Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke nuna mata zahirin so da tsantsar kauna.

'Yar dariya tayi tare da lumshe ido, personality ta kirashi da suna na mussaman wanda take kiransa dashi tunfil-azal.

Da murmushi a fuskarsa yace." Aysha Kinga Yaron da zaki kira da *JARUMI! NAN."* ya fad'a yana nuna mata hotonsa dake jikin jaridar.

Ta tsirawa hoton ido tana girgiza kanta, ingarman namiji maji k'arfi kyakykwa tamkar *SADAUKINTA* murmushi tayi Ta kalleshi da fadin." Lallai ni Ayshatu na sheda cewa babu *RAGO!* ga duk wanda ya amsa wannan sunan, ha'kika wannan yaron ya cancanta ayi masa komai saboda jarumtarsa! da kuma sadaukarwarsa."

Kansa ya girgiza da fadin." Sosai kuwa Aysha na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi wa yaron, Munyi waya da Asp Musa Baharu mun tattauna muhimman maganganu dashi na fahimta, ya kuma bani tabbas a kansa cewa ZINATU ta samu dukkanin kulawar da ta dace a gurinsa, ya tabbatar min da cewa yarinyar tana cikin koshin lafiya babu wani mugun rauni! a jikinta bayan wanda ta samu kafin zuwan shi wannan yaron da ya taimaka mata, sannan bayan haka kuma ya sheda min cewa daga zarar sun gama gudanar da binkicen daya dace to dashi kansa da yaron zasu kawo min ZINATU har gida, sosai yaron ya taka muhimmiyar rawa akanta babban abinda yafi burge ni dashi yanda yayi namijin kokarin ganin ya karya alkadarin takadirin d'an ta'addan nan! da ya addabi! 'kasa da al'ummar dake cikinta, Aysha wannan yaron jarumtarsa! har ta zarce tawa."

Murmushi tayi idonta cikin nashi tace."Ina shakku! akan maganarka ranka ya dade, domin kuwa ban yarda cewa akwai wanda yafi mijina jarumta ba, har yanzu kana nan yanda kake Jarumi! a gida kuma jajurtacce a waje."!

Hannuwanta ya rike yana jifanta da wani irin kallo.........Har yanzu Tana nan mak'ale a zuciyarsa, sam bata tsufa a idonsa, duk kwanan duniya sonta nunkuwa yake a zuciyarsa, Aysha ta zame masa jinin jiki.......... Ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta fahimci abinda yake da akwai, murmushi kawai tayi, tana mamakinsa, baya tsufa da soyayya, kullum da irin kalar soyayyar da yake nuna mata idan suka kad'aice, babu wani abu da ya samu tangard'a a zamantakewar auransu.

kusan a tare suka mike tsaye, 'kugunta ya ratsa da hannunshi, ya riketa sosai a jikinsa, kai tsaye bedroom suka nufa domin mutunta junansu.



*****
To Ranar da zasu cigaba da gudanar da binkice a sansanin *UBAN DABA!* Asp ya bada umarnin kwance masa sasarin! dake daure da k'afafunsa! 'yan jarida mane ma labarai suka cika harabar gurin, koda ganin fitowarsu sai sukayi caaa! a kansu sunayi musu tambayoyi.

Asp a takaice yayi musu bayani, shi kam be iya ce musu komai ba, mota kawai ya shiga ya zauna jami'ai biyu suka sanya shi a tsakiya, Asp shima yayi saurin shiga mota domin ya san idan ya biye musu to su ba zasu gaji dayi masa tambayoyi ba.


Tsit!! dajin babu alamun akwai wani dan adam dake rayuwa a gurin, kukan tsintsaye yafi yawa sai dai jefi-jefi suna jin kukan dabbobin dake can nesa!............binkice! suke sosai a gurin, sai dai kuma dukkaninsu a shirye suke domin Babu wanda ya saki jikinsa a cikinsu motsi kad'an zasu zabura! su juya gami da saita bindiga.

Gurin da yake tsammanin faruwar badakalar! tasu ya nufa, ya jima yana duba gurin kafin yayi tunanin cire wu'kar dake rataye a jikinshi ya fara tona 'kasar gurin da tsinin wuk'ar.

Cak! ya cire wu'kar ya ajiye a gefe ya tsuguna, hannu yasa yana tutture 'kasar data turbud'e abinda yake hasashen samunsa a gurin, lokacin da ya fito da sassan hannun yayi dai-dai da isowar Asp gurin!

Ya tsuguna kusa dashi gabad'aya idanuwansa ya zuba kan dungulmin hannun! yana jimanta al'amarin! babu shakka! wannan shine hannun mutumin da ya sanya aka zana masa hotonsa shekaru biyar da suka wuce! abinda ya sanya ya gazgata hakan, zabban zinare da azurfan dake jikin wannan zane sune jere a jikin yatsun dake gabanshi a halin yanzu.

Ya kalleshi da fadin." Yanzu na 'kara gazgata maganar ka, binkice ya k'are a kanka tunda ga sheda nan a hannunka wannan kad'ai ya isa a jinjina maka."!!!

Bece komai ba, ya ajiye sassan hannun daya riga yayi wani irin kumburi! kwanaki biyu kacal!

gefe ya matsa yana ya mutse fuskarsa, hannun har ya fara fitar da wari!

Asp ya tattara ma'aikatan gabad'aya ya nuna musu sheda! gabad'ayansu mamaki ya rufesu, dukkaninsu zuwa sukeyi har inda da yake tsaye suna 'kamewa da sarawa!! alamun jinijina!!

Asp abin ya burge shi, shima hularsa ya cire ya 'kame tare da sara masa! al'amarin ya bashi mamaki mutuka! Asp din yace." Wannan ba abun mamaki bane Cancanta ce ta janyo hakan.

A takaice dai basu bar dajin ba sai da suka tabbatar da cewa babu wani mahaluki da yake rayuwa a gurin, iya binkicensu ya nuna musu cewa d'an ta'addan! ya canza she'ka, hakan be basu mamaki! ba domin dama gabad'aya sunyi hasashen cewa babu yanda za'ayi ya cigaba da rayuwa a gurin domin ya tsira da rayuwarsa, to har yanzu dai suna nan akan bakansu zasu cigaba da gudanar da binkice a kansa, ba zasu fasa ba har sai bukatarsu ta biya a kansa.

Maigirma governor da kansa ya 'bukacin san ganin *GOJE!!* gani da ido domin tattauna wasu muhimman abubuwa.

Asp ne ya jagoranci tafiyar........shigarsu government house din keda wuya Maigirma governor ya mike daga kan kujerarsa, Asp yayi mamakin hakan sosai! koda yake yaron ya kai kuma ya cancanta da girmamawa! Governor be zauna ba har sai da suka zauna sannan ya koma ya zauna kan kujerarsa.

Cikin mutumci da girmama juna suka gaisa kafin su shiga tattauna abinda ya tarasu a gurin.

Ya jima kanshi a sunkuye yana nazari da tunanin maganganun governor a kansa. ya sauke ajiyar zuciya, cikin nutsuwa ya kalleshi da fadin." Wannan shine burina a duniya cewar na tabbatu gurin hidimtawa addinin Allah da kuma hidimtawa k'asata Najeria da al'ummar dake cikinta, amma ranka ya dad'e ya za'ayi nayi gogayya da manya-manyan ma'aikatan tsaro! bayan bani da cikkaken ilimi a kan hakan, ba zan boye maka cewa iyakaci na secondary skull ba shin dama hakan tana iya faruwa."?

Maigirma governor yayi dariya irin ta manya kafin yace." Malam bahaushe yace ta yaro kyau take bata k'arko! UMARU! ai bai cancata ka kira kanka da jahili ba, koda iyakacinka primary ka cancanta daka zauna a kujera irin ta Asp saboda jarumtarka, kayi abinda shi Asp din ya kasa dashi da wa'inda suke 'karkashinsa, sun buga! sun buga! sunyi-sunyi! Allah bai basu nasara ba, wannan dalilin ya sanya na d'auko hayar sojoji daga libiya domin su taimaka musu, sai gashi kai d'aya 'kwal kayi aikin mutum dubu! koda baka san (A) ba to ni na d'auke 'ka aiki a'kar'kashin mulki na, kuma zan biya ka albashi mai kyau! sannan kuma na baka kyautar gida da motar hawa, domin ka zauna da iyalinka a ciki."

Sai ya rasa bakin magana kawai ya zubawa Asp ido yana jimanta al'amarin, ganin ya rasa bakin magana ne yasa Asp din ya ari bakinsa domin yaci masa albasa.

Governor ya kalleshi da fadin." Asp babu batun godiya UMARU ya cancanci abinda yafi haka, godiyar ta isa haka, kai dashi duk kuna aiki kan gaskiya gami da kishin 'kasar ku, duka kun cancanci a baku lambar yabo."

Asp ya mika masa sannu cike da farin ciki yace." Mungode sosai da wannan karamci ranka ya dade Allah yasa ayi a gama lafiya." Ya amsa da "ameen ya Allah, kuma Allah ya taimake ku akan aikinku." gabadaya suka amsa da "ameen."

Hotona sukayi sosai suka sanya shi a tsakiya, sai kuma wasu da maigirman governor ya rungumeshi bayan ya bashi lambar yabo da girmamawa!! sosai ya samu kyaututtuka na mussaman daga gurin manya manyan 'yan siyasan dake gidan gwamnatin, su kansu sun jinjinawa kokarinsa,

Cike da tsantsar farin ciki da annushuwa suka fita daga gidan gwamnatin.


******
A daran ranar da al'amarin ya faru ZINATU da kyar ta iya runtsawa saboda 'bakin ciki da takaicin ganin yanda lokaci guda Allah ya daukakashi, ganin hotonsa da governor a lokacin da ya bashi lambar yabo da girmamawa ya mugun daga mata hankali, haka kawai take so ta ganshi a tagaiyare! a wulakance! amma hakan bata samu ba, babban bakin cikinta yanda taga manya mutane na girmamshi tare da kambaba! darajarsa, bata damu da kyaututtukan da ya samu ba kamar yanda ta damu da taga ya k'askanta!

Washe gari da 'kyar ta fito daga dakin domin breakfast, Asp din ya gidan be fita ba, ta gaisheshi kamar bata so, ya amsa yana nazarinta shi kansa d'abi'un yarinyar gabadaya basu bashi sha'awa, shiyasa yake so su shirya ranar da zasu kaita gaban mahaifinta kamar yanda yayi alkawari.

Ya kalleta sai kumbure-kumbure take alhalin babu abunda akai mata, da kulawa a maganarsa yace."ZINATU Ina fatan dai kina jin dadin zama damu ko."

Da 'kyar tace." Um ina jin dadin karamcinku a gareni nagode amma yaushe ne za'a sallame ni haka, tunda dai duk bukatunku sun biya."

Ya kalleta da mamakin maganarta yace." Kamar akwai abunda yake cikin ranki duba da yanayin maganarki."

Murmushi takaici tayi da fadin." Ranka shi dad'e wannan mutumin fa da kuka d'auki son duniya kuka d'ora masa bai da kirki ko kad'an! mugu! ne azzalimi! ni har yanzu ban yarda da gaskiyarsa ba."

Asp ransa ya baci da jin maganarta sai kawai ya rufeta da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, yace." Ban san wace irin kiyayya kike wa Umaru ba, shin me kike so muyi masa bayan wanda yafi haka? mutumin nan ya taimakeki a lokacin da kike bukatar taimako amma duk sanda za kiyi magana a kansa ba mai kyau bace! shin wai me yayi miki da zafi da kika tsaneshi haka."!

Cikin 'Kunci da takaici tace." Ranka ya dade mu bar maganar kawai domin duk abinda zan fada maka a kansa ba zaka yarda ba duba da ganin yanda zuciyarka ta hasala! kawai saboda na kiraye shi da macuci alhalin sunan daya cancanta dashi kenan."

Yace."Kin san Allah ba zan matsa daga gurin nan ba har sai kin sheda min irin cutar da yayi miki da har kike kiran sa da wannan sunan."

Ganin yanda ya kafe ta da idanuwansa yasa jikinta mutuwa, me zata ce yayi mata bayan alkairi, ta san ya taka muhimmiyar rawa a kanta amma haka kawai take jin haushinsa! a yanzu duk abinda zata fada a kansa sharri ne!

Ya katse tunaninta da fadin." Ke nake sauraro na fada miki ba zan bar gurin nan ba har sai naji dalilin da yasa kike tsaneshi."


Bakinta ya sub'ce gurin fadin"Saboda ya keta min haddi sakamakon kad'aicewar mu a dajin."

Ya zuba mata ido da so ya tabbatar da maganarta......."Ya keta miki haddi kamar yaya."?

Ko kunya ta sake lailayo wani sharrin......"Fyad'e yayi min." Tafad'a babu nadama a cikin maganarta.

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta kafin ya girgiza kai da fadin." Wannan shaci fad'i ne ban yarda zai aikata hakan ba."

Murmushin takaici tayi da fadin." Ai dama ba zaka yarda ba saboda jarumtarsa tana burgeka a matsayinka na babban mutumin mai rik'e da mu'kamin Asp bai kamata ace kana mubaya ga wannan k'azamin mutumin ba."

Maganarta sai ta bashi dariya, ya tsaya ya dara kafin ya mike yana duba agogon dake daure a hannunsa yace." Lallai yarinyar nan da gaske kike amma babu damuwa, wannan maganar kuma ba zan barta ba sai mun tattaunata da mutumin naki." Shuru tayi ba tace komai ba, har ya bar gurin, tana zaune a gurin suka fito tare da madam d'inshi dirarriyar mace kyakykawa da kyawun jiki sam ba za kace ta haifi 'yar shekara ashirin ba, hannunta rike da 'yar jakarshi ta rakashi bakin mota ta nayi masa fatan alkairi.
Koda ta dawo a falon ta zauna suna hira jefi-jefi ta d'an saki jikinta sakamakon mutunci da karamcin matar wanda ya janyo mata 'kima da mutunci a idonta......Sai dai kwata-kwata jininta bai had'u da Nabila ba, haka kawai ta tsani yarinyar alhalin babu wani abu da tayi mata na laifi........daidai gwargwado tana bata girma tunda ta fahimci cewa ta d'an girme mata sai take kiranta da Auntyna. hakan yana sake sanyawa kanta ya kara girma domin akwai ta da son girma, gata dai a gidan ubanta amma mulkar yarinyar take, da yake ita din mai saukin kai ce bata damuwa, domin bata mance ingantaccen hadisin nan da yake cewa "ka girmama bakon ka, wannan dalilin yasa take mata duk abinda take so, wanda ita kuma anata 'bangaran take ganin kamar ta isa ne! shiyasa take mata biyayya.....!




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*

*GOJE!!🏹*
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITER'S*
*ASSOCIATION📚🖊️*
____________________

_Mijina kazami! ne! to ni kam sai dai nace kiyi hakuri 'yar uwa domin akwai su a cikin maza amma ba duka ba, kuma bake kadai kike da matsala irin wannan ba, amma ki sani ke da kanki kina iya gyara abinki, da wayo da dabara, zahirin gaskiya kazamin namiji nada wuyar sha'ani! duk macan da take fuskantar wannan matsalar daga gurin mijinta akwai hanyoyi masu sauki da zata bi domin gyara masa dab'iu kamar yanda takeso ya kasance!_



FREE PEGE
*33&34*
Police barrack nan ne mafi akasarin ma'aikatan tsaro suke zaune da iyalansu, a nan gidan Asp yake, haka zalika ma anan ne mai girma Governor ya mallakawa UMARU gida tazarar su da Asp din babu yawa gida biyar ne a tsakaninsu, tsarin ginin gidan mai kyau ne, plate ne mai dauke da bangare uku, kowanne 'bangare a shirye yake tsaf da dukkan abinda za'a bukata na yau da gobe, abinda kawai ya rage a gidan mace, don a ranar da ya tare a gidan ma 'yan uwa da abokan arziki surutun da suke masa kenan, cewa a yanzu Allah yayi masa komai na rayuwa, abinda ya rage masa mace domin duk cikar mutum da kamalarsa mutukar bashi da aure to darajarsa dole tayi 'kasa..........'Kwarai hakane a yanzu ya san cewa cikar mutumcinsa shine aure, wannan dalilin ya sanya yaji sha'awar auran a cikin zuciyarsa, sai dai kuma babu wanda ya amsawa cewa zai auri 'yarsa a cikin wa'inda suke kawo masa tallan 'ya'yansu, da kansa zai duba wacce ta kwanta masa a ransa ya aura.

B'angare d'aya ya dauka Uwale da Hamra'u sai suke amfani da daya, Uwale ganin ba zata iya zama a gidan ita kadai ba yasa tace Hamrau ta ta zauna domin ta taya ta zama, hakan yayi mata dadi mutuka domin dama tana neman hanyar da zata kusanta kanta dashi.

Itace ta d'auki ragamar kula da gidan, ta tsaftacce ko'ina har sashensa idan zai fita take 'karbar key a gurinsa ta shiga ta gyara masa ko'ina tasa turare idan taga ya cire k'ananun kayanshi a toilet ta wanke masa tas ta shanya idan sun bushe ta ninnke tasa masa a wardrobe, kullum idan ya dawo daga gurin aiki tsaf-tsaf yake samun gurinsa yana kamshin turare na mussaman, kafin yayi wanka ya fito ta shirya masa abinci da duk wani abinda zai bukata, k'wazon yarinyar da yanda take kulawa dashi da kakarsa yana burgeshi! ba tun yau ba ya gane inda ta dosa a kansa, zai iya auranta saboda kyawawan dabi'unta dama wannan shine abin dubawa a cikin lamarin aure.

'Bangaranta kuwa shawarwari take da zuciyarta kan cewa ta sheda masa tana sonsa ko kuwa ta bari ya furta mata da bakinsa, a ganinta yanzu tunda yayi kudi yafi k'arfinta shiyasa kullum take jin tsoron tunkararsa da maganar gudun wulakanci, sai dai duk sanda masifar sonsa ta isheta daki take shiga taci kukanta ta koshi, kafin ta roki Allah ya za'ba mata abinda yafi alkairi a rayuwarta, amma tayi mamakin yanda akayi Uwale tayi shakulatun 'bangaro da maganar wanda ada can baya har kayan lefe take tarawa burinta bai wuce tabbatuwar auran ba, amma yanzu kwata-kwata bata maganar, ballanatana ta bashi umarnin auranta kamar yanda tayi alkawari a can baya.

Kamar yanda gwamnati ta mutuntashi ta kuma karramashi, shima haka ya mutunta yaransa ya karramasu yayi musu alheri sosai, domin duk rabin alherin da ya samu ya sadaukar musu, a cewarsa suma suna da hakki duba da irin muhimmiyar rawar da suka taka, hakan ya sake janyo masa kwarjini da farin jini a gurinsu da sauran jama'ar gari.

*******
Yau satin sa guda kenan da fara gudanar da aiki a ofis dinsa na mussaman, Uniform dinshi ma na mussaman ne, amma yayi kamanceceniya dana Asp amma kuma akwai bambanci sosai!

Da yake yana da hikima da nazari babu wani abu da ya shige masa duhu, aikin yake kamar wanda ya shekara yana aikin tsaron lafiyar al'umma!

Wasu takardu yake dubawa kira ya shigo wayarsa dake saman tevur din dake gabansa.

Ya ajiye takardun cikin nutsuwa ya daga wayar da fadin.'' Ranka ya dade barka da aiki."

Daga daya bangaran Asp ya amsa da "Barka dai *Jan wuya!* da yake sunan da yake kiransa dashi kenan, ya cigaba da cewa." Gobe ne fa tafiyar nan."

Yayi jim! yana tunanin maganar kafin ya dan ja siririn tsaki! ya manta shaf da maganarsu ta zuwa garin kano domin kai marakunyar yarinyar nan gaban iyayenta........Yace."Ogah me zai hana ka sata a mota ta tafi ai ita din ba yarinya bace zata kai kanta gida."

Ya girgiza kai da fadin." A'a mutumina ba za'ayi haka ba, ni nayi wa mahaifinta alkawarin cewa dani da kai zamu kai masa ita, sannan kuma ba haka dokar aikin take ba, dalilin da yasa ma tuntuni ban shirya tafiyar ba, saboda na fi bukatar yarinyar ta murmure na 'yan kwanaki hakan zai farantawa iyayenta rai su kuma ji dadin ganinta cikin koshin lafiya, to alhamdullihi yanzu naga tayi kyau sosai babu rama ko wani abu wanda ya danganci haka daga gareta."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin.'' Ranka ya dade don dai kawai ka shirya tafiyar nan dani ne amma da sai dai nace kaje kai kad'ai kawai dalili bana bukatar abinda zai sake danganta ni da yarinyar nan wallahi.''! Cike da takaici ya 'karashe maganar.

Asp na 'yar dariya yace." UMARU ban san me yasa kai da yarinyar nan bakwai jituwa ba, itama yanda kake jin haushinta haka take jin haushinka kullum bata da magana sai taka."

Da sauri yace." Tana zagi! na ko."? Asp din yasa dariya da fadin." In kaji zagi! ma d'aya kenan! shin ka san kuwa maganar da mukayi da ita kwanaki a kanka."?

Kai ya girgiza a k'untace yace." Sai ka fad'a." Jim yayi kafin yace." Na san sharri kawai tayi maka ba zaka aikata hakan ba, duk da dai zuciya bata da 'kashi kuma a lokacin hakan na iya faruwa saboda kusancinku da juna wanda dama shi shed'an burinsa kenan mace da namiji su kad'aice shi sai ya zama na ukunsu."

Tsaf ya fahimci inda maganar ta dosa, murmushin takaici yayi kafin yace." Banyi mamakin jin wannan maganar ba domin duk mutumin da yake 'kin ka, to babu irin k'azafin da ba zai yi a kanka ba, Asp wallahi tallahi! da naso keta haddin yarinyar nan da ba zata kai labari a hannuna ba, saboda na samu dama iri-iri a kanta amma sam ba wannan ne a gabana ba, burina shine na kubtar da ita, sai kuma sharri! ya biyo bayan alkairi."

Yace." Kwarai kuwa shiyasa a lokacin da take maganar na 'karyata ta domin na san ba za ka aikata hakan ba, kawai dai tana neman hanyar da zata tozartaka ne."

Yace."Shiyasa ai nace kayi tafiyarka kawai Asp wallahi kaji rantsuwar musulmi ba naso na sake ganin fuskar yarinyar nan."

Yace." A haba dai kada ka tsananta da yawa abu ne mai sauki wannan ki
'kiyayyar da kukewa junanku ta rikide ta zama soyayya irin wacce take da wuyar samu hakan na iya faruwa.

Ranshi ya 'baci da jin haka tevur din dake gabansa ya buga! murya a sama yace." Allah ya kiyaye Asp bana fatan Allah ya jarrabeni da soyayyar wannan yarinyar, kawai kayi min fatan alkairi ba irin wannan ba."

Asp din yayi mamakin yanda maganar ta fusata shi, sai ya sassauta murya da fadin." Colm dwon mana ka samu nutsuwa, wannan maganar dana nake maka a yanzu ba wai nace lallai hakan ya tabbata ba, kawai a jikina nake jin kamar akwai wani abu da zai ratsa tsakaninka da yarinyar domin anyi irin haka ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, kiyayya ce ake wacce tafi wannan daga karshe kuma sai ta rikide ta juya matsananciyar soyayya."

"Mtsssssw!!!! Yaja wani dogon tsaki kafin ya kashe wayar ya jefar saman tevur tunda ya had'u da Asp bai ta'ba 'bata masa rai irin yau ba........Shi kuwa Asp din sakin baki yayi da wayar a hannunsa yana mamakin al'amarin.


Da takaicin maganganun Asp ya isa gida, takalmanshi kawai ya iya kwancewa ya kwanta saman kujera ba tare da ya cire inform din dake jikinsa ba, rungume hannunsa yayi a kirji ya rufe idanuwansa yana hasaso kammanin yarinyar............. 'baka ce ba sosai ba, idan be manta ba tana da tsayi gami da cikar kirji da fadin kwankwanso, 'kirar jikinta kenan, tana da manyan idanu da d'an k'arami hanci wanda ke tsatstsafo da gumi ako da yaushe, wannan sune kad'ai abunda zai iya tunawa a game da ita!

Yaja tsaki! tare da gyara kwanciyarsa, har yanzu maganar ce take cin zuciyarsa! shi kam a rayuwarsa me zai yi da yarinyar da ta nuna masa tsantsar 'kiyayya irin haka, hanyar jirgi daban ta mota daban.

Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya bude idonshi tare da tsareta dasu, be tashi zaune ba yana daga kwance ya amsa mata, still idonshi na tsaye kanta, sai tace tunda suke bai ta'ba yi mata kallon kurrullah irin haka ba, duk sai ta tsargu dama ta shigo ne domin ta duba taga ya dawo ta kawo masa abinci, jikinta duk sai ya mutu sakamakon kafe ta da yayi da kaifin idanuwansa.

A sanyaye tace." Yayana sannu da zuwa ashe ka dawo."?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yun'kura ya tashi zaune yana kokarin b'alle botiran gaban rigarshi, yace." Na dawo my dear nagaji ne shiyasa ban leka gurinku ba, ina so nayi wanka na huta tukkuna."

Cike da kulawa tace." Sannu ya aikin? bari na had'a ma ruwan wanka ko."? yana kokarin cire rigar daga jikinshi yace." Godiya nake Allah yayi miki albarka." Cike da jin dadi ta amsa, kafin da sauri ta kama hanyar dakinsa, ido ya bita dashi har ta shiga dakin ya girgiza kai a fili yace." Wannan itace matar aure mai cikakkiyar tarbiya nutsuwa sanin ya kamata yayi imani ko zuria ya had'a da wannan yarinyar ba zaiyi kaico ba.

Ta fito falon ta sameshi daga shi sai vest wacce ta matse shi da gajeran wando domin ya cire gabadaya kayan jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta kunyar had'a ido take dashi, ganin haka yasa yayi murmushi ya tashi ya bar gurin, da sauri ta dauki inform din ta kai masa daki ta rataye masa kafin ta bude wardrobe ta dauko masa 'kananun kayan shan iska, ta ajiye saman gado da sauri ta fita daga dakin. tana jin wata annushuwa a cikin ranta, yau ta d'an fara ganin alamun sonta acikin 'kwayar idanuwansa....



*Free pege zai 'kare a

Please Login or Register in order to submit comment