Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dukkaninsu dawood najin wani sanyi da kasala na shigarsa sbd yasan babban burin rayuwarsa ne zai cika idan NUR dinsa tazamo matarsa,
godiya sukai masa sosai kafin suka miqe,

basu koma gidaba saida sukai sallar isha suna komawa suka shige daki duk da zuciyarsa a tsananin takure takedason ganinta amma hakanan ya daure sbd yasan idan ya matse mata zatacene bazatai aurenba gwara yabata space har yasamu adaura auren,
yanaji inna halima nayiwa baffa complain taqi fitowa har lokacin kuka takeyi yayi zuru tareda mayarda dukkanin hankalinsa kan qofar dakin datake,
sufyaan dake qoqarin sanardashi maganarsu saraah ganin hankalinsa baya jikinsa yasa yabari harsai bayan auren idan hankalinsu yadan kwanta.


da tsakar dare kasa kwanciya yayi sbd yana jiyo ajiyar zuciyarta alamun idanunta biyu sam bayada sukuni na jiki dana zuciya sbd rashin sanin halinda take ciki.

har asuba yana zaune ko gyangyadawa baiyiba sbd ita.,

suna fita sallar asuba itama tafito daqyar sbd ko gani batayi sosai sbd kumburin idanuwanta na kuka,

alwala tayi takoma ta tayarda sallah a zaunema tayi sallar sbd wani irin mugun jiri da zazza6i mai zafi dayake cinta,

tana gamawa ta dunqule gurin tana kakkarwa tareda wani irin wahalallen nishi.

hankalin inna halima ne yafara tashi ganin halinda take nan tazauna jiran dawowarsu baffa basu dawoba saida gari yayi haske sosai.


maganin zazza6i baffa yabayawa innar abata shima bayason matse mata dankarma ta tayarda maganar rashin son auren,

dawood ma ganin zai iya rasa nutsuwarsa yasa sufyaan jansa suka fita bayan gidan,

zama sukayi bakin wani dutsi ya rufe idanuwansa ahankali tareda jinginarda kansa jikin ice zuciyarsa na qara rasa sukunin halinda nur din ke ciki,
tabbas NUR itace rayuwarsa,farin cikinsa,baqin cikinsa,qaddararsa dakuma burinsa aduniya.

dafasa sufyaan yayi ahankali tareda tausasa murya yace,

idan andaura auren ya kake tunanin zamu fuskanci su mum?

bude idanuwansa yayi dasukai jajir ya qurawa qasa ido kafin ya dago cikin takaici yace,

idan na aureta she's mine,
my responsibility,
my future,
rayuwar danayi abaya cikin mummunan yanayi yasa na qara daukan wani life lesson so na shirya gyara rayuwana ta hanyar shimfida sabuwar rayuwa dan haka ba ruwana dasu mum or wata aleeya can,am gonna take her somewhere,where we can start a very happy married life sai bayan wani lokaci zamu dawo idan sunga dama su kar6emu idan sunga dama su gujemu.

jinjina kai sufyaan yayi tareda cewa,

ina bayanka lets start a new life afterall jass yakusa cika shakarunsa biyu yafito....

yes saura sati biyu yacikasu inaga wannan wata damace da allah yasake bamu mu shimfida kyakkyawar rayuwa mai tsafta.

murmushi suka saki dukkaninsu sai alokacin yaji dan sauqin abunda yakeji.

suna gurin baffa yazo wucewa gona sufyaan ya miqe yabisa dawood kuwa gida yakoma yashige daki ya kwanta yana kallon sama tareda lumshe idanu yana tunanin abubuwa da dama.


sufyaan kuwa saida sukayi nisa sosai yakalli baffa yace,

baffa inason shiga inda zansamu harkar banki maana wayayyen guri haka.

tsayawa yayi tareda juyowa gefen sufyaan din yace,

mezakayi dabazaka bari sai bayan daura aurenba?

gyara tsayuwarsa yayi yace,

inason nine zanbiya kudin sadakin abokina sbd wannan shine burin maska harya rasu shine yayi alqawarin biyawa dawood sadakin aurensa matuqar da NUR ne ayanxu dabaya raye inason dauke wannan nauyin.

murmushi baffa yayi yace,

to ai dan wannan ba matsala bane ni zan biya....

aa baffa kaine kazamo kamar kawu ga nur kuma kaine zaka bada aurenta baikamata ace sadakinta yafito daga garekaba nine nayi niyya kuma nine zanbiya insha allah.

to tunda kanaso hamisu rakasa kuje gonar mal jamilu kugani idan motar akori kurarsa bata wuce gariba saiku bisa yawuce daku idan zai dawo yadawo daku.

juyawa sukayi suka wuce shima ya qarasa gonarsu dake kusada rafi.


cikin saa suna zuwa suka tararda yadauki kayan miya zai wuce suka fada yawuce dasu atakure bama kamar sufyaan dabai ta6a shiga irin wannan motarba da duk qarfece ba guri mai laushi ko kadan ko gurin zaman duk ya cinye sosai yakecin duwawu amma haka yadaure sukaita gurxawa.


tafiya mai nisa sosai sukayi kamar bazata qareba daqyar suka iso wani dan gari ba laifi yanada cika sosai dakuma abubuwan zamani kamarsu bankuna biyu da yar babbar kasuwa da babbar tashar motoci harda babbar asibitinsu gasu da wuta koina.

bai tsaya bata lokaciba yashiga banki bayan dogon turanci daqyar ya iya cire kudi masu yawa ta slip yafito suka shiga kasuwar daqyar ya iya shigarta aka kaisa wani babban shagon saida kaya daqyar yasamu shaddodin dubu ashirin ashirin yasiya guda biyu agurin aka dinka musu shida dawood ba aiki ba komai kawai babbar riga hudu yace ayi musu ta ishesu tunda ana daurawa zasu wuce.

gasassun kaji dakaton na drinks yasiya da takalmi sai dogayen riguna guda biyu daya siyowa nur.
daganan lafiyayyar matarda bataji jikiba golf yayi musu shata tamayardasu da sharadin acan mai motar zai kwana washe gari bayan daurin aure zai fito dasu qauyen abuja zai kaisu.


sai bayan magriba suka iso nan ya miqawa inna halima kayan nur dakuma kajin sai baffa babbar riga daya hamisu daya shima daya sai ango daya.

dawood baiyi wani mamakiba sbd shidai amatse yake da gobe tayi adaura auren su wuce.

lokacinda inna halima takai mata kayan kar6a kawai tayi ta ajiye sbd tuni kuka ya qaurace mata tayi zuru zuru ko iya bude ido sosai batayi.

daren yau dinma daga ita harshi babu wanda yayi bacci uwa uba abinda yake tsananin cinsa shine yinin ranar gaba 'daya basu ga junaba ba qaramar azabtuwa da dauriya yayiba.


ana kiran asuba yasaki wata irin ajiyar zuciya shiya riga kowa fitowa yayi alwala kafin suka fito sukai alwalar suka nufi masallaci baki daya.

kamar koyaushe saida gari yayi haske suka dawo suna shigowa gidan cikin sa'a idanuwansa suka sauka akanta lokacinda take qoqarin aje butar data fito bayi.

sunkuyar dakai tayi daqyar dasashiyar muryarta dake rawa ta fito asanyaye ta gaida baffa dake gaba.

amsawa yayi cikeda farin ciki kafin yq wuce sufyaan dake bayansa fuska asake yace,

gud morning.

'daga masa kai kawai tayi tareda juyawa da sauri zata bar gurin yakasa haquri ya riqo hannunta ta tsaya cak numfashinta na futa da sauri sauri.

matsowa taji yanayi ta janye hannnunta da sauri tareda shigewa daki ta dafe qirjinta sbd bugawar dayake.

kallo yabi qofar dakin da shanyayun idanuwansa dasuka galabaita dasonta kafin ya wuce dakin dasuke shima.

sauran kajin jiya sufyaan yaci shukuwa bakinsa wata irin bushewa yayi yawunsa suka qafe babu abinda ke gabansa dayafi yaga andaura auren,
baida wata nutsuwa ko sukuni ayanzu saiyaga nur tazama tasa.

wanka yayi yamayarda kayansa da aka wanke jikinsa wani irin sanyi yayi sosai daqyar sufyaan ya taimaka masa yasaka babbar rigarsa sbd bai iya sakata ba.

koda baffa yafito yace su fito nan jikinta ya tsananta rawa tanason yin kukan amma takasa haka ta rarrafo ta fito ta tsaya gaban baffa ta sunkuyar dakai sbd idanuwanta dasukai jajir zatayi magana dawood dake gefen baffa yadawo gabanta tareda kafeta da lazy eyes dinsa murya amatuqar sanyaye yace,

zakice bakyson adaura miki aure danine sbd kema kinga na zama abun qyama ko?

'dagowa tayi ahankali takallesa sai takasa magana sufyaan na ganin haka yayi saurin cewa,

baffa muje su malam nacan najira .

wucewa sukayi kowanne na gyara babbar rigarsa shikuwa saidaya qara kallon fuskarta dake sunkuye kafin ya wuce.

suna futa ta shige daki tareda qanqame jikinta dake wata irin rawa wace irin masiface zata sameta yau ta auren mijin aleeyarta.


sukam suna isa dama tuni sukawai jamaa ke jira sbd anyi sanarwa daurin auren bayan sallar asuba nan aka fara sufyaan yafito da sadaki naira dubu hamsin nan take aka gabatarda daurin auren aka shafa fatiha.
#mamuhgee


vote and follow.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*33*
NOT EDITED.



wasu irin hawayene suka ciko idanuwansa dasuka qanqance sbd yunwa da wahala dakuma fargaba,
kallon mutanen dake miqa masa hannu yake kamar wani wawa sbd tsanananin mamaki da farin cikin daya kasa gasgatawa yau NUR tazama tasa da sauri ya miqe yayiwa allah sujjada yatashi tareda rungume sufyaan daketa faman washe baki farin cikinsa baya misaltuwa.

saida aka gama komai mutane suka watse suka sakeyiwa mal liman da baffa godiya sosai nan sufyaan yayiwa mal liman babbar kyautar kudi sosai sukai masa bankwana suka wuce sbd so suke su isa abuja da wuri,

gida suka nufa ahanya ya zare babbar rigar tareda zuba hannunsa a aljihu murmushi yake saki yana tafiya kwata kwata hankalinsa baya taredasu sufyaan da baffa shi wata duniyar tunanin dayake dabam,

sufyaan na lure dashi yasaki murmushin farin ciki yana girgiza kai tareda cigaba dayiwa baffa bayanin wucewa zasuyi yanxu.

kudinda yatanadar masa tun jiya ya ciro yabasa cikin girmamawa yace,

insha allah dakomai ya gama daidaituwa zasu sake dawowa sukawo gaisuwa.

godiya kawai baffan yayi tareda cewa,

bakomai allah dai yakawo fahimta acikin alamarin cikin sauqi.

amin''''sufyaan yace yana kallon gefen dawood da wani irin annuri ke fita fuskarsa baimasan mesuke cewaba.

suna isa gida cikin tsananin farin ciki inna halima tayi musu allah sanya alkhairi sufyaan ne kawai ya amsa dawood hankalinsa nakan qofar dakin datake yasan kuka takeyi kobaa fadaba.

ko dakuna basu shigaba sukace wucewa zasuyi,

inna halima tashiga dakin datake takalleta taga har lokacin ko wanka batayiba tana zaune yanda take tundazu harlokacin jikinta bai daina rawaba.

dafata inna tayi tareda yimata yar qaramar nasiha ta dagota daqyar suka fito tana fitowa idanuwanta suka sauka cikin nasa ta sunkuyar dakanta tareda dagawa baffa dake mata magana kai.

'yar nasiha baffan yayi mata tareda bawa dawood amanarta suka fito,

motarda sufyaan ya dauko musu tun jiya shata har qofar gidan ta qaraso suka shiga suka wuce hawayenta na saukowa ahankali na fargabar abunda zasuje sutarar.

sufyaan ne agaba itada dawood din abaya tunda tashiga ta juyar dakai gefe tareda rufe idanuwanta ahankali sbd ko jinsa zaune gefenta tsananta bugun zuciyarta yake bare ta iya kallon gefensa.

qura mata idanuwansa dasukayi laushi yayi cikeda wani irin farin ciki shikadai yasan irin rayuwar dayake musu tunanin shimfidawa kafin sudawo sbd bazai ta6a gangancin bari suje gida yanxuba a 6angale masa auren dako kwana daya baiyiba aduniya dan yasan sarai hakan zata iya faruwa takowane 6angare na mum dinsa kona su aleeya.



doguwar tafiya sukayi babu wanda yayi magana acikinsu basu iso abuja ba sai yamma sosai nan sufyaan yayiwa drivern magana kai tsaye ya nufi gidan maska dasu.


lokacinda suka isa gidan sosai taji habkalinta yatashi ta kalli dawood din da sauri ganin yaciro mukullin gidan inda suke aje spares cikin wata flower dake qofar shiga,

daure fuska yayi nantake yakoma dawood dinsa sbd karma tasamu fuskar jeho masa wani zancen,


ganin yanayin fuskarsa yasa ta sunkuyar dakai tareda rufe ido hawayen ciki suka sauko ta share ahankali,

suna shiga sufyaan yayi saurin shigewa bedroom daya yabarsu apalon.

kallonta yayi yaga yanda ta tsaya batada alamar motsawa ya matso ahankali yakamo hannunta yakaita har tsakiyar 'dayan bedroom din ya juyo yafito yakoma wanda sufyaan yake sbd duka gidan is two bedrooms flat ne,

tu6ewa yayi ya kwaso kayan daya cire yaje yazuba dusbin yadawo yashiga wanka,

kwanciya yayi cikin ruwan dumin tareda lumshe idanuwansa yasaki ajiyar zuciya ahankali wani irin kwanciyar hankali na shigarsa,

ya jima acikin toilet din yana dumama jikinsa tareda yin wankan daya jima baiyi irinsaba kafin ya fito daureda towel iya qugunsa.

yana fitowa ya tsaya gaban mirror tareda shiryawa cikin three quater black da black shirt mai hula yayi sallah yana idarwa ya kalli sufyaan daya fito wanka yace zashi gida yadawo.

dayake basu sallami drivern ba sai gobe tukuna saiya shiga motar suka fuce,

nesa da gidansu yasa drivern ya tsaya yajawo hular rigarsa yarufe rabin fuskarsa ya isa qofar gidan ahankali cikin saa babu kowa sai maigadi,

maigadi na ganinsa ya miqe da sauri cikin sauri ya girgiza masa alamar karyayi magana ya matso kusadashi sosai yace,

akwai mutane sosai aciki gidan?

bakowa yallabai alhaji yayi tafiya hajiyama bata dade da fitaba zuwa asibiti can gurin haj aleeya daaka kwantar kwana biyu yanxu sbd rasuwar mai dakin taheer.

wat yace da dan qarfi kafin yayi saurin yin qasa da murya yace,

kana haukane zakace nur ta mutu,,,get lost and karka fadawa kowa nazo komai rintsi.

cikin sauri yashiga gidan direct part din mum yafara zuwa yashiga dakinta yafara duddubawa baiga komai na nur ba yafito yashiga dayan dakin cikin sa'a yaci karo da handbag akan gadon dakin da sauri ya bude yana dubawa cikin saa yaga passport dinta bai tsaya cire komaiba yadauki jakar tareda akwatinta dayagani aje tun dawowarsu bata budesaba yasan ba shakka tatace,

maigadi yabawa yakai masa mota da sauri shikuma ya nufi part dinsa ya dauki passport dinsa dana sufyaan tareda wasu kayansa da laptop da duk wasu mahimman takardunsa da komai nasa mai mahimmanci ya fito.

saidaya qara gargadar maigadi tareda basa wasu kudi masu dan kauri daya tsinto a dakinsa suna barin gurin mum da Nana nadawowa daga asibiti sbd har lokacin anrasa gane kan aleeya ciwo take sosai anyi qarin ruwa da maganguna har anfara gajiya babu wani saiqi sbd ba qaramin bugun zuciyarta da qwaqwalwarta batun rasuwar layla yayiba ga 6angare guda annemi gawarta acikin motar baaganiba.

yana isa gidan yazauna palo tareda kallon sufyaan dake zaune palon yana waya da lndline ta gidan,

waya yake da wanda zaiyi musu komai so suke kamai rintsi gobe su wuce.
yana gamawa order daya bayar daga pizza kitchen ta iso ya bude qofa ya karbo tareda ajiye nasu ya miqawa dawood na layla.

kar6a yayi tareda jan akwatinta ya nufi dakin,

knocking yayi ahankali ya tsaya jiran ta bude.

tsawon mintuna bata budeba yasake knocking tareda tura qofar ahankali yashiga tareda turo qofar,

zaune take qasa kan daddumar sallah ta kwantarda kanta bakin gado idanuwanta alumshe.

qura mata ido yayi tsawon mintuna kafin ya qaraso ahankali tareda aje mata abincin gabanta cikin wata irin sanyin murya yace,

kici abinci ga kuma kayanki nan na dauko miki.

bude jajayen idanuwanta tayi takallesa tanason yin magana takasa sai kawai ta miqe ta zauna bakin gadon batareda tasake dagowa ta kallesaba,

kasa hkr yayi ya zauna bakin gadon kusada ita sosai tayi saurin miqewa zuciyarta na bugawa da sauri ya riqo hannunta tareda dawo daita ta fado masa ya zaunar da ita kan qafafunsa ya riqeta gam,

kasa motsi tayi sai kawai hawaye suka 6alle mata tafara fitarda kuka mai qaramin sauti sbd ba qaramin riqoyayi mataba,

jin kukan nata na shigarsa sosai yasa ya sassauta mata riqon tareda dago fuskarta yana kallon hawayenta murya a tausashe yace,

please NUR kukan ya isa haka,
tun shekaran jiya kike kuka har yanxu zaki jawa kanki ciwon kai nayi miki alqawarin komai zaizo da sauqi insha allah so please nur kina axabtardani da wannan kukan.

tsananta kukan tayi harda shesheka ya shigarda ita ahankali cikin jikinsa ya rungumeta tareda sakin wata kasalalliyar ajiyar zuciya,

saidatayi kukan har baya fita sai ajiyar zuciya kawai takeyi yana shafa bayanta ahankali alamar rarrashi hartayi shiru kafin ya miqar da ita yaja hannunta har toilet ya hada mata ruwan wanka masu 'dumi ya bude sabon brush yasaka mata toothpst yasaka mata cikin hannu kafin yafito yaja mata qofa,

ahankali ta daga kai takalli fuskarta ta mirror taga yanda kamanninta suka canza sbd kuka kafin tafara brush din ahankali tana qoqarin daidaita kanta da bawa kanta nitsuwa da qarfin hali kafin ta fuskanci aleeya sbd tasan tariga tazamo butulu agun aleeyarta.

wanka tayi sosai kafin ta dauro towel ta fito cikin saa baya dakin yafice.

ko mai bata shafaba ta bude akwatinta ta dauko doguwar riga mara hannu kawai tasaka takoma ta zauna tareda 'daukar ruwa kawai tasha sbd batajin zata iyacin komai.

anayin sallar isha ta miqe tayi ta koma gado ta kwanta tareda rufe idanuwanta ahankali tana tunanin hindasu aleeya suke ciki ayanxu dan tasan sunacan suna nemanta.

cikin daren komai na tafiyarsu ya kammalu suka harhada komai nasu gari na wayewa sukaje gidan mamyn maska sukai mata bankwana tareda yimata bayanin komai tareda aje mata kudade masu yawa
dazasu tafi tareda ita suka dawo sbd tace tanason ganin nur,

lokacinda tashiga dakinta da sallama azaune tasameta bakin gado tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar riga black.

tanaganin mamyn ta sunkuyar dakai tareda zamewa qasa ta gaidata cikin sanyin murya.

amsawa tayi tareda sakar mata murmushi tana kallon dawood daya zubawa laylar ido.

fita sukayi ta gyara zama sosai tafara yiwa laylar nasihar yarda da qaddara ta rungumi mijinta sbd aure dai anriga andaura gwara su tsaya su fuskanci yanda zasu gyara gaba da abunda zai biyo baya,

sanyi jikinta yaqara yi duk dadai babu mai karkare butulcin datayiwa aleeya.

lokacinda mamyn zata tafi tabata kyautar yankunnayen zinari da turaren datazo mata dashi
kar6a tayi tareda godiya hawaye na zubo mata,

bayan tafiyar mamy lokacin tafiyarsu yayi yashigo dakin ya tsaya daga bakin qofa tareda zuba hannayensa duka biyun cikin aljihun wandonsa yace tafito,

tasowa tayi ahankali tazo gabansa ta tsaya tareda kallonsa ta dauke kai cikin dasashiyar murya tace,

muje gida dan allah karmu tafi koina.....

girgiza mata kai yayi kafin yace,

zamu tafine yanxu sbd kar masu nemanki su kamaki yanxu zuwa gaba idan angano gskiya zamu dawo so please karkice bazakiba i promise to bring you back idan lokacin hakan yayi.

shiya jawo akwatinta tariqo handbag dinta suka fito kamar yanda suka zo daga qauyensu baffa haka suka nufi airport sune abaya sufyaan agaba har suka isa ba 6ata lokaci jirginsu ya daga.

tunda suka shiga jirgi yana riqe riqedq hannunta akai akai yakan juyo ya kalleta har wani irin wahalallen barci data manta rabonta dashi ya dauketa a kafadarsa.


sai dare sosai suka isa direct gidansu suka nufa nan kowa yayi hanyar dakinsa.
kasa zama tayi ganin daki daya zata zauna dashi ganin yanda takasa sukuni yasa ya riqo hannunta ya zaunar da ita bakin gado tareda sakar mata wani qayataccen murmushi yana kallon face dinta yace,

sweethrt relax ok,,,ba anan zamuyita zamaba zamu dan kwana biyune anan kafin jass yafito zamu tattara mukoma wani gurin ne acan zamu fara sabuwar rayuwa.

zame hannunta tayi tareda jinjina masa kai ya miqe yashige toilet.

wanka yayo wanda yasaka masa wata irin nutsuwa yafito daureda towel iya qugu ta dauke kai tareda miqewa ta shige toilet dindaya fito.
#mamuhgee

vote and comments pls.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*34*
NOT EDITED


Tsayawa tayi cikin toilet din tana qoqarin saita numfashinta kafin tayi wanka tareda dauro alwala ta fito,

akan daddumar sallah tagansa atsanake ta shirya cikin doguwar riga fara mara nauyi ta zura hijab tazo gefensa ta tayarda sallah.

tana gamawa yasata miqewa sukai nafilar godewa allah daya cika musu burinsu.

sosai yayiwa allah godiya tareda yiwa maska,taheer da jass addua sosai kafin ya miqe yafice dakin.

a palo ya tararda sufyaan tayi musu order abinci yashiga kicin ya dauko qaramin tray da spoons bayan ya dauraye ya jera mata tafeda ruwa da drink mai sanyi ya koma dakin.

zaune take har lokacin kan sallayar saidai idanuwanta dake lumshe.

ajiye tray din yayi tareda zama kusada ita yana sakin wani sahirtaccen murmushi,

bude mata abincin yayi chips ne da kidney souce sai chicken shawarma.

kallon abincin tayi ta kallesa tareda girgiza masa kai ahankali.

shima girgiza mata kai yayi yana smiling harsaida dimple dinsa ya lotsa ya matsoda ita jikinsa sosai ya debo da fork yakai bakinta tareda kafeta da idonsa.

budewa tayi dole ta kar6a yasakar mata qayataccen smile tareda matsoda bakinsa kunnenta cikin rada yace,

thaz my beautiful bride.

wani kallo ta watsa masa ya daga mata gira daya yace,

yes baby...

rasa abinyi tayi sai kawai tayi kamar bata jisaba yaci gaba da bata abincin tanaci,

sosai tayi mamakin yanda taci abinci sbd rabon dataci wani abincin kirki harta manta sai yau ga wani irin bacci datakeji.

ahankali tace,

ya isa haka na koshi.

daukar glass cup din ruwa yayi yabata tasha tana kallon fuskarsa dake fidda wani irin annuri na farin cikinda zuciyarsa ke ciki.

chips din kawai yaci shima kadan sai cocumber mix dayasha ya kwashe kayan yayi waje dasu.

koda yadawo tana zaune still yashiga toilet yayo brush da sauran aladunsa daya saba kafin ya kwanta yafito ya sanya dogon wando fari qal mai laushi da rigarsa mai budadden gaba ya juyo ya kalleta yaga yanda ta juyar dakai daga gefensa,

murmushi yasaki yana mamakin abubuwan datake masa yanxu wanda da ba haka take masaba akwai sakewa sosai tsakaninsu ada amma ko yanxu zaiyi qoqarin dawo da hakan,

matsowa yayi ba zato taji ya miqar da ita tayi saurin kallonsa ya hura mata iska cikin idon yana cewa,

kina buqatar hutu my love dan haka zamu kwanta da wuri.

cire mata hijabin jikinta yayi yajata zuwa toilet tayo brush kafin ta fito ya ciro mata rigar bacci mai dan kauri da laushi ya miqa mata.

toilet takoma ta sanyo tana fitowa yajata gaban mirror ya fesa mata turare tareda tattara mata dogon gashinta ya daure mata yajata bakin gado ta zauna ya dauki qafafuwanta ya dora akai tareda kwantar mata dakanta kan pillow ahankali yana kallon fuskarta datayi fayau.

saidaya fita yaje gurin sufyaan sun dan jima suna magana kafin yadawo lokacin hartayi bacci cikin yar kwanciyar hankali dan tadauka acan zai kwana kamar abuja.


kashe wuta yayi tareda qarasowa ya kwanta gefenta tareda ja musu bargo ya juyo gefen fuskarta ya qurawa face dinta ido cikin farin ciki mara misali harsaida wasu irin hawayen farin ciki suka ciko idanuwansa baisan wani irin so zuciyarsa keyiwa nur ba.
hannunta ya lalabo ya danqe cikin nasa ahaka bacci ya daukesa cikin nutsuwa,


itace tafara tashi da safe ahankali ta bude itanuwanta sai akan fuskarsa dake daf da tata suna fuskantar juna,

lumshe idanuwa tayi tareda sake budesu ta sake dora masa,
tsimin sonsa taji yana taso mata idanuwanta suka ciko da ruwa tabbas tasan har abada bazata raba zuciyarta da sonsaba,
sonsa acikin jininta yake bazata iya rayuwa lafiyayya babushiba itakadai tasan axabar datasha wancan karon data rasashi...

ajiyar zuciya ta sake ahankali ta zare hannunta daga nasa ta sauko ta shiga toilet,
alwala da brush tayo tana fitowa tagansa zaune yana jiran fitowarta,

alwala yayo shima yazo yayi sallah suna gamawa ta miqe zata zauna bakin gado tajisa bayanta
ta tsaya cak batareda tajuyoba,

zare mata hijabin yayi ahankali tareda rungumota ta baya ya xuro kansa ta wuyanta ahankali yabata wani lafiyayyan kiss a gefen fuska murya qasa qasa yace,

gud morning my angel.

kasa magana tayi sai juyowa tayi ta kallesa tareda daga masa kai,

murmushi yasaki tareda janta suka koma gado ya kwanta tareda dora kansa aqafafuwanta yana kallon fuskarta hannunta ya riqo yana cewa,

youre my happines love bazakiyimin magana ko so daya bane?

shiru sukayi dukkansu ahaka bacci yasake daukarsu,

basu tashiba sai ten yana tashi wanka yayi ya fice sbd sam ya manta zasu fita yau tunda safe da sufyaan.

saidayayi mata ordern breakfast ya aje mata adakin kafin yayi kissing lips dinta ahankali yafice.

yana futa ta bude idanuwanta zuciyarta wata irin nutsuwa take samu alhalin ita tana qoqarin hana hakan sbd ganin butulci ne da cin amanar aleeyarta.


wanka tayi ta sanya straight skirt black da dark blue shaking material riga mai dogon hannu,

zama tayi ahankali taci abincin kadan tareda miqewa ta fitar dashi takai dining anan taga kicin sai kawai ta shige tasaka sauran fridge saitaga fridge din akashe yayi qura komaima gashinan atsare saidai qura koina na kicin da palon.

zuwa tayi tasawa qofar shigowa lock tadawo tagyara kicin din tsaf ta goge komai ta wanke na wankewa tadawo palo nanma saidata goge komai ta kakkabe ta share tayi mopping ta kunna ac ac da tareda room spray data gani jere cikin wata qaramar showcase dake dining area yawancima duk sunyi expire sbd dadewa amma it make sense duk da hakanan,
lock din qofar ta cire sbd karsu dawo su bude yaqi
bedroom dinsu takoma ta gyare tsaf tareda wanke toilet tana gamawa dole ta sake wani wankan tana fitowa ba zato tagansa zaune kan couch yana saka laptop dinsa charge.

jawota yayi ya zaunar kan qafafunsa yana kallon face dinta har zuwa koina jikinta dake jiqe da ruwan wanka.

shafo fuskarta yayi tareda sakar mata murmushi yace,

go and get ready sweethrt we are goin out.

tashi tayi shima ya shige toilet wanka,

doguwar riga ash tasaka mai buudewa sai gyalan rigar data yafa ta fesa turaran da mamy tabata tasaka loafers tana zaune kanta aqasa ya shirya cikin wasu designers qananan kaya na armani,

hannunta ya riqo suka fito apalo suka tararda sufyaan zaune yana aiki sosai a laptop sbd so suke sugama hada komai nasu intime su bar qasar.

murya ba qwari ta gaisa da sufyaan kafin suka fice.

bude mata gaban lambogini dinsa yayi tashiga ya zagaya yashiga yatayar suka fice,

shopping din kayan sawa sukayi dana sauran abubuwan buqata kafin suka tsaya wani restaurant sukai lunch duk da takasa sakewa sosai har lokacin,

sai yamma suka dawo gida suna dawowa lokacin sufyaan yafita nan sukai wanka ya zaunar da ita tareda sata magana dole tun tana kauce masa dole tafara masa magana.


da daddare su uku sukai dinner a dining sbd dawood da sufyaan dakansu suka shiga kicin sukai mata girki na musamman,

duk yanda taso daurewa saidatayi murmushi ganin yanda sukai jiga jiga gurin aikin.

ba laifi abincin yayi maana taci kuma ta yabawa sufyaan dawood saidai tabisa da wani irin kallon daya kashe jikinsa ya riqo hannunta yayi kissing

1 Comments On DAWOOD
avatar
aisha-9-4-5

2 months ago

Reply

I love this book

Please Login or Register in order to submit comment