Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“Wai lafiya mike faruwa ne?”.
Mommy da Hassan yaje ya sanarma gidan babu lafiya ta faɗa tana ƙarasowa wajen. Babu wanda ya iya bata amsa saboda maganar da Daddy ya cigaba dayi a kausashe cikin kuma tsananin ɓacin rai....
“Wlhy na baka nan da zuwa ƙarfe sha biyun dare ka kawomin yarinyata gida, inba hakaba sai ranka yayi mummunan ɓaci Al-Mustapha!!”.
Cikin sauri Mommy ta dakatar da shi itama a fusace. “A'a Alhaji kamarya da wannan hukunci haka. Shine ya ɓatar da koma wacece ake neman da za'ace ya fita a wannan daren nemanta bay......”
“Babu ruwanki a wannan maganar, idan kuma kikace zaki shiga wlhy zan sakaki nadama ne!!”.
Gaba ɗayansu binsa sukai da kallo ganin yanda yabar wajen a matuƙar fusace. Banda Shareff da kansa ke ƙasa. Abba ne ya dubesa da damuwa shima, sai dai cikin sauƙaƙa murya dan bai kai Daddy zafi ba yace, “Son kayi kuskure. Ka manta Anam babu inda ta sani, ko anguwarnan bana zaton ta san sunanta ma, kag........”
A harzuƙe Mommy ta katse Abba “Anam!!. dama akan wannan tsifatar yarinyar ake wannan tada jijiyar wuyar? Shareff bance ka fita harkar yarinyarnan ba a gidan nan?”.
Bai iya ya ɗago ya kalleta ba, dan baisan wace amsa zai bataba. Tana ƙoƙarin nufosa isowar Gwaggo ya dakatar da ita. “Wai hayaniyar mi nakeji a gidanne haka kai?”. Duk juyawa sukai gareta. Ganin kowa ya kasa cewa komai Khaleel yace, “Anam ce bata dawo gida ba”.
“Shine miya faru kuma? Ita ɗin yarinyace?”.
“Haba Gwaggo ya zakice haka? Nawa Anam ɗin take? Sannan ina ta sani bayan kinsan kamar baƙuwa take a ƙasarnan bama garin kano ba”.
Harara Gwaggo ta zubawa Abba mai maganar. “Oh to kana faɗaminne ko kana tunamin Abubakar? Gallaƙeƙiyar budurwa da yanzu idan aka sakata ɗaki da namiji zata samo ciki kake sanarmin nawa take? Toni abindama ban ganeba mi'akema hayaniyar anan?”....
“Titsiye Shareff sukai yaje nemanta kamar shine yace ta tafi yawon tazubar ɗin, dan nasan bai wuci can ɗin ta tafi ba tunda an saba a inda aka fito..”
“A lallai kuna bukatar Addu'a Abubakar. Shi Mustapha ɗinne ya kaita ya ɓatar da zakuce yatafi nemanta a wannan daren bayan wahalar da yaje ya gama shawowa a wajen aiki ya dawo. Kai Mustapha muje naga ubanda zai saka fita ko nan da gate a daren nan dan.......”
Sauran maganar ta maƙale ganin kaf wajen babu alamar Shareff ɗin. Su dukansu babu wanda yasan yama sulale yabar wajen. Horn da ƙarar buɗe gate ya sakasu juyawa can gaba ɗayansu. Sai dai kafinma wani yay wani yunƙuri har motarsa ta fice.....

Wajen aikin nata ya fara zuwa, sai dai kamar yanda maigadin wajen ya faɗama Mubarak shima haka ya sanar masa. Lokacin da yake tafiya a hankali ya dinga tafiya kozai ganta a hanya. Amma ko alamarta babu duk da titin wajen tako'ina akwai hasken fitulun solar. Duk da hakan bai fasa sake bi a hankali yanzun ma yana dubawaba har ƙarshen titin. Ganin har tara ta gota na dare yay fakin gefen titi ya kifa kansa kan sitiyari dan ciwo yake masa matuƙa kamar zai faɗo ƙasa. Dama tuƙin yinsa kawai yake cikin dauriya.

