaukaci ina tunanin shikenan na rabu da
masoyiyata abar kaunata hasken zuciyata bugwan
zuciyata. na fashe da kuka a ranar duk wani tsoro
ya fita a raina bana jin ko tsoran duhun dajin nan
haka na hakura na koma naja mota na inata tunane
tunane. na nufi gida…………
mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group
.




bigboy
on-line 19.04 09:54
→BANI NA KASHE TABA←PART 12
na bigboy isah
TUN DAGA BAKIN KOFA naji gabana yana faduwa
duk tsoran maman mu nake. sai kuma nayi tunanin
ay bata san komai ba. kawai na shiga gida na nufi
daki na na kwanta. banyi barci ba har safe da
asuba nayi sallah a daki dumin bazan iya fita ba duk
na gaji saboda yawan da nasha jiya a daji ina gama
sallah na nufi dakin momy ai kuwa ina isa kamar
ance mata gani nan sai saukar mari naji tass tace
ina kakai musu yarinya nasan bazaka iya kisa ba
amma ina kakai.musu yarinya.nace mama wllh
BANI NA KASHE TABA momy ta zaroo ido dagaske
ta mutu. ai kuwa ta shake min wuya tana cewa. me
yasa kakashe ta me tama kane da zaka kashe
musu ita banyi zatan zaka iya kisan kaiba
zaharaddin sannan ta sake ni daga shake min
wuya da tayi idanuna duk sun cika da kwala. momy
ta koma gefe tana kuka. a hankali na durkusa nace
momy wllh BANI NA KASHE TABA ana nan yan
anguwa suka zo zasu toya mu sannan police suka
kore su aka kamoni akayo nan dani. ya mai girma
mai shari'a wllh gaskiyar abun da na sani
kenan.mustapah ne yace yallabai wannan ba abun
kamawa bane idan kayi la'akari da maganganun sa
akwai karya a ciki sannan yace na gode ya mai
shari'a. sannan alkali bayan yagama yan rubuce
rubucen shi yayi aziyar zuciya sannan yace
barrister fadila fa tana da tambaya. tamike tace
akwai ya mai shara'a. tace ina rokon kotu data bani
izini in kira hjjy karima maman deeny.alkali yace an
baki izini. ana bukatar ganin hjj karima maman
deeny. ta taso taje ta tsaya a inda aka tana.br
fadila tace da farko muna bukatar jin sunan ki dana
mijin ki.ta goge dan hawayan dake fuskar ta domin
ta tausayawa yaran nata. tace sunana karima mata
ga alh kabir . fadila tace wannan fa danki ne
kokuwa dan riko ne. maman deeny tace dana na
cikina. fadila tace maganar da ya fadi duk gaskiya
ne haka sun faru. maman deeny tace duk abun da
ya fada dangane da ni haka ne. tun safe ko karin
kirki baiyi ba yace min zashi gidan su halima da
yake ni nasan tsakanin su shiyasa ban tugume shi
mai zaiyi a can din ba. haka naita jiran shi amma
shiru bai dawo ba kanwar shi ma kuma haka da ta
dawo daga school ta takura min da tambaya ina
yaya deeny sai dai nace ya tafi gidan su halima. da
yake itama halimar kawar ta ce.har tayi shiri
makarantar islamiya amma deeny bai dawo ba
abun ya daure mana kai gaba daya. yaran da yake
cin abincin rana a sai gashi har 3:30 bai dawo ba.to
bayan fitar maryam ne ba'a jima ba sai ga mai
gadin gidan su halima da yan sanda wai sun zo
kama deeny anan ne suke shaida min wai ya kashe
halima. na dafe kirji sakamakon hani mumanan
faduwar gaba da naji. sannan na fada musu rabona
da shi. amma basu hakura ba suna ce boye shi
nayi duk saida suka har gitsa gida suka shiga ko
ina amma basu samai ba. suna gidan tun lokacin
har bayan isha'i amma bai dawo ba. ni kuwa abun
duniya ya isheni dan a lokacin har jini na ya hau.
saboda yada abun suka min biyu ga deeny ana
zargin shi da kisan kai sannan ga maryam bata
dawo ba. hakan yasa na shiga daki na kwanta
zazabi ya rufe ni ban tashi ba sai da safe………………08096831009












→BANI NA KASHE TABA← PART 13
na bigboy isah
barrister fadila. tace mun gode. zaki iya komawa
mazaunin ki. sannan br fadila tasa akata kira
mutane daya bayan daya. daga kan maman halima
har mai gadi duk wanda labarin deeny ya shafa. sai
yace eh maganar da ya fada gaskiya ce. barrister
fadila. tace ina rokon wannan kotun mai adalci data
rike labarin wannan bawan allah karta dauke su a
karya. bayan ga shaidu mun samu kuma duk sun
tabbatar da zancen sa haka ne. sannan ina rokon
kotu da ta tura jami'a tsaro dumin su tafi da deeny
ya kaisu har wannan wajan da yayi rami dan
tabbatar da gaskyar sa. na gode ya mai shari'a.
deeny kuwa duk ya tsure dumin a lokacin bai san
ma inda ya tunkara ba balle ya kai wanda za'a hada
shi da su yanzu. turkash. alkali yace munji kuma
mun yarda da zan can ki barrister fadila gobe za'a
hada shi da jami'an tsaro dumin su je su bincika
dan tabatar da gaskiyar sa sannan mun dage
wannan zama har zuwa jibi. alkali ya buga
gudumarsa…………kotu ta watse >>>>> cigaban labrin deeny>
lokacin da dan fulani ya dawo wajan sai ya tarar da
mutum a kwance kuma ga duk kan alamu wancan
da ya kora binne wannan din yazo yi. adan tsorace
ya nufi wajan a hankali ya juyo ta sai yaga ashe
macece ma daya kula sosai sai yaga da sauran rai
da sauri ya sabe ta ya nufi gida da zuwa kuwa
gwaggo ta tarye shi suka kamata suka ajiye a kan
wani gadan kara ita kuwa har yanzu bata dawo
hayyacin ta ba. nan gwaggo take tambayar isah ina
ka samu wannan yarinyar gata kamar yar bunni.
tana dan jujuyata.isah yakwashe duk labarin
abunda ya faru ya fadawa gwaggo gwaggo tace to
hike nan allah hukumusa'a. ya tashi yace gwaggo a
kula da shi ni na komai dawa. da yabi kwari da
gwafan shi yayi ciki.
da sasafe halima a hankali ta bude ido ta ganta
cikin bukka tayi mamaki sosai. a hankali ta taso
jikin ta ba kwari. tana tagal tagal. gwaggo ta taho da
gudu ta tare ta daga faduwar da zatayi. ita kuma
halima deeny take ta kira tana ina deeny na. deeny
nan inane. duk ta wani rikice. gwaggo tace kiyi
hakuri mana ki saurare ni nan ba garin ku bane.
nan kina cikin rugga ne. halima ta zaro ido rugga
kuma. gwaggo tace tabbas kuwa. jika na ne ya
tsunto ki jiya a can garkar su wani na kokarin binne
ki. halima tayi ajiyar zuciya tace yanzu ko wane
hali mamana da abbana suke cikin. hawaye kawai
suka shararo mata. gwaggo tace jikin ki ba kware
muje ki zauna. ai kuwa haka gwaggo ta taimaka
mata a hankali taje ta zauna…………>
mu hadu a https://m.facebook.com/groups/1232550283531628.


whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy
on-line 21.04 11:05
→BANI NA KASHE TABA← PART 14
N@ BIGBOY isah
acan kuwa bangaran maryam tashe sukayi suka
nufi gidan su anne. suna shiga suka iske iyayan
anne a tsakar gida suna hutawa suna yar hirar su.
suka karasa maryam ta gaishe su suka amsa cikin
fara'ar su sannan maman anne tace aneesat
wannan fa daga ina haka kamar yar bunni. anne
tace yar bunni ce mana yan fashi ne suka sato
ta,zasu kashe ta shine ta tsero har allah ya kawo ta
nan kuma a dandali muka hadu tataima ka mana ta
nuna mana maciji zai sare mu. shine har nake
tambayar ta gidan suea tazo sai ta bani lbr shine
nace bari muzo nan gidan ta kwana kafin akaita
garin su.abban anne yayi murmushi yace allah ya
miki albarka kinga dadin zaman birni kenan yaci
gaba da cewa ni naso in sama kudi ma a wannan
shekarar mu koma birnin nan mu duka har gwaggo
da yayan ki ya kalle anne. maman anne tace wllh
malam ba inda zaka halan kaje ka likewa wata kace
auranta zakayi ko wllh baza mu ba toh. su anne
gaba daya suka kwashe da dariya har maryam
dariyar take. ai kuwa sai gani nayi. maman anne ta
tashi ta shiga bukar su. nan anne da maryam da
baban maryam sukaita hirar su. maryam kuwa ta
saki jiki.baban anne yace aneesat tashi ku tafi daki
kusha fura sai ku kwana daki daya keda bakuwar
taki ko. anne tace to abba. suka shiga dakin daga
wani gadan kara bazai ci mutum uku ba na mutum
biyu ne ko katifa babu sai tabarmar da aka shin fida
da kuma barguna. da yake anne mai tsafta ce dakin
yar bukkar tata tsaf tsaf da ita. gefe kuma ga yar a
kwatin ta. hada nunawa maryam wai yayan tane ya
sayo mata. kuma duk ruggar nan babu mai kalan
ta. maryam kuwa me zatayi banda dariya. taga an
dakko wata tsohuwar akwati wai nan abu mai
daraja ne a garin. nan dai suka gama shirman su
suka gaji da hira suka kwanta. ai kuwa ranar da
dare maryam tasha jifga.daga anjima sai dai taji an
laf to mata kafa ta janye ana jimawa ta kara jin an
wullo mata. maryam tace na shiga uku wannan
kamar mage dai wannan ai mijin ki ya shiga uku. a
haka dai har asuba tayi. maryam ta tashi ta fito ta
dauki buta dama annee ta nuna mata bandaki. ta
fito tayi alwala. sannan taje tayi sallah tayi
adda'au. nan fa ta fara tunanin maman ta da kuma
yaya deenyta. tana cikin wannan tunanin taji matsin
anne ta farka ta murge ido taga maryam a kan
sallaya. tana kallan ta. tace ke kuma haka ake a
garin ku kita shi kiki tada mutane ko. maryam tace
ke tada ki ai sai jirgi ko kuma azo da bulala. anne
tace to miyasa baki dakko bulalar ba. maryam tace
ba komai ai akwai gobe. da sauri anne tace toh
gobe me zakiyi?. tace ahah bulala zan samo mana
saboda tada ki ba kince mi isa ban samo bulala ba.
anne tace wasa nake miki kinji yar kawata. ai
wannan lalausan jikin nawa bazai dauki bulala ba.
gaba daya suka kwashe da dariya. maryam tace.
katashi ka nema ruwa ka yi alwala kazo kayi
sallah. anne tace kai abun hada tsokala ai dai
allahn da yasa ni maganar fulanin ma bata kama
baki na ba.kinsan mu a burni muka girma. maryam
tace wai ina wannan yayan naki yake ne. sai kira
kike yayan ki yayan ki. anne tace yayana yana
gidan gwaggo gwaggo ta kwace mana shi ay. tace
bari dai in tashi wannan hirar ba karewa zata yi ba.
ta tashi taje tayi alwala. ta dawo ta iske maryam
tayi tagumi sai tunani take. anne tace maryam
maryam.firgigit ta dawo hayaccin ta daga tunanin
da take. anne tace kinga indai gida ne ki kwantar da
hankalin ki. yanzu da muka gaisa da mamana tace
gobe zata bawa yaya isah kudin mashin ya maida
ki garin ku. cikin fara'a da murna tace wow na gode
na gode. sosai.sis.anne tace bari inyi sallah ki
rakani zan kaiwa su gwaggo abin kari. maryam
tace toh shikenan………<
mu hadu a https://m.facebook.com/groups/1232550283531628 whatsapp→ 08096831009 Group
bigboy
on-line 21.04 11:08
→BANI NA KASHE TABA← PART 15
N@ BIGBOY isah
>tunda sasafe police uku tare da deeny suka hau
mota suka nufi daji shidai deeny ba zai gane
wannan garkar ba wacce yaje yayi rami haka sukai
ta shara gudu deeny na nuna hanya duk da ba gane
wajan yayi ba saboda da dadare ne shi sadda yazo
ana tafiya da ya hangi wasu garake can nesa yace
toh a tsaya aka tsaya aka firfito daga motar.
yansanda suka sa deeny a tsakiya har suka kunce
mai unkwar dake hannun sa wai a cewar su ya
za'a yi wannan dan yaran ya iya tserewa daga
hannun mu mu uku. ni kuwa dake gefe ido kawai
na zuba inga mai zai faru. haka sukai ta tafiya suje
wannan

Please Login or Register in order to submit comment