Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, dubu uku zan saya kuma ke da kike surutu ai idan na saya to tanadi nake miki kayan lefanki ne."

Murmushi tayi kafin tace."Uwale nifa jikina yayi sanyi sai nake ganin kamar burina ba zai cika ba."
Murya na rawa ta karashe maganar.

Tace."Aa ki daina sanya damuwa a ranki insha Allahu ba zakiyi zaman banza ba UMARU zai aureki koda baya sonki to ni zan umarceshi ya aureki.

Tace."Aa Uwale ni nafi so ya aureni dan yana sona bana so muyi irin wannan auran da iyaye suke hadawa daga baya a samu matsala."

Tace."Insha Allahu ba za'a samu matsala ba, domin ni kaina na gaji da ganinsa a haka babu aure sa'anninsa sun jima da aure da 'ya'yansu amma shi yana zaune a haka, idan za'a biye masa to zai kare rayuwarsa a haka wannan dalilin yasa zan tilasta masa auranki."

Hawaye ta share tana girgiza kai, itafa kwata-kwata bata son irin wannan auran tafi so da bakinsa ya furta mata kalmar so, amma dole haka zata hakura tunda yaki gane irin son da take masa. watakila idan Allah ya kaddara auran nasu Allah ya sanya masa kaunarta a cikin zuciyarsa.

Tace."Ki goge hawayenki ki daina kuka mutukar ina raye to kamar kin auri UMARU kin gama, shiyasa duk tsumi da tanadina ya kare akanki gashi cikin ikon Allah na kusa kammala hada miki lefe, kinga sai komai yazo da sauki."

Tace."Nagode Uwale Allah ya tabbatar mana da alkairi" Ta amsa da "ameen" tana kokarin tashi, Rakiya tayi sallama, gabadaya suka amsa, Uwale tayi saurin fadin." Yanzu nake maganarki a cikin raina nace har gida zanje na kai miki kudinki."

Tace."To ai baki fada min nawa kika sayi atampopin ba."

Ta ya mutse fuska da fadin." Gabadaya dubu uku na saya domin dai kema kin san atampopin naki an daina yayin irinsu bayan hakan haka kuma sun jima a ajiye sai warin ajiya suke."

Rakiya ta mika hannu da fadin." Ban siyar a hakaba bani na kai inda za'a saya da mutunci."


Baki ta bude da fadin." Rakiya ina zaki kai a siya da mutunci bayan nan, kin san dai idan kika kaiwa Delu siyan banza za tayi miki gwara ki tsaya mu sassanta."

Taja tsaki da fadin." Ai har gwara Delu a kanki Uwale sai kace kayan sata zaki saya dubu uku duk daya a kasuwa dubu biyu da dari biyar ce, idan sayan mutunci zakiyi ina laifi ki saya dubu biyar gabadaya."

Tace." Oh!oh zan dai saya dubu hudu idan kin sallama min a haka."

Jim tayi kafin tace."Na siyar miki amma kada ki tsinka min kudi ki bani kudiba cif."

Tace."Maganar kike so Rakiya ai a inda ba kasa anan ake gardamar kokawa da ban shirya ba ai ba zan karbi kayanki ba."

Rigar jikinta ta daga ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta kudi ta fito dasu, a dukunkune yawanci duk 'yan dari biyu ne, duk sun ya mutse, Hamra'u tasa hannu suka lissafa dubu hudu kudin me kayan ta mika mata da fadin." Gashi maganin karya hallara ki lissafa a gabana na san halinki kada ki dawo kice min basu cika ba." Rakiya ta dangwali yawun bakinta ta fara lissafa kudin ta kalleta da fadin "Sun cika." Tace."To masha Allah idan an samu wasu kayan ina bukata." Tana kokarin fita tace." To shikkenan idan an samu zaki jini."
Bayan fitar Rakiya daga gidan itama Uwale kayan dillancinta ta dauka ta fita, ya rage saura ita kadai a gidan, ta jima tana sakawa da kwancewa kafin ta tashi cikin sanyi jiki ta gyara gidan tsaf ta kulle da kwado, gidan Tasallah ta shiga ta bayar da mukkulin kafin ta kama hanyar gidansu, salo-salo take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki........."Hamra'u." da sauri ta juya jin muryar kawarta Zabbah, taja ta tsaya tana wasa da karan dake hannunta har ta karaso gurin da faratin goro da lemon tsami a kanta.

Zabbah ta karaso inda take da fadin." Daga ina kike haka naga duk jikin a sanyaye."?

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Daga gidan yayar mahaifina nake kullum ina zuwa nayi mata aiki kafin ta fita.

Zabbah ta fashe da dariya irin ta shakiyanci kafin tace."Hamrau kenan wai kenan kina kamun kafa ko? wallahi kina wahalar da rayuwarki domin kaf cikar karkarar nan banga wata mace da zata ja ra'ayin *GOJE! ba*

Tace." To ke Zabbah waye ya fada miki ina kamun kafa da Uwale a matsayin uwa take a gurina laifi ne don naje gidanta."

Zabbah ta tabe baki da fadin." Hamra'u bari na fada miki abunda baki sani ba, kaf 'yan matan garinan babu wacce bata san halin da kike ciki akan *GOJE!* ba kowa ya san kece kike sonsa baya sonki kullum sai kinji kinyiwa kakarsa aikace-aikace sai kace baiwa bayan haka ance idan yana gari kece kike masa wankin kayansa ki goge ki wanke masa takalma saboda rashin hankali irin naki kin mayar da kanki yar aiki bayan baki da tabbacin zai aureki.

Tace."Zabbah! duk abinda kika fada hakane babu karya ina san UMARU kuma ina rokon Allah yasa ya zama uban 'ya'ya na, bayan haka kuma duk wata bauta da nake masa ra'ayi na duk surutun da jama'a za suyi akan hakan bai dameni ba."

Ta girgiza kai da fadin." Shikkenan ai tunda kinyi nisa duk abinda zan fada miki a yanzu ba zaki fahimta ba, saboda haka muna zuba ido muga yanda za'ayi wannan auran.

Shuru kawai tayi bata sake magana ba, ita Zabbah ce keta surutu tana bata labarin saurayinta wanda zata aura uffan bata ce ba har suka rabu da juna.

Cikin kunci da damuwa ta shiga gidansu, nan ma ta iske wani bacin ran don mahaifiyarta fada ta rufeta dashi sosai tace."Ina ji ina gani kinfi karfina Hamra'u! saboda kulafucin namiji kullum da gari ya waye hankalinki na wani guri kisa kafa ki fita ki barni da aikin gida, kina can kina bauta a wani gurin, to wallahi nagaji ba zan hanaki ba tunda ke ki kasa kanki amma ba zaki kara fita ba sai kin gama min aikin gida."

Daki kawai ta shige tana kokarin danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin da wane bala'in za taji? ko'ina babu sassauci, bata samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai a gurin Uwale ita kadai ce ke kwantar mata da hankali, amma ita kanta wacce ta haifeta kullum habaici take mata akan wanda ta kwallafawa rai! kowa yana ganin laifinta bayan itama ba ita tayi kanta ba, Allah ne ya halliceta ya sanya mata soyayyar wanda bai san ta nayi ba, dole idan ya dawo ta cire kunya ta sameshi da maganar ko ta san matsayinta..




*Don Allah idan ba sayan littafi zaki ba kada ki dauki number ta Nagode🙏🏻*



*Ga mai bukatar Sadauki Omar 1k zai tura domin samun damar karanta littafi biyu Goje sadauki Omar return*
*#500 via 0542382124......Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari Katin airtal ko Mov
Aa


*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE

*29&30*
Kusan a tare suka d'auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d'an ja k'aramin tsaki da fadin." Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama."

Beso ya tanka a cikin al'amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar yasa yace." Akwai irinsu da yawa wa'inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu nada sarauta ko wani muk'ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al'umma jarabtace kawai daga Allah.'' Yace." Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki Allah ya shirya mana zuria baki d'aya." Ya amsa da ameeen ya Allah.

Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin 'yar tsokana Asp din yace." Akwai abinda na manta ban tambayi *MAI DAWA!* ba."?
Murmushi yayi da fadin." Akwai sauran tambayoyi kenan."? Girgiza kai yayi da fadin." Tambaya daya ce shin kana da iyali kuwa.''?

Girgiza kai yayi gami da dan ta'be bakinsa.........Asp ya dan zare ido da fadin." Kana nufin babu iyali kenan."
Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa.

Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin." Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji mata hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu." cike da alhini ya kare maganar.

Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace." Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.''

Yace." To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d'aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da yardar Allah sai na cike domin ina da ra'ayin hakan."

Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci a tsakaninsu."

Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani."

Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da godiya a gareshi.


****
Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa.


***
Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu.


Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani.

Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi masa bayanin abinda yake tafe dasu.

Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi.

Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron Allah."!

Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace." Tayi masa bayani abinda yake tafe da ita.

Hanci ta fyace kafin." Tace "Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d'aure kuna zarginsa da ta'addanci bayan ba haka gaskiya take ba."

Yace." Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu." Ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta, tace."Nagode sosai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da 'ameen kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa.

Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa abinda ke faruwa.
Ya k'ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin shigowa dasu.

Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi'i da 'yarsa suka zauna kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take sosai tana bashi hakuri.

Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik'ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri.

Ita kuma fadi take." Ku za'a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba.

Hankici ya ciro daga jikinshi, ya goge mata hawaye yana sake kwantar mata da hankali, sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya umarcesu da cewa subi bayan shi.


Kai tsaye ke'bantaccan gurin da aka ajiye shi suka nufa...........Aps din a gaba suna bayansa, yana shiga sai ya basu hanya. gabadaya suka hada ido dashi yana zaune kasan kafet da tire din abinci a gabansa tsaf dashi da nutuswa a tare dashi bashi da wata matsala bayan sararin! dake daure da kafafunsa

Hamra'u da gudu ta iske inda yake, kawai sai ta fad'a kansa tana wani irin kuka! wanda yake nuna tsantsar tashin hankalinta, itama Uwalen da kuka ta karasa gurin duk da ganin da sukayi masa cikin nutsuwa hakan be gamsar dasu ba.

Asp ya juya ya fita yana jimamin al'amarin.

Tun bayan data fad'i jikinsa yasa hannu a bayanta yana dan bubbugawa, a Hankali cikin taushin murya yake rarrashinta, ta dago kai tana kallonsa hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta, kai yake girgizawa alamun ta daina kukan, yasa hannu ya goge mata fuskar sosai yake mamakin irin k'aunar da yarinyar take masa, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai dai har yanzu bata saki hannunsa ba ta rike tsam a hannunta.


Ya d'ora idonshi kan Uwale da ta dage tana kuka sai kace wacce aka nuna mata gawarsa.

Murmushi yayi tare da mika hannunshi kan fuskarta hawayen ya share mata da fad'in." Kukan bashi da Fa'idah Uwale addua zaki min."

Tace."UMARU kukan shi yake kansa yin kuma shine samun salama, amma a zahirin gaskiya muna cikin tashin hankali bamu da kowa sai Allah shine kuma zai fitar damu."

Yace."Kin gama magana tunda ki kace Allah, kuma gaskiya tayi halinta tun kafin tafiya tai nisa gaskiya ta bayyana cewa wanda suke zargi bani bane nima kuma na san da hakan saboda haka ku kwantar da hankalinku insha Allah zan fito lafiya na cigaba da rayuwa da ikon Allah."

Tace."Idan hakane mai yasa basu kwance maka wannan d'aurin ba, duba fa yanda kafafunka suke daure.

Yace."Akwai dalilin da ya sanya hakan wannan ba matsala bace kada hakan ya daga muku hankali."

Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi musu.

Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin! tace."Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye wannan sana'ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya.

Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba.


*****
Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta........wani lotoin ta dauka tana jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska.

Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara'a sosai domin da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango.

Fuskarta yalwace da fara'a ta 'karasa shiga dakin da fadin." Yawwa kin fito ko ga kaya nan na ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.''

Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin." Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki ba."?

Tsaki taja da fadin." Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode."

Ranta ya 'baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace." Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci ."

Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta.

Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta.

A yatsine tace." Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba.

Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa a jikinta.

