Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nafisa?”.
Muryar Daddy da basuyi zato ko sanin yana biye da su ba ta karaɗe kunnunwansu, ya dakatar da Mommy dake ƙoƙarin juyawa ga Shareff da mutuwar tsaye ta samesa sakamakon marin da Mahaifiyarsu ta sakarma ɗan uwansa na bazata
“Nafisa! Wai miyasa akoda yaushe kike son nuna ƙarfin iko akan ƴaƴanki wajen wargazamin zuri'ata? To bara kiji, na rantse da ALLAH, daga ranar da tunanin ƴaƴanki ya fara sauyawa zuwa shiga hurumin zumincina da ɗan uwana ko iyalinsa kamar yanda kike ƙoƙarin yi, zan tabbatar da shigarki nadama irin wadda bakiyi tsammani ba daga gareni. Idan kuma kinaga bazan iyaba saboda ɗaga miki kafa danai na tsahon shekaru ku ku gwada aikatawa ku gani”. Ya ƙare maganar da nuna su Shareff cikin tsananin ɓacin rai tare da juyawa ya fice batare da ya jira cewar waninsu ba.
Daga ita har su da kallo suka bishi. Wani irin ɓacin rai na nuna kansa a fuskar Mommy. Ta watsama su Maheer wani mugun kallo batare data sake cewa komaiba itama tabar falon. Da kallon dai itama suka bita harta shige, Yaya Shareff ya sauke nannauyan numfashi da maida kallonsa ga Maheer, kafaɗarsa ya ɗan bubbuga alamar lallashi, dan fuskarsa duk tayi sayin yatsun Mummy.
Cikin ɗacin murya Maheer dake kallon yayan nasa ya ce, “Amma Yaya Mommy......”
Kai ya jinjina masa alamar baya son jin komai, ya ɗan ƙara bubbuga kafaɗarsa tare da ɗan hugging nashi ta gefe sannan ya fice. Maheer ya bisa da kallo....
Mommy da duk ke tsaye a bakin ƙofarta tana kallonsu tai ƙwafa. A ranta kuwa babu abinda take ƙullawa sai tabbatarma Daddy bataji maganarsa ba. Dan kuwa ko ana ha maza ha mata sai ta tabbatar da ƙiyayyar maƙiyanta a zuciyar ƴaƴanta ya jima baiyi abibda ya ɗauka alwashin ba. Iyaka dai yace ya saketa ko! To sai me, ko rabuwa tai da shi ta san yanzu Shareff da Maheer sun taka matsayin da zasu iya riƙe rayuwarta fiye da shi. Hussaina dake daga ɗakinsu tana sauraren komai itama ta ƙwalama kira, da sauri ta iso tana faɗin, “Gani Mommy”.
“Ki bimun Yayanku kiga ya tafine ko ya koma can gidan”.
“Okay Mommy”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa. Maheer ma yabar falon, dan haka ta fita da saurinta sai dai kuma dole tayo baya ta ɓuya dan hango yayun nata a tare. Yaya Shareff na waya ne, sai Maheer tsaye a gefensa alamar jira yake ya kammala.
Wayar ya sauke bayan yayi sallama da Dr Jamal. “Miya faru kuma?”. Ya faɗa cikin kafe Maheer da idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya. Shima Maheer ɗin kallonsa yake rai ɓace. “Ni zanje na ƙara duba Anam yanzu, dan bazan iya ƙinyin hakanba gaskiya”.
Wani irin murmushi da Maheer ya kasa bama fassara Shareff ya saki, sai kuma ya ɗago yana dubansa cikin ido “Brother be careful!”. Ya faɗa murmushin fuskar tasa na ɓacewa.
Da kallo mai ƙara harzuƙa zuciya Maheer ya bi Yayan nasa, dan tuni harya bar wajen ya nufi gate. Cikin dakewa itama Hussaina tazo ta wuce sa kamar aikenta akai, a mota ta samu Shareff, yana kwance cikin kujera idanunsa a lumshe, a can gefe ta ɓuya tana kallonsa, ya kai kusan mintuna goma a wajen kafin yayma motar key yabar anguwar. Juyawa tai ta koma gida, bata samu Maheer a inda ta barsa ba, dan haka takaima Mommy bayanan data aiketa. Jin Shareff bai shiga gidan su Anam ba yasa Mommy sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai dai acan ƙasan ranta ta gama shirya makaman yaƙar su Mamie ta yanda inhar suka tashi tafiya sai sun wuce da ƴarsu wucewar da har abada bazata sake leƙo Nigeria ba balle ta raɓu mata ƴaƴa.

★★★

Duk da ta faɗama Mommy damuwarta hankalinta bai kwanta ba. Sai faman kaikawo take na neman mafita. Zuciyarta ce ta bata shawarar kiran biyu daga cikin ƙawayenta da tafi aminta da su. Cikin sa'a kuwa dukta samesu, umarnin suzo gareta ta bada kai tsaye kai kace itaɗin haihuwarsu tai. Babu ko wanda ya musa mata saima tabbatarwa kafin mintuna shafiyar data basu zasu iso.
Hakan kuwa akai, dan mintuna goma sha biyu bai gama cika cif ba Sima da Amal suka iso. Amal da Sima ƴaƴan talakawane fitik, sun haɗune da Fadwa a media. Komai tayi a shafinta na istagram cikin yabonta da mata Comments suke, idan wani ya zageta zasu haƙiƙice wajen kareta koda kuwa akan gaskiya aka zagetan. Waɗan nan garkuwa da suka dinga bata yasa ta fara kulasu har takai da sun haɗu a zahirin rayuwa. Da farko ganin su ba ƴaƴan kowa bane yaso sakata ja baya da su, sai kuma hakan ya gagara dan suna taka rawar gani a duniyarta ta yanar gizo sosai. Dole ta buɗe bakin aljihu wajen gyara su Sima ɗin ta hanyar siya musu kayayyakin sawa da kaisu wajejen gyaran jiki na manyan yara. Maimakon ƙananun man bleaching da suke shafawa saita ɗaurasu akan manyan harka masu tsada, dan ita Amal ma allura akai mata. Cikin ƙanƙanin lokaci ta canja musu rayuwa suka fara karo da manyan yara. Fadwa nada wasu ƙawayen bayan su Sima dan ita macece mai yawan kwashe-kwashen ƙawaye, ita da mafi yawan ƙawayenta sunyi matuƙar suna a media musamman tiktok a yanzu dake taka rawar gani a rayuwar yaranmu. Komai na rayuwar Fadwa da ƙawayenta a bayyane yake, duk inda zasu samo location ko baground ayi vedio bai musu wahalar zuwa koda a wajen kano ne. A ɓangaren lalacewa bazamuce dukansu a lalace suke ba, dan kuwa akwai wanda a cikinsu da yawa babu ruwansu da mazan inba a ɗan ɗauka vedio ba ko abota shikenan. Fadwa na ɗaya daga cikinsu, dan tunda ta tashi Shareff kawai take gani a idanunta da soyayya. Hakan yasa duk haɗuwar namiji ko kuɗinsa bai cika zama a gabantaba inba wani abun hanunsa take buƙata ba, tana samu kuma zata watsar da shi a wuce wajen. Duk kuma tanayi cikin taka tsantsan da Shareff baisan hakan ba. Hatta harkar media ɗinta Shareff bai sani ba kasancewarsa mutum da yafi damuwa da aikinsa fiye da komai, idan ka gansa a yanar gizo akan abinda ya shafi cigaban rayuwarsane ba kalle-kallen banza ba, sai ko ganin labarai masu muhimmanci da yafi ziyartar irinsu bbc koya zauna ya kalla a talabijin ma yafi masa sauƙi. Amma a wani lokaci Fharhan ya taɓa masa shaguɓe da tsiyar da Fadwa ke tsulawa a yanar gizon harya nuna masa wani vedio. Ransa ya ɓaci matuƙa duk da iyayensune suka matsa ya auri Fadwa tun baya kulawa haryaji ya fara sonta saboda son da take masa bana wasa bane. Sosai ya mata faɗa da gargaɗi harda barazanar barin rayuwarta inhar ya sake ganin wannan shirmen banzar daga gareta. Tayi kuka da alƙawarin dainawa a lokacin har sai ta baka tausayi. Daga haka bai sake bin diddiginta ba dan baida wannan halin sam ga waninsa, ya daiyi imanin yanda yay mata insha ALLAH bazata sakeyi ɗin ba. Sai dai kuma ba hakan bane, dan kuwa ko sati biyu kasa cikawa Fadwa tai saboda ta riga ta saba, amma tabi shawarar ƙawayenta ta samu Fharhan har gida tai masa cin mutunci da gargaɗi bayan ta gano shine ya nunama Shareff vedion. Daga haka ta cigaba da harkokinta sai dai cikin taka tsantsan. A ɓangaren shaye-shaye kam basa shan komai sai shisha da yaranmu suka maida fashion a yanzun, wanda ta koyane shima wajen wata ƙawar tata har su Sima suma suka koya a wajenta...
“Baby Fady mike faruwa duk kin tada mana hankali?”.
Amal ta faɗa cikin nuna tsananin damuwa da tashin hankali.
“Miyema bai faruba Amal. Na tsaneta, na tsani yarinyarnan fiye da mutuwata amma Soulmate ya kasa fahimtar hakan. A yanda nakeji ALLAH zanfa iya kasheta ma....”
Idanu duk suka zaro na tsorata da kalamanta. Cikin girgiza kai da tarar numfashinta Sima tace, “Kinga nutsu kimana bayani yanda zamu gane Please. Wacece? Miye haɗinta da mijinki kuma da har ya kasa fahimtarki?”.
Maimakon amsa saita fashe musu da kuka. Hankalinsu sake tashi yayi, suka zagayeta suna lallashi. Sai da tayi mai isarta sannan ta fara basu labari. Da farko sun yabama salonta na kissing mijinta gaban Anam. Daga ƙarshe suka nuna tsantsar takaicinsu da biyema yarinyar da su Shareff sukai na yarda da wai taji ciwo.
Sima tai murmushi tana kaɗa kai da taune lips. “Karku damu inada shawara, wadda nasan inhar kika bita Fady har abada yarinyarnan sai ta fita rayuwarki, nifa tun randa muka haɗu da itan nan a Saloon tare da shi nasan yarinyarnan ba ƙaramar ƴar bariki bace, sai da kika sake sanarmin haihuwar turai ce tashin can na ƙara tabbatar da e lallai hasashena nakan hanya ashe. To a wannan karon aurensa kike, dolene kiyi komai domin ki rabata da mijinki dama hanyar gidanki gaba ɗaya......”
“Nifa wannan dogon bayanin naki ya isheni Sima. Dan ALLAH ki faɗa kawai ina saurarenki”.
“Hhhh daɗina dake wutar ciki Baby Fady. Kwantar da hankalinki, indai dan wannan yarinyar ce mai kama da ƴar tsanar roba kisa a ranki zamaninta ya shafe a duniyarki zo muje daga ciki”.
Bedroom ɗinta suka shige, suka shiga famfata tako ina. Sun ɗauka kusan mintuna arba'in kafin su fito fuskarta washar da murmushi kamar ba'itace a birkice ɗazun ba. Ganin har lokacin Shareff bai dawoba ta sakasu su gyara mata gidan. Duk da yanda ta sakasu aikin cikin bada umarni ya sosa musu rai haka suka zage suka hau mata gyaran lungu da saƙo, itako tana zaune a falo tana duba Comments na sabon posting da tai ɗazun a tiktok kafin su Anam suzo. Dan danan ko ina ya ɗau ƙamshi. Ta nuna musu jin daɗinta, amma duk da haka sai ta sakasu su mata girkin dare kuma tare da gyaro sashen Shareff. Kowacce da hanzari ta amsa ita zata gyara sashen Shareff ɗin. Hararsu ta shiga yi, sai dai kuma batare komaiba.
Da sauri Amal ta waske da faɗin, “Na fahimci kowa girkinne bayaso, to muyi girkin tare aje a gyara can ɗin tare”. Sima tace, “To hakan yafi kam”. Sai a lokacin Fadwa tai dariya da faɗin, “Duk zame-zamenkun dai sai kunyi, inba hakaba na fasa sayen ashoben Meerah ɗin”.
Suma dariyar suka shigayi da faɗin ai ba'ayi hakaba duk zasuyi. Hakan kuwace ta kasance. Sukai mata girki tare da gyaro sashen mijinta batare da hakan ya dameta ba. Dan hatta bedroom da toilet saida suka gyaro masa. Tsakar gida kuwa dama maigadi ke sharesa fes shiyyasa da wahala kaga datti. Ganin magrib ta kusa ta basu kuɗin ankon datai alƙawari da cewa su tafi mijinta ya kusa dawowa bata bukatar ya dawo ya gansu. Basuce mata komai ba akan hakan sai dariya da sukayi kawai, tai musu rakkiya har gate suka wuce.

