Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baba yace "toh ai ita tace tana so kuma na nema Mata, sannan da kike maganar wata makaranta ai nasan da makarantar kuma sai da na fada masa yace bakomai in ta tashi sai tana zuwa tunda tana son aikin".

Girgiza kai Mama tai tace "baxan taba yar da ba Malam, yarinyar da hankali bai wani gama shigar taba kake so ta dinga gyara wa gardi office baxai yibu wallahi".

Mikewa Baba yai a fusace yace "sai kiyi tayi kuma dama ai taimaka miki nai, in tana aikin albashin ai ya isa a dinga Tarawa har zuwa lokacin da Allah zai kawo mata miji tayi aure, kinga kin samu kudin da zaki rage wasu abubuwan, amma kiyi tunani dai wannan damar in ke baxa ki yadda ba zan fadawa Umma nasan da gudu zata bar Hajjo taje".

Kuka nasa da karfi ina girgiza Mama nace "don Allah kiyi hakuri ki bar ni naje Wallahi ina so Mama".

Tsaki Mama tai ta ture ni tace "sai kiyi tayi dai amma ba inda zaki je wacce bata san ciwon kanba kawai".

Zama nai a Palourn ina dora kaina akan gwiwa ta ina kuka, Allah ya sani ina son wannan aikin kodan In an min albashi na dinga siyo wa Mama kayan dadi tana ci da kuma su Omo tunda bata Sana'ar komai, duk abinda ta fara siyarwa sai Umma ko Inna fure su fara irin Sana'ar shi yasa kawai ta daina komai....


***********

Idonsa akan Saudat da take masa list din abubuwan da take bukata na bikin kawarta.

Lumshe ido yai a hankali ya bude bakinsa yace "uhm ina ji"

Gyara zama tai tana Kallonsa tace "yauwa Elhajj ankon guda biyu ne ba tsada sosai 300k ne kuma kaga kudin dinki da kudin veil da bag duka dai in Ka bani 500k ya isa sai gudunmawar da zan bayar 100k kaga bikin Kanwar Nabila ne fah".

Kallon ta kawai yake har ynxu yana mamakin irin kudin da take tambayar sa lokaci lokaci masu nauyi haka kuma sai tace wai ba yawa, tabe karamin bakin sa yai yace "yaushe zaki tafi Lagos din".

Murmushi tai tasan tunda yace haka ya yadda zai bata kudin in tayi sa'a ma ya kara Mata, fari tayi da idon ta tace "next week za'a fara amma in son samu ne na tafi ko Sunday ne zamuyi shirye shirye fa kasan nice babbar kawar Nabila".

Mikewa yai cikin rashin damuwa yace "xan Miki transfer din kudin gobe insha Allah, har da Wanda zakiyi booking flight din".

Cikin farin ciki tayi hugging dinsa tace "bara naje na fara hada kayana".

Bin ta yai da kallo kawai har ta sauka, ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin wai zaman aure ma suke yine shida saudat, tabbas yana Jin wani abu ba dai-dai ba amma bai San ta ina zai fara ba...

Ganin in ya fara tunanin hakan zai sa mishi ciwon kai karshe ya hana shi bacci kawai ya shiga dakinsa ya kwanta bayan yayi addu'ar kwanciya bacci....


*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387



Comments Nd share plz



Mrs A.M🥰

🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎

Free page 6

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Washe gari haka na tashi idona sunyi luhu luhu sbd kuka amma Mama ko nuna tasan mai nake yi batai ba.

Ko tsokanar Hajjo ban yi ba don ko da ta kulani banza na Mata kamar ba Dije ba.

Sai da yamma tai na shirya cikin hijab dina na zuwa makaranta, kallon Mama nai da ko kallona bata yiba tun safe a hankali nace "Mama na tafi makaranta".

A dakile tace "Allah ya tsare".

Ajiyar zuciya na sauke na fita cikin sanyin jiki, zuciya na bani kwarin gwiwar zuwa gun Inna kakata amma kafin nan gwanda naje gun Ya Hajara na fara fada mata.

Duka jikina a sanyaye yake, Allah ya sani naci burin wannan aikin ko ba komai Zan dena zama haka ba wani abu, duk da karancin shekaruna amma ina son naga ina samun hanyar da kudi xasu dinga shigo min ko dan Mama da kuma bakin kwadayina.

Ina wannan tunanin har na isa gidan, tura kofar nai na shiga tsakar gidan, ba kowa sai dai ina jin alamar TV daga palourn.

Ajiyar zuciya na sauke ina nufa hanyar palourn, sallama nai ina daga labulen na shiga, dagowa Ya Hajara tai dake zaune tana kallon Indian series a MBC Bollywood.

Zama nai akan kujerar dake gefen tata nace "ina wuni"

Ya Hajara data zubawa Dije ido ganin yadda ta shigo jiki a sanyaye tace "lafia qalau, lafia dai ko na ganki haka ko ciwon kafar Mama ne ya tashi?"

Bude idona dana lumshe nai nace "Uhm ba ciwon ta bane amma ina cikin damuwa wallahi Ya Hajara".

Da mamakin abinda yake damun Dijen tace "lafia dai koh mene ya faru?".

Rau-rau nai da idona nace "Ya Hajara kin san dai yadda muke samun matsalar kudi wani lokacin tunda Mama ba Sana'a take ba, kuma duk Sana'ar data fara sai su Umma sun fara irinta don su kashe mata kasuwa".

Cikin zakuwa Ya Hajara tace "nasan wannan tuni ai Mene ya faru?".

Turo baki nai nace "haba don Allah ki tsaya mana kiji abinda yake faruwa, kina katse ni gaskia".

Murmushi Ya Hajara tai tace "toh Dijen Mama na bar katse ki".

Gyada kai nai nace "yauwa, toh kuma dai kinsan yadda nake Nima, duk Sana'ar dana fara sai na cinye jarin garin kwadayi na, ko kuma gurin siyo Omo ko sabulu duk da dai ni bana wani wanka sosai amma Mama ai kullum tana yi".

Kara gyara zama nai ina marairaice fuska nace "shine fa nace wa Baba ya samo min aikin a companyn da yake aiki ko Shara da goge goge ne sai nayi, to Allah cikin ikon sa sai jiya yake cemin MD din companyn yace nazo ya dauke ni zan dinga gyara masa office amma Mama tayi tsalle ta dire tace baxab je ba, yau da kyar ta min magana sbd haushi ni kuma nidai ina son na samu aikin nan ne don mu dinga rufawa kanmu asiri kinga ba kullum Baba yake bada kudi ba".

Da Mamaki tace "haba Dije ai dole Mama ta hana ki wannan aikin, gardi fa zaki dinga gyara wa office kuma kar ki manta kina zuwa school duka duka shekarun ki 15 har zaki dinga aiki a company".

Cikin haushin maganar Ya Hajara nace "ai Shi MD din yace bakomai Zan iya zuwa duk lokacin dana dawo daga school bashi da damuwa, sannan maganar gaskia Mama ai tasan kalar tarbiyyar data min ni bana ma barin namiji na rike min koda hannu balle ace ciki zanyi haba haba a duba lamarin nan dai gaskia".

Kallona kawai Ya Hajara take yi taga alama son aikin nan yayi wa Dije katutu a zuciya, ajiyar zuciya ta sauke tace "ynxu toh me kike so ayi Malama Dije".

Murmushi nai nace "yauwa, ynxu kike magana kamar Ya Hajaran Dije, shawara nazo nema gun ki, so nake da naje na fadawa Inna tazo ta sa baki nasan in har tayi wa Mama magana zata yadda".

Rike baki Ya Hajara tai tace "fito fili kice karan Mama zaki kai kawai gurin Innar, toh nidai ba ruwana wallahi haka kurin baxa ki shafa min kashin kaza ba kije duk abinda ya biyo baya kar kice nasan maganar".

Kau da kaina gefe nai cike da takaici nace "Allah in har Mama tamin fada ce Mata zanyi kece kika bani shawarar zuwa gun Innar".

Salati ya Hajara tasa cikin fada fada tace "kinga Dije ki fita harka ta wallahi, ba ruwana kar ki sake ki sani a shirmen ki in ba haka ba ynxu na Kira Mama na fada Mata".

Mikewa nai kawai na dauki jakata na fita ina kunkuni, dake ba nisa daga gidan Ya Hajara zuwa gidan Innar duk unguwa daya ne.

Da sallama na shiga gidan ina fadin "tsohuwar tana nan ko ta wula ne".

Inna dake zaune a madaidai cin tsakar gidan ta tace "tana nan da rai bata wula ba tunna sai Naga ya'yan ki ja'ira".

Dariya nai ina shigowa, Zama nai a gefen ta nace "Inna ina wuni, ya jikin tsufa kuma".

Fuskar ta dauke da murmushi tace "Lafia qalau, ya wurin su Maman taku".

Turo baki nai ina kwantar da kai na akan cinyar ta nace "lafiar su qalau, ai a hanya na hadu da wani bazawari nayi masa tayin ki na gaji da ganin ki haka a zaune".

Duka ta kai min na mike da sauri ina fadin "Kayyasaaa..."

Salati Inna tai tace "wai dama kina nan da wannan banxar dabi'ar taki ta cewa kayyasa".

Fari nayi da ido nace "kayyasaaa Mai za'a fasa, kawai kwana biyu na dan rage sbd buge min baki Mama take".

Dariya Inna tai tace "tamin dai-dai ai haka ya kamata tan Miki".

Bakina na turo cike da shagwaba nace "Naga alama ynxu kin daina Sona ai dama".

Riko min hannu tai tace "haba dai kawas ai ban isa na dai na sonki ba, kece ma dai Zan ce kin daina yayina ynxu sam baki shigowa gun nawa".

A hankali nai kasa da kai na nace "makaranta aka koma shiyasa bana zuwa, mun shiga aji 4 fah".

Murmushi Inna tai tace "Allah ya bada sa'a ya taimaka".

"Ameen" na fada ina wasa da zaren tabarmar da muke Kai.

Inna dake lura da ni tace "lafia kuwa Kawas wani abun ne".

Ajiyar zuciya na sauke nace "wani abu ke damu na Inna, ban tsaya jin abinda zata ce ba na shiga bata labarin komai".

Inna data gama sauraro na tace "tabdijan gaskia dai Maman ba tai tunani ba, toh Allah na tuba meye a ciki don kina aiki, ni banga wani laifi ba tunda dai halaliyar ki zaki je nema kuma ai tare kuke da baban naku nasan kuma zai sa Miki ido sosai".

Murmushi nai cike da Jin dadin na samu wanda ya yadda Dani nace shine nace "bara nazo na fada Miki ko zaki Mata magana tayi hakuri ta barni, Allah Inna zan kiyaye dukkan wani abu dana San zai bata mata rai insha Allah".

Dafa kai na Inna tai tace "zan zo har gidan gobe na Mata magana nasan zata ji, ynxu ki tashi ki tafi an kusa tashi daga islamiyyar kar taga kin dade, nasan in har taji cewa guna kika zo ran ki sai ya baci".

Dariya nai ina mikewa nace "Ina Yusrah wai Inna, ban ganta ba".

Tabe baki Inna tai tace "wannan gantalalliyar tana islamiyya daga can kuma nasan sai ta biya ta gano uwar ta".

Dariya nai nace "haba dai Inna, to ina ruwan ki in taje ganin mamanta".

Hade rai Inna tai tana mikewa tace "dama ai bance komai ba, in ta dawo Zan ce mata kina neman ta goben sai Muzo tare Insha Allah".

Dan kiss na Mata a kumatu nace "I love you Innata".

Ture ni tai cike da Wasa tace "bana son wannan yahudancin meye kuma na tsotsar min kumatu".

Dariya nai nace "kayyasaaa, sai anjima"

A guje na fita ganin ta dauko murfin kwano, zata kwalo min.

Lokacin dana koma gida Mama bata cemin komai ba bayan abinci na data nuna min inda ta ajiye, Nima da yake nasan abinda naje na aikata sai naja kai na gefe ina gama cin abincin na fita tsakar gida gurin kanne na..



***********

Cikin dakin ta ta shigo hannun ta rike da gurasa guda biyu, ajiyar zuciya ta sauke ta kulle kofar da key.

Gaban wani katon standing mirrow dake dakin ta tsaya fuskar ta dauke da wani irin murmushi na mugunta, wani guri na danna a jikin mirror din kofar ta bayyana yar karama.

Key din hannun ta tasa ta bude kofar ta durkusa ta shiga, karamin daki ne sosai wanda yake a matse, a dakin da akwai toilet sit da tab, sai daga gefe kuma zani me guda daya a kasa.

Cikin mugunta ta sa kafar ta ta zunguri matar data kwanta a kan zanin ta dukunkune jikinta, a razane matar ta dago tana kallon ta .

Murmushi tai tace" sannu Amina kar ki damu kin kusa mutuwa ki huta da wannan azabar koh, lokacin ki ya kusa don na Kan dutse yace ya kusa bukatar jinin ki, kinga Nima na huta da dawainiyar kawo miki abinci kullum".

Wacce aka Kira da Amina ba abinda take sai hawaye, duk da an shafe tunanin ta bata gane komai tsawon shekaru 20 amma tasan cewa mugunta wannan matar take Mata, a hankali ta dago hannun ta da sukai datti sosai ta share hawayen ta.

Murmushi Matar tai tana wulla mata gurasar hannun ta, a wukakance tace "gashi nan abincin kine na yau da gobe sai kisan yadda zaki yi da su".

Daga haka ta fito daga dakin ta kulle kofar ta mai da mirror din yadda yake kai baxa Ka taba cewa da akwai wani abu a bayan kofar ba.

Amina kuka take sosai ita ta manta komai nata, tunanin ta ya shefe bare tayi addu'a ta nai mi tsarin Allah, ganin kuka ba maganin komai zai Mata ba kawai ta rarrafo ta dauki gurasar ta kai baki tana ci tana kuka......


********

Cikin takun sa na cikakken namiji yake takowa zuwa dakin taron, duk da fuskar sa a hade take amma ga wadanda suka San sa su gani suke yau da sassauci kodan sbd samun nasarar da companyn su yai akan sabbabin style din da ya fito dashi.

Dakin meeting din ya shiga kowa ya hallara wadanda suka dace ace suna gun, zama yai akan kujerar da aka tana da sbd Shi.

Da farko ya fara yaba musu ne bisa jajircewar da sukai gun kawo cigaba a companyn sannan ya musu albishiri cewa ko wanne ma'aikaci za'a basa kyautar rabin albashin sa yau.

Nan da nan suka fara tafi cike da murna, wannan ba sabon abu bane a gunsu, in har companyn su yayi cinikin makudan kud`ad`e toh yana musu kyautar kudi amma bai taba musu kyauta mai tsokar wannan ba.

Mike wa yai cike da jarumta ya fito gefen sa Salim ne magana suke a hankali, cikin nutsuwa yace "sai mun yi magana na gaji gidan Momma zan wuce'.

Da dan Mamaki Salim yace "acan zaka kwana wai?".

Lumshe idonsa yai ya bude yace "yes, Saudat ta tafi Lagos ne".

Hade rai Salim yai yace "gaskia Elhajj ya kama ta Ka taka ma Saudat birki, ita kullum tana hanyar tafiye tafiye haba zaman aure take fah".

Wani kallo yai ma Salim ciki ciki yace "matar Ka ko tawa?".

Dariya Salim yai yana matsawa yace "sarkin kishi matar kace ina ruwana shawara na bayar".

Hade rai yai yace "bana son shawarar toh".

Mota security dinsa ya bude masa ya shiga ko sake kallon Salim bai yiba.

Murmushi Salim yai bayan wucewar su yace "Allah ya shirya min kai Elhajj".

A gajiye ya shigo palourn gidan nasu, gaishe da Momma yai ba tare daya zauna ba yace ta sa a kawo masa abinci part dinsa anan zai kwana.

Wuce wa part dinsa yai yana zuwa kayansa ya cire ya shiga wanka, bai dade ba ya fito duk jikinsa ruwa.

A nutse ya goge jikin sa yasa Riga da wando masu taushi, turare ya fesa ya fito hannun sa rike da waya yana magana da Saudat dake masa korafin bai kirata ba yaji ya ta isa.

Lumshe idon sa yai a gajiye yana Zama akan kujera yace "na gaji ne kuma aiki yamin yawa uhmm".

Daga dayan Bangaren Saudat ta turo baki tace "duk da haka, bkm amma na hakura baxan iya dogon fushi da kai ba".

Dan murmushi yai yace "toh bara naji abinci xan Kira ki".

"Tohm" kawai tace ta kashe wayar.

Abincin da aka kawo masa ya bude, murmushi yai ganin tuwo da miyar kuka, yana son abincin gargajiya sosai amma saudat bata masa hasali ma bata iya girki ba mai aikin tace take musu ita ma kuma abincin na turawa ne yawanci shi kuma yafi son na gargajiya sosai.

Zama yai yana ci cike da nutsuwa abincin ya masa dadi sosai, sai da ya gama sannan ya mike ya nufi cikin gidan don gana wa da Papa akan sabon companyn da yake son budewa na robobi yana bukatar shawarar Papan.


********

Washe gari da wuri na tashi, alwala nai nayi sallah kasancewar girkin Mama ne, tsakar gida na fito na share bayan na share dakin mu, wannan dokar Baba ce duk mai girki itace zata sa yaranta su share tsakar gida da kuma wanke bandaki ko kullum har sai ta gama girkin.

A gurguje na wanke toilet ina gamawa na yi wanka sbd yau rabona da wanka kwana uku knn.......



*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387


Comments Nd share plz



Mrs A.M🥰

🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎

Free page 7

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ina gama wankan na shiga daki, a gaggauce na shirya cikin doguwar riga na fito na dora ruwan xafin Koko.

Kafin Mama ta fito har na gama dama koko na zubawa ko wanne daki a cikin jug dinsu, daukar namu nai na kai daki.

Ina cikin shan koko Mama ta shigo cikin atampa sai kamshi take, wannan dabi'ar tace tunda na tashi haka nake ganin tana yi kullum tace dakin Baba toh in zata dawo kullum a shirye zaka ganta fess tayi wanka tana kamshi.

Gaishe ta nai ta amsa fuskar ta adan sake, zama tai tana fadin "ko ke fa gashi nan kinyi wanka tsaf da ke amma ki dinga zama da kazanta nidai nasan wannan na dabi'a ta bace Sam".

Sunkuyar da kai na nai kawai ina juya cup din koko na a hannu, tabe baki Mama tai tace 'ban gane wannan sunssunkiyar da kan da kike ba, ko ni dince baki gane ba".

Murmushi kawai nai gabana yana faduwa, ai ni yau banga ta magana ba tunda nasan abinda naje na hada a gidan Inna.

Ganin naki magana kawai Mama taja tsaki tana janyo jug din zata hada nata Kokon tace "ke kika sani kuma, wannan sabon munafurcin in ma don na yadda ne kije kina aiki a gurin wani gardi toh a banxa don ba yadda xan yi ba".

Turo karamin bakina nai ina mikewa tsaye, fita nai daga dakin na kai cup din gun pampon mu da yake tsakar gida, wanke wa nai na dawo dashi na ajiye a cikin daki a wata drawer da muke sa kayan kitchen dinmu.

A dakin nayi kwanciya ta bacci ya dauke ni.

Cikin bacci naji an dala min duka a cinya, da sauri na mike ina murza idona don dukan ya shige ni sosai.

Yusrah ce a zaune tana dariya ganin yadda na tashi ina murza ido, ai ban tsaya komai ba na janyo hannun ta ta shiga dala mata duka a baya a fusace.

Dariya take kwalkwala wa tana fadin "haba Kawas Inna kiyi hakuri nidai gaskia kar ki burma min baya kinji'.

Cikin haushi nace "ban da iskanci ina bacci kawai xaki zo ki dala min duka haba banxa kawai".

Mikewa tai tana dariya tace "dallah can raguwa kawai".

Wani kallo na mata ina daura dankwali na nace wace "raguwar kema dai kinsan bani ba dai koh, sai dai in ke din".

Girgiza kai tai tace "gaskia fa, ai baxan manta cewa duka na kike ba da".

Mikewa nai ina tabe baki nace "tare kuke keda Inna?".

Daga min kai tai tana Zama a kan gadon tace "ai jiya take cemin kinzo kin ce, ta gaishe ni yau kuma da sassafe tace mu shirya muzo xata ga Mama".

Kallon ta nai naga taci kwalliya da mamaki na kama baki na xan yi magana Kenan nace "bara dai naje na gaishe da Inna sai na zo zamu yi magana".

Dariya Hafsa tai tace "oh Hajia Dije knn".

Palourn na fito anan na samu Inna da Mama suna zaune da alama magana suke yi, Mama na gani na ta galla min harara tayi kwafa.

Narai narai nai da ido na kalli Inna cike da tsoro nace "Inna kin ga Mama tana harara ta koh?".

Inna dake zaune ta dan rangwafo akan kujera tana gyada kai, kallona tai sannan ta juya ta kalli Mama tace "gaskia Maman Hajara bana son wannan abun, meye kuma zaki wani kalle ta fisabilliahi, toh ahir kar naji kar na gani kin Mata wani Abu bayan tafiya ta".

Kallon Inna Mama tai tana sunssunkuyar da kai tace "Inna bafa abinda nace xan mata".

Watsa Hannu Inna tai tace "atoh kar ki samo ma, in har da kin tsara yadda zaki lallasata bayan tafiya ta, yarinyar nan sbd ke take son fara aikin nan don ta dinga taimaka miki tunda nidai take fada min dalilan da zai sa tafara aikin nan bata ambaci kan taba, sau daya ne tace zata dinga siyo muku abin kwadayi kuna ci haba, amma ke sai kice baxa tayi ba haba haba".

Kan Mama a kasa tace "Inna ni gani nai da kinga makaranta take, gashi yarinya ce karama ga Dijen ba wani hankali ne da ita ba".

Daga ma Mama hannu Inna tai tace "dakata mana Maman Hajara taya zaki ce Kawas baa da hankali, Shekarun ta dai dai har 15, a shekarun ta fa aka miki aure da kuma kika zauna sannan kice yarinya ce ita".

Sunkuyar da kai Mama tai kasa tana jin yadda Inna take mata tonon silili, wato dai tun da ita aka mata aure a shekarun Dijen.

Gajeran tsaki Inna tai tace "sannan maganar makaranta da kike fada ina ji shi mai gidan yace Duk lokacin data tashi daga makaranta taje ai ba aikin zai hana ta ba, yarinyar nan kema shaida ce tana da kamun kai dai-dai gwargwado sannan ga baban ta shima acan yake aiki nasan zai sa Mata ido AI, nidai Don Allah ki bita da addu'a kawai taje tayi kika sani ma ko ta samo min sabon ango acan".

Kan Mama a kasa tace "toh shikn Inna, Allah yasa hakan shine mafi alkhairin sa Zan fada wa Malam din cewa na amince sai ya fadi ranar da zata fara zuwa".

Murmushi Inna tai tace "ko kefa, Allah ya miki Albarka dai".

Ni kuwa da nake gefe cikin sauri na koma daki jin Mama ta amince ina sauke ajiyar zuciya.

Kallon Yusrah nai dake waya da saurayin ta sai makale murya take, tsaki nai ina zama a gefen gadon lokaci daya ina janyo littafina na seera ina dubawa.

Sam bana Jin abinda Yusrah take fada don tayi kasa da murya sosai, ban

Please Login or Register in order to submit comment