Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin har ta tayar da sallar, jallabiya da gajeran wando ya sanja kana ya gyara dadduma shima ya tayar da tashi sallar.


******
Tun bayan daya sa'ba ta a kafad'a suke buga artabu a tsakanisu, rikon tsauri! yayi mata yana gudu tare da tsallake manya-manyan dutsina da ita a kafadarsa! tayi duk wani kokari gurin ganin ta ceci kanta abun yaci tura! domin mutumin mugun basamude! ne wanda cizo da yakushi basa shigarsa! dukansa take tana cizo duk ta dauke masa fata amma ko ajikinsa, ya riketa katamau! yana gudu! burinsa kawai ya kaita gaban ogansa ya san hakan zai faranta masa rai.

Hakan ne ya kasance kuwa, Ogan nasu yana cikin bacin rai! mai tsanani sakamakon rashin samun nasara! bai ta'ba fuskantar irin hakan ba sai a wannan lokacin, kai kawo kawai yake gurin ya rasa abinda yake masa dadi! ............Amma zuwan babban yaron sa da yarinyar ya faranta masa rai! mutuka, sai kawai ya kwashe da wata 'yar iskar dariya kafin yayi wani irin tsalle! da juyi na jin dadi, ya zuba mata kwala-kwalan idanuwansa!

Bakinsa kawai yake lasa, jikinsa na wani irin tsuma! komai na yarinyar yayi cif da cif! bata da makusa, cikakkiyar mace irin wacce ya jima bai kwanta da irinta ba!

Gurin ya tsit! gabad'aya yaransa sun zagayeta motsin kirki ta kasa, kanta ne ma yake juyawa a gurin, dishi-dishi! take kallonsa har ya karaso inda take zube!

Ya tsugana kusa da ita, sai tayi saurin janye jikinta, ya sha kunu; tare da matsawa jikinta, ta sake janyewa tana watsa masa mugun kallo!

Mahaukaciyar dariya yayi! ya cigaba da lasar lebansa, yana bin sassan jikinta da wani irin kallo na tsantsar sha'awa! Hannu ya kai jikinta, a zabure! ta fitar da hannu ta bashi kyakykyawan mari a fuskarsa! ko gezau! beyi ba sai dai yaransa da suka zabura! sukayi kanta!

Ya daga musu hannu da basu umarnin matsawa baya.

Suka matsa can nesa suka bar shi da ita, zaman dirshan yayi a gabanta ya mika mata tafkekiyar fuskarsa dake cike da kasumba! yace. " Idan hakan yana miki dadi ki sake aikatawa." Ya fada yana sake tura mata fuskar.

Tsaki mai tsayi taja! ta matsa nesa dashi! ya rarrafa kan gwiwarsa ya cimma inda take! kafafunta dake daure da takalmi ya tsirawa ido, babu abunda yafi tafiya dashi irin shara'ban kafafunta, ya kai hannunsa gurin yana shafawa da lumshe ido, janye kafarta tayi da fadin." Allah ya isa!!
Ya bude idanuwansa da suka rikice! da zazzafar sha'awarta!

"Ni kikewa Allah ya isa."? yafada yana nuna kirjinsa.

Ba ta amsa ba, wani irin kallon banza take mai, ya lumshe idonsa ya bude da fadin." Ina sonki saboda kinyi min, ban ta'ba amfani da mace na maimaita ba, amma gani guda da nayi miki naji cewa kece zaki zama mahadin rayuwarta, shekaru sun ja ya kamata ace nima na ajiye k'wai a duniya kece zaki zama uwar 'ya'yana, kinzo hannuna babu wani mahalukin daya isa ya rabani dake."

Maganganunsa suka dinga amsa kuwwa! a kunnanta, ta tsira masa ido tana mamakin furucinsa, kallonsa kawai take ta rasa yanda zata fasaltashi, shi ba mutum ba ba aljan ba.

Ya mike tsaye a kanta! saurin kauda kanta tayi gabanta na lugudan duka!

Blet din dake daure a kugunsa ya fara kokarin kwancewa, tayi saurin tashi tsaye! dariya ya fashe da ita, kafin ya cire blet din ya jefar dashi ya zame wandon............"Innalillahi- wa'ina ilahi raji'un! abinda ta ambata kenan, ta rintse idonta da karfi! tunda take bata ta'ba ganin tsaraicin namiji ba sai a kansa, yanda yake mara fasali to hakama gabanshi yake tamkar na mahaukacin doki!!

Wandon ya mayar jikinsa, yana kyalkyala dariyar hauka kafin ya fizgo kafadarta! fuskarta ya rike a cikin tafin hannunsa, ta rufe idonta gam! bata son kallon mummunar fuskarsa.

"Ina fatan kin shirya zama tare dani! masoyiyata nayi miki alkawarin baki dukkan wani jin dadi na duniya! gwarzo ne ni akowane fanni! na tabbata cewa ba za kiyi nadama da kasancewarki a tare dani ba."

Zuciyarta ta dinga tashi sakamakon warin bakinsa, fuskarta ta fizge! da karfi ta matsa can gefe tana numfarfashi! yawu ya cika mata baki! yana zuwa gurin da take ta fesa masa yawun a fuskarsa!

Ya sanya hannu ya shafo yawun yana lashewa! amma kuma fuskarsa ta rikide da alama yaji haushin abinda tayi masa.

Sai da ya lashe yawun tsaf! sannan ya kalleta, ta tsorata da yanayinsa, sai ta sunkuyar da kanta, a kausashe! yace." Wannan shine na farko kuma shine na karshe kada ki sake maimatawa idan ba hakaba zan ladabtar dake.

Ta cire tsorosa da fadin." Wawa!! kafara ladaftar da kanka kafin ka ladaftar da wani."

"Wawa!! kalmar tayi mai ciwo! sosai a ransa sai kawai ya dingi maimaita kalmar a fili yana zagayeta, ta dinga binsa da kallo duk inda yayi, ya shammaceta yasa mata kafarsa ta fadi a kasan a gurin! turmusheta yayi ya danneta iyakacin karfinsa! bakinta yake kokarin sumbata tana kautar da kai yana bin duk inda ta nufa, be fasa maimaimata maganar ba! suka dunga bugawa! domin duk yanda yaso hada baki da ita ya gagara! ta gumtse bakinta gam!!! sai ya zama kamar mahaukaci sai rawar jiki yake babban burinsa yaji yana shan bakinta.................Ba zato! ba tsammani! yaji saukar kibiya a gadon bayansa!!

Ya gantsare! tare da zabga ihu!! a zabure! ya mike tsaye! ya fizge! kibiyar ya jefar jini ya fara tsiyaya! tashin hankali kenan! waige-waige yake a gurin yana mamakin yanda akayi hakan ta faru.

Cikin zafin nama! ya mikar da ita tsaye sai numfarfashin wahala take, ya rike hannunta katamau! yana sake dudduba gurin!..................!

Wani abu dake daure a hannunsa ya murza! kafin ya kirayi yaran sa! kaf! suka kewayeshi! sai dai ganin jini na tsiyaya a bayanshi ya firgitasu! a garin ya akayi hakan ta faru!
Ya akayi ogansu ya bari aka cimmasa irin haka? a tarihin rayuwarsa kaf babu wani mahalukin da ya ta'ba fitar masa da jini sai zuwan wannan matashin saurayin lallai akwai wani abu da yake shirin faruwa!


Wani irin nishi! yake yana zazzare idonsa! shi kansa yayi mamakin al'amarin, yana da suddabaru! iri-iri! ya akayi har yaron ya samu damar ganin inda yake tare da samun damar harbinsa da kibiya!!

Sai kawai ya fasa ihu!!! ya dubi abunda ke daure hannunsa yana wasu irin surutai! ya sake murza abun! yana sambatu! gurun yayi tsit! babu mai kwakwkwaran motsi a cikinsu, domin sun shiga rud'ani da faruwan wannan al'amarin!!

Sautin muryarsa ne kawai yake tashi a gurin, yana wasu irin maganganu!..............Can kuma sai haushin karnkuna! ya maye gurbin maganarsa, Tsit! yayi gabansa na wani irin fad'uwa!!

Hankalinsu ya kai kololowa gurin tashi!! duk suna tsaye sun kasa tabuka! komai ya zabura! da karfi yace."Tsayuwar me kuke ba zaku ba zama ba har sai ya cimma na."

Da sauri suka rarrabu a cikin dajin suna neman inda yake..

Yana tsaye! a gurin sai kace dasashe! har yanzu kuma hannuta yana rike a hannunsa ya rike tamau!!


Haushin karnukan! suka cigaba da kusantowa inda yake! da saurin gaske ya fara kokarin janta tana turjewa! kawai sai ya dauketa ya sa a kafad'a, ya riketa da kyau! da niyyar neman mafaka! taku daya yayi yaji saukar wata kibiyar! ya gantsare! tare da sakin ihu!! amma duk da haka bai sauketa ba.


*"Ni ne GOJE!!! mugun! makangari sai kuree! Ni cinkun! naci garina kuma ni ke zuwa garin wasu yaki!! kandagarki kurmar dutse! mugun makangari sai kureee!*

Sautin maganarsa ya cika dajin gami da kunnuwansu.

Ya juya gabas kudu yamma arewa! domin hasashen inda maganar ke fitowa, bashi da tabbacin gurin, kawai sai ya umarci sauran wa'inda ke tare dashi cewa su tashi bomb a kowanne sassa na gurin!

Hakan ne kuwa ya faru tashin bomb! sukayi a gurin kowane sassa a dajin ya rikice! da hayaki! wannan damar ya samu yayi dirar mikiya! a gabansa! alokacin da yake kokarin neman mafaka.

Kallon kallo aka fara! Zinat kam ganinsa ya sanyata sauke ajiyar zuciya ta shiga godewa Allah!!!

Ido ya tsirawa! hannunta dake cikin nasa. wata kibiyar kishi ta sokeshi! cikin hargagi! yace."Sakar mata hannu ko na sheka da kai barzahu"!!

Ya tsira masa jajayen idonsa kafin ya fashe! da dariya ya sake rike hannunta da kyau! Yace." Kai ne dan iskan da kake ganin ka isa kayi gogaggaya dani ko.!

Yace" Eh ni ne UMARU! kuma ni zan kawo karshen ta'addancinka."!!!
Kaifaffar wu'kar dake rataye a jikinsa ya cire ba tare da zato! ba ya datse! masa hannu wanda yake rike da nata! hannun tun daga kafada har kan yatsu ya fadi a gurin yana wutsil-wutsil, jini kuwa sai tsartuwa yake! ya durkushe! a gurin, yana wani irin ihu!!!!!!

Kafin kice kwabo! kaf! kowa ya hallara a gurin, ganin ogansu a durkushe! babu hannu ga jini na zuba ya zaburar dasu! sukayi kansa! sai yayi gaggawar soka wu'ka a wuyan ogan nasu!!! *Uban daba!* ya sake rikicewa! domin bai shirya mutuwa ba, da hannu yayi wa yaran sa alama cewa su ajiye makaman dake hannunsa, sukayi yanda ya umarcesu!

Ajiye makamansu keda wuya suka fara jin jiniya alamun jami'an tsaro sun shigo gurin!!!! *Uban daba!* hankalinsa ya sake tashi, babu shakka ya san ya shiga hannun hukuma k'aryarsa ta kare! sai kawai yayi kwance-kwance ya shammaceshi! wani wawan duka ya sakar masa a gwiwarsa!. dukan ya shigeshi! sosai yayi taga-taga! zai fadi wannan damar ya samu ya k'wace! daga hannunsa a sukwane! ya bar gurin cikin wani irin gudu na ceton rai! sauran yaransa suka rufa masa baya...........!

Zubewa yayi k'asan gurin ransa a masifar bace! kwata-kwata bai so hakan ta faru ba, amma ba komai tunda har ya samu nasar raba shi da hannunsa guda, watarana zai samu babbar nasara a kansa!

Tsinin bindiga! yaji a saman kansa! da sauri ya bude idonsa sai kawai yayi arba da zaratan! sojoji da 'yan sanda! sun zagaye shi kowanne ya saita shi da bindigar dake hannunsa.........."Babban cikinsu shine yayi magana ."You under arrest."! Hannuwansa ya daga sama cikin bin umarni, suka d'aura masa zabgegiyar tsar'ka! kafa da hannu suka sa key suka kulle, kafin su mikar dashi tsaye....!



*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin airtal ko mov.


*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE



*19&20*
Cikin tsantsar tashin hankali! da gigita suka gurfana a gabansa kafin su sheda masa abinda yake faruwa.............."Ya wani mike a fusace! tare da mi'ka tafkaken hannunsa wanda yatsun ke cike da zabban zinare da azirfa! wani irin bahagon mari! ya dinga kifa musu kafin ya sanya kafarsa ya tunkudesu duka suka fadi wanwar! a gurin. gabadaya suka
Sunkuyar da kansu, jikinsu in banda rawa babu abinda yake.

Ya takarkare! da karfi! ya kurma uban ihu!!! lokaci k'ank'ani gabadaya kaf yaransa suka kewayeshi! ya goya hannu a baya yana kai kawo a gurun!

Tsit! gurin yayi babu mai kwak'wk'waran motsi a cikinsu.

Lokacin da yake kai kawo a gurin kallonshi nake ina mamakin muninsa! baki ne sosai gashi gajere dab da kasa, yana da katon kai da tafkekiyar fuska, gabadaya hallitunsa masu girma ne bayan gajartar da yake da ita, bakinsa kato haka nan hancinsa kwala-kwala idonsa kadai ya isa firgita yaro! jajawur! dasu, kasumba tayi kaca-kaca a fuskarsa babu kyawun gani!
kallo guda za kayi masa ka tabbatar da rashin imaninsa.!

Cikin kaushin murya! ya fara magana kamar haka." A jinin jikina naji cewar akwai ayarin da suka shirya min! Yau tsayin sati guda kenan idan na kwanta bacci nake ganinsu a idona! babu wani shirinsu da zai firgatani! na shiryawa zuwansu! na kuma yiwa kaina alkawari cewa duk yawansu sai naga bayansu! babu wani mahalukin daya isa ya tunkari inda nake ba tare da she'kashi barzahu ba! nafi karfin hukuma! ballanatana wani dan adam! saboda haka dukkunanin ku na umarceku da cewa ku zauna cikin shiri babu wanda zai fita da rai a cikinsu."! jiki na tsuma! yake maganar yana wani irin huci! gabadaya ya burkice sakamakon jin abin da yazo masa a bazata!


********
Saboda tsabar kwarjin da yayi musu sam sun kasa hada ido dashi, suna gurfane a gabansa, yayin da shi kuma ke kai kawo a tsakaninsu kafin yaja tunga ya tsaya a gabansu, hannuwansa ya goya a baya, babu wasa ya fara magana kamar haka." "Ya sunanku."?
babu wanda yayi magana a cikinsu. Ya sake maimaita maganarsa! uffan basu ce ba.
Ya juya baya yana kallon jama'arsa dake tsatstaye kowanne a cikin shiri.

"Alba bani wannan dorinar." yafada yana kallonsa.
Da saurin gaske ya ciro bulalar daga cikin gidanta, kaurinta ya isa! nayi imanin za ta iya dauke fatar mutum.

Ya gyara rikonta a hannunsa, cikin wani irin hargagi! wanda yasa gurin amsawa! yace."Ba zaku bude baki kuyi magana ba ko."? Duk da sun tsorata da yanayinsa, amma hakan besa sun magantu ba.

Ya zabura! ya juya tare da kiran Alba! yana zuwa ya umarceshi da ya cire musu kayan jikinsu kaf!
Alba yabi umarni!

Ya kai ya kawo ya gurin jikinsa na wani irin karkarwa! tsumin ne ya tashi! ganin haka ya sanya wasu daga cikin yaranshi suka bara buga gangi!!! da bushe-bushe? Ya sake rikicewa! wani irin tafka! yake musu! suna ihu! da birgima a gurin!
Birgima suke a gurin suna gurnani! yana binsu da tafkekiyar dorinar dake hannunsa yana tafka musu, wanda ya janyo tsiyayewar idon daya daga cikinsu.

Hankalinta a masifar tashi taje tana kokarin rike masa hannu kuka take kariris! tana bashi hakuri sunyi bala'in bata tausayi! bata san bashi da imani ba sai yau!

Tureta yayi ta fad'i kasa ta rirrike kafafunsa "Kayi hakuri wannan rashin imani ne, ka zubar masa da ruwan ido ga jini yana fita a jikinsu kada kayi kisan kai." Wannan maganganun nata besa ya fasa abinda yake ba, ya sanya kafarsa ya taka gwiwar wanda yake kokarin gudu! ya murza da karfin gaske! wani marayan ihu! ya saki kafin ya zube a gurin yana karkarwa jiki yace." Yi hakuri kada ka kasheni zanyi ma bayani."

Ba tare da cire kafarsa ba, ya buga musu tsawa! da fadin" Ya sunanka."? baki na rawa yace." sunana Yakubu ." Ya kalli dayan da yake matagugu a kwance "Kai fa."? Yace." Sunana Sulaiman."

Kafarsa ya cire yana wani huci! ya barsu a gurin.......Saman wani icce! ya zauna! wasu daga cikin yaranshi suka bishi! da ruwa...

Wasu na masa fifita wasu kuma na kara kambaba darajarsa!

Nad'in kansa ya warware kafin ya sunkuya tare da bada umarnin a zuba masa ruwa a saman kan.

Ya dago kan yana girgije ruwan sumarshi mai laushi tabi ta kwanta tana digar da ruwa. Alba yasa abu yana tsane masa ruwan.

Har yanxu babu sassauci a tare dashi, idonshi na tsaye a inda suke. tana tsaye a gabansu, magana a suke a tsakaninsu amma basa iya jin abinda suke cewa.

Ranshi ya baci da ganin abinda take, yarinyar ta nema ta lalata masa aiki. mikewa yayi da bulalar a hannunsa ya karasa gurin, kallon mara imani take masa, za tayi magana kenan, a zabure! yayi kanta da bulalar!! ta matsa gefe da sauri! gabanta na bugawa! jajayen idanuwansa ya tsira mata cikin mashahuriyar tsawar data kusa sanyata sakin fitsari yace." Wuce ki bani guri."! kafafunta na rawa ta bar gurin, bai ta'ba firgitata ba kamar yau.

Ya kallesu kafin yace." Ku tashi tsaye! suka yunkura da kyar suka tashi! gabadaya jikinsu ya sauya kama saboda duka! yayi musu wani kallo kafin ya juya da basu umarnin bin bayansa.


Ba tare da iya kallon fuskarsa ba ya fara yi magana kamar haka "Aikinmu shine ta'addanci! rai ba abakin komai yake ba a gurunmu, sannan muna tarewa jama'a hanya cikin dare mu farauci dukkanin guzirinsu, muna rabasu da matansu da 'ya'yansu, mu kwanta dasu, kamar matan auranmu daga 'karshe mu 'kona gawarwakinsu ko kuma mu fito dasu kan hanyar mu yasar! duk wanda ya shiga komarmu bama saurara masa muna da muggan makamai kuma muna da daurin gindi daga sama, kamar yanda ka sani cewa masana sunyi hasashen cewa gurin da muke rayuwa akwai albarkar kasa, to tabbas hakane akwai! amma maigidanmu yaci alwashin cewa babu wani mahalukin daya isa ya amfana da albarkar dake wannan guri sai shi da ayarinsa, yawancin mu musulmai ne magoya bayanshi, amma ya haramta mana ibadah! bama sallah bama salati da duk wani abu da ya cancanta, burin mu ako yaushe mu kashe duk wanda yayi yunkurin shiga gonarmu, maigidanmu yaci alwashi mai zafi! akan duk wanda yayi yu'kurin ganin bayan rayuwasa." Ya k'are maganar tare da sake risinar da kanshi kasa.

Beyi mamakin da jin wannan jawabi ba, hausawa sukace da dan gari akan cin gari, a jawabin da sukayi masa ya fahimci cewa gabadayansu musulmai ne amma suka yarda suka bada goyon bayan ta'addanci a kasa.

Ya girgiza kanshi da fadin." Yakubu-Sule daku aka hada baki wani wawa! zindiqi! mushiriki! ya addabi! kasa da al'ummar dake cikinta, shin me kuke nema a duniya da har kuka mayar da zubar da jini! abin banza? a matsayinku na Musulmai masu amsa sunayen annabawa! shin ya cancanta ku aikata wannan ta'addanci."!

Gabadaya suka shiga girgiza, jikinsu yayi wani irin laushi, yaja numfashii ya fesar! kafin ya cigaba da cewa." Dukkaninku baku cancanta da cigaba da rayuwa a duniya ba domin barin irinku a ban 'kasa had'ari ne."!

Jin abinda ke fitowa daga bakinsa ya firgitasu, a tsoroce! suka shiga bashi hakuri suna kiran sun tuba!!

Wani mugun mari! ya kifa wa daya da jikinsu, 'yar hantsile yayi ya kifa yaci da kasa! tsaye ya mike! yana zagaye a kansu. gabadaya sun tsorata da yanayinsa, su kansu yaran shi basu taba ganinshi a cikin irin wannan yanayin ba, jikinsa in banda tsuma! babu abunda yake, Zinat kuwa addua take a zuciyarta kada Allah yasa ya aikata kisan kai!

Da jan ido ya kallesu, da fadin." *Ni! ne zan kawo karshen ta'addancinsa! *GOJE!!* *Nake mai maganin wani takadiri! Nayi tawa! nayi ta wasu! wannan haka yake! ba'a zubawa dani a kwashe lafiya! *Billahil-lazi hurramanu!* *nayi wa kaina alkawarin ganin bayansah"!* Yanda yake maganar yana zazzare ido shi tabbatar da abinda yake cikin zuciyarsa hakan yake babu 'karya!

Shar'bebiyar wukar dake rataye a kafad'arsa ya fizgo! daga gidanta, wani masifaffan ihu! ya kurma!!! kafin ya fara dadura! wukar a wuyansa!!
Tashin hankali kenan! gabad'aya gurin ya kacame! dan yaran sa ma manyan wukake! suka fito dashi suna gurzawa a kowane sassa na jikinsu! . shi kuwa a wuyansa yasa wukar ya zage karfi sosai! yake gurzawa.!

kuka wiwi! ta dinga yi tana kallon badakalar dake afkuwa, ita tsoronta kada su kashe kansu, ta rasa ya za tayi da rayuwarta a cikin wannan mashahurin dajin!

Tana kuka na fitar hayyaci ta karasa inda yake gabanta na lugudan duka! hannu na karkarwa take kokarin rike damtsan hannunsa, "Ka bari don Allah! ka daina! ka umarci yaranka su daina kada ku kashe kanku."!!
Ko sauraranta beyi ba ya cigaba da abinda yake, jikinta na wani irin rawa ta rumgumeshi tsam! tana kuka tare da dukan bayanshi. wannan ya janyo sadudarsa! ya cake! wukar! a gurin tare da danneta da tafin hannunsa!
Numfarfashi kawai yake gumi na yankowa daga kowane sassa na jikinsa!

Tsit! gurin yayi sakamakon umarnin da ya basu, suka mayar da wukaken jikin jikinsu.

Har yanzu tana manne a kirjinsa ta kam'kamshi shi da yayi wani motsi zata kai masa duka! kuma bata fasan kukan ba.

Hannu yasa ya d'ago fuskarta, suka tsirawa juna ido! ya jima yana kallonta kafin yasa hannu ya goge mata hawayen da suke ta zuba! yayi namijin kokarin cireta daga jikinsa! ta sake kokarin rungumeshi! duk a kokarinta na hanashi aikata wani abun.
Hannu ya daga mata da ido! ya gargade ta, sai ta sunkuyar da kai! amma har yanzu bata dawo daidai ba.


Ya kalli Alba da fadin." Bani abun rubutu."

Da sauri ya fito da takarda da biro! ya mika masa.
A takaice ya rubuta."


_*(KA SHIRYA YAKI DA MAKASHINKA!!!)*_


Wanda yake da d'an sauran kuzari ya mikawa takardar da fadin." Sa'kona ne wannan kana isa ka bashi, cewa daga ni *MAKASHIN MAZA!*

Da kyar! ya mike ya kama hanya yana tafiya tare da waiwayen d'an uwanshi dake kwance cikin halin rai da rayuwa!


Koda ya karanta wasikar sai kawai ya fashe! da wata mahaukaciyar dariya! da mike tsaye tare da dukan! girkakken dutsen dake gabansa!

Hannuwansa yasa ya tallefe 'keyarsa! tare da sunkuyar da kanshi kasa!

Ya jima a haka kafin ya d'ago yana kallon yaranshi dake kewaye dashi, gabad'ayansu suma jikinsu yayi sanyi da wannan al'amarin.

Ya kalli Nuhu dake rakube! gabadaya kammaninsa sun sauya saboda wuyar da yasha, ranshi ya sake 'baci! kawai ba tare da kowa ya ankara ba, ya fille wuka! tana! walwali a wuya ya burma masa! a take ya fara shure-shure a gurin jini sai tsartuwa yake, kafin wani lokaci rai yayi halinsa!

Ya juyo kansu a sukwane! yana kallonsu da kwala-kwalan idanuwansa! Sun tsorata mutuka gaya da ganin tashin hankalin maigidansu.

*"Cike da cin laya yace."Kamar yanda na soke! wuyan wannan shashashan! to haka zan soke! wuyan wannan marakunyar yaron daya tunkari inda nake! Ni! nayiwa kaina wannan alkawari!! saboda haka zamuyi kwankwance! kafin mu afka inda suke da yak'i."*

Suka hada baki gurin fadin."Yanda kayi shine daidai maigida muna goyon bayanka ako wane yanayi."

****
Tun bayan tafiyar Nuhu! babu wani abu daya gilma, hakan besa sun saki jikinsu a gurin ba, sai da duhun dare ya shiga sannan suka fara neman abinda za su ci.

Ita dai 'ya'yan itacuwa kad'ai ta iyaci, tana zaune tana kallonsu sun tada wuta sai gashe-gashe sukeyi da kallon ikon Allah! da kudirarsa, ace wai mutum ya gasa majici gafiya da sauran dabbobi marasa kyau yana ci a cikinsa.

K'auri da karni! duk ya cika gurin! dole ta tashi domin sauya gurin zama, domin mutukar tana shak'ar hayaki da kaurin dake tashi agurin zata iya amayar da abinda taci.

Ido ya bita dashi! be dauke ba har sai da ta samu guri ta zauna can nesa dasu, inda Allah ya takaita akwai hasken farin wata a gurin.

Ta jima a zaune a gurin tana sakawa da kwancewa! sai yanzu ta san ya rayuwa take, ta taso cikin kulawa da gata da komai na jin dadin rayuwa, tunda take bata ta'ba tsammanin cewa akwai ranar da za tayi rayuwa mai muni irin wannan ba! babban tashin hankalinta rayuwa da d'an ta'addah! irin wannan, duk abinda yake a kanta bai janyo masa 'kima da mutunci ba, domin kuwa shine mutum na farko wanda yayi sanadiyar tagayyara rayuwarta, hakika ta tsorota da rayuwa da duniyar ma gabad'aya, A yanzu babban burinta ta samu ku'bta daga cikin wannan dajin, sannan tayi wa kanta al'kawarin ganin ta jefa rayuwarsa cikin kunci da tashin hankali kwantankwacin yanda yayi mata.


Saukar

Please Login or Register in order to submit comment