Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinci mai nauyi.

shiru yayi tareda qurawa ruwan lipton din ido wannan shine karo na farko dabaiyi ordern giyaba tun girmansa,
yau kuwa sam baya shaawar shanta sbd tunda yaga result din dawood yafara shanta yaji ya tsaneta sbd yasan zataiwa amininsa illa dan haka koda zai hanasa shanta saiya fara raba kansa da shanta wannan alqawarine ya dauka bazai qara shantaba insha allah,

kur6a biyu yayiwa lipton din ya ajiye sbd kwata kwata bayada apatite,

wayarsa ya 'daga yakira wanda yakeson gani yace yazo yasamesa a hotel,
cikin qanqanin lokaci wani babban saurayi ya iso yayi knocking room din yabude masa ya shigo,

cikin girmamawa yace,

dr barka da isowa nigeria,

murmushin qarfin hali maskan yasaki tareda cewa,

thank you sambo,aiki zan baka kuma koma meyene inason samun aikina ta kammalu zuwa gobe zan biya ten times na amount din aiki.

washe baki sambo yayi yana kar6ar wayar maskan dayake nuna masa hoton Nur,

bude bluetooth dinsa yayi yatura hoton cikin wayarsa tareda miqawa maska wayarsa yana sake kallon hoton yace,

dr wannan aikin anriga angamasa kafin safe insha allah sbd yau komai dare saina gano komai gameda ita,

daga masa kai kawai yayi tareda miqa masa envelope,

kar6a yayi ya fice yana kiran wanda zaifara tayasa aikin.


washe gari qarfe goma sambo yagama hado masa duk wani tarihi akan nur har asalin inda tayi zaman bara kafin mahaifinta ya rasu da address dinsu na lagos.

lokacinda yakawowa maska bayanin da wasu sabbin hotunanta datake tareda aleeya a instagram,

shiru yayi tareda qurawa hoton ido zuciyarsa cike fal da farin ciki mara misaltuwa sbd yasamowa abokinsa farin cikinsa,

bai tsaya 6ata lokaciba ya harhada ya wuce airport ko takardun bayanan bai kar6a ba ya wuce sbd matsuwar yaje yaga nur da aleeya suyi magana atare,


tunda yakama hanyar airport yake kiransu jass amma babu wanda wayarsa ke shiga,

sukuwa sunacan hankali amatuqar tashe sbd jikin dawood aya rikice musu amai kawai yake shararawa mum tayi kuka har idanuwanta sunfara kumbura amma duk da haka batajin zata bari a 'daga bikin gwara ayi matarsa tayi jinyarsa idanma wata qasar za'a fitar dashi,


ganin yakasa samunsu saiya yanke shawarar kiran numbern nur da sambo yabasa,

qaramin tsaki yasaki lokacinda yaji wayar bata zuwa,
shiru yayi tsawon lokaci kafin ya yanke shawarar kiran numbern aleeya yafara fadamata komai ta waya kafin ya iso,

numbernta da duka cikin binciken sambone aka samo yakira,


zaune take bakin gado ta tallafe kanta dake tsananin ciwo tayi zurfi cikin tunani,

ringing din wayar dake kusada itane yasa tadan juyo ahankali takalli wayar tareda lumshe idanuwanta dasukai jajir ahankali tasake ajiyar zuciya tareda dauke kai sbd hoton dawood ne kwance akan screen din wayar ta aleeya,

sake kira akayi ta miqe da sauri tabar 'dakin batareda tasake kallon wayarba.

tana fita siyama dake toilet na fitowa hararar wayar tayi tareda jan qaramin tsaki tana wucewa,

cak ta tsaya tareda dawowa da sauri ta duba numbern kamar wadda sarah ta turo mata ta tsohon 'dan iskan dakeson yiwa aikinsu shishigi,

wayarta taciro da sauri taduba numbern taga tabbas itace
kiran nasake shigowa ta 'dauka da sauri tareda daidaita muryarta tace,

hello

ajiyar zuciya yasake ahanakali tareda amsa sallamarta cikin qwarin gwiwa yace,

aleeya madibo please?

ahankali itama tace,

yes waye?

khaleefa maska aboki kuma 'dan uwan dr dawood,
inason maganane dake akan keda 'yar uwarki nur sbd samowa kanmu mafita gabaki daya,

wani yawu siyama ta hadiye mai daci na tsanarsa sbd da allah baisa itace tadau wayarba kenan haka zai lalata musu komai,
wlh zaiyayi danasanin wannan karanbanin bashibama duk wanda yayi shishigin ha'da wainnan masoyan saiya biya da abinda yafi qarfinsa,

daidaita muryarta tasake yi cikin sanyi tace,

gskia ayanxu banason muyi wannan maganar agida sbd nur batasan nasan komaiba dama ina neman mafita dan haka yanxu saidai muhadu wani guri muyi magana,

shiru yayi nadan lokaci kafin yace,

ok kibani address na.....

aaa kabani address na inda zan sameka ni zanzo.

ok idan na iso lagos zanmiki sendin room no na hotel dinda na sauka.


kashe wayar tayi tareda sakata silent ta tura cikin jakarta sbd karya turo address din wayar bata hannunta,

shiryawa tayi tafito ta nufi 'dakin ammy ta tarardasu kamar koyaushe cikin kwanakin,

layla da zaune tana gyarawa ammy wardrobe amma sam hankalinta na wani guri,
aleeya kuwa tana qoqarin gusar da damuwartane ta hanyar qoqarin taya bilal wani aikin a laptop amma itama hankalinta na wani gurin ammy kuwa waya takeyi na kayan datayo order na aurensu itamadai daga sautin muryarta kana iya jiyo sanyi da samuwa aciki,

wani irin 6oyayyen murmushin farin ciki tasaki sbd haka takeson ganin rayuwarsu na sauyawa zuwa qunci,damuwa,baqin ciki yazamo ba abunda yarage musu sai kuka,kuka,kuka.

sulalewa tayi ta fice daga gidan da sauri,

tana fita direct wata shegiyar anguwa ta nufa bata fito mota ba takira waya tareda cewa,

seeya ina gurin kasameni,

tana kashewa bada jimawaba saiga wata baqar blackmaria tayi parking gefen taxi dinda take ciki.

fitowa tayi kai tsaye tashige gaban motar sukabar gurin,


qarfe biyar ya sauka a lagos zuciyarsa har wani bugawa takeyi agajiye ya isa wani babban hotel yakama daki yashige,

saidaya fara tura mata text na numbern dakin kafin ya tube yashige toilet yayo wanka tareda yin odar fruitsalad kawai,

tunda yayi sallah bai tashiba yayita kwararo adduoi da istigifar yana nemarwa amininsa sauqi da mafita agurin allah,


knocking akayi ya miqe ahankali ya bude ganin fuskarda baisanibane yasa ya 'dan 6ata fuska yace,

lafiya?

lumshe ido tayi tareda cewa,

masha allah.

ra6asa tayi ahankali tashige dakin tareda zama
afusace ya juyo fuska adaure zauyi magana yaji saukar qarfe atsakiyar kansa ko motsi baiyiba ya zube gurin jini na fita ta hancinsa da kunnensa,


kallon seeya tayi tareda jinjina masa kai kafin suka sawa qofar key tafito da wayarta tadauki hotunansa ta turawa sarah tareda kiranta,

ajiyar zuciya sarah tasauke tace,

yanzu abinda za'ayi zan turo miki dubu dari uku kibawa su seeya da yaransa dubu 'dari da hamsin kiriqe sauran kisiya ticket sbd inason kixo dan yanzu mutuwarsa zata saka sauran maida himmar qarasa abinda yabari,

tsaki siyama taja tace,

wai meyasa bazasu barmu muhuta bane yanzu bayan wannan akwai wasu kuma,,,,koda yake zasu qarasa abinda wannan yabari ne idan basuda masifar kansu,
zamu gayyatowa kowannensu masifar dabazata barsa yatsaya kallon ta waniba...

