Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba”.
“I will slap you in baki tashi ba”.
Miƙewar tayi fuska a kumbure. Ya nuna mata hanyar waje, ko kallon saurayin baiyi ba yayma waiter nuni tazo. Kuɗinsu ya bata, tareda wasu yace ta masa takeaway na naman rago. Fadwa da ko lauma ɗaya bataiba dama ta miƙe tsam da wayarta a hannu ta fice, bayansu yabi, sai dai kafin ya fito Fadwa ta tsaida napep ta shige abunta, Anam ko jikin mota ya sameta ta haɗe fuska tamau. komai baice mata ba ya buɗe ya shiga, a dai-dai nan aka kawo masa takeaway ɗin da ya saka akayo. Jin ya kunna motar tai saurin buɗewa itama ta shiga. Sai lokacin ya lura babu Fadwa, motar ya sake buɗewa ya fito yana dube-dube.
Wata shaƙiyyar dariya Anam ta ƙyalƙyale da ita harda kwanciya, tana ganin zai dawo ta haɗiye kayarta da gyara zama ta fuske...
A dake yace, “Malama dawo nan”.
Ido ta ɗan waro tamkar bata san mike faruwa ba. “Yaya Auntyn kuma fa, ba fitsari taje bane?”.
Kallon banzar daya watso mata ya sata buɗe murfin ta fita tana danne dariya da ƙyar, ƙasa-ƙasa take faɗin, “Ai daga yau daga kai har ita kun shiga uku da ni. Sai tasan ita ƙaramar ƴar iska ce”......

★★★★

A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin ɓacin ran dake tattare da ita. Tunda Gwaggo Halima ta kirata ta sanar mata abinda ya faru take kiran wayarsa amma yaƙi shiga. Kasa daurewa tai ta dawo falo tare da tura Hussaina gate zaman jiran shigowarsa. Mintuna goma kuwa ba'aiba cikakku da zaman Hussaina a gate sai ga motarsa ta shigo. Anam ce ta fara fitowa, Hussaina ta bita da kallo harta shige sashen Mom. Shima dake binta da kallon fitowa yay hanunsa ɗauke da ledar takeaway. Hussaina ta taso da sauri tana washe baki dai-dai yana sama motar lock da key ta waje.
“Yaya sannu da zuwa”.
Batare daya kalleta ba ya amsa mata. Idonta akan ledar hannunsa ta kuma faɗin, “Yaya Dama Mommy ce tace kaje tana nemanka”. A yanzu kam idanunsa ya ɗago yana kallonta. Sai dai baice komaiba tsahon sakkani ya janye. Ganin zai bar wajen takai hannu ga ledar. “Bara na ɗauka maka to”. Harararta yay, babu shiri taja baya tana tura baki gaba. Baibi takantaba ya nufi sashen Mom. Fawwaz kawai ya samu a falon zaune yana kallon cartoon. Yaron ya taso da gudu ya nufosa. Ledar ya ajiye gefe fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗagashi sama. “Oh my Friend ya kake?”.
“Lafiya lau Yayanmu. Good morning”.
Kumatunsa ya ɗan ja yana murmushi. Kafin ya ɗan kalla falon. “Gentlemen ina Mom ne?”.
“Tana ɗaki da aunty Rahma tazo”.
“Okay! To kace ina gaisheta.”
Kai ya jinjina masa. Sai kuma ya kai bakinsa kusa da kunnen Shareef ɗin, cikin raɗa yace, “Aunty Anam kuma yanzu ta dawo sai fushi takeyi”.
Idanu ya ɗan waro waje kamar yanda yaron yayi, “Haba dai?”.
“ALLAH kuwa. Ko kulani ma batayiba ina gaisheta da nuna mata Cartoon ɗina”. “Ayya am sorry my dear, maybe bata da lafiyane. Amsa wannan ka kai mata sai kuci tare”. Duk da ledar ta masa nauyi da ɗan gudunsa ya nufa ɗakin cike da murna yana ƙwala kiran “Aunty Anam! Aunty Anam!!”.
Idanu yaɗan lumshe a hankali da harɗe hannayensa duk biyu a ƙirji yana murmushi har yaron ya shige ciki. Haka yake shi mutum ne mai tsananin son yara. Bai shirya aure yanzu ba, amma saboda son da yakema yara ya sashi amsar tayin su Mommy dan ta matsu taga yay aure ya rasa dalili?.

Shigowarsa falon yasa Hussaina saurin yin shiru ta haɗiye sauran gulmar da take faɗama Mommy. Sai dai kuma yama riga yajita, kallon daya watsa mata yasa tai saurin barin falon tana tura baki gaba.
“Shareff kai dawa kaje gidan Halima!!”. Mommy ta faɗa a fusace tunkan yace mata komai. Ɗan jimm yayi na wasu sakanni, sai kuma ya ɗago yaɗan dubeta. “Mommy ni ban shiga gidanba ma balle naje da wani”. Harara ta watsa masa. “Wlhy Al-Mustapha ka kiyayeni a gidannan. Idan kace zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai bazakajita da daɗi ba! Yanzu na kiraka nace kasata a napep ta dawo shine danka rainani ka ɗauketa kukaje wajen wadda ke shirin zama matarka har kana mata walaƙanci a gabanta ko?! Ita kuma shegiyan yarinyar mai kama da ifiritin aljanu haihuwar bakwaini tana mata rashin kunya, to idanma wani abune a ranta tun wuri ta fiddashi dan har abada bazan haɗa zuri'a da Usman ba, sunga ta rasa miji a can shine zasu kwasota su kawo nan talla......”. Murmushin yay da tasowa ya dawo kusa da ita, sai dai a ƙasan carpet ya zauna ya ɗora kansa jikin ƙafarta, hanunta ya riƙo cikin nasa murya a sanyaye, “First-luv Please cool down, yaronki bashi da wata mata bayan zaɓinki, idan ma hakane a ransu ai bani kaɗai bane ɗa a gidan ko?!.....”
“Ko kai kaɗaine bazaka aureta ba, kuma ko yanzu dan kayi aure idanma hakane a ransu Maheer ma yafi ƙarfin nan sai dai suje can su nema mata miji dan ko Khaleel saina hana uwarsa yarda”.
Murmushi ya saki mai faɗi da lumshe idanunsa. Yayinda kunensa ke cigaba da sauraren banbamin masifar Mommy. A haka su Aysha suka shigo suka samesu. Gaisuwar da suke masa ce ta sashi buɗe ido da tashi daga jikin Mommy yana kallonsu. Kafinma yace wani abu Hassan yay saurin faɗin, “Yaya daga aikan Gwaggo muke fa”. Komai baiceba ya miƙe ya fita a falon.

___________________

A yau da Anam ke cika kwanaki biyar a gidan ya kamata ta fara shirin fita aiki, amma mutuniyarku barcinta take sharɓa saboda jin daɗin ɗan sanyi-sanyin safiyar dan bata isashen barcin dare daboda zafi. Da zarar an ɗauke wuta bazata sake rintsawaba. Dan ƴar fan ɗin da Mom ta bata Fawwaz ya joganeta jiya taƙi ɗaukar caji. Gaba ɗaya Mom ta shafa'a da batun fara fitar Anam ɗin yau itama, shiyyasa batai tunanin tadata ba tanata ƙoƙarin shirya su Fawwaz karsu makara tafiya makaranta suma. Sai daga baya ta tuna taje ta kakkaɓeta da ƙyar..

Kamar kullum cikin shirin fita office ya fito. Shareff mutum ne mai himma, bashi da wasa akan aikinsa shiyyasa a kullum cikin haɓaka kamfani yake. Zamansa tsayayyen mutum yasa ma'aikatan ke tsananin shakkarsa da kiyaye dokokin kamfani, dan shi babu ruwansa yana ganin baka serious zai sallameka ne acewarsa a kwai dubu masu buƙatar gurbinka zaune a gida. Sashen Mommy ya fara shiga, ƙanensa nata ƙoƙarin karyawa suma. Cikin girmamawa duk suka gaidashi. Amsawa yay yana ƙoƙarin kaiwa zaune a ɗaya daga kujerun falon dan bazaka taɓa ganinsa cikinsu yana cin abinciba. Mommy dake tsaye itama a dining ɗin tana haɗa masa tea ta ƙaraso garesa. Tunkan ta ƙaraso ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mug ɗin. “Good morning First-luv”.
“Morning dear, how are you?”.
“Alhamdulillahi”.
“Haka ake so ai. A saka maka Irish ɗin?”.
“No Mommy wannan ɗin ma is ok for me. Yau na makara gashi inada meeting eight thirty”.
“To aiko gara ka hanzarta tunda gashi eight ɗin gab yake dayi”.