A gida kowa ka kalla a cikin damuwa yake, idan ka cire Gwaggo da Mommy da suketa bala'i da kowa ya kasa fahimtar dalilin yinsa. Aysha harda kukanta. Dan ansan ko wayarta aka nema baza'a samuba tunda bata da layin Nigeria. Abba da Daddy da Khaleel ma sun fice police station.
“Aunty wayarki sai haske yake tun ɗazun”. Hassan ya faɗa yana duban Aysha data zuba uban tagumi tana sauraren masifar Mommy kawai daketa faman kai kawo tsakanin bedroom ɗinta zuwa falo. Kamar Aysha bazatabi takan wayarba sai kuma tacema Hassan “Ciromin daga cajin”. Ciro mata yay, ganin bata san no ɗinba tai tsaki ta ajiye. Duk kiran da aka cigaba dayi har kusan sau biyar bata kulaba. Sai ma ɗaukar wayar datai rai a ɓace zata kashe sai saƙo ya shigo da no din da aketa kiran nata. Guntun tsaki tai ta buɗe dan taga wai waye ma ya addabeta ya barta taji da damuwarta ma itakam. Zumbur ta miƙe da waro idanu, har zata fasa ihu sai kuma tai saurin gumtse bakinta da satar kallon inda Mommy take. Tai saurin haɗiye farin cikinta ta nufi bedroom ɗinsu da sassarfa. Jikinta har rawa yake ta maida ƙofar ta rufe harda saka key tana dailing number ɗin...
“Blood da gaske kece?”.
Kamar jira Anam keyi ta fashe mata Aysha da kuka. “Ya ALLAH Blood Please kibar kuka, kina ina ne yanzu? Ga gida duk hankalin kowa a tashe da rashin dawowarki su Yaya dasu Abba duk sun fito”. Ta ɗanji sanyi, amma hakan bai hanata jin zafin Shareff ba. Da ƙyar tace, “Zan tura miki address ɗin yanzu bansan inaneba”..... Aysha na katse kiran tai kiransa.

Har yanzu kwance yake kawai akan sitiyari, yama rasa wane kalar tunani zaiyi shi kam. Ring na wayarsa ne ya katse masa tunani. Yay banza da wayar harta tsinke aka sake kira. Nanma bai ɗaukaba sai ana uku ya ɗago a fusace da nufin cin uwar mai damun nasa yaci karo da sunan Aysha. “Lafiya kika isheni da kira ke kuma?”.
“Kayi haƙuri Yayah. Anam ce ta kiranifa yanzu da wani number sai kuka take.”
Idanu ya rumtse da ƙarfi yana sauke wata irin bahaguwar ajiyar zuciya da har Aysha na jinsa. “Turomin number”. Ya faɗa a takaice kawai da katse kiran. Mintuna biyu kacal number ɗin da address ɗin data turo mata duk ta turo masa. Wayar ya cilla gefensa yayma motar key da fisgarta a guje yabar wajen. Tafiyar mintuna ƙalilance ta kawosa wajen saboda uban gudun daya zabga..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107





