Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ki tashi kije sashen 'yar uwata ki nemi afuwarta akan irin abubuwan da ki kayi mata, idan kin gama da wannan to d'aya bayan d'aya ki kira wayar 'yan uwanki ki gaisa dasu, har shi babban yayanku Magajin sarki wanda ki ka dauki karan tsana ki ka dora masa har kina gaba dashi saboda yana nuna miki hanya mai kyau, to shima ki nemi number sa don yanzu haka yana Egypt ki kirashi ki nemi gafararsa, wannan kadai za kiyi ki faranta min rai."

Ajiyar zuciya ta sauke murya a dashe! tace."Shikkenan Mammah zanyi duk yanda ki kace amma don Allah kema kiyi hakuri ki gafarceni ki kuma dena yi min mugun baki."

Girgiza kai tayi da fadin." Tunda kike shaid'ancinki na ta'ba jifanki da wata muguwar kalmar."? girgiza kai tayi da fadin " A'a." tace." To yanzu ma raina ne ya 'baci da al'amarinki, idan kina bukatar albarka to kiyi gaggawar gyara kuskuranki sai mu samu zaman lafiya da juna."

A sanyaye tace."Insha Allahu zan kiyaye amma kice kin yafe mun." jim tayi na 'yan mintina kafin tace." Na yafe miki Allah ya shirya min ke shirin addinin islama Allah kuma ya baki miji nagari wanda zaiyi jimiri da hakuri dake da halayenki."

A zuciyarta ta amsa da "Ameeen ta dan samu sassauci kad'an, da kyar ta yunkura ta tashi tace. "Zan shiga gurin Mommy kamar yanda kika bukata." Shuru tayi ba tace mata komai ta bita da ido har ta bude kofa ta fita.


*****
Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin, ta dan samu sassauci daga gurin mahaifiyarta, suna zaune lafiya wani sa'bani bai sake shiga tsakaninsu ba, kuma tana kokarin yi mata biyayya daidai gwargwado sai dai har yanzu mahaifiyar tata bata wani saki jikinta da ita sosai ba, A gurin Safah kawai ta samun walwala dan wani sa'in ma can take yini, wannan ce damar da ita Safah din ta samu take k'ara nusar da ita hanya mai kyau kuma take kwadaita mata son aure a cikin zuciyarta, sai dai kuma inda gizo ke sa'kar a yanzu bata da wani tsayayye a hannu lokacin da take kan ganiyarta take dasu rurutu amma duk ta koresu, a yanzu dai da zasu dawo da tantance nagartacce a cikinsu, ba kuma ta tunanin neman daya daga cikinsu a ganinta kamar hakan zubewar mutunci ne, ta san dai yanzu labarin dawowarta ya isa ace yaje kunnuwan masoyanta to tana zuba ido duk wanda ya damu da ita a cikinsu zai kawo kansa daga nan sai ta fitar da gwani.

Sai dai kuma a ranar tunaninta ya rushe dalilin hukuncin da mahaifinta ya yanke mata, be fito fili ya sheda mata abunda ke zuciyarsa ba, amma yayi mata hannunka mai sanda cewa mutukar bata fitar da miji a cikin satikan daya bata ba, to lashakka shi zai aura mata wanda yayi ra'ayi.

Tabbas mahaifinta yana tsananin sonta irin son da bayayi wa sauran 'ya'yansa amma ta sheda cewa shi din kaifi d'aya ne, a haka yake baya ta'ba yanke hukunci ya janye, ita a ganinta kamar hukuncin yayi tsauri da yawa, har yaushe ta dawo da za'a d'ibar mata sati biyu ace ta fito da mijin aure kamar akwai rashin adalci a cikin al'amarin.

Ta samu mahaifiyarta da maganar cewa sati biyu yai mata kad'an tayi masa magana ya 'kara mata sati biyu ya zama wata daya, Gimbiya Aysha ta nuna sam babu ruwanta a cikin maganar dalili ta riga ta san abunda yake rufe wanda ita Zinat din bata san dashi ba..........da ta samu Safah da maganar itama cewa tayi babu ruwanta kawai dai tayi kokarin ganin ta fitar da miji kafin lokacin daka a bata ya cika, sosai ta shiga cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa tunani kaf ya ta'allaka a gurin neman mafita, babu yanda za'ayi tabi wani daga cikin samarinta nada tace yazo ya aureta wannan zubar da mutunci ne, tsintar kanta tayi da tashin tsakiyar dare domin neman zabin Allah, duk da bata da wani cikakken ilmin addini, a hakan take gabatar da nafila ta zauna saman dadduma tana salatin Annabi kafin ta mika kukanta ga mai kowa da komai.

*****
To kamar yanda suka tattauna maganar commissioner of police da Asp abunda ya faru kenan, domin a daran ranar da ya dawo ya bukaci zama dashi..................Suka fara tattauna maganganu kamar gaske sai dai kuma tafiyar ba tayi tsayi ba suka samu sa'bani dalili bambacin ra'ayi, a take gurin ya nuna masa cewa shi din *Jan wuya!* ne tafiyar su ba zata zo daya ba, ya nusa masa cewa bashi yakewa aiki ba 'kasar sa yakewa aiki don haka bai isa ya gindaya masa wasu sharud'a wanda suka sa'bawa dokar aiki ba. mutukar yana bukatar tafiyarsu tazo dai-dai to kowa ya zauna a matsayinsa.

Sosai commissioner din yayi mamakin yaron, koda yake tun yana can ya samu labarinsa da kuma irin alakar dake tsakaninsa da Asp Musa Baharu wanda ya zame masa kadangaran bakin tulu, babu shakka ya sake ya bar wannan ala'kar ta cigaba da gudana to akwai matsala, dole ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu, domin samun cigaba da gudanar da al'amuransa hankali kwance.

Ganin cewa ba zai samu yanda yake so ba yasa yayi saurin b'oye manufarsa yayi saurin gyara kuskuransa, kwantar da kansa yayi ya nemi maslaha dashi, sannan ya sheda masa cewa ya shirya tafiya training a sati a mai zuwa zai turashi can *Abeokuta* 'karo sani akan aikinsa." Cike da kwarin gwiwa ya amsa masa ba tare da wata fargaba ba.


*******
Yau ne ya kasance cikar kwanakin da aka d'iba mata, kwance take sai juyi take ta rasa yanda za tayi da rayuwarta, tabbas da kuka yana magani da tuni yayi mata, babu yanda ba tayi da mahaifiyarta kan cewa ta sa baki a cikin al'amarin ba amma fafur! tace babu ruwanta ta dinga kuka tana rokonta amma taki sauranata, sai ta shiga kiran wayoyin 'yan uwanta tana sheda musu halin da take ciki, 'yan uwanta mata ne kawai suka saurareta amma Magajin sarki kashe wayarsa ma yayi yace hakan shine daidai idan bata fito da miji ba to duk wanda ya dace a daura mata aure dashi.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta mike zaune tare da sauke kafafunta k'asa! kawai ta tsirawa kasan kafet ido kamar me neman wani abu.

Turo kofar dakin yaja hankalinta ta tsirawa kofar ido har sai da ta shigo tare da sallama a bakinta, ido kawai ta zuba mata har ta 'karaso kusa da ita, ta zauna gefenta tare da ajiye ajakar dake hannunta, wani irin kallo take mata kafin tace." Me zan gani haka ni Sakina 'kawata haka ki zama kamar wata zautacciya shin wai bayan kin dawo jinyya kika kwanta dubeki don Allah kin rame kinyi wujiga-wujiga dake."!

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta kalleta da fadin." Sakina baki da kirki wallahi ace wai don wulakanci sai yau ki kaga damar zuwa duba ni bayan ta dalilinki na samu matsala, yau satina uku da dawowa amma saboda baki da mutunci sai yau ki kazo."

'Yar dariya tayi da fadin." Ki bari kawai 'kawata wallahi abubuwa ne sukayi min yawa kin san dai harkar siyasa sai a hankali kullum cikin uzuri muke wannan dalilin ya hana ni zuwa duba ki amma wallahi kina cikin raina."

Tace."Ban yarda ba Sakina ai na gane matsayina a gurinki kin nuna min kudi ya fini babu komai ai." Da sauri tace."Don Allah kada wannan ya janyo mana samun sa'bani 'kawata kiyi min uzuri ki kuma yafe min, kina nan a zuciyata."

Ta'be bakinta kawai tayi ba tace komai ba.

Tace." Zinat kina da damuwa gaskiya ba haka na san ki ba, ko dai mutanan nan sun samu nasara akanki ina nufin sunyi keta miki haddi"?

Girgiza kai tayi da fadin." Ko d'aya Sakina kawai ina cikin wani lamari ne wanda na garara fita a cikinsa na rasa yanda zanyi."

Tace."Menene yake damunki."? Kallonta tayi ta girgiza kai kafin ta sheda mata abunda ke faruwa.

Taja tsaki da fadin." To yanzu ke ya za kiyi ? tunda kince ke ba zaki nemi tsoffafin samarinki ba, hakan yana nufin cewa kin amince da zabin mahaifinki."

Hawaye ta share da fadin." Sakina kai tsaye ba zan saduda ba, na san tabbas yau zai kira ni domin jin ta bakina ni kuma anan zan sake rokar alfarma ya kara min kwanaki ina tunanin kafin lokacin na samu mafita."

Ta'be bakinta tayi da fadin." Shikkenan ai amma wallahi da nice kai tsaye zan bijire na nuna rashin yarda ta, haba ai tuntuni an daina yayin auran dole."

Girgiza kanta tayi da fadin." Sakina ni yanzu sulhu nake nema da iyayena farin cikinsu nake bukata dole nabi komai sannu a hankali amma ni kaina bana tsammanin zan amince da auran wanda bana ra'ayi."

Tace."Wannan shine tunani mai kyau, ki zauna kiyi nazari da kyau domin ki taimaki rayuwarki."

Haka suka wanzu a daki suna k'ulle-k'ullen yanda za'ayi su rusa hukuncin da yake da niyyar tabbata a ranar.

Sai yamma likis tayi mata sallama ta tafi bayan ta bata shawarwarin da take ganin sune kwanciyar hankalinta.

Lokacin da sakon maimartaba ya sameta sai da cikinta ya murd'a tsabar fargaba da tashin hankali, ta kai minti goma a zaune tana sa'kawa da kwancewa kafin tayi namijin kokarin amsa kiran.


Tun kafin ma ya fara magana ta fara kuka, kawai sai ya zuba mata ido yana kallo, ta rarrafa har inda yake ta rirrike k'afafunsa tana wani kuka da fadin." Ranka ya dade kaji tausayina don Allah kada ka tarwatsa min farin cikin rayuwata bana so ka aura min wanda bana ra'ayi yanzu an dena auran dole idan kace za kayi min hakan zai janyo matsala babba.

Numfashi ya sauke kafin ya tallafo fuskarta, ya sanya hannu yana share mata hawaye rarrashinta yayi da fadin tayi shuru suyi magana ta fahinta.

Da 'kyar ta iya dakatar da hawayen dake zuba, ta zuba masa idanunta dake cike da fargaba burinta kawai taji abinda ke bakinsa.

Babu alamun wasa a tattare dashi yace." Wannan shi ya nuna min da cewa baki da matsaya kin dauki maganata a banza ace duk a cikin mane ma auranki baki da gwani wanda kike ganin zai zama abokin rayuwarki, wannan karon ba zan tausaya miki ba, domin ni na haifeki amma na gaji da ganinki a haka babu aure, tunda har na baki dama kika watsar to ni ina da wanda nake ganin ya dace dake wanda kuma nake da tabbacin cewa idan na bashi auranki zai rike min ke da gaskiya da Amana, wannan hukuncin nawa babu wanda ya isa ya janye shi ZINATU mutukar ni na haifeki to baki da mijin aure wanda ya wuce takwarana UMARU ina nufin yaron nan daya cece rayuwarki a daji a kwanakin da suka wuce shine wanda na za'ba miki a matsayin mijin aure, kuma na sheda masa kyautar da nayi masa a ranar suka dawo dake gida, shi din ya kuma tabbatar min da cewa ya kar'ba kyautar da nayi masa saboda haka kada ki bani kunya ko kiyi jayayya da umarnina, insha Allahu nan da wata biyu auranku zai tabbata da ikon Allah."!

Wani irin bugawa! gabanta yake kanta yana juyawa! tunda ya fara maganar ta nemi yawu ta rasa a bakinta! wani rikitaccen yanayi ta shiga wanda ta kasa fassarashi! kuka take ta gayyatowa amma fafur! yaki amsa gayyatarta idanuwan ma soyewa sukayi sai wani dan banzan zafi suke! jijiyar idon data kanta sun had'u sun d'aure guri daya wanda hakan ya janyo mata mugun ciwon kai irin na 'bari guda, sama-sama takejin maganarsa a lokacin da yake bata umarnin tafiya.

Jiki a masifar sanyaye ta iya kai kanta dakinta, kawai ta zube kasan kafet tana janyo numfashi da kyar! ke kace ita din mai jinyya ce wacce ke fama da cutukan dake da ala'ka da numfashi.

Wai ace kamar ita jinin saurata gaba da baya, sannan kuma bata rasa komai ba na matantaka ba, Matar manya manyan mutane masu kudi da mu'kamai! aka dauketa kacokan aka bawa wani ma'kaskanci kyauta! mutumin data riga ta raina masa hankali, bashi da komai na rayuwa! bak'auye dashi, wanda ko direbanta be kai matsayi ba amma wai yau shi mahafinta ke ikirarin bawa auranta, koda wasa ba tayi tsammanin hakan na iya faruwa ba! har yanzu ta kasa gano dalilin da yasa mutane suke k'aunarsa! a'iya nazari da tunaninta, ta fahimci cewa jarumtarsa ce take kawai ke burge mutane.......Wannan shine babban dalilin da sanya mahaifinta yin sha'awar bashi ita a matsayin matar aurensa, tabbas kuwa idan ya sake akayi auran nan to zai gane shayi ruwa ne a hannunta, domin sai ta nuna masa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, sam-sam! ba zata yarda wannan karan ya samu nasara a kanta ba, babu ruwanta da jarumtarsa! tunda a zahiri ta fishi komai, to dole shi zai rusana mata!!!!
*TURKASHI!!*


*Tofah! yanzu za'a fara wasan😃 ko ya zaman auran nasu zai kasance oho? ni ban san ma me zance muku ba, amma dai muje zuwa..............!*



*Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, don darajar Allah da Annabi idan kin san ba siya za kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min magana🙏🏻*




*#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment