Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makara”.
Kai kawai ta jinjina masa. Ta watsama Fadwa harara ta juya ta fice a ɗakin. Da ƙyar Fadwa take iya amsa tambayoyin Khaleel, gaba ɗaya a birkuce take da kalaman Anam. Domin kuwa zancen Anam ɗin na nuna mata tabbas taji duk shirunsu da su Sima kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama jiƙe mata jiki. Har Khaleel ya fahimci haka ya tambayeta ko jikin ne?. Kanta ta jinjina masa cikin kaƙaro murmushi. “Kawai inaga allurar da sukai mince bata gama sakina ba barci nake ji”.
“Ayya ALLAH ya ƙara lafiya. Doctor ɗin ma yace zuwa anjima zai sallameki, inaga bara na ajiye Anam a wajen aiki karta makara zan dawo yanzun”.
Kanta kawai ta iya jinjina masa nan ma. Yana fita ta jawo wayarta cikin rawar jiki. WhatsApp ta shiga, ta haɗa group da sauri tare da adding su Siyyah a ciki. Cikin sa'a ta samu Bibah da Sima a online. Cikin bada umarni tace suyi kiran Amal da Siyyah su hau online tanada magana da su. Duk sun san tana asibiti tun jiya, sai dai basu zo ba kamar yanda suka shirya har sai ta koma gida dan karma wani ya zargi wani abu. Tsoron yin voice note wani yajita ko kiransu ya sata tafa musu duk yanda tai da Anam yanzu. Suma hankalinsu ya tashi amma duk sai suka danne kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinsa.
Maganar Sima ta sakasu duk maida hankalinsu gareta, dan zancen ya dauki hankalinsu. *Sima* _Inaga ba hankalinmu ya kamata mu tayar ba, idan ita tace kwalba ce uwar sheri sai mu nuna mata muɗin gilasai ne mun fita haɗari. Kafin ta faɗama wani zancen nan dolene mu juya komai kanta, hakan ma zai zama hanya mai sauƙi da zata bar miki gida dan koshi mijinki daba son cikin yake ba na tabbatar sai ya tsaneta._
Cikin ɗan tsumar jiki ta tafa saƙo tana tagging maganar Sima. _Kinga Sima bar zagaye-zagaye faɗi minene shirin naki kai tsaye kawai dan ALLAH_.
*Sima* _Kafin ta faɗi kin zubar da cikin mu zamu fara sanarwa itace ta zuba miki maganin zubda ciki._
*Bibah* _Ta yaya hakan zata faru tunda bamu da wata hujja Sima?!”._
*Sima* _Muko keda hujja. Doctor zamu samu ya faɗama su cikin ya zube ne ta hanyar magani da aka sha, bayan kowa ya gama ji da ɗaukar ɗumi akan maganar mai-aikinki ta tabbatar musu taga shegiyar sanda take zuba maganin. kinga sai mu samu ƙwaya asa a abinda kika sha na karshe dan ya zama shaidarmu ta biyu, yanda kowa yasan ita da iyyenta ba ƙaunarku suke ba tuni za'a yarda wlhy”_.
*Siyyah* _Woow gaskiya wannan shawaran yayi Sima. Shiyyasa kike birgeni, dan kuwa na tabbatar wannan maganar bazata zama ta wasaba. Maybe ma a kanta har sai iyayen Shareff sun maidata inda ta fito”._
A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi, jin motsin kamar za'a shigo ya sata ajiye wayar da sauri ta zame ta kwanta tana fidda numfashi ɗaɗɗaya.

★Kamar yanda suka shirya ɗin hakance ta kasance. Dan kuwa bayan dawowar Khaleel Doctor yake sanar masa bayanan bincikensu akan zubewar ciki. Hankalin Khaleel ya tashi a take ya kira Daddy a waya ya sanar masa. Cikin ƙanƙanin lokaci magana taje kunen kowa daya dace, dan haka daga asibiti gidan su Shareff aka wuce da Fadwa. Anan su Gwaggo suka tirketa da tambayoyi. Faɗa musu tai ita wlhy bata sha komai ba dan cikin ya zube. Daga dai gama shan lemo cikinta ya kama ciwo shine tace Aysha ta rakata asibiti, suna kuma zuwa Doctor yace cikin na barazanar zubewa. Yay mata allurar kariya daga hakan amma sai ba'a dace ba. Kan kowa ya kulle da zancen, daga ƙarshe Abbah ya tambayi su nawane a gidan.
Cikin kukan da take faman sharɓa ta sanar masa su huɗu da mai aiki sai maigadi a waje da Khaleel da sai dare yake zuwa, da safe kuma ya fice. Babu ɓata lokaci aka tattaro kowa har maigadi sai kulle gidan yayi. Su Anam dama daga wajen aiki nan suka yo. Kafin kowa yace komai Gwaggo Halima ta fara zazzaga masifa akan bazata yarda ba, duk wanda ya salwantar mata da jika sai inda ƙarfinta ya kare, Hakama Mommy sai kumfar baki take. Itako Gwaggo sai ta saka kuka tana kafe Anam da kallo...
Hakan yasa kowa maida hankali kan Anam ɗin. Ta nuna Anam da yatsa tana sake fashewa da kuka. “Kar ku raba ɗayan biyu yarinyar nan ce ta aikata. Lallai ilallah itace da wannan aika-aikar, tunda tana ganin Mustapha ya mata nisa shiyyasa ta ƙulla wannan sharrin na salwantar masa da ɗan tayi. Kai wannan yarinya anyi azzaluma makira, dama yaya ɗan ɗan uba zai taɓa son abokin burminsa da alkairi, dama ni dai dan kar ace an hanata zuwa ne amma naji ajikina wani abu mai muni zai faru, sai dai banyi zaton mai girma irin wannan ba........”
Abbah ya katseta da sauri cikin ɓacin rai, “Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce haka. Yaya Anam zatai wannan babban al'amarin nawa take?”.
“Eh kace haka fa, Abubakar kasan miye mace kuwa? To mace ko ƴar kwana ɗaya ce ta wuce da saninka a fanin makirci da shaiɗanci. Idan kana ganinta karama wlhy sai ta aikata maka abinda mai ɗari bazaiyiba. Kuma idan kitsa mata hakan akayi fa...”
“Wannan dai maganar bashi da amfani gaskiya a bari dai ayi bincike. Ƙilama ita Fadwan da kanta tasha abint.....”
“A'a gaskiya Yaya kar kai irin wannan yanke hukuncin. Taya za'ai ciki na jikinta ta zubar”. Gwaggo Halima ce ta katse Daddy a matuƙar harziƙe mai maganar.. Ran Daddy ya ƙara ɓaci amma sai baice komai ba yay shiru. Abba ne ya ƙara dakatar da hargowar Mommy da Gwaggo. Dole sukai shiru aka fara yima Aysha tambayoyi. Bayan ta gama bada amsa aka juya kan Anam da zuciya tazoma wuya da kalaman su Gwaggo Halima duk da ba komai take fahimta ba saboda hausa sukeyi. Tambayarta itama Abbah ya shigayi sai dai ta kasa bada amsa ko guda ta saki kuka....
“You see! Kun gani ko. Shi mara gaskiya ai ko'a ruwa jiɓi yake. Munafuka dangin tsiya wlhy ko za'a tada yaƙi bazan yarda ba”.
Mommy ce mai maganar, dan haka Daddy ya katseta a tsawace har sai da Anam ta zabura ita da su Aysha. Fadwa ta watsama mai-aikinta harara cike da gargaɗi saboda hango tsoro da firgici cikin idanunta. Ƙyale Anam Abbah yayi ya maida hankalinsa gamai aikin dan ya fahimci zuciya ce ta tokare Anam ɗin. Tiryan-tiryan yanda suka tsara mata ta faɗa. Ko haɗiyar yawu bata gama ba su Mommy suka hargitse falon da hargowa har suna kaima Anam duka da ranƙwashi sai dai Khaleel ya fara kareta. Duk yanda su Daddy suka so suyi shiru hakan ya gagara. Dole Khaleel yaja hanun Anam suka fice da sauri. Mota ya turata ya tayar yabar gidan a guje duk da kiran da Gwaggo Halima ke masa akan ya dawo da Anam ɗin bai saurareta ba..


★Kuka take sosai har numfashinta na fisga. Yayinda Khaleel ke waya da Shareff cikin bacin rai da ƙunar zuciya. Shima daga can yana jiyo shashshekar kukan Anam ɗin. Sun jima suna wayar kafin ya miƙo mata. Ƙin amsa tai sai da Khaleel ya ɗaura mata akan kunne yana faɗin, “Yaya Shareff ne fa”.
“Malama amsa wayar ban son shashanci”. Ya faɗa da alamun ɓacin rai a muryarsa daga can. Amsar tayi, sai dai ta fashe masa da sabon kuka. Shiru bai sake cewa komai ba da alama dai yana saurarenta. Tsawon minti ɗaya taƙi tai shiru ya yanke wayar yana jan tsaki. Kanta ta cusa cikin ƙafafunta tare da sakin wayar ta saki wani sabon kukan. Ba sharrin su Fadwa ya sata wannan kukan ba. Zagin iyayenta da su gwaggo Halima keyi da aibanta su ne ke mata zafi. A hakan ma dan ba komai take iya ganewa ba musamman manya-manyan hausa. Tana matuƙar son iyayenta, bata ƙaunar a aibanta mata su. Amma tunda ta fara wayo ta fahimci waɗanda Abie ɗinta ke kira family nasa basu da wani buri daya wuce cin zarafinsa shi da Mamie da ita kanta dake matsayin ƴar su. Ta rasa mi iyayenta sukaima Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima haka da zafi a duniyar nan?...
Khaleel da kukanta ke ƙara ƙona zuciyarsa da takaicin su Mommy ne ya shiga lallashinta, da ƙyar ta ɗago idanunta da sukai jajir tana kallonsa. Zatai magana ya girgiza mata kai alamar tai shiru. Shirun kuwa tayi sai dai hawayenta sun kasa tsayawa. Khaleel ya miƙa mata goran ruwa dai-dai kira na shigowa wayarsa. Ganin mai kiran ya sashi ɗagawa babu ɓata lokaci ya kai kunne sa.
“Bata wayar”. Daga can aka faɗa cikin bada umarni. wayar ya sake miƙa mata. Bata musa ba ta amsa tana cire goran data sha kusan rabin ruwan cikinsa. A jajjare ta dinga sauke ajiyar zuciyar dake shiga har cikin kunensa daga can.........✍


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/26, 1:26 PM] Marsy😘: *_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_26_*


..........Gyaran murya ya ɗanyi bayan yaja wasu seconds yana sauraren yanda take sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Bazaki daina wannan kukan ba wai?”. Ya faɗa a hankali tamkar ba shi ba...
“Na daina”.
Ta bashi amsa wani kukan na sake kufce mata. A karon farko taji yayi murmushi har tana iya jiyo sautinsa a cikin kunnenta, ya ɗanja numfashi da sake sauƙaƙa muryarsa “Ya isa nace ko. Ki ɗauka ruwa ki wanke fuskarki zan ƙara kira”.
Cikin jan numfashi tace, “Nace fa na daina Yaya”. Dan haka kawai take jin daɗin yanda yake mata magana da lallashi.
“Ni banji kin dainaba ai, tunda ga hawayenki ina gani na sauka a z....” cikin sauri ya haɗiye sauran maganar da dafe goshinsa yana cije lips ɗinsa jin zai saki layi. Itama da ba wani gama fahimtar maganar tasa tai ba cikin rawar murya tace, “Yaya dan ALLAH ka faɗama Abie zan dawo Malaysia, idan nice nace zaimin faɗa shi da Mamie”.
Furzar da numfashi yayi, cikin ɗan kaurara muryarsa yace, “Bazan sanar musu ba, kuma kema karna sake naji kin sanar dasu wani abu ok”.
“Amma Yaya kag.....”
“Umarni ne ba shawara ba”. Yay saurin katseta. Baki ta tura da hararar wayar kamar yana gabanta, “To nidai bazan koma gidanka ba, sai dai na koma gidan uncle Jafar da zama (Ɗan uwan Mamie da abie ne).
“Ashe kuwa zan zane miki jiki da bulalai”.
“To ni Yaya ya kake so nayi? Sai na dinga zama inda ba'a son ganina kamar wata mara gata”.