Jinjina al'amarin tayi kafin tayi 'yar dariya da fadin." Lallai 'kawata kina ji da gayu amma idan ba haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki." Cike da wasa ta karashe maganar..........Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin." Ke kin san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar."? Ta'be bakinta tayi tace." Ina zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b'akuwa shiyasa nake karramaki bahaushe yace." bakon ka Annabin ka."

Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna..........Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana mamakin al'amarin.


Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.'' Ya akayi ne? bata gama shiryawa bane."?

Baki ta dan ta'be kafin tayi 'yar dariya da fadin." Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man da zata shafa."

Cike da mamaki tace." Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi mata."?

Tace."Hakan take nufi."

Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba.

Da murmushi a fuskar matar gidan tace." Kin fito."? "Umm." tace kawai ta nemi kujera ta zauna sai wani basarwa take.

Ta kalleta da fadin." Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki dauko mata wasu."

Tace."Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso ba tunda ta fini kiba."

Ta kalleta da fadin." Zinatu baki takura ba dai ko."?

Girgiza kai tayi da fadin." Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka suke." Tace." To masha Allah ku tashi muje muci abinci." kusan a tare suka mike kai tsaye gurin cin abincin suka nufa.



To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad'a komai ya turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa'inda da ke da alhakin hakan, sai dai ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta'addancin zasu shiga sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma governor yayi na'am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar.


*'Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN DABA!* *bashi da ala'ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara karya alkadarin d'an ta'addan da ya addabi kasa da al'ummar dake cikinta, domin tabbatar da gaskiyar magana kakakin rundunar 'yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a jallo...........Sannan kakakin rundunar 'yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu haka akwai d'iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu 'bata gari sunyi kidnapping d'inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha'kan su bai cimma ruwa ba sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta'addanci mai suna UMARU wanda jama'a suka fi sanin sa da GOJE!* *shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta bayan ya samu nasara akan wa'inda sukayi garkuwa da ita............Wannan shine cikakken rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.*


Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin bayyanuwar ta............Fada ta cika da jama'a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta da 'yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga.

Gimbiya Aysha da 'yar uwata tare da 'ya'yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin 'yan uwanta ta nufi b'angaranta jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai....



*Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! 😄 kada ki sake ayi bbu ke 'yar uwata kada ganin k'yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai kankantarta!!!*


*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin mov ko airtal



*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE

*23&24*
*Biyu da rabi na sulusin dare!*
Cikin firgitaccan yanayi ta tashi zaune tana kiran sunan Allah! hakan ya janyo farkawarsa dama can bashi da nauyin bacci, zaune ya tashi kafin ya rike hannunta dake wani irin rawa, yace."Menene Aysha."? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka ta rungumeshi tana girgiza kai da fadin." Zinat ce ranka ya dade yarinyar nan na cikin mugun yanayi Allah ya nunan hakan a mafarkina."

Sake rungumeta yayi a jikinsa cikin sigar rarrashi yace."Aysha mafarki ba gaskiya bane kada ki gazgata abinda ki ka gani, bana tsammanin cewa mafarkinki zai tabbata, jikina yafi bani cewa yarinyar nan tana a raye kuma daf take da ta dawo garemu da ikon Allah."

Kallonshi tayi hawaye na tsere a saman fuskarta tace.''Ranka ya dade koda Allah ya nufa yarinyar nan ta dawo gida bai zama lallai a sameta da cikakkiyar lafiya ba ka san dai yanda duniyar nan ta lalace da rashin gaskiya wannan shine babban tashin hankalina."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kada ki fadi haka Aysha! zuciyarki ta dinga halarto miki alkairi akan yarinyar nan! adduarki a gareta karbabbiya ce a gurin Allah, kada ki yarda zuciyarki ta yarda da wannan mafarki ki dauka cewa k'anzon kurege ne, a yanzu abinda zakiyi ki faranta min shine ki tashi kije ki dauro alwala ki gabatar da nafila a gaban ubangiji kana ki mika masa kukanki."

Ta sauke ajiyar zuciya da jin sassauci acikin zuciyarta, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga gadon ta nufi toilet domin daura alwala.

Tana fitowa shima ya tashi ya shiga ya daura alwalar ya fito,

Please Login or Register in order to submit comment