*_ALLAH yasa yau a rama mana marinmu😹😹😜🚶🏻_**_Typing📲_*




*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_08_*


..........Tunda ya amsa wayar ya turama wadda ta kira da sister ɗinta address ɗin inda suke yaketa lallashinta ko ruwa tasha amma taƙi sai faman sharɓan hawayema takeyi. Hakan yasa yay tagumi kawai yana kallonta. Komai tai birgesa takeyi, Duk da ƙaramin jiki da take da shi kai kasan ba yarinya bace, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci lallai ƴar gatace a gidansu dan saurin karayanta yayi yawa. Hoto ya fara mata yana murmushi batare data sani ba.....
Tunda ya shigo idonsa ya sauka a kansu. Wani irin baƙin ciki da ɓacin ransa sai suka ƙara ninkuwa. Nufarsu yay rai a ɓace sai dai bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba duk da ya ciskulleta sam babu fara'a. Kamar ance ta ɗago idonta ya sauka a kansa. Babu shiri ta miƙe zumbur dan yanayinsa ya tsorarata, bata manta dukan da yay musu ita da Aysha ba. Wani irin mugun kallo yay mata ya ɗauke kansa ya maida ga saurayin da shima ya miƙe dan ya gansa. Kallon banza da tsana yake masa yayinda shi saurayin yay ƙoƙarin mika masa hannu suyi musabaha yana murmushi duk da yaga kallon banzar amma ya shanye.
Kallon hannun yay ya wani ɗauke ido da maidawa kan fuskarsa yana mici-mici da idanunsa dan sarai ya gane shine ranar yayta binsu daga wannan restaurant ɗin.....
“Kana buƙatar ka zauna lafiya?!!”.
Duk da a yanda yay maganar cike da isar gadara hakan bai hana saurayin sakin murmushi ba da jinjina kansa. Cikin sauƙaƙa tasa muryar yace, “Sosai kuwa babban Yaya. Ai magabatanmu kance zaman lafiya yafi zama ɗan sarki”.
Kansa ya ɗauke duk da shine ya buƙaci amsar kuma aka bashi. Wani ɗan juya harshensa yay cikin bakinsa cike da basarwa yana sakin murmushi mai harshen damo. Sai kuma ya jinjina kansa da sake maido dubansa ga saurayin fuska a haɗe. “To daga yau, daga yanzu, karka bari na sake ganin wannan fuskar taka a inuwa ɗaya da ita. Inba hakaba......”
Ya ƙarasa da wani shegen murmushi dimple ɗinsa na loɓawa, yaɗan bubbuga kafaɗar saurayin. Bai saurari amsar da saurayin zai bashiba ya fisgi hanun Anam dake maƙure waje guda zuciyarta kamar zata kifo ƙasa. Da tasan shine zaizo ɗaukar tata data aminta da shawarar saurayin daya buƙaci Aysha ta tura address ɗin gidan shi ya kaita amma taƙi. Jakkarta dake kan desk ɗin ya fusga itama tare da wayarta yay gaba da sake yima saurayin warning da idanunsa dake rine matuƙa fiye da yanda ya shigo wajen.....
Turata yay a motar ya rufe har saida ta zabura dan kaɗan ya hana ya datse mata yatsun hannu. Ya zagayo mazauninsa tare da figar motar a guje yabar wajen. Yanda yay ɗin yay masifar sake firgitata har sai da ta faɗa gefen hanunsa ta ƙudundune fuskarta tana kiran sunan ALLAH, dan ta zata gabzama motocin gabansu karo zaiyi ma. Ƙuwwww!!! Ya taka birki da daka mata wata razananniyar tsawa. Saurin sakinsa tai tai baya a firgice, sai kuma ta fashe da kuka dan gaba ɗaya ya sake firgitata ta tsani tsawa...
“Stupid! shut up!!. Idan baki rufemin shegen bakinki ɗin nan ba na fara kashe fuskarki da maruka sai kin suma. Wawuya kawai. K har idonki yay tsurin bin motar saurayi kuje restaurant?! Dama abinda kikazo yi kenan a Nigeriar?!!!”.
Yanda ya ƙare maganar a matuƙar tsawace ya sake birkitata. Amma sai ta danne cikin ƙarfin hali tace, “ALLAH ya kiyaye danni ba mayyar maza bace”.
Ya sake watsa mata harara kai kace cinyeta zai da jajayen idanun nasa. Sai kuma yay ƙwafa da ɗauke kansa yana sake tada motar. Ko motsin kirki bata sakeyi tunda ta samu bai maketa ba. Kukan ma ta daina na zahiri na zucici takeyi. Gaba ɗaya jitake tama gama tsanar Nigeria, ita dai gaskiya bazata iya wannan masifar ba, tun farko abinda ta guda kenan amma su Mamie sukaƙi fahimtarta. Itakan duk ma yanda za'ai a satin nan sai tabar Nigeria hidimar ƙasar nan bazata yuwuba.....

Ko gama dai-daita parking baiyiba ta fita dan mutanen gidan duk suna tsakargida tsaitsaye Gwaggo da Mommy ne kawai babu sai irin su Fawwaz da sunyi barci tuni basu san abinda akeyiba. Aysha ce ta taho da gudu suka rungume juna, sai kuma ta saketa taje ta rungume aunty amarya da Mom. Su Daddy da tuni Aysha ta kirasu suka dawo gida zaman jiran isowarsu suma ajiyar zuciya kawai suke saukewa..
Mom dake shafa kanta da murmushi tace, “Kukan ya isa haka mana mamana. Tunda kuma an dawo gida sai muce Alhmdllhi. Jeki gaida iyayenki”.
Babu musu ta saki Mom tana share hawaye ta nufi su Abba. Gaishesu tai hawaye na sake silalo mata, abinka ga ƴan boko kasa daurewa Daddy yay sai da ya ringumeta. “Haba Mamana ina kika shige haka duk kin tada mana hankali”. Ya faɗa yana mai ɗagota a jikinsa. Murmushi tai tana share hawayen da suka ƙi tsayawa. “Daddy na kasa ganewane, idan na tsaida masu keke ɗinnan sai suce basu gane yanda nake faɗa musu gidan ba”. Tausayinta sosai ya ƙara kamashi, kanta Abba ya shafa yana murmushi. “Dole ki dage ki koya hausa a zaman nan Mamana, dan rashin iyawan ya taka rawar gani cikin accident ɗin nan”.
“A'a Abba dan ALLAH ni zan koma Malaysia”.
“Tsit gurin yay babu wanda ya iya cemata komai. Sai Shareff ne ya wani taɓe baki da barin wajen ko uffan baicema kowaba balle bayanin yanda ya samota dan a matuƙar gajiye yake ga ciwon kan nasama zazzaɓi yake neman komawa. Daddy ya kashe shirun wajen da faɗin, “Kuje ciki tai wanka taci abinci dan tana buƙatar kwanciya da wuri. Mamana mayi magana da safe”.
Badan tasoba tabi Mom dan bata iya musu ba kuma. Duk da yanda Aysha ke tsoron faɗan Mom haka tabi Anam sashen Mom da ƙudirin su kwana tare, dan jitake kamar kafin safiya za'a ƙara cemusu ba'a gantaba ta sake ɓata.

Washe gari tunkan ma Anam ta kira Abie ɗinta ta sanar masa Daddy ya kirasa sukai magana. Yayma Shareff kuma faɗa sosai kamar zai ari baki. Daga ƙarshe ya kafa masa dokar hukuncinsa shine kai Anam wajen aiki kullum ya kuma ɗakkota. Idan ko wata matsala ta sake shigowa akan Anam to lallai ya kuka da kansa dan sai ya matuƙar ɓata masa rai a gidan.
Shi dai Shareff ɗin baice komai ba akan hukuncin. Sai Mommy ce tace sam bata yardaba ɗanta ba driver bane ba. Ko kallonta Daddy baiba, ya dai tabbatar mata idan Shareff ya isa yaƙi bin umarninsa.
Ai wannan magana ta dagula ran Mommy a safiyarnan. Dan tata masifa ita da Gwaggo data fito tana goya mata baya. Daga Daddy har Abba babu wanda ya sake tofa tasa dan sukam dai yanzu sai dai su kalla Gwaggo kawai tunda sun fahimci bata ƙaunar zaman lafiyarsu da ɗan uwansu, Halima ce kawai ta kasa fahimta sun kuma barta wataran zata gane da kanta musamman da suka san idan akai auren nan na Fadwa da Shareff.

★★★★

Duk yanda Mommy taso hana Shareff ɗaukar Anam hakan bai yuwuba. Dan shi dai haƙuri kawai ya bata da nuna mata illar fushin mahaifinsa a garesa. Ya roƙeta ta kwantar da hankalinta a hankali zai janye jikinsa ya samama Anam ɗin driver kowa ma ya huta. Wannan magana tashi ce taɗan kwantar mata da hankali ta maida kanta ga hidimar shirye-shiryen bikinsa.
Daga ɓangaren Anam ma taci uban borinta akan malaysia zata koma ta fasa hidimar ƙasar su Mamie suka lallasheta da tabbatar mata cewar idan sukazo bikin Shareff zasu san abinyi. Hakanne yaɗan kwantar mata da hankali ta zauna zaman jiran lissafin kwanakin bikin. Yayinda ta cigaba dabin Shareff ɗin a takure. Shike kaita shike ɗakkota, daga gaisuwa babu abinda ke haɗasu sai harara. Ita kuma tata tura baki kenan da ɗaure fuska ita a dole haushinsa takeji duk da bata da riƙo sam wannan karon dai ta riƙe.

Yau a gurguje yay shirin tun 7 ma batai ba ya fito saboda wani babban uzirin dake gabansa a office ɗin. Ga baƙi zaiyi akan wani babban project da suke saran samu insha ALLAH. A tsaitsaye ya shiga sashen Mommy suka gaisa koma shayin bai zaman shaba yau dan yaran kansu duk suna ɗaki basu gama shiri ba. Baije sashen Gwaggo ba dan ya gaji da mitarta akan ɗaukar Anam da yake yasan zata ɓata masa lokaci. Aunty Amarya ma a tsaitsaye suka gaisa ya nufi sashen Mom. Bayan sun gaisa da Mom ɗin cikin raba ido da kallon ko'ina na falon yace, “Mom tana ina zan makara?”.
Da mamaki Mom ɗin ke kallonsa. “Wai kana nufin Anam?”.
Kansa ya jinjina mata. “Eh Mom, yau zan fita da wuri inada uziri shiyyasa na sanar mata tun ɗazun ta shirya da wuri”.
“Tab ɗi, to aiko banama zaton ta tashi a barci Babana. Ni kuma ban saniba ai da na tadata ta shirya”.
Cikin ɓacin rai ya ɗan sake duban agogonsa da rumtse idanunsa. Ganin Mom ta nufi ɗakin yaja ɗan siririn tsoki. “Mom bara naje idan Khalel zai fita su taho tare inada meeting ne mai muhimmanci”.
“To bara na tasheta dan nasan shima ɗin gab yake da fitowa kuwa”.
Komai baice ba ya juya ya fita.
Ba ƙaramin jan ido Mom taima Anam ba kafin ta tashi. A gurguje tai shiri saboda Khalel daya leƙo ya mata gargaɗi. Tasan halinsa shima ba mutunci ya cikaba shiyyasa tai ƙoƙarin shiryawa aɗan gurguje tanata kunƙuni dan barcin bai ishetaba. Tsaf ta shirya cikin kayan NYSE kamar koyaushe, sun mata cif kamar ka saceta ka gudu, ƙaramin baby hijjab tasa yau. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Khalel da gaba ɗaya yake ƙage da fitowar tata hanata zaman shan tea ɗin da Mom ta haɗa mata yayi.
“Mom Please ki barta tasha a hanya ko a office ɗin, ALLAH idan na makara Yaya zaimin faɗa duk da shine yace na ɗauketa, gashi meeting ɗin nan inada alaƙa dashi nima.”
“Amma Khalel ta fita bata karyaba? Bayan kasan bako wane abinci take iyaci ba. Kai da Shareff ɗin duk wutar ciki tamuku yawane kawai, amma duka ƙarfe nawane yanzu ɗin? An faɗa muku kowane zai dinga iya uban sakkonku da aiki kamar matching?”.
“Mom bazaki ganeba wlhy. Please ki barta nidai”.
Kafinma Mom ta sake magana Anam tace, “Kibari zansha a can ɗin Mom kinsan masifar wancan mutumin tafi ta Yah Khaleel”. Murmushi kawai Mom din tayi yayinda Khaleel ke hararta.

Sosai Khalel ya zumbuɗa gudu a hanya, lokacin da suka isa wajen aikin nata har bakwai da rabi ta kusa gotawa. Sai dai sauƙinsa ma babu nisa mai yawa da company ɗinsu dan duk titi ɗaya ne. Baki ta taɓe ganin yanda duk Khalel yabi ya damu kansa tunda suka taho yake mata masifa a mota wai idan tace lalaci zatai to zata dinga hawo motar kasuwa kuwa shi dai baza'a dinga sashi ya jirata ba. Ita dai komai batace ba sai faman ɓata fuska dai takeyi tana cin inibi ɗinta data taho da shi daga gida da buga game a waya har suka iso.
“Kije idan an fita break zan kawo miki abinci”.
Sosai ta waro idanu waje. “Har ƙarfe nawa kenan Yah Khaleel?”.
Harararta yay yana ƙoƙarin jan murfin data riƙe zai rufe. “Lokacin zuhur mana”.
“Haba Yah Khaleel one fa kenan? Kaga ƙilama yunwa ya halakani kawai”.
Dariya ta bashi amma sai baiyiba. “Naji zan roƙa Ya Shareff idan an tashi meeting zanyi squeezing time na kawo miki”. Kafia tace komai yaja motarsa yay gaba. Tabi motar da kallo tana tura baki gaba.

Kamarko yanda yay alƙawarin ya cika. Dan wajen sha ɗaya aka kawo mata saƙo. Koda ta buɗe sai taci karo da takeaway na abincin da take tsananin so. Daɗin da taji ya sata tura masa text message na godiya, dan hakan tamkar tarbiyyar su Mamie ne a gareta, indai an mata alkairi komin ƙanƙantarsa sai tayi godiya harma da addu'a.
Saƙonta ya shigo wayar Khaleel ne a dai-dai sanda wayar ke a hanun Shareff. Yazo nuna masa hoton wani zane da aka turo masa daga lagos sai kira ya shigo masa a ɗaya wayarsa, bazai iya ɗaukar wayar a gaban Shareff ba shine ya fita. Baiyi niyyar buɗe saƙonba, amma ganin sunan daya turo saƙon ya sashi buɗewa. Shiru yay na wasu sakkani yana kallon saƙon tamkar mai bitar karatunsa, sai faman cizar lip yake, sallamar Khaleel ta sashi danne saƙon ya aunashi a delete gaba ɗaya. Wayar ya miƙama Khaleel batare daya kallesa ba. “Kaje da shi zamuyi magana daga baya kawai”.
Ɗan jimm Khaleel yay yana kallonsa, dan sanin maganar tasu muhimmiyace, hasalima shine ya damesa da kira tun ɗazun akan yazo duk da yasan suna meeting ne. Amma kuma sai bai kawo komai a ransaba yace, “Okay Yaya. To koma dai na tura maka shi kawai saika sake nazari kafin?”.
“Okay yayi”.
Ya faɗa a taƙaice kawai. Kasancewar shima Khaleel ɗin miskilin kansa ne sai bai sake tofa komaiba ya miƙe ya fita abinsa. Haka kawai ya samu kansa da binsa da harara harya fice. Tsaki yaja da rumtse ido kamar irin mai takaicin kansa ɗin nan. Ya sake jan tsaki ya miƙe gaba ɗaya yabar table ɗin. Can jikin ƙaton window da aka ƙawata office ɗin da shi wanda ake hango har titi da cikin compound ɗin company ɗin kasancewar a saman upstairs office ɗinsa yake yaje ya tsaya. Ya jima wajen a tsaye hannayensa duka a aljihu yana kallon kaikawon mutane daga titi zuwa cikin company ɗin...

Da lokacin tashi yay addu'a tai tayi ALLAH yasa Khaleel zai dawo ɗaukarta, har kiransa tayi dan taji sai dai bata samesaba network ya hana. Tun shigowar motarsa wajen tasan addu'arta bataci ba. Ɗan duban Yaseer abokin aikinta kuma shima ɗan hidimar ƙasa ne dake gefenta tai a sanyaye. Ya sakar mata murmushi dabinta da ƙyaƙyawan kallon da yake hanata sakewa da shi. “Ga Yayana yazo bye”.
Manyan idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta. Shima ya miƙe har lokacin idonsa a kanta. “Haba dai Friend haka ake Friendship ɗin anama juna rowan dangi? Kamata yay kice muje na gaida Yayanmu ai ko? Kullum sai dai naga yazo ɗaukarki baki taɓa gayyata ta na gaisar da shi ba”.
Murmushi kawai tai batare da tace komaiba. Ganin tayi gaba yay saurin bin bayanta har sai da tafiyarsu ta dai-daita. Kasancewar tinted glass ne yasa Yaseer knocking duk da sarai yasan wanda yake ciki ya gansu. Shiru babu alamar za'a sauke ya ƙara knocking fuskarsa faɗaɗe da murmushi. Zai ƙara na uku Anam ta girgiza masa kai a hankali, dama abinda ta gudar masa kenan shiyyasa taso hanashi tun farko. Tana ƙoƙarin buɗe baki ta bashi haƙuri aka sauke glass ɗin a hankali.
Kallon daya watsa mata ya sata kauda kanta tana taɓe baki, Ƙara ɗaure fuska yay da duban Yaseer daketa faman shafar ƙeya yana murmushi.... Kafinma yace wani abu Yaseer ɗin yay saurin faɗin, “Good afternoon Yayanmu”.
Kamar bazai amsaba sai kuma ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha, babu musu shima Yaseer ɗin ya basa suka gaisa, a mamakin Anam harda cema Yaseer ɗin, “Yaya aiki?”. Yaseer ya amsa fuskarsa na sake washewa ga sinne kai yana famanyi kamar wanda ke agaban surukai. Anam ta ɗan taɓe baki tana jinjina kanta, a ranta kuwa gulmarsa take. Tana son ɗagama Yaseer dake ɗago mata hannu nata hanun tanajin shakka, sai da taɗan faki idonsa ta ɗaga sau ɗaya ta fuske. Sai dai batasan yama rigada ya gantaba. Bai daiyi maganaba ya tada motar suka wuce.
Shiru babu wanda ke magana tsakanin shi da ita sai redion motar daketa karaɗi, ganin inda suka shiga saɓanin gida daya kamata su nufa ya

Please Login or Register in order to submit comment