Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matuƙa. Babu yanda ta iya dole tabi umarninta, su dai su Aysha sai faman dariya suke. Bata kulasuba ta shiga tai wanka, ta fito ta shiryawa a ɗaya daga cikin kayan fitar biki da su Daddy sukai musu. Sai dai kalar nata daban tasa saɓanin ƴan uwanta da duk suka saka atamfa. Sosai lass ɗin yamata ƙyau kasancewarsa skirt da riga kuma bata saba sakawa ba. Tai ɗas abinta kamar itama amaryar ce (Anam team😜).

_________________________________

Alhamdulillahi bayan idar da sallar juma'a dake massallacin juma'a na anguwarsu ɗunbin al'ummar musulmi daga sassan daban-daban na Nigeria da wajenta suka shaida ɗaurin auren *_Al-Mustapha Muhammad Shareff_* da amaryarsa *_Fadwa Sadiq Dakata_* akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Ɗaurin aurene daya tara manyan mutane masu alaƙa da ango da iyayensa harma da ɓangaren amarya.
Kamar yanda nan gidan su Shareff ke cike da ƴan uwa da abokan arziƙi acan gidansu amarya Fadwa ma hakane. Taci ado na faɗa aji daya amsa suna ado irin na amare ƴan ƙwalisa masu ji da lokaci (😘😍Sai dake tawan😂😉). Tana tsakkiyar ƙawayenta daketa aikin zuba hotuna da videon ɗorawa a tiktok. Tun kafin yau amarya Fadwa ta roƙi angonta da zarar an ɗaura aure ya taimaka ya kirata ya fara sanar mata da kansa. Da farko bai amsaba, sai dai yanda ta dinga nacin damunsa da maganar tsahon lokaci yace zaiyi. Shi mutum ne dabai ɗaukar alƙawari bai cikaba, sai dai hakan ta kasance bisa akasi. A yanzun ma harya shafa'a alƙawarin ya faɗo masa a rai. Yana tsaka da gaisuwa da abokansa yay excusing kansa ya koma gefe yana mai ƙoƙarin cikawa. Ga amarya Fadwa kam harta fidda rai zuciyarta sai faman kaikawo take kamar ta fasa kuka. Ta riga ta gama shiryawa da ƙawayenta domin jiran wannan lokaci, sai dai shiru kakeji sun fara jin kishin-kishin na cewar an ɗaura auran. Dama tasan itama gangancine kawai, Shareff ba irin mazan da ke ɗaukar kowane kalar shirme bane, hasalima ita har yanzu bai san tana harkar yanar gizo ba, da tana da tabbacin sai sun kwashi ƴan kallo da shi.......
Ring ɗin wayarta ya katse mata tunani, tamkar maijin tsoro ta ɗauka wayar tana dubawa badan ta saka ran ganin shi ɗin bane. Kasa ɗagawa tai har sai da babbar aminiyarta Sima ta ɗaga mata tasa a hansfree dan sunada tabbacin abinda suke zaman jiran ji ne daga angon dama. Sassanyar muryarsa data ratsa cikin wayar ta saka ɗakin ƙarayin tsitt, masu video recording na faman ɗauka. Cikin rawar murya ta amsa, dan haka kawai taji kuka ya taho mata batare data san dalili ba. Daga can yay murmushi saboda jin yanayinta, ashe da gaske aure yaƙin mata ne, dan yasan abinda zai saka Fadwa karaya ba ƙarami bane. Yay ɗan gyaran murya da sake kwantar da murya. *_“Habibtie kin zama Matar Al-Mustapha, ina roƙon UBANGIJIN daya nufemu da ganin wannan rana ya bamu lafiya da zuri'a masu albarka, tare da haƙurin zama da juna, mai cike da kulawa da soyayya na har abadan. Finally Al-Mustapha ya zama naki”._* Kalamansa sun ratsata daga ita har ƙawayenta da abun yay matuƙar burgesu, sai kawai ta sakar masa kukan da taketa faman haɗiyewa. Murmushi yayi, da sake faɗin, “Congratulations once again dear, i love you”.
“I love you too”.
Ta amsa masa da sake fashewa da kuka. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin ihu da sowa harda masu guɗa. Jama'a dake waje kuwa har ture juna ake wajen son shigowa aga mike faruwa.

Cikin ƙanƙanin lokaci video ɗin da ƙawayenta suka ɗauka suka ɗaura a tiktok, istagram ya fara yawo fiyema da yanda sukai zato ko tsammani a kowane shafi na sada zumunta kamar yanda sauran hotunan da suketa ɗaurawa na sauran kwanakin ke yawo dama . Wanda ma followers ɗinsu basu kaiba tuni ƙaruwa suke. Comments da like kam ai bama a magana. Ƴammata sai alwashi ake ɗauka da zuwan tasu makamanciyar wannan rana. Wanda ko bikinsu ke shirin zuwa next week dama cikin satin tuni sun fara neman angunan nasu da ƙawaye yanda zasu tsara nasu suma. (Hummm media-media gidan kashe ahu😣).

★★★

Daga wajen ɗaurin aure gayyar abokan ango da abokan su Daddy dama sauran jama'a suka ɗunguma hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci domin su. Anci ansha anyi hotuna kafin ango da tawagarsa su nufo gida. Yanzun kam sai da suka fara shiga gidansu yakai kansa ga Mommyn sa. Rungumesa tai cike da farin cikin yaronta ya zama babban mutum yau burinta ya cika. Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tayasa murna da masa fatan alkairi. Anyi hotuna shida dangin Mommy dama sauran jama'a har da wanda ke a tsakar gida na kusa. Daga nan gidan su Anam suka nufa da gayyar abokansa tunda dama nan ne masaukin nasu, Mamie kuma tama sake shirya musu wasu abincin anan dama.
Nan ɗin ma gidan cike yake da ƴan uwa da abokan arziki. Shigowarsu ta saka wasu fara sakin guɗoɗi, yayinda maroƙa keta aikin kirari na al'adar biki. Su Aysha da duk suke zaune a harabar gidan suma kan kujerun roba da aka zube miƙewa sukai cike da farin ciki suka nufi Yayan nasu dan tayasa murna suma. Anam dake faman latsa waya duk hayaniyar da ake gidan batako ɗaga kanta ba taja siririn tsaki, tare da gyara zamanta dan babu alamar zata bisu.
Har aka fara ɗaukar hotuna bata ko kalli sashen da suke ba. Sai ma mikewa tai da nufin barin wajen taji an riƙo hanunta. Juyowa tai a fusace da tunanin cikin su Amrah ne, sai tai arba da aunty Mimi. Baki ta tura idonta na tara hawaye, aunty Mimi ta girgiza kanta da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Mamana”. Hanunta taja har cikin taron, ta kaita har gaban Shareff ta tsayar.
Ƙoƙarin haɗiye hawayen dake son zubo mata ya hanata iya ɗagowa ta kalli kowa take, ga idanu tanaji a kanta da maganar da aunty Mimi ke mata akan ta ɗago mai hoto zai ɗauka. Aunty Mimi zata ƙara magana Shareff ya girgiza mata kai, tare da yima camara man ɗin nuni daya dauka kawai. Aiko ɗaukar ya farayi abinsa, bayan an musu su kaɗai kusan kala uku mutane suka fara shiga, daga haka aka cigaba da ɗauka batare da ko sau ɗaya Anam ta kalli camara ba. Daga ƙarshe ma ƙoƙarin zame jikinta a wajen ta shiga yi dan kukan da take dannewa ƙoƙarin fin ƙarfinta yakeyi. Taku ɗaya tai taji an riƙo hanunta, cak ta tsaya, tare da juyowa da sauri zuciyarta na ƙara zuwa wuya. Ɗaukewa numfashinta ya nemayi a dalilin shigar idanunta cikin nasa, ya kuma sarketa da su da iyakar ƙarfin ikonsa. Ga hanunta har yanzu yana riƙe a cikin nasa. Tuni camara man ya maida hankalinsa a ɗaukarsu hoto. Ƙoƙarin janye hanunta tayi ya hana hakan, ga idanunta ma sun gagara fita a cikin nashi. Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo a fuskarta a hankali, ta fisge hanunta da sauri tabar wajen harda ɗan haɗawa da gudu. Waɗanda hankalinsu ke kansu duk suka bita da kallo kamar yanda shima ya bita har sai da ta ɓace. Ido suka haɗa da aunty Mimi yay saurin ɗaukewa shima yana barin wajen..........✍

*_Ko anƙi ko anso, aure dai ya ɗauru, murna muke daga zuciya har zuwa ranmu💃🏻😍😜. (Anam team ya take ne🤣😂😉😜?)_*


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽*_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*




*_13_*


..........Gab da magrib aka kawo amarya Fadwa, kamar yanda Daddy ya bada umarni nan gidan aka kawota wajen Mamie. Hakan ba ƙaramin zafar Mommy da su Gwaggo Halima da aka kira aka sanarwa abun yayi ba. Gwaggo kuwa kasa shiru tai sai da ta tanka, Daddyn yace ya gama yanke hukunci, miye ma abin magana bayan gobe idan ALLAH ya kaimu za'a maidata gidanta. Badan rigimar ta kwantaba akai daiyi shiru kowa yaje ya fara shirin tafiya dinner.
Bayan sallar isha'i aka fara kwasar mutane inda za'a gudanar da dinner, sai dai har aka gama kwashe kowa babu Anam babu alamarta. Hasalima tuni taje tai kwanciyarta a falon Abie batare da kowa ya sani ba. Wajen dinner ya ƙayatar matuƙa. Amarya da ango sunyi ƙyau har sun gaji. Anci ansha ƙawayen amarya sun sami yanda sukeso suda amarya wajen daukar hotuna da videos wasu har live suke ɗauka ana kaiwa tiktok. Nera tayi kuka kamar yanda aka zubar da mutunci galan-galan dan anci rawa casss da warrr ƙawayen amarya ta rashin mutunci, amaryar kanta ta cashe kamar babu gobe, sai dai rashin yin rawar ango ta jawo cece kuce sosai dan wasu na ganin amarya Fadwa ta zaƙe da yawa. (Komadai miye ni ina ganin ranar farin cikin tace a barta ta shana😜). Ƙarfe sha biyu taro ya tashi lafiya aka kwaso jama'a aka dawo gida.

WASHE GARI aka gudanar da walima tare da yinin biki anan gidan, yini guda babu wanda zaice yaga Anam sai Mamie kawai da aunty Mimi, dan tana falon Abie kwance babu lafiya zazzaɓi ta kwana da shi har sai da doctor yazo ya dubata da safe ma, dan haka yau ko kwalliyar bikin ma batai ba abinta. Lokacin da taji sallamar Shareff zai shigo falon wajen Abie tashi tai ta gudu bedroom ɗin Abie ɗin, tanaji yana faɗama Abie baida kafiya shima da ciwon kai ya kwana kuma har yinin yau ɗin bai sakesa ba yana ganin hayaniyar nan ce. Baki ta taɓe cikin rashin damuwa tai kwanciyarta har sai da taji ya fita. Har dare bata sauka ƙasa ba dan bata buƙatar ganin Fadwa har tabar gidan. Hakan kuwa akayi, dan washeri lahadi akai buɗan kai bayan sallar azhar. Anayin la'asar aka ɗunguma raka amarya Fadwa gidanta, yayinda a bangaren ango yaketa ƙoƙarin sallamar abokansa na nesa da zasu wuce gida yau. Hakama baƙin nan gidan wasu daga rakkiyar amarya bazasu dawo nan ɗin ba...
Gidan amarya kam sai sambarka. Komai yaji zam masha ALLAH. Har kusan bayan magrib sannan mutane suka gama watsewa aka barta ita da ƙawayenta kawai dake jiran abokan ango.....

★★

“Wai nikam wane irin ango ne kai Al-Mustapha? A irin wannan ranar irinka ɗoki da zumuɗi baya barinsu amma kai tun ɗazun sai fama ake da kai ka shirya a rakaka kanata jamana aji”.
Duk da sarai abinda Dr Jamil ɗin ke faɗa yana shiga kunnensa tunda a kusa da shi yake amma babu alamar zai motsa. Sai cigaba da danne-dannen tab ɗinsa yake hankali kwance. Fharhan dake faman musu dariya ya miƙe ya fige tab ɗin. Ɗagowa yay yana harararsa da miƙa hannu, Isma'il ya amshe tab ɗin daga hanun Fharhan shima yana dariya. “ALLAH baza'a baka ba. Garama ka tashi kaje ka shirya mu miƙaka muma muje musa haƙarƙarinmu a katifa matanmu na jiranmu.”
Isma'il ɗin ya kafe da idanu kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kai kawai. Dr jamil ya dafa shi, “Wai nikam Musty ko tsoron amaryar kake ne? Idan akwai matsala inada kayan gyara masu inganci wlhy da zaka baje kolinka babu ragi babu ragowa”.
Naushi ya kaima Dr Jamil, da sauri ya duƙe yana dariya su Fharhan na tayasu. Hararsu yay da miƙewa ya shige bedroom.

Jin gidan ya rage hayaniya sosai ta sakko downstairs. Su Mamie ne kawai zaune da ƙannenta, gaishesu tai kowa na tambayarta ya ƙarfin jikinta. Tace da sauƙi tana zama gefen Mamie ta kwantar da kanta a kafaɗarta. Ko mintuna uku batai da zama ba suka shigo da sallama. Shine a gaba cikin ɗanyar shadda milk color sai ƙyalli take harda hula a kansa. Sai su Fharhan biye da shi. Jitai kusan su dukansu idanunsu akanta suke kamar ta tashi ta arta da gudu, sai dai ta dake dan bata fatan sake tafka abin kunyar datai a ranar ɗaurin aure😝.
Sai da suka gama gaisawa da su Mamie Dr Jamil dake jin kamar ya haɗiyeta fuska ɗauke da murmushi yace, “A'a Anam banda ke a kai amaryar kenan?”.
Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi batare data kallesu ba. “Banda lafiya ne shiyyasa”. Ta faɗa a hankaki tana ƙara sinne kanta jikin Mamie.
“Ayya ai ban sani ba dana kawo ɗauki. Yaya jikin yanzun?”.
“Na samu sauƙi”. Ta faɗa a taƙaice tana ɗan ɗagowa. Cikin idonsa natan suka shige, tai saurin janyewa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi....
“My son kuje kar dare yayi an bar ɗiyata ita kaɗai, ALLAH yay muku albarka, ya bada zaman lafiya na har abada. Ayi haƙuri ayi haƙuri ayi haƙuri. Mu mata a duk inda muke haƙuri ake damu akan komai dan halittane masu wahalar sha'ani. Banda yanke hukunci cikin fushi, duk abinda aka gani ba dai-dai ba abu asannu a ruwan sanyi a kawo maslaha a cikinsa. Ayi ƙokurin sauke duk hakkin da ALLAH yace duk da bani da damuwa a kanka game da wannan. ALLAH ya azurtaku da zuri'a masu albarka”.
Gaba ɗaya suka amsa da Amin. Anam dai ma ta maida hankalinta ga wayarta kamar bata jinsu. Ƴan uwan Mamie ma sun masa tasu nasihar suka sallamesu dan dare na ƙarayi. Dai-dai yana mikewa suka ƙara haɗa ido da Anam data ɗago itama. Wani kasalallen kallo suka sakarma juna. Ta kauda kanta tana taɓe baki zuciyarta na mata zafi. Shima iska ya ɗan furzar yana janye nasa a wani yanayi. Bata sake yarda ta ɗago ba har suka fice Dr Jamal na faɗa mata sai yazo dubiya ta musamman. Bata tankasa ba, sai Aunty Nasara dake kamar ƙanwar Mamie ta bashi amsa cikin dariya.
Tsam ta mike tabar falon dan ji take wani ɗan zazzaɓi ma na neman rufeta, ta nufi ɗakinta da fatan su Aysha su kwana a cikin gida yau bata bukatar su anan......

*_MONDAY MORNING_*

Tana tsaka da barcinta na safe mai daɗi kasancewar bata samu yin na dare ba sosai saboda zazzaɓi mai zafi data sake kwana da shi aunty Mimi ta tasheta akan ta tashi ta shirya za'a aiketa.
“Wayyo aunty ina su Aysha ki aika a kira miki su suna cikin gida fa ALLAH bana jin daɗi”.
Hararta Aunty Mimi tayi. “Ai nasan dasu Ayshan na tasheki. Maza tashi kina ɓatamin lokaci. Da ƙyar ta miƙe ta shiga bayi kamar zatai kuka. Wanka tai da ruwa mai ɗumi dan duk son sanyinta kuma bata wanka da ruwan sanyi. Gudun masifar aunty Mimi ya sata shiryawa a ɗan gurguje cikin shigar da tafi so a ko yaushe wando da riga ta ɗaura abaya pink a sama ta naɗa veil ɗin abayar. Tayi ƙyau sosai sai zuba kamshi take duk da bawani kwalliya tai mai yawa ba. A falon ƙasa ta sameta har su Mamie wanda suka makara nata breakfast. Gaishe dasu tai tana karasawa inda Aunty Mimi take.
“Yauwa ɗiyar albarka. Ai jeki kawai waje ga Ikram can na jiranki a mota da driver ”.
“To aunty saƙon fa?”.
“Yana wajensu a motar”.
Kai kawai ta jinjina taima su Mamie sallama ta fita. Baya ta buɗe ta shiga yayinda Ikram ke gaba tanata zubama driver surutu da hausanta da bata iyaba wai ita a dole koyan hausa takeyi. Itace autar aunty Mimi shekararta goma sha uku, kasancewarta girman turai sai take abu kamar wata yarinya ƙarama ga tabara ta autoci.
“Good morning aunty Anam”.
Ta faɗa lokacin da Anam ke ƙoƙarin rufe murfi. “Morning dear how are you?”.
“Am fine, sai ƙafana dake ciwo saboda rawan da mukai a wajen dinner ranar”.
“Good for you”.
“Kai aunty maimakon kimin sorry”.
“Tunda ni na aike ki”.
Dariya Ikram tayi. Sai kuma ta shiga bata labarin yanda shagalin dinner ya kasance. Shiru Anam tai mata, da taga zata isheta sai ta buɗe bag ta ɗakko bluetooth ta saka waƙa har suka iso gidan da bazata taɓa iya mantawa ba. Kasa motsi tai balle magana har driver yay horn maigadi ya buɗe masa gate suka shige. Jitai kanta na juyawa, ta dafesa tana ambaton sunan ALLAH. Da tasan nan aunty Mimi zata aikosu da duk ma yanda zatai taƙi zuwa ALLAH da sai tayi. Yanzu kuma tana ƙin shiga wannan akku sarkin zancen zataje ta bazata a fassarata a mai baƙin ciki. Siririn tsaki taja da buɗe motar a fusace ta fita dan Ikram tuni ta fice har driver ya buɗe mata booth suna fidda kayan breakfast da sukazo da shi. Ƙin daukar komai tai sai driver da ikram ɗinne suka kwasa.
Daga can baya ta tsaya Ikram ta shiga yin knocking tana kiran sunan Yaya Shareff. Sun kai kusan mintuna goma sha sannan aka buɗe har ta gama yanke shawarar juyawa ta koma. Shine ya buɗe ƙofar Ikram ta riƙo hanunsa cike da shagwaɓa. (Wayyo Yaya ƙafafuna har zafi suke da hannuna”.
Kanta ya dafa da rufe idonsa daya nuna alamar a barci ya tashi yana buɗewa. Ya matsa mata alamar ta shigo yana maida dubansa ga Anam datai tsaye tana kallon wani waje daban. Kusan minti ɗaya yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yay magana.
“Tsaiwar ta miye?”.
Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska. Batare da tace komai ba ta nufosa. Harta ƙaraso idonsa na kanta yanzu ma. Ya ɗan matsa mata alamar ta shiga itama. Ɗagowa tai suka haɗa ido, tai saurin janyewa da raɓashi ta shige tana murguɗa baki. Shine ya shiga da kayan cikin falon da kansa, Ikram sai faman yaba falon take dan babu ƙarya naira tayi kuka. Itako tana tsaye tamaƙi zama, ta dai jingina da bango tana daƙilar wayarta.
“Ina kwana”.
Ta faɗa batare data yarda ta kallesa ba. Bai amsata ba, sai hankalinsa daya maida ga Ikram da bakinta yaƙi shiru. Haushi ya ƙara kume zuciyarta, gashi ta fara gajiya da tsaiwar, amma sai ta cigaba da daurewa. Kusan mintuna biyar yana biyema shirmen Ikram tamkar ma ya manta da ita a falon. Ƙaton agogon dake bangon falon ya duba, tare da dawo da kallonsa gareta.
“Bani plate a kitchen”.
Kallonsa tai da mamaki, sai kuma ta sake ɓata fuska. “Ni ban san kitchen ɗin ba”. Da hannu ya nuna mata ya ɗauke kansa. Kitchen ɗin ta nufa wani haushi na ƙara turniketa, cikin taɓe baki take bin ko'ina na kitchen ɗin da kallo. Tabbas yayi ƙyau, sai dai hakan ba yana nufin wani abu na cikinsa ya burgeta ba. Abinda ya aikota ta nufa ta ɗauka, sai dai ta nufi sink dan ta ɗauraye, sai ƙunƙuni takeyi da bazaka iya sanin mitake faɗa ba. Juyowa tai tana jan tsaki, da sauri taja baya har plate ɗin na neman suɓuce mata. Duk ta daburce dan sam bata san ya biyo bayanta ba, ga idanunsa masu kaifi daya kafeta da su. A hankali ya tako gabanta duk hannayensa cikin aljihun jallabiyar jikinsa, ya tsaya dab da ita har tana iya jin hucin numfashinsa. Sai taji gaba ɗaya kwarjininsa ya cika wajen har bata shaƙar numfashi a wadace...
“Ya jikin ki?”.
Yay maganar cikin taushin muryar da bata taɓa ji daga garesa ba. Kasa jurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa. Har yanzu idanunsa a kanta suke, tai saurin janye nata tana girgiza kanta. Muryarta da ɗan rawa tace, “Alhamdulillahi”.
“Kin tabbatar?”.
“Nifa zazzaɓi ne dama kawai Yaya MM”.
Jin baice komaiba ta ɗago ta dubesa, still dai har yanzu idonsa a kanta. (Ya ALLAH! lafiyarsa kuwa?) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin son barin wajen. Amma sai furucinsa ya sakata dakatawa babu shiri.
“I'm sorry”.
Kasa yarda tayi daga bakinsa furucin ya fito, musamman da babu alamar shi ɗin ya faɗa a yanayinsa. Sannan bata san dalilinsa na faɗarba. Kamar ya fahimci ƙarin bayani take buƙata sai ya bar wajen cike da basarwa. “Zoki dafamin lipton”. Shiru bata motsa ba, da alama bata tare da tunaninta ma. Ya juyo ya dubeta fuska a tsuke. “Badake nake magana ba!”. Itama fuska ta haɗe, sai dai cikin sanyin murya tace, “Yaya matarka fa?”. Ido ya tsura mata na wasu sakanni, sai kuma ya janye. “Nasan da ita ai na sakaki. Sannan ganin amarya a kicin irin wannan ranar kema kin san bamai yuwuwa bane”.
Da hausa yay maganar, dan haka ba komai ta fahimta da ƙyau ba. Amma sunan amarya kawai daya shigo ciki ya saka yanayinta ƙara canjawa. Sai dai bata sake cewa komai ba, ta ɗauka tunkuyar daya fiddo mata domin dafa shayin ta ɗauraye, ruwa ta zuba dai-dai shan mutum ɗaya, tana ƙoƙarin rufewa taji tsaiwarsa a bayanta, kafin tayi wani yunƙuri ya janye hanunta da sake buɗe murfin ya buɗe fanfo ya ƙara ruwan.
“Nadai bazan dafama wata ƙatuwa shayi tana kwance tana barci ba”.
Karon farko ya saki murmushi, sai dai komai baice ba ya rufe mata tukunyar. Zata sake magana ya dakatar da ita. “Zakimin abinda na saki ko tsiwa? Trouble maker!”.
“Ga babbar Trouble maker can ka bari a ɗaki”. Tai maganar ƙasa-ƙasa yanda bazaiji ba. Da kansa ya kunna mata gas ɗin, ta ɗaura tukunyar sannan ta ɗiba kayan ƙamshi da lipton da duk ya fiddo da kansa ta zuba. Flask daya fiddo a kwali shima ta ɗauka ta ɗauraye tare da kofi duk yana tsaye yana kallonta. Baiyi mamakin yanda take komai a tsaftace da kuma tsari ba, dan sai dai ya bama wani labarin Mamie badai a bashi ba, yasan kuma hakan duk tarbiyyar data samune daga gareta. Yana kitchen ɗin harta kammala komai, ya sake ɗaukar kofuna uku ya ɗauraye da kansa ya haɗa da wanda ta wanke. Bata tanka masa ba, ta ɗauka flask ɗin kawai ta fita. Shine ya ɗauka sauran kayan ya fito da su, samunta yay tanama Ikram masifa akan ta tashi su wuce gida, ashe da wayarsa ya haɗata shi ya tafi neman magana kitchen..
“Sai kun karya, tunda tace bakuyi breakfast ba kuka fito”.
Ranƙwashi takaima Ikram ɗin, amma sai ta kauce tana dariya da faɗin, “Wlhy Yaya ita a barci ma aka tasota gara ni nasha tea”. Wani ranƙwashin zata sake kaimata ya zuba mata hararar data sata dakatawa, sai dai tayi gefe da kanta tana ƙunƙuni.
“Oya zauna ki haɗamin yunwa nakeji”. Ya faɗa yana ajiye ledar

Please Login or Register in order to submit comment