Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

leemah tai ta kalli Esha tace "wallahi Esha ko zanyi yawo tsirara sai na auri wancan guy din sbd ya min ne ya kwanta min, in kuwa ban aure sa ba tofa sai na dandani zumar sa..."

Wani murmushi Esha tai tace "tabbas zaki iya kawata..."

Dariya suka sa a tare suna tafawa.

*****

Ni kuwa muna shiga na shiga yin istigfari da karfi ina yarfe hannu.

Ganin abin bana karewa bane Elhajj ya kalle ta yace "Ke lafiyar ki?".

Da sauri nace "ina fa lafiya na aikata babban sa'bo nace kai Mijina me wannan abin kunya ina zan Kaisa tabdijan".

Cikin ko in Kula yace "toh sai me?".

Zaro Ido nai nace "sai me?, tabdijan to wannan babban abun kunya ne Ka haife ni fa da auren kauye aka maka ynxun ma inaga kana da 'ya kamar ni, toh ni kawai sai na auri tsoho fisabilliahi".

Wani kallo ya mata yace "nine tsohon?".

Daga kai nai nace "ai in aka hada Ka dani tsoho ne ka Zama sugar daddy".

Kauda kansa kawai yai yana murmushi, a ransa kuwa wani tunani yakeπŸ€”.

Muna zuwa companyn na bude kofar da sauri na fito, so nake kafin ya hawo na shiga office dinsa na gyara masa don an kusa tashi.

Ina shigowa palourn na samu wata mata a hakince ya juya min baya.

Jin taku yasa Momma data zo domin barbada garin maganin nan tashi ta juyo.

A tare zuciyoyin mu sukai wani irin bugu, ni kuwa abinda nake gani a tattare da matar ne yasa jikina ya soma rawa ta ciki.

Momma da tayi mutuwar tsaye kare ma Dije kallo kawai take, tuni taji masifaffan kaunar ta ya doki zuciyar ta, wani irin murmushi ta shiga sakar Mata tana jin tunda take bata taba jin tana kaunar wata halitta ba kamar yadda take Jin kaunar wannan Yarinyar ynxu haka da kuma take Jin zata iya aikata komai domin ta mallake ta koda kuwa za'a bukaci jinin Hajja(mahaifiyar ta).
......



πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯TOFAπŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Su waye suke son ganin bayan Elhajj?

Waye yayi wa Elhajj da Malam farraku?

Shin waye ya shiga office din Elhajj har Dije ta gansa?

Wa ke yiwa Elhajj zagon kasa yana fitar masa da information akan aikin sa?

David wa yake yiwa aiki?

Wacece wacce aka kulle a daki tsawon 30 years, sannan wace ta kulle ta?

Salim zai samu Dije kuwa? Kuna tunanin zai rabu da Dije?

Momma zata ci nasara akan aikin ta da boka ya sata? Zata ci nasara akan yin sex da Elhajj?.

Hajia Batula fah dake son Papa?

Alh Hussain wani mataki zai dauka akan Papa?

Wacece Leemah? Xata yi nasara akan plan dinta?.

Momma dake Jin kaunar Dije fah? Wani irin abu kuke tunanin zata yi don ta same ta?.

Gidan su Dije fah?

Uncle Mustapha fah? Uncle din su Dije dake sonta Wanda yace Yana jiran ta gama secondary school ya fada mata?.

TUKUNNA MA WAI WACE SAUDAT MATAR ELHAJJ?

Duk zaku samu wadannan answers din a cigaban littafin nan insha Allah, ki biya 300 dinki ki karanta cikin salama da nutsuwa✍️




*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387



Comments Nd share plz



Mrs A.M

🀎🀎🀎🀎
*ELHAJJ*
🀎🀎🀎🀎

Paid page 16

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

*Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.*

*Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.*
09066728387

*DEDICATED TO ZEE CHOCOLATE MARUBUCIYAR KADDARAR MU, WANI HANIN GA ALLAH ND KISHI DA ALJANA*.

*WANNAN PAGE DIN NA KI NE HAJJAJU ZEE KIYI YADDA KIKE SO DASHI, ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUN KI NA ALKHAIRI MUTUNIYAR KIRKI.*

HOME OF SUPPLEMENT AND KAYAN MATA MMN MUJAHEED


Y'AR UWA WANI TANADI KIKA KAYIWA SANYI SANYI YAZO SAIDA GYARAN JIKI GYARAN FATA DA GYARAN KASA WANNA YANA YI SA MUKE CIKI INFECTION YAFI DAMUWA MATA TSUHUN INFECTION DA SABO DUK GA SANYI SUNA TASHI YANA DA KYAU KIKULA DA JIKIN KI Y'AR UWA KIKULA DA JIKIN KI RINKA KIYAYE KA'IDA SANYI DA KA'IDA KAMUWA DASHI SANNA KIRINKA SHAN MAGANIN DA ZAI MIKI WANKE MIKI SANYI DA DATTIN MARA LOKACI ZUWA LOKACI


MUNA HADI KALA KALA NA GYARAN JIKI

BANI BADA MAGANI SAI NAJI INDA MATSALA KI TAKE IN MAGANIN SANYI KK BUKATA SAI AHADA MIKI


WATA BUSHEWA GABA TAKE FAMA DASHI NA INFECTION

WATA BUSHEWA GABA TAKE FAMA DASHI NA RASHIN NIIMA

WATA TUSAR GABA TAKE FAMA DASHI NA SANYI

WATA TUSAR GABAN DA TAKE FAMA DASHI NA BUDEWA GABA NE

WATA MATSALA TA TA ASIBITI CE IN MATSALA BATA WABACE ZAN BADA SHAWARA AJE AGA LIKITA

WATA MATSALA SIHIRICE DUK AIKIN DA NISAN BANAWA BANE BANSA HANNU NA DASHI


KIYI BAYANI ABAKI DAI2 DA MATSALA KI

INA MASU FUSKANTA MATSALA WURIN MIJI

WASU MIJI NA MUSU WALAKANCI KIN KASA GANE MATSALA INDA TAKE

MUNA HADI KALA KALA IYA KUDINKA ITA SHAGALINKA


MUNA DA MAYUKKAN SUPPLEMENT MASU FIDDA HASKEN FATARKI KIFITU KIYI FRESH KIYI KYAU AKWAI NASHA DANA SHAFAWA


AKWAI MASU SA HASKE

AKWAI MASU GYARAN JIKI DA NIIMA DA MATSI

MUNA DA MAN GYARAN GASHI YANA SA TSAWON GASHI DA BAKIN GASHI YANA KARA YAWAN GASHI DUK WADDA TASSAN CHEBE ORIGINAL TASAN HAR MAGANIN DAN DRUFF YANA YI MUNA SAIDA SET OIL NA KARKAR DA CHEBE POWDER DA STEAMING CREAM DA BUTTER DA SHAMPOO


KADAN DAGA PRICE DIN KAYAN MU

KAZA AKWAI TA 5K, 4K,

DAHUWA KIFI 2K

TSIME TABAJE 3K GURA 500

JAN TSIME 3500 GURA 600

GUMBA MADARA 4K
TA AYA DA DABINU 2500

TA SHINKAFA 2K

TA HATSI 1800

ZUMA BATA GINDIN KISHIYA GA WADDA KISHIYA KE MATA FANKAMA TA HANATA RAWAR HANTSI 3K BABBA MEDIUM 2500 KARAMA 800 MUNYI HAR TA IRE IRENMU 500

ZUMA KIBA 2K

GARURUKA IRIN SU
GARIN DAN SATI 1
EMERGENCY
BABANBADE
TUKUDI
SHAKAMATSE
RUBA DUK 500

MAN AYYU KWALBA KARAMA 300 BABBA 700
KADA AL'AJABI 500

SAURAN BAYANI SAI MUN HADU GA ME BUKATA


MUNA KEBBI & SOKOTO MUNA AIKAWA KU INA 08066726866 MMN MUJAHEED KAYAN MATA AND SUPPLEMENT.


Kallon juna muke yi kawai kowa da abinda yake aiyana wa a ransa, ganin kallon da matar take min ya soma damuwa kawai sai na fara La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.

Cikin sanyin jiki na karaso cikin palourn na nemi waje na zauna.

Da sauri Momma itama ta zauna tana bina wani irin kallo murmushi dauke a fuskar ta.

Ganin naki Mata magana yasa ita cewa "barka dai Yan Mata abin ba gaisuwa uhmmm".

Kallon ta nai kawai sai na turo baki nace "ba ke bace kike kallona irin haramun kallo".

Wani dadi ne ya mamaye zuciyar ta har sai da tayi wata dariya tana gyara Zama sannan tace "A'a ni ba kallon haramun nake miki ba kawai dai ina mamakin yaushe kika fara aiki a wannan company don ban san ki ba, ko ba aiko kike yi ba?".

Ba tare dana kalle taba nace "aiki nake yi a office din Ya Ustaz nice nake gyara masa office AI".

Cikin rashin fahimta Momma tace "waye kuma Ya Ustaz?".

Da hannu na nuna mata office din MD ban yi magana ba, murmushi tai tace "wai son?, d'ana ne fah".

Da sauri na juyo na kalle ta ina dan kare Mata kallo, sam basa kama da Ya Ustaz bakina baxai iya shiru ba don haka nace "kiyi hakuri amma d'a dai na haihuwa?".

Murmushi Momma tai tace "A'a dan yayata ne, data rasu sai na auri baban sa tun yana karami amma ni nake Kula dashi".

Marairaice fuska nai nace "wayyooo Allah dama Maman Ya Ustaz ta rasu?".

Itama Momman matse hawaye ta fara tace "wajen 30 years knn, abin tausayi gashi sun saba sosai da maman tasa".

Shiru nai cike da tausayin sa nace "Allah ya jikanta ya Mata rahama".

"Ameen" ta fada tana miko min ruwa wai nasha.

Girgiza kai kawai nai nace "ngd sosai amma cikina a cike yake dam".

Muna zaune tana jana da hira jefi jefi ina amsata.

Elhajj shigowa yai yana takun sa a hankali, birki yaja ganin Momma tana hira da Dije.

Kallon su kawai yake yana mamakin wai Momma ce take hira da Dije, shi dai a iya sanin sa Momma bata hira da talaka ko kadan don taki hada koda Inuwa daya da talaka ne shiyasa masu aikin ta suke shan fada.

Dago wa Momma tai ta kallesa tace "sannu da zuwa son, tun dazu nake ta jiran ka AI".

Dan gajeran murmushi yai yana takowa inda muke, tsugunna wa yai yace "barka da yamma Momma".

Murmushi Momma tai tace "barka kadai dan albarka, ya aiyukan".

"Alhamdulillah Momma", ya fada yana dan satar Dije data zuba musu ido tana kallon su.

Murmushi kwance a fuskar Momma tace "ai tun dazu nazo aka ce Ka fita sai na zauna jiran ka, toh kuma xai ga Khadija tazo take tayani ma zaman".

Yana mikewa daga tsugunnan da yake ace "eh na dan fita ne Momma, shigo muje office din".

Da sauri ta girgiza kai tace "A'a jeka kai dai amma ni ina zaune anan tare da Khadija in an tashi sai mu tafi tare kawai".

Daga mata kai kawai yai yana mamakin wannan sudden change din a gurin Momman..

Hira take min sosai, nidai har na gaji nayi shiru ina rufe ido kamar bacci ne ya dauke ni.

Zuba mata ido tai tana kallon ta wani kaunar ta yana kara huda Mata zuciya, murmushi tai ta mike a hankali na nufi office din Elhajj daya fita.

Kasa hakura nai ganin ta shiga office din sai na mike nima a hankali nabi bayanta, a jikin kofar na tsaya daga gefe yadda baxa a iya ganina ba sosai.

Gaba nane yayi wani irin bugawa da karfi ganin ta tsaya a jikin kujerar da Ya Ustaz yake Zama ta fito da wani kyalle ja, ban san abinda ke cikin kyallen ba amma naga ta sa hand glove ta na dibo abinda ke cikin tana barbadawa a akn kujerar.

Duk jikina ba inda baya min rawa sbd tashin hankali, ina kallonta ta Kara sa barbade garin gaba daya ta juyo da sauri zata fito.

Da sauri na koma inda na tashi na kwanta kamar dazun ina salati a zuciya ta don yadda jikina yake rawa.

Fitowa tai tana sakin ajiyar zuciya ranta fess, sai da ta tsaya a kaina tace "wayyooo baby gashi kinyi bacci bare muyi sallama, amma tunda anan kike aiki ai dole ne ma na dinga zuwa akai akai gaskia".

Juyawa tai ta fita tana taku cike da isa.

Sai da na tabbatar ta fita sannan na mike a guje na shiga office din, ruwan robar dana gani a kan table na bude kafa bakina nai a kai na karanta ayatul kursiyuu kafa bakwai, suratul iklas da falak da nasi uku uku.

Kin kimar kujerar nai na fito da ita daga office din gaba daya, wani store dake farkon floor din na Kai ta, ina ajiye ta na dauko ruwan nayi bismillah na fara zubawa akan kujerar, ruwan yana fara taba kujerar wani bakin hayaki ya fara tashi Wanda har saida yasa na toshe na hanci ba.

Sai da nagama zuba ruwan tass sannan na fara tunanin mai zanyi wa kujerar yadda zata haramta wa Elhajj zaman ta har abada.

Dube dube na farayi a store din har Allah yasa nagano wani karfe mai dan tsini.

Gun kujerar nai na jawo kayi tun daga farkon sit din har karshen sa, sai dai irin layin dana ja baxa Ka taba cewa wai layin ana sane aka yisa ba.

Ajiyar zuciya na sauke sanna na fito daga store din duk na hada gumi.

A tsaye na ga Elhajj a kofar store din yana kallona, duk sai jikina ya fara rawa ina tunanin ko yaga abinda nayi masa.

Fuska a hade yace "ina kika kai min kujera ta?".

Ajiyar zuciya na sauke ina kara goge gumi na, ashe bai ga abinda nai ba kenan.

Marairaice fuska nai nace "don girman Allah Ya Ustaz kayi Hakuri, mishkila aka samu ina cikin goge ma office wani karfe ya fado ya karci kujerar, ynxu maganar da nake ma dai kujerar ta tashi daga aiki gaba daya sai hakuri".

Folding hannun sa yai yace "wani hakuri a salary dinki Zan cire kawai".

Dafe kirjina nai da hannu ina zaro manyan idona nace "kayi wa Allah kayi hakuri, ynxu in Ka ciri kudin kujerar can ai baxan tashi da komai ba, bayan na gama cin burin salary din nan nawa".

Da mamaki yace "me xakiyi da kudi yar Karama dake?".

Kallon sa mai ina murmushi nace "ni kuwa nasan abinda zanyi da shi, daga a kudin Zan raba gida biyu na bawa Baba rabi ya boye min, in an tashi yimin abun sai ayi amfani da kudin".

Idonsa akan ta yace "meye abin?"

Fuska ta na rufe da hijab ina jujjuyawa nace "abin mana don Allah".

Da rashin fahimta yace "ina zan san wani abun wai, meye shi?".

Juya masa baya nai ina rufe fuska ta sosai nace "aureee fa nake nufi haba".

Bai san lokacin daya sa dariya ba, dariya yake sosai yace "wai auren ne baxa ki iya fada ba".

Juyowa nai na zuba masa ido kawai ina kallon yadda yake dariyar, abin ba karamin burgeni yayi ba, bama kamar dimples dinsa da suke lotsawa sosai.

Da kyar ya tsayar da dariyar tasa yace "mai zakiyi da ragowar kudin toh?"

Turo baki nai nace "zan siyo waya ta 8k touch kaga bani da waya dama, a wannan wayar Zan dinga turo Indian film ina kalla abuna, ragowar kudin kuma na raba biyu shima, rabi na siyo mana kayan dadi nida Mama mu dinga fadawa a daki muna cinye wa mu biyu, rabi kuma na dinga kudin mota kaga baba ba sai ya dinga bani kudi ba koh?".

Kallon ta kawai yake, gata dai yar karama amma sam bata da hayaniya da son kyale kyale irin na yaran zamani.

Daga mata kai yai yace "kinyi tunanin mai kyau, amma banji kince zaki siyi turare ba ko kayan kwalliya".

Tabe baki nai nace "ai ni bana kwalliya Sam, turare kuma ina da alimun xan dinga gogawa a hammatar, ai ni in ciki na ya dauka bani da damuwa".

Girgiza kai yai a ransa ya a fadin da sauran ta dai har ynxu, juyawa yai kawai ya nufi office dinsa.

Ajiyar zuciya na sauke bayan shigewar sa office din, ina juyawa naga Yasir a tsaye da alama ya dade da shigowar bamu ji bane.

Hannayena na daga sama nace "bkm wallahi, kawai dai munyi dan magana ne haka".

Dariya yai yana girgiza kai yace "Allah ya shirya mun ke wallahi, toh ni mai zance dama, ai godia ya kamata na miki ma tun da na fara aiki da MD wajen 5 years ban taba ganin dariyar Saba sai yau".

Daga kai nai na kalle sa da mamaki nace "baka taba ganin dariyar Saba kuma?"

Daga kai yai alamun tabbatar wa yace "shiyasa nake cewa ke yar baiwa ce gaskia, har hira da naga kuna yi tare".

Haka muka zauna yana aiki yana fada min yadda MD yake magana da mutane da yadda yake hade rai sai jinjina kai nake ina mamakin dalilin daya sa yai min dariya dazu toh.

Lokacin da aka tashi ina rataya jaka ta a kafada ya fito daga office dn bkm a hannun sa sai ledar daya karbo a restaurant din a muka je.

Direct guri na ya nufo yana miko min ledar yace "karbi"

Hannu biyu na sa na karba nace "kasa zai kai Ya Ustaz".

Hade rai yai sosai Jin sunan data kirasa yace "naki ne".

Da mamaki na bude ledar na leka kaina nidai bangane ko meye ba, amma naga wani Abu a nannanade a takadda har uku sai robar ice cream babba, da kuma wani kwali guda biyu.

Kallon sa nai ganin har yayi gaba zai shiga elevatorn na rug a guje muka shige tare.

Kallona yai yana dauke kansa ba tare dayai magana ba.

Ni kam ledar na tura masa nace "gashi sir wannan meye shi".

Yana danna iPad dinsa yace "in kinga dama ki yar dashi a Bola".

Shiru nai da bakina nama kasa godiyar.

Da muka fito ynxu ma kamar dazu kowa zuba mana Ido yai, nidai ko ta kansu ban bi ba na nufi kofa.

Gurin Baba naje Yana gyara machine dinsa zamu hau, Amma yaki tashi yayi yayi Amma ya kasa.

Jakarsa baban dana sa a kafada ta na gyara nace "Baba ya zamuyi ynxu toh?".

Shima cike da damuwa yace "ban sani ba wallahi Dije, ko Zan bar sa anan ne kawai mu shiga adaidaita tunda Magriba ta matso koh?".

Daga masa kai nai nace "shikenan ba, goben sai azo da Mai gyara".

Gate muka fita muna tafiya Ina fada masa Ya Ustaz ya bani wannan ledar ni dai in Ka cire ice cream din ban gane komai ba, shine ya duba ledar yace shawarma ce 3 da burger 2.

Muna tsaye a bakin titi muna jiran adaidaita Nura ya karaso gurin mu, gaisawa sukai da Baba yace MD ne yace suzo ya kaisu gida.

Duk sai Baba ya rude yace ya koma ya fada masa zamu bau adaidaita, nida ina gefe ina rokon Allah yasa Baba ya yadda don na kara shan AC.

Da kyar Baba ya yadda muka nufo motar fuskata fes da murna, don ma a haka wai ina tunanin Momma a zuciya ta.

Yana daga bayan motar yana kallon su suna tahowa, Ido ya zuba Mata Yana jin wani iri akan yadda take takawo akan titi kowa yana kallon ta, ga fuskar ta ta Kara haske sosai duk gashi ya mammane Mata a goshi tunda Hijab din ya dan yi baya sai gyarawa take amma still gashin yana bayyana.

Ba tare da ya kalli David dake cika yana batsewa ba ya basa umarnin ya fita daga motar Nura zai kai mu.

"Ohk Oga" kawai ya iya fada ya fita yana Jin a duniya bashi da ma'kiyi sama da Dije.

Bude na Baba front sit Nura yai don yaga fitowar David, sannan ya bude min back sit kusa da MD yana wani murmushi a ransa.

Shiga nai ba tare da tunanin komai ba ina shakar kamshin motar.

Baba ne yake nuna wa Nura hanya har muka isa gidan.

Godiya sosai Baba yai muka fita a tare muka shige gidan, har na shiga na dawo baya da Sauri na daga wa motar hannu alamun bye bye.

Wani murmushi ne ya subuce masa Wanda ya bayyana har hakoran sa, zubawa kofar gidan ido kawai yai yana mamakin yadda mutane suke rayuwa a irin gidan, duk da gidan bawai ya lalace bane amma ba penti ko kodewa yai ne ma bai sani ba.

Ya dade yana kallon gidan sannan ya bawa Nura umarnin tafiya....



*DON ALLAH KAR KI FITAR MIN DA LITTAFI, BOOK DINA NA KUDINE IN KIKA FITAR MIN DASHI NA BARKI DA ALLAH*


*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment