Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

azaba tareda 6oye tissuen kar mum ko su jass sugani,

hankalinsu baqaramin tashi yayiba ranarda yaringa kwararo aman jini nan suka kwashesa sukai asibitinsu,
lokacinda sukaga result din bincikensu akansa kuka sosai jass yazauna yanayi sufyaan na qoqarin danne nasa gurin lallashinsa sbd sun sadaqar da shima rasashi zasuyi kamar yanda suka rasa maska tabbas dasun tabbata marayu idan babu maska babu dawood.


tsawon wata hudu da dawowarsu babu siyama babu dalilinta ga ummanta ta daga musu hankali da koke koken nemanta nan hankalin ammy yasake tashi ga abba sosai hankalinsa ke tashe gurin ganin ansamo inda layla take kusan shekara kenan babu labari,

tareda abba ayau suka sauka porthrct direct headquatr suka nufa gurin jin bayaninda akakirashi akansa cewar antsinci gawar wata mata da jariri sabo.

wata mummunar sarawa kan aleeya yayi tayi saurin jada baya tana qoqarin zubewa daidai kawowarsa shima ya iso hankali tashe jin kiranda akai musu kan case din nur.

fado masa tayi idanuwanta na qoqarin rufewa jikinta nason saki,

riqeta yayi dakyau tareda cewa abasa ruwa masu dan sanyi,

miqo masa abba yayi jikinsa na rawa,

kadan ya zuba mata amma ko alamar motsi babu atareda ita nan abba ya rude suka kwasa asibiti hankali tashe,

bayansu yabi da kallo ahankali tareda kallon qaramin gyalan doguwar rigar dake jikinta da akabari ajikinsa,

nauyi yaji azuciyarsa akaro na farko daya ta6ajin hakan ya dafa zuciyarsa ahankali tareda qurawa gyalen ido yana sauraron abinda ake fada masa kan gawar daaka tsinta,

shiro yayi cikin tsananin tashin hankali yafito yanufi gida yana tsoron fadar zancen kar dawood yaji gashi tun jiya yana asibiti jikin yatashi sosai cikin dare,
yana isa asibiti kallon sufyaan dake daurawa dawood jini yayi ya girgiza kai idanuwansa na cikowa da hawaye.

lokacinda ta farfado kuka takesonyi amma yaqi zuwa tsabar tashin hankali da firgicin datake ciki.
zaidai jajir da idanuwanta sukai lokacinda abba zaije dubo gawar saidai yakaita gurin mum dan harlokacin bata dawo daidaiba,

kallo daya sukaiwa juna itada mum suka tausayawa kansu nana datuni aka barwa mum ita ita tayita fama dasu ko ruwa daqyar sukesha har abba yakira yasanardasu ba gawar nu bace,

washe gari aka dawo da dawood gida ana shigowa dashi palon idanuwanta acikin na jass suka fara sauka kusan atare suka dauke fuska kowanne babu walwala,
shikuwa dawood baisan wayene akansaba harlokacin,

ganin halinda yake ciki yasake girgixa kwanyarta tayi kuka adaren da ita da mum ba'asan mai rarrashin waniba bare da tsakiyar dare abin yataso yayita aman jini tuni suka fitarda rai akansa banda kukansu su duka nabu abinda kd tashi,

sannu ahankali yafara gane wainda ke kansa nan aleeya tayi masa alqawarin nemo masa nur da kanta takawo masa da wannan alqawarin suka dan fara sabawa itace ke kulada cinsa da maganinsa,

ahaka harsuka sake shekara babu nur duk wata rayuwarta ayanxu ta tattarane gurin kula dashi,
bata iya barci kullum kwana take azaune,
mum ma ahankali tafara ciwo nan abubuwa suka taru sukai mata yawa musamman yanxu da ciwon dawood yake sake gangarawa dan yanxu kam yafi wata akwance ko motsi bayayi tun ranarda ya kwana yana aman jini,

kallonta ammy tayi cikin hawaye tana cewa,

aleeya mukoma gida kiyi jinya wlh kema bakida lafiya ji yanda kika kashe rayuwarki gurin jinya.

share hawayenta tayi da dogayen yatsunta dasuka rame murya a sanyaye tace,

ko ayanxu na mutu nasan wannan danakeyi shi ake kira sadaukarwa babu cutatarwa babu 6oyo da zuciya daya nakeyi kuma wlh komai danakeyi inayine damin layla bazan ta6a bari abinda takeso ya wulaqantaba,
ni layla da dawood sune tawa qaddarar.


shuru ammy tayi tana fidda qaramin sautin kuka ahankali sbd gabaki daya aleeyar ta canxa tamafi wanda ke jinyar lalacewa sbd abin ita a zuciyarta yake cinta.
wannan wace irin soyayyace allah ya jarabci aleeyar da ita akan dawood da layla.

kuka sosai ammy tayi na tausayin yarta haka takoma sbd aleeyar taqi yarda tabita,

bayan tafiyar ammy mum tayi sabon kuka dan tabbas gskia ta fada aleeyar na buqatar kulawa fiyeda ita sbd ita kanta tana hango qunci da tsananin ciwon zuci da aleeyar ke fama dashi.

aranar da suka dawo gida da dawood tazauna takallesa taga yanda ciwo yamayar dashi sai aranar tasamu kuka yazo mata tun bayan tsawon lokaci,

bude idanuwansa yayi daqyar tareda lumshesu cikin azabar ciwo yace,

thank you aleeya.

giegiza masa kai tayi cikin tsananin kuka ko mgn bata iyayi,

sake bude baki yayi daqyar yace,

duk ranarda kikaga nur da abinda ta haifa nabaki amanarsu and pls forgive me aleeyaaa'''''ya qarasa fada cikin wata irin azaba tareda fara tari

tsananta kukanta yayi kamar zata shide,

mum ce tashigo ta tarardasu ahaka arikice ta qaraso ganin jini fiyeda na kullum salati tasaki mai qarfi jikinta na rawa nan aleeya ta dago tana ganinsa tafuta cikin tsananin firgici daidai isowarsu sufyaan da kwalayen drip drip suna ganin yanda yaks suka watsarda komai aka kwashesa suka koma asibiti cikin sabon tashin hankali.



****
DAWOWA LBR

zama taji anyi kusada ita shiyasata dauke jajaye idonta dagakan sunan asibitin ta sunkuyar dakai qasa,

anty aleeya'''''taji ankira sunanta murya na rawa,

kobata dagoba tasan muryar bilal ne sai kawai ta share hawayen dasuka sauko mata ta dago ahankali,

taheer tagani tsaye bayan bilal yana kallonta cikin tsananin tausayawa sbd tabbas ta jarabtu,

kama hannunta bilal yayi yana kallon tsakiyar red swollen eyes dinta yasaka mata takarda cikin hannunta yace,

anty aleeya hawaye da damuwar danake gani cikin idanuwanki har abada bazasu barni na zauna cikin sukuniba,
layla da dawood ne farin cikinki tuntuni nayi alqawarin dawo miki da farin cikinki,
ban nemo laylaba sbd tana yar uwata na nemotane sbd ke.

kallonsa tayi da sauri idanuwanta na cikowa yace,

layla itace warakar dawood insha allah ke kuma warakarsa da ganinta itace taki ina fatan komai yazo qarshe.

kallon takardar tayi hawayenta na saukowa kafin tadago tasake kallon bilal din da sauri ta fada jikinsa tareda sakin wani irin kuka.

saidatayi kamar bazata bariba kafin ya miqar da ita tashiga dakin dawood taquara masa zuciyarta na karaya tsawon lokaci ta sake kallon takardar hannunta ta juya ahankali ta fuce tareda sake waiwayarsa.

tan fitowa sukaci karo da jass zaishigo kallon juna sukayi kowanne ya wuce,

kallonta taheer yayi yace,

muje nizan kaiki lets finish this today insha allah.

gyada masa kai tayi hawaye na gangaro mata suka wuce kosu mum basu saniba.
#mamuhgee


vote and follow.
_*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*_This page is for you AUFANA thank you for the love,love you too_*💋




*39*
not edited.




bilal ne riqeda hannunta har cikin motar taheer suka zauna baya still hannunta na riqeda nasa sosai takejin rashin sukuni a zuciyarta,
lumshe jajayen idanuwanta tayi tabude cikeda abubuwa da yawa ciki hardajin zafin yanda koyaushe layla tafi shaawar barinsu batareda taqara laakari da halinda zasu shigaba shin meyasa kullum kukanta da damuwarta akan layla ne,
ada kam fushi tayi sbd abinda sukayi amma ayanxu ne zata dauki matakin gaske matuqar ta tararda laylan da gangan tabarsu cikin wannan baqar wahalar ciwuka sunqi ci sunqi cinyewa ayanxu kam tagaji itama tana buqatar kulawa da tata rayuwar iya so da qauna ta nuna saidai tagaji dayi abanxa ana tsallaketa ana guduwa she needs to accept the fact hakanan.


airport taga sun nufa takalli bilal daya hana tasa rayuwar sukuni sbd su,
tabbas tasan yana tsananin kewar yar uwarsa saidai yana qoqarin dannewane yanuna mata kulawarsa dan kusan duk sati saiyazo prthct dubata shi sam baya son dawood arayuwarsa sbd shine silar komai daya samesu yake gani.


jirgi suka shiga itada bilal din da taheer kowannensu shiru da abinda yake saqawa shi kansa taheer zuciyarsa bugawa takeyi da qarfi ta yanda zai kalli macen dayafi komai so amatsayin matar dan uwansa harda qaruwa tabbas bazai ta6a iya qara zama akusadasuba zaicigaba da rayuwarsa acan inda yafara ayanxu.


bilal kuwa zurfi yayi cikin tunanin yanda sukasha baqar wuya shida taheer kafin suka samu inda take,

lokacinda suka fara nemanta a porthrct basu samuba duk iya kashe kudi da bincike taheer da dad sunyi amma babu alamarta nan taheer ya yanke shawarar mayarda binciken abuja,

canma tsawon lokaci babu wani alamar zaaganta anan nan ya yanke shawarar komawa lagos,
komawarsa lagos yasa dole ya nemi bilal sbd jin ko akwai guraren dayake tunanin zata iya zuwa maana acan rayuwarsu ta baya nandai suka fara bincike a 6oye shida bilal din da bincike da dubara har qauyensu baffa dahiru sukaje amma babuta nan shima baffan hankalinsa yatashi sosai musamman dayaji kusan tsawon shekara da 6acewarta.

shiru yayi cikin nazari kafin ya dago yace,

suje har adamawa inda komai yasamo asali sugani.

aranar suka koma abuja washe gari suka sauka adamawa,

lokacinda suka fara bincike daqyar bilal yagano unguwar dasukai rayuwarsu tada sbd canje canje da gyara da gurare suka samu,

saida suka share sati biyu babu wani cigaba suka tattara suka koma aranar dazasu koma a airport yahadu da wata matashiyar mace da yaranta biyu duka maza,

gudu sukeyi sukayo gurinsa suka boye mamar tabiyosu cikin fada tana cewa,

kuxo muje mana kokuwa so kuke sai ALEEYA tayita jiranku harta gaji.

da sauri suka fito sukayo gurinta kowannensu na cewa,

ummy nine anty zata bawa aleeya idan na girma.

dariya tayi tareda dagowa ta kalli bilal din dake kallonsu tace,

sorry sunxo sun damuqeka...

no its ok yarane ai koba komai naji sunada yar uwa mai sunan tawa yar uwar danake jida ita.

kallonsa tayi tasake kallonsa zuciyarta nadan rawa sbd kamar dayake mata da fuskar sani duk da dai ya girma sosai yazama saurayi amma kamannin still sunanan,,,bilal ta furta ahankali ga mamakinta saitaga ya juyo yace,

kinkirani ne?

baki ta rufe cikin tsananin mamaki da farin ciki tace,

bilal din laylah?

dawowa yayi da sauri shida taheer harsuna hada baki gurin cewa eh shine.

murmushin farin ciki tasaki tace,

bilal kaine ashe kaima zanganka raheenatu ce damukai zama tare tun baabanku nada rai katuna kuwa?

tabbas ya tuna da ita sbd itakadaice mai nuna musu qauna da kulawa tun wancan lokacin qawar layla ce jiyayi jikinsa yayi sanyi sbd ya dauka watace daban tasan inda laylan take,

sakin murmushin yaqe yayi cikin qarfin hali yace,

allah sarki nakuwa tuna duk da kamannin sun canza.

dariya tayi tace,

gaskia ne kam saidai ina kuka shiga tsawon lokaci haka.

shafa fuskarsa yayi cikin yanayi na damuwa yace,

abubuwa da dama sunfaru babban ciki shine nur muke nema yanxu tsawon lokaci mai tsayi anata nema amma haryanxu shiru bamuda tabbacin tana raye ko tana....

katsesa tayi da cewa,

nur nanan raye saidai.....

ganin irin zaburowar da su biyun sukayo yasata saurin rufe bakinta tareda rintse ido cikin jin zafin subutar bakinda tayi saidai ita kanta dama tanason sanin inda su bilal da aleeyar suke sbd kawo qarshen komai tun kafin aleeya tafara tambayarsu ina daddynta dan ana gaf da fara hakan.

juyawa tayi da sauri zatabar gurin sukasha gabanta atare bilal baisan lokacinda ya zube qasaba cikin sanyin murya yace,

dan allah ki taimaka rayuwar mutane da dama na cikin wani hali sbd ita ka sanardamu inda take idan kinsani..

kallonsu tayi cikin yanayi na tausayawa tace,

kubani numbernku zan kiraku na sanardaku idan na isa gida kuje kurage damuwa layla na taredani tun ranarda tabaro gida aranar muka hadu.

jiki na rawa suka rubuta mata numbibinsu sbd dagewar datayi bazata iyayi musu komaiba ayanxu.

da wannan suka fasa tafuya suna zaman jiran kiranta shiru shiru babu bayani suka tattaro suka dawo aranarda suka sauka lagos aranar tayo musu txt na address din gidanta dake adamawa kuma aranar sukayo porthcrt suka damqawa aleeya address din.

juyowa yayi ya kalleta lokacinda jirginsu ya sauka yaga har lokacin idanuwanta na rufe.

saukowa sukayi babu 6ata lokaci suka dauki drop zuwa address din.


kallon tangamemiyar gate din gidan tayi taja numfashinta dake fita da sauri ahankali tanajin wani irin qarfi da jarumta azuciyarta duk da sosai takejin nauyi aciki,

mai gadi bai hanasu shigaba sbd madam dinsa ta sanardashi zuwansu suka shigo kowanne da kalar bugunda zuciyarsa keyi,

suna gaf da shiga palon taji ankira sunanta,,

ALEEYAH..

cak ta tsaya tareda jan numfashi kafin ta juyowa ahanki bugun zuciyarta na tsanan,

yarinyace fara sosai kyakkyawa dabata baro ko yatsa daya na mahaifintaba da kakarta dan har jajayen lips dinsa saidata dauko da kalar tafiyarsa cikin sanyi,
sanye takeda riga da wando red an gyara mata gashinta andaure,

qurawa yarinyar ido tayi jin yaron yasake kiranta da aleeyah.

rufe bakinta tayi da duka hannayenta biyu sbd kukan dakeson zuwar mata zuciyarta na karyewa,
basai anfada mataba tasan wannan itace 'yar dawood da layla kuma sunanta laylanta tasawa yarinyar batasan lokacinda hawayenta suka saukoba lokaci daya taji quncinta yafara gushewa ganin yarinyar sbd mutanen datafi sone suka sameta,

dafata raheenatu data fito tayi tana kallon little aleeyah tace,

aleeyah zoga mummy aleeyaan ummynki.

juyowa yarinyar tayi suna hada ido da aleeya tazo da gudu ta fada jikin aleeya cikin wani irin shauqi aleeya ta rungumeta sabbin hawaye na gangaro mata,

bilal da taheer ma daurewa kawai sukai basuyi hawaye ba daqyar suka qarasa palon little aleeya na damqe ahannun aleeya sbd kobada laylaba yanxukam tasan little zata kawo sauqi arayuwarsu insha allah,


zama sukayi aka kawo musu ruwa amma babu wanda keda nutsuwar kallon ruwan amatse suke dasuji inda layla take,

cikin sanyin murya tace,

mijina ya rasu yabarni da yarana biyu a porthct daga baya na shirya tareda tattara duk wata dukiyar damuka gada nida yayana nayi shirin dawowa gida adamawa
aranarda layla tabar gida aranar cikin qaddarawar allah nice na bugeta da mota a porthct kuma bugu sosai dan kuwa qaddarawa da ikon allah kawai yasa cikin dake jikinta ya tsaya bayan doguwar wahalar jinyar datasha kafin daga baya muka dawo adamawa tare muka cigaba da jinya tsaqon lokaci harta haihu,
haihuwarma tazo da babbar matsala saida muka koma jinyar uwa da jaririyar bayan haihuwa kafin daga baya komai ya daidaita ga jaririyar inda da kanta ta6arwa yarta sunan aleeyah saidai haryanzu ita babu wani sauqi sai agurin allah,

layla tafada mini komai sbd acewarta duk ranarda ta rasu nakai little aleeya gareki aleeya sbd tanasakaran bazata sake ganinkuba arayuwarta,

tuntuni naso mu nemoku sbd halinda take ciki amma tasani alqawarin rshin yin hakan saidai kullum da fargaba nake kwana da ita nake tashi sbd gudun karta rasa ranta ahaka cikin damuwa da qunci shin mezai hana ataru anemi mafita wa wannan alamari sbd sam wannan bashine hanya mai 6ullewa ba,

little aleeyah ta taso da tsananin qaunarson ganinki aleeya sbd mahaifiyarta data cusa mata qaunarki mai tsanani aranta ta hanyar yimata maganarki kullum duk da tanacikin mawuyacin hali.

zubewa qasa raheenat tayi cikin yanayin na hawaye tace,

na roqeki aleeya ji yafewa layla abinda tayi sbd hakan yasa takasa cire damuwa aranta harya zamar mata ciwo ki yafe mata kodan darajar qaunar dakike mata,
ki yafe mata sbd kashe kanta takeyi ahankali batareda tasaniba.


kasa dagowa aleeya tayi sbd tsananin kukan dayafi qarfinta wannanwace irin rayuwace sukeyi mara tsari da tawakkali,


kallon aleeya tayi tareda cewa,

bismillah muje nakaiki gurinta,

miqewa sukayi wannan karon qafafuwanta har rawa sukeyi sbd bugawar da zuciyarta keyi suka nufi sama zuwa wani daki.

bude qofar raheenat tayi tareda matsawa gefe aleeyar tasaka qofa tashiga dakin itakuma ta fito tafeda ja musu qofar,

tsayawa cak tayi tsakiyar dakin tareda qurawa nur din dake zaune qarshen gado ta takure,

wasu irin hawaye masu zafi da ciwone suka gangaro mata ganin yanda laylar takoma,
mezata gani haka layla takoma kamar wanda tayi shekara goma tana jinya,


LAYLAHH'''''ta furta muryarta na wata irin rawa,

kamar amafarki taji muryar aleeyar ta dago kai ahankali ta dorawa fuskar aleeyar ta sake dubawa dakyau taga itace
sai kawai ta sunkuyar dakai ahankali hawayen datafi shekaru dason yinsu sai yau suka ciko idanuwanta amma basu saukoba sai rawa da jikinta yafara dauka,

qarasowa ahankali aleeya tayi tareda zama kusada ita tayi irin zamanta suna fuskantar juna cikin rawar murya aleeya tace,

i miss you like hell my laylah.

