Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbacin abun na ranta kamar zanen dutse har yanzu suka shiga rige-rigen sakkowa. Cak ya tsaya yana kallonta, kuka take sosai kamar wadda aka doka, kusan tsahon minti guda da wasu sakanni ta gagara tsaidasu. A hankali ya rumtse idanunsa, tare da furzar da ƙaramin huci daga bakinsa. Shiru bashi da alamar cewa komai balle lallashinta, itako sai ƙara matso hawayen take wani baƙin ciki da takaicinsa na sake hasalata, tabbas da ace lafiyar ƙafarta ƙalau ɗakin zata bar masa....
“K sau nawa ina hanaki tarayya da wannan yaron amma kika maidani sauna? Bayan shi ba muharraminki ba itako *Matata ce!*”.
Karan farko da tunda ta fara kukan ta ɗago jajayen idanunta tana kallonsa cikin tsakkiyar ido. Shima kallon nata yake a tsakkiyar idon......
Ita ta fara janyewa cikin ƙunƙuni tana faɗin, “Ni dai baza'a rabani da masoyina ba”.
Sosai kalaman nata suka daki ƙirjinsa. Sai dai kafin yay wani yunƙuri aka dakatar da shi.
“Mike faruwa anan?”.
Aunty Mimi dake shigowa ta faɗa cikin dariya. Ita ta fara janye nata idanun, batare da tace komai ba ta zame ta kwanta. Shima numfashi ya ɗan fisga, cikin yanayi kamar mai borin kunya ya ɗaga kafaɗarsa. “Nothing Aunty. Zan wuce gidane goodnight”. Kafin ta samu damar cewa wani abu yayi ficewarsa. Da kallo ta bisa har ya fice, kafin ta juyo ga Anam dake faman sauke ajiyar zuciya.
Komai batace mataba, sai da ta tadata zaune ta bata abincin da kanta tare da magungunanta sannan ta fiskanceta da ƙyau. Kai tsaye tace, “Mamana kina son Shareff ko??!...”
“God for bid Ummie”.
Ta faɗa cikin tarar numfashin Aunty Mimi da saurai.
“Sure?”.
“Yes Ummie”.
Yanda ta bada amsar da ƙwarin gwiwa yasa Aunty Mimin haɗe fuska tana mata kallon sama da ƙasa. Cikin rashin wasa tace, “To *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!”*.
“Kishi kuma Aunty? A dalilin mi zanyi kishinsa?”.
Ko amsa ɗaya Aunty mimi bata amsa mata ba, sai dai ta kafeta da ido ganin hawaye na ciko mata ido. cikin ɗan ɗage kafaɗa tace, “Okay fine kwanta kiyi barci”.
Kwanciyar tayi, tana ta faman ALLAH ya kiyaye ta so wannan mutumin a zuciyarta, a fili dai bakinne kawai ke motsawa babu sautin fitar magana......

★★

A hankali yake driving ɗin tamkar baya so ko kuma shi kaɗaine a titin, motoci da yawa sai sun masa horn yake ɗan kaucewa ya basu hanya su wuce, ga kiran Fadwa dake faman shigo masa waya babu ƙaƙƙautawa. Sai da tai wajen bakwai baida alamar ɗauka, ana takwas ɗinne ya fisgi wayar a fusace daga change daya sata yakai kunne. Sai dai baiyi magana ba dan inhar ransa ya ɓaci baya son ya ringa cewa komai....
“My son!”.
Muryar aunty Mimi tazo masa a bazata. Da sauri ya cire wayar a kunensa ya kalla. Tabbas Aunty Mimi ɗince ba Fadwa ba. Yawu ya haɗiye da ƙoƙarin saisaita kansa. “Yes small Mom ko nayi mantuwa ne?”.
“Da alama tunda ka tambaya ƙila kayo ɗin”.
Ƴar dariya yayi yana shafa kansa da lanƙwasa kan motar ya shiga layin gidansa. “Aunty kenan, da alama magana kike nema dai kawai”.
“Kusan hakan, sai dai kai tsaye zan yita, kamar yanda nayi a ɗayan ɓangaren”.
A hankali ya tsaida motar a ƙofar gate, sai dai baiyi horn ba. “To ina saurarenki mamana!”.
“Babana kana son Anam ko?!”.
Da ace ruwa yake sha ko cin abinci babu shakka sai ya ƙware dan abinda Small mom ɗin nasa ta faɗa yazo masa a baza. Ya haɗiyi yawu da sauri jin maƙoshinsa na ƙafewar danshi. Yay ƙoƙarin saisaita kansa kai tsaye yace ni da nai aure sati guda kuma”.
“Ba labarin aurenka nake tambaya ba, dan nima ban manta lissafin ba. Ka bani amsata kawai”.
Steering ya ɗan daka yana cije lips, cikin son kauda mata dukkan wani tunani babu ko gargadar murya ya bata amsa.
“Aunty ni matata kawai nake so, bayan ita babu wata a raina”.
Shiru Aunty Mimi tai, sai kuma ta saki murmushi mai sautin da har yaji, cikin dakewa tace “Sure?”.
“Babu kokwanto a maganata Mom”.
“Okay fine. To amma *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!*”.
“Kishi kuma?! Sai dai na zuminci”.
Ƴar dariya aunty Mimi tai da faɗin, “Lallai kam”. Tana yanke wayar.
Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka yay baya luuu jikin sit ya kwanta, idanunsa da suka canja launi ya lumshe, tsahon mintuna ya kasa horn balle yunƙurin shiga gidan. Ga kiran dake shigo masa waya da baya raba ɗayan biyu Fadwa ce amma ya kasa yin komai. Sai da ya sake shafe kusan mintuna goma sha biyu har mai gadi ya gaji da leƙowa ransa fal mamakin lafiya sannan yay masa horn.
Da ɗan gudunta ta fito, duk da ranta a ɓace yake saboda kiran da take jera masa yaƙi dagawa sai ta danne saboda shawarar su Sima da take hange mafita a gareta basai ta cigaba da tada jijiyar wuya a wajensa ba. Ta ɗanesa tare da maƙalƙalesa, ko kulada yanayinsa batai ba ta haɗe bakinsu. Ƙoƙarin janyeta yay yana kauda kansa kodan maigadi da yake da tabbacin zai iya hangosu amma ta hanashi damar hakan. Dole yay ta maza ya tura murfin motar da kafarsa ya ɗauketa gaba ɗayanta yay sasheta bayan ya raba bakinsu da ƙyar. A kujera ya zube da ita jikinsa, babu wani ɗaga kafa ta sake maida bakinta kan nasa. Baya buƙatar komai a halin yanzun, sai dai bazai iya ƙin bata hakkintaba koda ace faɗan doke-doke sukai indai ta nema zai biya mata, balle ma baya buƙatar haɗa wata matsala tasa ta waje da cisgunawa iyalinsa wannan alƙawarine ya daukama kansa insha ALLAH, laifinta kuma zai mata hukunci a lokacin daya shirya. Duk da babu wani karsashi tare da shi ita ke kiɗanta tana rawarta bata damuba, sai da ta tabbatar ta isar da saƙon da take bukata sannan ta barsa tana mai kallonsa cikin ido cike da so da kaunarsa.
“I love you my Soulmate”.
Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akanta. Batare da yace komai ba ya lakaci hancinta da yatsansa. Sai kuma ya ɗanbi falon da kallo. Ganin komai tsaf yaji haushinta ya ragu a ransa. Ya ɗan rungumota jikinsa da sumbatar hancinta. “Haka nake so na dinga ganinki k da gidan nan a koda yaushe”.
Kai ta jinjina masa tana murmushi da faɗin, “Zaka sameni mai aikatawa”.
“ALLAH yay miki albarka bari naje na ɗan watsa ruwa”.
“Kodai ka fara cin abinci”.
Ɗan kallonta yayi na wasu ƴan mintuna, “Sure baiyi ƙauri ba na yau?”.
“ALLAH bai yiba”.
“Okay muje”.
Duk da ba son cin abinci yake ba haka ya dinga turawa, dan babu makusa a girkin sai abinda ba'a rasa ba. Dan kawai ya bata ƙwarin gwiwar cigaba dayi kamar hakan ya yaba tare da saka mata albarka..

★★★★★

Kwanaki sun cigaba da shurawa Anam na samun lafiyar ƙafarta. Tun daga ranar dai bata sake ganin Shareff a ƴan dubiya ba. Sai dai takanji maganarsa yazo gidan ko su Amrah suce mata yazo. Dan kamar da gayya sai ya daidaici lokacin da bata falon yake zuwa. Bata damu ba, dan a wannan gaɓar bama ta buƙatar ganin nasa sam. Tana son ƙara zama nesa da shi dan tunanin da aunty Mimi keyi a kanta ya gushe har abada. Kwanakinta biyar ta take ƙafarta sarai ta koma zuwa aiki. Kullum takan shiga gaida matan gidan cikin gida kamar yanda Mamie ke jaddada mata. Sai dai kuma iyakar Mom da Aunty Amarya kawai take zuwa ta gaida bata shiga sashen Mommy dana Gwaggo. Wajen aiki kam tare suke fita da Khaleel, wataran ya dawo da ita wataran Yaseer ya maidota dan yanzu ta ɗan fara sakin jiki da shi ganin bai nuna mata wata alama data danganci soyayya sai abota kawai. Muzzaffar ma yasha gwada zuwa ɗaukarta a office ɗin amma taƙi bashi fuska sam, hakan yasa ya fara zuwa gida kai tsaye dan shikam dai yaga matar aure. Tun tana noƙewa harta ɗan fara sakewa saboda huɗubar Aysha. Sai dai duk da hakan taƙi yarda ta amsa tayin son sa. Tana dai saurarensa darajar Abbansa abokin Abie ne kuma abota mai ƙarfi tun ƙuruciya dan tare sukai secondary school, a yanzu haka kuma suna ɗan huɗɗar kasuwanci tare.
A haka kwanakin hutun Shareff suka cika, Maheer ma ya koma katsina wajen nasa aikin tun satin daya shige. Da farko Shareff baya zuwa gidan da safe sai ya taso aiki yake shigowa ya gaidasu. Sai randa yazo sallama da su aunty Mimi da zasu koma Malaysia saboda yara makaranta ya samu Yaseer ya kawo Anam gida. Kuma har cikin gida Yaseer ɗin ya shigo gaishe da su Mamie, a yanda suka amshesa da alama ba wannan ne ma farko ba kamarma ya zama ɗan gida. Komai baice ba, sai dai koda Yaseer ya gaida shi hannu kawai ya ɗaga masa, daga karshe ma ya miƙe ya fice batare da an kammala sallamar ba. Da kallo kawai aunty Mimi ta bisa tana ƴar dariya, Anam kam ta taɓe baki da sake maida hankalinta ga Yaseer tana dariyar maganar Amrah kamar ma bata san da Shareff ɗin ba. Dan koda ta shigo ta gansa a taƙaice tace “Yaya good evening” tai wucewarta. Shi kuma bai amsa mata ba sai hararar da yabi ƙafafunta da su dan kansa a duƙe yake yana daƙilar waya.
Washe gari da shi akaima su aunty Mimi rakkiya airport, daga can kuma yay wucewarsa office. Anam kuma suka wuce tare da Khaleel daya buga mata warning ɗin kar ta sake tabi wata mota zai zo ya maidata gida da kansa koda bai tashi aiki ba. Badai tace masa komai ba, amma ta bisa da kallon mamaki. Hakan kuwa akai, tun kan ma a tashi aiki yazo yana zaman jiranta, washe gari ma haka sukai haka har kusan sati biyu da su Mamie suka fara shirin komawa suma. Nan fa hankalin Anam ya tashi, ta dinga kuka da magiyar zata bisu Mamie tace bata isa ba. Daga ƙarshe tai mata kaca-kaca sannan ta dawo lallashi da nasiha. Haka tanaji tana gani suka tafi suka sake barinta a Nigeria ita kaɗai. Cikin gida ta sake komawar dai sashen Mom dan nasu gidan an rufe kuma, ranar haka ta yini sukuku kamar mara lafiya, da ga ƙarshe ma har zazzaɓin sai da tayi. Sai da Khaleel ya samo mata magani.
Su Mamie juma'a suka wuce, dan haka bata fita ko'ina ba sai monday tai shirin zuwa wajen aiki. A cikin ɗaya a dogayen abaya da Mamie tazo mata da su tai shirin, bayan ta saka kayan hidimar ƙasa a ciki dan sanyi takeji yau. A hankali ƙamshinta ke fita, ga black skin nata na shining exactly cikakkiyar ƴar Africa. Bisa matsawar Mom ta zaman yin breakfast da abinda take iya ci da Mom ta jura girka mata batare da gajiyawa ba. Kaɗan ma taci ta miƙe tana faɗin, “Alhmdllhi”.
“Badai ƙoshi ba?”.
Mom ta faɗa tana kallonta. Murmushi tayi mai sanyi tana jinjina kanta, dan gaba ɗaya ta zama wata sukuku. “ALLAH Mom na ƙoshi, yau kwata-kwata banajin cin komai ne”.
“Anjima fa zaki iya jin yunwa”.
“To Mom bara naje da shi office ɗin”.
Babu musu Mom ta juye mata a kula mai ƙyau. Sai da ta jira Khaleel yasha shayi shima sannan, fita yay akan ta samesa waje zai shiga ya gaida jama'ar gidan. Saboda kar yasata binsa zuwa gaida su Mommy da tun kan su Mamie su wuce bata zuwa gaida su, shiyyasa ta noke akan zata samesa a mota. Sai da ya fita da kusan mintuna huɗu sannan ta fito. Waige-waige ta shigayi a harabar gidan babu alamar motarsa, tasan yakan kaita waje wani lokacin, dan haka ta nufi gate idan ya fito kawai sai su wuce.
A wajen gate ɗin kuwa ta samu motar Khaleel tare da makanike, ta ɗanyi tsai tana kallon motar da tai fakin a kusa da motar Khaleel ɗin. Kamar tasan motar, sai dai ta manta mai ita dama yaushe ta taɓa ganinta.... Horn ɗin da akai ya sata haɗiye sauran tunaninta. Makaniken dake duba motar Khaleel ya ɗago yana kallonta “Hajiya kamar dake ake fa”.
Ba laifi yanzu kanta ya ƙara buɗewa da jin hausa fiye da yanda tazo, ta jinjina masa kanta kawai batare da tace komai ba. Da farko bataji zataje ba, sai kuma ta canja shawara da tunanin ko Yaseer ne ya ɓadda kama. Murmushi ta saki akan wannan tunanin tana nufar motar.
Yanayin sanyinta a tafiyar ya sashi kafeta da ido cike da nazari, gashi bayan murmushin dake fuskarta babu wani alamun nishaɗi ko farin ciki a tattare da ita.
Zuciyarta ta gama yanke mata shawarar Yaseer ne, hakan yasata nufar ɗayan gefen batare da neman sanin waye ba ta buɗe ta shiga cikin ƴar dariya tana faɗin “Lallai ma Yaseer, kana tunanin ɓadda kama zata sa na gaza gane k.....” Sauran kalmomin suka kasa ƙarasa fita a bakinta saboda ƙamshin turaren da sai a yanzu ta samu nutsuwar banbancewa. Da sauri ta juyo batare data ƙarasa rufe motar datai yunƙurin yi ba. Har cikin rai ta tsorata da katoɓararta, amma sai ta dake cikin son kame kanta tace, “Oh Yaya yi haƙuri, ALLAH nama zata Yaseer ne ina kwana!”.
Shiru kamar bazai amsaba, dan tunda ta shigo bai kalleta ba ko sau ɗaya. Idanunsa da suka surku da ɗan ja ya ɗago ya zuba mata. Ƙoƙarin dannewa da ɓoye tsoranta take a fili, ta kai hannu kan ƙofar da nufin buɗewa ta fice ko zata samu damar shaƙar iska yasa lock.
(Ya ALLAH, wannan mutumin zai iya cinyeni fa a motar nan wlhy gara na lallaɓa) ta ayyana a zuciyarta. Idanu ta marairaice kamar gaske ta ɗago tana kallonsa, “Yaya kayi haƙuri ALLAH ban san kai bane”. Motar yayma key batare da yace mata komai ba ya fisgeta har yana bulama bakaniken dake duba motar Khaleel ƙasa.
Sunayen ALLAH kawai take ambata a ranta dan tasan itakan yau sai romanta za'a samu a hanun mugun nan......
“Mina faɗa miki akan yaron nan kwanaki?!”. Ya faɗa a kausashe dai-dai yana hawa kan babban titi. Kallonsa tai fuska a dake, ta kuma ɗauke da sauri saboda tasa fuskar ma tafi tata dakewar. Cikin ɓata fuska da tura baki tace, “Toni Yaya bamfa san wa kake nufi ba ai”.
Komai baice mata ba, ya cigaba da driving nasa, sai da suka iso dai-dai wajen nata aikin yay fakin daga ɗan nesa. Da mamaki ta kallesa, “Yaya yanaga ka tsaya na.....?”
Rinannun idanunsa daya dasa a kanta ya sata haɗiye sauran maganar muƙut, tai ƙoƙarin ɗauke idonta ya hana hakan cikin tsareta da nasa da duk suka firgitata. “Ni kike faɗama bakisan wa nake magana akai ba.”
Da ƙyar ta fisgi idanunta tai ƙasa da su zuciyarta na bugawa da sauri saboda yanayinsa ya masifar tsoratata. Da sauri ta rumtse idanunta saboda jin yatsun hanunsa a kan haɓarta, ya ɗago fuskarta sosai tare da matsota garesa har suna iya shaƙar numfashin juna. “Buɗesu kona mareki!!”.
Buɗewar tai da sauri saboda kusancinsu ba ƙaramar rikitata yay ba, hatta shi kansa yana iya jin sautin bugun zuciyarta ta hanyar ɗagawa da ƙirjinta ke ɗanyi da sauri-sauri..........✍



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko
[10/21, 2:25 PM] Marsy😘: *_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_18_*

..........Sosai idanunta ke faman marmari ga ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a cikinsu.
“Juwairiyya!! Wlhy! wlhy! daga yau na sake ganin yaron nan ko wani ya ɗaukeki a motarsa koya kaiki gida sai na miki mugun dukan da zaki kasa tashi, kuma ki koma gidana da zama stupid kawai”. Ya ƙare maganar da ture fuskar tata gefe.
So take ta fashe da kuka amma tana ƙoƙarin son dannewa, sai dai hakan bai hana rawar jikinta bayyana ba. A tsawace ya sake faɗin, “Get out of my car! Kafin na marmashe ƙashinki anan stupid”.
Da sauri ta ɓalle murfin ta fice tamkar mai jiran umarnin nasa dama. Yaja dogon tsaki da figar motar yay gaba, badan titi bane da sai ya bula mata ƙura, murfin ma sai da yay gaba kaɗan yaja abinsa ya rufe.
Duk yanda taso ƙoƙarin danne komai hakan ya gagara. Dole ta samu wani dutse a gefen titin ta zauna ta fashe da kuka. Duk abinda kaga Anam ta zauna yima kuka lallai ya taɓata sosai, dan tsiwarta da giringiɗishi bai cika barinta maida abu serious ba, ga kuma yanayin rayuwar data tashi a ciki, ita kaɗai a gidansu sannan a ƙasar da kowa kansa ya sani kawai.
Ring da wayarta ta farane ya sata share hawayenta ta daga dan tasan su Mamie ne, a kullum tana waya dasu a irin wannan lokaci da kuma in zata kwanta. Video call ne, dan haka ta shiga son ɓoye damuwarta da murmushin farin cikin ganinsu. “Good morning my sweetheart”.
Dukansu babu wanda ya amsa mata, dan duk da ƙoƙarin da take na ɓoyewa idanunta sun tabbatar musu tayi kuka. Abie yaja numfashi a hankali yana sake kafeta da ido. “Mamana mi yake faruwa da ke? Waya saki kuka? Ko baki da lafiyar ne har yanzu? A ina kike nan?”.
A karan farko ta saki murmushi dan jin tambayoyin mahaifin nata a jajjere. Samun kanta tai da kasa faɗar gaskiya duk da ƙarya ko ɓoye-ɓoye ba halinta bane, ta sake share hawayen da suka ciko mata ido tana murmushi, “Abie ba komai fa, kawai kewarkuce har yanzu ALLAH. Kuma a wajen aiki nake ban dai shigaba ka gani”. Ta juya masa wayar yanda zai iya hango gate ɗin wajen.
A jiyar zuciya suka saki shida Mamie, kafin su shiga lallashinta duk da ita Mamie a ranta bata gama yarda da cewar har yanzu kewar tasu bace. Amma sai ta barta a hakan dan tasan Anam da rashin ɓoye-ɓoye koma miye wataran da kanta zata sanar musu. Sai da suka tabbatar sun sakata farin ciki tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ba sannan sukai mata sallama Mamie na faɗin ta gaida mata Yaseer. Farin cikin waya da iyayenta ya taushe abinda Shareff yay mata ta shiga wajen aikinta da walwala kamar yanda ta saba ko yaushe.

*_MALAYSIA_*

“Humairah waye naji kina faɗin Mamana ta gaida miki?”.
Cikin rashin damuwa Mamie tace sirikinka ne duk da dai naga ɗiyar taka bata son a gane hakan.....”
Cikin sauri ya ɗago yana kallonta, har ya kasa dannewa sai da ya ambaci “Suruki kuma?”.
Ƴar dariya Mamie tai, “Eh bashi kake fatan ganiba daman?, bayan shi ma ai akwai wasu. Yaron nan Muzzaffar da kuma wani abokin Shareff Jamal. Amma naga hankalinsu yafi zuwa ɗaya da Yaseer ɗin nan kamar”.
Jin shiru baice komaiba ta ɗago ta kallesa, kallonta yake kamar mai nazari ko tunani, ta ɗan taɓashi, ajiyar zuciya ya sauke. “Abien Anam akwai matsala ne?”.
Kai ya ɗan jinjina mata yana gyara zamansa, “Babbama kuwa Humairah, miyasa tun muna Nigeria baki sanar min hakan ba.”
Sosai maganar tasa ta sakata kafesa da ido dan mamaki, amma ta kasa cewa komai. Fahimtar hakan ya sashi jinjina mata kai, “Basai kin tambayeni komai ba Humairah, amma idan lokaci yayi ko baki tambayeni ba zan baki amsa da kaina”.
Gaba ɗaya kanta ya ƙara ɗaurewa ita kam, sai dai rashin sabo dayi masa dagiya yasa ta kasa cewa komai ta bisa da kallo kawai ganin ya miƙe yana kai waya kunensa. Yana gab da shigewa ɗakinsa taji ya ambaci sunan Yaya (tasan Daddyn Shareff yake kira da hakan). Jitai kamar ta tashi ta bisa amma sai ta dake kawai, zata bisa a sannu dan tasan dalilinsa na son hana Anaam ɗin tsayawa da samari bayan kuma duk fatansu kenan ita da shi tunkan ta wuce Nigeria.....

★★★★

Sauraren sakatariyarsa kawai yake batare da yana fahintar abinda take faɗa masa ba, idanunsa ma gaba ɗaya nakan kula ɗin daya shigo dashi, wadda baya raba ɗayan biyu Anam ce ta manta ta...
“Kinga jeki zan nemeki”.
Ya faɗa cikin katse sakatariyar da ke faman zuba bayani cike da yanga da kwarkwasa. Bataso hakan ba, sai dai sanin shi sam baya wasa yasata bin umarninsa. Sai da ta fice da kusan minti ɗaya ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi, yakai bayansa kwance jikin kujerarsa yana mai lumshe idanu. kusan mintuna uku ya ɗauka a hakan kafin ya bude idanun, kular ya ɗauka ya buɗe. Ya tsirama abinda ke ciki idanu tamkar mai irgawa ko lissafa abinda aka sarrafashi da shi. Abincine irin na ƴan ƙasar malaysia, shima yana bala'in son sa a lokacin da ya rayu acan, ko yanzu kuma da yake a Nigeria yakan je takanas ya siya a inda yasan zai samu. Hannu yakai ya ɗauka spoon ɗin dake ciki ya ɗiba dan tabbas wannan ɗin da gani an masa haɗi da girki na musamman ne. Sosai ya lumshe ido lokacin da yake taunawa, koda ya haɗiye sai ya sake ɗiba yakai baki, kamar da wasa sai gashi ya cinyesa tas dan dama bai karyaba ya fito gidan, shayi kawai ya sha, shima sai da Fadwa ta ɓata rai dayin korafin ganin saurin da yake faman yi duk da ta fahimci shi mai fitar wuri ne office sannan ya sha a tsaitsaye ya barota tana tura baki gaba.......
Shigowar Fharhan ta sashi ture kular gefe yana goge bakinsa da tissue. Fharhan dake kallon kular da murmushi ya kai zaune yana faɗin, “Ɗan gatan madam, abincin ma sai an baka kazo office kuma ba gayyatar masu tayaka ci ka kulle office

Please Login or Register in order to submit comment