Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Cikin nutsuwa nace "Baba Ka kaini wurin Ogan naka na gaishe sa kaji.."

Wani kallo Baba ya min yace "matsalata dake baki da saiti Dije, ynxu kawai sai na dauke ki na kaiki gurin Ogana, mutumin da ni kaina ban cika ganin sa ba sai in ta kama, lallai ma".

Turo baki nai cike da Shagwaba nace "Baba ai ba maula zan je masa ba, aiki zan ce ya taimaka ya dauke ni, kaga dai yadda nake ina fara Sana'a nake cinye jarin to tubarkalla mutum ne Allah yayi sa da shegen kwadayi sai addu'a, shiyasa nake son na samu aiki ni ko 5k ne a wata ina so wallahi xan yi kaga sai na dinga siyawa Mama omo da sabulu in baka bata kudin ba".

Kallon na kawai Baba yake, gyada kai yai yace "toh wani aiki zaki yi keda ko secondary baki gama ba".

Washe hakorana nai nace "mai sauki ai ba wani abu Zan yi ba, kawai shara ce da goge gogen office kasan zan iya sbd badai tsafta ba ni dinnan".

Tafa hannu Umma tai tana dariyar tace "Allahu Akhbar su tsafta manya, au tsafta ce dake tabdjan ai ina da yakinin cewa wallahi ko aikin jiran kare baxa a iya baki ba balle wai goge goge".

Rai na a bace na kalli Baba nace "Baba kana jin Umma koh, ni kuma ba da ita nake magana taba fah".

Cikin rashin damuwa yace "ai ba karya ta fada ma gaskia ne ta fada, wani mahaukacin ne zai baki aiki kina wannan kazantar, tsakanin ki da Allah yaushe rabon ki da wanka?".

Sosa kai na nayi nace "kwana uku knn Baba"

Tsaki yai cike da takaici yace "kuji fa don Allah, kina mace amma baki son wanka shiyasa gaki nan ko saurayi babu kina kallo yar uwarki zatai aure ta barki sai na gaji zan bada sadakar ki a masallaci".

Turo baki nai nace "ai taimakon Ka nake yi, bana asarar ruwa sosai kuma ai ina wanke bakina kullum, wankan ne kawai bana yi".

Takaici Kamar ya kashe Baba yace "tashi ki bani waje duk kin cika gurin nan da tsami, wai ke na tambaye ki ma kina aske gashin hammatar ki?".

Xaro manyan idona nai nace "lalalala Baba ba ruwana wallahi".

Girgiza kai yai yace "Allah ya nuna min ranar da zanga kina tsafta Dije".

Kasa kasa Umma tace "ba Ameen ba", na bude baki zan yi magana Mama ta kwala min Kira dole na tashi na shiga dakin, a cikin daki na ganta ta kwanta akan gadon mu.

Zama nai a gefen gadon nace "gani Mama"

Fuskar ta a hade tace "gobe da safe kina tashi ki dora ruwan zafi da kaina zan Miki wanka mara mutunci".

Ware ido nai nace "Mama kamar ya kimin wanka?".

Fuska a hade tace "abinda na fada knn kuma nasan kinji, tunda ke kazantar taki kullum gaba take kina can kin bude baki kina fada musu rabon ki da wanka kwana uku knn toh gobe har kitso zan miki".

Ganin da gaske Mama take nace "kiyi hakuri don Allah Mama, zan yi da kaina ba sai kin min ba, kuma ynxu fa na girma kawai sai ki min wanka don Allah ki duba lamarin nan fa".

Juyawa min baya tai cikin ko in Kula tace "kin dai ji ni da kyau, naga alama ke yarinya ce shiyasa baki son wanka so kike a miki toh kuwa zan dinga Miki da kaina".

Kamar Zan kuka nace "Mama ya kike son ki min wanka wai, za fa ki kalle min jiki na su kayan arziki na duka".

Mikewa Mama tai ta make min baki, kama bakin nai ina kallon ta kamar zanyi kuka.

Tsaki tai tace "don ubanki wai ban haka ki cewa kayan arziki ba ke wai meye yake damun ki".

Turo baki nai nace "toh Mama kin ce kar nace Nono toh me Zan dinga kiransu".

Dafe kai tai tace "Innanillaihi wa innanillaihir raji'un, Allah ya shirye ki" kawai ta juya ta kwanta.

Tashi nai nayi shinfida ta a kasa na kwanta ina ta turo baki, ban dade da kwanciya ba bacci ya dauke ni.

Washe gari kamar yadda Mama ta sani, ina tashi bayan nayi sallah na dora ruwan zafi, ina yi ina turo baki gaba.

Sai da ya tafasa sannan na fawa Mama, kallona tai tace "fara wanke ban dakin tukunna gani nan zuwa".

Fita nai kamar zanyi kuka, sai da na wanke shi tass sannan na Kara dawowa na fada wa Mama, zani ta bani na dora muka fita.

Tsayawa tai a kaina a bandakin ina wanka ina kuka, duk abu na bana bari a kallar min jiki, shiyasa ma kusan kullum zaka ganni da hijab.

Tsaki Mama tai tace "zaki dai na min kukan nan ko kuwa, badai kince ke baki jin magana ba zan koya miki hankali kuwa, kullum tsayawa xan dinga yi a kanki kina wankan kuma in naga baki fita ba na karba na dirje ki sosai".

Nidai banyi magana ba sai kuka da nake ina wanka, sai da ta tabbatar na wanke ko ina yadda ya kamata ta sa ni nayi shaving sannan ta wanke min kaina sosai.

Alwala nai muka fito tare hannuna rike da kwandon kayan wankan mu, a tsakar gidan muka tarar dasu Inna Fure da Umma suna zaune da alama zaman gulmar jiran mu suke.

Suna ganin fitowar mu Inna fure tace "oh Allah Maman Hajjo wai mutum da girman sa amma sbd kazanta sai an masa wanka wannan abin kunya da Mai yayi kama, ai ynxu koh Humaira bana Mata wanka sbd ta girma".

Shewa Umma tai tace "ke kuwa ai kinsan mutum kala Kala ne wani tsagaron kazantar sa ma ai bazai bari yai wanka ba, ni ba wannan ne damuwa taba Kar fa aje sbd wannan hali a tsofe mana a gida ba miji".

Bude baki nai Zan magana Mama ta fisgo ni muka shige daki, muna shiga nakara fashewa da kukan takaici nasan Hajjo sai ta fada a makarantar mu cewa Mama ta min wanka bayan kuma ba wankan tai min ba kawai tsayawa tai a kaina.

Mama bata bani damar wani abu ba kawai pant da bra nasa na daura zani a kirji tace na zauna ta fara min kitso, duk da tsantsin kai na haka Mama ta lallaba ta min kitso madaidai ta masu kyau matuka.

Shafa kan na fara yi kuma ina murmushi ni kaina dadi nake ji don wata iska ce Mai dadi take ratsani.

Sunkuyawa nai na Mata kiss nace "I love u Mama".

Girgiza kai tai tana murmushi tace "ki dai Kula ki fara tsafta don rashin tsaftar nan taki in kika fara al'ada ban san ya zanyi ba, Allah ma ya taimake ni baki fara da wuri ba da naji kazanta kala Kala".

Turo baki nai ina rufe fuska nace "haba Mama ta, kina sani Jin kunya fa kuma ai nace ki kaini asibiti a duba ni Hajjo fa ta dadd da farawa nice dai har ynxu shiru kake ji".

Dangware min kai tai tace "ko kunya kike cewa kin matsu ki fara al'ada, zaki wuce ki tafi ki shirya ko kuwa sai sun tafi sun bar ki tun da ba son zuwa school din kike ba dama ai".

Daki na wuce nasa uniform dina dana wanke jiya, turaren mama na dan fesa sai na tsaya ina kallon kai na a mirror nayi kyau sosai, murmushi nai na fito ina tafiya a hankali jina nake kamar sarauniya sbd nayi wanka nayi kitso.

Ina fitowa nasha koko kadan don kar na bata kayana, sallama nai wa Mama muka fita tare da yaran zuwa makaranta...


********
Aiki yake sosai a computer dinsa Kan sa a kasa, yunwa yake ji sosai don sam bai ci abinci ba tun jiya da daddare, shafa cikin sa yai yana dan lumshe idonsa gashi duk a gajiye yake.

Bude kofar office din akai aka shigo dauke da sallama, dago kansa yai ganin waye zai shigo masa office haka bayan yace baya son ganin kowa yau yana da aiki sosai.

Farin Dattijo ne mai cike da kamala da dattako, kallon farko in ka masa zaka san cewa wannan mutumin bafulatani ne na usuli.

Dan hade rai yai yana kau da kai daga kallon dattijon, Murmushi Malam yai yana girgiza kansa a hankali.

Masauki yai ma kansa akan kujerar dake fuskantar ta Elhajj, fuskar sa dauke da murmushi ya dubi jikan nasa yace "fatan kana lafia dai Mamman?".

Ba yabo ba fallasa yace "lafia qalau, barka da rana".

Murmushi Malam yai yace "barka kadai, komai lafia dai koh?".

Kara hade rai yai yace "Alhamdulillah, da ka kira ni sai nazo ai basai kazo ba har nan Kai".

Fuska dauke da murmushi yace "ai nasan halin Ka baxa Ka taba zuwa din ba, so nawa ina cewa kazo amma kake kin zuwa, baxan gaji da fada ma ba ka tashi tsaye kana addu'a zagaye kake da makiya ta ko ina Mamman".

Sai lokacin ya kalli Malam, zuba masa lulu eyes dinsa yai yana nazarin maganar sa kafin yace "wai Malam waye yace ma ina tare da makiya ne ni kam".

Dauke kan sa Malam yai daga duban Elhajj, mike wa yai a hankali ya zagayo ta bayan Elhajj, hannun sa yasa ya rike kafadun sa sosai.

Murmushi yai yace "ba wanda ya fada min alamomi ne suka bayyana kansu, Ka sa ido akan dukkan motsin mutanen dake zagaye da kai, wani soyayya zai dinga nuna ma amma fa Ka sani ba masoyin ka bane haka wani kiyayya xai na nuna ma a badini amma baya nufin Ka da sharri a zuciyar sa".

Ajiyar zuciya ya sauke yace "ka daure Ka daina wasa da azkar din safe da maraice jikana, Insha Allah zaka fi karfin ko waye, a kullum ina gode wa Allah da baka kasance mai Wasa da sallah ba amma Ka dage kana sakaci a fannin addu'a Maman".

Shiru yai tabbas yasan yana da sakaci a fannin addu'a, bai san mai yasa ba lokuta da dama ko ya zauna zai yi addu'oin safe da maraice kawai sai tunanin sa ya sauya ya fara tunanin wani abu da haka har ya manta.

Maganar Malam ne ya dawo dashi hayyacin sa, cike da tausayawa Malam yace "nasan ni kaina ba a son ran Ka kake kin zuwa waje na ba, amma ka daure kaji ba sai Ka zo dinba Ka dinga addu'a don Allah, duk abinda zaka ci kayi addu'a ko daga hannun waye kuwa".

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace "insha Allah Malam, ngd".

Murmushi Malam yai ya mika masa jarkar daya shigo da ita, kallon jarkar yai yace "meye wannan kuma".

Girgiza kai Malam yai yace "Qur'ani ne ka daure Ka shanye kaji, Ka ajiye a inda ba wanda zai gani".

Hade rai kawai yai yana turo baki gaba, mikewa Malam yai yana dariya yace "Allah ya ji Kan mahaifiyar Ka ya haskaka kabarin ta".

Lumshe idonsa yai a hankali yace "Ameen". Bai bude idon ba har Malam ya tafi tunanin rayuwar sa ta baya kawai ya tafi...

*Wanene Elhajj*

Muhammad shine asalin sunan sa, da daya tilo a gurin mahaifin sa Alh Hassan, mahaifin sa attajirin dan kasuwa ne da yake harkar gold da fata, yana da arziki sosai tun yana matashi.

Auren soyayya sukai shida Hajia Amina wacce ta kasance marainiya bata da uwa sai mahaifinta da ya kasance Malami, ta tashi a hannun kishiyar mamanta wacce suke Kira da Hajja.

Hajja mutuniyar kirki ce sosai bata taba banbanta Amina da diyar ta Sa'adatu ba komai tare take musu, har akai auren Amina da Alh Hassan.

Shekarar su biyu da aure ta haifi Muhammad, tun da aka haife sa bata kara haihuwa ba har yakai shekara takwas, a lokacin ne kuma wata tafiya da tai zuwa bikin kawarta zariya tayi hatsari motar ta kone, da kyar aka fito da ita don ta kone sosai, wannan ahalin sunji mutuwar Amina ba karami ba kasancewar ta mace mai mutunci da sanin ya kamata.

Tausayin halin da Muhammad zai shiga ne yasa Malam bawa Alh Hassan Sa'adatu ya aura, in da ita kuma da farko taki amincewa sai da kyar Malam da Hajja suka rarrashe ta ta amince tunda dama ta dade a gida ba Miji.

Sa'adatu wacce Elhajj ke Kira Momma ta rike sa da amana, ta mai dashi matsayin aminin ta ko mai xatai sai tayi shawara dashi tun yana yaro, shiyasa shima ya tashi da kaunar ta a ransa wanda hakan ba karamin dadi yake wa Papa ba.

Elhajj ya samo sunan ne daga gurin Ummin sa(Amina), tun yana karami take kiran sa da haka don ya kasance mutum mai sha'awar kasuwanci sosai, kullum in yana wasa to fa zaka ji shi ne yana magana akan harkar kasuwanci.

Salim dan kanin Papa ne Usaini, tare suka girma cike da shakuwa da yadda da juna, tare sukai makaranta a China inda dukan su suka karanci business Administration.

Tunn a China Elhajj yake kasuwancin textile da kudin da papa yake turo masa na kashewa, maimakon ya dinga kashewa sai yake juya su, kuma Allah yasa albarka a harkar nan da nan arzikin da ya fara yake habaka.

Yana dawowa Nigeria ya bude companyn sa, a lokacin ne kuma sukai aure da Saudat budurwar sa.

A ynxu shekarar su takwas da aure, a shekarun nan sau hudu saudat na haihuwa amma suna zuwa basa kwana bakwai suke rasuwa.

Shekarar Elhajj 38 a ynxu haka Saudat na da 30.

Wannan Kenan......


Mikewa yai a hankali ya nufi toilet don yin alwala jin ana kiran sallah, bai dade ba ya fito daga bandakin yana Mai da links din rigar sa.

Dago kai yai ya kalli table da mamaki ya bude baki sai kuma ya kalli kofa ganin.....



*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

09066728387


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎

Free page 5

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Dago kai yai ya kallo table din da mamaki ya bude baki sai kuma ya kalli kofa ganin bai ga jarkar rubutun da Malam ya ajiye masa ba, shi dai yasan bai dauke ba kuma yana toilet bai ji alamun an bude kofa ba balle yace an shigo ma.

Da tsananin Mamaki yake dudduba office din amma bai gani ba, wannan shine karo na hudu kenan da Malam yake kawo masa rubutu yasha amma kafin yasha sai ya ne me shi ya rasa.

Lumshe ido kawai yai ya fita daga office din zuwa masallaci....

Bayan sun fito har zai wuce yaga wani kamar Baba Auwalu kamar yadda suke kiran sa bai man ce shi ba tsohon ma'aikacin sa ne da a old site yake daga baya da aka bude new site yasa sunan shi a jerin wadan da zasu dawo New site din.

Kara sa wa gun sa yai ganin yana ciki cikin mikewa da alama zame wa yayi a gun, taimaka masa yai ya mike cike da kulawa yace "Baba Auwalu kana lafia dai".

Washe baki Baba yai yace "Alhamdulillah MD, dan zame wa nai, ina wuni".

Gajeran murmushi yai yana shafa sajen sa yace "Allah ya kiyaye gaba, ai ni ya kamata na gaishe Ka Baba Auwalu".

Dariya Baba yai yace "A'a MD ai gaba kake dani a fannin aiki da matsayi, ai kamar kasan jiya yarinya ta take cewa tana so tazo ta ganka ta gaishe Ka wai in zata samu aiki ko na goge goge ne tana so tayi ita dai a biyata albashi kawai ko 5k nace bata da hankali waye zai dauke ta aiki haka".

Fuskar sa dauke da murmushi yace "in ta shirya ko yaushe zaka iya kawo ta a cikin satin nan ina neman mai share min office dina".

Dan shiru yai sai kuma yace "ina son na samu mace dama da zata na gyara min office sosai fatan dai zata iya koh".

Da Mamaki Baba yace "wai Ka dauke ta aiki knn, zata iya zuwa ko gobe ne tana fa zuwa makaranta da safe rigimar tace kawai fah".

Cikin rashin damuwa Elhajj yace "zata iya zuwa duk lokacin data tashi daga school din wannan ba damuwa, bane in tazo zamuyi magana akan albashin ta".

Baki bude Baba yake kallon sa har ya wuce, shifa fada masa kawai yai ganin ya samu damar magana da MD yau a sauwake, lallai kuwa in haka ne baxai yi Wasa da wannan damar ba ya san tabbas za'a biyata albashi mai tsoka daga nan sai ya dinga tara kudin in auren ta ya tashi ai barkan sa.

Cikin nishadi ya koma bakin aikin sa ransa fess....


*******

Dambe muke kamar me, na danne ruwan cikin Amal class mate dinmu sai naushi nake, ihu ake a kan mu ba wanda yayi kokarin zuwa ya raba mu ba yau na fara dambe ba duk Wanda yazo da niyar raba mu kansa nake koma wa.

Daka min tsaya Uncle Mustapha yai discipline teacher, da sauri na daga Amal din ina kunkuni.

Gyada kai yai yace "ku biyo ni office ynxu nan".

Duban inda Amal take nai naga sai kuka take tana gogewa da Hijab dinta, kwafa nai nayi gaba bayan na sabi jakata.

A office dinsa muka sa me sa yana zaune ga bulala nan ya ajiye akan table.

Hadiyar yawu nai cike da tsoro nace "Uncle zan fara bayanin abinda ya faru".

Bai bani amsa ba sai kallon Amal yai yace "mai ya hada ku?".

Kuka ta Kara fashewa dashi cikin kuka tace "Uncle kawai don Hajjo ta zo tana bamu labari cewa yau Maman Dije ce ta mata wanka sbd tsabar kazantar ta shine ta kama ni ta ke duka kuma bayan bani kadai bace nake tsokanar ta muna da yawa".

Da sauri nace "Uncle karya take wallahi, ita ce nan har Kida take min wai ga Dije kazamiya ni kuwa naga baxan dauki iskancin banxa ba nace wace kazamiyar ta kalli idona tace ke Dije shine nake kilar ta fah"

Kallon mu Uncle yai yace dukan ku kuna da laifi, "ke Amal bai kamata ki dinga kiran ta da kazama ba sannan ba ruwanki ko Maman tace ke mata wanka kullum ai mahaifiyar tace koh?".

Daga kai Amal tai tana kuka don fa ta bugu ba karya.

Kallona yai yaga sai cika nake ina batsewa murmushi yai kawai yace "Khadija ban haka ki fada ba, kina mace amma baki da aiki sai fada ehe".

Turo baki nai cike da Shagwabar da nake yiwa kowa nace "Uncle tsokana ta suke yifa, ai in ba Wanda ya tsokane ni bana fada".

Murmushi yai yace "ki dinga hakuri dai kinji, ynxu ku bawa juna hakuri bana son fadan nan daga yau".

Kallon ta nai nace "kiyi hakuri fah Amal kin sanni bana daukar iskanci amma za'a kiyaye".

Dauke kan ta tai tace "kiyi hakuri kema".

Watsa hannu baya nai nace "mafi mishkila".

Murmushi Uncle Mustapha yai yace "ku tafi Maza an dade da tashi".

Fita mukai a tare sai harara ta Amal keyi ina kula da ita nai Mata banxa don bana son wani fitinar kuma ynxu na gaji yunwa nake ji.

Bayan fitar su mikewa Uncle Mustapha yai yana murmushi, shidai Allah ya zuba masa kaunar Dije a ransa tun tana ajin farko yake sonta jira yake ta shiga ajin karshe ya fada mata abinda ya dade yana jira kuma yana fatan insha Allah Dijen gala tasa ce.....

Ina isa gida abinci na fara ci ina ci ina bawa Mama labarin fadan da nai a makaranta, itadai ko kula ni batai ba sai sakar rigar sanyin da takeyi kawai.

Ina gama cin abincin na wanko hannuna na dawo daki, kayan makarantar na cire na zira Riga da skirt ban sa hula ba don bana son hula na fito Palour.

Kwanciya nai akan kujera nace "Mama ki bani tsakar na karasa Miki, naga dai rigar nan ni kike yiwa toh ki bani kawai na karasa kayata kinji".

Ganin taki min magana na tashi zaune ina turo baki, kamar zanyi kuka nace wai Mama don Allah kina ji sai na dinga magana amma ki min banxa kamar baki ji ba.

Ba tare data kalle niba tace "ah toh meye zan tsaya ina biye miki bayan maganar ba mai muhimmanci bace ba, ai da mai muhimmanci ce sai na tsaya ina saurara har na baki amsa ma".

Turo baki nai ina komawa na kwanta bana son naji ina magana amma a ki biye min kawai a share ni shiyasa nayi shiru abuna.

Ganin na daina magana kuma da alama ba bacci nai ba tace "mai kike yi ne Dije? Ko bacci kike".

Ina daga kwancen a hankali nace "na gaji ne kawai".

Murmushi Mama tai tasan fushi take shiyasa tace haka, ita dai bata sake Mata magana ba sai da akai la'asar ta tashe ta.

Yinin yau gaba daya ban zauna a tsakar gidan ba ina daki a kwance alwala ce kawai ke tayar dani.

Ina kwance bayan sallar Isha'i Baba ya shigo palourn.

Mike wa nai nace "Baba ina wuni".

Murmushi kwance a fuskar sa yana Zama a gefe na yace "lafia qalau Mamana, yau ban ganki ba kin zo mini sannu da zuwa".

Turo baki nai ina juyar da kai na gefe.

Mama dake zaune tace "fushi take wai Malam haka ai, tun dazu nima taki min magana".

Kallona Baba yai yace "mai aka yiwa Mamana ne ehh".

Tabe baki Mama tai tace "mai kuwa za'a mata Malam, shirme tazo tan fada min don na Mata banxa shine take fushi".

Murmushi Baba yai yace "toh tashi nazo miki da albishir".

Juyar da kaina nayi ina turo baki nace "tsokana ta Baba kawai kake yi".

Girgiza kai yai yace "dazu nake yiwa MD magana kince kina son aiki ko share share ne, shine yace dama yana neman wacce xata dinga gyara masa office duk lokacin da kika shirya muje tare".

Mikewa nai da sauri nace "don Allah Baba da gaske kake".

Dan hade rai yai yace "karya zan miki toh".

Ihu nasa ina rungume Mama nace "Mama na samu aikin da zan dinga samo miki kudi, kinga sai mu dinga cin kayan dadin mu koh".

Ture ni Mama tai ta kalli Baba tace "ban fahimce Kaba Malam mai kake nufi ne wai".

Gyara zama Baba yai yace "jiya take cemin ko zan nema Mata aiki a companyn da nake, toh Allah cikin ikonsa yau na samu magana da MD din companyn a saukake kuma ya dauke tama".

Da mamaki tace "ina Dijen ce zatai aiki wai a companyn da kake".

Daga kai Baba yai cikin tabbatar wa yace "insha Allah kuwa".

Hade rai sosai Mama tai tace "ban yadda ba Malam, yarinyar da take zuwa makaranta Ss 1 fa take shine za'a ce zata je tana aikin share share, baxai yi ba haba Malam Ka duba Ka gani, mai ta rasa ci ko sha?".

A Dan hasale

Please Login or Register in order to submit comment