Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da baya ta farayi kafin ta juya a sukwane tana falfala gudu hade da kiran sunansa *GOJE!!* shi kuwa Gwaggon birin nan dariya yayi da ya fahimci tsoronsa take sai ya kudiri aniyar tsokanarta, ya fara bin jikin bishiyu yana tsalle yana mata dariya har ya dura a gabanta.

Zubewa tayi tana daga masa hannu yawun bakinta ya bushe "Don Allah kayi hakuri! wayyo Allah na wayyo na shiga uku kuka ta dinga yi hawaye da majina sunyi kaca kaca da fuskarta.

Daya bayan daya suka kewayeta iyaye da kakanni! da alama sassaninsu ta shigo bata sani ba.

Kanta ne ya dinga juyawa a gurin kafin ta fadi, suma tayi, ba tare da bata lokaci ba wannan dattijon birin ya dauketa yasa a kafada, kataf-kataf ya fara tafiya da ita iyalinsa suka rufa masa baya.


Dabaru irin nasu sukayi mata ta dawo hayyacinta koda ta bude ido ta ganta a tsakiyarsu, sai ta mayar da idonta ta rufe jikinta sai karkarwa yake, su kuwa suna zazzaune sai cin manya manya ayaba sukeyi suna gurnani da alama zantuka suke a tsakaninsu.


Sai gefin magariba suka dawo, hankalinsa ya tashi lokacin daya duba sama da kasa be ganta ba,

Dajin ya shiga yana yana sasssare mattatun itatuwan da suka cika gurin, ya fito da sarewa yana busawa tare da cigaba da ratsa cikin dajin.

Zumbur! ta tashi zaune jin busar sarewar na kusanto gurin da suke, daga can nesa ya tsaya yana hango tawagarsu tana tsakiyarsu sai kace 'yar tsana saboda kankanta.

Kai tsaye gurin ya nufa yana cigaba da busa sarewar dake bakinsa, tsakiyarsu ya shiga yayi wani irin tsugo gaban dattijon birin nan yana me cigaba da busa abinda ke bakinsa,

Murmushi yayi ya dora hannunsa me cike da gashi da farata zako-zako a hannunsa a saman kansa, kafin ya cire ya nuna masa ita, yana gurnani!

Kansa kawai ya girgiza ya nufi inda take, hannu ya mika mata ta mike tsaye kafafunta sai kyarma! suke a haka suka bar gurin.

Saboda fargaba da mutuwar jiki yasa gabadaya kafafunta sukayi sanyi da kyar take iya jansu, bakinta ya mutu murus! tsabar tashin hankali binsa kawai take duk inda yaja ta, b'angaransa kuwa yana sane yaki goya ta saboda tayi bala'in bashi haushi, ya tabbata idan wata dabbar ce sai yasha mutukar wahala kafin ya samu damar fito da ita daga cikinsu idan sun barta da rai kenan.
Wannan Gwaggon birin sun saba dashi sosai duk sanda zasu shigo farauta dajin basu da matsala dashi da iyalinsa, wani sa'in ma har kyautar ayaba mai yawa suke basu.

Cikin mawuyacin hali suka karasa gurin da suka yada zangon ya jefar da ita ta fadi kasan gurin, zaune ta mike tana kallonsa ya juya mata baya gabadaya jikinta yayi sanyi domin ba tayi tsammanin zata cigaba da rayuwa ba.

Cikin wani irin amo! taji maganarsa. "Kada ki kuskura ki sake barin gurin nan dana ajiye ki domin kuwa yin hakan na barazana da rayuwarki, babu inda yake da tsaro a cikin dajin nan fiye dana nan gurin, idan kika sake fita yawo to ba zan sake yunkurin ceto rayuwarki ba, yau kwananmu biyu sai kuma munyi sati guda kafin mu koma gida don haka ki kiyaye rayuwarki kibi umarnina kuma mutukar kina bukatar cigaba da rayuwa.''

Kuka ta fashe! dashi ra rarrafa ra rike kafafunsa, " Kada kace haka mana! ka tausaya min a matsayina na mace mai rauni ka fitar dani daga wannan dajin ni ba zan iya sati a guda a cikin wannan tashin hankalina ba, wallahi komai kake bukata mahaifina zai maka ka taimakawa rayuwata."

Yanda take kuka tana rokonsa sai ku dauka mutuniyar kirki ce, haka take dama a duk lokacin da zata ganta cikin wata ukubar takan gigice ta saduda amma daga an kwana biyu sai ta koma baya.

Kafafunsa ya cire ba tare daya ce mata komai ba ya bar gurin, Hakan da yayi ya 'bata mata rai! sai kawai ta kullaceshi a ranta, ta kuma kudiri aniyar wani abu a ranta zata tayar masa da hankali wanda zai daga
Masa hankali dole ya kaita gaban iyayenta........



*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Katin Mov ko airtal



*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________



*Mijina mazinaci ne*
_________
_Mazinacin namiji daban yake a cikin maza, duk irin kokarin da za kiyi a kanshi to hakan ba zai hanashi neman matan banza ba, da yawa daga cikinsu jarabtace daga Allah! amma kuma son zuciya yafi yawa a ciki, 'Yar uwa idan Allah ya jarrabeki da auran mai irin wannan dabi'ar, ba zama zakiyi ba addua zaki tsananta akan Allah ya kawo miki mafita, Allah kuma ya shiryeshi ya gane hanya mai kyau. amma mafi alkairi a rayuwarki rabuwa da auransa domin samun zaman lafiyarki, koda kuwa akwai zuria a tsakaninku rabuwar ita tafi alkairi._

*Ubangiji Allah ka shirya mana mazajenmu ka dauke hankalinsu daga kan haram ka mayar da hankalinsu kan halalinsu, mu kuma Allah ka bamu hakuri da juriar dawainiya da bukatunsu.*


FREE PEGE
*17&18*
*UBAN DABA!*
Ya gagara! yayi shura! a harkar ta'addanci! ya addabi 'kasa da jama'ar dake cikinta, ran mutum abun banza ne a gurinsa, da yawa jami'an tsaro suka shiga sassaninsa, basa fitowa da rai! idan anyi sa'a wasu su fito a raye to za'a samu muggan raunika a jikinsu, shekaru bakwai kenan daya kafa sansani a cikin dajin dashi da jama'arsa, manya manyan bishiyun kuka ciki suka fafake ya zama makwancinsu, duk abunda yake faruwa a cikin gari yana samun labari akwai redio a tare dashi, bayan haka kuma yakan tura yaran sa suyi badda kama su dauko masa rahoton abinda kasa take ciki.

Masana sunyi hasashen cewa Gurin da ya kafa sansani akwai albarkar kasa a gurin, irinsu gold da man fetur da sauransu, wannan dalilin yasa shima ya tsaurara matakan tsaro a gurin, babu wanda yake amfana da albarkar dake gurin sai shi da jama'arsa, duk sanda suka haqo gold din akwai wani hamshakin dan kasuwa dake zuwa ya saya. cikin dare ya kan shiga dajin kar'ba! ya basu kudi da kayan masarufi, sannan a duk sanda sukayi ra'ayi zasu badda kama su shiga cikin gari suyi siye-siyen abunda suke bukata.

*Mashekin daji!* Hatsabibin mutum ne wanda yake da suddubaru! duk sanda hukuma ta tura jami'anta binkice a dajin, basa nasarar ganin sansaninsa amma kuma shi da jama'arsa suna ganin duk irin d'auki ba dadin da jami'an tsaron keyi a kok'arinsu na ganin sun ga mafakarsu, wannan damar suke samu su karkashe wanda sukayi ra'ayi, sai dai a fito da gawarsu.

*GOJE!* Ya jima da jin labarin hatsabibancinsa, kullum tunaninsa ya za'ayi ya kawo karshen ta'addancin daya ke a kasa.

Kafin ya yanke shawarar tunkarar inda yake sai da ya zauna da yaransa domin yaji ra'ayinsu, da yawa daga cikinsu jikinsu ne yayi sanyi domin dai sun san tunkarar mutumin babban al'amari ne! dalili shi akwai kayan aiki a tare dashi da jama'arsa, duk da suma suna da dabaru amma a ganinsu tunda sojoji da 'yan sanda suka kasa samun nasara a kansa to waye zai iya .

Ganin jikinsu yayi sanyi yasa ya karfafa musu gwiwa da fadin." Su cire tsoro a cikin ransu, kada su sanya a ransu cewa *masheki* da jama'arsa zasu samu nasara a kansu, idan sun yarda da kansu cewa sunfi karfi wuka da bindiga to tunkarar inda yake abune mai sauki bayan haka kuma su dauka cewa wannan aikin da za suyi kamar jahadi idan ma Allah ya kaddara mutuwarsu a gurin aljanna ce makomarsu.

Wannan maganar da yayi ya sanya suka samu karfin gwiwa, suka kwanta da shirin tunkarar *masheki* ba tare da k'asa ta san abinda suke shirin aikatawa ba.

Tafiya suke tsakankanin bishiyu da manyan tsaunika, gami da kwazazzabe, gabadayansu, babu alamun gajiya a tattare dasu, tafiyar suke suna bushe-bushe tare da farautar duk wata dabbar data gilma a gurin, ita dashi ne a gaba, yayin da jama'arsa ke take masu baya, tayi masifar galabaita! bakinta ya bushe cikinta in banda qugi! babu abinda yake, ba komai ke damunta sai yunwa,

kallonshi tayi kamar tunda aka halliceshi be taba dariya ba, tunda ya rike hannunta da zasu tafi be sake kallonta ba ballantana magana ta had'asu,

Magana takeso tayi masa amma tana jin shakka! don yanayin sa kadai dole ya baka tsoro! sai taja ta tsaya cakk! tana sauke wani irin numfashi!

Kallonta yayi na minti biyu, kafin ya juya yayi masu magana da ido, sun gane abinda yake nufi, sai suka samu guri suka zazzauna wasu kuma suka fara hawa kan bishiyu suna kad'o 'ya'yan itace.

Kan wani ice ta zauna tana kallonsa sai kai kawo yake a gurun.........."Ina bukatar ruwa da abinci." tafada tana dam hararar bayansa. Yana jin maganarta amma be juyo ba.

"Ina magana fa."! tafada kamar zata fashe da kuka.

" Alba." sunan d'aya daga cikin yaransa kenan. Yayi saurin zuwa gurin, yace."Ka bata ruwa da abinci." Yace." An gama maigida.

Gabanta ya k'araso da wata 'yar jarka ruwane a ciki, ya mika mata da fadin." Kisha yanda kike so"

Cike da k'yan'kyami take bin jarkar da kallo, 'ya'yan wasa sun tashi a cikin ruwan.

Tsaki! taje cikin tsawa! tace."Wuce ka ban guri waye zai sha wannan kazantaccen ruwan."

Maganar ta dauki hankalinsa ya juyo yana kallonta, shi kansa Alba d'in ransa ya baci da jin irin tsawar data buga masa.

Ya kalleshi da fadin." Jeka kawai." Ya girgiza kai, da fadin" Angama." Gurin ya bari. Shi kuma ya juya mata baya, tunda ba zata sha ruwan da kowa yake sha ba sai ta zauna a haka.

Ranta ya baci ganin ya juya mata baya tace." Wai me ake nufi ne."?

Ba tare da juyo ba yace." Ya kike so ayi miki? an baki kince bakya so akwai wanda kike so ya zama ruwa a cikinmu kisha."?

Tace." Ruwan fa bashi da kyau, bayan haka ya za'ayi na hada bakina dana wannan 'kazamin."

Ya girgiza kai da fadin." Sai ki zauna da ishirwarki ."

Kuka! ta fashe dashi! da fadin" Allah ya isa tsakanina da kai mugu azzalimi."!!

Ya juyo da fuskar bacin rai yana kallonta.....Alba dake kokarin zuwa gurin yace."Oga wannan yarinyar fa tana da matsala wallahi! da zaka bani dama sau daya dana koya mata hankali ."

Ya kalleshi na minti biyu kafin yace." Ko bana guri ban amince da hakan ba amana ce a gurina." da sauri yace."Allah ya huci zuciyarka."

Ya gyada kai da fadin ." Wanke lemon ka bata." Da sauri yayi abinda aka umarceshi, ta kar'ba tana yatsine fuska.

Yana kokarin barin gurin yace."Bani wannan jakar ruwan ta hannunka." Ya mika masa, a gabansa ya bude murfin ya zubar da ruwan ciki. Ya bar gurin da ita a hannunsa.

Ita dashi duk suka bishi da kallo yana tsallake manya duwatsu kafin su daina ganinsa, gabanta ya tsananta fad'uwa ganin baya gurin, ta dora idonta kan Alba dake tsaye yana zazzare mata jajayen idanuwansa, saurin sunkuyar da kanta tayi, tsoro takeji kada yayi mata wani abun, sai da ya gama cije-cije kafin ya bar gurin.

Ya kasance sai ita kadai a gurin, sai motsi da maganarsu da takeji a saman bishiyu, ta daga kai tana so ta hangesu, amma ta kasa ganinsu,

Dajin ta dinga bi da kallo, kanta yana juyawa, manya dutsina da tafka-tafkan bishiyun dake gurin sun juyar mata da kai.

Da sauri ta kama hanyar da taga yabi, tana tafiya tana waiwayen bayanta.


Sai da yayi tafiya mai tsayi sannan ya cimma ruwa yana gudana daga kasan wani tsabtataccan dutse gare-gare dashi.........Ya haura wasu manya duwatsu kafin ya samu nasarar d'ibar ruwan.

Yana juyowa kibiyar ta gilma ta gefan fuskarsa, da alama saita shi akayi Allah be bada nasara ba.......Da mugun sauri ya daga kanshi sama, can ya hango su saman wani dutse sun kai su biyar, yayi gaggawar fitowa daga tsakanin ruwan.

Suma basu fasa harbinsa da kibiya ba.
A gaggauce ya fara kurd'awa inda jama'arsa suke baya su cimma inda suke ba tare da shiri ba. sai dai me! biyoshi sukayi suna sakar masa harbi ta ko'ina!!

K'aro sukayi da juna!! ya rike hannunta tamau! bayan wata bishiya suka 'buya, suka 'karaso gurin suna sassare matattatun itacuwan da suke gurin.

Hannunsa dake cikin nata yake kokarin cirewa ta rike da kyau! tana girgiza masa kai! wai kada ya fita, ya sake yunkurin cire hannunsa ta rike! hawaye masu tsananin zafi suka wanke mata fuska, bakinta tasa a kunnansa, a hankali tayi magana "Kada kaje."

Jajayen idonsa ya tsira mata! ta marairaice fuska, tana ro'konshi da idanuwanta.

Tausayi ta bashi ganin yanda jikinta ke wani irin karkarwa, cikin zuciyarsa yace."Ba yanda za'ayi yana ji yana gani nasara ta kufce mai wannan ce hanya mafi sauki da zai tunzura zuciyar abokin gabarsa.


Kafin ta ankara, ya fuzge! hannunsa, ya fice! ta leqa kanta tana hango artabun da suke a tsakaninsu, su biyar ne shi d'aya, amma cikin ikon Allah ya samu nasara a kan mutum biyu ukun kuma suka gudu!.

Ya k'wace wukaken dake jikinsu, da sauran kayan ta addanci, kana ya d'aure musu hannuwa, gaba ya tisa su har inda suka yada zango shida jama'arsa.



*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin Airtal ko mov


*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE

*15&16*
Sosai ta kwanta jinya sakamakon artabun da sukayi ita dashi, jikinta yayi mugun tsami! ta shar'be! a guri guda da kyar take iya motsa hannu saboda tsabar sanyi da jikinta yayi, al'amarin bai tashi tsananta ba sai da dare ya tsala tukkuna, ta kasa rintsawa gabadaya jikinta ya dauki ciwo! ga wani irin kaikayi da ciwukan jikinta keyi.
Kuka ta dinga yi tana jan hanci! ita kam wannan bala'i bata san ina zata kai shi ba.

Can cikin baccin daya dan fizgeshi ya dinga jin shashshekar kukanta, zumbur ya mike zaune, dama babu wata tazara a tsakaninsu, ya d'auki fitilar dake gefansa ya kunna yana daga inda yake zaune yake haska gurin da take.

Hannu tasa ta kare fuskarta ta sake takure jikinta tana cigaba da zubar da hawayen azabah!.

Ya karaso gurin da fitilar a hannunsa, ya dudduba ko'ina babu wani abu. tsugunawa yayi a gabanta yana duba fuskarta, hannu tasa ta doke fitilar ta fadi. a take ta mutu gurin yayi duhu! ya lalubi fitilar yana kokarin gyara batir din, amma ina ta rikice! yayi-yayi ta kama taki, haka ya hakura ya ajiyeta kafin yace." Kukan me kikeyi ko wani guri yana miki ciwo a jikinki."? Shuru tayi masa, ya sake maimaita maganarsa, uffan ba tace masa ba.

Sai ya yun'kura da niyyar barin gurin tayi saurin rike gefan rigarsa, a rikice tace."Jikina ne duk yake ciwo ko'ina babu dadi."

Yanda yaji tana magana a rikice da alamun kuka ya sanya ya gazgata maganarta, bece komai ba ya sake yunk'urin tashi. Ta rike gefan rigarsa da kyau! yaja! taja! sai ya juyo yana kallonta, da k'yar ta mike zaune kafin tace."Kada ka tafi kayi wani abu wallahi zan iya mutuwa."

Yana da tsananin tsausayi mussaman akan 'ya mace! sai duk jikinsa ya mutu, ya koma ya tsugana yana dan ganin shatin fuskarta duk tayi wani iri idonta yayi jajawur! fuskar duk ta kumbura!.

Be iya tausasa murya ba, amma sai ya tsinci kansa da sassaita muryasa yace."Yi hakuri ki sake min rigar na samo miki magani."!

Hanci taja kafin ta sakar mai rigar ya tashi, tabi inuwarsa da kallo tana sauke ajiyar zuciyar wahala.

'Daya daga cikin yaranshi ya umarta daya had'a masa maganin ciwon jiki, da yake duk suna tafe da guzurinsu, ba tare da anja dogon lokaci ba, ya harhad'a komai ya nufi inda take dashi a hannunsa.

Samun ta yayi tana rawar d'ari, domin lokacin sanyi asubah ya fara sai zazzabi yake kokarin rufeta, sai datse hakoran bakinta take.

Cikin wani irin yanayi ya mika mata maganin da fadin." Kar'bi kisha wannan za kiji sasaauci sannan zaki samu bacci."

Kasa kar'ba tayi saboda halin da take ciki kawai ido ta tsirawa fuskarsa hawaye na sharara! jikinta gabadaya yaki tsayuwa a guri daya saboda karkarwa!.


Ya ajiye maganin hannunta ya lalubo ya rike a cikin nasa, nan yaji zafi rau!! ya sake shiga damuwa da ya fahimci zazzabi ne a jikinta.

Sosai ya zauna a gurun ya kama dukkanin hannunta cikin kokarin sassaita muryarsa da sigar rarrashi yace."Zazzabi ne ko."?


Sai ta fashe da kuka! mai karfi! kamar me jiran kiris! da sauri yasa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai!

Hannunsa ta cire tana me cigaba da janyo kukan dake cin zuciyarta.

Kawai sai ya tsinci kansa da janyota jikinsa, ya sata cikin katuwar rigar dake jikinsa, ya san nauyin rigar zai zame mata garkuwa gurin karkarwar da take.

Da yake taimako take nema ba tayi wani turjiya ba mussaman da taji ta kan faffadan kirjinsa dake cike da gargasa ga wani irin dumi da ya fara ratsa jikinta, luf tayi ta kwanta sosai tare da sanya hannu a bayansa ta rikeshi kam! tana sauke ajiyar zuciya daki-daki.


Sai da ya fara jin saukar numfashinta a hankali sannan ya dan gyara zaman shi, cikin wannan muryar daya aro yace." *GIMBIYA!* Yanda ya kira sunan yayi masifar kassara mata gabobin jikinta.

Taji shi sarai! tayi shuru motsin kirki ta kasa mamakin ma take yanda akayi ta saki jikinta a kirjinsa ba tayi tsammanin zata yarda numfashinta da nasa ya hadu ba sai gata a kwance a kirjinsa male-male maimakon taji wari! ko wani abu makamancin haka na fita a jikinsa sai taji akasin haka, jikinshi baya fitar da wari! ko kad'an sai ma wani irin dumi! da takeji na ratsa ta, nutsuwa da kwanciyar hankali na sauka a sassan jikinta.

*"GIMBIYA."* Ya sake kiran sunan daya sanya mata a lokacin, koda yake daman Gimbiyar ce shiyasa shima ya ara ya yafa.

Dan motsi tayi amma bata amsa ba, kuma bata sakeshi ba, ya dan ja numfashi, jin yanayinsa yana sauyawa, ya fara kokarin cireta daga jikinsa. Ta dage! harda gyara kwanciya kamar wacce take kan katifa.

Mamaki sosai ya rufeshi, tunda yaji tayi shuru kuma numfashinta ya daidaita ya san ta samu sassauci bayan haka kuma jikinta ya daina karkarwa da alamar zazzabin yayi nasa a guri, amma meye amfanin abinda take.

Namijin kokari yayi ya cireta daga jikinsa, babu kunya ta zuba masa ido kamar wanda yayi mata laifi.

Ya saisaita yanayinsa kafin yace."Sannu kina bukatar magani ko."?

Shuru tai na minti biyu kafin ta kalli hannunsa, maganin ne yake kokarin sanya mata a baki. Tasa hannu ta buge kwaryar maganin gabadaya ya zube kasan gurin da jikinsa

Cike da takaici da bacin rai yake kallonta, ta 'bata rai da fadin.'' Wane irin magani ne wannan me wari zaka sa min a baki."

Ya hadiye b'acin ransa wannan karan bai sassauta murya ba da yanayin maganarsa yace."
Ke ki kace jikinki na ciwo maganin karfin jiki ne."

Ta'be baki tayi da fadin." Bana bukata." Bece komai ba ya tashi daga gurin tare da jin takaicin abinda tayi.

Ta kalleshi da fadin." Ka bani aron wannan rigar ta jikinka na rufe jikina da ita tana da d'umi."

Uffan bece mata ba ya bar gurin, minti uku ya dawo da irin rigar a hannunsa. Ya mika mata, ta kalleshi da fadin." Ta jikinka nake so."? Yace."Duk daya ce da wannan din."

A yamutse tasa hannu ta kar'ba tana kokarin sawa a jikinta ya bar gurin .

Sai kace suddabaru! hankalinta ya gaza kwanciya koda tasa rigar ta kwanta domin jin d'umi kasa nutsuwa tayi ta tashi zaune tana rawar jiki.......Me yasa ta kasa samun abunda takeso a jikin rigar! ita a tunanin kaurin rigar ne ya saukar mata da nutsuwa sai taga akasin haka. "Ba rigar bace mai rigar ne yasa miki nutsuwa da kwanciyar hankali."
zuciyarta ce take mata wannan maganar.

Da sauri ta k'aryata zuciyarta ta sake rurrufe jikinta da rigar tana korar abinda zuciyarta ke raya mata, babu yanda za'ayi ta amince da cewa wannan gantallalan ne zai zama garkuwa a gareta.