Koda ya fito sashen Mommy wajen aunty Amarya ya shiga suka gaisa kamar yanda ya saba duk safiyar duniya zai shiga ya gaida kowa na gidan. Daga nan kuma babu mai sake ganinsa sai wata safiyar, sai dai duk ranakun juma'a da laraba zai sayo fruit bayan ya tashi aiki ya shiga kowane sashe yakai musu, hakama duk ƙarshen wata zai sayi kayan tea dasu sabulai omo MacLean kayan dai buƙata kananu yakai kowane sashe. Tun Mommy najin haushi da masa faɗa har dai ta tattara ta zuba masa ido amma hakan na damunta da ɓata ranta saboda zugar Gwaggo. Sashen Gwaggo ya nufa itama ya gaisheta dan itace a tsakiyar Mom da aunty amarya. Yasanta da son su zauna hira dan haka ya maƙale daga ƙofa suka gaisa duk da tayin kunun gyaɗa da take masa kuma ransa naso.
“Gwaggo na makara, amma zubamin zanje da shi office nasha. Bara na gaida Mom a kaimin mota”.
Kafinma tace wani abu ya fice da sauri zuwa sashen Mom idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Gaisuwar su Fawwaz ya fara amsawa dake fita da gudu zuwa school bus ɗinsu. Kafin ya ƙarasa cikin falon su gaisa da Mom. Itama nan koda tai masa tayin abinci cayay Alhmdllhi ya fito da hanzari. A jikin motarsa ya samu Ladi mai aikin Gwaggo ɗauke da ƙaramin basket. Tunkafin ya ƙaraso ya buɗe motar da key tai ƴar ƙara. “Ranka ya daɗe gashi inji Gwaggo”. Baice komaiba ya amsa basket ya ajiye a gefen mai zaman banza, fitowar Daddy ta dakatar da shi daga yunƙurin shiga motar da yay niyya ya nufi Daddyn ɗin duk da sun gaisa bayan fitowarsu massalaci da asuba, tare kuma suka fita motsa jiki....
“Babana har an fito?”.
“Eh Daddy nama so makara dan inada meeting”.
“To ai yau da gobe sai ALLAH ko”. Daddy ya faɗa dai-dai da fitowar Anam daga sashen Mom. Tsaf take shirya cikin kayan NYSE da sukaima jikinta cif kamar ka saceta ka gudu. Ta naɗa yololon veil ɗinta tare da ɗora p-cap ɗin samansa, saita goya bag ɗinta mai suffar teddy data zuba komai a ciki. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufo inda suke, sai da ta sauke hular daga kanta tace, “Good Morning Daddy”.
“Good Morning Maman Daddy. how are you?”.
“I'm fine Daddy, sai dai zafi da dare barci babu daɗi”.
“Ayya mamana ba'akwai fan a ɗakin naku ba?”.
“Akwai Daddy, idan suka ɗauke nepa ɗinne fa, fan ɗin da Mom ta bani yaƙi ɗaukan cagi jiya”.
Kanta ya ɗan shafa da faɗin, “Am sorry insha ALLAH za'a saya miki wata to koda an ɗauke wutan, koma ac za'a sayo dai?”.
Ƴar dariya tayi da satar kallon Shareff da tun zuwanta wajen ya haɗe fuska yana danna waya kamar bai san da zuwan nata ba. Shima Daddyn dariya yay da duban Shareff ɗin, “Kun gaisa da Yayan naki ko?”.
Baki taɗan tura gaba da ɓata fuska, sannan tace, “Good morning”.
Duk da sarai yajita bai amsaba, sai duban Daddy yay yana tura wayarsa a aljihu da faɗin, “Daddy bara na wuce ina ƙara makara”.
Daddy yace, “Ato shikenan sai kije ya saukeki tunda hanyarsa ce”.
Idanu ta waro da ƙyau tana ƙyaƙyƙyafta su. “Daddy Abie yace driver zai dinga kaini”.
“No na dakatar da shi ai. Duk motocin gidan nan ace sai an ɗauka miki wani driver. Idan Shareff zai fita sai ya dinga tafiya dake, idan ya tashi aiki kuma ya ɗakkoki ba shike nan ba”.
Zatai magana ya girgiza mata kai alamar kartace komai. Shirun kuwa tai, sai dai kamar zatai kuka takeji. Sam bata buƙatar haɗa sabgarta da shi. Duk miskilancin Khaleel tafi jin daɗin zama da shi, shiko Maheer dama mutum ne mai sauƙin kai da faran-faran, shiyyasa da akace mata bayanan taji duk babu daɗi.
Ganin shima baice komai ba Daddy ya dubesa “To ALLAH ya bada sa'a. Sai ka wuce da Mamana ko”. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan rissinar da kansa ƙasa da fadin. “Mu yini lafiya”. Jinjina masa kai shima Daddyn yayi. “ALLAH yasa. Mamana bishi ALLAH ya bada sa'a”. “Amin Daddy” ta faɗa dabin bayan Shareff da tuni yay gaba abinsa kamar ta make masa ƙeya..........✍

_🤭🤗maza ki make to dan ALLAH_.


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_07_*


.........Tunda suka tafi tsakanin shi da ita babu wanda yayma ɗan uwansa magana. Yanata tuƙinsa da amsa wayoyi itako tana buga game a wayarta cike da nishaɗi har suka iso. Motar ta buɗe tai ficewarta tana taɓe baki, sai da ta rufe masa ƙofar batare data kallesaba tace, “Jazakallahu khairan” tai gaba abinta. Fusgar motar yay da ƙarfi yay gaba har yana tada ƙura. Hakan yasata faɗin, “Kaji dashi in kayane dai”.

Koda ya tashi a aiki baibi takanta ba yay wucewarsa gida. Tun Anam na jira da marmari har ranta ya fara ƙuna gashi bata sayi layin Nigeria ba har yanzun. Sosai ranta yake a ɓace ga yunwa dake bala'in cin hanjinta dan bawani abun kirki taci da safeba ta fito, da rana ko inibi data taho dashi a bag kawai tasha da strawberry. Ganin yamma na ƙara mata, gashi bata san yanda zata kira wani a gidan ba tunda babu waya ta fito domin samun abun hawa ko zata iya ganewa. Ga wani irin zafi dake ratsata duk da rana ta risina kasancewar anyi la'asar, sai dai ita zafi takeji matuƙa kodan inda ta fito akwai ac ne.
Ta tare abin hawa yafi sau huɗu amma ta rasa yanda zata musu misalin anguwar, wasuma basa gane jagulalliyar hausarta da yaren malay ya cinye, turancin ma idan tayi wasu suce basaji wasu suce basu fahimci kwatancenta ba. Kanta ta dafe ƙwalla na cika mata ido dajin wani irin tsanarsa a cikin ranta, tabbas bata ƙaunar wulaƙanci shiyyasa bata wulaƙanta kowa, kai bama ta tashi taga iyayenta na wulaƙanta wani ba kowa abin girmamawarsu ne koda bai kaisu wani matsayi na duniya ba. Hannu takai a hankali ta share ƙwallar idanunta tana maijin kewar iyayenta da ƙaunarsu, waɗannan matsalolin na ɗaya daga cikin abinda ta guda a zuwanta hidimar ƙasa Nigeria, amma su Mamie suka kasa fahimtarta.......
Harya gota ta ya dawo baya da mamakin kodai gizo idonsa ke masa. Dai-dai saitin da take yay parking da sauke gilashin motar. Tabbas itace inhar bai ruɗeba, dan yanda yarinyar ta shiga ransa bayajin zai manta fuskarta koda a barci ya tashi.
“Beauty!”.
Ya faɗa cikin tsantseni da taraddadin wasiwasi.
Duk da tajisa tunma tsayuwarsa hakan baisa ta ɗago ba. Sai ma sake haɗe fuska da tai ta ɗauke kai gefe fiye da yanda ya sameta. Murmushi ya saki dan yanda tai ɗin ya tabbatar masa ita ɗince. Buɗe motar yay cike da farin ciki ya fito. “A gafarce ni. Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Duk da bata saki fuska ba ta amsa masa. Ya koma ta gabanta cikin sake raunana murya. “Inaji a jikina ke rabonace Beauty. Ranar Yayanki ko saurayinki ne ban saniba ya gudumin dake gashi yau ALLAH ya haɗamu daga ni sai k”. Karon farko ta ɗan ɗago ta dubesa, ya sakar mata murmushi. “Dan ALLAH kar kice baki ganeni ba”.
“Bamma taɓa ganinka ba”.
Ta faɗa da ƙoƙarin barin wajen. Sauri bin bayanta yay. “Please dan ALLAH karkimin haka. Ni ne wanda muka taɓa haɗuwa a GJ restaurant da daddare”. Sarai ta ganesa tun kiranta Beauty da yay dan muryarsa bata bace mata ba. Amma sai ta sake ɓata fuska aɗan fusace tace, “Bani bace Please kabar bina”.
“Kiyi haƙuri bazan iya daina binki ba wlhy dan kullum cikin addu'a da sadaka nake akan ALLAH ya sake nunamin ke. Ya kuma amsamin sai nayi sakaci da damata”.
