Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wakkali,yana fita waja motar na parking kallo ɗaya yay mata yasan ta Daddy ce,sanye take da ƙaton hijab har ƙasa sai kyakkyawar fuskarta data baiyana tashin hankali,zubawa Mom ido yay ko ƙiftawa babu cikin sauri ta ƙarasu wajanta tana zuwa kafin tayi magana ya faɗa jikinta yana sauke ajjiyar zuciya akai-akai bayansa ta shiga bubbugawa"sorry beb i know u arw hurting sorry dan Allah everyting will be ok"kai kawai ya ɗaga mata kafin ya zare jikinsa yabar wajan yay hanyar garden ko tsoro ba yaji,domin daya tsaya Daddy ya sameta a wajan ƙwamma kome zai sameshi ya sameshin.

Turus Daddy yay ganin Irfan yay tafiyarsa kuma yana da tabbacin ya ganshi.



Hospital
Lokaci kaɗan ya ƙarasu yana zuwa aka amsheta tare da ɗurata akan bed ɗin marasa lafiya aka huce da ita emagency room.


Sunja lokacin kafin su fitu a ɗakin a nan wajan dr yaywa Aryan bayanin cewa cikin dake jikin tane ya zube sabida tsoratar da tayi,sunyi mata wankin ciki tare da ɗurata bisa maganin zuwa safiya insha Allah zafa farka.


A one week lrt

A gurguje tashin hankali Amrah ta shiga ba kaɗan ba domin abincima bafa iyaci sai Mom tayi da gske a haka dai akai sadakar uku,yawan nasihar mom data Dad yasa ta fauwallawa ubangiji al'amarinsa domin shike rayawa kuma shike kashewa babu wanda ya isa ya ɗauki ran wani sai ubangiji yay niyar hakan,Allah yayi ba zatai rayuwa dashi mai tsayi ba hakan yasa ta dage dayi masa Addu'a.

Twinst kowa ko jikinsu domin basu samma meye mutuwar ba dahar zasu ɗaga hankalinsu akai.

Kullum sai Irfan yaje wajan Jidda amma haryau bata farka ba hakan sata gaba yayta kallonta har zuwa dare sallace kawai ke ta dashi,maganar Office kowa yasa a side acewarsa bazai bar amanar ƴar mutune ita ɗaya ba.


Yau kwana bakwai cif da rasuwar Abban twinst wanda yay kwannan Jiddah 7 akan gadon asibiti amma haryau bata farka ba.

Tun safe yaywa Jessica waya akan ta sameshi a asibiti,ba ƙaramin daɗi taji ba hakan yasa ta shiga shiri kamar zata sauya fata.


Yana zaune akan duguwar sofa wacce take gefe guda a room ɗin da aka kwantar da ita,shanyayyun manyan idonsa ya zuba mata yana kallon yadda numfashinta ke sauka a hankali ta tare sosai amma kamar an ƙara mata kyau domin har mamakin kyanta yake,tym to tym na'orar ɗakin na ƙara kaɗan wanda yake nuni a koda yaushe zata iya farkawa.


Knoking ƙofar aka shigayi cikin gajiyawa yace" come in" shigowa tayi tare da rufe ƙofar tayi wani masifaffan kyau sai zabga ƙamshi take,wando ne pencil a jikinta sai wata ƙaramar riga ta jiki,pink ɗin After dress ta ɗura akanta wacce ta buɗe daka gaba,kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa ya maidashi kan Jidda.

Itama Jidda ta kallo tare dajan tsaki kaɗan wajansa ta nufa tana zuwa ta faɗa saman jikinsa tare faɗin"i missed u dear ka sani damuwa da yawa"


Lumshe lulu eyes ɗinsa yay haɗi da cije jajayen laɓɓansa masu kauri ya fara fitar da numfashi mai zafi sabida abinda Jessica keyi masa.


A hankali² ta shiga ɗaga zara-zaran eyelash ɗanta wanda sukaiwa idonta rumfa,saurin mai dasu tayi sabida hasken da yay idonta yawa,ajjiyar zuciya ta sauke kafin ta ƙara buɗesu a karo na biyu ta manna idonta akan drip dake saƙale a sama,ɓata fuska tayi jin bakin babu daɗi sai wani ɗaci data keji,hannunta ta ɗaga tare da saukesa akan saitin zuciyarta wacce ke ɗagawa ta sauri.

Lumshe idon tayi tana sauraran saukkan ruwan cikin jikinta,wani sauti ne ya fara zarya cikin kunnanta haɗi da saukan numfashi akai akai,banza tayi domin bata buƙatar hayaniya,saurin buɗe idonta tayi jin ance "auchiii..yaahhh"ɗan juya fuskarta tayi kaɗan cikin sa'a idonta ya sauka akan hannun Jessica lokacin data ɗurashi saman mararsa..



*idan ba kuyi wasa ba zai zama na kuɗi book ɗinan domin ana yimin ruwa comments🥵*
[12/9, 5:50 PM] +227 99 46 01 51: ```💞HEARTBEAT💞```
*JIDDAH*

```MALLAKIN😘
ANTY NI'EEMERH
Nimcyluv```

CHAPTER 20-21
```THE WALET

```Wattpad@nimcyluv```


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻



20-21


Ɗan runtsa idonta tayi tunaninta shine ya nuna mata ba dai² ba,abinda baifi 3second ba ta ƙara waresu zuciyartace ta buga da ƙarfi lokaci guda hawaye masu zafi suka shiga zubuwa daga cikin idonta ji tayi gaba ɗaya ta tsani matar haɗi dashi kanshi ɗin domin ba tayi tunanin cewa lala tacce bana sai yanzu,ƙirjin tane ya fara sama da ƙasa sabida yadda zuciyarta ke gudu akai² bata samun damar shaƙar numfashi wada tacce.

Drip ɗin dake manne a hannunta ta tsige tare da tashi zaune,wajan 3min ta miƙe tsaye a hankali ta fara tafiya zuwa wata ƙofa wacce ta tabbatar da toilet,tafiya take tana tangaɗi kamar zata kifa sabida yadda jikinta yake babu ƙwari a zahirin yadda take tafiya zaka ɗauka tana sani take duk ɗaga ƙafarta guda sai dukkan jikinta yay sharking,a haka ta hucesu cikin wannan halin yana kwace kamar kungi ko hannu baya mutsawa sai fitar da numfashi kawai yake.


Hannu tasa ta buɗe ƙofar tare da shige ciki ta rufe da sauri,zaman dirshan tayi a cikin toilet tana tsiyayar da hawaye haɗi da kuka mara sauti,tasan cewa a koda yaushe ƙaddara abace mara tabbas domin tana iya sauyawa a ko wanne lokacin a ko wacce dakiƙa ƙaddara na iya sauya,uban data ɗauka shine gatanta shine bangon da zata jingina dashi taji daɗi,shine mai kure dukkan wata damuwa a ranta,shine ya cireta sahun ƴar ƴan daya haifa ya ƙirata da matacciya bayin tana da ranta,saurinyi data kejin babu wacce ta fita sa'ar samun kamarsa ta ɗura masa dukkan wata yardarta bata haufi akan sonta yake mata,a kullum da sonshi take kwana take tashi shine aka wayi gari ya gojeta akan wani dalilinsa mara toshe ko kuma nace silar mahaifina,Faizak ya nuna mata so a wajan aikinta tana ganin motuncinsa sosai hakan yasa ta fitu ta gaya masa yay hkr da son da yake mata bata da wani labarin da take bashi saina Irfan,ashe shima yana ɗauke da niyar fansar abinda tayi masa,waje guda ta dake jin duk wani farin ciki dajin daɗinta ya ƙare sai wani haske ya ɓulluwa rayuwa wanda ya bata kula fiye da wacce zata samu wajan iyayenta,ta ɗaukesa matsayin ɗan uwa kuma yayanta mai kula da dukkan wani farin ciki nata,yau shine ya nuna bai damu da rayuwarta ba tana gadon asibiti jinya amma saida ya kira karuwarsa har asibitin da kuma ɗakin da aka kwantar da ita...

Wani kukane ya kwace mata jikinta har rawa yake dalilin ta farfasar da zuciyarta keyi mata,wani zafi haɗi da raɗaɗi ta kejin a cikin zuciyarta amma wanda ta isa ta gayawa domin babu mai share mata hawaye...

Ƙarar rufe ƙofar shine ya dawo dashi cikin hayyacinsa, blue sexcy eyes ɗinsa ya ware saman bed ɗin da take kwance akai tana bacci,ture Jessica yay daga jikinsa ganin babu ita babu dalilin,babban tashin hankalinsa idan ya kasance taga abinda ya aikata ko kuma aka aikata masa dafe forehead ɗinsa yay tare da furta "ya rabb solve this problm"

hannu yasa gaba ɗaya ya hargitsa sumar gansa tare fesar da numfashi mai zafin gaske,jin anyi hug ɗinsa ta bayane ya sanya ya juyo a hankali tunaninsa itane duk yasa da huya ta iya hakan a gareshi.

Tsaki yay mara sauti ganin Jessica ce kallonta yay tare da ɗauke kansa gefe guda ya daɗe a haka kafin ya wara laɓɓansa yace"get out pls"ƙara riƙesa tayi ta shiga goga masa jikinta wata muguwar tsawa ya daka kafin yay mgn tuni tabar ɗakin sosai tsawar ta hargitsa mata lissafi.


Sautin kukan tane ya fitu ta cikin toilet ɗin cikin nutsuwa take rera kukanta a yadda kukanta yake dukkan kunansa hakan yake jin wata a zaba da kunci yana sauka cikin zuciyarsa,saukar kukan kowa jinsa yake kamar saukar ruwan dalmane.


Kan sofar yaje ya zauna yana dafe da kansa yasan koda yay knoking ba zatai respond ba,dalilin hakan ya zubawa ƙofar ido har zuwa lokacin da zata fitu..

Ta ɗauki lokacin mai tsayi a toilet ɗin kafin ta buɗe handle ɗin ƙofar toilet ɗin ta fitu,sanye take da pink ɗin towel mai ɗan tsayi wanda ya rufe mata ƙirjinta zuwa laps ɗinta domin bai sakko har legs ɗinta ba.


Mutumin daya ganta naked akan bed wani na samanta to wanne ɓoye zatai masa,a hankali ta taka zuwa kan bed da taga an gyarasa ba kamar ɗazu ba,zama tayi haɗe da sadda kanta ƙasa ruwa na ɗiga daga gashin kanta zuwa jikinta.


Tunda ta fitu ya zuba mata shanyayyun idanunsa masu firgita dukkan mace da tayi arba dasu,babu abinda yafi jan hankalinsa a jikinta sai yalwatattun gashin da yaywa farar fatar dake jikinta ƙawanya duka luff adukkan jikinta har zuwa yuwanta,ɗan lumshe ido yay tare da fesar da numfashi ta hanci.

Lura yay da yadda take rawan sanyi kuma ya kamata ta saka wani abu a jikinta hakan yasa ya miƙe cike da nutsuwa ya taka zuwa inda take,tsayawa yay a kanta kafin yaja numfashi ya zauna gefe da ita cikin cool voice ɗinsa mai cike da karshashi yace"i'm sorry for what i did pls"shuru kawai tayi kuma yasan ba lallai tayi mgn ba,zamewa ƙasa yay tare da tura kansa ta tsakanin laps ɗinta,datse lips yay domin bai samu nasarar ganin abinda ya keson gani ba,yasu yay arba da kwayar idonta wacce take sashi nutsuwa amma hakan bai samu ba,tashi yay tare da zama kusanta yace"4eyes!!" nan shuru tayi a matuƙar kiɗime yasa hannu ya jawota zuwa jikinsa babu abinda ya tsana sama da silent ɗinta.

Nauyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da ɗumin jikinsa ya haɗu da fatar jikinta,sosai take sauke ajjiyar zuciya sbd yadda ɗumin ke ratsa jikinta ba ƙaramin daɗi yay mata ba,duk da tana jin haushinsa hakan bai hana ta lafe cikin jikinsa ba..

Cikin nutsuwa take shigewa jikinsa rashin sani yasa da ɗura laɓɓanta a wuyansa sanyin lips ɗinta shiya sanya ya ƙara matseta jikinsa,sun ɗauki lokaci a haka kafin ta fara ƙoƙarin kwace jikinta daga nasa dalilin photon abinda ta gani ɗazu a shiga faɗu mata cikin kwayar idonta.

Kuka ta saki mai sauti ganin yaƙi bata damar kwace jikinta,bai hanata kukan ba sai bayanta daya shiga bubbugawa har kukanta ya tsaya ta shiga sauke numfashi.

Ya nayin fitar numfashinta mai zafi da yaji yana sauka a wuyansa shine ya tabbatar mata masa bacci yay gaba da ita.


Cireta a jikinsa yay tare da ɗurata bisa cinyarsa,ware idonsa yay sosai akan fuskarta ganin jini na fituwa ta hancinta rasa abinyi yay sai zubawa jinin ido yay dan bai kawo komai cikin ransa ba.

Tana jikinsa ya jawo wata leda tare d zaru wata dark blue ɗin abaya ya zira mata a jikinta tare da shimfiɗeta akan bed ɗin ya zare towel dake jikinta dashi yay using wajan goge jinin dake fita ta hancinta,kafin ya cire audiga kaɗan yaɗan tura cikin ƙofar hancin nata ɓangaren da jinin ke zuba,sunkuyawa yay tare da sakar mata sumba sakiyar kanta sannan ya juya ya nufi toilet.


To ganin jikin nata da sauƙi yasa dr basu dukkan maganinta tare da rubuta masu takaddar sallama,suka koma gida sosai Jidda tayi jimamin mutuwar Amrah domin bata samu labari ba saida suka koma gida.

A wannan ranar Irfan bai baro gidan Amrah ba saida ya tabbatar 4eyes tasha maganinta domin yaga alamar ba tasu daƙyar yay mata dabara dasha su sannan ya kuma gida a gajiyye tunda ya shiga bai fitu sabida gjiyar da yay sosai yake rabuwar baccin da bai samu zarafin yinsu a baya ba,har sallar issha a gida yay sannan yay shirin kwanciya bacci.


40days ltr

Anyi sadakar arba'in ɗin Abban twints yasha addu'a wajan jama'a sosai,ganin bata da wata idda sabida zubewar cikin jikinta yasa ta koma wajan aikinta da take a *HOUSE OF DISAPPLE* da Irfan ya daɗe da ginawa tun yana ƙasar waje yana son wajan sosai ƙananun yara marasa ƙafa ko hannu ko idu kurma makaho babu wanda babu a wajan.

Haka Jidda ta kuma Library da aikinta zuwanta na farko ta haɗu da wani mai suna NAJEEB yana da nutsuwa haɗi da barkwanci lokaci guda ya nuna mata yana sonta cewa tayi ta bashi lokaci,tana dawowa gida taci sa'a sun shigo shida Aryan suna cin abinci babu wanda ta kula domin haka take idan gajiya tayi mata yawa,wanka tayi ta saka riga da wando na pakistan masu kyan gaske sannan ta fitu daining area ɗin.

Zama tayi kujerar da take parcing ɗin Irfan ɗin kasanciyar Amrah tabar wajan shima Aryan ya tashi daga wajan ya rage daga ita saishi.

Lemu ya tsiyaya cikin glass cup yana ƙokarin kaiwa bakinsa yaji saukar muryarta na faɗin"wani yana son na amincewa soyyayarsa a karo na uku"

Matse cup ɗin yay da ƙarfi ƙokacin guda glass cup ya farfashe a hannun har yan kassa yayi,murmushi kawai yay mata kafin ya miƙe tsaye yace"idan yay maki ki amince mana"yana faɗin hakan ya fici daga gidan gaba ɗaya.

Ji tayi ba taji daɗin abinda yay ba miƙewa tayi ba tare da taci abincin ba ta shige cikin ɗakinta,tana shiga ta faɗa saman bed lokaci kaɗan bacci yay gaba da ita tunaninsa fal zuciyarta.


Ɓangaran Amrah kam lokaci kaɗan ta fahimci abinda Aryan yake nufi akanta tunda ita ba ƙaramar yarinya bace da zata kasa fahimtar abinda yake nufi.

Ɓangare guda na zuciyarta na gaya mata wannan abun bazai taɓa yiyuwa ba domin yaya kike wajansa ta zarar shekara uku ai ba wasa ba,ita kunyama ta keji ace wai tana soyyaya da yaron data goya ta share masa majina da dai sauransu,kawai zata ɓoye masa da gani.

NAJEEB yaji daɗin amsar da Jidda ta bashi nan suka shiga soyyaya babu kama ƙafar yaro wani tym ɗinma yazu gidan Amrah a gaban Irfan ake saidai ya miƙe ya basu guri haka Aryan zai sashai gaba yayta dariya ko yace"zauna kallon ruwa yaro kwaɗo yayma ƙafa babu ruwan wani"tsaki Irfan yake ya miƙe yay ficewarsa daga gidan gaba ɗaya ya dawo kusan kullum sai yasha barasa ya kejin daɗi.


Manyan sun shiga maganar duk da cewa mahaifin ɗin Najeeb baya gari an saka rana biki 2week kacal.


A hankali yake murza kan mota basu jima ba suka ƙarasu Shoprite siyyaya sosai yay mata shima yaywa kansa da Huda da Taslim ta kwasarwa toy masu kyan gaske,shima wata ƙartuwar teddy ya ɗauka pink colour kuɗinta ya duba ya taɓe baki sabida yadda teddy yay kyau ya ɗauka kuɗinsa zaifi haka mutunci.


Bayan sun gama siyayyar yace "muje"tsayawa tayi tana raba ido tare da ƙiftasu kamar mara gsky,kallonta yay yace"akwai wani abune?"ya faɗa yana riƙe hannunta ganin wani balarabe ya zuba mata ido.


Runtsa idonta tayi da ƙarfi kafin ta ɓoye kanta a shoulder ɗinsa tace"babu pad fa" kut ya faɗa da ƙarfi saurin toshe masa baki tayi murmushi kawai yay yaja hannunta suka nufi wani waje,"ɗauki kallan wacce kikeso banda dai ta iyaye mata"turo baki tayi gaba ta ɗauƙi leda biyu.

Tsaki yaja yace "ke kwashi da yawa babu mai yimin tashin dare kona safe akan wannan abar"kunyace ta kamata amma hakan bai hana ta ɗiba da yawa kamar yadda yace ba.

Ice cream ta kwasarwa su Huda da yawa kala² wajan biyan kuɗi ya nufa ya zaro A.T.M ɗinsa aka cire sannan suka huce compound na Shoprite ɗin nisa yay mata sosai,ɗago kai tayi zatai masa magana ta hangi wani ya zura hannu a pocket na aljihun wani Alhj ya ɗauki walet ɗinsa,cikin sauri tasha gabansa walet ɗinta ƙarɓa tun kafin tayi mgn Irfan ya ƙarasu wajan walet ɗin ta miƙe masa tace ɗauka yay ajikin wajan.


Buɗe walet ɗin yay yaga ansa IMRAN MAI FATA cillawa ɓarawon walet ɗin yay sannan yaja hannunta da niyar barin wajan.

Kwacewa tayi tace"bafa tasa bace"..idon care" ya faɗa a zafafe "but i do"shine amsar data basa tana kwace walet ɗin daga hannun mutumin ta nufi wajan Alhj yana gaf da shiga mota tace"sir ur walet"amsa yay tare dayi mata gdy dasa mata albarka...bata tanka ba ta juya da sauri tana faɗin Irfan..Irfan a karo na farko Alhj ne ya rufa mata baya jin sunan data amba wajansa ta ƙarasa tare da riƙe masa hannu.

Hankaɗata yay ta faɗi haka tare da faɗin"get lost" yana faɗin hakan ya faɗa mota tare dajan motar da gudu yabar wajan...


*Fadar ummu faresat🥵matar kulle fans🥵Real ladingo fans🥵Marautar hasfst a garkuwa🥵Matar soja fans🥵wlh wlh zan daina yi maku posting tunda ba za kuyi alkunyar yimin comment ba kuma i knew kuna karantawa idan na daina posting ba shike nan ba😂😂*


Comments....Comments..Comments shine kawai mgn

[12/9, 5:50 PM] +227 99 46 01 51: ```💞HEARTBEAT💞```
*JIDDAH*

```MALLAKIN😘
ANTY NI'EEMERH
Nimcyluv```

CHAPTER 22-23
```BAD DREAM```

```Wattpad@nimcyluv```


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻


22-23

Motar tabi da kallo tana mamaki zuciya irin ta Irfan to meye laifin akan ta kaiwa mutumin da walet take mallakinsa,kodai yana goya bayan sata akan gsky ne,wasu siraran hawaye ne suka zubu mata kafin tayi ƙarfin halin sa hannu ta goge ɗan runtsa idonta tayi jin hannunta nayi mata wanda ta tabbatar bigewa tayi,tsaiwar mutum taji akanta shine ya bata damar ɗago kai ta kallesa da sauri ta miƙe haɗi da sunkuyar dakai domin ba tayi tunanin ganinsa a nan ma ta ɗauka tunda ta bashi walet nasa ya tafi,shima kallonta yay lokaci guda ya fahimci yarinyar bata da mgn haka bata son hayaniya shine ta kwanta masa a rai sosai" can i drop you home dear if you don't mine?" mganarsa ta sauka a kunanta,kai ta girgiza masa alamar "a'ahh"...
Juyawa yay badan ransa yasu ba ya nufi wajan motarsa yana zuwa drever ya buɗe masa ya faɗa cikin motar aka ja motar da gudu but he still looking for her.

Kalamar "get lose" daya faɗa ita ta dawo mata cikin kunanta shinme yake nufi da hakan da zai ɗauki wannan hukuncin a akanta,ina zata yanzu infact ma bata san inda za tace a kaita ba,ƙara gyara zama tayi haɗi zabga tagumi zuciyarta banda suya babu abinda yake domin ko kuka ta kasa wanda take fatan yazu mata ko ta samu sauƙi cikin zuciyarta.
Wani mutum ne ya tsaya gabanta tare da saka hannu ya ciro kuɗi duba ɗaya ya miƙa haɗi da faɗin"Allah sarki yarinyar kyakkyawa kuma ƙarama dayin bara abun babu daɗi"baki da hanci ta saki tana kallonsa yayin zuciyarta ta bada bugu damm da ƙarfi harsai data riƙe, laɓɓanta ta shiga taunawa a ƙoƙarinta nason furta masa ko kalla ɗaya ne amma ta kasa kafin tayi mgn ya ajjiye mata kuɗin gabanta yay tafiyarsa,sai a lokaci wani zazzafan hawaye ne ya shiga zubu mata daga cikin idonta badai kuwa kallon Al'majira yake mata ba.
Iskar wajance mai daɗi take ƙara kaɗawa yayinda gaba ɗaya jikinta yay weak ba tajin zata iya tashi bare tafiya wani wajan,ɗan jingina tayi da jikin bishi ta zure waje guda iskar sai kaɗawa take lokacin kaɗan bacci yay gaba da ita.


*IRFAN POV*

Sabida gudun da yake bai wani jima a hanya ba ya ƙarasu Faraw horn yaywa get man,get ɗin gidan aka wangale ya samu nasarar cinna hancin motarsa ciki,parking a parking space kwantar da kujerar motar yay a hankali ta kwanta dashi zuwa baya,laɓɓansa ya tauna a hankali ya kejin wani abu mai kama da damuwa yana shigarsa,mai yasa yake yawan tunaninta aduk wani fitar numfashi nata meyasa ya damu da damuwarta akasin ita da takeson abinda baya so,huci ya shiga fitarwa ta hancinsa gaba ɗaya jijiyar kansa ta firfitu waje gashin jikinsa ya mimmiƙe gaba ɗaya baya son damuwa domin idan ya shigeta bata yiwa kowa daɗi,hannu ta cikin motarsa ya buɗe booth kwalbar giya ya ɗauka tare da ɓalle murfin kwalbar ya kafa a bakinsa haka yay ta kwankwaɗa bai ajjiye ba saida ya shanye tas kasancewar ƙaramar kwalba ce,surutu ya shigayi kamar zautacce yana kallon lokacin da Aryan yaja motarsa ya bar gidan.
Idon sane ya fara lumshewa sabida giyar data fara kwasarsa wayarsa ya ɗauko tare da shiga folder photo nansa folder gudu yay pic ɗinta wanda bata san ya ɗauka ba,pics ɗin ya shiga gani wani da ɗan ƙwali wani babu wani kuma ta turu baki gaba wani kuma tana jagula abinci,akan wani pics ɗinta ya tsaya wanda bata san ya ganta da kayanba,wata rana tana bacci ya shigo ɗakin ya ganta a ƙwance ta rungome Teddy sai mamulal lips ɗinta take,beauty body ɗinta ya shiga kallah,daga ita sai three guater da vest mara hannu,tun daga foot ɗinta ya fara kallon jikinta har zuwa manyan laps ɗinta wanda gargasar gashi ta cikasu.
Lumshe ido yay yana jin wani abu mai kama da feeling na rasa dukkan wata gaɓa dake gangar jikinsa,ganin tabbas idan ya tsaya kallonta za'a iya abin kunya shine ya fitu da wayarsa ƙirar iphone 11 pro ya shiga yi mata snap.
Dalilin daya haryau pics ɗin ke cikin wayarsa idonsa ya manna akan wayarsa yana faman kallon photon nata kamar mai san fahimtar wani abu.
Wayar ya manna a ƙirjinsa ya shiga jera ajjiyar zuciya akai² a haka bacci yay gaba dashi a cikin mota.

*ARYAN POV*

A yau ya ɗauki niyar gayawa Amrah abinda ke zuciyarsa ruwanta ta amince ruwanta taƙi shidai ya gaji da dakwan wannan soyayyar tana gaf da illa tasa,sanye yake da blue ɗin shadda tayi masa kyau sosai sai zabga ƙamshi yake a haka ya isa gaban tamkeken get ɗin gidanta.
Horn yay mai gadi ya buɗe masa,kan motar ya tura cikin compound ɗin gidan yay parking a parking space,buɗe motar yay ya fitu hannunsa ɗauke da wata ƴar kyakkyawar leda mai cike take da gaya.
Tafiya ya fara harya isa ƙofar da zata sa dashi da babban parlo,shiga yay saida yay tafiya sannan ya karya kwana zuwa wata ƙofa tun daga nan ya fara jiyu surutu twinst,murnushi kawai yasa hannu ya buɗe ƙofar yana shiga idonsa ya faɗa cikin nata har kusan faɗuwa yay sabida mugun kyan da tayi masa.
Sanye take cikin wata blue blac ɗin night gwan wacce ta tsaya mata iya cinyarta rigar ta zauna jikinta sosai tayi tufke gashin kanta zuwa bayanta,idonsa ya ɗura akan lips ɗinta wanda ta shafa masa beby lipstic mai kyau.
su Huda ne sukayo kansa suna faɗin *UNCLE NE* uncle oyoyo,sama ya ɗaga Huda ya riƙe Taslim a hannu idonsa ya ƙara hurgawa inda ya ganta gani yay babu kuwa alamar ta gudu "weldone beb i'm coming to you" zaunar dasu yay haɗi da basu ledar chocolate nan suka fara tsalle da murna.

A tsurace Amrah ta shige cikin ɗakin tana sauke ajjiyar zuciya na excap ɗin da tayi daga wajansa,ƙarar kullen ƙofa taji a tsorace ta juyo.
ganinsa tayi jingine da jikin ƙofa ya lumshe idonsa,ba ƙaramin yau yay mata a idonta ba,sosai ta shagala da kallonsa ganin yana shirin buɗe idonsa ne tayi saurin ɗauke nata tare da juya ta bashi baya.
"ya beb nayi kyau oyya tell me mana kada kiji kunya i'm yours fa"
Ƙirjita ya buga damm bata ce komai ba sai sadda kanta ƙasa da tayi,ajjiyar zuciya ta sauke sabida hannunsa daya ɗura akan waist ɗinta murzawa yay kaɗan tare da juyo da ita gaba ɗaya zuwa gabansa .
Kallon juna suka shigayi kafin ta ɗauke idonta,hannunsa ya ɗura a shoulder ta ƙoƙarin kwace take taji gaba ɗaya ya jawota ya mannata a ƙirjinsa sassayar ajjiyar zuciya suka sauke gaba ɗayansu,bayanta ya ɗan buga kaɗan yace"ur heart beating so fast u miss ba?"kaita girgiza alamar a'a..ok les play a new game idan kinci na hƙr dake idan naci zaki amince min as ur husband..

*IRFAN POV*

Wani wajene wanda ya cika da ƙanan bishiyo haɗi da ƙorama masu kyau babu abinda yake tashi a wajan sai kukan tsuntsaye.


Please Login or Register in order to submit comment