Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi tubus, ta kasa hanashi sarrafata.

Bai damu da kallon wasu sassan na jikinta ba, domin gabad'aya babu wani feelings a tare dashi, tunda yake sai yace babu ranar da wata mace ta ta'ba tayar masa da hankali duk zubi da kirar dake gareta, Asalima yakan jima bai shiga yanayi na bukata ba, shiyasa auran baya gabanshi, wanda uwar rikonshi wato kakarsa Uwale keyi masa surutu akan hakan.

Da kanshi ya lalubi inda kunamar! ta harbeta ya shefe gurin da magani, ganin duk yaran nashi sun bar gurin yasa ya bude mata jikin domin qunar tasha iska.

Har ya gama abinda yake a gurin bata daina zubar da hawayen takaici ba, tayi turr! da wannan rayuwar da take ciki, a tunaninta hanya ba zata iya had'awa dashi ba, sai gashi w *Kazami- Bagidaje!* irin sa yana ganin sirrin jikinta. tana ganin wannan ko hadimanta (masu yi mata bauta) sun fishi kyawun gani sai gashi a banza yana yin yanda yake so a kanta ya tatta'ba jikinta babu tsoro ko shakka a tare dashi hawaye masu zafi ta goge tana jimanta al'amarin.


Taji dadin maganin sosai domin tana tsaka da tunanin hanyar da zata bi domin kubutar da rayuwarta bacci mai nauyi ya dauketa.

*****
Kana ganinta kaga bafulatana, doguwa ce sambal kyakykyawa a fuska, gata fara tas! ta tara duk wasu abubuwa da da namiji ke bukata amma hausawa sukace wai Dan Adam tara yake be cika goma ba, Hamra'u bata da cikkar kirji hakanan kuma babu baya a tsaye take kamar muciya da zani, sai dai akwai tarbiya da kunya irin ta fulani.

A nutse tayi sallama a gidan, Uwale dake uwar daki ta amsa, da fadin.'' 'Yar halak yanzu nake maganarki a zuciyata.

Murmushi tayi ta cire takalminta, ta shiga dakin, Uwale na kurbar kunu ta mika mata kofin da fadin " Bisimillah."
Girgiza kai tayi tana murmushi tace." Ai daga gida nake kuma sai dana karya kafin na fito.

Dariya tayi irin ta tsoffi tace." Hamra'u kenan wai me yasa duk sanda zan baki abu sai kice daga gida kike ko dai kankyamina kike ne."?

Da sauri tace."Aa Wallahi ba haka bane Uwale na koshi."

Tace."To ai shikkenan duk ya mutan gidan."? Tace."Suna nan lafiya lou alhamdullhi babanmu yace a gaisheki da kyau.''

Tace."Ina amsawa ai a cikin satin nan nake so nazo gidanku mu gaisa sai kuma *UMARU* Yayi tafiya gashi zai dauki sati guda bai dawo ba.

A sanyaye tace."Yanzu fa nake shirin tambayarki ina yake shine zakice yayi tafiya kuma sai yayi sati zai dawo."


Tace."Eh haka yace min da zai tafi kin san dai yanayin al'amuranshi, wani sa'in ma har wata guda ya kanyi yana gwagwarmaya a daji"

A raunane tace." Ni wallahi ba naso yana irin wannan yawace-yawacen tsoro nake kada 'yan fashi su kasheshi ko kuma namun daji su cinyeshi."

'Yar dariya tayi tana sud'e kofin kunun data gama sha tace."Sai dai kiyi hakuri Hamra'u wannan mijin naki yayi nisa addua kawai zaki dinga yi masa.

Tace."Kullum inayi masa addua tare da sauran jama'a." Tace."yawwa hakan yana da kyau, sannan ki cigaba da hakuri insha Allahu, hankalinsa zai karkato kanki."

Idonta ya cika da ruwan hawaye, tace."Uwale sai nake ganin kamar baya sona tausayina kawai nake gani a kwayoyin idonshi.

Tace." To in banda abinki Hamara'u ai sai da so ake tausayi, da baya sonki ba zai tausaya miki ba."

Shuru tayi tana nazarin maganar, itafa tunda take dashi babu wata kalmar so daya taba furta mata, asalima yana kiranta da kanwata, amma bai taba cewa Hamra'u ina sonki ba, sai dai yana tsananin bata kulawa komai take bukata idan tayi masa magana kai tsaye yake mata, wannan dalilin yasa iyayenta da ita Uwalen suke ganin kamar sonta yake, ajiyar zuciya ta sauke ta kudire a ranta cewa idan ya dawo zata cire kunya ta tambayeshi matsayinta a zuciyarsa.

Hamra'u 'yar kanin Uwale ce, tun tana yarinya Allah yasa mata so dakaunar Goje tun be fahinta ba har Allah ya fahintar dashi, be ajiyeta a wani matsayi na daban ba face wanda take dashi a zuciyarsa, gabadaya tunda ya taso baya da ra'ayin soyayya, shiyasa baya fahimtar tarin 'yan matan dake k'aunarsa, Samari da yawa a karkarar tasu suna kishi dashi, a cewarsu sai kace shi kadai ne namiji ko wacce budurwa bata da magana sai tasa, ransu yana baci mutuka, suna kuma bala'in kishi a kan haka, ita kanta Hamra'un akwai wanda yake mutuwar sonta amma fafur taki amince masa ita dai Umaru takeso wanda bata da tabbas a kansa..............

Uwale, kayan dillacinta ta dauko ta nada gammo ta dora aka, tana gyara yafan mayafi take fadin."Hamra'u ni zan fita dama a irin wannan lokacin nake samu na nemi halalina idan kin gama gyara min gidan ga kwado ( dan mukulli) akan taga ki kulle gidan ki bawa Tasallah ta ajiye min."

Tace."Uwale inace Yayana ya hanaki yawon dillaci nan kuma kin san Babana ma baya so me kike bukata ne a duniyar nan."

Tsaki taja da fadin." Sai kiyi kuma kinga tafiya ni babu wanda zai hanani neman kudi." tana gama maganarta tasa kai ta fita daga gidan.
Hamra'u girgiza kanta kawai tayi idan da sabo ta saba da hakan , a nutse ta mike ta fara ayyukan dake gabanta....

***********
*WAIWAYE*
K'allo d'aya nayi masa na fahimci wanene a gabana, ko da yake koda zanyi shekara d'ari ba tare da na sanyashi a idona ba to ba zan mance kammaninsa ba, *Sadauki Omar* kenan Sarkin dake kan karagar mulki a jahar *Kano* Adalin sarki wanda al'ummarsa ke jin dadin mulkinsa.

Yana nan a yanda kuka san shi tsayayye! kuma jarumin namiji! kamanninsa suna nan sai dai alamun girma da ya baibayeshi amma a tsaye yake da jarumta babu abunda ya samu nakasu a cikin halayensa da d'abi'unsa.

Yana tsaye a tsakiyar babban falonshi hannuwansa goye a banyanshi yana kai kawo a gurin, kallo daya kayi masa zaka fahimci yana cikin damuwa.


Cikin nutsuwa da kamala tayi sallama be juyo ba ballantana ya amsa sallamarta,
kai tsaye inda yake ta nufa, sai na bita da kallo, ina hasashen a inda na san fuskarta, Gimbiya *Aysha ce fa* zuciya tayi saurin tuna min ita

Cike da dumbun mamaki nake kallonta tana sanye cikin laffaya milk color da adon zaiba kafarta sanye da takalmi rufaffe irin na sarauta, ban hango wata tawaya a tare da ita ba domin kuwa jikinta ya nuna alamun hutu da jin dadi sai dai alamun shekaru sun tura hakan ma sai ka 'kura ido a kanta sannan zaka fahimci cewa ta kwana biyu a duniya.

Hannunta ta d'ora kan kafadarsa, a nutse ta kira sunanshi *"Jarumi."* be juyo ba ballantana ya kalleta, sai ta dora kanta kan kafad'arsa, hawayen da take boyewa suka kufce, wai shin ya za suyi da wannan ibtila'in da yake kokarin ruguza musu farin cikin da suke ciki na tsayin shekaru masu yawa................




*Ga wanda bai samu damar karanta Sadauki Omar ba, zai tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu tare da Goje! Sadauki Omar return*



*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Mutanan Nijar zaku turo min katin Mov ko airtal na Dala dari.



*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE
*7&8*
_*Banyi tsammanin rubuta wannan littafin a kusa ba, asali ma nayi wa kaina alkawari cewa na daina sakin littafi sai na kammala, amma cikin ikon Allah ya nufe ni da fara rubuta wannan littafin ba tare da nayi tunanin hakan ba, ina rokon Allah ya bani hakuri da juriyar rubuta abinda za'a amfana dashi, sannan ina mika godiya ga dubbanin masoyana wanda na sani da wanda ban sani, hakika duk wanda Allah yayiwa baiwa ta jama'a dole ya gode masa, babu abunda zance da masoya sai godiya da fatan alkairi, sannan a cigaba da hakuri da yanayi na rayuwa, koda zanyi wa wani laifi a bisa rashin sani to ina neman afuwa🙏🏻 d'an adam ajizi ne, ina fatan zaku bibiye ni a wannan littafin nawa mai suna a sama, ku bani hadin kai sannan ku bini a sannu a hankali domin isar da sakon dana dauko, #500 kacal zaku biya domin karanta cikakken labarin.*_


*WANNAN NAKI NE*
_(AUTAR MANYA)_
*A cikin marubuta ke ta dabban ce a gurina🤝🏻🥰*


Jin kukanta yake har tsakiyar kansa, koda can baya son ganin tana zubar da hawaye ballanatana yanzu da ta riga ta zama garkuwa a tare dashi.
Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo tare da rike kafad'unta, hannu yasa ya share mata hawayen dake zuba a saman fuskarta, ta rike hannunsa da fadin.'' Ka bari nayi kukan domin shi kadai zanyi na samu sassaucin abinda nake ji a cikin zuciyata."
Ya girgiza kansa da fadin." Ke kin san bana son zubar hawayenki Aysha me zai sanya ki kara tayar min da hankali bayan wanda nake ciki."
Ta tsira masa idanuwanta wanda suke cike da ruwan hawaye " Me yasa ka kasa fahimta ta? me yasa ka dauki laifi kacokan ka dora a kaina bayan idan adalci a za'ayi kaine babban mai laifi dangane da faruwar wannan al'amarin."

Girgiza kansa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin zafi da k'yar ya iya magana." Bani da laifi Aysha ba zan haifi d'a a cikina na lalata shi ba, ba zan gaji da fadi miki cewa tarihi ne yake maimaita kansa."

Ranta ya 'baci da jin furucinsa, a duk sanda zai fadi wannan kalmar akan wannan al'amarin sai taga kamar akwai rashin adalci a cikin maganarsa.

Tana kokarin magana, Safa ta shigo da sallama a bakinta, suka amsa tare da bin ta da kallo har ta karasa inda suke tsaye. fuskarta kadai zai nuna maka cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tare da ita, ba ita ta haifi Yarinyar ba amma tafi kowa shiga tashin hankali da rashinta.

A raunane ta kalleshi da fadin.'' Ranka shi dade har yanzu babu wani labari ko."?

Kanshi ya daga da fadin." Babu wani labari Safa watakila ma yarinyar nan bata raye domin duk iya binkice anyi amma ba'a samu wani labari mai dadi ba."

Kuka ta fashe dashi, ta nemi guri ta zauna tare da rufe fuskarta da tafikan hannayenta.

Ganin tana kuka yasa Aysha da sauri ta kama hanya domun fita bata so duk su lalace a gurin koke-koke domin mutukar tana kallon kukan Safa to itama zata iya taya ta.

Karo sukayi da juna, Aysha kanta a kasa yake shiyasa bata ga shigowarta ba, Maijidda ce matar mijinsu, da ya aureta bayan shekara masu yawa da suka wuce.

Kasancewar basa shiri da juna yasa tayi saurin kauda kanta ta wuce, ita kuma hamshakiyar ta bita da wani irin kallo kafin ta ta'be bakinta cikin wata irin tafiya ta isa da ta'kama tayi sallama a falon.

Shi kad'ai ne ya amsa sallamar Safa har yanzu kuka take yana tsaye ya gaza rarrashinta shima da zai samu yayi kukan da yaji sassauci a zuciyarsa.

Wawan kallo takewa Safa kafin tace."Ke a ganinki hakan kauna ce? kullum baki da aiki sai kuka uwar data haifi yarinyar ma har ta fiki dauriya Safara'u kuka bashi ne mafita ba."

Safa ta dago kanta tana kallonta da mamakin furucinta, za tayi magana kenan, Yace." Abinda nake ta so su fahinta kenan yanzu ita kanta Ayshan ta gama nata ta fita, na fada masu cewa addua itace abinda ya cancanta.

A tausashe tace."Hakane ranka ya dade shiyasa ko kadan ban zubar da hawaye na akan wannan al'amari ba, abinda nayi shi ya cancanta, ya kuma kamata, tun ranar da al'amarin ya faru na sanya almajiran mahaifina suyi saukar al'kur'ani na tsayin sati guda, da izinin Allah yarinyar nan tana hannu nagari za kuma ta dawo gida cikin aminci."


Safa ta watsa mata wani irin kallo na zargi kafin ta tashi tare da kama hanyar fita.
Sunanta ya kira ta juyo tana kallonsa babu walwala ko ta kwabo a fuskarta.

Yace."Kada ki cigaba da wannan kukan bashi da fa'ida ko kadan addu'a zakiyi kinji ko."

Ba tace masa komai ba ta fita ta basu guri, kai tsaye sashen Aysha ta nufa, ta sameta tare da babban yaron su wanda suke kiransa da magajin Sarki.

Tana shiga ya mike tsaye yana mata barka da zuwa, ta zauna kusa da 'yar uwata kafin ta bashi umarin zama.

Ya zauna kasan kafafunsu, a nutse yace." Mommah don Allah ku kwantar da hankalinku bana so naga daya daga cikinku na zubar da hawaye ni nayi imani da Allah da manzon Allah yarinyar nan tana hannu nagari da yardar Allah zata dawo gida cikin koshin lafiya.

Aysha bata iya magana ba, Safa tace."Babana ina mamaki idan naji kai da mahaifinka kana maganar mu kwantar da hankalinmu, ta ina hankalinmu zai kwanta? a cikin wannan yanayin yarinyar nan sace ta akayi kuma akwai sanya hannun makusanta bana shakka a cikin maganata."

Yace."Hakan tana iya kasancewa amma Mommah kada ki manta fa yarinyar *Zinatu* bata jin maganar kowa kuma a daran da al'amarin nan zai faru gabadaya sai da kuka hanata fita amma saboda rashin tarbiya ta tsallake maganarku to me zai sanya hakkinku be bibiyeta ba."

Shuru sukayi domin kuwa babu mai bakin magana a cikinsu, abinda ya fada gaskiya ne, yarinyar ta fita zakkah a cikin zuriarsu, sai kuma Allah ya jarabcesu da tsananin sonta, shi kansa maimartaba wato mahaifinta baya son laifinta, ko kad'an duk da ya san abubuwan da take na rashin kyautawa a masarautar duk zafinsa baya iya tsawatar mata, sai 'yan uwanta mata dake gidajen auransu suke tsaye a kanta, wani sa'in su din ma bata saurara musu rashin kunya take musu kuma ta kwana lafiya, babu wanda take shakka sai shi Magajin sarkin, shima a bayan idonsa zaginsa take tana fadin be isa ya hana rayuwar jin dadi tun bayan dawowarta daga kasar waje bayan ta kammala karatunta ta dawo da mugayen dabi'u irin na turawa, duk wanda ya nuna mata kuskure akan abinda take cewa zai shafi masarauta da martabar mahaifinta sai ta d'aura gaba dashi, halin da ake ciki shi kansa Magajin sarkin ba tayi masa magana saboda yana tsawatar mata akan abubuwan da take na rashin tarbiya, jin kade - kade sanya matsatsun kaya bayan baiwar da Allah yayi mata na qira, yawace-yawacen pary cloub club babu inda bata shiga tayi b'arna da kudi da famkama da manya motoci ta fito babu abunda ya dameta.
Da yawa mutane ba sayi mata kallon cikakkiyar mace saboda mummunan dabi'unta. Don akwai lokacin da wani babban malami ya nemi ganawa da maimartaba akanta, suka tattauna sosai maimairtaba ya fahimceshi ya san me kaunarsa shine zai zo har gabanshi ya fahimtar dashi abunda ya shige masa duhu, a lokacin ya tashi tsaye a kanta, kuma ya gargadeta kan cewa mutukar bata sanja hali ba to zaiyi mata aure duk wanda yayi ra'ayi, hakan ya tsorarta da ita, tayi sanyi na kwana biyu amma kwanaki suna turawa ta cigaba da abinda take, Gabadaya sai ya dauki al'amarin ya jinginashi a matsayin jarabta, abin na damunsa mutuka amma ya rasa me yasa baya son bacin ran yarinyar, Dan uwanshi, Abbas wanda yake Waziri a gareshi ya bashi shawara kan cewa aurene kadai abinda zai daidaita nutsuwar yarinyar saboda haka shi zai umarci babban yaron sa domin yazo su fahimci juna, maimartaba yaji dadin shawarar dan uwansa.
Koda Taufiq ya sameta domin bin umarnin mahaifinsa rufe ido tayi taci masa mutunci harda zagi kamar ba jininta ba, aikuwa ya fusata! ya gaggaura mata mari hade da farfada mata mumunan magana, "Bani da ra'ayi auran mace mara tarbiya irinki umarnin mahaifina nabi har nazo neman auranki saboda haka wallahi ko ba dazi rasa mijin aure ba zan aureki ba shashaha mara hankali kawai "
Bata saduda ba tana kuka tana zaginsa, Magajin sarki ya samu labarin abinda tayi wa abokinsa ya shiga har dakinta ya zaneta da belt ya fito yana huci! Gimbiya Aysha na zaune a falo yazo ya wuce ba tace masa komai ba.

Washe gari ta hada kayanta kaf ta koma sashen Safa, itama anan din bude mata wuta tayi ta nuna mata kuskuranta, kafin ta bar sashen sai da tayi mata rashin kunya tasa wata baiwa ta daukar mata akwatin kayanta ta nufi sashen Maijidda, a maimakon ta nuna mata kuskuranta, sai ta hau rarrashinta ta nuna mata cewa itake da gaskiya kuma ba zata bari ayi mata auran dole ba, a takaice dai da sanya hannun Maijidda komai ya lalace! itace kuma ke daure mata gindi tana iskanci iya son ranta.


To wannan dalilin yasa ita Ayshan take ganin harda sa hannunsa dana matarsa gurin lalacewar yarinyar, amma tun sanda al'amarin ya faru ya dauki laifi ya dora mata, kullum idan zai budi baki magana daya yake fada *(Tarihi ne zai maimata kansa)* tana jin bala'in haushin wannan magana, ta san a lokotan baya tayi sharafi amma abinda tayi be kai wanda ita yarinyar keyi ba, dalili iyayenta da tayi rashinsu a halin yanzu a tsaye suke a kanta, abunda tayi be kai wanda 'yar cikinta keyi a yanzu ba, ita dashi suka san hakan, amma idan ya tashi magana saboda rashin gaskiya a gaban kowa fadi yake abinda yarinyar take gado ne don haka itace sila akan faruwar al'amarin.
Ta kalli Safa bayan fitar yaron nasu, tace."Duk ranar da Maijidda ta sake magana al'amarin nan sai tayi data sani domin duk irin abinda take aikatawa ina fahinta na gane itace ke zugashi yana daukar laifin yana dorawa a kaina."

Safa ta girgiza kai da fadin." Eh ba zan hana ki ba ni kaina zan tayaki cin mutuncinta domin ta kai ni bango abin mamaki kuma har yanzu laifinmu yake gani, akan hakan ta shigo ta sameni cikin halin damuwa tana min maganar banza ya goya mata baya, ta kaini karshe duk sanda ta sake min katsalandan a gabanshi zan taka mata burki sai dai duk abinda zai faru ya faru."

Tace."Safa ba zaki iya dasu ba, ki kyaleni ita dashi duk zanyi maganinsu, nagaji da wannan abun zanyi magani."

Zuciyarta tayi sanyi da jin furucinta, ba tun yau ba, ta san halin Aysha ba kanwar lasa bace da sannu za tayi maganinsu gabad'aya.

*********
Lokacin data farka garin yayi duhu, kuma bai kunna fitila ba tun bayan daya gabatar da sallahr isha'i sai ya kishingida a gefenta, saboda ita ya sanya bai jagoranci yaran sa farauta ba, sai kawai ya turasu daga shi sai ita ya rage a gurin, sai kuma kukan 'kananun dabbobin dake tashi.

Cike da tsananin tsoro! da firgici! ta mike zaune tana lalube a gurun, masifaffan tsoro ne da ita, rarrafe ta fara ko'ina zata oho! yana kokarin tashi zaune ta afko kansa, fuskokinsu suka hadu, bakinta ya hadu da nasa, lokaci guda numfashinsu ya had'u! da sauri ta kautar da fuskarta, ta danne kirjinsa da hannu tana kokarin barin jikinsa, ba tare da wata manufa ba ya zuba dukka hannuwansa kan kwankwansonta, gefe guda ya ajiyeta, ta sake yunk'urin barin gurin domin kan ciyayi a ajiyeta tana kuma jin tsoron wani mugun k'waron ya cijeta, kafarta daya ya rike, can kasan makoshi yace." Ki samu nutsuwa."! kafarta ta fizge, da rarrafen ta lalubi daddumar ta zauna tana ya mutse fuskarta, gabadaya cinyoyinta sun dauki kaikaiyi da azabar zafi.

Fitila ya kunna yana kallonta, sai yamutse ya mutse take, mikewa yayi ta kalleshi, yana kokarin barin gurin, da sauri tace." Ina zakaje."?

Bai juyo ba domun ji yayi tambayar tayi kama data rainin hankali sai kace uwarsa tana masa magana gatse-gatse! Ya cigaba da tafiyarsa ba tare da ya amsa maganarta ba, kallonsa ta dinga yi tana mamakin girman jikinsa dogo mai garin jiki yana yanayi da jarumin kasar hindu *( Parbahs bahubali)* idonta a hanyar da yabi gabanta sai faduwa yake, can taji wani irin kukan dabbah! a bayanta, a zabure! ta juya tana zare ido! jin kukan na kara kusanto inda take yasa ta kurma ihu! sai ta fara jan gwiwa tana waiwayenta bayanta.

Jin ihunta ya tashi hankalinsa da saurin gaske yasa bakin kokon dake hannunsa ya kamfaci ruwan dake gudana ya juyo da saurin gaske, me zai gani ita ya hango a gigice! tana rarrafe tare da d'aga masa hannu, haushi ta bashi, bega abun gudu a gurin ba, tuntuni sun saba yada zango a gurin, babu wata dabbah mai cutarwa da ke zuwa gurin. saboda su kansu dabbobin sun gane gurin, basa tunkarar zuwa sun san idan sun shiga basa fitowa cikin dadin rai.

Koda ya k'arasa inda take sai kawai ta rike masa kafafu tana karkwarar jiki, "Allah yasa tsakanina daku azzalimai macuta." Kalmomin da suka futo daga bakinta kenan ta nayi tana dukan gwiwarsa harda cizo.

Gabadaya ta kanainayeshi, tana dukansa, kuka take sosai! bece mata komai ba har sai da ta gaji da kukan ta cikashi, ta daga kai tana kallonsa, ya cije baki kamar yanda ya saba idan zaiyi magana "Na fahimci duk gidan da ki kaka fito babu tarbiya, bana shiri da mara kunya ba kuma na san raini! meye laifina anan? ina iya kokarina akanki kina zagina saboda kina takama da mulki da sarauta ko."?
Hannu ta daga masa da fadin." Kaga malam ya isa haka kawai ni ka daukeni ka bar gurin nan dani."

Ya girgiza kansa kamar koda yaushe idan zaiyi magana yace."Ba zaki samu hakan ba, yanda kika rarrafo da gwiwarki hakanan zaki biyo bayana." yana gama maganarsa ya fizge kafafunsa ya barta a gurin.

Da kyar tayi yunkurin tashi tsaye, ta daga masa hannu da fadin." Don Allah kada ka tafi kayi hakuri ka dawo kafafuna sunyi tsami ba zan iya tafiya mai tsayi dasu ba."

Yana jin maganarta be juyo ba ya cigaba da tafiyarsa, yana so ya fara koya mata hankali tunda ya fuskanci bata da mutunci.

Takawa take tana ciccije baki, hawaye kuwa sai karakaina yake a fuskata, abubuwa da yawa sunyi mata dabaibayi, ciwo! tsananin fargaba da tashin hankali bakar azaba da yunwa ta rasa da wane bala'i za taji.

Tun tana hangensa har ta daina, ta dinga tafiya cikin ciyayi tana jin saukar kwarika a kafafunta, ta riga ta saduda ta barwa Allah da wannan masifar da take ciki gwara wata dabbar ta cinyeta.


Ya kai minti ashirin da isa amma shuru babu labarinta, a jikinsa yaji akwai wani abu tunda babu wata tazara mai tsayi tsakaninsu da bakin kogin.

Bayanta yabi yana haske fitilar hannunsa, yaci tuntube da ita, kwance kafafunta sun rufta cikin wani rami da alama na wasu dabbobin ne, sai kici-kici take tana kuka, hannunsa ya mika mata, ta rike da kyau! yasa karfi ya fizgota!
Ajiyar zuciya suka sauke a tare, be jira komai ba, ya sunkuya tare da juya mata baya, kafira!😂 bakin rashin kunya ya mutu, tana zazzare ido ta haye bayansa ya mike tsaye da ita, hannunta tasa sosai ta matseshi, sai ajiyar zuciya take, shi kam cakumar da take masa ta sanyashi shiga tashin hankali wanda sai yayi shekaru be shiga irinsa ba, huci kawai yake yana cizan lips dinsa,
cikin mawuyacin hali suka isa gurin,
Yayi gaggawar sauketa, tayi kwance a gurin tana fitar da numfashin wahala, shi kam can gefe ya matsa tare da juya mata baya, matsalarshi guda a yanzu halin da ya shiga, shigarsa a wahala amma fitarsa nada wuya yakan yi kwana da kwanaki kafin yanayin ya bar jikinshi.



*Ga wa'inda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu biya 1k domin samun damar karanta littafi biyu*
*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan

Please Login or Register in order to submit comment