Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuni Ya Ustaz".

Girgiza kai kawai yai yace "lafia, wani abun ne?".

Yasir da shima ya mike din yace "MD nima haka na ganta tun da na shigo".

Turo baki gaba nai a shagwabe nace "sbd kawai na saba surutu shiyasa don nayi shiru yau ake ganin kamar ban da lafia, gaskia ya kamata na daina surutu daga yau".

Tabe baki Elhajj yai yace "u're not serious".

Murguda bakina nai ina juyar da kai na gefe.

Da sauri ya bar gurin ganin murmushi na neman subuce masa, shi dai wannan Yarinyar tana basa mamaki sosai.

Yasir ma murmushi yai yace "amma kin bani tsoro gaskia, na dauka ko baki da lafia ne fah".

Dariya nai nace "haka kake Sona dama wai".

Fuskar sa dauke da Murmushi yace "ba dole naso kanwata ba, har Umma na fada mata cewa nayi kanwa a gurin aiki".

Dariya nai na bisa gurin table dinsa ina tambayar sa yaushe zai Kira min Umman mu gaisa.

Anan na zaune yana aiki ina kallon sa, daga fara zuwa na har na soma sanin wasu abubuwan a Kan computer da yadda ake sarrafa ta, don tunda na nuna wa Yasir sha'awa ta akan iya amfani da ita yake koya min kuma Alhamdulillah na fara fahimta.

Lokacin da aka tashi a kasa na samu Baba yana jirana, bayan machine dinsa na hau ina daga wa Yasir hannu muka wuce.



********

Alh Husain ya kalli Hajia Batula cikin jinjina kai yace "ina sauraran Hajia".

Gyara zama hajia Batula tai tace "na fadawa malamin duk abinda muke so, ba dai kudi keke so Yaya ya baka ba, sannan kuma in so samu ne ma duka dukiyar Ka ta Zama tasa".

Murmushi Alh Hussain yai yace "tabbas kuwa Hajia, ai ni kinga ko dukiyar sa bata Zama tawa ba ban damu ba, ni dai kawai ya bani kudin nan".

Murmushi itama tai tace "toh an gama, ya bani kwalli yace Ka saka a idon Ka, in zaka je gurin sa sannan Ka tabbatar cewa kun hada ido sannan Ka tambaye sa kudin, toh da a take a gun zai baka kuma baxai ce ka mayar masa ba".

Wata dariya Alh Hussain yai yace "Hajia Batula sarauniyar Mata, ynxu ma ai sai naje kawai koh ya kika ce?".

Da sauri tace "A'a ba ynxu ba dai koh, Ka bari sai zuwa gobe da daddare sai kaje kaga lokacin sawu sun dauke".

Daga kai yai yana Dan bata rai yace "gaskia amma ban ji dadi amma nifa a yau naso naji saukar kudin nan".

Dariya tai tana riko hannun sa tace "kwantar da hankalin ka shalelen Batula, kamar mun samu kudin nan mun gama.."

Nan suka shantake suna fadin yadda zasu samu kudaden nan Kota yaya ne....



*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387




Comments Nd share plz




Mrs A.MπŸ₯°
🀎🀎🀎🀎
*ELHAJJ*
🀎🀎🀎🀎

Free page 13

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*


A gajiye na shiga dakin mu, duk jikina a sanyaye ga yunwa da nake ji sbd ban ci abinci ba na tafi.

Kallona Mama tai tace "sannu, ai dama ynxu a gajiye zaki dinga dawowa ba dai kin na ce sai kinyi aikin nan ba".

Turo baki nai a shagwabe nace "Kayya Mama an kusa mana salary dai, saura 2 weeks ana mana salary zan siyo waya da zan dinga kallo a ciki, kema Mama zan chanja miki waya".

Dariya Mama tai tace "Allah ya shirye ki, ynxu ke a albashin nawa ne da har zaki siya min waya kema ki siya wa kanki".

Langwabe kai nai nace "Mama ai 25k ne fah, ya isa na siyo waya kema na siyo miki, sannan na siyo mana su Indomie mu dinga dafawa tun da muna da karamin risho a daki ko?".

Shiru kawai Mama tai tace "Allah ya tsare ki a duk inda kike ya miki jagora".

Washe baki nai na tashi na rungume ta nace "yauwa Mamana ta kai na".

Tashi nai na fita tsakar gida, ban hadu da kowa ba in banda Humaira dake Wasa, toilet na shiga nayi alwalar magriba da ake ta Kira.

Daki na shiga na tada sallah a gefen Mama, ina idar wa na janyo flask din da Mama take ajiye min abinci na in har banci ba.

Shinkafa da miya ce Amma miyar bako dadi sbd girkin Inna Fure ce, dama ita haka take duk ranar girkin ta sai hakuri kawai.

A haka na cinye tass a raina ina fadin ana min albashi zan siyo mana kayan miya da yawa muyi mu ajiye hadda kaza zan siyo mana.

Shiru mai ina tunanin Wanda na gani yau ya shigo office din MD, kamar na fadawa Mama sai kuma kawai na share na kwanta a Palour duk jikina a gajiye yake sauki na ma gode weekend.

Washe gari da safe bayan nayi sallah, wanka nai don ynxu kam ina wanka so daya a rana, sai dai in abin ya motsa sai na kiyi.

Shiryawa nai cikin doguwar rigar atampa, duk da roba ce amma ta min kyau sosai bama da ya kasance a shape ne dinkin, mayafi na dauka don bana ra'ayin sa Hijab din yau.

Fitowa nai daga daki ina fari da ido ni ala dole nayi kyau bayan ko powder ban shafa ba.

Kallona Mama tai fuska a hade tace "koma kije ki sako rigar mama ke kullum sai na Miki dole akan sa rigar mama, da girman ki".

Kamar zan yi kuka nace "Mama don Allah to na saka hijab ba sai na sa bra din ba takura min take wallahi".

Tsaki tai tace "in zaki saka toh in kuma baxa ki saba sai ki zauna ki fasa zuwa".

Haka na koma daki na sako bra din, don takaici ma sai kawai na dora hijab akan rigar.

Sallama nai wa Mama na fita, gidan Ya Hajara nake son zuwa in azahar tayi na tafi islamiyya daga nan sai na dawo gida, gobe kuma nake son zuwa gidan Inna.



********

Lumsassun idanun sa ya zuba mata yana kallon yadda take serving dinsa abinci cike da nutsuwar ta.

Dan murmushi yai mata, nutsuwar ta na daya daga cikin abin da yake kara masa kaunar ta a zuciya sa, shi dai baxai ce ga ranar daya soma son ta ba, amma yana kaunar ta sosai, ga tausayin ta da yake ji.

Itama tana lura da irin kallon da yake Mata sai tayi murmushi kawai tana Zama a gefen sa.

Tea din sa ya dauka ya soma sipping a hankali yana kara zuba masa lulu eyes dinsa.

Cike da kunya ta sa hannunta ta rufe fuskar ta tana fashe wa da dariya, shima murmushin yai yace "uhm lafia".

Wani kallo ta masa tace "kai zan tambaya ai irin wannan kallon haka kamar zaka cinye ni".

Cup din hannun sa ya cire daga bakin sa Yana kankance ido yace "ko muje na cinye ki din?".

Dan bude idon ta tai tace "lalala ba ruwana dear, gaskia ni dai ina da kunya".

Mike wa yai a hankali yace "kin sa na koshi ma, muje nayi breakfast din da ke kawai".

A guje ta nufi sama tana dariya tace "tab, ba ruwana daga dawowa ta zaka tara min gajiya".

Taku uku yai ya kamo ta, daga ta yai cak kamar ya dauki jaririya ya nufi saman da ita, sai zillo take tana dariya.

Dakin sa ya shiga da ita ya rufe kofa, soyayya ya shiga nuna mata mai tsayawa a rai, bai bar ta ba sai da ya tabbatar ya sauke mata duk wani nauyi dake marar sa sannan ya kyale ta.

Da kyar ya mike tana turo baki gaba, a shagwabe tace "gaskia dear mugunta ka min yau dinnan".

Wani murmushi yai yace "ni nace ki tafi ki bar ni uhm".

Kwal-kwal tai da ido tace "ai na baka hakuri baxan sake ba, wancan din ma don Umman Nabila din ce tace naje kuma ina jin kunyar nace mata a'a".

Tabe baki yai kawai ya nufi toilet a ransa yana tunanin ko sai yaushe Saudat zata dinga basa hakkin sa duk lokacin da ya bukata kamar ko wanne magidanci.

Shi gashi abin ma ba wani kosar da shi yake ba, kawai manage yake ga raki a gunta kamar me sam bata da juriya.

Yana wannan tunanin ya fito daure da towel, bai gan ta a dakin ba dama kuma yasan ba lallai ya same ta a ciki ba.

Shiryawa yai cikin manyan kaya as usual farare kar, taje sumar kansa yai yana kallon kansa a mirror.

Sai da ya gama shirin sa tsaf sannan ya fesa turare ya sauko kasa hannun sa rike da iPad dinsa yana duba wani design din tabarma.

A Palourn kasa ya samu Salim zaune yana kallo.

Hannu ya basa sukai musabaha sannan ya zauna, a kasalance yace "ya Junior da Mamansa".

Murmushi Salim yai yace "yana lafia qalau, rigima fa ya gama min wai sai ya biyo ni tunda gun ka Zan zo".

Dan kallon sa Elhajj yai yace "mai yasa baka zo dashi ba, nima na dade ban gan sa bafa".

Yar dariya Salim yai yace "baka so ganin sa bane Elhajj, when last kazo gidana kullum ni nake zuwa".

Shiru Elhajj yai yana murmushi yace "shine matsalar Ka?".

Hararar Wasa Salim yai masa yace "kwarai kuwa, tun da aka haifi junior fa ina jin sau daya kazo baka sake zuwa ba".

Bude ido Elhajj yai yace "kai Salim ban da karya ooo".

Fashewa da dariya Salim yai yana Kai ma Elhajj duka a kafada, shima sai ya saki murmushi Wanda ya bayyana hakoran sa sosai.

Tattauna wa suka shiga yi akan kayan da suka shigo da su, da yadda zasu sa musu farashi mai sauki yadda mai kudi da talaka kowa zai iya siya a companyn.

Sai bayan Azahar sannan Salim ya tafi, shima Elhajj din bai zauna mikewa yai ya fita don kasuwar singa yake son zuwa ya duba shagunan sa da yake siyar da kayan masarufi.


********

Da sallama na shiga gidan ina fadin "Ya Hajara gani nan Allah ya kawo ni yau sai na cika cikina da abinci yadda ya kamata, in da akwai dajjaja na yiwa Mama takeaway".

Jin shiru batai magana ba yasa na nufi Palourn, ja nai na tsaya a bakin kofar ganin Baban Aisha a zaune gefensa Ya Hajara ce sai Aishan a Kan cinyar sa.

Zaro manyan idona nai ina kama bakina nace "Abba(kamar yadda Aisha take ce masa) Ka ji abinda na fada dana shigo don Allah".

Dariya yake kawai, Ya Hajara kuwa sai harara take zuba min don takaici.

Marairaice wa nai nace "wasa nake yi fa Abba, na cika cikina a gida taf ba space har na tafi baxan ji yunwa ba, sannan da nace zan yiwa Mama takeaway din dajjaja toh karya nake, ko akwai dajjaja din baxan kai mata ba".

Katse dariyar sa yai yace "toh Dije ko kin kai wa Mama mai zan ce ai Mama Nima mahaifiya tace, itace fa ta haifa min habibty dita".

Janyo hijab nai na rufe fuska ina fadin "Abba wannan kalmar tayi tsauri Ka sassauta".

Dariya ya fashe da ita kawai Yana cewa don nace "Habibity Dije?".

Daga kai nai ina kara rufe fuska ta ni ala dole an fadi kalmar iskanci.

Mike wa yai yana kwantar da Aisha data fara bacci akan kujera, cikin murmushi yace "saki fuskar ki Dije ni kinga ma tafiya xan yi".

Sai a lokacin na cire hijab din dafa fuskata nace "amma dai a dinga sakaya wa don Allah Abba".

Girgiza kai yai ya kalli Ya Hajara yace "Habibity na tafi kinji, ki kula da kanki".

Kokarin mikewa take yai saurin zaunar da ita yana fadin "a'a yi xamanki ki huta ba sai kin yimin rakiya ba, Allah yayi miki Albarka ya sauke ki lafia".

Murmushi tai tana kashe murya tace "Ameen Habibi, Allah ya tsare ya bada sa'a".

Fita yai yana cemin in na koma gida na gaishe da Mama.

Ban iya basa amsa ba sai tagumi da nai ina kallon su, nifa a raina kallon yan iska nake musu, don yadda suke yiwa juna magana suna wani kashe Ido ai sai Yan iska.

Tsaki Ya Hajara tai tace "kedai zanga yaushe zaki yi hankali wallahi".

Ajiyar zuciya na sauke nace "ai baxan iya baki amsa ba , don kun tsotse min man kai tass, Ya Hajara dama haka kike lallai sai na fada wa Mama tabdijan".

Dakuwa tamin tace "Zan ci mutuncin ki wallahi Dije, shashasha kawai".

Da sauri na mike ina fadin "a'a basai kin zage ni ba Ya Hajara, bara na koma gidanmu daga zuwa sada zumunci sai zagi ya biyo baya lala-lala".

Tagumi tai tana kallona tace "ynxu sai ki koma gidan Dije?".

Cike da tabbatar wa nace "tabbas, yo mai zan xauna yi kina zagi na"

Kwantar da Murya tai tace "toh kinga yi hakuri, zauna Wasa nake miki haba yar kanwata".

Turo baki nai sannan na zauna, ina cewa "yau shinkafa da wake zan mana koh Ya Hajara".

Dariya tai tace "kamar kinsan dama jiya ya siyo min kayan salad, bani labarin gurin aikin naki mana".

Gyara zama nai na shiga bata labarin yadda office din suke da yadda MD yake mgana, har kokayar sa nake.

Cikin tsokana Ya Hajara tace "uhm su Dije wannan Ya Ustaz din kodai kodai".

Da mamaki nace "ban fashimta ba, kodai me Ya Hajara?".

Dariya tai tace "kodai kin fara son sa ne".

A razane na mike tsaye kawai sai na fashe da kuka ina yarfe hannu.

Itama mike war tai tace "lafia".

Kuka nake sosai ina fadin "Na shiga uku na ni Khadija Auwalu, taya xaki ce ina son Ya Ustaz wannan babban sa'bo ne kika fada, ya kusa haifa ta fah innanillaihi wa innanillaihir raji'un".

Kokarin danne dariyar ta Ya Hajara tai tace "shikenan yi hakuri tsokanar ki nake dama".

Da kyar nayi shiru amma maganar tana raina, duk sai naji ma raina ya baci in banda sabo taya za'a hada ni da Ya Ustaz.

Sai bayan Azahar na tafi islamiyya lokacin na cika cikina dam da shinkafa da wake.

Gab da magriba na dawo, ban samu Mama ba sai dai Inna fure ta cemin ta shiga makota dubiya.

Zama na nai a kofar dakin mu ina azkar din maraice cike da nutsuwa.


********

Shigowa yai paloun ba tare da yai sallama ba kamar yadda bokan ya fadawa Hajia Batula.

Papa dake zaune a kan kujera hannun sa rike da Hisnul Muslim yana karanta addu'oin maraice ya dago suka hada ido da Alh Hussain.

Abin da ya gani a idon sa ne yasa shi saurin dafe kansa Yana fadin *Hasbunallahu wani'imal wakil*

Murmushi Alh Hussain yai cike da kwarin gwiwa ya zauna yace "Yaya barka da yamma".

Murmushi Papa yai yace "barka kadai Hussain ya iyalan naka?".

"Alhamdulillah" Alh Hussain ya fada yana gyara zaman sa.

Shiru Papa ya masa ya cigaba da Azkar dinsa, bai saurare sa ba sai da ya gama ya ajiye sannan ya juyo ya kalle sa yace "ina jin Ka".

Da kyar Alhaji Hussain daya gama cika sbd share san da yai yace "dama akan 500m din da nake so ne shine nace bara nazo Ka bani yauu".

Kallon sa kawai Papa yake a ransa yana tunanin Anya Hussain kan sa daya kuwa.

Nutsuwar sa ya kara tattaro wa yace "tun tuni ai na fada ma baxa Ka samu wannan kudin a hannun ba koh, haba Husain Ka sake duba wannan abin da kake son yi, bafa lallai bane kudin Ka su dawo har da riba ba yawanci irin wannan asara kawai ake yi".

A fusace ya mike yana cewa "Yaya kawai in baxa Ka bani ba kace baxa Ka bayar ba, ba sai Ka tsaya kana min baki ba haba".

Murmushi Papa yai yana mikewa yace "baxan bayar ba Hussain". Daga haka ya fita zuwa masallaci.

Bin bayan sa da kallo Husain yake ji hake kamar yabi bayansa ya shake sa don haushi.

Fita kawai yai yaja motar sa zuwa gida a ransa yana fadin tabbas Hajia Batula sai nayi maganin ki wallahi tun da kudin dana baki a banxa Kenan, aiki bai yi ba.

Lokacin da ya isa gida ko tsayawa yin kwakkwaran parking bai yiba ya bude kofar ya fito a fusace.

Cikin gidan ya shiga amma bai same ta a Palourn ba sai ya nufi dakinta.

A zaune ya same ta akan kujera yana danna waya, fisge wayar yai cikin huci yace gurin wani dan iskan malami kika je, gashi kwallin ba aikin da yayi Yaya idona ya kalla yace baxai bani kudin ba wannan wani irin wulakanci ne.

Mikewa Hajia Batula tai tace ban fahimci zancen naka ba Alhaji.

Tsaki yai yace ke kinga Bana son iskancin banxa, duk gurin Wanda kika je ya baki wannan kwallin ki Koma ya dawo min da kudina, don na fasa sam bai san abinda yake ba.

Daga haka ya fice a dakin yana banko Mata kofa.

Bin bayansa da kallo tai tana yatsina fuska, dogon tsaki taja tace aikin Banxa aikin wofi, ai ni ynxu abinda nake so shine na hallaka Ka, ta haka ne kawai Zan mallaki asalin masoyi na Hassan abin kaunata, ba kai ba da nake zaman hakuri da Kai............


Tooofaaaaaa😱😱😱😱😱


*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387


Comments Nd share plz



Mrs A.MπŸ₯°
🀎🀎🀎🀎
*ELHAJJ*
🀎🀎🀎🀎

Free page 14

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*


Washe gari kam ban yi wanka ba, don da kiwar tashi nai wanka na tashi.

Shiryawa kawai nai cikin riga da zani, sai dogon hijab dana sa, ban bari Mama ta gane ban yi wanka ba don nayi dakale a bandaki.

Sallama nai Mata na fito hannu na dauke da ledar da Mama ta bani na kai ma Inna, tafiya nake a kafa cikin nutsuwa ina tunanin yadda zan gano Wanda ya shigo office din Ya Ustaz shekaran jiya, kawai haka nake ji kamar cutar sa ake son ayi.

Na hau titi ina tafiya kawai naji an watso min ruwan gefen titi daya taru, wani irin birki naja na tsaya ina kallon Jikina da ya baci gaba daya da ruwan har Kan fuskata.

Daga ido na nai daya soma kankance sbd bacin rai na kalli tsaleliyar motar da take dawowa baya, sunkuyawa nai na dauki dutse a hannu na na nufi gurin motar data dawo ta tsaya.

Duka window din gaban motar na fara yi da karfi ina fadin fito, fito wallahi baxan yadda da wannan cin mutuncin ba.

Baya na matsa ganin an bude kofar an fito, kankance ido na sake yi ina kallon sa, kamar dai na taba ganin sa amma na rasa a ina ne.

Tabe baki nai nace "sannu, meye fisabilliahi zaka watsa min kwatamin titi har fuskata, sbd Ka ganni yar 'kan'kanuwa shine zaka min wannan cin kashin, to tsaya kaji bar gani na haka shekaru na 30 kawai dai kyaun jiki ne da Allah ya min".

Dariya yake son yi amma yasan matukar yayi dole a samu damuwa, shiyasa ya daure yace "haba Malama Khadija kiyi hakuri bamu sani bane, kin ga ma bani nake driving din ba".

Baki na kama nace "lala-lala wato ashe da mai yankan kai nake tare, taya Ka san sunana daga gani na, na shiga uku ni Dije".

Ynxu kam sai da ya saki dariyar sa son ransa sannan yace "baki gane ni ba wai, Nura ne fah security din MD".

Zare ido nai nace "sai kace min Nura ne mai daurarriyar fuska, toh ba abinda ya shafe ni dole sai kun bani hakuri akan wannan wulakancin da kuka yimin, meye zaku watsa min ruwa a fuska da jiki gashi duk kun bata kayana".

Numfashi na sauke na cigaba da cewa "ko dan kace min security din Ya Ustaz ne Kai kana tunanin zan kyale Ka, lala-lala dole sai kun bani hakuri".

Rage murya ta nai nace "kai Malam Nura ko shi kansa ya Ustaz din ne dole ya bani Hakuri".

Ido ya zaro yace "MD din da Kan sa Khadija?".

Wani lumshe ido nai cike da Jin dadi nace MD zai bani hakuri nace "tabbas, ko ance ma ni ina Jin tsoron sa ne".

Zai yi magana wanda ke zaune a driver sit ya bude motar ya fito, hararar sa nai ina kau da kai na gefe.

Shi kuwa bai ko kalle ni ba sai Nura daya kalla yace "Oga na magana fah".

Daga masa kai Nura yai ya matsa ta gefen back sit, window din aka dan zuge kadan yai masa sannan ya maida window din ya rufe.

Dawowa guri na yai yace "Oga yace ki shiga mu kai ki inda zaki je".

Idanu na bude sosai ina dafe kirji nace "wa, ni Dije tabdijan ai ba abinda zai sani na shiga cikin wannan tsaleliyar motar haka kurin".

Sassauta murya yai yace "don Allah ki shiga Malama Khadija, kinga ba abu bane mai dadi ace kina tafiya a haka duk hijab dinki ya baci".

Girgiza kai nai nace "ngd amma an hanani shiga motar wasu, in Mama ko Baba suka ji labari sai sun dake ni".

Langwabe kai yai yace "ki shiga kinji, ai ko baban in yaji Oga ne baxai fada ba".

Hannu masa na rike kugu nace "Mama fah, kai kasan Mama kuwa tace min in mace na shiga motar Maza cikin shege suke mata ta haihu, ni baxan shiga ba gaskia haka kurin ayi min ciki".

Kama baki yai yana kallon ta Ashe dai duk kaudin baki ne amma bata san komai ba.

Murmushi yai yace "Oga ne fah Amma baki yadda da shi ba?".

Kau da kai na gefe nai nace "ban yadda dashi ba Sam, don Mama ta cemin ko waye in har ba Baba bane ko Dan gidan mu kar na shiga motar sa in yace na shiga, ba ruwana".

Gurin Mirrow din ya Dan sunkuya ya kwankwasa, sauke glass din akai yai magana aka rufe.

Dawowa ya kara yi gurin zai yi magana, Aka bude kofar motar ya fito cikin nutsuwa.

Lumshe idona nai jin lafiyayyan kamshin turaren da nasan shi kadai yake amfani dashi ya cika gurin.

Da sauri na daga kai na na kalle sa, yana sanye da manyan kaya light blue, yayi kyau sosai Kan sa sanye da hula wacce ta dace da dinkin rigar tasa.

Gabana ne yake faduwa ganin yadda yake takowa gurin da nake tsaye.

Shi kuwa bai tsaya ba sai da yaje daf da ita sannan ya tsaya, zuba Mata lulu eyes dinsa yai kafin a hankali kamar mai jin nauyin bakin sa ya bude yace wuce ki shiga mota.

Shagwabe fuska nai ina mar-mar da ido na, kafin nace nidai gaskia bana so na shiga ya Ustaz, Mama tace ciki ake yiwa mutum.

Kara zuba mata narkakkun idon sa yai yana jin wani abu kamar magnet yana jan sa

Please Login or Register in order to submit comment