rintse ido layla tayi sai kawai kuka ya qwace mata suka rungume juna da sauri kowannensu na sakin kukan daya jima baiyi irinsaba raheenat dake qofa takoma palo tasanardasu taheer nan suka sauke wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya atare tareda roqon allah yasa iyakacin wahalar kenan.

little aleeya kuwa murna takeyi yau zatabi mummy aleeyarta sutafi.


kuka sukai sosai saida suka gamsarda zukatansu kafin suka saki juna aleeya ta miqa mata hannu tace,

lets go home.

kallonta layla tayi da jajayen udanuwanta zatai magana aleeya ta katseta da cewa,

wlh har abada babu dawood cikin zuciyata yanxu,
komai ya isa hakanan namiki alqawarin inganta rayuwata matuqar zakimin alqawarin kulada dawood harya samu cikakkiyar lafiyarsa,
nabar dawood nikuma kimin alqawarin kinbarmin little aleeyah.

gangarowa hawayenta sukayi murya a shaqe tace,

aleeya takice har abada kece uwarta saidai nima babu abinda zanyi arayuwar dawoo....

baki gaji da ganinmu cikin wannan halinba kenan tun farko arayuwa taurin kankine yake jawo mana matsala dan haka daga yanxu kingama yanke kowane hukunci idanhar nice aleeyarki nice zan yanke hukunci daga yanxu,
and we are goin back home today.

tana fada ta miqe zuciyarta na daci sbd taurin kan layla yafara zama wani abin..
riqota layla tayi da sauri tareda goge hawayenta tace,

karkiyi fushi dani aleeyah konan gaba dan allah.

dawowa tayi ta rungumeta tana cewa,

har abada bazan qaraba insha allah idan har bazaki qara 6oyemin komaiba.

bazan qaraba i promise.

daqyar suka lallashi juna ta riqota suka sauko qasa bilal na ganin yar uwarsa kasa hkr yayi yataso da sauri suka rungume juna cikin tsananin qauna da kewar junansu.

taheer daqyar ta iya kallonsa suka gaisa qasa qasa sbd ko kallonsa takasayi.

duk yanda raheenat taso su kwana kasawa sukayi abincima daqyar suka samu cusawa suka juya da layla da little aleeya sbd amatse suke dasuga sun kai nur din gaban gadon dawood.

suna sauka airport direct asibiti suka nufa jikin layla nan take yafara rawa idanuwanta suka canxa ahankali aleeya ta riqo hannunta tareda girgixa mata kai tana sakar mata murmushin bata qwarin gwiwa gwara suyi facing komai once and for all kowa ya huta.
#mamuhgee


vote and follow.
[2/5, 8:18 PM] 0mmr Farouk: _*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*40*
Not edited.




Bilal ne yabudewa aleeya qofar motar taheer kuwa ya budewa layla suka fito kusan atare har lokacin jikin layla rawa yakeyi saidai tana qoqarin 6oyewa dan nunawa aleeya she is ok duk da kallo daya zakai mata ka gano bata cikin cikakkiyar nutsuwarta sbd bugawarda qirjinta keyi da qarfi,

hannunta aleeya ta riqo tareda janta suka shiga,
tun daga nesa mum ta hangosu takasa yarda da abinda idanuwanta ke gane mata ta ta6a sufyaan dake kusada ita ta nuna masa murya na rawa tace,

NURRR,

miqewa sukayi dukkaninsu atare shida mum sbd jass na ciki yana cirewa dawood din jinin daaka daura masa ya qare,

karaf idanuwan mum suka sauka kan little aleeya dake hannun taheer daya dauketa,

murza idanuwanta tayi cikin wani irin yanayi da shauqi kobaa fada mataba tasan wannan jinintace gudan jinin sweetboy dinta wata irin murna da hawaye tafara lokaci daya da sauri ta kar6eta daga hannun taheer ta qanqame jikinta kota kan laylar bata farabiba saidai sufyaan ne yayita yiwa allah godia idanuwansa na cikowa da hawayen farin cikin samun cikar burin dawood dinsu,

Nana kuwa rungume layla tayi tana hawayen farin ciki sbd ita kanta tasan tana tsananin qaunar layla har cikin ranta,

daqyar mum tabari sufyaan ya kar6i little tareda rungumeta dakyau wata irin qaunarta mai tsanani na shigarsa don kuwa jiyakeyi kamar gudan jininsace aka haifo koba komai suma sun zama dadys daga yanxu,,,alhamdulillah ya allah''''''ya furta ahankali tareda sakarwa little din murmushi yana cewa,

welcom dadys princess mai iyaye da yawa.

cikin 'doki da zumudin farin ciki Nana ta matso zata kar6eta ahannunsa hannuwansu suka hadu wani irin tsigar jiki yaji da sauri ya dago ya kalleta itama kallonsa tayi tareda sunkuyar dakai ta kar6i little din ta juya yabi bayanta da kallo kafin ya kalli tsigar jikinsa data tashi,

rungume layla mum tayi takasa mgn sai hkr take bata tana roqonta karta sake barinsu,

jijjiga kai tayi tana share hawayenta babu wadda takeson gani yanxu kamar ammynsu tasan itama tana cikin hali na tausayi da damuwa,

bilal dake faman waya dasu ammy yanata yimusu bayani ta kalla tanason cewa yabata ammy amma tanajin nauyin ammyn sbd sai yanxu dataga halinda kowa ke ciki tayi nadamar dcision dinta,

ahankali aleeya ta miqe ta shige dakinda dawood din yake daidai shikuma ya juyo ganin waye yashigo,

cikin idanuwan juna idanunsu suka sauka ta dauke kanta tana kallon dawood din cikin farin cikinta daya kasa 6oyuwa afuskarta,

qura mata blue eyes dinsa yayi akaro na farko dayaga murmushi kan fuskarta jiyayi kuzarinsa na ragewa ya juyarda kai cikeda mamakin abinda yasata farin ciki suna cikin wannan halin,

cikin wata irin murya tace,

kanasaran zai farfado nan kusa i mean yaushe kuke sakaran farkawarsa?

dan juyowa yayi ya kalleta yace,

anytime soon tunda jinin yagama shiga.

juyawa tayi tafice batareda taqara wata maganarba wannan ne karo na farko da magana doguwa irin wannan tashiga tsakaninsu.

tana fitowa takalli layla dake sharewa mum hawaye tariqo hannunta tareda miqar da ita tace,

nida mum munyi namu now its your turn zaki kulada mijinki mukuma zamu koma gida muyi jinyar kanmu.....

katseta mum tayi da cewa,

no aleeya ina zata iya jinyarsa itama fama takeyi da kanta..

murmushi aleeya tayi tana cigaba dajan layla zuwa dakin tace,

mum na tabbatarda ciwon laylana ya warke alokacinda muka hadu da juna abinda ya rage aciwon dr dawood zai qarasa warkar dashi.

kallonta layla tayi da sauri saikawai taji kunya da nauyin zancen meyasa tabari sonda takeyiwa dawood ya bayyana har haka aleeya tagane.

sake tura qofar tayi ahankali wannan karon jass yana juyowa da little yafaracin karo yaquramata ido kafin yayi mgn idanuwansa suka sauka kan nur da sauri yamaida kallonsa kan little aleeya kafin yakalli aleeya dake kallonsa ta gyada masa kai cikin murmushin farin ciki tace,

yes she's our little princess my little....

rintse idanuwansa yayi kafin ya zube qasa yayiwa allah sujjada hawayen tsananin farin ciki mara musali suka gangaro masa yataso da sauri ya dauke little sama yana jera mata kisses a goshi da fadar,

yes i'm a father now nima inada 'ya yanxu,,,,

murmushi aleeya tayi tana kallon yanda yake nunawa aleeya wata irin qauna kamar zai hadiyeta yace,

nine zanzama real dad naki sweethrt kowa ya hakura nixa'abarwa....

matsowa aleeya tayi gabansa tareda 'dan tamke fuska ta miqa masa hannu alamar yaba ita tace,

sorry dr amma she's my already so.......

dariyar daya manta rabon dayayi yayi tareda saurin ficewa dakin sbd tunowa dayayi akwai patien da sauri tabi bayansa tana cewa,

ji wannan dan qarfin halin.


tunda suka shigo idanuwanta suka sauka kansa tayi saurin dafa gado sbd wani irin mummunan jiri daya 'dibeta,

rawa jikinta yakejyi sosai da qyar ta qarasa bakin godon ta zube qabansa tareda sakin wani irin kuka mai ciwo ahankali,

tabbas bazata ta6a yafewa kantaba tunda tasaka dawood cikin wannan masifar tayi tunanin rashinta zaisa ya dangana ya rungumi aleeya amatsayin abokiyar rayuwa amma ga abinda hakan ya jawo,
tabbas koyaushe bin ra'ayinta ba alkhairi bane daga yanxu tadaina bin tunaninta sbd kullum shiyake kaisu ga masifu irin haka,


daqyar ta iya tsaida kukanta ta dago tareda qurawa fuskarsa ido ta lumshe idanuwa ahankali tanajin tsananin tausayinsa nabin jijiyoyinta duk yanda take tunanin cirewa ko danne soyayyar dawood azuciyarta wannan abune dabazai ta6a yiyuwa agaretaba duk kuwa baqar wuyar datake sha gurin gwada yin hakan,

hannunta ta dago ahankali yana rawa ta doro kan nasa dake kan cikinsa tasaki wata irin wahalalliyar ajiyar xuciya kafin takai kanta ahankali ta kwantar gefen guskarsa numfashinta na fita zuwa cikin kunnensa.




awaje kuwa abu soyayi yazamarwa jass da aleeya fada qarshe dai dole yabata sbd gida dazasu dukkaninsu shida sufyaan ne kawai zaa bari a asibitin sbd kar dawood ya farfado babusu akusa dan sunasaka ran farkawarsa koyaushe sbd jinin daaka saka masa.
#mamuhgee


vote and follow.
[2/5, 8:18 PM] 0mmr Farouk: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*41*
Not edited.

suna isa gida hankali kwance cikin nutsuwa da farin ciki mum tayi wanka tayi sallar magrib da ishai takwanta tanajin kewar mijinta ko abinci batajin zata iyaci sbd farin ciki fatarsu daya yanxu dawood ya farko yaga nur dinsa da little aleeyansa.

aleeya ma wanka tayi tayiwa little tayi sallah suka shirya cikin kayan bacci masu dan kauri sbd sanyi takalli Nana dake waya da ammy tana vata labarin little harda fada mata kamanninta ammy duk hankalinta yakasa nutsuwa yayo nan jitake kamar tajawo gobe tayi da wuri suxo tareda abba,

kar6ar wayar aleeya tayi ammy najin muryarta tasaki ajiyar xuciya jin muryar aleeyar cikin walwala da kwanciyar hankali,
tabbas tagodewa allah daya bata 'ya kamar aleeya mai tawakkali da rungumar qaddararta hannu bibbiyu babu tsawwalawa kai duk da tasan dole deep down zataji zafin rasa mutumin datake so saidai hakan datakeyi shine mafi alkhairi ka 6oye damuwarka kabarwa allah za6in mafita da mafi alkhairi sbd sawa kai damuwa bashine mafitaba saima cutardakai da kuma cutarda na kusadakai,,,,cikin tsananin qaunar 'yarta tace,

aleeya allah yaza6a miki miji mafi alkhairi dazaisoki fiyeda yanda kikasan so.

amin ta furta ahankali hawaye na ciko idanuwanta kafin tayi saurin mayar dasu ta jawo little jikinta ta dora mata wayar nandai suka lalace gurin fira da ammy kafin suka fito suka shiga kicin Nana tayi musu indomie da egg sharp sharp sukaci little kuwa goldenmorn mummynta tahada mata tabata suka sakeyin brush

1 Comments On DAWOOD
avatar
aisha-9-4-5

2 months ago

Reply

I love this book

Please Login or Register in order to submit comment