“Waye baya son naki?”.
“Matarka mana. Kuma ALLAH idan bata fitamin a ido ba zan fito mata da ainahin kalata, dan zan koya mata hankali...”
Dariya ce ke son kufce masa, sai dai ya riƙeta ya dai saki murmushi. “Uhuyim! Ke har wata kala ce da ke ashe? To faɗamun yaya kalar taki take dan mu kiyaye ni da matata”.
“To ni ai bance kai ba”.
“A idan zaki koyama matata hankali ai dole ina ciki. Kinga gara mu kama kammu kar truth color ɗinki ta samu barin Nigeria auntynmu”.
A yanda yay maganar ya saka Anam fashewa da dariya. “Oh oh ya kaga Anam Auntyn su Yaya, gaskiya kowa zaiji a jikinsa ne, yanda kake mana mazurai nawa sai yafi ALLAH Yaya”. Sai ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya.
Kansa ya ɗan girgiza da shafawa yana sakin murmushi, yasan ta iya surutu, sai dai bata taɓa sakewa da shi ba irin haka. Sai dai yaji surutunta da wani. Ya ƙara sakin murmushi da fesar da numfashi a hankali yana lumshe idanunsa da sake lafewa cikin kujerar falon daya kasance masaukinsa. Haka kawai ya tsinci kansa cikin nishaɗi dayin wayar tasu......

Yayin da Anam da Shareff ke waya anan acan gidan Mommy ce ke neman wayarsa a fusace saboda hukuncin da Daddy ya yanke cewar Anam bazata bar gidan Shareff ɗin ba kamar yanda suka buƙata har sai ya dawo kamar yanda shima ya buƙata. Amma sai taƙi samunsa anata nuna mata waya yakeyi. Ranta ne ya ƙara ɓaci ganin mintunan dake ta ƙara tafiya amma ana sake jadadada mata ana amfani da layin. Ta tura massege babu reply. Ga Fadwa nata musu kuka ita indai Anam zata koma mata gida to ita bazata koma ba..
“Wai ni yaron nan da ubanwa ma yake waya hakane? K Hussaina jeki ki gano min Daddynku waya yakeyi”.
Miƙewa Hussaina tayi tana amsawa da to ta fice. Mintuna kaɗan ta dawo ta sanar mata ba waya yake ba, hira yakeyi ma shi da Abba.
“Kai! To da ubanwa yaron nan ke waya?”.
Kuka Fadwa ta sake fashewa da shi. “Wlhy yanzu haka shegiyar yarinyar can ce ta kirashi tana ƙulla mana sharri a wajensa. Na tsaneta, bana sonta. Idan ta koma min gida saina kasheta”.
Shigowar Gwaggo falon ya hana Gwaggo Halima da Mommy bama Fadwa amsa. Takai zaune tana murmushi idonta akan Fadwa. “In dai bazaki kiyayi gaggawa akan al'amuranki ba kuka yanzu kika fara shi. Da kinyi haƙuri kin cigaba da jiran nawa shirin da ba'akai ga haka ba. Ku kuma kun biye mata. Duk yanda kuke tunanin yarinyarnan tabar gidan Mustapha da ƙarfin tuwo bazai yuwuba, wannan kuma zancen ita ta zubda ciki da kuka ƙulla ƙara kusantata ma da gidan kukayi tunda gashi su Muhammadu sun tabbatar muku yanzuma ta fara zama. Duk wanda ya baku shawarar juya zancen zubewar ciki da ita ta zubar ya baku gurguwar shawara ne ga tabbaci kun gani”.
Mommy da takai zaune cikin sanyin jiki da maganganun Gwaggo ta dubi Gwaggo Halima. “Maganar Gwaggo haka take Halima. Munyi kuskure nima na fahimta. Da Fadwa ta sanar mana zatai hakan ya kamata mu dakatar da ita mu fara yin nazari, tare da bincikarta wanda ya bata shawarar yin hakan tunda mun san zubewar cikinta bashi da alaƙa da yarinyar da gaske”.
Itama Gwaggo Halimar ajiyar zuciyar ta sauke. Sai kuma ta jinjina kanta, “Hakane Gwaggo anyi kuskure, ba kuma kowa ya jawo hakan ba sai Fadwa da shegen gaggawarta. Na faɗa mata ta kwantar da hankalinta mu jira naki shirin amma rashin haƙuri yasata yanke wannan hukuncin. Gashi yanzu bai haifar da ɗa mai ido ba tunda abinda take son yay nesa da ita da mijin nata damu baki ɗaya bai tabbata ba. Kuma tabbas zaman yarinyar nan cikinmu ba alkairi bane, na tabbatar yanda bamu ƙaunar ubanta shima bazai taɓa son mu ba, amma ya kawota cikinmu saboda sharri irin na ɗan uba da baka ganesa sai ALLAH kawai. Gwaggo kiyi haƙuri, yanzu minene mafita?”.
Baki Gwaggo ta taɓe. “Toni mizance yanzu kuma. Nawa shirin ma ai kun ruguza da shirmen ƴarku. Sai kubar yarinyar ta koma gidan kamar yanda Muhammadun ya faɗa. Zanje na sake sabon shiri a kanta dan wannan karon dole ne muyi shirin da zata koma inda ta fito kuma har abada bazata sake dawowa ba. Kai bama ita da suka haifa ba, har Usman da Maryam (Aunty mimi) bazasu sake waiwayo ƙasarnan ba har abada balle ita karan kaɗa miya”.
A take fuskokinsu suka washe da murmushin jin daɗi. Fadwa tace, “Amma ni dai gaskiya ayi da sauri. Dan wlhy idan ina ganinta a gidana ji nake kamar na shaƙeta ta mutu. Bana son Soulmate ya dawo ƙasar nan tana gida na”.
“Batun kafin ya dawo ƙasar nan bazai yuwuba. Domin kin ɓata komai ga shirin yin hakan kuma ai. Dolene muyi ɓadda kamar da zasu cire ɓaranɓaramar da kikai a ransu gaba ɗaya daga nan har zuwa lokacin bikin Maheer, so nake da bikin idan sun zo su tattara ƴarsu su wuce yanda bazasu sake dawowa cikinmu ba har abada. Idan kuma kika ƙara yin wanu shirme to kiyi kuka da kanki bani Hannatu ba kuma”.
Baki Fadwa ta tura gaba sai dai batace komai ba. Nan su Mommy suka shiga jadadada mata ta kiyaye kar kuma a sake samun wata matsalar kamar yanda Gwaggo ta faɗa. Idan tai haƙuri komai zai zama labari dan suma basu da burin daya wuce Anam ta bar gidan ai. Miƙewa Gwaggo tayi, “To bara nayi nan karma wani ya shigo ya ganni. Shima kuma Mustapha kar wanda ya kirasa akan maganar mu jira muga ko wani zai sanar masa a cikinsu”.
Duk sun gamsu da hakan. Daddy dake bakin ƙofar yaja da baya a hankali yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa. Dama yazo ne dan ya sake kwantar ma da Fadwa hankali da nuna mata tabar zargin kowa akan zubar cikin ta ɗaukesa matsayin ƙaddara. Amma sai gashi yaji ainahin abinda ma ke faruwa. Bai bari Gwaggo data fito tana murmushi ta gansa ba, sai ma ya juya yabar wajen ya fasa shigar...

Washe gari Daddy ya sakasu komawa can gidan Fadwa na ɗacin ran kasancewa da Anam. Khaleel ne ya ɗauke su su huɗu har mai aikinta dan maigadi shi tun jiya ya koma. Anam tai murmushi tana kauda kanta gefe ganin uwar hararar da Fadwa ke zuba mata kamar idanunta zasu zubo ƙasa. Sosai murmushin ya ƙular da Fadwa, sai dai batai magana ba har suka iso.
Kiran da Abie yay ma Anam a waya ne ya sata dakatawa su suka shige su uku. Itako ta tsaya anan jikin motar Shareff dake lulluɓe tana amsawa. Ta jima tana wayar kafi. ta nufi ciki itama fuskarta ƙawace da murmushi. Matar gidan kawai ta samu a falo zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jijjigawa da yanka apple. Sai mai aikinta dake gyaran falon. Yi tai kamar bata ganta ba tai ƙoƙarin wucewa........✍🏻

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment