Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ita ba".

Girgiza kai Mama tai tace "ynxu dai da Aishan kike kishi yarinyar da bata fi shekara hudu ba".

Daga kai mai ina mar mar da ido, girgiza kai kawai Mama tai tace "wannan kayan Hajara ce ta saki wanka koh?".

Daga kai nai ina murmushi na cire hijab din nace "har wanke min kai tai amma sai da ta bani 200 sannan na yadda".

Rangwashi na Mama tai tace "Allah ya shirye ki, wankan ma wanda ke zai amfana sai kin karbi kudi".

Turo baki mai ina sosa kan nawa na Mika mata ledar hannu na nace "Mama kinga fa nace ta bani ne sbd na siya mana Omon wanki da sabulu namu ya kare kuma Baba baxai bada kudin da zamu siya ba sai karshen wata kin san shi fa".

Shiru Mama tai tana duban Dije cike da kauna, Ashe duk shirmen ta tana kula da sabulun su daya kusa karewa, murmushi tai tace "Allah ya miki Albarka amma da baki karbar mata kudi ba'ai koh, ki wa kanki fada don Allah ki dinga tsafta aure fa za'a miki wata ran Dije".

Boye fuskata nai a bayan Mama nace "tab ba auren da zanyi mama ina nan tare dake kawai sai nayi aure nifa ko saurayi ban da shi, ina kallon yadda Hajjo take ta tara samari amma ni ba Wanda yake cewa yana Sona".

Dariya Mama tai tace "taya za'a ce ana sonki bayan kazanta kike, ita hajjon baki ga kullum take wanka ba tana sa turare amma ke turaren ma sai ana fama kafin kisa".

Sosa bayan wuya na nai nace "toh Zan kiyaye Mama, zan dinga tsallaken kwana daya daya ai nayi kokari ko kuma xan dinga sa alumun".

Tabe baki kawai Mama tai tana kara volume din radion ta.


********
Cikin takun sa cike da kasaita yake fitowa daga building din, gefen sa Salim ne magana suke akan wani business da Elhajj din yake son fara wa, na sabon companyn da zai bude wanda za'a dinga leda da robobi.

Mota Elhajj ya shiga yace "sai gobe ma karasa Salim na gaji sosai".

Dariya Salim yai yace "tab! Lallai tunda yau Elhajj guda ya gaji dole kowa ma ya gaji".

Murmushi Elhajj yai Wanda ya sa dimples dinsa lotsawa gaba daya, girgiza kai yai yace "Allah ya shirye ka".

Dariya sosai Salim yake yace "sai anjima a gaida Madam".

Daga kai yai ya rufe motar, ba tare da ya kalli Driver din ba yace "Gidan Momma"

Cikin bin Umarni yace "ohk sir"

Yana bayan motar yana zana wani sample na atampa da yake son a masa irin su, ya dukufa a zanen har suke iso, bai fita daga motar ba sai da ya gama zanen ya tura sannan ya fita daga motar.

Masallacin dake jikin gidan ya fara shiga yai sallah, tare suka fito shida Papa suna tafiya a tare amma ba Wanda yai ma wani magana.

Sai da suka shiga cikin palourn suka zauna sannan ya kalli Papa yace "ina wuni"

Daga kai Papa yai yace "lafia Elhajj, kuna lafia?"

Daga kai yai a hankali ba tare da yai magana ba, murmushi Papa yai yace "miskilancin naka har yau dai bai sauka akai naba koh".

Sunkuyar da kansa yai yana sakin murmushi kadan

Shigowa Momma tai bayanta masu aiki ne dauke da flask na abinci da tray, Zama tai tana dariya fuskar ta a washe tace "son sannu da zuwa ynxu kazo amma koh".

Murmushi yai ya daga Kai yace "Ina wuni Momma".

Murmushi tai tana kallon sa tace "lafia qalau son, ya gida da harkokin?"

A gajarce yace "Alhamdulillah"

"Masha Allah", ta fada tana mikewa zuba masa zobo Mai sanyi tai ta mika masa tace "gashi nasan tunda ka fita ba lallai kaci abinci ba".

Bai Mata musu ba ya karba yana kaiwa bakin sa idonsa akan TV, sai da ta tirsasa shi yaci abincin kadan don baya cin abinci sosai sai fruits.

Mike wa yai zai fita bayan yai musu sallama da sauri tace "son kaje gurin Malam kuwa, ya min magana rannan yace kana lafia dai koh".

Hade rai yai sosai kawai yasa kai ya fita, kallon Papa tai kamar zatai kuka tace "ban san me yake damun son ba ya dauke kafa daga zuwa gurin Malam gaba daya, kuma in an masa magana ya shiga hade haden rai".

Daga kai Papa yai cike da jimamin sabon sauyin da yake gani a tattare da dan nasa yace "Nima na lura da hakan don ya chanja sosai ba kamar yadda yake ba, duk da miskili ne amma ynxu abin yafi worst".

Rausaya kai Momma tai tace "sai addu'a kawai zamu cigaba da yi masa".

Sai da ya tsaya ya siya wa Saudat tsire don yasan tana son sa sosai sannan suka karasa gida.

Cikin nutsuwar yake tafiya hannun sa rike da jakar sa sai ledar tsiren ta, da sallama a bakin sa ya shigo tana kwance akan kujera tana kallon Sunna TV, da sauri ta mike ta taho a guje ta fada jikin sa.

Dan murmushi ya saki yana tapping bayan ta yace "sannu da zaman gida".

Sakin sa tai tana turo baki tace "uhm sannu koh, ai kai xanwa sannu Elhajj kai ka gaji sosai muje kayi wanka".

Bai ce komai ba yayi gaba tabi bayan sa, Sama suka hau inda dakin sa yake, fita tai ta barshi don tasan bai cika son takura ba a irin wannan lokacin daya dawo a gajiye.

Wanka yai ya zira jallabiya ash colour, turare ya fesa ya fito palourn saman Wanda ya kasance nasa, a nan ya sami Saudat ta tasa tsiren a gaba tana ci.

Murmushi ya mata kawai ya sauna a kan kujera, watermelon juice din da take masa kullum ya dauka ya fara sha yana kallo, sai da ya gama shayewa tas sannan ya kalli Saudat da zuwa lokacin itama ta gama cin tsiren nata.

Mike wa yai yace "muje mu kwanta",

Dan mika tai tace "muje Elhaji na".

Tare suka kwanta ba tare daya neme taba don yasan koya neme tama sai dai ta sa masa kukan shagwaba, tun yana kokarin neman ta sosai har ya hakura sai in ita ta nema da kanta tunda bata cika son yana neman ta ba....


*********

Yau Monday zamu koma school, tunda na tashi nake kunkuni da bata rai bana son makarantar boko kamar me, bama yadda ake kirana da kazama, kuma ina gane karatun dai-dai gwargwado kawai dai bana son zuwa ne don ana takura min da tsokana.

Mama tana lura dani ta min banxa, sai kunkuni nake shiryawa nai cikin uniform dina Riga da wando sai hijab mai girma har ya kusa gwiwa ta, nayi kyau sosai kuma anyi sa'a yau nayi wanka ga kayana a wanke.

Jakata na rataya a baya na kalli Mama nace "nidai gaskia Mama wannan abun ya ishe ni ynxu haka zamu tafi ba'a gama abinci ba gaskia su Umma suna gasa mu wallahi, koko ne fa zasu dama kawai amma sun tsaya nauyin jiki haba don Allah kamar ba Mata ba".

Make mata baki Mama tai tace "ke ban hana ki wai yin rashin kunya ba don gidan ku, na rasa ina kike koyar wadannan maganganun haba, kullum baki da aiki sai yiwa manya rashin kunya".

Buga kafata nai a kasa nace "Mama lokaci fa ya tafi haka zamu tafi ban sha komai ba haba haba ayi adalci a lamarin nan".

Hajjo ce ta turo kofar palourn tace "ki fito zamu wuce ko zaki tafi da kanki".

Hararar ta nai nace "toh sarauniyar iyayi gani nan zuwa, an gama kunun ne?"

Tsaki Hajjo tai tace "aikin banxa mutum sai shegen ci kamar gara, to ba'a gama ba sai ki zo mu wuce ai koh".

A harzuke na taho kusa ita nace "ni kike fadawa maganar banxa, sa'ar kice ni?".

Wani kallo ta min tana Jan tsaki tace "aikin banxa kawai, ai baki kai matsayin da zan tsaya ina fada Miki magana ba wallahi, banxa kazama nafi karfin ki".

Kut** bansan lokacin danai jifa da jakata ba na rarumo wuyanta, cikin duka karfin da Allah ya bani na hankada ta wajen kofar ta fadi ban bata damar mikewa ba na mara mata baya na hau ruwan cikin ta ina danna Mata naushi na baki.

Da sauri Mama ta fito daga dakin kokarin daga ni Mama take amma sai kara sukuwa nake akan cikin hajjo ina bata naushi, ita kuwa ta kasa ko cizo na don duk na hana ta damar da zata cije ni ko ta dake ni.

Ihun yaran gidan ya fito da Baba daga dakin sa da sauri, jan burki yai yana kallon yadda Dije take dukan hajjo duk ta hada mata jini da majina,.

Zuwa yai ya sa kafa ya hambare ni nayi baya na bugi da bango, wani ihu nasa ina mikewa tsaye da sauri ina sosa hannu na inda na buge.

Kallona Baba yai yace "wata iriyar muguwa ce keh, zaki hau cikin ta ki dinga duka".

Sosa hannu na nake na kalli Hajjon dake tsungunne Umma na zuba mata ruwa tana wanke bakin ta daya fashe.

Turo baki gaba nai nace "rashin kunya ta min fa".




*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387


Comments Nd share plz


Mrs A.M


🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎

Free page 3

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Hajjo data gama wanke bakinta ta dago idon ta fal kwalla tace "Baba wallahi karya take min, daga naje kiran ta tazo mu tafi kawai ta fara fada min maganganu".

Hararar ta nai nace "wai ke mai yasa baxa ki daina karya ba, ko da yake kin sha a nono ba shakka".

Wannan Karan Mama ce ta bige Mata baki da karfi, cikin fushi tace "don ubanki ban hana ki wannan rashin kunyar ba wai, taya zaki dinga zagin babba wallahi ki shiga hankalin ki Dije bana son iskanci".

Da sauri Baba yace "A'a a'a Maman Hajara ba sai kin zage ni a fakaice ba, fito fili ki zagan".

Baki bude Mama tace "kamar ya na zage Ka kuma Malam, Allah ya sauwaka na zage Ka kamar wata mahaukaciya".

Yatsina fuska Baba yai ya kalli Dije yace "don uwarki ban hana ki rashin kunya ba, shegiar yarinya kawai".

Turo karamin bakina nai gaba nace "toh Baba kai ma dai ynxu Ka rama zagin da Mama ta auto min, duk kuyi hakuri na makara".

Fita daga gidan nazo yi Umma ta janyo ni baya cikin bala'i tace "kin isa ma ki fita daga gidan nan yau, bayan kin fasa wa y'ata baki ai baki isa ba yarinya".

Kokarin kai min duka take ina kauce sai zillo nake ina kallon Mama da ta koma daki abinta bayan ta ajiye min school bag dita a kofar daki.

Ihu nake ina zillo sai jawo wa Umma Riga nake ina kanannade ta, Inna fure fake murmushi tai saurin mikawa Umma wata karamar ice tace "ungo maza bige ta da shi kafin Malam ya fito, kinsan in ya fito baxai yadda ki buge taba".

Karba tai da sauri ta shiga dukana da ita sai ihu nake ina zillo amma taki sakina, sai data fasa min gefen wuyana sannan ta kyale ni.

Baba da ya shiga ban daki ragewa ya fito a guje yana fadin "lafia meya faru".

Kuka kawai nake ina sosa wuyana da ke jini kadan kadan, ko kallon Baba ban yiba don haushi yake bani ma, ai yana ji ina ihu amma bai zo ya kwace ni ba, dama in har Mama ce nasan baxa ta yi magana ba.

Daka min tsawa Baba yai yace "ba magana nake miki ba, kin tsaya kina kuka wai ke meye matsalar ki ne".

Kallon Umma nai dake ta huci sai kumbura take, hararar ta nai yadda baxa ta gani ba sannan nace Umma ce tasa itace ta dinga dukana gashi ynxu ta karya min wuya ko motsi yaki yi.

A hasale Umma tace "a gidan Uban wa na karya miki wuyar shegia kawai".

Baba dake tsaye yace "ni fa ban gane mai kuke nufi ba, yau sai wani zagina kuke yi".

Kunkuni nai ina mikewa nace "wallahi ba shegia bace ni ga ubana a tsaye nan".

Inna fure dake bayana tace "kana ji koh tana cigaba da fitsarar tata ba".

Jakar makarantar ta na dauka kawai na fita ina sa hijab don ba wanda nake son Kara wa magana kuma.

Sai da suka gama tijarar su sannan Baba ya fita zuwa companyn da yake aiki a matsayin Office assistant, companyn da ya kusan shekara 12 yana aiki wato *ELHAJJ TEXTILE INDUSTRY*

A makaranta ma ban shiga harkar kowa ba kamar yadda na saba, karatu na nai ana tashi nayi gida don bana ciki da magana yau neman abinda zan yiwa Umma na huce nake, tunda nake ba'a taba duka na da icce ba baxa ta daki banza ba.

*WACECE DIJE*

Auwal shine sunan Baba, haifaffan garin kano ne anan iyayen sa suke, su uku ne a gurin su Baba shine Babba sai Maryam da auta Musa, sun taso Kan su a hade kuma Alhamdulillah sun sami ilimi dai-dai gwargwado na Addini dana zamani.

Allah yayi ma iyayen su rasuwa duka, Khadija mahaifiyar su ita ta fara rasuwa sannan baban su shima Allah ya masa rasuwa shekaru 10 baya knn lokacin an haifi Dije.

Mama ce matar sa ta farko, kuma Allah ya albarkace su da samun Yaya Hajara, ganin Yaya Hajara tayi shekara 6 Mama bata sake ko batan wata ba yasa Baba karo aure ya auri Umma.

Zuwan Umma bai sa Baba ya juya wa Mama baya ba don da soyayya mai tsafta a tsakanin su, kusan tare Mama da Umma suka samu ciki farin ciki a gun Baba ba'a magana, an riga haifar Dije da sati daya aka haifi Hajjo, daga nan haihuwa ta tsaya wa Mama sai da Umma ta haifi Yara hudu duka maza(Yusuf, Usman, Sani).

Daga baya Baba ya Kara auro Inna fure bazawa ce ita, don haihuwar ta biyu a gidan data baro, zuwan ta yasa suka hadewa Mama kai sai dai kasancewar ta mace mai gudun bacin rai bata kulasu sam, ya'yan Inna fure Uku biyu Maza mace daya kuma itace autar gidan (Adamu, Ahmad,Halima).

Kamar dai yadda kuka sani Dije bata son wanka ko kadan, da akwai ta da ibada sosai amma fa ita ta tsani wanka da wankin Kai, shiyasa kullum gata nan dai kawai.

Ga shi bata daukar raini, bata jin magana ko kadan lamarin nata sai addu'a kamar yadda Mama take yawan fada.


*****Cigaba

Cikin kwana biyu na rage magana sosai a gidan, wannan shirun nawa ya basu mamaki tunda kowa yasan nidai ba zan yi shiru haka kurin ba ko rashin lafia nake ana Jin magana ta.

Ina kwance a Palourn mu idona a tsakar gida ina jiran naga yaushe Umma zata shiga bandaki na aiwatar da plan dina, don har ynxu ban yafe mata ba kawai dai nayi shiru ne.

Har na cire rai naga ta kai ruwa bandaki ta fita da alama soso zata dauko, a guje na mike na salallaba yadda ba wanda zai ganni na shiga toilet din, jikina har rawa yake na ciro ledata wadda na daure kararan dana siya da kyau a ciki, murmushi nai na bude ledar na juye gaba dayan sa a ciki.

Da sauri na fita tun kafin ta kamani, babbar dustbin dinmu fake hanyar fita naje na yar da ledar na koma daki kamar ban yi komai ba.

Cikin tuhuma Mama tace "mai kika je kika yi Dije".

Kallon ta nai ina narai narai da ido nace "ynxu Mama ba dama na fita sai kin tuhume ni kuma, dubawa nai fa koh Yusuf yana nan, zan aike sa ne".

Girgiza kai Mama tai tace "Allah yasa".

Muna zaune muka jiyo ihun Umma sai ihu take tana fadin "na shiga uku wayyooo Allah kaikayi".

Da sauri muka mike nida Mama muka fito tsakar gidan, tana sanye da zani tayi daurin kirji sai sosa jikin ta take.

Mama ce ta nufi gunta da sauri tace "lafia mene ne?"

Kuka take kashirban tana fadin "kaikayi ku taimaka min don Allah, na shiga uku".

Tuni yaran gidan sun cika tsakar gidan suna ta kallon yadda take ihu.

Ina daga gefe ina murmushi raina fess, nasan ko a haka aka tsaya na rama.

Da kyar Mama ta lallaba ta suka shiga toilet din, wani ruwan taja Mata ta mata tace tayi wanka sosai bayan ta zubar da ruwan da ke toilet din.

Kallona tai ta gyada kai kawai ta shige daki, da sauri nabi bayan ta ina fadin "Mama meya sami Umman wai naga sai kuka take yi tana soshe soshe".

Harara ta Mama tai tace "tun da bakya ji bari Malam ya dawo aure zamu yi miki".

Ihu na shiga yi ina birgima akan carpet dinmu amma Mama tayi biris dani, daga karshe ma kyale ni tai ta shige daki abinta.


********

Kallon Salim yake ran sa in yayi dubu ya baci ko daga yanayin fuskar sa zaka fahimci hakan, dukan table dinsa yai ran sa a bace yace "wannan shine karo na uku knn ana min irin wannan satar, sai na fitar da design Zan sa a min kawai wani company ya buga irin design din da ni na zana da kaina".

Cikin lallashi Salim yace "calm down Elhajj, zamu bi komai a sannu har mu gano waye wannan maci amanar".

Wani kallo yai ma Salim yace "so kake fa kace min na nusu Salim, kar ka manta fa na riga na karbi miliyoyin kudin mutane akan wannan harkar, ynxu mai kake so nace musu knn ehe? Ka san irin asarar da company dinnan zai yi kuwa?".

Cikin rashin mafita Salim ya dora hannun sa a goshin sa yace "ban san me zamu yi ba ynxu Elhajj amma abin yayi yawa, ko kiran su za kai Ka basu kudin su?".

Wata gajeriyar dariya yai wadda kana gani kasan ta takaici ce yace "in ce musu design din da na nuna musu an fitar wani companyn sun yi sa never, nasan yadda zanyi handling situation din".

Kallon sa kawai Salim yake yace"mai zaka yi Elhajj?".

Gajeran murmushi yai yace "gobe zan tura sabon sample din da za'a musu, nasan kuma Insha Allah sai yafi wanda aka fitar kyau".

Gyada kai Salim yai yace "Allah yasa".

Bai kuma magana ba sai maida hankalin sa yai ya dukufa gurin tsara sabon design din, baxai ma nuna wa kowa ba har sai ya tura shi companyn sa dake China tukun.

Bashi ya gama ba sai karfe 10 na dare, ajiyar zuciya ya sauke yana shafa fuskar sa, mike wa yai bayan ya kashe komai na office din ya fita.

Ko da ya isa gida a Palourn kasa ya sami Saudat tana ya zagaye palourn, tana ganin sa ta tafi kansa da sauri ta fada kirjin sa.

Murmushi yai yana rungumo ta jikin sa yace "sorry dear".

Turo baki tai tace "ba wani sorry da zaka cemin Elhajj, kasan yadda hankali na ya tashi kuwa gashi ina ta kiran wayar ka kaki picking call din daga baya ma in na kira sai dai naji switch off".

Murmushi yai a hankali yace "aiki ne ya min yawa shiyasa, amma gashi na dawo ba uhm"

Kallon kauna tai masa tace "muje ciki kayi wanka toh, nasan ka gaji kafin Ka fito bara na hawo ma da juice dinka".

Peck yai mata a goshi ya haye saman, wanka yai ya fito daure da towel a kugunsa, a zaune ya ganta akan couch din dake dakin tana danna wayar ta, bai Mata magana ba sai gaban Mirrow da yaje yana kyalkyale jikinsa kamar mace, shafa wannan goga wancan...

Ido kawai Saudat ta zuba masa tana kallon sa cike da alfahari, ita kanta kasan tayi dacen samun miji kamar Elhajj, kyakkyawana ne buga wa a jarida, shidai gashi ba baki ba kuma na fari ba skin dinsa ko daga kallo zaka san zatai laushi sosai, kakkarfan namiji ne mai tsayi da jiki dai dai mai dauke da faffadan kirji, yana da tarin suma mai laushi irin ta asalin Fulani, Allah ya albarkace sa da gashin gira dana ido Zara Zara ga dogon hancin sa tubarkalla daya dace da fuskar sa, yana da siraran lips pink colour, ba abinda zai fi daukar hankalin Ka a fuskar sa sai Lulu eyes dinsa masu lumshe wa kamar wanda ke Jin bacci, ajiyar zuciya ta sauke tana kallon sa yadda yake gyara zaman rigar baccin sa.

Mikewa saudat ta tace "ko na shigo ma da juice din?".

Daga Mata kai yai kawai yana danna system din gabansa, yana zaune ta dawo bai bar abinda yake ba sai juice din daya ke Karba in ta miko masa, in ya shanye na bata cup din ta Kara zubo masa wani.

Sai da ya gama abinda zaiyi sannan ya kalle ta, yau duk da ransa a bace yake amma yana bukatar mace a wannan lokacin, in bai manta ba kusan 1 months knn bai kusanci Saudat ba.

Hannun ta ya riko yace "ina da bukatar hakkina".

Murmushi tai masa kawai tana narai narai da ido tace "tsoro nake ji kar muje ciki ya shiga, kaga haka nake shan wahala fa in na dau ciki kuma nazo na haihu amma sai dan ko y'ar su koma, sai hudu fa knn".

Matsa hannun ta yai cikin son fahimtar da ita yace "a kullum ina fada Miki duk abinda ya sami bawa rubutacce ne daga Allah, dama can Allah yayi su din ba zaunannu bane kiyi addu'a Allah ya bamu wasu rayyayun masu albark, Allah shi kadai ya barwa kansa, ki kasance mai yadda da Kaddara kinji Saudatu na".

Fadawa kirjin tai tana dariya, murmushi yai shima yana rungumo ta jikin sa cike da kauna......


********

"Toh Allah ya kyauta" Mama ta fada tana janye kafafun ta daga kan tabarmar ganin Inna fure tazo fuu kamar zata taka ta.

Cikin jimami Baba yace "abin da mamaki fa ina fada muku, MD ya gama tsara zanen fa kawai wai yau sai gani yai a news wani company ya buga style din sak da irin Wanda MD yai, Hmm! kuma an rasa wani munafikin ne yake fitar da zanen sau uku knn fah, kuma Karin kayan haushin sai anga zai samu makudan kudade ake masa haka abin tausayi wallahi".

Umma kam dake cin tuwon ta cike da takaicin kaikayin da jikinta yake tace "toh Kai Malam meye naka na damuwa, ruwan sa ai tunda asarar shi kadai ta shafa banda ku".

Tsaki yai yace "shiyasa ban cika baki labari ba sam bakya da gane wa, ai ko asarar muce muma tunda companyn da muke aiki ne sannan da ace wannan harkar tayi wu MD zai mana ihisani mai kyau kamar yadda ya saba, fatan mudai Allah ya taimaka in ya sake wani style din kasuwa ta karbe sa sosai".

"Ameen" Mama ta fada tana mikewa ta nufi daki, don bacci take ji kuma tunda ba girkin ta bane bata ga amfanin cigaba da zaman ba sauro na cizon ta.

Ganin wucewar Mama na mike daga kofar dakin mu na nufi Kan tabarmar Baba, cikin nutsuwa nace "Baba Ka kaini wurin Ogan naka na gaishe sa kaji".



*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387


Comments Nd share plz




Mrs A.M🥰

🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎

Free page 4


Please Login or Register in order to submit comment