Shawarar da suka bata ce ta sata goge duk wani ɓacin ranta har na rashin dawowar Shareff gidan har yanzu. Wanka tayi tare da tsara kwalliya mai ma'ana. Ta tsuke cikin wandon jeans da top da sukai matuƙar fidda ainahin ƙyawunta da ƙyawun sura. Kamar yanda gidan ke kamshi itama kamshin take bulalawa. Ganin yanda tai ƙyau saida tai ɗan shot video tare da bin waƙar da akafi yawan challenge akanta a yanzu ta ɗaura a shafinta na tiktok da istagram. Ita ɗin mai followers ce, cikin ƙanƙanin lokaci likes ɗinta suka fara hauhawa, video ɗin ya fara trending ko'ina kamar ita kaɗaice ke lokaci. Sosai farin ciki ya mamayeta damuwarta ta ƙara gogewa baki daya musamman da ƴan koranta na kusa suna koɗata da zafafan Comments. Yayinda masu kishi da ita da ganin ta fisu suka fara jefa Comments na baƙar magana harda masu zagi, a gefe masu gaya mata gaskiya na jeho nasu akan ya kamata ta rage yin video da ƙananun kaya da gashi a buɗe kodan igiyoyin aure dake a kanta a halin yanzun. Su Sima ne suka taƙarƙare wajen maida murtani ga masu irin wannan Comments da masu zaginta, itako sai ma ta kashe datar acewarta sai Comments ɗin sun taru zatazo ta duba....

★★★

Ɓacin ran jin asalin abinda ya faru daga bakin Anam duk da bashi take faɗawa ba da tabbacin Fadwa ce ta kira Mommy ta sanar mata wannan Accident ɗin ya hanashi komawa gida. Dan ya tabbatar in har ya koma a yanayin da yake zai iya yanke mata kowanne irin hukunci da yazo masa a rai. A yanzu kuma baya buƙatar haka a garesu, dan bazai so ace daga yin aure sati ɗaya kwana biyar da tarewa hakan ya fara faruwa ba. Office ya wuce kai tsaye, inda Fharhan da Khaleel sukai mamakin ganinsa tunda sun san duk wani abinda zai iya kawosa office ɗin sun kai masa shi har gida ya duba.
Ko gaisuwar da sakatariyarsa ke masa bai amsa ba, hannu kawai ya ɗan ɗaga mata duk da washe baki da take faman yi da tayasa murnar aurensa. Har ya kama handle ɗin ƙofar office ɗinsa zai shige ya juyo. “Bana bukatar kowa yasan ina nan ok”.
“Yes sir”.
Ta faɗa cike da girmamawa a garesa. Shigewarsa yay harda murzama ƙofar key, bai zauna a cikin office ɗin ba ya shige ainahin ɗakin da yake gudanar da zane-zanensa. Har mafi yawan ma'aikata suka tashi babu ɗuriyarsa, Khaleel yaso shiga ya dubasa sai kuma ya fasa saboda tun bayan shigiwarsa ya biyo bayansa amma sakatariya ta sanar masa yace baya bukatar kowa.
Kiran sallar magrib ya sashi fitowa, shiru companyn alamar kowa ya tafi gida, sai masu gadi su biyu kawai dake gate. Nan ya tsaya yay salla tare da su a massallacin dake cikin company ɗin sannan ya fito. Harya ɗauka hanyar gidansa ya canja, gidansu ya nufa, sai dai kai tsaye a gate ɗin gidan su Anam yay horn, mai gadi ya buɗe masa ya shige.

Duk suna falo gaba ɗaya zagaye da Anam dake faman rakin za'a gasa mata ƙafa da ruwan zafi. Taƙi yarda Mamie tai mata hakama aunty Mimi da suka dawo ɗazun. Amrah ce ta kira Abie, isowar Abie ɗin kusan dai-dai da shigowarsa, kusan su duka suka juya suna kallonsa da amsa masa sallamar da yayi. Cikin girmamawa ya rissina ya gaida Abie da Mamie, aunty Mimi ma suka gaisa.
Tun shigowarsa ta ƙara ƙarfin kukanta, takuma ƙi yarda tako kalli sashin da yake. Haushinsa takeji sosai batare da tasan dalili ba. Takaici ya saka Mamie daka mata tsawa..
“Wai wane kalar iskanci ne hakan Anam? Shin ke ɗin ƙaramar yarinyace da kowa zaita fama dake akan abinda zai amfaneki.....”
Da ido Abie yay mata alamar tayi haƙuri, ta ɗauke kai da ƙoƙarin barin wajen cikin takaicin ƴar tata. Abie yay murmushi da maida kallonsa ga Shareff da ke faman daƙilar waya kamar bai san abinda ake a falon ba, sake kallon Anam ɗin yayi cikin sigar lallashi “Mamana to Yayanki yay miki ko?”.
Da sauri ta ɗago tana girgiza kanta, “Garama kowa yamin akan shi yamin Abie”. Ta faɗa cikin zafi-zafi da share hawayenta. Amrah ta taɓe baki da barin wajen, yayinda aunty Mimi da Abie ke dariya.
“To saboda mi baki son nashi? Bayan tun ɗazu muke nan ana fama dake ga ruwan har sun huce”.
“Aunty Mimi nidai bana so ke kimun”.
Aunty Mimi zata kai zaune Shareff da har yanzu bai nuna yasan mi suke ba ya dakatar da ita. “Aunty barta, a canja ruwan dai”. Babu musu Aunty Mimi ta bashi waje ya zauna, ruwan zafin ta ɗauka ta nufi kitchen. Anam kuwa ƙafarta ta shiga ja baya, sai dai ta kasa jan jikinta saboda table daya tokare ta. Shi dai bai kulata ba har aunty Mimi ta dawo da ruwan, Abie kuma dama yayi ficewarsa saboda wayarsa da aka kira. Ganin yanda ruwan ke turirin zafin ya ƙara ɗaga hankalin Anam, cikin marairaicewa take duban Aunty Mimi amma tai kamar bata gantaba itama.
“Ni wlhy bana son naka!!”.
Ta faɗa da ɗan ƙarfi da son sake jan jikinta baya ganin ya amshi towel babba da ƙarami a hanun aunty Mimi. Babban ya ɗaura akan cinyarsa batare da ko kallonta yayi ba, ƙafin kuma ya saka ƙaramin a ruwan zafin, ƙafar tata ya kamo takai hannu zata rike, wani mugun kallon daya sata janye hanunta babu shiri ya watsa mata,
“Idan hanunki ya sake kawowa nan saina ɓallashi shima kiyi jiyyarbaki ɗaya”.
Kamar ta rushe da kuka takeji, sai dai tayi alwashin bazata bar hakan ta faruba insha ALLAH. Yana ɗaura towel ɗin daya naɗoma ruwan akan kafarta dake kan cinyarsa alwashin nata ya zama tarihi, dan da gaske kukan ta sanya musu mai ƙarfi tana ƙanƙame ƙafar aunty mimi dake kusa da ita tana matso masa towel ɗin daga ruwan zafi.
Sosai yanda takeyi ɗin ke neman sakashi dariya, amma ya danne da ƙyar ya cigaba da daddana mata ƙafar a nutse. Ta haɗa uwar zufa kafin a gama, hatta da aunty mimi da tasha riƙo ta haɗa tata zufar dan ba riƙon wasa Anam tai mata ba. Su Amrah da kukan Anam ɗin ya sasu sake fitowa dole sun kasa daurewa sai dariya suke kwasa, aiko ta wawushi throw pillows ta shiga jifansu da shi. Duk yanda yaso daurewa kasawa yay sai da ya shiga layin ƴan dariya da Abie ma ya dawo yana yin tasa a gefe, Mamie ma dake a kitchen dariyar take kwasa dan borin Anam dabanne dana kowa.
Ba ƙaramin ƙuleta dariyarsa tayiba fiye data kowa, shi dai da baisan laifinsa ba bai bartaba sai da ruwan ya huce ya shafa mata man da aka bata a asibiti sannan ya saki ƙafar da kumburin har ya fara saɓewa, sai ga mutuniyar gyangyaɗi na ɗibar idonta. Da ɗan sauran murmushin da bai bar fuskarsa ba yake tambayar aunty Mimi ko taci abinci dan yana son tasha maganinta.
“Inafa taci, tunda Aysha ta kawota fa takema mutane bore a gidan nan har sai da Mamie ta mata tas. Anam ɗin ya kalla cikin ido, babu zato hararar data wullo masa ta iso garesa. Da sauri ta kauda fuskarta dan batai tunanin zai juyo ba. Abie dake kallosu a gefe yace, “Bara na maidata ɗaki sai taci abincin acan kawai ta kwanta”.
Dakatar da Abie ɗin yayi cike da girmamawa, dan bai kamata shi yana wajen ba yabarsa yay jigilar ɗaukar Anam ɗin. Cikin matuƙar zaro idanu da suɓutar baki Anam tace, “Wai Yayan ne zai ɗauke ni?”.
Harara ya wurga mata, ta kauda kai gefe cikin ƙunƙuni take faɗin, “Ni dai ALLAH bana so, garama a nemomin wheelchair........”
Ranƙwafowarsa kanta na shirin ɗaukar nata ya sata haɗiye abinda take faɗar da sauri tana ƙoƙarin zabura gefe...........✍


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko



*_ALLAH ka gafartama iyayrnmu_*😭🙏🏽[10/21, 2:25 PM] Marsy😘: *_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO.. 👉🏻AREWABOOKS🫶🏻_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_17_*


........Kasancewar Abie a wajen ya sashi ƙin cewa komai ya ɗauketa gaba ɗayanta ya haura sama aunty Mimi biye da shi. Ɗakin Mamie suka nufa kamar yanda Aunty mimi tace.
Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfin gaske lokacin da yake ajiyeta akan gado, dan tunda ya ɗakkota ta ɗauke numfashinta da rumtse idanu zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Shi ɗimma dake ƙoƙarin dannewar tashi zuciyar bugu take da gudu a ƙirjinsa har numfashinsa na seizing. Ajiyar zuciyar ya sauke tamkar ita, sai dai tasa ta fitane a ɓoye. Sallamar Mamie ta sashi haɗiye abinda ke masa kaikawo, tray ɗin hanunta ya amsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Mamie da kanki”.
Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, ta harari Anam dake kwance lamo tana sauke ajiyar zuciya. “Mai rakin tsiya yanzu waye yaji daɗin? Nikam zanga yanda zaki ƙare lokacin rainon ciki balle ranar haihuwa, mijinki dai yaga takansa ai”.
Dariya aunty Mimi ta sanya, yayinda Anam ke tura baki gaba, taɗan saci kallon Shareff sai ko idonta cikin nashi. Sosai ya sarƙeta da su, sai da ƙyar ta samu damar fisgewa tari mai alamar sarƙewar yawu na kufce mata. Wani irin yanayi data kasa bama fassara ta karanto a cikin ƙwayoyin idanunsa, hatta da tsigar jikinta yamutsawa ta shigayi, ga tarin yaƙi tsayawa har sai da Aunty Mimi ta tadata zaune tana bubbuga bayanta. Kamar ba shine sanadin komaiba cike da basarwa ya miƙama Aunty Mimi ruwan, a baki ta saka mata, sai da tasha sosai kafin tarin ya lafa idanunta har sunyi jajir. Sannu Mamie tai mata tana ƙoƙarin ficewa domin nuna kara garesu tunda dai duk suna ƙoƙarin nuna kulawa gareta bai kamata ita saita tsaya ba.
Yana daga tsaye har Aunty Mimi ta bata umarnin fara cin abinci bayan ta ɗaura mata tray ɗin akan cinyarta. A hankali ta fara cin abinci, sai ƙunƙuni take a zuciyarta na zamansa ɗakin. Oho bai san tanayi ba, dan babu alamar zai fita ɗin. Aunty Mimi ta miƙe ta fita saboda kiran mijinta daya shigo mata a waya.
Shiru ɗakin bakajin motsin komai sai na ƙarar spoon da take juyawa a plate, dan gaba ɗaya tama kasa cin abincin yanda ya kamata, tarasa mike damunta, kunyarsa ko haushinsa, dan abinda ya faru a gidanta ɗazun ya gagara barin zuciyarta. Jin shiru kamar baya ɗakin ya sata ɗan ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka sake haɗa ido. Kanta ta maida ga abincinta tana sake tsuke fuska.
(Sai kallon tsiya) ta faɗa a ranta. Kamar yaji mitake faɗa ya zura wayarsa a aljihu yana ɗan jan siririn tsaki. “Baki iya komai ba sai kallon mutane laziness”.
Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa idanunta cike da tsiwa. “Toni da baka kalleniba zaka san ina kallonka ne.....”
“What!”.
Ya faɗa cikin ɗan kausasa murya da waro idanunsa kanta sosai. “K! Wai yaushe na zama abokin wasanki ne a gidan nan?”.
Ƙin cewa komai tai, sai dai bakinta a sama kamar zai taɓo silin. A ranta ko addu'a take aunty Mimi ta dawo kafin ya fara zazzabga mata maruka. Ganin yana matsota tai saurin faɗin, “Amma matarka ɗazun datai iskanci agaban mutane baka hukuntata ba sai ni, kuma jinina da aka zubar sai na rama”. Ta ƙare maganar wasu zafafan hawaye dake nuna

Please Login or Register in order to submit comment