Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaqara tashi gashi batason rarrashinsa Dan karya canxa mata ra'ayi Kuma tasan dazarar yatafi bazai sake dawowa kusaba qilama sai matarsa dayakeso sunyi aure.

Dafe goshi tayi cikin tsananin damuwa da neman mafita.
Wani tunani ne yafado Mata ta 'dauki wayarta ta danna Kiran maska.

Cikeda kulawa ya 'dauka asake yace,

Hello mum.

Cikin sauri sauri da tashin hankali tafara yimasa bayanin abinda ke faruwa ta 'dora da cewa,

Son please do something, call him tell him koma meyene I don't want him to go please my boy kayi wani.

Numfashi yasauke sbd jikinsa dayayi sanyi Jin wannan rikicin dakuma tsananin tausayin halinda dawood zai shiga idan mum tacigaba da dagewa akan rabasa da Nur..
Gyara murya yayi yace,

Mum meyasa kikeson Dole saiya rabu da Nur? they're so much in love with each other mum.

Son please just call him now zamuyi sauran maganar but for now kasan yanda zakayi ka hanasa tafiya.

Ok...yace tareda kashe wayar Yana kallonsu jass dake sauraronsu.

Wayar dawood yakira Amma Bai 'dagaba harsaida yayi Masa kusan Kira uku.

Yana 'dauka yanayin muryarsa yasa jikinsa sanyi a tausashe yace,

Dawood mum called.

Numfashi Mai zafi ya sauke murya a shaqe yace,

I love her maska but I can't do this,
Zanyi komai Dan ita Amma wannan karon ta 'dauko babban al'amari sbd I can't live without Nur.

Bazamu so ka rabu da farin cikinba ba but karkayiwa komai garaje kabi mum din ahankali I'm sure zata barka da farin cikinka tana sonka sosai bazata juri damuwarkaba so karkayi fushi.,

Qaramin tsaki yaja cikin 'dan zafi yace,

Zantafi idan ta sauka zan dawo sbd ba yanda za'ayi naje gidan datake son naje.

Kar6an waya sufyaan yayi yace,

You'll have to go dawood sbd idan wancan 'din na sonka zatace ta hakura ka samu wadda kakeso kawai kaje kafada Mata gskia you don't want to get married to her kanada wadda kakeso I think this will work.

Shiru dawood yayi ransa na qara quna sbd har cikin jininsa yakejin tsananin qiyayyar yarinyar ko ganinta bazaiso yayiba ace kamarsa harsaiya tsaya yiwa wata bitch bayani kafin yasamu wadda yakeso Amma it's like he has no other option,
Akan Nur zai iya zuwa ko inane yayiwa duk mutanen duniya bayani.

Zubewa yayi bakin gado tareda dafe kansa dake Sara Masa sosai ga wani zafi da zuciyarsa keyi Amma bayason ya qara 6ata lokaci ayau zasu wuce gidansu yarinyar.


Su maska kuwa suna gama waya dashi dukkaninsu sukai tsit suna juya tsananin damuwar da abokinsu yake ciki ayanxu Dan kuwa sune shaidai tsananin son dayakewa Nur din,
Tun tasowarsu Basu ta6a ganinsa yaso Abu da tsanani hakaba kamar yanda yakewa Nur.

Ajiyar zuciya jass ya sauke cikin kulawa yace,

This is not good.

maska dake juya zancen aransa yace,

Dole zamuje da wuri yana buqatar wani akusadashi Dole.

Waya sufyaan ya 'daga yafara Kira ayi musu booking tickets na zuwa Nigeria.






Wanka yasakeyi ya shirya cikin qananun Kaya dark blue da facing cap tareda shades black yafito su mum kuwa tuni suka shirya sai washe Baki takeyi tana Nan Nan dashi suka fito gabaki 'daya suka nufi airport.

Lokacinda aka bugo aka sanarda zuwansu tuni su ammy suka hau shirye shiryen tarbon baqi gashi itama Nur dawood yakira yasanar da ita yau zaizo da dad 'dinsa zuwa dare ko gobe da safe idan sun baro gidan abokin dad dinsa.

Musamman mum tasake bugowa tafadawa aleeya suna hanya ba 6ata lokaci cikin farin ciki aleeya ta damu Layla Dole suka fita sukaje wani queens beauty pal&spa.