Daya daga cikin yaranshi ne ya kawo mata ruwa da asuwaki da abin kari. ganin yanda maigidansu yake bata kulawa ya sanyashi gaisheta, bata amsa ba sai wukalantaccan kallon da take masa shida tarkacen da ya ajiye a gabanta. Girgiza kansa yayi baki a cije! ya bar gurun ba don kar ya dauki mataki akan yarinyar ya samu matsala da maigidansa ba, da sai ya fasa mata baki domin yaji ciwon kallon banza da tayi masa.

Har gari yayi haske sosai tana takure cikin rigar har yanzu ta kasa tantance a wane iri yanayi take,

Can ta hangoshi yana zuwa inda take, ido kawai ta tsira masa babu kiftawa sosai take mamakin tsananin kamar da yake da jarumi(Barbahs) tana bala'in son jarumin saboda jarumtarsa da iya soyayyarsa idan yana abu a film kamar gaske, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin karyata abinda zuciyarta ke raya mata a kansa.

Tsaf yake cikin shirin fita, ya sauya rigar jikinsa doguwar jallabiya ce browan mai gajeran hannu sai ya sanya dogon wadon jens kanshi nannad'e da bakin yadi yayi gammo sosai! idanuwan nan rad'au! da bakin kwalli! kafad'unshi rakwacam! da tarin kayan farauta, har da irin doguwar bindigar nan, hakanan wuyanshi da damtsan hannuwansa wasu irin abubuwa ne a d'aure.! kafafunsa sanye suke da wani irin takalmi mai tarin igiyoyi a jikinsa.


Tunda ya tsaya a kanta take kallon kafarshi, mamakin kyawun kafar take, bata ta'ba kallon kafarsa ba sai yau, faratanshi tas babu kazanta sai kananun gashi dake kwance saman yatsun kafar.

A tsorace ta dinga sauke ajiyar zuciya tana kokarin kawar da idonta daga kan kafar. taji muryarsa cike da wani irin amo!! "Tashi zaune."

Yanda ya fadi maganar babu wasa yasa ta tashi tana kallon fuskarsa, babu fara'a yace." Zanja ragamar yara na wani aiki a cikin dajin nan, ina so ki kula da kyau! kada kiyi kuskuran barin gurin nan! ki kiyaye! mutukar kina so ki cigaba da rayuwa a duniya.

Kuka tasa tana kallonsa da fadin." Me yasa ba zaka tafi dani ba, saboda tsabar mugunta shine zaka had'a kan yaranka ku tafi ku barni ni kad'ai! bayan ka san dajin bashi da kyau komai yana iya faruwa da rayuwata."

Yace." Nan gurin yana da tsaro bayan haka kuma gurin da zamu shiga yana da had'ari shiyasa na yanke shawarar barin ki anan sai yafi miki kwanciyar hankali."

Ta girgiza kai tana shakar hanci tace."Aa nifa ba zan zauna ba wallahi ko kun tafi sai na biyo bayanku."

Yanda tayi maganar babu alamun wasa a tare da iya yasa yaji shakkar tafiya ya barta.

Ya kalleta a lokacin da take kokarin mi'kewa. "Na fad'a miki abinda yake da akwai kina kuka ko."?

Hannu ta d'aga masa da fadin." Nifa ba zan zauna ni kadai a wannan gurin ba." Tana gama maganarta ta kama tana tafiya babu takalmi a kafarta, ga kanta babu dankwali."

"Ki tsaya nan nace."! Cikin tsawa yayi maganar. taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba.

Yaja tsaki tare da komawa baya, takalmi ya lalobo mata tare da wani farin yadi.

Ya karasa inda take da fadin." Kar'bi wannan ki rufe jikinki dashi." ba tayi musu ba ta kar'ba, ta lullube jikinta har kasa. Ya bata takalmi ta tsuguna tana kokarin sawa, ganin tana 'bata masa lokaci yasa ya tsuguna da kansa ya d'aura mata takalmin sosai yanda duk wuya ba zai fita a kafar ba.

Hannunta ya rike a cikin nasa suka nufi inda ayarin jama'arsa suke tsayuwar jiransa, ganinsa tare da

Please Login or Register in order to submit comment