Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbatar idan ta koma gidanta a haka tofa tanayin sallama jibgar Anam ce zata biyo bayanta. Mamah (Gwaggo Halima) batai mamakin ganinta ba, saboda babu jimawa suka gama magana da Gwaggo a waya, sai dai su dukansu babu wanda yay tunanin nan Fadwa ɗin ta taho. Hasalima kiranta take son yi sai gata. Kuka ta fashema Mamah da shi, dan haka ta tsaya tana kallonta kawai.
“Wlhy Mamah sai dai na dawo nan da zama inhar akace sai ta zauna min gida. Ai dama tun farko haka mukai da shi zan zo nan na zauna har sai ya dawo, amma yana zuwa can gidan aka canja masa tunani, ni na gane Mommy da Gwaggo duk bakinsu ɗay.....”
“K bana son shashanci, ke ko Fadwa wai sai yaushe ne zakiyi hankali ne? Idan an faɗa miki ki dinga saurara..”
“Mamah dan baki san abinda ke faruwa bane fa, baƙar yarinyar can ɗiyar wancan mutumin na Malaysia fa aka kawo wai su tayani zama gida ita da Aysha. Na nuna masa ban yarda ba yana neman min azaba da masifarsa. Na faɗama Mommy amma Gwaggo ta nuna wai tanada shiri. Wane shiri gareta? Na fahimci tsohuwar nan bata sona kawai yanzun...”
“Fadwa!!”
Mamah ta katseta a tsawace. .......✍🏻


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/25, 1:10 PM] Marsy😘: *_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_23_*


.........“Anya ƙwaƙwalwarki na aiki da ƙyau kuwa? Kin san wacece Gwaggo a wajen mu? To muna mata kallone tamkar mahaifiya, domin tana bamu dukkan gata irin na uwa tun mahaifiyarmu na raye. Su kansu su Yaya da suke mata wani abun a yanzu babu abinda ke ɗawainiya da su sai asiri da ƴan uba sukai musu saboda su basa samun koda sakin fuska daga gareta, sai dai Alhmdllhi na gagara a garesu, ƴan uwana ma zan dawo da su hanyar da aka kautar dasu. Bari na tuna miki idan kin manta, shi wannan auren da kike takama da shi Gwaggo ce tai ruwa tai tsaki akan kowa har shi Shareff ɗin da uwarsa, dan haka kisa hankalinki waje guda, na tabbata tunda tace mu bata lokaci akwai abinda take shiryawa. Kema ina so ki kwantar da hankalinki Fadwa, kinga bake kaɗai bace ba, ba'a bukatar duk wani tashin hankali daga gareki yanzun, indai matsalar ƴar Usman ce dake gidanki, ki bamu ƙankanin lokaci, ba gidanki kawai ba, Nigeria gaba ɗaya zata bari, barin da har abada bazata sake waiwayowa ba ita da iyayenta. Sai dai hakan bazai faru ba har sai kin haɗiye komai yazama ba komaiba, inba hakaba tashin hankalinki na nufin samun cikar burin Usman na ganin ya nanama Shareff ita ya aura.....”
Wani mugun tari ne ya sarke Fadwa, sai da Mamah ta bata ruwa tasha, hawayena sharara a fuskarta. “Mamah dan ALLAH kar kimin baki”. “Ba baki nake miki ba Fadwa, mun jima da fahimtar ƙudirin Usman na son haɗa auren ƴarsa da Shareff, a yanda su Yaya suka canja kuma komai zai iya faruwa idan har ya fiddo buƙatarsa a zahiri. Shiyyasa muke son amfani da zamanta a gidan naki tunda mijinki bayanan mu mata abinda zatama bar ƙasar gaba ɗaya har uban nata bazai sake sha'awar zuwa ba balle tunanin ƙulla wata alaƙa damu”.
A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya. “To amma Mamah bana ƙaunar ganin yarinyar nan wlhy”. “Haka zaki daure na ɗan lokaci ne, kiyi kamar ma baki san da zamanta a gidan ba, dan so muke ta saki jiki sosai saboda shirinmu yay tasiri”. Har cikin rai bawai ta gamsu bane, dan ba ƙiyayyar wasa takeji a zuciyarta akan Anam ba. Dan kamar an raini zuciyarta da tsanar iyayen Anam ne tun tana ƴar karamarta, hakanne yay tasiri matuƙa tare da cakuɗuwa da kishi ya nunku akan Anam ɗin, dan ko yaya Amrah kan samu sassauci a wajenta duk da itama ba sonta take ba kamar yanda bata son mahaifiyarsu. Sosai Mamah ta zauna ta kara lallashinta da maganganu masu daɗi har ta ɗan huce, kwanciyarta tayi anan sai washe gari ta koma gidanta da yamma.

Aysha kawai ta samu, Anam bata dawo aiki ba. Itama Ayshan ƙin sake mata tayi, sai daga baya kuma mitagani oho mata saita fara janta da hira da tambayar jiya basuji tsoroba dai ko su kaɗai. Aysha bata da saurin fushi, duk da tsumewar da Fadwa ta shigo tana mata sai bata ɗaukesa komai ba. Kanta tsaye fuska da murmushi ta shiga bata amsar basuji ba saboda Yaya Khaleel yazo da wuri, shine ma yake sanar musu bazata dawio ba sai gobe. Murmushi kawai tai, daga haka ta canja hirar.
Sai kusan ƙarfe bakwai Anam da Khaleel suka shigo, da alama bayan sun tashi aiki can gidan ya wuce da ita, sai da ya gama kimtsowa suka taho tare. Yanda Fadwa bata kulata ba. itama sai batabi takanta ba tai shigewarta ɗaki ta barsu suna gaisawa da Khaleel, tanaji suka zarce da hira bata fitoba sai ma tai kwanciyarta dan dama taci abinci wajen Mom abinta. Har tai barci Aysha bata shigo ba, sai da ta farka ta ganta kwance, dama Aysha a ƙasa takeyin kwanciyarta dan Anam bata iya barci ita da wani a gado, shiyyasa a ranar farko tai kwanciyarta a sofa, ganin hakan yasa Aysha jiya tace ta hau gadon ita zata kwanta a ƙasan dan Anam ɗin kasa barci tai. Alwala tayo tai nafilfilinta sannan ta dawo ta sake kwanciya.
Koda sukai sallar asuba bata koma ba, shirin fita aiki tai har Aysha na mitar sammakon nata bata dai kulata ba. Lokacin da suka fice ita da Khaleel Fadwa bata fito ba ma. Sai mai aikinta da jiya tazo da ita daga gidansu ce keta faman aikin gyaran falon.....

________________________★

Yau kwanakin Shareff biyar kenan da wucewa ƙasar China. A zahiri tsakanin Anam da Fadwa babu mai shiga harkar wani. A baɗini Fadwa ta kasa jin zata haƙura da jiran shirin su Gwaggo. Dan kuwa kullum jin ƙarin tsanar Anam ɗin take a ranta musamman idan tana waya da Shareff ya tambayeta lafiyarsu. A yanzun ma har faɗa sukai dan yace taba su wayar su gaisa tace Aysha kawai zata bama wayarta banda Anam. Ya tambayi dalili tace saboda Anam ɗin bata isa ba.
“Nasihar dana muku kafin na taho bata shigaba kenan? Fadwa miyasa kike son kawo min raini ne akan duk abinda na sharɗanta miki?”.
“Ni laifina kawai kake gani ita bazaka bincika mitaiba. Yarinyar nan tunda tazo gidan nan sai dai taci ta kwanta tai wanka ta fita. Ko gaidani batayi, kai kallo ma ban isheta ba ina matsayin matar gidan. Ya kake so nayine Soulmate? Sai naita binta tana jana a ƙasa duk da ina sama da ita? Ai Aysha ba haka takeba, zata zauna muyi hira ta taya mai aiki aiki, kai kullum ma itace mai mana abinci, finta tai a gidan da ita bazata zauna ayi da ita ba. Shiyyasa tun farko nace ban yarda ta zaunamin gida ba amma kaƙi saurarata....”
Ƙittt ya kashe wayar, hakan ya sake harzuƙa zuciyarta sai kawai ta fashe da kuka. Kuka taci har ta gode ALLAH. Tana cikin kukan sai gasu Sima tamkar an jehosu gidan har su huɗu. Anam na baranda zaune tana karatu suka wutota. Yanda basu mata sallama ba itama ko kallonsu batai ba dan ta gane Sima. Turus sukai suna kallon Fadwa da duk ta koɗe ta fita hayyacinta a kwana kaɗan, dama sun bar ganin posting ɗinta ne gaba ɗaya shiyyasa sukazo suga ko lafiya, dan bata cika zama gwanar kiran waya ba ita dama, ko kiranta kai sai ta gadama take ɗagawa.
“Baby Fady kina lafiya kuwa?”.
Cewar Siyyah da tun randa suka kawo Fadwa ɗin bata sake tako gidan ba sai yau. Komai batace ba, sai wasu hawaye da suka sake gangaro mata. Da sauri Amal takai zaune kusa da ita ta rungumota jikinta tana shafa bayanta cike da lallashi, kusan mintuna uku Fadwa ta fara sauke ajiyar zuciya, hakan yasa Amal ɗagota. Tissue Sima ta ɗibo ta miƙa mata, babu musu ta amsa ta share hawayenta. Bibah da tunda suka shigo batace komaiba sai yanzu ta kalla Fadwa. “Baby Fady kinsa duk jikinmu sanyi, badai namijine ya fara nuna miki butulcinsu na cin moriyar ganga a yada kaurenta ba, kin ganki kuwa duk kin wani yamutse kin fita a kamaninki kamar wata mai ƴaƴa huɗu”.
Baki ta buɗe zatai magana turaren ɗaya daga cikinsu dake ta faman hawa mata kai ya sata tashi da gudu tai toilet. Da kallo duk suka bita, sai da ta fara kakarin amai ne suka mike a zabure suka rufa mata baya. Da taimakonsu ta wanke bakinta, Sima na yatsine-yatsine ta gyara wajen.
“Tabɗi babbar magana. Da alama dai Baby Fady cikine da ke”. Siyyah ta faɗa cikin riƙe baki. Sima ta ƙarɓe zancen da “Wane irin ciki kuma ana zaune ƙalau Shamsiyyah?”.
Fadwa da ta fahimci turaren Bibah ne ke hawa mata kai hanunta toshe da hancinta tace, “Bibah turarenki ne matsalata wlhy, buɗe Wadrobe ki ɗau wasu kayan ki canja a fidda waɗan nan karki kashen.....” bata karasa ba aman ya sake tahowa dole da sake mikewa da gudu tai bayi. Yanzu kam yi sukai kamar bazasu bitaba, sai daga baya cikin ƙunkuni Sima tabi bayanta ta taimaka mata. Kodan karsu cigaba da bautar kwashe amai dole suka takurama Bibah ta tashi tai wanka ta canja kaya. Daga haka aka samu sauƙi hankalin Fadwa ya samu nutsuwa harta kira mai aikinta ta kawo musu abinci da kayan ciye-ciye. Ta tambayi Aysha fa? Tace barci take. “Bakar yarinyar nan fa?”. “Ranki ya daɗe tana waje tun ɗazu kamar karatu dai take”. Baki Fadwa ta tabe, cikin bada umarni tace rufemin ƙofar falo bana bukatar shigowarta har sai ƙawayena sun wuce”. “Okay ranki ya daɗe an gama”.
Bayan fitar mai aiki su Sima suka shiga tambayarta tana da damuwane ko kuwa cikinne ya maidata haka har yazam ba'a ganinta a online gaba ɗaya. Ranta a ɓace yake sosai da abinda ya faru tsakaninta da Shareff yanzu, ga damuwar hanata ɗaukar mataki akan Anam da su Mamah suketa famanyi har yanzun. Ita kuma tanajin cewa bafa zata iya juriyar zaman jiransu ba a halin yanzu tunda har takai mijinta na kashe mata waya dan ta faɗi laifin Anam. Su Sima ƴan amanarta ne da take kallo fiye da kowa a cikin ƙawaye. Bibah da Shamsiyya ƙawayentane tun na ƙuruciya sannan ƴan uwanta ta ɓangaren mahaifi. Dan haka kanta tsaye ta shiga zayyane musu dukkan damuwarta akan zaman Anam a gidan dama abinda take tsoro wanda dukan sunsha cemata dama suna zargin Shareff da Anam na soyayya ne tana gwalisesu.
Dukan su kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. Dan kowannensu akwai manufarsa a kanta tun ba yanzu ba. Fadwa nada ƙyau gwargwadon iko sun sani, mahaifinta nada arziƙi gwargwado shima sun sani. Sai dai Bibah ta fita ƙyau nesa ba kusa ba, hakama mahaifin Siyyah yafi na Fadwa arziƙi nesa ba kusa ba. Amma ta fisu abubuwa da yawa da suke ganin ya kamata ace sune ke da shi ba ita ba. Hatta su Sima data raini wayewarsu da ɗaukakarsu da kanta kowanne da nasa manufar....
Ta bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya idonta cike da ƙwalla. “Ina son kowannen ku ya bani shawara guda ɗaya akan matsalata domin kaina ya kulle ina neman mafita. Mafita ta gaggawa kafin matsalarmu da mijina tafi haka faɗi dalilin ta”..........✍


_😹😹😹Keda ke a gidan aure, amma kina neman hanyar warware matsalar rayuwar aure a hanun wanda basu taɓayi ba. Bayan kin fisu sanin abubuwa da yawan daya kamata ace a wajenki zasu nema shawara idan sunyi nasu auren. Mata a kula, nasan akwai masu hankali acikin wanda basuyi auren ba da yawa da zasu iya baki ƙyaƙyƙyawar shawara mai ɓullewa. Sai dai ki sani, ba kowacce ƙawa bace zakiyi aure ki barta a titi taso ta ganki cikin nutsuwa da farin ciki a gidan aurenki kema. Hakama wanda suke gidan auren ba kowacce bace zata so ta ganki a samnta. Amma kumuje zuwa muji ko shawarar da Fadwa zata samu ga ƙawayenta ita zata ɓulle da ita🤕🤕🤧._


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[10/25, 1:10 PM] Marsy😘: *_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_24_*


..........Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu mintuna kamar kowa bazaice komai ba, kusan mintuna uku Amal ta nisa. Cikin ɗan ɗari-ɗari ta fara magana. “Ni dai a nawa nazarin da hange sai naga kamar cikin nan shine matsalarki. Kin san fa wasu mazan basu son da anyi aure ace ciki ɗin nan. Kigafa yanda Shareff ke sonki amma ace haka na faruwa tsakaninku wata baifi uku ba da aure, amma dai bamu san zuciyarsa ba kuma”.
Ta ƙare maganar da ɗan shafo gefen wuyanta ganin yanda suka tsura mata idanu su duka. Yanzu ma kamar bazasu ce komai ba, harta fara tsarguwa sai Siyyah ta katse fargabarta.
“Kuma fa maganar Amal kamar tana a kan hanya. Musamman idan mukai dubi da yanayin mijinki. Anya kuwa cikin nan bashine matsalar ba...”
Nufashi Fadwa taja da ƙarfi, zuciyarta babu abinda take hasaso mata sai yanayin Shareff a randa Dr Jamal ya tabbatar musu tana da ciki, ƙanensa da iyayensu kowa na murna amma shi bataga ko murmushinsa ba, da suka dawo gida ma baice mata komai game da cikin ba amma yana bata kulawa da duk take buƙata. Kenan in dai maganar ƙawayenta gaskiya ne kulawar yana bata ne kawai domin kar ace baya farin ciki? Ya ALLAH itako yaya akai ta kasa ganewa sai yanz.........
Sima ce ta katse tunaninta da faɗin, “Fady nima dai ina ganin maganar su Amal nakan hanya gaskiya, dan na tabbatar badan cikin nan ba maybe ma tare da ke zai wuce ku ɗanyi honeymoon ɗinku. Amma gashi ciki ya muku cikas dole yayta maida allura galma a tsakaninku, ta hakanne kuma wannan yarinyar zata samu damar cika burinta akansa. A yanzu ma ɗaukar ciki duk ta wajigaki miji na gudunki inaga kin haihu, wlhy yara haukataki zasuyi ki fita hayyacinki. Baki ga miji hatta da followers naki sai sun gudu, dama kece mai kankaro mana mutunci saboda a yanzu kina cikin manyan tiktokers dake lokaci da kuma tarin followers a arewacin Nigeria, sunanki ya riga yayi zarra, da kin saki video tamkar wuta jaje haka yake danne duk wani posting, kiyi tunani”.
Da ƙyar ta iya haɗiye hawayen da suka ciko mata ido saboda maganganunsu sun matuƙar shigarta. Ta sake nisawa cikin ɗacin zuciya batare data kallesu ba. “Naji duk bayanan ku, sai dai ban san yaya kuke so nayi da cikin ba tunda ya riga ya shiga jikina, tun kafin faruwar haka ya kamata na ɗau mataki, amma a yanzu na riga nayi latti..”
“Bakiyi latti ba Fady, har yanzu kina da sauran dama”.
Ido ta tsirawa Bibah da tai maganar. Bibah ta jin jina mata kai da cigaba da faɗin, “Da gaske bakiyi latti ba, kwata-kwata cikin ana maganar ko wata biyu bai cika ba, ki zubar da shi kawai, hakan zai baki damar sasantawa da mijinki tare da fatattakar shegiyar yarinyar can a rayuwarsa. Idan ya fara nuna son ƴaƴan da kansa sai ki bama cikin damar shiga hankalinki kwance”.
Sosai maganar ta doki ƙirjin Anam dake saurarensu ta jikin window, dan a inda take zaune windown ɗakin Fadwa ne, tun kuma shigarsu ɗakin tana iya jiyo tattaunawarsu, sai dai da farko bata maida hankali ba sai da Amal ta fara danganta ciki da matsalar Fadwa. Duk da bata son Fadwa addu'a take a ranta kada ta ɗauki shawarar su Sima........ Ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani, Mamie ce, hakan ya sata mikewa a wajen tilas tana amsa kiran dan video call ne.....

Wayarta da Mamie ta hanata jin ƙarshen hirar su Fadwa, dan dai-dai tana kammala wayar suke fitowa kowannensu fuskarsa ɗauke da dariya. Su dukansu kallon banza suka shiga watsa mata suna jan tsaki, wasun su ma har da jeho mata kalmar zagi. Batako kalli inda suke ba, tamayi kamar bata gansu ba. Koda Fadwa ma ta dawo daga rakkiyarsu bata nuna ta ganta ba itama.
Itama ciki ta koma zuciyarta na kaikawo na neman mafita duk da bata san yaya ake ciki ba a yanzu. Fadwa ta karɓi gurguwar shawararsu kokuwa?Ba komai ta fahimta a hirar tasu ba dan ma suna haɗawa da turanci ne shiyyasa na zubda cikin yafi tsaya mata a rai. Ganinta shiru yasa Aysha data fito a wanka tambayarta ko lafiya. “Babu komai” ta bata amsa tana mikewa itama ta faɗa bayi.

Kusan sati ɗaya dayin wannan magana har Anam ta sakankance Fadwa bata amshi shawarar ƙawayenta ba sai kawai ga Khaleel da yazo ɗaykarta an tashi aiki yake sanar mata Fadwa na asibiti ta samu miscarriage. Tsabar yanda zancen ya daketa batama san sanda ta maimaita kalmar miscarriage ɗin ba cikin waro iro. Da damuwa a fuskar Khaleel ya gyaɗa mata kai. “To ya za'ayi, haka ALLAH ya ƙaddara, wajen 3 na yamma Aysha ta kirani wai Fadwa tace cikinta na ciwo ta rakata asibiti. Suna zuwa likita yace cikintane ke son fita yay mata allura don hana faruwar hakan amma ba'a dace ba. Yanzu haka su Mom ma duk suna can nima dan ɗaukarki na fito dan ta zubar da jini sosai gaskiya”.
Har cikin rai Anam kejin zafin abin dan ta tabbatar Fadwa da kanta ta zubar da cikin nan, kuma tabbas da likitan suka haɗa baki dan a ɓadda kama wa Ayshan. Jin batace komai ba Khaleel ya dubeta. “Ya naji kinyi shiru?”. Numfashi ta fesar da zuƙa, cikin kauda kai tace, “Ba komai ALLAH ya kiyaye gaba”. “To amin ya rabbi. Amma dai kowa baiji daɗin fitar cikin nan ba. Yaya Shareff ma koda na kirasa kasa magana yayi ya yanke wayar. Sai daga baya na sake kiransa wlhy bakiji muryarsa ba kamar yayi kuka. Hakan yasa na fahimci ba ƙaramin so da ƙwallafa rai yayi akan cikin nan ba fiye da kowa”.
“Huhmm!”.
Kawai Anam ta iya cewa saboda sun iso asibitin. Duk ƴan gidansu suna a wajen har Mommy da Gwaggo Halima. Ta gaida kowa da tambayar mai jiki ta koma kusa da Aysha. Babu jimawa da zuwansu su Abbah ma suka iso, daga gani daga wajen aiki suka wuto nan suma. Har sannan ba'a bar kowa yaga Fadwa ba. Amma dai doctor yace da sauƙi sun mata allurar barci ne dan ta jigata matuƙa.
Kasancewar kusan duk daga wajen aiki ko makaranta sukayi nan Daddy yace suje gida haka nan abar wanda zai zauna da ita. Gwaggo da ƙanwar Fadwa ɗin aka bari, sai Gwaggo Halima da tace sai zuwa anjima zata tafi ita. Su dai sallama sukaui musu suka wuce kowa na cigaba da jajanta abun a ransa.

Washe gari kafin su wuce office nan suka fara zuwa ita da Khaleel, sai Aysha data biyosu dan kawo breakfast. Sun samu Fadwa zaune tana waya da alama ita da mijinta ne, dan sai faman marairaice murya take hatta da Gwaggo dake kusa da ita bawani jinta take ba. Ganin tana waya Khaleel ya fita dan ganin doctor, Aysha tabi bayansa da sauri dan tana son amsar kuɗi a wajensa nayo cefane daya manta bai bada ba. Gwaggo da tun shigowarsu tai kamar bataga Anam ba ta miƙe tana ɓantarar goro. Hanyar fita ta nufa dan so take ta tare Khaleel a waje ta amshi kuɗi itama. Ɗakin ya rage daga Anam sai Fadwa dake waya tana ɗan ɗaga murya yanzu wai dan Anam taji. Anam ɗin kuwa tana ji, sai dai tayi kamar bataji ɗin sai faman buga game take a waya. Lokaci-lokaci takan kai yatsa ta gyara zaman gilashinta.... Tsakin da Fadwa taja lokacin da ta kammala wayar yasa Anam ɗan dubanta. Kallon juna sukai cikin ido, Anam ta janye nata cikin halin ko in kula.....
Yanda tayi sai ya batama Fadwa rai, duk da halin da take ciki muryarta ko fita bayayi da ƙyau ta watsama Anam harara da jan tsuka a karo na biyu. “Ban cika son ganin wanda ban gayyata cikin lamurana ba, ko kuma ban sani ba ko zargin namu ya zama gaskiya ne lashemin jariri akayi..”
Da turanci tai maganar, hakan yasa komai ya shiga kunnen Anam. Batai niyyar harta bar asibitin ba tai magana amma sai ta kasa hakan, dan a wannan gaɓar taga ya dace ta bama Fadwa amsa dai-dai da ita. A hankali ta taka gaban gadon tana zira wayarta a aljihun wandon uniform ɗinta na hidimar ƙasa. Babu alamar tsoro ko shakka a cikin idanunta ta tsaya gaban Fadwa dake mata kallon mamaki. Idanunta dake cikin farin gilashi ta lumshe ta sake buɗewa akan Fadwa. “Tabbas jaririnki kam cinyesa akai amma da allurar zubda ciki. Dan haka masu zargin zan basu amsar da suke bukata har shi mai cikin dan yasan ɗansa ko ƴarsa sun salwantane ta hanyar abortion bisa shawarar ƙawayenki masu ɗauraki a hanyar da bazata taɓa ɓullewa da ke ba. Ai ban san ke ɗin cikon bench bace ba sai yanzu. Ki fita a sabgata, idan kuma kikace zaki iya dani wasan biri zanyi da ke a tsakkiyar kasuwa na rantse da ALLAH! Be careful”. Ta ƙare maganar da ɗalla yatsunta biyu a saitin fuskar Fadwa tana wani irin murmushi da kashe mata ido ɗaya.
Numfashi Fadwa taja da ƙarfi, dan tun fara maganar Anam tai sumar wucin gadi........✍🏻


_Wannan yarinya tsaurin idonta yayi yawa kudinga mata fada ta kiyaye Fady babynmu inba hakaba za'ai yakin duniya na 79 a kanta☹️👩🏻🦯_


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_[10/26, 1:26 PM] Marsy😘: *_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_25_*


........“A'a lafiya?”.
Khaleel dake shigowa ya faɗa idonsa a kansu. Baya Anam ta ɗan ja tana murmushi, ta girgiza masa kanta. “Ba komai Yaya ina dubata ne kawai”.
“Okay tom ai haka yana da ƙyau. Bara nima mu gaisa sai mu wuce kar ki

Please Login or Register in order to submit comment