cikin takaici sarah ta katseta da cewa,

suna tsananin qaunar junansu bazasu ta6a barin junansu dan matsalar gabansuba,,,,,,

dariyar takaici siyama tasaki tana cewa,

banda wannan karon kibari kiga yanda kowannensu saiyayi shawa'awar dama shine ya mutu ba maska ba.


dariyar farin ciki sarah tasaki tana cewa,

seeya ya qarasa maskan and make it look like suicide ma'ana kuyi hanging dinsa abun yayi kamar shiya kashe kansa ne sannan ku rubuwa wasiya as shine yabarta cikin wasiyar kusa ya kashe kansane sbd abokinsa dawood.


su seeya ne suka cicci6esa suka daure wuyansa sukayi hanging dinsa daidai lokacin kiran sufyaan yashigo wayarsa suna kallo suka fice suka barta yanata shure shure yana kallon wayar na ringing wasu zafafan hawayene suka gangaro masa ta gefen idonsa ya rufe ahankali.





*****
shiru sufyaan yayi da wayar ahannunsa yana kallo kafin ya 'dago yakalli jass dake zaune kusada dawood dinda yayi wani irin fari fat kamar baida jini sai bakinsa daya bushe murya asanyaye yace,

bai daukaba,

lumshe idanu dawood yayi cikin ciwo kafin dayar ya iya cewa,

kasake kiransa inason magana dashi,
meyasa zaije adamawa bai jirani natashiba muntafi tare i know he's lonely acan please call him again i want to talk to him.
#mamuhgee
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*26*
NOT EDITED.




Dafasa jass yayi cikin sanyin murya yace,

please dont stress your self dawood may b he is praying or sumthing,he will call back wen he saw the missedcall.

girgixa kai yayi yanajin wani rashin sukuni na damun zuciyarsa.

shiru dukkaninsu sukayi tsawon lokaci kawanne zuciyarsa ba dadi,

har tsakar dare babu wanda ya kwanta cikinsu dawood kuwa saida sufyaan ya hada masa da allura sbd dagewa yayi saiyabi bayan maskan ayau.

restrnt na cikin hotel din dayayi order fruitsalad waiter din yadawo kawo masa chanjinsa yana dora hannu zaiyi knocking yaji qofar ta bude,

wani mahaukacin ihu yasaki yana kiran jesus...

arikice wasu roomservice biyu dasuka kawo suka matso qofar dakin ai nan take hankaki yatashi da gudu dayan yaje yakira manager da sauran securities.

hannu manager ya dora akai cikin tashin hankali nan take takira police.

ahankali suka kwanto gawarsa suka shimfide tsakiyar dakin cikin maikatan wasu harda hawayensu duk da basusan dalilinsa na kashe kansaba.

rufesa sukayi daidai lokacinda wayarsa tasake ringing babban officern yakai hannuwansa dake sanye cikin handgloves ya dauka.

sufyan naji andauka yayi saurin tashi zaune cikin qaguwa yace,

maska mey...shiru yayi tareda kallon gefen da dawood yake kwance cikin baccin dole na allura saidai yana tunanin tashinsa kowane lokaci shiyasa ya kalli gefensa.

ganin yanayinsa yasa jass dake zaune ya quresa da ido tasowa danjin abinda ake fada.

rawa yaga jikin sufyaan nayi sosai jiri na neman dibarsa atsorace yace,

what is it?

hawaye yaga suna gangarowa daga idanuwansa tuni yasake rikicewa atsawace yace,

tell me wat is it.

sunkuyar dakai yayi tareda fashewa da wani irin kuka abunda baita6ayiba arayuwarsa aikawai sai jass din shima ya zube gefensa zaisake magana cikin wata irin murya sufyaan yace,

khaleefa haydar maska is gone,
our friend our brother has left us he is no more,,innalillahi-wainnalayhirrajiun.

kallon sufyaan jass yake ko qyaftawa bayayi idanuwansa da hancinsa tuni sukai wani ja sosai jikinsa ke wata irin rawa har sufyaan baisan sanda ya rungunesa da sauriba wani sabon kuka na zuwar masa.

kamar daga sama sukaji andafasu sufyaan ne kawai ya dago yana ganin dawood yayi saurin miqewa tsaye yana kollonsa cikeda fargabar halinda zai shiga ciki idan yaji rasuwar maska.

wani ja idanuwansa sukayi bakinsa ya qara bushewa yaji komai saidai jin zuciyarsa yake ta bushe masa kamar dutse babu abunda yakeson gani kawai yanxu banda maska.

daqyar ya bude bakinsa dayayi mugun bushewa yace,

muje maska na buqatarmu yanxu.

sai alokacin kuka mara sauti yazowa jass ya dago yakalli dawood yaga yanda idanuwansa sukayi da yanda jikinsa ke rawa yasan tabbas zaifisu shiga wani halin rashin maska.

sufyaan ne yayi qarfin halin sanarda taheer yakaisu airport,
suna isa cikin saa suka samu ticket na jirginda zai tashi zuwa lagos alokacin,

harsuka sauka lagos babu mai iya magana acikinsu kowanne idanuwansa jajir abunka da dukkaninsamu farare.

wayar maska sufyaan yasake kura sukaji sunan hotel din sbd ba'a dauke gawarsaba su ake jira.

tunda suka isa harabar hotel dun jikin dawood ya tsananta rawa sufyaan yayi saurin riqesa.

ALLAHU AKBAR,,shine abinda sufyaan ya furta da wata irin wahalalliyar murya lokacinda yabude gawar maska yatabbarda shi 'dinne ya rasu.

kuka sosai jass yakeyi musammam da aka sanardasu shine ya rataye kansa da kansa.

wani irin murmushi dawood yasaki yana kallon gawar yace,

nasanshi tun tasowana bazai ta6a kashe kansa da kansaba.

matsowa officern yayi ya dafasa cikin jimami yace,

a iya 'dan bincikenmu dole zamuce shine ya kashe kansa.


kai tsaye bayan rubuce rubuce aka basu gawar suka wuce kaduna.

koda mamynsa tayi ido biyu da gawar 'danta yanke jiki tayi ta fadi saida aka hada da dr ta farfado gari naqarasa washewa tuni gidan yafara cika da dangin daddynsa sbd mahaifunsa tuni ya rasu.

wani irin yaji da zafi idanuwan dawood keyi sbd tsananin tashin hankali gashi kukanma yaqi zuwa sai rarraba jajayen iduwansa yake akan gawar yaqi masa ko ina yana kusada gawar jiyake kamar maskan zai tashi sukoma rayuwarsu tada mai cikeda farin ciki jin dadi da qaunar juna.


lokacinda aka gama yiwa gawar komai za'a tafi da ita sai alokacin wani irin kuka nai ciwo yazo masa ya sunkuyar dakai yanayi nan jikin duk wanda ke gurin yaqara sanyi musamman dangin dadynsa dasukafi kowa sanin kirki da kyawawan halayensa sbd shine dauke da nauyin karatun 'yayayensu.

dad dinsa da taheer dasuka biyo jirgi da safe sukazo jana'izar suma sun tausayawa dawood dasu jass matuqa sbd ganin halinda suka shiga na rashin amininsu rabin jikinsu.

kuka dawood yayi sosai harsukaje suka dawo nanma hankalinsu yaqara tashi sbd ganin sunrabufa kenan har abada sun rabu kenan da maska musamman ma jass dayaga yanda ake rufe gawa nan take wani irin tsoro da imani yashigesa sbd yasan wata rana zasubi maska da guda guda suna fitowa maqabarta ya kar6i musulunci yana wani irin kuka a hannun limamin dayayi sallar batareda ma su sufyaan sun saniba sbd shikadai yasan ciwon dayakeji na rashin sanin adduar dazaiyiwa maska kamar yanda yaga su sufyaan sun masa.

suna dawowa dakinsa suka shige sunyi kuka har babu wanda zai iya bawa wani hkr acikinsu musamman ma dawood dake ganin duk akansa komai ke faruwa,
meyasa tun farko yafada soyayya,
meyasa Nur ta 6ace masa har rayuwarsa ta lalace harma data waindake taredashi,
kallonsu sufyaan yayi da jajayen idanuwansa yaga yanda sukai wani kalar tausayi bayason yarasasu ko wani abu suma ya samesu dan haka zaiyi nesa dasu sukoma suci gaba da aikinsu su fuskanci sabuwar rayuwa bayason rayuwarsu ta lalace kamar tashi sbd ya rasa NUR,yarasa MASKA, yarasa SOYAYYAR MUM dinsa sbd baya tunanin akwai so yanxu atsakaninta dashi,ya rasa FARIN CIKI, yama rasa komai tunda ya rasa maska da nur.


bayan angama zaman gaisuwa anwatse saida suka qara kusan sati 'daya suna qara kwantarwa da mammyn maska hankali,

ranar dazasu tafi riqe dawood tayi tanata wani irin kuka,
kasa riqe nasa kukan yayi saida sukayi mai isarsu kafin daqyar suka tafi bayan dawood yakira taheer anema masa babban gida a abuja zasudawo da mammyn kusadasu a abuja zasu siye mata sbd shine111 babban abinda zasuyiwa maska bayan ransa.


ranar dasuka dawo gidan kamar gidan zaman gaisuwa sbd ko abincin kirki cikinsu bamai iya ci mum ce keta yawo ranason taga kowa yasake sbd bikin nan batason ace za'a dagasa,


tunda dawood yadawo yarasa sukuni zuci sbd yakasa kankarewa zuciyarsa duk shine sanadi har lokacin jin rasuwar maska yake sabuwa gashi jass ma lafiya na neman gagararsa sbd rashin sabo da wahala gashi mum 'dinsa takirasa akan dad dinsa kwanakin zuciyarsa na tsufa na yawan tashi.


hakanan su dawood suka fara shirin tafiya sidney gurin dubo yanayin jikin dad din jass saidai jass din yace su bari saisun gama settlin komai na dawo da mammyn maska abuja tukuna saisu samesa daga baya.



ana gobe zai tafi saraah tabugawa siyama waya tace duk yanda za'ayi ko nawane zata kashe asamo mata abunda takeso sotake idan jass yasa qafa yatafi har abada bazai iya dawowaba ko yaso dawowar,


gyara tsayuwa siyama tayi daga cikin toilet din datake wayar tace,

me kike ganin zai hanasa dawowa ga aminansa biyu dasuka rage masa?


murmushin mugunta tasaki tace,

bazai iya dawowaba koyaso sbd abunda na shirya masa ko airport din qasar bazai bariba za'a wuce dashi prison daurin rai da rai idanma ba'a kashesaba kenan,
kedai kibawa seeya dubu dari biyu komai dare komai asubanci akawomin abunda nace.

dariya siyama tayi tace,

wlh koda masifa kuwa sai saqonnan ya iso hannunki.
dariya sukayi suna qarasa qulla muguwar aniyarsu kafin suka kashe ta fito toilet bayan tayi waya sa seeya har tayi masa transfer kudinda saraah ta turo mata.


kallon nur dake kwance aleeya na miqa mata tea tayi awuqance sbd ganin kullum taqi lafiya sai wahalarda mutane take munafuka bikine dai baza'a dagaba sai anyi sbd abba yace gwara dai ayi kowacce taje mijinta yayi jinyarta.



har airport suka kaisa kallon sufyaan jass yayi da idanuwansa dasuka jeme fuskarsa jajir ahankali yace,

take gud care of him.

rungumesa sufyaan yayi jiki amace yace,

take care please.

daga masa kai yayi tareda sakinsa ya rungume dawood da tuni idanuwansa suka canza murya a matuqar mace yace,

we'll be there soon insha allah,take care please.

daga masa kai yayi yana share fuskarsa da handkchf sbd hawayen dakeson xubo masa yace,

see you guys soon.

juyawa yayi ya wuce sbd tuni aka kira flight dinsu.


suna tsaye har ya shige suka sauke ajiyar xuciya ahankali tareda juyowa suka kalli juna suka wuce kowanne zuciyarsa ba dadi musammqn ma dawood da ciwo ke cinsa daurewa kawai yake.

shiru yayi tareda rufe idanuwa kewa da tsananin son ganin Nur dinsa na qarawa zuciyarsa nauyi da wani irin ciwo.
#mamuhgee



karku zamto masu yanke tsammani akoda yaushe ku ringa bari kuga shin wane irin darisine wannan yake dauke dashi musamman ma irin wannan daya tara kusan abubuwa da dama.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*27*
NOT EDITED




Suna isa gida suka zauna shiru sarah tazo tayita surutanta babu wanda ya iya ko kallon gefenta qarshe miqewa tayi ta fice tana ta6e baki aranta tace,

duk zaku raina kankune lokacinda kaima sufyaan plan dina yagama kammaluwa akanka ka shiga naka gararin kaikuma dawood kazo tafin hannuna.

washe gari shiru shiru basuji kiran jass ba gashi basa samunsa tuni hankalin sufyaan yatashi yayita qoqarin 6oyewa dawood sbd ganin yanayin jikinsa daya qara dawowa.

dawood din dakansa yakar6a wayar yayita kira baa samu daqyar sukaga maraice yasake yi nan dawood ya danna kiran num din mrs smoake mum din jass din.

kiran farko ta 'dauka saikawai ta fashe masa da kuka.

tashi zaune yayi daqyar yana qoqarin tambayarta.

kasa magana tayi saima kashe wayar datayi.

cikin tashin hankali sabo yasa taheer yimusu cuku cuku suka bi jirgin asuba suka tafi batareda ko mum tasaniba dad kawai sai taheer ne sukasan halinda ake ciki.

sai dare suka sauka kai tsaye gidansu jass din suka nufa anan suka tararda tashin hankalinda yasa dawood kusan sumewa sbd saida aka zaunar dashi sufyaan kuwa kuka yake resas lokacinda mrs smoake tasanar dasu ankama jass tun a airport sbd miyagun qwayoyin daaka samu ajakarsa tun jiyan aka wuce prison dashi lokacinda aka sanar dasu atake hrt attck yakama dad dinsa ya rasu.

prison din suka wuce daqyar dasaka hannun wani abokin dadyn dawood aka bari suka gansa kallo daya sukaiwa junansu suka fashe da kuka kamar yara qanana sbd wasu irin chains ne aqafafu da hannuwan jass din kammaninsa tuni suka sauya sbd azabar da aka kwana ana gana masa,

kuka sukeyi sosai kafin suka sanar dashi rasuwar dad dinsa,

cikin kwana biyu suka kashe kusan fiyeda rabin dukiyoyinsu gurin ganin sun fitarda 'dan uwansu amma tuni aka hanasu ko ganinsa ga mum dinsa tasa abin aranta sosai nan hankalinsu yatashi sunyi kuka baida iyaka kowannensu tuni yakoma sai dogon wuya da dogon hanci.

ahaka suka dauko mrs smk suka dawo da ita new jersey tareda siya mata dan madaidacin gida tareda tattaro dukiyar dadyn jass data jass din suka damqa mata danta kulada ita bayan sun samar mata mataimaki mai qwazo da amana.

koda suka dawo nigeria tuni aka rasa mai tallafar wani tsakanin dawood da sufyaan idan suka fita tun safe suna bar suna shan mai qarfi sai dare suke dawowa duk lokacinda abar tasakesu kuka sukeyi sosai suna istigfar,

ana saura sati biyu bikin ranar dawood ko mai yakasa sawa cikinsa sbd komai yasa sai yayi amai nantake ciwo yayi masa mugun kamu sbd tuni giyar tafara yimasa mummunar illa,

aranar yafara wani irin aman jini sufyaan yayi kuka har numfashinsa baya iya fita gashi dawood yasakasa yayi masa alqawarin bazai ta6a fadawa kowa bayada lafiya,

idan mum ko dad da taheer sun shigo daurewa yakeyi ya zaune csuna fita zai fara amai ko wani abun,

zaune sufyaan din yake gaban gadonda dawood din ke kwance cikin qarfin hali yana masa firar rayuwarsu ta da dasuke su hu'du cikin farin ciki,

hawaye sufyaan yake yana girgiza masa kai sbd bayason firar sbd jinta yake kamar wasiyace dawoid din ke basa,

miqewa yayi da sauri ya zari mukullai ya fice,

yana fitowa daga harabar gidan yaci karo da saraah data dawo daga airport dauko siyama ya wuce da mugun speed,

juyarda kan motar tayi tabi bayansa siyama tace,

ina kuma zamu?

binsa zanyi dama ina neman damar zamunsa shika'dai.

binsa sukayi bayan tayiwa su seeya dake gari tun satin daya gabata waya.

yana gaf da isa bar din wata black jeeb tasha gabansa

burki yaja da sauri tareda qoqarin fara ribas motar sarah ta taresa ta baya.

kallon anguwar yayi yaga tsit gashi dare ne fitowa yayi sbd sarai yagane sarah ce amotar bayansa yana fitowa suma suka fito tsayawa tayi gabansa tana watsa masa kallon banza tace,

poor dr sufyaan,
kaine mai binkicen mutuwar maska da abunda yasamu jass ko?
to bari na sauqaqa maka wahalarka abinda kuke gani SAKAMAKO(SURAYYAHMS?^_-)ne na abinda kukai min,
and there is more to come
saidai im really sorry to say bakanan bare kagani,
yarinyarda kuke ta fafutukar nemewa abokinku bazaku ta6a samuntaba duk da gatanan itace wadda qanin dawood din zai aura dan haka yanzu abinda nakeso dakai shine kafadamin wayene kuke binciken mutuwar maska da jass tare?

fadamin sbd nasan kaida wanine fadaminshi and nikuma zan saka yarana suyi maka sauqi sbd......

wani gigitaccen marin dayasata zubewa qasa baki na jini yasakar mata cikin tsananin takaici da danasanin neman mata sbd da ace yau basuyi neman mataba dabazasu hadu da wannan masifarba ta haduwa da saraah arayuwarsu.,
tabbas yanzu yagane neman mata na daya daga cikin sanadin shigarsu wannan balain dakum.......

saukar wani hakaukacin dukan qarfe yaji atsakiyar kansa nan take ya zube agurin yana shure shure,

daukarsa su seeya sukai suka saka mota suka tafi tareda motar sufyaan din,

tafiya mai nisa sukayi ta daji saida suka kai wani daji mai ruwa suka jefasa ciki tareda motarsa suka tafiyarsa batareda sun tsaya tabbatarwa koya mutuba sundaisan yama mutu dan bazai iya daukar wannan dukanba.

shiru shiru ba sufyaan nan dawood yalalla6a yatashi yakira taheer yafita dashi,

duk inda yakesa ran ganin sufyaan yaje baigansa ba har gidan mammyn maska yaje duk wata bar dasuke zuwa sunje nan hankalin dawood yatashi aahankali yace,

shima yatafi inaji ajikina sufyaan ma yatafi yabarni,

ganin halinda yashiga yasa taheer dawo dashi gida shikuma yakoma yakai report dukkanin polince stations,

cikin kwana biyu tuni dawood yakoma wani iri zuwa lokacin tuni kowa yasan yafara shan alcohol sbd idan yasha yanzu tana bugar dashi sosai haka zaizo yayita zagin mum baruwansa da baqinta
tun tana 6oye 6oyen abun tuni hankalinta yafara tashi tayi kuka babu adadi gashi tuni gidanta yafara cika da yan biki ammq haka zaita abubuwansa idan yayita amai yawuce daki ya kwanta.
duk wani kwanciyar hankali da farin ciki tuni ya qauracewa gidan nan hankalin dadynsa yatashi yafara binciken abinda yasamu rayuwar dansa ya lalace,

tunda mum taji dad zaiyi bincike hankakinta ya qara tashi tayi kuka ba adadi tasamu sarah ta sanar da ita akan tana roqonta data tafi har hankali ya kwanata.

sarah na sanarda siyama akan sudau mataki akan dad sbd har abada bazai ta6a bari ta auri dansaba harararta siyama tayi tace,

idan kika kashesa kina tunanin za'ai wannan auren ne yanzu?
dagasa zaayi gwara kibari bayan auren masan abinyi dashi dan wlh yana gano komai kashemu zaai dan wlh ko hukuma bata kashemuba sai dawood yayimana kisan wulaqanci.

wani yawu saraah ta hadiye sbd sam ita ko maganar mutuwa bataso tsoronta take saidai abu daya data sani duk wanda yadauki hanyar bankado asirinsu kashesa zasuyi dan wlh bazata yarda akashetaba.



*******
yau akesa lalle tunda akai aka gama babu mai doguwar walwala acikinsu sai yaqe sukeyi siyama data dawo yau sai murna da farin ciki takeyi sbd ganin ko ahaka ta tarwatsa farin ciki da kwanciyar hankalinsu saidai qasan zuciyarta wani zafi da quna takeyi na kishin taheer dan yanda takejin sonsa da qaunarsa ko layla zata iya kawarwa dan tasamesa.

tunda aka fara bikin take fama da ciwon qirji sosai saidai tana dannewa kar hankalin aleeya yatashi saidai abin yafara bata tsoro sbd har jini jini take gani idan tayi tari,Nana ce kawai tasani take dan kulawa da ita duk da hankalin nanar yatashi sosai da ganin hakan amma ta hanata fada,

duk wani buri da shirin dasukaiwa aurensu bai yiyuba sbd babu wadda zatai kyawun gani musammman ma layla da tuni tafara fita kamannninta sbd rama,

ammy ma batai wani gayyataba hakanan aka lalla6a aka daura auren aranar layla tayi kukan daya haddasa mata ciwon mai tsanani,

tunda bilal yace mata andaura aurenta da taheer,dawood da aleeya ta sulale tashige dakin nana,

rungumeta nana tayi da qarfi ta qanqameta sbd ganin wani irin kuka datake mai cin zuciya jikinta na tsananin rawa,

ita kanta nanar kuka takeyi sosai na rausayin layla kamar ranta zai fita,

ammy tunda akace angamo daurin aure take neman layla sbd tasan yau tanacikin wani mummunan hali,

dakin nana ta nufa tana ganinsu ahaka idanuwanta suka cika taf da hawaye bayasan lokacinda ta qarasoba ta janyo laylar ta rungume hawayenta na tsiyayowa.

kamar daga sama aleeya tashigo dakin nemansu tana ganin halinda auke ciki jikinta ya qara sanyi ahankali ta qaraso tq zauna kusada ammy tareda kiran sunan layla ahankali,

kasa dagowa layla tayi saima wqni sabon kukanne yazo mata mai ratsa zuciya ta juyo suka rungume juna tuni itama aleeyar ta fashe da kuka,

kuka suke sosai kowanne da abinda yake tunawa cikin ransa ammy ma saidata yi kukan daqyar nana ta lallashesu tana sakin ajiyar zuciya ganin sunqi yin shiru yasa takira bilal yana shigowa jikinsa yayi mugun sanyi ahankali ya qaraso ya durqusa tareda jawosu gabaki daya ya rungume yana mayarda hawayenda suka ciko idanuwansa,

koda aka tashi tafiya da amaren qarfe uku na rana abba koda yayi musu nasiha layla bata hayyacinta hakanan dia aka lalla6a suka wuce airport sukabar ammy cikin mummunar damuwa da kuka.
#mamuhgee



idan kunyi hkr zakuga inda zamukai komai na duniya bamai tabbatuwa

1 Comments On DAWOOD
avatar
aisha-9-4-5

2 months ago

Reply

I love this book

Please Login or Register in order to submit comment