Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

part din nasu dan tasan Sarai baza'a rasa mace cikin part 'din ba Kuma har cikin ranta takaici takeji idan tagansa da Mata sbd Taya uwar 'dakinta kishi datakeyi.

Saidayaga shigewarta qofar dazata sadata da apartment 'din saraah kafin ya taka motar ya fice da gudu Dan dama tunda yafito security ya wangale Masa gate.

20 minutes tayi ahanya kafin ya Isa babbar asibitin dayake aiki a matsayin babban consultant likitan Mata wato gynecologist..

Yana Isa harabar asibitin yayi parking saidayayi kusan wasu mintuna hudu Yana waya da mum dinsa cikin kashe murya kafin ya fito ya nufi office dinsa Yana kashe dukkanin wayayinsa tunda yafito mota tundaga kan sauran doctors wainda basukai matsayinsaba da nurses harma da sauran ma'aikata ke qarasowa suna sharara Masa gaisuwa Yana amsa da hannu harya Isa office dinsa da'aka rubata DR DSD ( CONSULTANT DAWOOD SIDDEEQ DAUDA) ya shige....

Ko zama baiyiba ya duba diamond bylgari watch 'dinda ke daure a hannunsa yaga 20 minutes to theater dazasu shiga sai kawai ya shige shirya cikin kayansa na theater ya fito nurses biyu na biye dashi rungume da  files sai Dr sufyaan daya qaraso cikin nasa kayan tiyatar da sauri Yana kar6ar file 'din da Dr Andre ke miqo Masa dukkaninsu fuskokinsu da hankalinsu na tattara ga aikinsu bazaka ta6a kallonsu kace gwanayen neman Mata bane kamar yanda suke gwanaye a aikinsu,,

Sun dauki aikinsu da mahimmanci matuqa sbd yanda a hospital suke tsananin Jan girma da class dinsu musamman Dr dawood 'din da matuqar batare yakedasu sufyaan da Sameer ba bazaka ta6a ganin ko sakewar fuskarsaba bare kayi tunanin zai iya kallon mace harya nemeta.,

Sam ko nurses 'dinsa baya sakewa sbd 'daukar girma class uwa uba ego dayake dashi akan ganin matsayinsa kyawunsa da kudinsa Wanda yake ganin shidin Dole komai girma,kyau,class,gata,ilimi da dukiyar Mace Dole ta kallesa ta qara kallonsa duk da arayuwarsa baisa ranar dazai yiwa Mata kallon abin so ba ko burgewa bayan kawai abiya buqata dasu abiyasu sbd su 'dinne basu 'dauki kansu da darajaba,,,

So da dama idansu sufyaan na santin haryanxu akwai matanda suke virgin ma'ana Basu ta6a yin sex ba yakan kallesune kawai sbd a iya hange da iliminsa baya tunanin akwaisu Koda akwaisu Yana tunanin sai qasar dad 'dinsa wato Nigeria Wanda Suma yanasa ran duhun Kaine da rashin 'yancin Kai dasuke ba 'yayansu sbd yayi zaman kusan shekara 'daya acan Bai wani Jima da dasowaba sbd iyayensa dasuka koma can duk da bawai sun koma dindindin bane Amma a gigice yadawo sbd bazai iya rayuwaba a qasar Sam.,

Aryuwarsa baisan damuwa ko baqin ciki sbd ya taso tareda iyayensa duka biyu uwa da uba,
An haifesa cikin gata da daular dukiya  yataso cikin tsananin gata da soyayyar iyayensa musamman mum 'dinsa data 'dauki so da kulawar duniya ta 'dora akansa duk da yanada qani TAHEER Wanda suke kamar wasu abokai sbd rashin tserewarsu dakuma yanda taheer 'din yafisa zama matured and responsible man Dan kuwa shi lawyer ne Mai zaman kansa Kuma Wanda ke tashe a fagen lashe kowane irin case sbd dagewarsa da dukkanin time 'dinsa na rayuwarsa daya jingine a aikinsa yasa ko zama Bai cikayiba kullum meetings da clients ko sharia trip.,

Yanayin aikinsa da ganin qwazonsa da Kuma sunan dayayi a iya aikinsa yasa gabaki 'daya dukiyar gidan da takardun duka kadarorinsu Yana hannunsa sbd ataqaice dai kusan shine lawyern mahaifinsa,mahaifiyarsa da brothernsa dawood.

ASSIDDEEQ DAUDA tsohon chief judge ne daya zauna manyan kujeru na manyan muqaman alqalanci a qasar Malaysia tsawon lokaci kafin ya aje Dan girma da manyanci dayazo masa,

Ya taka muqaman ne bisa mahaifin matarsa faraah Wanda yake former minister of justice na qasar Kuma babban Mai fada aji..

Faraah da iyayenta 'yan asalin qasar ne Wanda asalinsu are not Muslims saidai dayake basa rayuwar takura Kai tunda ta hadu da Assiddeeq ta gabatarwa da iyayenta dashi Basu takurata ba ganin Shima Yana sonta kamar yanda takesonsa sai kawai suka barsu suna soyayyarsu,

Saida suka kammala karatunsu dadynta ya Samar Masa aiki a babban guri Mai tsoka kafin sukai aure anan qasar daga baya ya taho da ita Nigeria gurin mahaifiyarsa  sbd ita kadai  ta rage masa akai musu nasa kalar auren amatsayinsa na musulmi.,

Bayan anyi komai Basu wani Jima Nigeria ba suka koma tareda ammynsa sbd kaita wani Muslims old age home data Dade tana fatan zuwa sbd samun damar bautawa ubangiji sbd anci mulki da iko lokacin mijinta na raye yanxu kuwa tsufa yazo ba miji ba 'da sbd tana shekara koma fiye Batasa 'dan nata a idoba shiyasa tace yakaita old age home inda tsofi sa'anninta suke musamman ma aminiyarta tun ta yarinta tana can.

Bayan aurensu da tsawon lokaci yasamu cigaba da dama tuni Shima yafara zama multibillonaire a qasar sbd tuni MR DAMIEN OLIVER ya aje aiki yabar Masa ragamar komai.

Faraah nada cikinta na farko ta musulinta Koda ta haihu ta haifi 'da ammy datazo takanas dan ganin jikanta na farko aduniya da kanta tace asa Masa dawood wato sunan mijinta mahaifin siddeeq 'din,

Tun bayan haihuwar dawood kowa ya 'dauki tsaninin soda qauna suka 'dora Masa sbd shikadai suke gani as the only little one dasuke dashi.

Dawood is 3years old mum 'dinsa tasake haihuwar wani yaron still ammy tasa Masa suna taheer sbd har time din Bata koma old age home ba tun haihuwar dawood sbd tanason tabasa tarbiya da kishin qasarsu da addininsu.

Bayan haihuwar taheer da four years dad 'din faraah ya rasu Wanda su duka sun girgixa matuqa
Bayan komai ya lafa suka tattara suka koma Miami inda dad yafara bude companies da dama..

Mum din faraah Mrs Damien ta musulinta tun bayan rasuwar mijinta sai ya zamanto itada ammy da Nanny's 'dinsu dawood suke kula da tarbiyar yaran sbd daga mum har dad din ba zama sukeba sbd aiki musamman ma ita da yanxune take matsayin justice.

Lokacinda su dawood suka girma suka Kai munzalin shiga high school lokacin Mrs Damien da ammy suka koma old age home tare sbd Sam gidan kullum bamai zama dagasu sai maids Masu aikin gidan.

Mum irin manyan high class madams 'dinnanne da bazaka kalleta kace ta aje manyan handsomes samari ba sbd kyan jikinta da yanda take maintaining 'dinsa kasancewarta tun farko Yar gayu,
Sam mum Bata yarda tasa Abu Mai sauqi ko arha ajikinta sbd takasance mace Mai tsananin izza da son komai nata ya zamto higher level tun kuwa daga kan mutanen dazatai muamala dasu har kan aikinta da komai nata,,

A aladarta ta tsananin tsaftarta da gayunta ko komai nata tafison tayi order nasa direct daga company
Sannan a rayuwa ba komai zakai Kai Mata daidaiba Wanda shiyasa Sam ko na qasa da ita Basu cika Jin da'dinta ba sauqinta 'daya dasuke ji Sam Batada rowa Wanda ita idan tayi kyauta jitake wani sabon girma da iko na shigarta na ganin itace fa koyaushe asama saidai a risina mata.

Duk duniya ba abinda tafiso kamar baby boy 'dinta dawood Wanda Sam rayuwarta takasa hada sonsa da komai Kuma shikadaine ya Isa yasata Abu tayi,
Taheer kasancewar yafi dawood din zama matured kamarma shine babba yasa Sam baidamuwa da yanda take fifita dawood din saima tausayi dasuke basa sbd ganin yanda gabaki 'daya dawood 'din yazama Mama's boy Sam baison hayaniya da yawo Koda da friends ne kullum Yana jikin mum tana tarairayarsa Wanda Sam shi dad ko ajikinsa sbd dukkaninsu rayuwar turaice ke yawo a jininsu.

Kusanma dawood din ya biyo mum din harya zarceta gurin high level classy life sbd shi hatta shower cream nasa da duk abubuwan amfaninsa takanas yake bada ordernsu direct from the company shiyasa komai nasa is unique and classy
Sbd dawood mum tayi retire ta aje aiki sbd Sam bai yarda da kulawar kowaba sai ta mum 'din ko breakfast Dole itace take Masa yanda ammy tasaba yi Masa sweet sweet Nigerian dishes,

Shekararda dad yayi retire ashekarar suka koma Nigeria zuwa time din tuni dawood ya kammala karatunsa Yama Fara aiki a new Jersey shida friends dinsu su uku 2 are from Nigeria one is an American Wanda tun primary sukai tare wato Jasper inda suke zaune cikin wani qaton apartment suna hole rayuwarsu sbd ba Wanda yakeda niyya ko tunanin wani Abu aure.
Dr dawood,Dr sufyaan,Dr jasper and dr maska sun kasance the hottest young billionaires doctors dake tashen class,kyau gata wayewa tareda  kwarewa a fannin iya neman Mata sbd sun kasance irin mazanda kowace mace zataso tasamu.

Lokacinda su mum suka koma Nigeria Taredasu ammy suka koma gaba 'daya harda taheer daya koma can Shima harya Fara aiki sbd shikam ba laifi qasar tamai Shima Saida yayi kusan 1 and half year kafin yadawo Wanda Sam jiyake he just can't even think or imagine living in qasar....wheewww I'm damn tired man yafada Yana shiga office dinsa sufyaan na bayansa Shima a gajiye ya zauna bayan ya 'dauko robar ruwa a fridge din office din yace,

Thank God it was a successful operation after doguwan wahala.

Lumshe manyan fararen oily eyes dinsa yayi Yana kwantarda kansa jikin couch 'din office dinsa dayake zaune ahankali yace,

I need the hle night alone Dan na huta sosai yau...

Murmushi sufyaan yayi tareda miqewa sbd Kiran Jassper daya shigo wayarsa yace,

Let's go Jass ya iso.

Miqewa yayi tareda daukar wayoyinsa da sauran kayansa a gajiye ya fito Yana lumshe ido suka nufi ha'daddiyar bughatti car din Jassper da shikadaine baiyi tiyata ba yau Bai tattareda gajiya kamarsu Dan dama sumtimes hakan sukeyi kowa zaizo cikin ha'daddun motarsa Amma idan sun tashi kusan duk Wanda Bai tareda gajiya shizaijasu sukoma gida amotarsa sauran motocinsu kuwa saidai drivers na asibitin su kaimusu gida.


#mamuhgeee
#Vote
#comment
#share
#and follow
[12/31, 10:50 AM] ‪+234 706 677 7871‬: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_



*4*
Suna Isa gida jass yayi parking a babbar harabar gidan dukkaninsu suka fito kusan kowannensu agajiye yake Dan haka Kai tsaye suka nufi apartment 'dinsu sufyaan ne agaba sbd 'dan saurin daya ha'da dashi sbd dama amatse yake daya dawo ya duba yanda yabarta duk da yasan yayi Mata allurar bacci sbd ta huta sosai kafin yadawo.

Wani banxan kallo dawood yabisa dashi Yana yamutsa fuska coz sumtimes Yana mamakin yanda maza kewa Mata rawar jiki ko lallashi its irritating him.

Murmushi jass yayi ganin kallonda dawood yabi bayan sufyaan dashi Yana 'dauke gira 'daya yace,

Cool man...karkaga laifinsa you don't know meyakewa rawar jiki and.....

Shigewa parlour yayi batareda yatsaya Jin sauran abinda jass 'din zai fadaba...

'dauke kansa yayi Yana shiga parlon sbd ganin Wainda ke zaune apalon.

Zaune take kan sofa tayi crossing dogayen legs 'dinta dake sanye cikin blue parrazo trouser da milk loose shirt sai gashinta datayi coiling Shima a 'daure tsakiyar kanta,

Cup ne a hannunta da gani coffee ne takesha sbd 'dan tiririn dake fitowa daga cup 'din,

Kyakkyawace ba laifi saidai gayunta da hutu tareda maqidan kudin datake kashewa gurin gyaran fatarta yasa kyawunta da burgewarta fitowa fili.

Cup 'din hannunta ta aje ahankali tareda kallon maska dasuke Shan coffee 'din tare suna fira tace,

My man is hia so.....

Yana kallon yanda dawood ya 'daure fuska yayi hanyar bedroom 'dinsa Yana dariya yace,

No no carry on sweetheart go.

Dariya tayi tareda nufar bedroom 'din cikin tafiyarta ta 'daukar hankali.

Yana shiga bedroom 'din ya jefa wayoyinsa kan couch ya tu6e direct ya fada lafiyayyan babban toilet dinsa yashiga cikin bathtub ya kwanta tareda lumshe fararen oily eyes dinsa 'dumin ruwan na rage masa gajiyar jikinsa.

Tana shigowa taga baya cikin room 'din ta kalli qofar toilet tareda 'dan yamutsa fuska ahankali tace,

I don't feel like yin wani wanka yanxu but duk da haka lemme help.

Toilet 'din ta nufa ta bude qofar tashiga tareda rufowa ta jingina jikin qofar ta qura Masa idanuwanta,

Dawood you're my love and also my weakness,
I love you morethan anything,
You're the only man I intend to spend my life with,
I can do anything to keep you for my self,wen I said anything I mean anything Dan Babu wata Rai dabazan iya kashewaba akanka shiyasa nake fatan ko yanxu ko gaba karkayi kuskuren Fara son wata coz I won't think twice or hesitate to move anybody out of my way including poor Mrs assiddeeq Damien...
Sbd ko ita data haifeka bazata iya rabani dakaiba you're only meant for me alone.....

Ahankali ya bude idanuwansa dasukai taushi ya 'dorasu akanta fuska a 'daure yace,

You need something???

Murmushi tasaki harsaida dimple 'dinta suka lotsa ahankali ta qaraso gurinsa ta 'duqa ahankali tayi kissing lips 'dinsa tace,

No I was just looking at the man who stole away my heart,,

Lumshe ido yayi sbd qamshinta daya ha'du Dana shower creams 'dinsa ya cika toilet 'din Yana kallon tsakiyar idanuwanta yace,

And who was that man?

Wani shu'umin murmushin tasaki tareda zura hannunta cikin ruwan dayake cikin ta shafosa tana cewa,

Are you sure you want to know him?

Jawota yayi cikin ruwa Yana cewa,

0 percent sure.

Dariya ta qyalqyale dashi tana sbd cakulkulin daya Fara yimata Nan suka Fara wasa cikin ruwan suna ta6e ta6ensu tuni ya manta da wata gajiya suka cigaba da sha'aninsu harsuka gama sukayo wankan tare suka fito.

Shine namiji Amma fatarsa ma tafi Tata glowing duk kuwa da itama qarshe gurin kashewa jikinta kudi da bawa kanta hutu.

Cikin qananan Kaya marasa nauyi suka fito
Shi black trouser da white transparent shirt sai designer slippers 'din channel dake qafafunsa farare qal kamar Bai ta6a taka qasaba.

Ita kuwa wata loose half gown tasaka Dan dama Bata rasa Kaya room 'dinsa..

Tana Maqale a gefensa suka fito suna tana dariyar yanda idanuwansa sukai laushi sbd yunwa dayakeji.

Sufyaan ne kawai a palon gurin dining area yanata faman ha'da tea.

Kallonsu yayi tareda barin abinda yakeyi cikin farin ciki yace,

Thank God you are hia guys yunwa is killing someone hia.

Kallon dawood tayi tana cewa,

Yeah baby Let's go somewhere and have dinner that silly idiot yau batayi aiki ba wai she's not feeling well..

Maska ne yafito room dinsa ya qaraso Yana cewa,

Muje nima yunwar nakeji.

'daki sufyaan yakoma ya 'doro black shirt kan farar singlet dinsa yafito.

A Lamborghini car din maska suka fita dukkaninsu
Wani babban restaurant sukaje kowa yabada order abinda zaici suna gamawa suka dawo gida bayan maska yayi order sabbin tsadaddun kwalaben wine 'dinsa sbd shikadai ne cikinsu baya neman Mata saidai shi alcoholic ne kowa yayi hanyar room 'dinsa itama dai kamar lokuta da dama ranar agurinsa ta kwana batareda takoma apartment dinta dake gefen nasu ba.




*******
Tunda tazauna qofar 'dakin tasake kwantarda kanta kan gwiwowinta tayi shiru tana kallon sama yanda gagarumin hadari ya ha'du iska na kadawa.

Kamar daga sama Salim yaron dasuke bara tareda Bilal ya rugo yazo gabanta Yana haki cikin tashin hankali yace,

NUR Bilal mota ta takesa Kuma......

Bai qarasaba ta miqe tsaye tareda Kama hannunsa ta matsar dashi daga qofar 'dakin sbd kar baabaa yaji cikin sanyin murya tace,

Mekake cewa?

Duk da Yana yaro kuma yake cikin tsananin tashin hankali Saida yayi mamakin ganin yanayinta sam Babu razana ko firgici saidai idanuwanta dasuka ka'da lokaci 'daya bawai Dan Bata shiga firgici ko tashin hankalinba ita haka Allah yayita baya bayyana saidai zuciyarta tayita 'dawainiya da dakon wahalar tashin hankalin da firgicin.

Da saurinta fice gidan hartana hadawa da gudu ta qarasa gurinda ta tararda anyi cincirindo ansa Bilal din agaba anata masa fita sbd Wanda ya ka'desa ya gudu.

Rungumosa tayi jikinta da sauri hawayen idanuwanta suka sauko ta 'dago kanta ta kalli mutanen gurin murya na rawa tace,

Dan Allah ku taimakeni ku kaimu asibiti.....

Watsewa taga mutanen sunfarayi sbd maganar taimako data ambata
Jikinta ne ya'dau rawa tasake rungume Bilal 'din hawaye naci gaba da tsinke Mata.

Maigadin companin dasuke ne yaqaraso da sauri Yana salati akidime yace,

NUR maza kamosa mukaisa chemist tunda ba qarfin zuwa asibiti.

To,,,tace tana miqewa jiki na rawa ta kamasa ganin takasa iya 'daukarsa yasa ya kar6esa sukai hanyar chemist 'din dake gefen titin da sauri daidai lokacin ruwa Masu qarfin gaske da iska Mai qarfi suka taso Nan jamaa suka Fara gudu kowa na neman mafaka Musamman ganin yanayin qarfin iskan.

Gabanta ne yayi mummunan fa'duwa tunawa tayida duk ana iska da ruwa irin haka fitowa suke daga ginin harsai angama ruwan sbd gujewa faduwar ginin Dan tuni dama want gefe yafara rugujewa.

Kallon Bilal da'akewa allurori ana dressing inda yaji ciwuwuka tayi tareda miqewa jikinta na rawa tayi hanyar fita
Damqo hannunta dahiru Mai gadi yayi cikin fada yace,

Bakida hankaline Zaki fita cikin wannan ruwa da iskan Masu qarfi ya kukaji da neman na abincima bare na ciwon mahaifinki gana bilalu yanzu sannan kina qoqarin samawa kanki wani...

Qwacewa tayi hawayen idanuwanta na qara gudu tace,

Baabaa nacan nasan cikin gidan Nan Babu Mai fiddasa zuwa zanyi na fito dashi.

Ke dalla yiwa mutane shiru idanma kin fiddosa wani gurin gareki na kaisa yanzu cikin wainnan ruwan Kuma.......

Zuwan Raheenatu hankali tashe tana ihun kukan daya mugun ka'da kayan cikinta tayi gurinta jikinta na wani irin mazari ko magana takasa yi sbd tashin hankali da hannu ta tambayi Raheenatun jikinta na tsananta rawa.

Cikin tsananin kuka tana nuna hanyar waje tace,

Gini ya Fado Kuma....Kuma....

Wani wawan turi tayi Mata cikin tsananin tashin hankali ta fice da mugun gudu
Hankali tashe dahiru da sauran jamaar chemist din sukabi bayanta dahiru nakiran sunanta..

Sam ko gani sosai batayi sbd tsananin qarfin ruwan Amma Sam ko ruwan bataji duk inda tasamu jefa qafarta takeyi..



#Mamuhgee
#vote
#comment
#follow
#and share
[12/31, 10:50 AM] ‪+234 706 677 7871‬: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_



*5*
Tana Isa Bata tsaya tunanin komaiba tafara qoqarin kutsawa ciki mutanen dake gurin suka rirriqeta suna cewa Batada hankaline tana ganin gini na zubewa zatashiga...

Qwacewa tayi cikin tsananin kuka tana Kiran baabanta jikinta ba inda baya rawa..

Cikin zafin nama dahiru ya damqota tareda riqeta da qarfi
Ihu take da kuka sosai tanason qwacewa Amma ba qaramin riqo yayi mataba Dan kuwa ayanda take ba cikin hayyacinta ba idan aka saketa zata iya shiga ginin Wanda tuni ya qarasa rugujewa....

Ihu tasaki Mai qarfi ganin yanda gaba daya ya qarasa rugujewa kamar ba'ataba dogon giniba agurin.,,

Arikice dahiru ya girgixata Yana Kiran sunanta cikin tsoro da tashin hankali sbd ganin kamar Bata numfashin..

Layla... Layla..ke tashi karki mutu ahannuna..innalillahi

Arikice Raheenatu tafara jijjigata tana Kiran sunanta cikin tsananin kuka Amma Sam ba alamar tanada sauran numfashi...

Cicci6arta sukayi suka koma gefe sbd ruwan saman ya 'dauke mutane sun qara taruwa agurin ana kallon yanda ginin ya zube...

Kallon Raheenatu yayi cikin tsoro yace,

Ke kamata muje chemist idan Bata tashiba to tafiyata zanyi wlh ba ruwana.

Cikin tsananin kuka ta Mike suka kamata suna Isa chemist din hamisu Mai chemist na ganinta yace,

Aa wannan tafi qarfin chemist asibitin zakuje Dan da alama kamar bugawar zuciya ne kamarma ta Dade da mutuwa..

Ehhh,,, dahiru yafada cikin tsananin tashin hankali da tsoro Yana zaro jajayen idanuwansa
Nan Take jikinsa yadau rawa ya kalli Raheenatu Yana cewa,

Nayi iya yina saiki 'dora Kuma wlh ka sunana yafito ciki.

Ficewa yayi jiki na rawa Yana sharce gumi duk da sanyin ruwan da aka gama.

Kallon Nur din tayi cikin sabon kuka tace,

Kiyi hakuri Layla nima bansan ya zanyi Miki ba Dan banida wata taimako Kuma.

Miqewa tayi ta fice batareda tabari hamisu Mai chemist ya luraba.

Wani mugun ashar ya sako lokacinda yagama sallamar wani yaga sun gudu sun bar Masa gawa
Ai nantake 'yan hanjinsa suka ka'da Bai tsaya wata wata ba jiki na rawa ya zagayo yasa qarfi ya cicci6eta ya lalla6a yakaita gefen gininsu daya zube sbd duhun magrib yariga yagabato yadawo ya cicci6i Bilal yakai gefenta ya aje yadawowarsa ya rufe chemist dinsa yayi gida.

Babu Wanda yakuma kawosu arai sai tsakar dare guraren qarfe uku suka farfado kusan atare sbd sanyin asuba daya sawo Kai dakuma sanyin ruwan da'akayi.

Daqyar ta iya lalabawa ta tashi zaune ta bude idanuwanta da sauri ta rufe sbd ganin a inda suke yashe kan hanya kusada bola.

Da hannu ta lalabo Bilal dake kukan azabar ciwo ahankali ta rungumesa tareda sakin qaramin kuka ahankali tana kiran sunan mahaifinsu,

Sun zama marayu basuda uwa basuda uba basuda kowa dazasu gani ko sukira nasu
Tun adaren da mahaifinsu ya rasu sun Fara shiga garari tunda gasu da kwana gefen bola.

Jin kukan azabar da Bilal keyi yasata bude ido ta sake qanqamesa tana basa haquri Dan kuwa raunika ne sosai a jikinsa duk saiya qara 'daga Mata hankali ta birkice.,

Daqyar taga lokacin sallar asuba yayi anyi gari ya 'dan Fara haske takamasa daqyar suka 'dan matsa daga kusada bolar ta samo wani jikakken kwali ta shimfida Masa ta kwantar dashi.

Rawar sanyi yakeyi sosai ta rasa ya zatayi cikin hawaye ta kalli lifayarta data gama tsufa da faffashewa tasa hannu ya farketa biyu ta lullu6esa sauran ta 'dan budeta ta rufe jikinta Wanda Bata rufe dukaba saima taqara fitowa datayi a sadaka yallah dinta.

Koda gari yayi haske sosai jama'a kowa nata harkokin gabansa Babu Wanda ko kallo suka ishesa gashi har lokacin Bilal sosai yake cikin azabar ciwukan jikinsa ga zazzafan zazza6in dake cinta.

Daqyar ta miqe ta kamasa suka qara matsawa daidai bakin ginin ta kwantar dashi duk da daqyar take iya daukarsa.

Zama tayi kusadashi tareda cusa Kai cikin qafafunta tanason tayi kukan Amma yaqi zuwa ga mutane suna 'dan taruwa sake kallon ginin dakyau cikin haske.

Ahankali taga su Raheenatu da iyayensu suna zuwa suna zaunawa kusadasu kan kace me gurin ya 'dan cika da mutane mabarata da musakai.

Raheenatu ce cikin Jin nauyi da tausayinta ta matso murya a sanyaye tace,

Ya jikin Bilal?

Kallonta kawai tayi da jajayen idanuwanta sbd ko magana batajin zata iya.

Allah yajiqan baabaa,,,tasake cewa tana kallon ginin.

Sake rintse ido laylar tayi Jin abinda Raheenatun tafafa ko Amin din takasa cewa.

Kaf gurin Raheenatu ce kawai ta iya yimusu mgn ta miqe takoma gurin Yan uwanta.

Shiru tayi jikinta na 'dan rawar zazza6in dake tsananin cinta.

Ido dahiru yayita warewa harya hangota raku6e gefe kunya yadanji ya Sosa Kai tareda fuskewa ya nufi gurin tareda 'dan yaqe Baki yace,

Layla ya jikinki Dana bilalun?

Sake cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta batareda tace komaiba.

Kingane ki kwantarda hankalinki insha Allah zaku samu mafita wannan taruwar dakikaga wainnan munafukan sunyi na zuwan Alhaji Mai companin ne sbd zaizo yayi ta'aziyar abinda yafaru yakuma taimakawa wainda suke zaune suje su nemi wani gurin Kinga ke zakufi kowa kaso Mai tsoka tunda ke mahaifinku ya rasa ransa qila abin Nan zai biya...um um mema ake cewa sunan abun idan za'a biya....ummm yauwa diyya..Kinga daganan saina taimaka muku nasamo muku gurin zama da.....

Manyan jeeb jeeb dinda suka doso gurin yasashi miqewa da sauri Yana gyara fuskarsa zuwa kalar tausayi ya nufesu jiki na rawa haryana tuntube
Sauran mutanen dake cikin gurin kuwa tuni suka Fara fuskar kalar tausayi wasu harda kuka wasu kuwa kwantawa sukayi ana musu fifita da sannu.

Motocin na tsayawa tuni Yan press yo caaa suka rufesa da tambaya daidai lokacinda drivernsa yabude Masa ya fito motar.

Tambayoyi sukai tayi Masa Yana amsasu cikin nuna jimami da tausayawarsa ga alamarin.

Ahankali take kallon mutanen cikin tausayawa ta cikin glass din motar batareda tafitoba,
Rintse idanuwanta tayi sbd yanda gabanta ke tsanan faduwa duk lokacinda idanuwanta suka sauka kan 'daya daga cikin mutanen...

Qura Mata ido tayi zuciyarta na ingizata ga zuwa gurinta..

Saurin 'dauke Kai tayi numfashinta na fita da sauri.


Tunda yazo dukkaninsu suka Fara rawar jiki har lokacin Bata 'dogo kantaba saima qarfi da zazza6inta yaqara.

Ahankali yafara binsu 'daya bayan 'daya Yana Basu kudi Masu yawan gaske suna wucewa haryazo kanta.

Kallonsu yayi cikeda tausayawa itada qanin nata ganin qarancin shekarunsu sosai.

Cikin jimami dahiru dake gefe ya matso daga gefen securities din Alhajin yace,

Alhaji wainnan sune marayun 'yayan Wanda yarasa ransa.

Sanyi jikinsa yayi yasake kallonsu kafin yakalli PA dinsa yace,

Aminu ayi gaggawar Ciro gawarsa.

Ok sir,,,yace tareda Ciro wayarsa Yana danna Kira tareda komawa gefe.

Kallonsu yasakeyi cikin taushin murya yace,

Layla kamar yanda dahiru yafada sunanta.

Kasa 'dagowa tayi saima sake cusa kanta datayi cikin qafafunta tana kuka ahankali Jin gawar baabaansu daza'a Ciro sbd tana kwatanta irin azabar dayasha kafin ransa yafita lokacinda ginin yafado Masa.


Cikin qanqanin lokaci motocin aiki sukazo aka Ciro gawar saidai duk Wanda ke gurin Saida imani da sanyin jiki suka kamasa sbd ganin yanayin gawar abin babu kyawun gani saidai adduar Allah yaji qansa.

Kukanta yaqara tsananta sanyin jikinsu musamman qananun shekarunta daga ita har qaninta.

Basubar gurinba harsaida akayi jana'izarsa Nan Alhajin yaciro dubu 'dari yabawa dahiru yace yakula dasu sbd cewa dayayi zai kaisu gurin innarsa ta riqe.

Suna barin gurin ya miqo Mata kudin cikin farin ciki da zumudi yace,

Ungo riqemin zuwa anjima idan zani gida zan kar6a sbd karna fita dasu yanxu a yankemin aljihu.

Kar6a tayi batareda ta 'dagoba ta tura qarqashin kwalinda Bilal ke kwance Allah ya taimakesu ba Rana.

Agurin suka yini sai magriba Bilal ya farfado ta zaunar dashi jikinta na rawa
Kallo 'daya tayi Masa taji jikinta yaqarayin sanyi sbd ciwo da yunwa data hango qarara nacinsa.

Ita kanta ciwo

1 Comments On DAWOOD
avatar
aisha-9-4-5

2 months ago

Reply

I love this book

Please Login or Register in order to submit comment