Sosai ya bata dariya a wannan gaɓar, wai sadaka. Dan kawai ya ganta zaiyi sadaka. Hararsa tai zata sake wucesa ya babbake ko'ina. “Dan ALLAH ki saurareni”. Kanta ta dafe dan yanata faman haɗata da abinda bazata iya jayayya ba. Hakan yasa dole ta nutsu ta sauraresa. Bawata magana sukaiba damar kaita gida kawai ya nema. Bata da mafitar data wuce binsa, amma maimakon gida da yace zai kaita sai kawai ta buƙaci ya kaita inda zata sai layin waya. Bai musa mataba, dan a ganinsa hakanma wata damace.
Kai tsaye office ɗin mtn dake cikin wata plaza yakaita duk da yasan sun tashi aiki yanzu. Sai dai yanada alfarmar da za'a iya biya mata buƙatarta a wajen. Ilai kuwa tarba ta mutuntawa taga ana masa a wajen, yanda kuma suke gaisuwa da ogan wajen taji a ranta ɗan uwansane ko aboki.
“Mutumina wannan ƴar shilar fa haka?”.
Abokin ya tambaya cike da shaƙiyanci cikin zaurancen hausa da Anam ta kasa gane komai dan shima ya fahimci bata iya hausan ba, saboda yanda yay mata tambaya da hausa ta gagara bashi amsa mai ƙyau. Dole suka koma magana da turanci. Murmushi kawai yay batare daya bashi amsaba, sai ma danna waya da yake faman yi abinsa.
“Wai ka zama kurma ne?”.
Abokin ya sake tambaya yana harararsa.
“Sarai ina jinka. Kai dai yi aikinka kawai ba buƙatar tambayar ne”.
Dariya kawai abokin yay ya cigaba da ƙoƙarin ɗaukar Anam hoto. Tun a gurin ta ɗora layin akan wayarta, ta kuma tambayesu ko zata iya amfani da shi. Kasancewar abokin nasa babban ma'aikaci sai ya amshi wayar yay ƴan danne-danne ya miƙa mata. “Indai kiran gaggawa kike sonyi da shi bashi nan da mintuna talatin sai kiyi”.
Godiya ta masa tare da duban saurayin da har yanzu ko sunansa bata sani ba. “Zamu iya tafiya?”.
“Why note Beauty”.
Ɗan murmushi kawai tai da mikewa. Shima ya bama abokin nasa hannu suka cafke. “Friend ina zuwa ka jirani Please ”.
“Ba damuwa”.
Cewar abokin nasa yana dariya.

Ganin sun ɗan gota plaza ɗin tace su ɗan tsaya mintuna talatin ɗin su cika. Bai musaba sai dai ya kalla agogonsa duk gudun kar lokacin salla ya shiga. “Beauty inaga muɗan matsa gaba akwai massallaci sai na shiga nai magrib ko”.
“Babu damuwa”.
Ta faɗa hankalinta akan wayarta. Tun fitarsa a motar babu abinda take sai irga mintuna har ALLAH yasa suka cika. Kai tsaye number ɗin Abie tahau gwadawa dan ta loda kati daga kuɗinta na bank a ciki. Taƙi samunsa saboda network. Komawa tai kan Mamie itama dai yaƙi tafiya kiran. A take idanunta suka sake cika da ƙwalla, ta kife kanta a gwiwarta tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki. A haka ya dawo ya sameta. Sai dai tanajinsa tai azamar goge hawayen nata ta haɗiye kukan.
“Beauty ina muka dosa yanzu kenan?”.
“Abinda nake tunani kenan, dan kona maka kwatance ba lallai ka gane ba. Amma in ban takurakaba ka kaini restaurant ɗin nan kawai ka ajiye zan samu mafita”.
Kallonta kawai yake cike da nazari. “Na miki wani tambaya mana in bazaki damu ba?”.
Shiru kamar bazata amsashi ba. Sai kuma taja numfashi da jinjina masa kanta. Gyara zamansa yay sosai yana fuskantarta. “Harshenki ya tabbatar min idan ma ke ƴar Nigeria ce ba'anan kike rayuwa ba? Hakan na nufin ke baƙuwace shiyyasa bazaki iya gane inda zakije ba?”.
Nanma kamar bazata amsashi ba sai kuma ta ɗan kallesa ta duƙar dakai. “Karka damu ka kaini inda nace kawai Please”.
“Baki son na sani ko?”.
“No, kawai”.
Ta faɗa a taƙaice. Bai sake magana ba ya ɗan rausayar da kansa da yima motar key yana murmushi.

Koda suka iso kamar yanda ta buƙaci ya tafi ya barta a wajen bai yarda yayi haka ba. Cikin lallashi ya sata suka shiga wajen. Yabi ya takura mata akan ta faɗi mi take son ci amma taƙi, dan Anam nada wani hali inhar bata saba da kai ba bata taɓa yarda ta sake da kai. Shi kansa badan tana neman mafitaba bazata bisaba tun farko ko wane irin naci zai mata kuwa. Haƙura yay ya amsar musu drinks kawai da snacks amma ko kallon natan bataiba balle yasan zataci.
Tunanin kiran Aysha ne yazo mata a rai. Ta sake zaro wayarta dake cikin bag ta hau lalubenta. Cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, sai dai harya katse ba'a ɗaga ba. Bata gajiba ta cigaba da kira har wajen 8missed call amma babu amsa. Da ƙyar ta iya ƙoƙarin danne kukan dake son taho mata......

_______________________

Ko kaɗan baiyi tunanin bazata iya maido kanta gida ba. Hasalima zuciyarsa raya masa take tuni ta dawo ɗin saboda yayi over time a office yau yana aiki, ga kansa na masa ciwo. Daya shigo gidan ma a ɗan gurguje ya shiga suka gaisa da Mommy ya fito. Wanka yayi a gaggauce shima saboda magrib dake kusantowa. Koda ya kammala shiri ya fito a compound ya haɗu da Abbah da Khaleel suma zasu massallaci. Tare suka fice, bayan an idar da magrib basu dawo gidaba sukai zaman jiran isha'i....

Tun kafin su ƙaraso suka hango Mom da Aunty Amarya tsaye cirko-cirko a ƙofar sashen aunty Amaryar. Dukansu sai suka nufi can dan da alama babu lafiya. Shidai kusan shine ƙarshe dama. Daddy da suka haɗu a massallacin ne ya fara jefama su aunty amarya tambayar “Lafiya kuke tsaye anan haka?”. Aunty amarya ta bashi amsa cikin damuwa da ruɗani. “Daddyn Shareff lafiya ba lafiya ba. Anam ce bata dawo gidaba har yanzun. Mubarak yaje har wajen aikin nata kuma maigadi ya tabbatar masa babu kowa a ciki ita ɗincema kusan ƙarshen fita, ta kuma jima a titi kafin yaga wani ya ɗauketa a mota”.
“Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un”. Daddy da Abba suka faɗa kusan a tare. Shareff ma dake daga bayansu gabansa ne ya faɗi, suka haɗa ido da Daddy daya juyo yana masa kallon tuhuma. cikin son danne abinda keson taso masa yace, “Shareff nasan dai kaji mi mamarku ta faɗa ina ka baromin yarinya?”.
Sosai ƙirjinsa ke luguden duka. Ya girgiza kansa da risinar da idanunsa da sukai sirkin ja kaɗan saboda gajiya da ciwon kai.
“Ba girgizamin kai zakaiba ka buɗe baki kai magana!!”. Daddy ya sake faɗa a tsawace.
Kansa a ƙasa yace, “Ban baro office ba sai kusan 6, shiyyasa nai tunanin ta dawo gida”.
“Shareff are you out of your senses?!! Har kake gayamin kazata tama dawo gida. Kana da hankali kuwa? Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”.


Please Login or Register in order to submit comment