Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abu taji saman wuyanta, da sauri tasa hannu ta buge! ta mike tsaye! wata lafceciyar tsutsa ce ta fado daga saman bishiya.

Rintse ido! tayi tana kiran sunan Allah! kafin taji zirrrrrr a kan kafarta, tayi tsalle ta matsa gefe tana kallon gurin, ashe gabadaya gurin tsutsutsine suke yawo.

Jiki na wani irin rawa ta bar gurin, tana isa inda suke ta iske sunyi shimfida sun gatange gurin da itacuwa tare da rufe gurin da Net!

Tsayawa tayi a gurin ta kasa shiga, domin gabad'ayansu mugun haushinsu takeji! daga nesa ta hangoshi ya nufo gurin, d'auke kanta tayi tare da jan tsaki a cikin zuciyarta.


Koda ya iso gurin bece mata komai ba, ya kama hannunta! kallonshi tayi kamar za tayi magana sai dai tayi shuru, jan hannunta yayi suka shiga gurin.

Guri guda ya zaunar da ita, muryar rarrashi da kwantar da hankali ya aro yace." Ki kwanta anan gurin nayi miki alkawai cewa babu abinda zan bari ya sami rayuwarki."

A maimakon hakan ya faranta mata sai kawai taja masa tsaki! ta kawar da kanta tana zumbura baki!

Hakan da tayi ya bata masa rai amma sai ya danne! be dauki mataki ba ya fara kokarin barin gurin, ta bude baki da fadin." Mamugunci! insha Allah sai naga karshenka."

Maganar ta bashi mamaki mutuka! sai ya juyo da wani irin murmushi a fuskarsa ya nuna kirjinsa da fadin." Me yasa kike so ki kaga bayana."?

Ta zabura! da fadin." Saboda kai din azzalimi ne macuci.!!

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta" Saboda kai din azzalimi ne macuci."! to wai shin da take kiransa da wannan sunayen wane irin zalinci yayi mata tun farkon had'uwarsu?

Still murmushin ya sake kafin ya furzar da iskar bakinshi, cikin gaggawa ya fita ya bata guri domin yana ji idan ya kara second a gurun zai iya nakastata.

Ya jima yana fesar da hayaki kafin ya samu sassauci a zuciyarsa, zazzafar ajiyar zuciya ya sauke! yana me sake jin sautin muryarta na amsa kuwwa! a kunnanta a cikin kunnuwansa, tunda ya taso lokacin kuruciya da girma gwargwamaya yake da *Maza!* bai ta'ba sanya mata a cikin al'amuranshi ba, saboda sanin hallayarsu! yana da tausayi mussaman akansu amma baya yarda da raini daga garesu, mace daya ce yake jinta a cikin zuciyarsa, domin duk ta tara abinda yake da bukata, hankali nutsuwa ilimi tarbiya da sauransu, ita kad'ai! yake ji a zuciyarsa zai rayuwa mai tsayi da ita, ya kai ma'kura a gurin iskancin da yarinyar nan take masa, yana tausaya mata amma ya lura ita bata gani ta daukeshi a matsayin macuci! to yana ganin zai fita daga harkata domin ya samu zaman lafiya. tare da gudanar da aikin dake gabanshi.


*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin Mov ko airtal


*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________




*RASHIN ADALCI A TSAKANIN MATA*
___________
_*Mata da yawa su kanyi kukan rashin adalci da mazajensu keyi a tsakaninsu. maza kuji tsoron Allah kuyi adalci a tsakanin matanku. lallai wajibi ne kuyi adalci tsakanin matayenku ga wanda yake auran mace sama da d'aya dole yayi adalci, ya sani cewa dukkan abinda yake gudana Allah yana sane kuma yana ganinsa, kuma wallahi sai Allah ya tambayeshi akan zaman da yayi dasu a goben kiyama.*_

*Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkan wanda yake da mata biyu sai ya karkata ga daya baya yiwa dayar adalci, to zai zo ranar alkiyama bangaran jikinsa guda a shanye)*

*Malamai sunce karin aure ba wajibi bane, ba mustahabi bane ga wanda yake da ikon ya 'kara amma wajibi ne kayi adalci, idan har kasan ba za kayi adalci ba to kada ka fara neman k'ara auran ma domin k'arin zai iya kai ka zuwa ga halaka.*
*Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkaninku masu kiwo ne kuma dukkan ku abin tambaye ne akan abinda aka baku kiwo a gobe kiyama)*
*Allah a cikin alkur'ani yayi hani akan kada maigida ya karkata gabadaya zuwa ga wata daga cikin matansa ya kyale sauran matan saboda rashin adalci*
*Allah ya baku ikon adalci a tsakanin matayenku🙏🏻*




FREE PEGE
*25&26*
"Kada ku yarda ku bari ya kubce daga hannunku, mugu! ne macuci! ya jima yana ta'addanci a k'asa! kuyi masa hukunci mai tsauri! domun da bakinsa yake fadin cewa yafi karfin hukuma! yau tsayin kwana shida kenan daya raba ni da iyayena yayi kidnapping dina domin samun makudan kudi daga gurin mahaifina, " Sunana ZINATU ni 'yar asalin jahar kano ce mahaifina kuma shine sarki dake kan kujerar mulki a jahar." Bilhaki da gaskiya take maganar.

Gabad'aya hankalinsu ya koma kanta a lokacin da take wannan maganar, da yawa daga cikinsu ba su lura da ita ba, maganarta ce ta janyo hankalinsu kanta. ganinta a firgice babu sutturar arziki yasa suka gazgata maganarta, babban cikinsu ya kwantar mata da hankali da cewa komai yazo karshe kuma sunyi alkawarin kaita gaban iyayenta idan sun gama gudanar da binkice.

Beyi mamaki da jin furucinta akansa ba, ita kad'ai ce zata bada cikakkiyar sheda a kansa, amma ba tayi hakan ba, to ba zai tsananta ba, ba kuma zaiyi jayayya da hukuma ba, zai bi doka da odar amma ya san ita gaskiya d'aya ce kuma a kanta yake babu gudu babu ja da baya babu shakka! Allah za bayyana mai gaskiya.

Da kansa ya haura ya shiga motar ya zauna, sojoji uku suka zauna hagu da damanshi, ya kalli na hannun damansa cikin nutsuwa yace." Akwai sauran yarana da suke n........ ya katseshi ta hanyar buga masa tsawa da fadin.

"Rufe mana baki ko kai zaka nuna mana aikinmu."? Kansa ya girgiza, yace." To kabi umarnin mu domin shine samun zaman lafiyarka."

Be sake cewa komai ba ya kauda kansa gefe yana hangensu suna ta binkice a gurin...........Can ya hango sun taso sauran yaransa a gaba! suna dukansu! bai dauke idonsa ba har sai da suka karaso gurin, gabadaya sun galabaita domin wasu harda rauni a jikinsu bayan wa'inda suka kone sakamakon bomb din daya tashi, ya tausaya musu sosai, domin ya san shine mujaza! domin da yawa daga cikinsu ba'a son ransu hakan ta faru ba.

Suka dinga turasu cikin motar suna dukansu da wata murtukekiyar bulala irin ta karfe!

To duk iya binkincensu a gurin Allah bai nuna musu dungulmin hannun *Uban daba!* da 'kasa ta turbudeshi a gurin ba, Yana kallonsu suka 'karaci dube-dubensu suka shishshiga mota da niyyar fita daga dajin.

'Bude baki yayi da niyyar magana kawai ya hangota tare da wani soja yana kokarin bude mata gaban mota domun shiga........Yaji wani irin ciwo a cikin ranshi! bakinsa ne yayi nauyi ya gaza furta maganar dake cikin cikinsa har suka fita daga cikin dajin bai dago kanshi ba! wani irin kuttun bakin ciki ya tsaya masa a wuya, tunda yake bai ta'ba ganin butulu irinta ba.

Da yayi motsi zasu saita shi da bindiga! da fadin." Ya kiyaye idan kuma yayi wani yunk'uri na gudu to zasu harbe shi! murmushi kawai yake musu, wanda hakan ke 'kara tunzura musu zuciya.

Labari kaf ya cika garin Katsina da kewayenta cewa A yau 11/3/2007 jami'an tsaro sunyi nasarar kama babban dan ta'addah nan wato *Mashekin daji!* wanda ya addabi k'asa da jama'ar dake cikinta.

Headquarter 'yan sandan kuwa cike take da 'yan jarida da jama'ar gari masu ganin kwal uwar daka.


Koda motocin jami'an tsaron suka shiga headquarter 'yan sandan sai gurin ya hargitse da hayaniya kowa burinsa yayi ido hudu dashi, Mussaman 'yan jarida masu daukar rahoto.

Sai da suka rufe masa fuska sannan suka fito dashi a dadd'aure! Suka rirrikeshi da kyar yake cire k'afa sakamakon sark'ar da tayi masa dabaibayi!

Duk da hakan sai da yan jaridan suka dinga daukar hotonsa tun daga sama har kasan Kafafunsa, da yawa daga cikin 'yan jaridar da jama'ar dake gurin sunyi mamakin ganinsa ingarmar namiji a labari dai sun san cewa ba haka kammaninsa yake ba gajere ne mara fasali ya akayi kuma a zahiri basu ga haka ba.

Har sai da aka shiga dashi ofis din Asp sannan kowa ya watse, jama'ar gari suka tafi da zancan a bakunansu, su kuma 'yan jarida suka fara gudanar da ayyukansu.


****
Cikin tsananin tashin hankali Saude matar Alba ta shiga gidan tana kuka hannunta rike da jarida.

Uwale ta tare ta tana tambayarta abinda ke faruwa.

Jaridar ta nuna mata da fadin." Uwale kin san abinda yake faruwa kuwa."? ta kar'bi jaridar tana dubawa tace." Saude kin san ban iya karatu ba me yake faruwa."

Tace."Ki duba hoton jiki mana Mijina Alba ake tuhumarsu da ta'addanci."

Gabanta ya fadi! tace." Ta'addanci kuma Saude! su da suka tafi farauta mai ya hadasu da ta'addanci inace gobe zasu dawo."

Saude na kuka tace." Uwale kisa kunne da kyau ki saurari jawabin da zanyi miki."

Jiki a sanyaye tace." Ina sauraranki."

"Jami'an tsaro ne suka kama UMARU wato jikanki dashi da yaransa saboda zargin da ake musu na ta'addanci, a yanda na karanta rahoton cewa wai ana tunanin shi UMARU shine wannan d'an ta'addan da ya addabi kasa! yanzu haka dai gabad'ayansu suna hannun hukuma! jama'a da yawa sunyi imani da cewa hukuncin kisa za'ayi musu."

Hankalinta ya tashi sosai sai ta fashe! da kuka ta tsirawa hotonsa ido duk da fuskarsa a rufe take hakan be hana ta ganeshi ba, ta tsirawa kafafunsa ido tana wani irin kuka tace." UMARU wannan ranar nake gudu a gareka, itace rana mafi muni da ba zan ta'ba mantawa da ita ba, ashe tsautsayi ne ya sanya ka tsunduma kanka wannan harkar, ni na san halinka UMARU kuma zan bada sheda a kanka, ka taka sawun 'barawo insha Allah sai Allah ya wanke ka daga zargin da ake maka." Kuka sosai takeyi hawayenta duk ya jika takardar dake hannunta.

Hamra'u ta shigo gidan cikin kuka na fitar hayyaci! tana zuwa ta rugumeta da fadin."Uwale ya za muyi da wannan kaddara hukuma ta kama Yayana da laifin ta'addanci! bayan bashi da laifi Yayana bashi da mugunta baya cin hakkin wani burinsa kullum ya za'ayi k'asa ta samu cigaba, amma ya taka sawun barawo jami'an tsaro sun kamashi dumu-dumu a cikin sansanin da *Uban daba!* yake zaune da jama'arsa, Uwale ya za muyi bamu da kudi bamu da ikon da zamu tunkari hukuma! domin kalubantar zargin da sukeyi akan wanda bai ji bai gani ba."

Tace."Hamrau bamu da komai wanda zamu tunkari hukuma dashi, amma muna da Allah shi kadai zai ne zai mana jagoranci Allah ba azzalimin sarki bane yana tare da masu gaskiya insha Allah cikin hikimarsa zai bayyana mai gaskiya."


Asp Musa Baharu shine shugaban 'yan sandan jahar, kuma duk wani jami'in tsaro a karkashinsa yake, mutumin yana da hankali da nutsuwa gami da sanin makamar aiki, koda aka shigar masa dashi ofis din kallo daya yayi masa ya tabbatar da cewa bashi suke da bukata ba, amma be nuna hakan a zahiri ba, sai kawai ya bawa wa'inda suka shigo dashi umarnin fita, ya rage su biyu kacal a ofis din.

Shi baya ganin komai saboda har yanzu fuskarsa a daure take, amma shi Asp din yana kallon duk wani motsinsa.

K'ira ne ya shigo wayarsa, daga gidan gwamnati , cikin cikin girmawa ya daga da fadin." Ranka ya dade barka da wannan lokaci."

Mai girma governor yace." Barka dai Asp barkanmu da samun nasara! wannan ranar ba zamu ta'ba mancewa da ita ba, yana kuma da kyau ayi rubutu na mussaman domin ajiyewa a kudin tarihi."

Asp ya d'anyi murmushi da fadin." Hakane ranka ya dade, labarin samun nasara ya cika gari da sauran garuruwa jama'a da yawa sun kirayi waya suna yi mana murna! amma ban san me yasa ni nake shakku! akan hakan ba."

Mai girma governor yace." Asp wannan wace irin magana ce? da farko kafin isowar rudunar da muka tura kaine ka kirayi wayata kake sheda min cewa an samu nasara ya za'ayi kuma yanzu kace na shakku akan hakan."

Gilashin dake idonsa ya cire ya ajiye saman tevur din dake gabansa, ido! ya tsira masa yana sake nazartarsa, yace." Ranka ya dad'e ni da kai da sauran jama'ar gari bamu ta'ba ganin *Uban daba!* a zahiri ba, sai dai muna hasashe akansa cewa shi din wani irin mutum ne mara fasali sanin hakan ma ya samo asali ne daga bakin d'aya daga cikin yaransa da Allah ya bamu ikon kamawa a shekarun baya, shine yake sheda mana kammaninsa, a lokacin da al'amarin ya faru, banyi 'kasa a gwiwa ba na samu yaron daya haddace zane ya zana min kammaninsa domin samun sauki gurin binkice a kansa, amma abin mamaki! a yanzu wanda yake gabana a yanzu kuma muke hasashen cewa shine wanda muke nema ruwa a jallo kammaninsa yasha bambam! da wannan hoton zanen da nasa aka zana min a shekarun baya."

Mai girma governor yace." Asp ya akayi hakan ta faru? kana so ka sheda min cewa bashi bane."?

Ya mi'ke tsaye da wayar a kunnasa, kujerar ya janye ya fito daga tsakankanin kai tsaye inda yake zaune ya nufa!.......Yana wayar yana kokarin kwance masa fuska dake d'aure.

Tsaf ya warware d"aurin fuskar, idanuwansu suka hadu guri guda, kujera yaja ya zauna suna fecing din juna.

Ya cigaba da cewa." Gani gashi a halin yanzu kuma yanzu zan dauki hotonsa na turo maka dashi domin ka sheda maganata, amma duk wani binkice zanyi a kansa domin samun tartibiyar magana."

Mai girma governor ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Okey to babu damuwa ina tsumayinka." sallama sukayi kafin ya kashe wayar, ya tsira masa ido! shima nasa idon ya tsira masa suka dinga kallon kallo suna nazarta juna, shi Asp din shine ya fara janye idonsa daga kanshi, ya jima kanshi a kasa kafin ya dago ya sake mai da idonsa gareshi yace." Inaso naji cikakken sunanka gami da jin asalin tarihin rayuwarka."?




*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* katin mov ko airtal.



*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________



*JAMILA MUHAMMAD-ALI*
_(( (MMN BOBO💞) )_
Ina gaisuwa gami da fatan alkairi, Nagode sosai da kulawa da shawarwari Allah ya raya zuria, ya jikan MAMA yai mata rahama🙏🏻


FREE PEGE
*27&28*
Ya jima kansa a 'kasa tun bayan 'kare maganar Asp din yake cikin nazari da tunani, kafin ya d'ago kanshi ya fara magana kamar haka............Sunana *UMARUL-FARUKU* Ni d'an asalin wannan jaha ne wato jahar katsina.".........Asp din ya kalleshi na 'yan sakkwani kafin ya mayar da hankalinsa kan takarda da biron dake hannuna, yace."Ina sauraranka." numfashi ya fesar kafin ya cigaba da cewa." Kamar yanda na fada maka hakane an haifeni a karamar hukumar malumfashi cikin wani k'auye mai suna *'Kafur* ban taso na iske mahaifiyata a raye ba amma na taso da mahaifina da kakata wacce ta zama garkuwa a gare ni, mahaifina asalin sunansa Tanimu, amma da yawa jama'ar gari sunfi kiransa da *mai jakai!* dalilin sana'arsa ta jidon 'kasa akan jaki domin siyarwa da masu aikin gini da sauraransu. mahaifina ya bani dukkanin wata kulawar da ta cancanta ya ilimatar dani ilimin addini daidai gargwado yanzu haka ina da izifi sittin na al'kur'ani maigirma, duk da acikin k'auye muke sai da yayi k'okarin ganin na samu ilimin zamani (boko) hankalinsa bai kwanta ba sai da na kammala 'karamar makaranta wato secondary school............bayan hakan sai ya fara koya min sana'a domin dogoro da kai, a lokacin dana kai shekaru ashirin da biyar a duniya sai tunani na ya sauya wani guri, a zahiri dai kowa ya sanar sana'ar mahaifina wato *Jaki da mangala* ban gaji farauta ba, amma sa'i guda na tsinci kaina dumu-dumu a cikin harkar, mahaifina baya so ko kad'an saboda yayi wa harkar mummunan fahimta, dalili duk wata nutsuwa da nagarta ina da ita, amma daga ranar dana fara harkar farauta sai wasu daga cikin dabi'una suka sauya, ni zanyi shedar kaina cewa tunda na fara wannan harkar ban ta'ba haura gidan wani nayi sata ba, ban kuma ta'ba tarewa wani hanya nayi masa k'wace ba sannan kuma ba'a ta'ba kamani da laifin fyad'e ga yaran mutane ba, wannan sune munanan laifukan da zan aikata a kira ni da wani mummunan suna! busa hakin sigari ko Shakar Shisha wannan sanya kai ne ga wanda yayi ra'ayin hakan. wannan dabi'ar da nakeyi sai ta janyo cecekuce da surutai a gari cewa na zama d'an iska takai ta kawo babu irin sunan da mutane basa kirana dashi, mahaifina ya d'au damuwar hakan yasa a cikin ranshi har ciwo ya kama shi wanda shine ya zama ajali a gareshi, lokacin da ya fadi ya mutu jama'ar gari suka dauki mutuwarsa suka ala'kanta ta dani cewar b'acin raina ne ya kashe shi, a duk lokacin naji wannan maganar hankalina yana tashi mutu'ka! ni dai na san babu wanda ya isa ya kashe kuma babu wanda ya isa ya raya sai Allah! amma jama'a sun juya maganar domin wani sa'in ma ita kanta kakata Uwale takan jefeni da maganar a duk sanda ranta ya b'aci dani.........Da yawa yawan mutane suna ganin rasuwar mahaifina zata karyar min da gwiwa na janye kudirina sai abun ya basu mamaki! domin ana adduar bakwai na cigaba da harkoki na! idan na fita farauta na kanyi kwanaki ko satittika a daji! kuma da ikon Allah na kan farauci duk abinda nakeso kuma nayi guzurin magunguna iri-iri! ba zance maka ga iya adadin mutanan da suka samu lafiya ta dalilina ba, ina kar'bar 'karamar sadaka na bada magani daga cikin irin ilhamar da Allah yayi min, wannan hanyar itace ta zama hanyar abincina, domin ko bana gari kakata takan bada magani tayi d'awainiya da kanta bayan 'yan sana'o'in da take........Tafiya tana 'kara tafiya ta kowanne fanni ana samun cigaba da tarin masoya da kuma tarin ma'kiya domin duk abinda zaiyi ba zai rasa d'aya daga cikin abinda na fada a yanzu ba, shekara biyar da ta wuce ina fita farauta ni kad'ai! cikin ikon Allah sai na fara samun magoya baya a hankali a hankali na tara jama'a da yawa wanda muke tafiya tare dasu wannan harkar! jama'ar gari suka dauke mu mutanan banza saboda muna yawo da karnuka bayan haka kuma shaye-shayen magungunan tauri da sauransu, yanda jama'a suke kallonmu muma haka muke kallonsu a hangunce! domin mu mun san bama aikata wani mugun aikin da zai janyo mana zubewar mutumci wannan harkar ba *Daba!* bace, ba kuma *Ta'addanci* muke ba, muna neman halak dinmu ne domin mu tsira da mutuncin mu." Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya 'kare maganar!

Shuru ta ratsa gurin tun bayan 'kare maganarsa Asp din yake rubuce-rubuce yayi 'yan mintina a haka kafin ya d'ago kansa suka had'a ido! ya d'anyi murmushi da fadin." *UMARU-FARUK!* Maja ya'ki! ni Asp Musa Baharu! nayi imani da cewa babu *RAGO!* ga duk wanda ya amsa wannan suna domin Asali al'amarin ya dau'ko."

Murmushi yayi wanda ya tsaya kan fatar bakinsa......Asp din ya cigaba da cewa." Yanda kayi min cikakken bayanin tarihin rayuwarka cikin nutsuwa babu inda-inda yasa naji bana shakka a kanka amma ina so yanzu ma kayi min cikakken bayanin yanda akayi har ka samu nasarar shiga sansanin mutumin da jami'an tsaro suke shakkar tunkarar inda yake, hukumar tsaro tayi mutukar mamakin! yanda akayi kai da yaran ka kuka samu hanyar shiga wannan gurin, bayan baku da manyan makaman kare kanku."

Murmushi yayi wanda yake fito da zahirin kyawunsa ya tsira masa ido kafin yace." Me yasa kai ka yarda dani da sauri haka? me yasa har yanzu baka gazgata cewa Ni ne *UBAN DABA BA."?* Asp din yayi murmushi da fadin." Saboda sanin makamar aiki shiyasa kallo guda nayi maka na tabbatar da cewa ba kai ne wanda muke da bukata ba."

Girgiza kansa yayi still da murmushi a fuskarsa, Asp ya cigaba da cewa." Kayi min cikakken bayanin yanda akayi kuka samu nasarar shiga wannan guri da kai da jama'arka ina sauraranka."

Huci! mai zafi ya fesar! kafin yace." Na jima ina jin labarinsa na yawo a gari a duk sanda muka fita farauta sai mun ci karo da irin ta'addanci da yake, muna cin karo da gawarwarkin mutane bila adadin! mata da maza harda kananun yara! idan mun nausa mu ci karo da motoci irin na haya dana gida a k'one! wasu da rai wasu babu rai! mukan tsaya mu basu taimako daidai gwargwado kafin mu wuce! to wannan dalilin yasa ni d'aukar alkawarin ganin 'karshen ta'addancinsa duk da na san bani da alhakin hakan amma zuciyata bata karye ba, na zauna da yarana muka tattauna, da yawa daga cikinsu ba suyi na'am ba, sai dai kuma suka bi umarnina domin bana ajiye kara su tsallake! sannan kuma ba kai tsaye muka tunkari sansanin ba sai da muka bi matakan kariya kamar yanda yake da dabaru! da suddabaru iri-iri to muma muna dashi, domin sai da mukayi kwana biyar a dajin bai san da zaman mu ba! sai lokacin da naso ya san hakan, sosai yayi mamaki da faruwar al'amarin nayi masa bazata! kuma na fara karya alkadarinsa kenan tunda har na samu nasarar fitar masa da wani sassa na jikinsa to da ikon Ubangiji sai na gurfanar dashi a gaban hukuma."!! ya kare maganar cike da cin alwashi da cikawa kansa al'kawari!

Asp yayi murmshi mai ma'ana kafin ya latsa wayarsa serving yayi na recoding din da dauka. yasa wayar gaban aljihun rigarsa, mai da hankalinsa yayi kan rubutun da yake, bayan ya kammala ya sauke ajiyar zuciya da fadin." *JAN GWARZO! MAJA YAKI!* Yanzu zamu d'an huta zuwa anjima zamu d'ora insha Allah, bari nasa nasa a kawo maka abinci da ruwa idan kuma akwai bukatar yin wani uzuri kana iya magana."
Key yasa ya kwance masa hannu amma be kwance kafafun ba.


Ya fito da waya ya kira wani jami'i minti uku ya shigo, ya bashi umarnin kawo abinci mai kyau da ruwa da lemo." Ya 'kame tare da sarawa kafin da sauri ya juya ya fita daga ofis din cikin bin umarni.

Idonsa ya sauke kan agogon dake kafe a ofis din, daya da rabi na rana lokacin sallah yayi, sai ya mike tsaye Asp din ya kalleshi tare da tambayarsa, Uzurinsa ya fada masa, da kansa yaje ya bude masa kofar toilet din ya bashi hanya har ya k'araso bakin toilet wanda da kyar yake cire kafa sakamakon sasarin dake d'aure da kafafun!

Alwala ya d'auro ya fito, shima Asp din ya shiga ya d'aura alwalar ya fito suka tada sallar a tare............... Tare sukaci abinci har suka kare babu wanda yayi magana a tsakaninsu sai dai nazartar junansu da suke.

Asp wani jami'i ya k'ira ya umarceshi da ya shigo masa da yarinyar da suke maganarta.

Tare suka shigo ofis din ya kame tare da sarawa kafin ya fita, Asp ya kalleta tare da nuna mata gurin zama, ta zauna kujerar dake kusa dashi sai ya kasance gabad'ayansu suna fecing Asp din.

Tunda ta shigo kanshi yake k'asa sam baya so ya daga kai ya kalli fuskarta saboda tsabar

Please Login or Register in order to submit comment