Gyara na musamman akayo Mata har wani irin qyalli take tayi tayi Layla tayi tace aa sbd dawood bayason hayaniyar kwalliya yafisonta a natural 'dinta.

Koda suka dawo gida qarfe biyu ta 'dan wuce Dan haka sallah kawai sukayi ta canxa kayanta zuwa doguwar Rigar wata Julius Holland dark brown ta 'daure gashinta ta 'daura qaramin vail akanta tareda zura bedroom slippers ta Taya aleeya shiryawa sai farin ciki suke suna fira Nan Bilal ya shigo aleeya ta kallesa da sauri tace,

Little qani sun iso?
Kaga brother inlaw 'dinka?
He's very handsome right?


Dariya ya bushe da ita kafin ya matso ya zauna kusada ita Yana kallon yanda tayi kyau kamar wata model yace,

Daina rawar jiki sunfasa sai gobe Kuma....

Zaro Ido tayi zatai magana layla tayi saurin Kai Masa duka a kafada tana cewa,

Mode spoiler.

Ajiyar zuciya tasake da qarfi tareda miqewa tabi bayansa da gudu tana cewa,

saidakasa zuciyana tsinkewa Allah saina ragewa coconut head 'din Nan naka girma.

Dakin ammy yayi Yana dariya tabisa Nan ammy taraba rigimar Layla tace,

Allah ammy ya rainamu yaron Nan jifa yanda yatashi saka kwalliyar damuka tsara"""tafada tana gyarawa aleeya gyaran gashinta da sul6insa yasa yafara zarewa daga ribbon.


Sallamar siyama ce tasa dukkaninsu juyawa cikeda mamaki sbd ba Wanda yasakaran ganinta.

Fuska 'daukeda murmushi da farin cikin da baikai zuciba ta qaraso tareda rungume aleeya tana cewa,

Wow cousin you're looking fabulous.

Murmushin yaqe tasaki tace,

Thank you siyama saukar bazata.

Eh wlh naso baku surprise ne,
Ammy ina wuni ya nasameku?

Lpia klau siyama,
Yasu anty Nana da babanki.

Duk suna gaisheku.
Kallon Layla tayi fuska asake tace,

Layla ya gida.

Lafiya qlau""tace tareda miqewa ta fice tana cewa,

Bari naje naqara duba cake 'din da Nana keyi koyayi.

Tana fita aleeya da siyama suka biyo bayanta suna 'dan fira.

Suna bedroom 'dinsu sukaji isowar baqin kusan atare zuciyoyinsu suka buga lokacinda Bilal yashigo yafada musu baqin na Palon Abba.

Fira sukeyi Amma kowa kusan Rabin hankalinsa baya gurin.

Acan palon kuwa taheer ne yashigo taredasu dad dawood kuwa harabar gidan ya tsaya Kiran numbern Layla Amma yakasa samu jiyake kamar zai zauce idan baiji muryarta alokacinba.

Ammy ta gaisa dasu sosai cikin girmama takalli taheer dake gaidata ta amsa a mutumce sbd tunanin shine dawood din kafin sukai palonta da mum.

Nur ce agaba sai aleeya da siyama abayanta suka shigo palon ammy.

Zuciyar mum cikeda farin ciki ta amsa gaisuwarsu tana qara godewa Allah dazai cika Mata burinta.

Nur dake gefen ammy ta kafawa Ido ganin wani irin hutu da kwarjini dake fita a jikinta Nan take taji tana yiwa kanta sha'awar ace sirikarta ce,
Tabbas tafi dacewa da dawood 'dinta saidai lokaci ya qure saidai taheer 'dinta.

Ficewa sukai daga 'dakin ammy tace,

Layla kije ki qarasa da dawood din guests palour zaifi sakewa sbd su abban Naga hirar business suke tukuna.

Ok ammy.

Aleeya da siyama bedroom suka koma ita Kuma ta nufi palon Abba Kai tsaye.

Da sallama ta shiga..

A cikin idanuwan taheer idanunta suka Fara sauka tayi saurin sunkuyar dakai numfashinta na fita da sauri.

Gaidasu abban tayi tasanarda abinda yakawota Nan taheer daya Dade da mutuwar zaune miqewa sbd baita6a tunanin Laylar ta zarce yanda take a hoto sosai.

Fitowa sukayi palon yace Mata dawood na harabar gidan.

Shigar dashi palon tayi suna qara gaisawa ta juya tana cewa,

Bari naje na shigo dashi.

Tundaga nesa ta hangosa ya bada baya Yana waya saidai kallo 'daya tayiwa bayansa ta tsaya hakanan taji numfashinta na fita da sauri ta tsaya cak kamar wadda aka tsayar.

Wayarta yaqara Kira cikin sa'a tayi ringing.

Saurin kallon wayar hannunta tayi shikuwa Jin qaran waya bayansa yasashi juyowa.

Wani irin jirine ya 'dibeta tayi saurin juyawa ta shige Palo batareda tabari yaqarasa juyowaba.

Rawa jikinta yakeyi sosai daqyar ta lalubi kujera ta zauna tana qoqarin Jan numfashinta ya tsaya.

Sake shigowa Kiran yayi tana gani ya katse zuwa lokacin ko wayar ta kasa riqewa rawa jikinta keyi sosai arikice ta miqe tayi dakin Nana sbd can ne kawai tasan ba Wanda zai ganta cikin wannan yanayin.
#mamuhgee








VOTE
COMMENT.
[1/8, 8:37 PM] 0mmr Farouk: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*19*
Kasa zama tayi kodata shiga 'dakin ta tsaya tsakiyar 'dakin tana qoqarin samarwa kanta nutsuwar fahimtar abinda ke tabbatuwa arayuwarsu,

Wasu irin hawayene suka gangaro Mata tana qoqarin danne kukan dakeson biyo bayansu.

Dawood 'dinta shine dawood 'din da aleeyarta keso meyasa takasa fahimta tuntuni daya sanarda ita garinda iyayensa suke.?

Meyasa dawood yaqi fada Mata cewar,

Iyayensa sun nemar Masa Mata...?

Wannen wane irin alamarine ya kusantosu.
Rufe Ido tayi tana tsananin Jin zafi azuciyarta,
Rawa qafafuwanta suka Fara yimata ta sulale tsakiyar 'dakin hawayenta na tsananta gudu sabuwar doyayyar dawood takeji har cikin jininta,
Soyayyar dawood tariga tazamo wani 6ari na jikinta wani irin zafi da nauyi takeji ayanxu data gansa amatsayin na aleeyarts to Yaya aleeya zataji idan taji shine dawood 'dinta.

Girgixa Kai tayi hawayenta na qara gudu cikin rawar murya ahankali tace,

Wlh zafi nakeji sosai cikin zuciyana aleeya bazanso kiji wannan zafinba  Bazaki iya juresaba.

Ahankali tafara kuka Mai qaramin sauti har lokacin jikinta Bai daina rawaba.

Tunowa da ammy yasa ta tsayarda kukanta tareda tattaro qarfin Hali tasawa zuciyarta ta share fuskarta tareda miqewa da sauri ta fice tana roqon Allah yasa ammy da dawood basuga junaba.

'dakin ammy ta nufa tana qara qoqarin danne halinda take ciki.

Ammy ce kawai a 'dakin itama wayarta tazo 'dauka takoma palon gurinsu Abba.

Ahankali ta qaraso gaban ammy ta riqo hannunta tareda dawowa bakin gado suka zauna.

Sunkuyar dakai tayi hawayen datake qoqarin dannewa sunason fitowa Amma ta 'daure ta mayar dasu Amma idanuwanta sun jajir.

Sanyi jikin ammy yayi ta qura Mata idanuwa ta lurada yanda jikinta ke 'dan rawa ta riqo hannunta da sauri cikin tsananin fargaba tace,

Layla?

'dagowa tayi takalli ammyn Nan take ammy ta qara shiga ru'dani ganin Jan idanuwanta tace,

Layla meke faruwa?

Ammy tunda na taso cikin quncin rayuwa da talauci na taso,
Babu Wanda ya ta6a yimin kallon mutum bare ya bani mutuntawa da darajar da Allah yabawa mutum,
Ni Almajirace 'yar bola Mara asali da gata,
Ammy duk duniya bayan iyayena dasuka haifeni Babu Wanda nake tsananin so da qaunar farin cikinta irin aleeya sbd itace takalleni amatsayin mutum ta miqamin hannu ta cironi daga qanqantacciyar rayuwar titi da bolan danakeyi Wanda da yanxu na zama wata abar qyamar.,

Ammy har abada ina roqon Allah daya nesantani da abinda zaisa nakawo damuwa a fuskar aleeya.,.....

Sosai jikin ammy yayi sanyi murya a sanyaye tace,

Layla meyasa kike tado da abinda yazamo tarihi?.....

Dr Dawood ne Wanda aleeya zata aura..

Yawu ammy ta ha'diye sbd gudun garajen fahimta tace,

Banganeba Layla sakemin bayani.

Ammy dr dawood shine 'dan abokin Abba dasukazo yanxu.

Mummunan fa'duwa gaban ammy yayi ta lashi busasshen bakinta sai alokacin tasake qurawa layla Ido taqara hango mummunan halinda take ciki tana qoqarin dannewa.

Layla wannan ba abun damuwa bane tunda ba auren aka 'dauraba zanyiwasu abbanku bayani yanxu..

Miqewa tayi laylar ta riqo hannunta tareda dawowa gabanta ta sunkuyar dakai cikeda qarfin Hali tace,

Ammy ke uwace dabakyason kan 'yayanki ya rabu,
Kin manta nayi Miki alqawarin toshe duk wata hanya dazata kawo 6araka atsakaninmu,
Ammy wannan shine alqawarina dazan cika bazan ta6a Bari hawaye yasauka kan fuskar aleeya ba ta hanyata,
Ammy kiyimin alqawarin har abada Bazaki ta6a fadawa kowa wannan maganarba...

Girgixa Kai ammy tayi cikin tsananin tashin hankali da damuwa tace,

Wannan shirme ne kikeyi layla sbd bazai ta6a yiyuwaba,
Idan har farin ciki kikesowa aleeya to Bazaki Bari ta auri Wanda baya sonta yanada wadda yakeso wace irin rayuwar aure zatayi da Wanda keson wata mace ba itaba...

Hawaye ta goge da bayan hannu tace,

Ammy shine farin cikinta,shitakeso bazata ta6a iyason waniba bayansa....

Kidaina fadamin haka sbd wannan ba sacrifice bane Layla rayuwarku ce ku uku zata lalace,
Kalli halinda kike ciki yanxu,
Ji yanda kike qowarin danne quncin dake ranki Amma ina iya ganinsa,

Dawood ke yakeso bazai ta6a son aleeya ba sbd tun farko ba ita yakesoba.

Tsananta hawayenta sukayi tace,

Ammy Koda Baki yardaba na yafe dawood har abada sbd bazan iya cigaba dason abinda aleeya kesoba,
Wannan alqawarina ne duk ranarda aleeya taji zancen Nan zan tafi tafiya ta har abada ammy sbd bazan iya hada Ido da itaba nayi tarayya da ita akan abinda takeso nakasa cirewa zuciyata cewa hakan ba laifina bane.

Tsananta tashin hankalin ammy yayi tace,

Layla meyasa zakiyi haka Dan kuwa hakan shine babban kuskuren dazaki tafka wannan ba mafita bace.

Kuka tasake ahankali ammyn tayi saurin rungumeta tana danne nata hawayen sbd Laylan tasakata a tsaka Mai wuya sbd rayuwarsu duka su biyun ne zata lalace garin toshe 6araka za'ayi gaba Mara da'di.

Jin motsin shigowa yasa laylar zamewa ta miqe ta shige toilet 'din ammy.


Siyama dake jinsu tun farko ta gyara tsayuwarta tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,

Hmmnn dagani abubuwa zasu zomin yanda suka Dace,
Dawood sukeso dukkaninsu hmmm,
I will make this my mission matuqar inada Rai da lafiya bazan ta6a Bari aleeya tasan da wannan zancenba sbd dataji kamar koyaushe Layla xata samesa hakan na nufin koyaushe itace a gabanta..
Duk Wanda yayi qoqarin ha'dasu kuwa saita 'dorasa adaidai inda bazai qara kallon matsalar waniba tasama tafi qarfinsa.
Mission 'dinta na biyu kuwa taheer,
Kallo 'daya tayi Masa ya tafi da zuciyarta Dan haka kuwa duk duniya batasaran zata zauna ta huta batareda burinta na aurensa ya cikaba.

Daki takoma tana zuba murmushin farin cikin samun sauqin abunda yakawota.



Aleeya kuwa tunda sukaje palon taheer kawai suka tarar suka gaisa siyama kallo 'daya tai Masa tasaki Baki tuni tafara tunanin yanda rayuwarta zata canza idan ta auresa.
Ganin zata zubarwa da kanta aji gurin kallonsa yasa tamiqe takoma 'daki anan kunnuwanta sukayo Mata farin ji.

Fira suke hankalinsu kwance akai akai saiya Fadi sunan Layla saidai kawai tayi Masa dariya sbd tun acan tafada Masa akwai Wanda Laylar keso.


Daqyar taheer yaje yashigo dashi sbd lokaci 'daya ya burkice sbd rashin Jin Nur gashi yanxu ta kashe wayar gabaki 'daya ma.
Kodaya shigo Sam mantawa yayi da maganar inda yake daqyar taheer yayita basa Baki yadan sassauto ya nutsu.

Kallon inda take yayi fuska a ha'de..

Lumshe Ido yayi cikin tsananin takaici,
Mum Sam batamasan abinda zai iya soba,.

Fa'duwa gabanta yayi ganin irin kallon daya jefeta dashi amma duk da haka zuciyarta cike take fal da farin cikin ganinsa Wanda tuni sonsa yaci gaba da ninkuwa a zuciyarta.

Kasa magana yayi sbd yanda nutsuwarsa ke qara hautsinewa ya miqe tareda fiddo wayarsa ya fice Yana cigabada Kiran Nur.

Taheer ne yabiyosa da nufin fada Masa abinda yayi Bai daceba Amma ganin yanayinsa sai jikinsa yayi sanyi yace,

Dawood please relax kabari zuwa anjima saika sake Kira yanxu bakaga muna gidan kunya bane.

Wani mugun kallo ya watsa Masa tareda juyawa ya tada motar dasukazo da ita daga gidansu nanan yabar gidan gaba 'daya.
#mamuhgee.
Vote
Comment.
[1/8, 8:38 PM] 0mmr Farouk: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*_godiya da jinjina ga members na DAWOOD fans group_*💋



*20*
Jingina jikin qofar toilet 'din ta jingina tareda zamewa ta durqusa tareda sakin kukan datake dannewa gaban ammy ahankali,
Shesheka takeyi sosai tasa hannu ta rufe bakinta kukan ba tsananta.

Rarrashin kanta tayi ta miqe ta tsaya gaban mirror tareda kallon fuskarta taga yanda lokaci 'daya tayi jajir.

Wanke fuskar tayi jiki ba qwari ta goge fuskar da towel tareda qara tattaro juriya ta fito.

Har lokacin ammy na zaune bakin gadon ta rafka tagumi da hannuwa biyu takasa miqewa bare ta fita takoma Palo.

Fitowarta yasa ammy 'dagowa ta qura Mata ido ta yanda fuskarta tayi jajir lokaci 'daya har wani fa'dawa fuskarta tayi.

Qofa ta nufa zata fice ganin kallon da ammy ke Mata taji tace,

Layla matuqar Bazaki auri dawood ba aleeya ma bazata auresaba.

Da sauri ta juyo tana kallon ammyn.

Eh wannan nawa hukuncin ne sbd Babu dalilin dazaisa ta auri Wanda baya sonta ko ka'dan 'yar uwarta yakeso.

Dawowa tayi ta zauna murya a karye tace,

Ammy kenan niba 'yar uwar aleeya bace.

Me kike fada layla??har abada aleeya Yar uwarkice.

Idan har 'yar uwatace Ni 'yarkice to ammy bazaki hanata samun abinda takesoba sbd ni bansamu ba.,
Ammy mezamu fadawa su Abba idan kikace aleeya bazata auri dawood ba?
Kowa zaisan abinda yake faruwa daganan za'a iya samun rashin fahimta daga wasu Kinga qarshe dai abinda ake gujewar zai faru Kuma dukkanin 'yayanki zasu rasa farin cikinsu hakan zai ta6a zuciyarki da kwanciyar hankalin gidannan,
Ina roqonki ammy daki Bari aleeya tasamu farin ciki da Wanda takeso.....

Katseta tayi cikin 'dan 'daga murya da cewa,

Layla kin kasa ganewa farin cikin ne bazata samuba har abada idan ta auresa.,Kuma me zai faru idan dawood ya ganki amatsayin 'yar uwarta kina tunanin zaiyi shiru ne?

Numfashi Mai ciwo ta sauke murya a karye tace,

Bazai qara ganinaba ammy sbd na yanke duk wata alaqa dashi saita wadda zamu Fara yanxu bayan aurnsa da aleeya amatsayin 'yar uwar matarsa.

Ammy kiyimin wannan alqawarin na bazaki fadawa aleeya ba.

Me kike cewane Layla?""sukaji anfada daga bakin qofa.

Itakadaice ta juya da sauri tana qoqarin danne halinda dake ciki ganin aleeya a tsaye bakin qofa.

Ammy kuwa miqewa tayi ta fice batareda takalli su duka biyunba sbd zuciyarta na ingizatane ga fadar gskia saidai Kuma fadar gskiar zai iya kawo rashin fahimta sbd shaidan zai iya saka musu kishin juna ko yayane sbd za'a iya cewa ya auresu duka Wanda kwata kwata har abada bazataso hakanba Dan Dole watarana za'a samu sa6ani.

Qarasowa tayi jikinta amatuqar sanyaye,
Da sanyin jikin abinda dawood yayi Mata ta shigo Amma Jin abinda Layla ke fada ya qara sanyaya jikinta.

Zama tayi kusada laylar tana kallonta cikeda mamaki da fargabar ganin sauyi sosai atareda ita,
Idanuwanta dasukai jajir da fuskartama gaba 'daya takalla tuni kafin taji koma meyene idanuwanta suka cicciko Nan take damuwar datake ciki ta dawood ta 6ace asanyaye tace,

Dama Layla akwai abinda harzaki saka wani alqawarin kar afadamin??
Wane irin sirrine da Ni bazan iya 6oye mikiba har kike guduna dashi....

Jin muryar aleeyar tafara rawa yasa tayi saurin riqo hannunta tana qoqarin Hana hawayenta fitowa Amma Saida suka gangaro tace,

Har abada Babu wani sirri dazan 6oye Miki idanma akwai to kisaka aranki Dan ciganki da farin cikinki ne...

Inason sanin koma menene Layla kifadamin tun kafin zuciyata ta buga da fargaba.

Share hawayenta tayi ahankali tace,

Dawood iyayensa sun Masa Mata har antsayar da ranar aurensu bazai ta6a aurena......

Tun kafin laylar takai qarshe kukan datake riqewane ya kubce Mata tayi saurin rungume laylar cikeda wani irin tausayinta dama tanason yin Kuka Dan rage zugin zuciyarta na tsantsar qiyayyarta data hango a idanuwan dawood idan ba kuskuren gani tayiba.

Kuka take sosai na tausayin Layla da kanta saidai tafasa fadawa Layla damuwarta Akan qiyayyarta data gani a idon dawood sbd karta qara Mata damuwa ko ammy bazata fadawa ba zata bar maganar aranta ta Taya 'yar uwarta jimamin abinda yasameta..

Sosai tayi qarfin Hali ta nunawa aleeya ta rumgumi hakan amatsayin dama bashine mijinta ba.

Girgixa Kai aleeya tayi tana fitarda sabbin hawaye tace,

Yanda kikesonsa har abada bazaki daina sonsaba,
Tun zamana dake akwai wasu farin ciki da annashuwa dashine kadai yake sakiyinsu koni bana sakaki duk kuwa danasan babbn matsayin danake dashi agunki,
Layla bazaki iya babushi ba Ni zanje har gurinsa na roqesa yadawo gareki zan qasqantar da kaina na roqesa qasqantarwa ta qarshe Dan yadawo gareki..

Share hawayenta tayi tana qaqalo murmushin qarfin Hali sbd so take arufe maganar dawood da ita gaba 'daya ayau basai ankwanaba ga kanta dake tsananta ciwo zazza6i Mai zafi takeji sosai.

Aleeya na dangana nabarsa har abada Dan haka daki tayani nemosa gwara kitayani mantawa dashi.

Sake rungumeta aleeya tayi cikin tsananin tausayinta da Jin zafin dawood 'din daya za6i wata yabar Layla Nan take taji ta tsanesa Koda zai dawo bazata ta6a barinsa ya auri Laylan ba sbd Bai cancancetaba
Laylanta ta cancanci Wanda yasan darajarta fiyeda komai.

Jin jikin laylar da zafi yasa ta ja hannunta suka koma bedroom 'dinsu ta kwantarda ita tareda ja Mata bargo cikeda kulawa tace,

Have some rest zakiji qarfi zuwa anjima.

Miqewa tayi ta zame kayanta tasa jeans da vest tadawo bakin gadon da laylar ke kwance ta rafka tagumi cikeda tunani da damuwar kanta data laylar.

Itama Layla rufe idanuwan kawai tayi.

Daqyar ammy ke sakin murmushin yaqe hardai Abba ya tambayeta maganar iyayen manemin Layla kawai suke jira su qaraso yanxu.

Rufe idanuwa tayi tareda ha'diye wani 'daci a maqoshinta cikeda damuwar abinda zata fada tace,

Saidai ayi hkr akwai wadda iyayensa keso ya aura Dan haka sun fasa zuwa saidai zuwa gaba idan ansamu fahimta.

Fada Abba yahauyi Rai a6ace yace,

Dama dai bada gskia yakeyiba Dan da bazai Raina Mana hankaliba yace zasuzo.

Hakuqi CJ yabawa abban Yana cewa,

Agodewa Allah bama Saida akazo 'daurin aure yace yafasaba.

Exactly fa ai gwara da tun yanxu akasan stand nasu""""mum ce tafada hakan tana nuna tausawarta ga ammy datayi nisa a tunani ko abinda suke fada bataji.

Zuciya ba da'di hakanan Abba da dad suka tsayar da bikin wata biyu Masu zuwa hakanan mum ta haqura badan tasoba sbd da wuri taso ayi.

Koda suka koma gida dawood bayanan Kota kansa batabiba tayita harkokinta cikin farin ciki.


Baidawo gidanba sai dare sosai kallo 'daya zakai Masa yabaka tausayi sbd kwata kwata Bai saba da wahala ba Amma yau ko ruwa baisawa cikinsaba haukacewane kawai baiyiba gurin Kiran layinta yakira yakira,yayi yawo agarin harya 6ata saidaya Kira taheer yaje yadawo gida dashi.

Ganin yanda daqyar yake bude bakinsa daya bushe yasa mum da taheer hankalinsu Fara tashi Nan tahau lallashinsa akan yasha Koda juice ne Amma yaqi.


Wasa wasa saiga zazza6i Mai qarfi ya kwantar dashi adaren Babu Wanda ya rintsa cj cikin tashin hankali yasa sukabi jirgin safe suka dawo Abuja.

Koda suka dawo babu abinda yayi sauqi gashi yahanawa kansa sukuni da daina Kiran layinta.

Da daddare Dr dayazo tasashi yayi mixing alluransa Dana bacci yayi Masa Nan take bacci yayi gaba dashi.

Dr na fita ta 'dauki wayarsa ta duba numbern datake nema ta goge tareda duk wasu massages daga gareta duk wani Abu daya danganceta saidata goge ta 'daga wayar sama ta sakota qasa tareda ficewa daga bedroom 'din.
#mamuhgee
Vote,
Comment,
Follow and share.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*21*
Washe gari sai guraren qarfe goma ya tashi
Idanuwansa kawai ya bude ahankali ya sauke kan bedside clock yaga time.

Lumshe idanuwansa yayi cikin wani irin zafin zuciya da takaici sbd yagane allaurar da akai Masa kasancewarsa qwararren likita..

Tashi zaune yayi Dan Babu Wanda yakeson ya amsa Masa tambayoyinsa kamar mum sbd idan ba itaba ya tabbata Babu Wanda zaisa ayi Masa alllurar bacci yanason yasan dalilinta nayin hakan.

Zuro qafafunwansa qasa yayi sai akan wayarsa da sauri yakai hannu Yana cewa,

No no no no please..

Kaca kaca screen 'din yayi ya shafe ba'a ganin komai kamarma ta mutu gabaki 'daya.

Yanda zuciyarsa ke tafarfasa ne yasa ya aje wayar tareda nufar toilet yayo alwala yayi sallar asuba Yana qara Jin zafin allurar d sbd irin yanda yayi lattin sallar.

Yana idarwa ya miqe tareda 'daukar wayar ya nufi gurin mum.

Yana shiga ya tararda suna rigima da taheer akan yanason Layla tunda Wanda ke nemanta ya fasa itakuma tace Sam ba'a zuriarta ba 'yar tsintuwa sbd tasan 'ya 'daya Tak Abba yakeda ita.

Basusan dashiba saijin tayi ya riqo hannunta yasaka Mata wayar idanuwansa taf da hawaye sunyi jajir Yana qoqarin rage zafin rai da tsananin fushin dayazo dashi yace,

Cikakken bayani zakiyimin akan abunda yasamu wayana bayan kingama fadamin dalilinki nasawa aimin allurar bacci.

Kallonsa tayi takalli taheer dashima fuskarsa ke 'daure sosai
Itakan wane irin masiface ke Shirin rufo Mata ta hanyar 'yayanta akan mata shi dawood Nur shikuma taheer Layla.

Mai aikice ta qaraso da warm milk da mum tasa adafa Masa
Wata gigitacciyar tsawa ya daka Mata wadda tasa mum firgita tana kallonsa cikin tsananin mamakinsa tace,

Mi'amor komai nayi I did it for your own good,,I mean can't you see hw stress and....

Meyasamu wayana?
I know you broke it mum,
Why?
Why? Did you realize wat you did by doing this...idan har kinyine danki rabani da ita then you are wrong,
You are wrong mum sbd har abada bazai ta6a faruwa,
You called me your love but I don't see anything like that anan mum,
Zan Baki shawara amatsayina na 'danki,
Kibarwa Allah komai yayi ikonsa ayanda yaso sbd idan Kika matsa akan haka ina gujemiki abunda zai biyo baya sbd Zaki iya rasa 'dan ki har abada..and one more thing maganar aure banayi bazanyi ba
And i'm leaving this house now coz I can't spend another minute hia,,I feel suffocated.

Riqosa tayi niyaryi ya juya yabar gurin sbd hawayen idanuwansa zasu iya zubowa kowaneokaci.

Duk wani Abu dazai buqata ya ha'da ko wanka baiyiba ya fito har lokacin zuciyarsa zafi da ra'dadi take masa ba abinda yake son gani kamar Nur sbd ganintane kawai zai yaye Masa qunci da ciwon da zuciyarsa ke Masa.

Kallon taheer mum tayi cikin tashin hankali tace,

Honey please kaje karka barsa yatafi please don't let him leave....

Girgixa Kai yayi cikeda tausayin 'dan uwansa dashi kansa da Allah yabasu selfish mother da she can do anything to get wat she wants.

Fita yayi ya nufi gurin dawood Amma cikin rashin sa'a Bai tarardashiba ya wuce.

Gurin mum yakoma ya kalleta yace,

Yatafi and and I will follow his steps anytime soon nima zan iya tafiya idan Kika hanani samun Layla.

Juyawa yayi ya wuce yabarta da Baki sake,
Takaici da 6acin Rai taji yataso Mata Dan sunga tana lalla6asu sukeson su riqa yin abunda sukaga dama,
Zata nuna musu itace ta haifesu basune suka haifetaba.

Taheer na Isa bedroom 'dinsa yakira aleeya yafada Mata shizai auri Laylan idan tabasa dama yayi alqawarin Bata farin cikin dazata manta komai.
Bata nuna Masa amincewaba tace yabari zatai magana da laylar tukuna.

Daganan direct gurin dad yanufa yasanardashi shi yanason layla zai aureta
Mamaki sosai dad 'din yayi kafin yayi farin

1 Comments On DAWOOD
avatar
aisha-9-4-5

2 months ago

Reply

I love this book

Please Login or Register in order to submit comment