Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yunwar na cinta Amma Batada yanda zatayi.

Kuka yasake daqyar yabude Baki yace,

Yunwa nakeji Kuma inajin ciwo Layla kisamomin magani da abinci kona cikin bolane Ni zanci.

Kukansa yayi tsanani daga Mata hankali rashin sanin abinyi yasa itama tasa kuka tana rarrashinsa amma kamar tana qara Masa ciwone Dan har wani irin rawa jikinsa keyi.

Tunawa tayi da kudin da'aka basu ta 'daga kwalin taciro kudin ta zari 'daya ta mayar tareda miqewa tace,

Zan dawo yanxu kaji.

Da sauri ta juya ta nufi Mai abincin kusada chemist din hamisu tasiyo Masa shinkafa da ruwa ta kar6o Masa magani gurin hamisu ta dawo da gudu.

Cak ta tsaya cikin tsananin tashin hankali jikinta na daukar rawa ganin Bilal cikin jini kwance kamar matacce.

Watsi tayi da abincin tayo kansa da gudu tana jijjigasa tareda kiran sunansa..

Bilal meya sameka?..meye yayi maka haka wannan jinin.....

Daqyar Yana kuka yace,

Kudin dakika aje sukamin duka suka 'dauke duka sun gudu.

Wani irin kuka da ajiyar zuciyane sukazo mata lokaci 'daya kafin tayi magana dahiru yaqaraso da saurinsa yace,

Yauwa Layla bani kudinnan Kuma kutashi muje..

Sunkuyar dakai tayi cikin kuka tace,

An dauke duka.

Harara ya watsa Mata tareda gyara tsayuwa yace,

Kinga banason baqin ciki nida zan taimaka muku banmuku baqin cikiba sai 'dan kudinda zan qaru dasu shine zakumin baqin ciki Amma wlh bakida imani Layla...

'daga kwalin yayi ya zazzage baiga komaiba.

'dagowa tayi ahankali takallesa tace,

Wlh ansace sunema aukaiwa Bilal haka....

Ke dalla yimin shiru muguwa kawai Amma wlh kin cuceni Dan har bashi naci yanzu Koda uwarwa kukeson nabiya,
To wlh kanku kukayiwa Dan saiku nemi gurin zuwa wlh ba inda zan kaiku tunda bakida Jin qai da tausayi.

Juyawa yayi afusace kamar zai rusa kuka ya wuce Yana masifa.
#mamuhgee






VOTE
COMMENT.
[12/31, 10:50 AM] ‪+234 706 677 7871‬: _*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*6*
Bayansa tabi da kallo harya 6acewa ganinsu ta Sunkuyar dakai hawayenta na qaruwa takalli Bilal cikin hawaye tasake miqewa tareda komawa tasake siyo Masa abinci da sauran canjin hannunta da ruwa tadawo ta 'dauki maganin dazu data siyo.

Tuni jikinsa ya rikice da zazza6i takamasa daqyar sbd itama qarfinta yayi qasa sosai ta tayar dashi zaune ta basa abincin kadan yaci yasha magani ta 'daure sauran a Leda ta aje gefe tasake lullu6esa tana Masa sannu ahankali.

Dare nafarayi zazza6insa yayi tsanani ga mage mage dasuka dinga Bata tsoro Dan wani irin kuka sukeyi Mara dadi ta kalli bolar Nan tsoro yaqara rufeta ta miqe jiki na rawa ta tattarosa daqyar ta Goya nauyinsa na rinjayarta haka tabar gurin tana tunananin gurin fakewa kafin safiya.

Saidatayi nisa sosai da anguwar kafin taga wani qonannen shago bakin titi daga gani gobara yayi ta qarasa ahankali ta saukesa tareda zubewa gefe tana fidda numfashi daqyar sbd yunwa gajiya da zazza6in dake cinta.

A wahalce bacci ya daukesu su duka Bata farkaba sai da gari yayi haske tana bude ido taga Bilal zaune Yana kallon waje.

Tashi tayi ahankali ta dawo kusadashi murya Bata fita sosai tace,

Kaji sauqi Bilal?

Eh yace Yana qoqarin bawa kansa qarfin jiki Dan haka bazatai musu ba Dole zasu Fara bara danshi Sam bayada jimirin yunwa ko kadan.

Layla muje bara Kinga Ni yunwa nakeji wlh Kuma Kinga baabaa tuntini Yana cewa mu iya nema da kanmu kintuna.

Kallonsa tayi da idanuwanta dasukai jajir sukai mugun nauyi sbd kuka taga yanda duk ya kumbura fuskarsa da sauran jikinsa sbd kadewar da mota tai Masa dakuma dukan da akai Masa ga raunikansa sunanan saima quda dake qoqarin hawa ta girgixa Kai zuciyarta na qara karyewa tace,

Bazaka iya fita baraba kabari ga saurin naira 'dari biyu a hannuna zamuci wani abu da ita.

Miqewa tayi ta fita tana dudduba inda zata samo abinda zasuci.

Duk Wanda tabi ta gefensa saitaga ana kaucewa sbd kallo mahaukaciya da ake Mata.

Qosai taga wata Mata nayi gefen wani shago ta qarasa tun kafin tafadi qosai tazo siya matar ta taso Mata cikin masifa tace,

Matsa daga can karki zubomin dau'da Kinga kima tafi bana bada sadaka nima nema nake.

Matsawa baya tayi murya asanyaye ta miqo kudinta tace,

Siya zanyi harda koko.

Wani mugun kallo ta watsa Mata kafin ta fizgi kudin ta zuba Mata kosan 'dari kokon 'dari a Leda baqa.

Kar6a tayi tareda tsayawa jiran canji.

Harara ta watso Mata tace,

Meye Kuma?

Canji zakiba.....

Canjin me Kuma ai kosan 'dari ne kokon'dari jeki Kisha saikin ture.

Girgixa Kai tayi tace,

Banason na duka.

Rufe Ido Mai kosan tayi ta koreta cikin rashin mutunci kafin taci gaba da aikinta tana masifa ita kadai.

Komawa tayi takaiwa Bilal sosai yasha itakuma kadan Tasha Dan karya qare anjima su rasa ta 'daure sauran a Leda.

Ranar haka suka wuni cikin gurin Saida yamma tabasa sauran Kokon ya shanye tareda sauran paracetamol din daya rage musu ita saidai ta kwana hakanan.

Washe gari tunda safe saiga Mai shagon yayi musu korar wulaqanci kamar zai dakesu sbd kai Masa labari da'akayi sadaka yallah zasu mayar da shagonsa gida.

Suna fitowa suka hau titi suna gararanba harsuka Kai wani gurin siyayya sukaga mabarata da musakai zazzaune suna jiran duk Wanda ya fito ya Basu sadaka.

Ba 6ata lokaci Bilal yaja hannunta Bata musaba sukaje sukabi sahu Dan dama ko ruwa Babu acikinsu Bilal yayi kukan harya gaji yasawa kansa dauriya.

Tunda suka zauna ko acikin mabaratan sun fita daban sbd tsananin bushewar dasukayi ga dau'da da mataccin kaya hakadai suka zauna jiran tsammani.

Tunda suka zauna kusan so hu'du ana bada sadakar kudi sai mutanen su rabe abinsu ko kallo Basu ishesu.

Hawaye ta sharce tareda cewa Bilal yatashi sutafi wani gurin.

Qin tashi yayi saima matsawa daya qarayi kusa da qofar super market din daidai kuwa fitowar wani saurayi tareda yarinya kimanin shekarun Layla.

Da sauri Bilal ya matsa gurinsa yace,

Munajin yunwa nida yayata Dan Allah kabamu abinda zamuci tun jiya muke jinta.

Kallon Bilal din yayi ganin yanda bakinsa ke bushe yasa ya yarda da zancensa yaciro 'dari biyar yabashi.

Saboda murya ko godiya baiyiba yayi gurin Layla da gudu yace,

Nur tashi muje munsamu.

Girgixa Kai saurayin yayi ita kuwa Layla ta qurawa Ido tanajin wani irin so da qaunar Layla na shigarta..
Tun ranar farko data Fara 'dora idonta akan Layla ranar dasukaje gurin faduwar ginin da abbanta takejin wannan connection,
Tun ranar takasa cireta cikin ranta.

Harsuka shiga mota sukabar gurin Bata daina kallontaba harsaida suka 6ace.

Sukuwa barin gurin sukayi cikin farin ciki Dan kuwa ko ita Layla yau saidata nuna farin cikin samun kudin.

Shinkafa da wake da manja suka siya ta 'dari biyu sukaci suka qoshi daga Nan suka cigaba da bulayinsu har dare yayi suka la6e gefen wata islamiya suka kwanta da zazza6i dukkansu suka kwana Amma gari na wayewa suka bazama bara bawai don sundaina jinsaba saidan ba amfanin kwanciyar Dan korarsu ma akayi tun Basu tashiba.

Koko suka siya da qosai sukasha daganan suka koma super market din jiya suka zauna.

Ranar Kam ba sa'a har Isha Basu samu komaiba jiki ba qwari suka koma inda suka kwana jiya suka kwanta bayan sun siya alalar hamsin sun raba sunci.

Tsawon sati uku da rasuwar baabansu Babu wani sauyi ko taimako saima ta6ar6arewa da rayuwarsu tayi Dan zuwa yanxu duk inda suka samu kwana sukeyi hartakai idan sunga kangon gida murya sukeyi dare yayi su kwanta gari ya waye suyi gurin bara..

Tsawon lokacin Basu ta6a ko wanka ba kayansu tuni suka qarasa yayyagewa Nan take suka zama kamar wasu aljanu,
Yawon dasuke yini sunayi ko mashin ne saiyaso hutu bare 'dan Adam gashi bamai takalmi acikinsu daga bayane Bilal ya tsinto musu wasu fasashi a bola idan yasa yau gobe ita tasa.,
Duk wahalarsu ba kullum suke samuba ko sunyi barar.

Tafe suke Bilal na Bata labarin yanda suke bara dah kafin baabaa ya rasu ta kallesa tace,

Bilal to meyasa yanxu bama samun sadaka.

Ko dacan fa gidaje muke zuwa muyi bara ko mu zubar musu da shara kafin abamu koya kwana munaci.

Qarasawa bakin wani babban mall sukayi tana cewa,

Yaudai Allah yasa musamu da wuri muje mu nemi gurin kwana karmuyi irin na jiya duhu yayi bamu samu gurin kwanciyaba Dole muka kwana gefen bola nidai tsoron bola nakeji banaso muna kwana anan.

Zama sukayi Bilal ya aje matacciyar robar daya samo musu ta bara dacin abinci.

Har kusan magriba Basu samu komaiba sai wani guntun biscuit da wata yarinya ta jefar gurin rigima ta fito gurin da uwayenta.

Kallonsa tayi cikin sanyin murya tace,

Bilal muje ko gurin kwanciya mu nema kar duhu yayi.

Sabon garari suka soma na neman gurin kwanan yau Amma duk inda suka Fara qoqarin zama da gudu ake korosu gashi yau akwai hadari sosai daga ita harshi tsoron walqiya da tsawa suke shiyasa duk jikinsu yayi sanyi.

Basu ankaraba aka Fara yayyagi saikuwa ruwa Mai qarfi da gudu suka raku6e qarqashin wata bishiya duk da ba wani ruwa take karewa ba Amma haka suka fake tareda qanqame juna.

Ruwa Mai qarfi akayi sosai sai tsakiyar dare ya tsagaita daqyar taja Bilal suka ra6e gefen shagunan gurin sbd rawar sanyin dayakeyi ko motsi yakasa.

Suna raku6ewa gurin itama ta dunqule jikinta na jijjiga sosai.

Ana fitowa sallar asuba gari na Fara haske takalli Bilal dake baccin wahala tace,

Bilal tashi muje karsuxo su dakemu kaga sunce duk suka sake ganinmu Nan saisun Mana duka.

Da qyar yatashi zaune takamashi suka miqe sukabar gurin tana riqeda hannunsa.

Doguwar tafiya sukayi ya sulale qasa ya zaune gefen wata babbar makaranta ya lashi busasshen makinsa daqyar yace,

Nagaji mu huta nan.

Zama tayi kusadashi tareda qurawa makarantar Ido.

Baccin wahala ne yasake daukar Bilal ta qura Masa Ido sai kawai ta fashe da kuka tana tunanin badai haka zasuyita rayuwaba harsu girma su mutu.,,
Ahankali tace gwara mota ta ka'demu tare mu mutu tare mu huta.

Suna gurin har qarfe biyu hayaniyar tashin 'yan makarantar ne yatadashi ya tashi zaune yana kallon gate din  makarantar yace,

Nur zanje na roqesu abinci idan sun rage.

Bai rufe bakiba wasu 'yan Mata uku suka fito suna dariya da manyan school bags dinsu goye.

Cikin sauri yace,

Dan Allah ku bamu sadaka muci abinci..

Wani mugun kallo suka watsa mishi atare Layla na ganin haka ta taso ta riqo hannunsa batareda ta kallesuba.

Harsun juya 'dayar taciro nera goma tace,

Kar6i.

Da sauri Bilal ya juyo gurin kar6a ya ta6a hannunta wani wawan Mari ta sharara Masa cikin tsananin Jin zafi ya tureta harsaidata fadi yace,

Allah ya isa muguwa..

Zaro Ido sukayi dukkaninsu cikin hasala ta miqe tareda rufesa da shuri da sauri Layla ta rungumesa ta Kare
Qara quluwa tayi tasa qafa takaiwa laylar mugu bugu a goshi Nan take goshin ya fashe hannu ta qara dagawa zata Kai Mata Mari aka riqe hannunta.

Aleeya""""""tafada tana kallon cikin idon wadda ta riqe Mata hannu sbd batasaran ganintaba gurin zuwa daukarta.

Sake Mata hannu aleeyar tayi tareda juyowa ta kalli Layla dasuke kuka antaru anata kallonsu.

Hannu ta miqawa laylar.

Miqewa tayi tareda riqo Bilal suka juya zasu wucewarsu aleeya tayi saurin riqeta murya na rawa tace,

Zan taimakeku.

Atare itada Bilal suka qurawa aleeyar Ido sbd yaushe Rana ta farko da wani yace zai taimakesu duk kuwa gwagwarmaya da gararin dasukayi.
#mamuhgee




                *VOTE*
            *COMMENT*
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*7*
'daure fuska siyama tayi sosai tana kallon aleeya tace,

Wat do you think you're doing aleeya?

Abinda Yakamata nayi tun ranar farko banyi shi zanyi yanxu.

'dari biyu siyama ta Ciro cikin school bag dinta ta jefawasu Layla tareda Jan hannun aleeya tace,

Let's go zuciyana tafara tashi da warin dau'darsu.

Fizgewa tayi cikin 'daga murya tace,

Dasu zan tafi so gwara ki dauki 'dari biyunki zatai Miki amfani gurin Hawa taxi kar kafin mukai warin dau'darsu yasaki amaye kayan cikinki..

Wat?,,,,siyamar ta fada tareda matsowa gabanta tana rage murya tace,

Karma kifara tunanin 'daukar wainnan sadaka yallah din Dan haka salin alin kibasu sadakar dazaki Basu mutafi coz wannan abin dakikeyima you're disgracing your self.

Hannu ta qara miqawa Layla akaro na biyu laylar taqara qanqame Bilal har lokacin kuka sukeyi.

Tsaki siyama taji cikin tsawa tace,

Kubar Nan shegu matsiyata.

Miqewa sukayi aleeya ta damqo hannun Layla tareda kallonta Ido cikin Ido tace,

Zan taimakeku zaku bini?

Qura Mata ido Layla tayi akaro na farko,
Sake tambayarta aleeya tayi tana kallonta tace eh zasu bita.

Murmushin farin ciki tasaki tareda qara riqe hannun laylar suka nufi mota batareda taqara waiwayar siyama ba ta sakasu mota tacewa driver sutafi.

Wani mugun huci siyama ta furzar tana cewa,

Allah yasa wannan taimakon yazamo muguwar qaddarar rayuwarku ta har abada,
Ina muku baqin bakin Allah yasa wannan shegiyar sadaka yallar tazamo babban bala'in dazai wargaza rayuwarku gabaki 'daya atare...

Idan ita Bata zamo muguwar qaddararki ba Toni zanzamo muku muguwar gobarar dazata qone farin cikinku da rayuwarku duka.

Tunda suka shiga motar tayi shiru tana kallon Layla itakuwa Bilal daketa farin ciki ta qurawa ido yaune karo na farko dasuka ta6a shiga mota arayuwarsu.

Babban gidan dasuka shiga yasa ta qanqame hannun Bilal harsuka fito motar.

Kallonta aleeya tasakeyi tareda qara riqo hannunta suka nufi cikin palon gidan.

Ammy da abbanta na zaune apalon suna magana tashigo da sallama hannunta na riqe qam da hannun Layla dake biyeda ita kamar raqumi da akala.

Tsaye ammy ta miqe tana kallonsu Layla dasukafi Mata Kama da mahaukata arikice tace,

Aleeya suwaye wainnan?

Ahankali tasaki hannun Layla ta matso gaban abbanta ta durqusa murya a sanyaye tace,

Abba ina qaunarta tun ranar farko Dana ganta ranar da mahaifinsu ya rasu mukaje Dan Allah Abba ka taimakesu.,

Kallonta yayi cikin kulawa ya tayarda ita ya jawota kusadashi yace,

Aleeya ai nabasu taimako tun.....

Girgixa Kai tayi tace,

Abba sonake kazama uba agaresu inason sudawo Nan taredamu ingantacciyar rayuwar dakake bani nakeso kabasu.

Kallonsu Laylar ammy tayi taga yanda sukayi wani iri kalar tausayi saitaji jikinta yayi sanyi Nan take wata zuciyar ta ingizata data kar6esu matsayin 'yaya kodan 'yarsu qwaya 'daya tal data nuna son hakan.

Shiru Abba yayi ganin tafara hawaye yace,

Shikenan yanxu dai zasu zauna kafin gaba zansan abinyi.

Rungumesa tayi tareda cewa,

Thank you Abba.

Ammy miqewa tayi ta miqawa Bilal hannu tace,

Zoka fadamin sunanka.

Ahankali yakalli Layla kafin ya matsa kadan yace,

Bilal.

Jin tsami da warin dasuke tashi ajikinsu yasa tayi saurin Kiran shafa'atu Mai aiki tace taje dasu tayi musu wanka.

Harsunbi bayanta aleeya tayi saurin riqo hannun Layla tareda sakar Mata murmushi tace,

You're my responsibility from now on so I will be the one to clean you up..

Sunkuyar dakai layla tayi sbd batasan abinda aleeyar tafada ba saidai binta datayi har cikin qaton lafiyayyan room dinta dayaji adon komai blue and white Bilal kuwa shafa tatafi dashi danyi Masa wanka.

Kallon Abba ammy tayi bayan tafiyarsu tace,

Allah zai biyaka for this kaida 'yarka sbd tun farko haka Yakamata kayi kodan ita babbar dake mace.

Sauke numfashi yayi ahankali yace,

Tunda aleeya na qaunarsu I have no other option but to Join the Q,
Insha Allah zan kwatanta Basu kyakkyawar rayuwa.

Allah yatamu riqo tace tana kallon qofar dasukabi.

Kayan jikinta tasata cirewa tareda miqa Mata blue towel 'dinta daqyar ta tube ta 'daura tana cewa,

Ina Bilal.

Murmushi aleeya tasake tana tattara tsumman kayanta data cire tana cewa,

Anje yimasa wanka ki kwantarda hankalinki kinji.

Toilet suka shiga tsoro da mamakin gurin Yakamata Amma miskilancinta yasa hakan Bai fitoba
Aleeya tajata bakin shower tun ba'afara wanke kaiba ruwan datti suka Fara zuba Nan take towel ya canxa kala sbd dama qin cirewa tayi.

Mamaki da tsoro dau'dar dake fita ta Bata Amma hakanan takejin Bata qyamarta tasa shampoo tayita wanke Mata Kai harsaida ta qararda kusan robar shampoo 'din.

Sabulu da soso ta damqa Mata a hannu tareda juya tafice daga toilet din.

Jiki asanyaye tayi wankan tafito daure da sabon babban towel 'dinda aleeyar ta nuna mata arataye.

Tasowa tayi tajawota ta zaunar gaban mirror tana goge Mata jiqaqqen gashinta tana kallonta ta cikin mirror fuskarta 'daukeda murmushi tace,

Haryanxu Baki fadamin sunanki ba nadaiji na qaninki 'dazu saura naki.

Kallonta Layla tayi kafin ta sauke Kai ahankali tace,

LAYLA Amma baabana nakirana da NUR.

Murmushi aleeya tasaki tareda dawowa gabanta ta riqo hannunta tace,

Ni Baki tambayi sunanaba.

Ahankali tace,

Naji dazu anfada.

Ok kifada naji da bakinki.

Ahankali ta "dago takalli aleeyar tace,

Aleeya.

Miqewa tayi tana Jin farin cikin daga yanzu tasamu 'yar uwa Kuma qawa bazata qara komai ita kadaiba.

Kayanta ta 'dauko gown black da sabon pant da vest tabata tana cewa saka Bari nakawo Mana abinci.

Ficewa tayi taje kicin da kanta ta 'debo musu abinci a plate 'daya takawo tareda robar coke biyu.

Kallon abincin Layla tayi ta ha'diye wani tsinkakken yawu kafin ta 'dauke Kai tana wasa da sarqar hannunta.

Aje abincin tayi tana kallon sarqar da Laylar ke wasa da ita tace,

Sauko ga abinci.

Kallon abincin tasakeyi kafin asanyaye tace,

Tareda Bilal zanci.

Karki damu Shima gashican za'a saka Masa nasa.

Miqewa tsaye tayi tana qara sanyaya muryarta tace,

Dan Allah inaso naci taredashi munsaba bamaci dabam.

Okay okay Bari nakirashi sai yazo kuci wannan Ni naci nawa dabam.

Da sauri taje takirawosa suna shigowa da gudu yayo gurin layla Yana cewa,

Layla dubi kayan da'aka sakamin Masu kyau Kinga harda takalmi aka bani kumafa harda wanka akamin kema ji anbaki Kaya Masu kyau Dan Allah Layla karmu tafi muyita zama anan harmu gir......

Rufe Masa Baki tayi tana murmushin farin cikin ganin yanda yayi fes farin ciki da murna fal ataredashi.

Abincin gabansu aleeya ta nuna Masa cikin dariyarsa tace,

Ga Kuma abinci Yana jiranka kaci saika ture.

Zaro Ido yayi yawunsa na katsewa ganin taliya da miyar kwai da namomi.,
Tunda suke Basu ta6acin taliya ba har gwara nama idan sallar layya tayi idan yaje yawon bara ko aikin yakan samo tsokoki suci.

Zama yayi da sauri Yana jawo hannun layla Yana cewa,

Zo muci layla Kinga harda namafa.

Zama tayi ganin ganin aleeya ta fita Nan suka Fara cin abincin jikinsu har rawa yakeyi dukkaninsu
Kallonta yayi cikin dariyar Jin Dadi yace,

Layla wlh abincin Nan Dadi Allah yasa su riqemu suce suna sonmu wlh idan suka koremu ba inda zamu kuka zamuyatayi muqi tafiya..

Dariya tayi ahankali tana Kai lomar taliya bakinta tace,

Da ganifa sunada kirki bazasu koremu ba kumama aleeya nada kirki tana sonmu.....

Dariyar datake riqewace tun dazu data samesu sunata faman cin abincin  ta kubce Mata ta qaraso tana cewa,

Bilal layla tafadi gskia ko kowa baya sonku ni ina sonku daga yanxu nima nazama yayarka.

Cikin Jin Dadi jikinsa haryana rawa yace,

Da gaske zamuyita zama anan bazamu qara kwana bola ko titi ba.

Hawayen tausayinsu suka ciko idanuwanta ta jawosa jikinta tace,

Name alqawari insha Allah bazaku qara rayuwa ako inaba sai taredamu.

Ahankali Layla ta 'dago murya a sanyaye tace,

Mungode.

Zaunawa tayi tareda saka hannunta a abincinsu tana cewa,

To nima aci Dani tunda daga yanxu nima Dani za'ariqa cin abincin.

Suna gamacin abincin ta sake jawosu suka nufi palon Abba suka qara gaishesa ahankali ya riqa yimusu tambayoyi akan rayuwarsu Nan Bilal yayita fada Masa komai tin talauci da wahalar dasukasha tun baabansu nada rai har zuwa yanxu itadai tana rakube gefe.

Cikeda tausayawa ammy tajawota tana cewa,

Sannu kinji Layla.

Kai ta 'daga ahankali tana wasada sarqar hannunta Wanda yake 'dabiarta.

Janta aleeya tayi suka koma 'dakinta shikuwa Bilal zagewa yayi yanata bawa Abba labari abban na sauraronsa qaunar yaron nashigarsa sbd kewar yara qanana data shigesa gashi ba ranar samunsu sbd bazai qara ta6a haihuwa ba.

Ammy kuwa dariya da tausayin labarin da Bilal din ke bayarwa kawai take sbd duk yakai qarshen kalma saiyace Dan Allah su riqesu karsu koresu.

Mamaki da tausayine yakama aleeya lokacinda sukazo sallah taga yanda laylar keyi Sam ba ilimi aciki suna gamawa ta juyo ta kalleta tareda gyara zama tanayi Mata gyara.

Ita kuwa sunkuyar dakai kawai tayi tana sauraronta.
#mamuhgee


                          VOTE
                     COMMENT
[1/1, 11:03 PM] ‪+234 701 680 1465‬: _*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*8*
Lokaci yaja Ahankali tafara sabo da kowa na gidan Bilal kuwa ba ruwansa tuni yayi sabo da kowa musamman Abba kamar dama Nan aka haifesa ammy kuwa Layla takeji matuqar ji da it's duk da har lokacin takasa sakewa gabaki 'daya aleeya ce madai ta sake da ita sbd yanda take matuqar ji da ita Wanda Dan Dole kowa keji da Layla agidan sbd aleeya.

Wata 'daya sukayi agidan suka tattara suka koma Lagos sbd can dama suke da zama hutu da aiki sukazo yi duk da dai su Yan asalin Nan 'dinne.

Sosai su Layla sukayi mamakin ganin girma da kyawun gidansu nanan din Dan duk kyawun na adamawa wannan yafi.

Decorations din dakin aleeya aka canxa musu komai bibbiyu aleeya blue Layla pink Amma gadonsu 'daya.

Kaya sosai ammy ta 'dinka musu kusan komai iri daya sbd gabaki 'daya aleeya cewa tayi batason komai nata asiya musu sababbi iri daya da Layla.

Ba iyayenta da Masu aikin gidan kadaiba hatta ita kanta layla mamakin tsananin qaunarda aleeya ke Mata takeyi sbd kaf rayuwarta ba'a ta6a nuna Mata qauna irin wannanba saidai iyayenta.

Bilal kuwa 'dakinsa dabam da Mai kula dashi Shima komai ansaka Masa tundaga kan wardrobe kayan wasa dana karatu sbd suna dawowa Basu wani jimaba aka sakashi makaranta primary 1 Amma ana hada Masa da lesson sbd yayi saurin fahimta Dan na class na Masa wuyar ganewa tunda ba ta6a shiga aji yayiba.

Layla kuwa Mai lesson guda aka dauko Mata sunayi ba qaqqautawa ga malamin arabic dake zuwa har gida Yana musu su duka uku Dan dama aleeya Bata zuwa islamiya saidai malam yazo gida ya karantar da ita.

Kullum dare kafin su kwanta sai aleeya tayita nanata Mata karantunta na lesson na addini kuwa sai sunyi sallar asuba.

Ada aleeya Batada wata walwa ko sakewa kullum tana daki kwance Wanda hakan ke matuqar ta6a zuciyar iyayenta harsuka dauko siyama 'yar yayar ammy riqo Amma rawar kanta da rashin nutsuwarta yasa suka mayar da ita gashi Sam basa shiri sosai da aleeya kullum cikin fada suke da kokawa da komai sai anrabasu Amma yanxu zuwansu Layla yasa hankalinsu kwanciya matuqa sbd ganin farin ciki a rayuwar 'yarsu su kansu yanxu hankalinsu yaqara kwantawa ganin gidan yasake kammala da yara Dan kuwa dukkaninsu jinsu sukeyi kamar yayan dasuka haifa uwa uba yanda Bilal yasake musu Yana yanda yakeso kamar sune suka haifesa ba ruwansa.

Lokacinda su aleeya zasu rubuta junior waec aka kutsa layla cikinsu ta zana duk da batai wani kyauba Amma ba laifi tasamu 4 credit shima sbd antaimaka matane sosai gurin rubutawar hutun shiga senior class suka fara cikin farin ciki sbd next hutu tare zasu koma and this time around boarding school zasu duk da ammy bataso sune sukeso Abba yace kuma tunda sunaso sai ankaisu.

Kwance suke a 'daki suna kallon hotunan dasukai a wayar ammy Bilal yashigo hannunsa riqeda wayar ammy 'daya Yana game yace,

Ammy tace kubata wayanta.

Ba Wanda ya kallesa cikinsu aleeya tace,

Ka Kai Mata na hannunka wannan muna hotuna ne.

Juyawa yayi da gudu saidai suka jiyo ihunsa da qarfi Yana Kiran Layla.

Azabure suka fito suna kaiwa Palo suka tsaya kallon wadda ke tsaye da babban akwatinta da alama shigowarta kenan sukaci karo tayi wani mugun ball dashi.

Da sauri aleeya ta qarasa ta riqosa daidai fitowar ammy tana cewa,

Lafiya waye ya ta6asa aleeya kune ko....

Ganin siyama tsaye yasa sake fara'a tana cewa,

Siyama kece daga zuwanki Kika ta6amin 'da.

Wani 'dacin baqin ciki ta ha'diye daqyar ta qaqalo murmushi tace,

Wlh karo mukayi bamu luraba.

Nasan arina dama bayason tafiya kullum saidai gudu,
Sannunki da hanya tafiyar bazata Kuma fa ko 'dazu nakira antin mun gaisa Amma Bata fadaminba.

Eh wlh ammy ninace Dan Allah karta fada muku nafiso ku ganni.

To ai kin kyauta saiku wuce ciki ki huta kici abinci.

Dakinsu ta nufa da akwatinta batareda ta kalli ko gefenda Layla takeba sbd zata iya ha'diyar zuciya sbd baqin cikin ganin yanda harta zarta aleeya kyan gani duk da aleeya ma ba bayaba gurin kyau.

Ammy Jan Bilal tayi suka wuce dakinta layla kuwa na ganin haka tayi kicin gurin shafa'atu tana tayata aikin abincin dare.

Aleeya ma kicin din tazo bayan taje sun 'dan ta6a fira da siyamar ta zauna kan freezer tana kallonsu suna aiki sai surutu take musu na wani labari suna dariya hankalinsu kwance.

Da daddare ma kafinsu kwanta Saida siyama taso cin zarafin layla kamar ammy tasani ta Aiko Bilal yakira layla tace tayi kwanciyarta a 'dakinta itakuma ta wuce dakin Abba.

Tunda siyama tazo gidan yazamewa layla wani iri sbd tsangwama duk da alamu dayawa sun nuna su Layla sun fita matsayi agidan yanxu hakan ke qara Mata wata irin tsanar Layla har cikin jininta takejinta duk da layla da ammy sunqi Bata fuskar wulaqantasu laylar duk saitaji zama gidan yafita ranta daqyar tayi sati biyu ta tattara takomawarta gida ta shiryawa uwarta qarya da gaskiya akansu laylar Nan itama umman ta qullaci ammy akan wulaqanta siyamar da'akayi kan sadaka yallah 'yayan tsintuwa.

Siyama na tafiya gidansu yadawo yanda yake hankalinsu Layla ya kwanta gashi lokacin tafiyarsu makaranta yayi tuni akayi musu komai

1 Comments On DAWOOD
avatar
aisha-9-4-5

2 months ago

Reply

I love this book

Please Login or Register in order to submit comment