Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai a lokacin.
Sai faman kulawa da warwarewa yake shi kadai a ran shi abin duniya duk ya damay shi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
1⃣2⃣

A LOKACIN MUKE,,,,,,


Nocking din kofan take a hankali yayin da take jin sautin kida ya na tashi daga dakin, sai dai ba a da niyan bude dakin a lokacin.
Kara sautin nocking din da takeyi tayi sai ji tayi ana cewa wai waye please ke damuna haka.
Mai dakin tana bude daki sai suka fara kallon kallo a tsakanin su don ba wanda yasan wani a cikin su.
Kina neman wani please ?
Har lokacin tana tsaye ta tare kofan dakin nata ta inda mutum zai iya shiga dakin.
A,a gurin ki dai nazo.
Ni kuma ta fadi cikin dan mamaki a fuskan ta tare da dan sake fuska tana dan kada idanuwan ta cikin mamaki.
Eh duk da dai nasan baki sanni ba amma dai gurin ki din ne nazo ai.
Ok tau shigo daga ciki mana ko ?
A tare suka shiga dakin a lokaci guda suna nuna a jere da junan su.
Kujeran dake dakin ta nunawa Raiha ta zauna inda Raihan ta gane nufinta ta ta zauna kamar yadda ta bukace ta da yi.
Juyawa tayi zuwa ciki sai gata dauke da kwalin juice da cup a hannunta inda Raiha take zaune tazo ta aje drinks din tana cewa bisimillah.
Raiha ko sai bin dakin take da kallo wanda dakin yai mata kama da ta mai zaman kanta ko kuma wace tazo karatu a garin.
Idon ta ya kai akan kwalaben syrup din maye dake saman wani dan table can gefe guda.
Kisha mana bisimillah ko sai takai idon ta akan kwalaben da Raiha take kallo, tace,
Ko kema dai yar hannu ce na miko maki ki surka dasu ne?
A,a barshi kawai ni sai dare nake sha idan zan kwanta yafi min caji don ina gudun mutane su gane ina wanan harkan.
Dariya Nura tayi har fararen hakoranta suka haska daga bakin ta tana cewa.
Kai har kin bani dariya wallahi ashe da sauran ki ke har yanzu dasha da rana da dare ai ni duk daya na dauke su a gurina.
Haka dai kika ce amma akwai banbanci gaskiya baki dai ganewa ne kowa da nashi irin ra,ayin nake gani.
Kurba biyu Raiha taiwa juice din sai ta aje cup din tana kallon Nura cikin murmushi.
Nura tace ni kin barni a duhu ban fa gane kiba gaskiya har yanzu gashi kuma kince guri na kika zo.
Raiha tace eh gaskiya baki sanni ba nima haka Sunana dai Raiha amma mutane suna kirana da Raihanatu musanman ma iyayyena.
Ok ni Nura nake karatu ne yakawo ni wanan garin ina karatu a dan fodio university ne.
A ran Raiha tace shikan karatu kikazo kika buge da harka ke nan a garin da ba,a sanki ba.
Raiha tace cikin murmushi ko kin san Nasir Habbib mai aiki a sokoto cement ?
Nura tace a ranta au budurwan Nasir ke nan ta biyoni don nai mata snatching din shi a gurin ta ko?
Aiko yarinya kinzo gida wallahi don zan maki wankin babban bargo yanzun nan kuwa.
Amma sai ta kyale a fili tana cewa nasan shi kuwa kwarai da gaske anjima kadan ma zaki ga yazo nan ai idan ya taso daga gurin aiki.
Raiha tace good zan iya kiranki da Anty Nura don ko ba,a fada ba nasan kin girmay ni.
Dafatan zaki saurari maganan da nazo maki da ita da kunnen basira batare da kin fassara min zance na ba da wani abu.
Ok ke nake saurare ina jinki ai.
Da farko dai kamar yadda na fada maki sunana Raiha kuma ni haifafan wNan gari ne muna zama a uguwar arkilla ne nida iyayyena.
Sai kuma tai shiru tare da dan kallon saman silin din dakin zuwa dan wani lokaci, Nura tace ke nake saurare fa kada mu bata lokaci.
Ba zancen bata lokaci ai don magana ce mai muhinmanci da zata amfane ki nazo dashi.
Tace ok ai ina sauraren ki ko?
Raiha tace kafin Nasir ya nemay ki ni Raiha ya fara nema amma sai Allah ya tsallakar dani daga mugun nufin shi a kaina.
Kamar ya mugun nufi kuma Nura ta tambaya a cikin mamaki da son karin bayani ga Raiha din
Raiha tace niyar shi na shigewa yan mata ya sace zuciyar su da so da kauna kamar yadda yake maki a yanzun haka.
Amma fa daga baya zaki zo ki sha mamaki don ba nufin shi ke nan ba a kanki.
Nura tace a gatsale Allah ko ?
Hmmm Raiha ta dauki cup din drinks din da ta aje takara kaiwa a bakin ta tadan kurba kadan sai ta juya gurin Nura tace.
Wallahi wallahi ifan bakiyi hankali ba a karshe zaiyi safaran ki ne zuwa kasa shen turawa ya tura ki karuwanci a can ya kuma karbe passport dinki duk gudin da zaki samu sai dai dila ya turo mashi ta account din shi.
"Ke
Kada ki maisheni karamar yarinya mana kedai kinzo da tsigar nabar maki Nasir don ki yaudareni da wanan magana naji tsoro nace ban son ki sai ya koma maki ko ?
Allah sarki babu ko daya wallahi don idan da na yarda da yanzu nima nazama tarihi a gurin iyayyena da yan uwana a nemay ni a gari a rasa inda na shiga.
Amma sai Allah ya kare ni da yake banda rabon wahala nasamu wani abokin shi ya tausaya min ya fada min ainihin gaskiyan abinda ke nan.
Raiha ta mike tana cewa ni zan tafi tunda naga kamar baki yarda dani ba yanzu amma nasan watarana zaki tuna da wanan dan zaman da mukayi dake.
Ni zan tafi kuma ban tsoron ki fada mashi cewa nazo gurinki don yanzu a shirye nake da na tona mashi asiri a harkan da yakeyi .
Ta juya tare da daukan jakarta dake saman kujera tana cewa idan kin shirya saurarena sai ki nemay ni.
Har Raiha takai kofa zata murda kofan Nura tace kinga dawo ki zauna ai bamu gama magana ba tukun ko?
Baki da niyar saurare na shiyasa kina ganin kamar kishin Nasir na tare dake yasani zuwa gurin ki ko?
Ba haka na bane amma akwai wasu yan tambayoyi da zan maki ina bukatan amsa daga gareki in naji su daidai kinyi gaskiya.
Raiha ta dawo ta zauna tana kallon Nura ido da ido tace ina sauraren ki ko?
Hmm wai ma ta ina zan fara tambayan ki ne duk kin sani a caji wallahi.
Duk ta inda kika fara in na sani zan baki amsa insha Allahu.
Ok tau dan Allah kunkai kamar tsawon wani lokaci dashi Nasir din a tare dashi.
Ummm gaskiya mun kai kamar wata takwas muna tare inda a sannu ya fara koya min wasu abubuwa na rayuwa.
Kallon ta Nura tayi da kyau tace hmmm lalai ma amma ce min yayi tunda matar shi suka rabu bai kara neman wata ba bayan ni.
A,a karya yai maki don kafin ni akwai wasu da har yai galaba a kan su yanzun haka suna waje on behalf of him suna karuwanci a Spain.
Kai wai da gaske kike da zancen ki ni yar uwa wallahi ba karya a magana ta sai tsabar gaskiya kawai.
Ok ya taba zuwa dake tafiya ne ke dashi kubar garin nan zuwa wani waje?
Tace kwarai mun je lagos da sunan yatafi aiki ashe yakaini ne gurin yan commuty din su sugan ni idan zan yi sai ya dawo ya shirya tafiya na.
Mikewa tsaye Nura tayi tana fadin ikón Allah na ko yarda da zancen ki don duk inda muka tafi sai naji ana cewa she is ok,
Very pretty you will get a high level on dis pretty,
Sai da nai mashi magana ya daina kaini ana fada min hakana don ban son jin wanan kallaman daga bakin arna.
Murmushi Raiha tayi tace a can bai nuna maki true color din shi ba ne ko ?
Kamar yaya Nura ta tambaya.
Murmushin takaici Raiha tayi tare da fara fada mata duk yadda yayi da ita a garin Iko din.
Mikewa Nura takarayi tsaye tace umm ummm na yarda da zancen ki gaskiya don nima ya jawo wani abokin shi akan na tarda mu kwana tare dasu su biyu amma bai san ina jin lokacin da suke maganan haka ba sai na bijire mashi tun kafin dare nace period yazo min.
Mikewa Raiha tayi tace nasan koke can akayi shiyasa nasa a saka min ido a kan shi nai alkawarin duk yarinyar da yai niyar batawa sai na kwatota daga halaka hannun mugu azzalumi mayaudarin banza macuci kawai.
Nan suka zauna sukai ta hira akan yadda zasu dau mataki a kan shi don kada yaci gaba da abinda yakeyi.
Tun wanan ranan suka kulla kawance da junan su inda ta rako Raiha tana mata godiya.

****** ********* ******
Tun daga kofa yake kwala wa mariya kira har zuwa cikin gidan, maria wace ke duke tana wanke wanke taji kiran a bazata yai mata yawa.
Ta mike tana fadin gani nan babban Abba lafiya dai ko kira haka daga waje babu kakautawa.
Yace cikin hasala yanzu naga malam a kasuwan mu yake ce min wai yaran nan yanzu basu zuwa makaran ta ko yaushe.
Shi Abba ma sai ya makara kullun kafin yaxo in ma har yaje din yace yai magana yan uwan shi suka ce wai talla yake zuwa.
Tace tallafa tallan may wani kallo yai mata na ban yarda dake ba fa.
Tace ba gaskiya bane in zai yi talla ai ban dora mashi ban fada maka ba balle ma nasan ba yarda zakayi ba.
Shi dai kila yara sunyi mai yawa yanzu bai gane zuwan su da rashin zuwan su shiyasa ya fadi hakan.
Yanzu ina suke ya tambaye ta tare da tsureta da idanuwan shi tace sun tafi tin da karfe hudu suna can.
Yace ai zan tafi nagani ko suna makarantan ya mika mata ledan ce fanen da yayo ya dauki buta zuwa ban daki.
Nan ta samu tafa leken zaure ko Aliyu yana tafe saiko gashi ya sayar rataye da roban shi na talla a wuyan shi.
Da sauri ta tare shi ta karbi roba da kudi tai mashi magana kuskus a kune yaron ya juya da sauri yabar gidan.
Kafin maigidan ya fito ta boye roban da kudin da sauri a dakin kayan su ta kama aikin ta.
Yafito daga ban daki yana fadin yanzu zan tafi nagani idan suna can ko kuma wasa suke tsayawa yi a hannya.
Yafita tana ce mai a dawo lafiya bai amsa mata ba don a cike yake ran shi ya baci sosai.
Don shi bai wasa da hakkin iyalin shi a kan shi don haka yake matukar saka ido akan al,amarin yaran shi dama ita kan ta matar tashi.
Tun daga nesa ya hango su a zaune gaba dayan su don haka sai bai karasa kusa ba ya juya zuwa kasuwa ko zai dan kara samun wani abin tabawa a can.
Kafin ya dawo yaran sun rigashi dawowa gida Aliyu da yuwan taci ta ishe shi abinci yafara nema yaci sannan yai wanka zakace bai tafi ko ina ba .
Taja ma yaran kunne akan duk wanda yace Aliyu yana fita talla sai ta yankewa yaro kauna a gidan.
Bayan maigidan ya dawo ne yake tambayan yaran inda suke tsayawa basu zuwa makaranta da wuri yanzu.
Sai cewa sukayi suna zuwa andai canza masu ajine malam baiganin su yanzu.
Haka yasa yaja bakin shi yai shiru ya yarda da maganan su tunda ya gansu dazun a makaranta sabanin yadda malamin ya fada mai.
Haka Aliyu yaci gaba da zuwa tallan ruwan shi batare da mahaifin su ya fahinci komai ba tunda shi ba mai zaman gida bane ko yaushe.
Haka yaron ke kawo mata dan kudi itako tana bunkasa bankin ta dashi kullun tana farin ciki.

****** ********* ******
Tun ranan da akai wanan rikicin a gidan hankalin Bintu a tashe yake da mutanen gidan baki dayan su.
Ance babban gida babban magana ashe har da ita da take ganin ta kama kanta da kowa a gidan bata tsira ba ga matan gidan.
Don har da zaman ta gurin Maji ya tsone masu ido sai yanzu tagane nufin maji na bata magani tare da sauran diyan ta a baya.
Gashi yau Alhaji da kan shi yake fadin korafin da sauran matan shi sukayi a gidan kan zaman ta da Maji.
Wanda ba komai suke wa kishi ba sai basu kaunan suga ta karu da komai kankantan abu a gidan,
Wanan dalilin gitinan yasa damuwa ya dan fara yiwa Bintu yawa arai sai kafa kafa take da komai a gidan.
Tun da har mai gidan yai mata warning din shiga harkokin mutananen gidan shi da kan, shi.
Sai lokacin take mai jin zafin gwagonta hajiyan masa da tazo gidan mutane ta yar da ita kamar wata wacce bata da uba ko gata.
Da uwarta da uban da ransu a duniya amma yau ta zama,marainiyar karfi da yaji a duniya.
Ba don Maji mace ce mai halin alheri ba da bata san iya inda al,amarinta zai tsaya,ba a,rayuwa.
Amma gashi Allah ya hada ta da mace tagari wace tasan ciwon kanta tasan zafin ta a rayuwa.
Ta rike ta amana tankar itace ta haife ta ko kuma ince wata yar uwarta ta jini can daban.
Yanzu Bintu ko falon maji bata son zama da yawa ko yause tana cikin dakin su a kumshe.
Idan kuma aiki tafito yi zata yishi gudu gudu ta gaba ta kara komawa tashige daki wai ita tana taka tsatsan da kanta.
A haka zancen tafiyan sadauki zuwa kwallon farko da zai fara fita ya buga yazo masu.
Maji bata zauna ba sai faman karban taimako take akan dan nata akan shaye shaye da kuma na tsarin jikin shi.
A cikin hakane maji tace wa yaranta su shirya sukaiwa kakan in su ziyara kafin yatafi don kada sai yatafi su samu labari baza suji dadi ba.
Sadauki bai so wanan tafiyan ba amma ba yadda zaiyi ya zama dole yabi umurnin iyayen shi.
Sai faman shiri suke amma Maji bataji duriyar Bintu ba don ko falo bata fito ba don ba,a shiga makaranta ranan.
Da kanta tashiga dakin na yaran tun zuwan Bintu gidan ko yaushe zaka samu dakin tsab dashi ba wani datti a cikin shi kaman baya can da dakin yake motsutsu kowa na kyashin gyarawa .
Kwance ta samay ta ta kifa kanta a saman filon da ta ke akai.
A hankali maji takira sunan ta,da Fatima abinda ya dan sata firgita ke nan don bata san da shigowan Maji dakin ba a lokacin.
Cikin dan firgita ta amsa da na,am mama tare da saurin kokarin mikewa zaune daga kwanciyan da take.
Zama maji tayi daga gefen ta tare da dan kura mata ido tana cewa waiko lafiyan ki kalau kuwa Fatima?
May ke damuwanki ne duk kwanakin nan kin koma,shiru kina kuma nisanta kanki da kowan mu?
Dan murmushi Bintu ta kirkiro a fuskanta tana cewa ba komai mama kaina ne ke dan ciwo shine nadan kwanta.
Tun yaushe kanki ke maki ciwo baki fada min ba fatima baki sha magani ba yaya zaki ji sauki.
Shiru Bintu tayi tana fadin dama gashi zamuyi tafiya zuwa garin mu gobe tunda safe gashi kuma baki da lafiya.
Don haka dole na barki nan har mu dawo don ba,a daukan ciwo akai kauye.
Da sauri Bintu ta daga kai ta kalli Maji, sai kuma ta dukar da kanta don bata iya jure kallonta ido da ido haka.
Maji da ta fahinci may Bintu take nufi sai tace kada ki damu ba,a nan zanbarki ba gurin hajiya kubura zan barki don kwana biyu zamuyi mu dawo insha Allahu.ko kuma guda yadda dai tafiyan namu ya kasance don wanan mai tafiyan.
Bintu ta kara kallon Maji alaman ranta baizo hakan ba take cewa mama da abarni ko anan din zan iya zama ai.
A,a haba Fatima yaya zanbarki karaman yarinya dake a daki ke kadai kuma gashi ko lafiya,bai isheki ba ma.
Kada ki dmu nasan zata rike ki da kyau har mu dawo daga tafiyan, kamar Bintu tace taji sauki zata tafi amma kuma sai take cewa tau mama.
Maji tamike tana cewa don haka saiki shirya kayanki wanda zaki dauka tun yau ki koma can.
Bintu tanaji tana gani Maji da kanta ta dauki dan jakar kayan ta zuwa dakin hajiya kubura.
Nan suka dan zauna suka taba hira a tsakanin inda tai mata sallama dacewa gobe asubanci zasuyi zuwa tafiyan su.
Hakan akayi don koda gari ya waye har sun tafi ko don can ne kauyen Niger state iyayyen ta suka koma da zama don noma.
Bintu bata farka,ba don maganin da tasha mai sa barci sai zuwa takwas na safe lokacin har hajiya kubura ta shirya zuwa gurin aiki tana cikin uniform din ta.
Dakin da Bintu take ta leka tasamay ta zaune tana lazumi ta idar da sallah a lokacin.
Kin tashi Binta ya jikin naki Bintu ta amsa a sanyaye da Alhamdullahi ga breakfast din ki a falo idan kinyi wanka sai kici ni zan fita sai na,dawo.
Sai kindawo mummy ta bata amsa tare da kokarin mikewa da ga saman abin sallah da take zaune akai.
Zuwa rana kadan ta dan samu sauki nan ta mike tafara gyaran part din sai da taima ko ina tsab a part din sai bedroom din mummy ne kawai da ke a kulle bata gyara ba.
Tana gamawa tashiga tai wanka bayan tafito ne ta dan zauna sai kuma tai tunanen kada su dawo da yaran ta basu samu abinci ba.
Kitchen din ta shiga inda ta samay shi sabanin na Maji don wanan komai na zamani ne a cikin sa.
Ga kayan abinci na kala kala babu abinda babu cikin sa komai gashi kamar ba saye akeyi ba.
Ta yanke shawaran tai masu tuwo don taga kullun yaran ta na zuwo rokon tuwo a gurin maji don ita bata da time din tukawa ko yaushe busy take.
Nan ba bata lokaci ta girka tiemwon shinkafa da miyan agushi da manja tai amfani da naman da tagani a fridge din.
Gashi ranan girkintane ta kwashe a wani kula da bai saurin sanyi takara hada masu pepper surp din kayan cikin rago da drinks din hannu na kayan fruit din data gani a kitchen din.
Takara gyara gurin ya koma tsab takoma daki ta kwanta sai yamma mummy tadawo da yaran ta inda tun a,wajen part din ta soma ganin canjin yanayin shiyan nata.
Tana shiga dakin gaba daya taga duk ya canza mata sai ta tuna da lokacin da take amarya a gidan komai nata tsab yake a lokacin.
Ba irin yanzu ba da,bata da lokacin tsayawa gyara komai kamar yadda ya dace mace tana gida tayi.
Yaran suna shiga daki suka fara ihun da murnan ganin yadda komai nasu ya canza a lokaci guda.
Dan karamin sune yafara maganan abinci Bintu dake fitowa daga dakin da take ciki take cewa Anwar zo ga abinci can kazo kaci taja hannin yaron inda ta tsaya daga kofa tanawa mummy sannu da dawowa.
Mummy tace Bintu ke da baki da lafiya kika sha wanan aiki haka sannu da fama nagode.
Tana fitowa taga Anwar a hannun ta take cewa kaikuma may yafaru Bintu tace wai abinci zaici.
Uwar tace kaida andawo kace zakaci abinci har yaushe muka dawo na girka maku abinci.
Bintu tace a sanyaye mummy ai na yi girki tun dazun ma nagama bari na debo mai.
Da mamaki uwar tace kinyi girki Bintu bayan wanan uban aikin da kikasha haka.
Murmushi Bintu tayi ta juya rike da hannun yaron ta debo mashi abinci ta zauna tafara bashi.
Saiga Mummy tafito daga daki idon ta ya sauka akan plate din da yaron ke cin abinci take taga mai Bintu ta girka masu.
Wani irin dafi ne ya kumay ta tace kai amma wanan yarinyar Allah yai maki albarka.
Nan tashiga kitchen ta samu komai tsab kamar ko ina mamakine ya kama yadda karamar yarinya kamar Bintu tai irin aiki haka mai yawa ita kadai.
Gashi kuma,ba lafiya ne take dashi ba ajikin ta take taji kwadayin zama da yarinyar ya kamata don irin haka take son yaron ta dashi.
Ba,wani abinda aka taba mata ko aka lalata hatta sharan da tayi bata zubar ba ta tara a wani roba har mummy din tazo tagani idan babu abinda take so daga ciki dai a zubar dashi.
Haka mummy ta dinga jin dadin zama da Bintu kamar kada uwar rikon ta tadawo take ji.
Suko matan gidan ai nan gulma ya fara tashi akan zaman Bintu gurin Hajiya kubura na kwana biyu kafin maji ta dawo don ance babban gida ba,a raina dan magana kadan,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,,
1⃣3⃣

A LOKACI MU KE,,,,,,



Bintu bata da wani matsalar komai tsakanin ta da mummy da take zaune a shiyan ta.
Don mummy dai irin wayyayun matan nan ne masu faraf faraf da mutane ba,a gane gaskiyan cikin su.
Wata, yammaci da dare, Bintu tana kwance tana barci don yayi saurin kwanciya don ta gajiya sosai gashi bataci abinci ba da yunwa ta kwanta hakana.
Cikin dare yunwa ya damay ta don haka ta bude idon ta don ta sauko saman gadon da take kwance akai.
Tana son fitowa zuwa kitchen don dauko abincin ta da bata ci ba a daidai kofan dakin mummy take jin sautin muryan ta tana waya kamar haka.
Wallahi ina fada maki yau kwanan ta uku bata gidan tana can garin su ana mugun a bu,
Yanzun haka yarinyar da take gurin ta,da nake fada maki tana dakina ta barta ba,aje da ita ba.
Wai kin san may wallahi ni kin san ba yarda nayi da su ba matan gidan nan baki daya.
Kada taje can ta yi sa,a har ta samu galaba a kaina, don nasan kowan wansu ba wai ta zauna bane.
Duk yadda za,ayi gobe ki je min gurin nan ya kasance duk abinda ma taje garin su ta kullo a lalata min shi baki daya.
Bintu bata tsaya ta karasa jin komai ba ta juya a hankali ta koma dak8n da take ciki kwance,
Jin motsin mummy tayi don haka tamike zuwa dakin da Binta take kwance a ciki tagani in

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment