Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gurin yan duniyan da suka fita iya duniyan ci sosai.
Taro yai tsit saboda fara gabatar da bukin da,aka,soma wanda suka ce sunyi shi ne don tunawa da kafa gungiyar su mai shekara biyar da,kafuwa yanzu.
Inda,wasun su sin mutu wasu kuma,sun dain harka suna wani kasar haka dai maigabatar wa yai ta bayane na,shirmay a guri a na ihu da,sowa irin na yan iskan matasan zamanin nan.
Sai kuma aka fara rawa da da,zagaye duk wanda aka jefa a bu ya fada a kan shi dole ya fito yai rawa ko a ci mai shi taran kudi.
Irin wanan jifan ne koda aka jefo sai abin yafada akan jikin Raiha wace ke can ta juya tana magana da kawar ta.
Jin an sa ihu yasata juyawa don ganin may akewa ihu haka,sai jin kyalen rawan tayi a kan ta inda,zasuyi rawa da,wani sauri dan dogo fari dashi.
Dole badon Raiha ta so ba ta mike tafita filin don bata da kudin biyan tara har dubu biyar idan bazakai rawan show ba.
Fitowan ta yasa mutane da,dama gurin suka,san da,zuwan ta a,filin, inda aka sa masu kidan tausi watau cool music,
Rawa na ban mamaki sukayi da saurayin a filin inda,suka bada show yaron ya,dinga juyata yadda ake rawan kidan na ai nahi.
Wanan abin ne ya haska Raiha,a idon mutane don dama Raiha yarinya ce mai kiran mata duk wani abinda ake so gajikin mace ta mallake shi ko.
Wani matashi wanda tun fara,event din ya kafa hular shi a gaban goshi kamar baya kallon abinda ke faruwa a gurin ya mayar da hankalin shi a kan raiha,sosai.
Yarinyar ta,tafi da imanin shi don haka ya yanke shawara a,ran shi cewa dole ne ya nemay ta don ya gana da ita,yadda yake so.

****** ********* ******
Yanzu abubuwan sun dan yi sanyi wa Maji akan Sadauki don tun ranan da tai mafada sai ta dan samu sauki daga gare shi.
Don haka shawaran hajiyan masa yai mata rana a gurin ta sosai maimakon fada na fitan arziki ga yaron yanzu nasiha da ban baki yafi komai sauki ga yaron yau.
Don yanzu sam ba ruwan shi da kowa gidan kwata kwata yafita batun yaran su amma fa idan ka,shiga shirgin shi duk da haka bai ragawa mutum.
Safiya ce matan gidan kowa sai harkan gaban ta takeyi ba,ruwan wata da wata a gidan kowa tasa tafisshe ta haka zaman su yake.
Sallaman Bintu ya,dakatar da Maji daga aikin da takeyi daga cikin uwar dakin ta.
Tafito suna gaisawa da maji a cikin mutunci da ladabi da tsintsiya a hannun ta Bintu sai take mika mata ledan da,gwagon ta, ta bata ta kawo wa maji din.
Tare kuma da karban tsintsiyar dake hannun Maji Bintu ta karba duk da Maji ta so hanata amma yadda ta marairaice yasa Maji mika mata tsintsiyan sharan.
Nan ta kara yabawa da hankali da tarbiyan yarinyar tana dama ace nice da haihuwar wanan yarinyar ma hankali da sanin ya kamata haka.
Tas ranan Bintu taiwa dakin tare da kawar da komatsan dake a fili ta,shige mata dasu daga ciki don yanzu dama duk Maji ta sukurkuce bata da,wani kuzari a jikin ta saboda dafin bakin cikin dan ta ya fara tabata sosai.
Bayan Bintu ta gama da gyara waje ta kofan part din Maji ne ta shigo dakin tana,saye da dan hijjab din ta mairuwan cingan .
Tana cewa Mama na rarage ni zan tafi gida kada gwago taga na dade ban dawo ba.
Nagode Fatima Bintu Allah yai maki albarka Allah ya albarkaci ruwan ki, Bintu ta amsa cikin yar muryan ta, da Ameen mama nagode.
Ta fita daga gidan matan gidan sai binta da kallo suke da take aikin suna mamaki don dai su sun san yaran su basu iya wanan aiki da yar karamar yarinya tayi haka.
Duk wanda ya,shigo ya,samu yadda Bintu ta gyarawa Maji guri sai yai maga suce kai Maji amma yau kan kun sha aiki sosai maji waban gyaran guri haka.
Tace wa Ameera bani fa nayi shi ba yar gidan hajiyar masa ce ta gyara min shi haka ta shigo ta samu ina shara sai ta karba shine tai min wanan aikin haka,
Yarinya yar albarka da ita da mutunci ga sanin ya kamata a yar karamar yarinya da ita haka.
Amira tace ni dai yarinyar tana bani shawa wallahi don tasan girmama na gaban ta sosai.
Har maigidan sai da yaiwa Maji magana dacewa yau shiyan nan naki yai min kyau ga kamshi na tashi sosai.
Murmushi maji tayi tana cewa ya ta yar albarka tazo tai min wannan aikin yar gidan hajiyar masa na makwabtar mu
A,a tayi kokari su wayan nan katar banzan may sukeyi ne da,bazasu iya gyara guri ba,sai wata tazo ta gyara masu.
Maji tace halin yaran nan ai sai su don ko sunyi basuyin yadda wanan karamar yatinyar tayi.
Tun wanan rana kwana bibiyu sai Bintu ta shigo gidan gurin maji ta dan yi mata aikin da ya kamata tai mata sai ta koma gida.
Sannu sannu har Bintu tafara fahintar cewa Maji tana fuskantar matsala a gurin mutanen gidan don basu kaunarta sam.
Ga fitinar dan ta da koyaushe ya shigo gidan tana jin yadda yake uwar ke fama da shi akan wasu matsalolin da bata fahinci aini cin yawan laifin da yakeyi ba ako da yaushe don maman nashi bata fitowa fili tafadi sai dai taganji tana cewa.
Baba kaiwa Allah ka rufa min asiri ka,daina halin nan naka don girman Allah.
Sai ya kan katse uwar da wani irin magana a gala baice da cewa ni mama mai nayi ne wai kullun ace wai mutum yai laifi.
Sai yafita a kasalance yabar dakin zuwa waje maji kan bishi da kallo har yabar dakin ta sauke ajiyan zuciya tace Allah ya kyauta.
Yawan ganin da Sadauki yakewa Bintu a gurin mama bai sa ya,sake da ita ba asalima dai shi yarinyar haushin ta yake matukar ji a,ran shi sosai.
Don tafaye yin abu kamar muna fuka idan ta ganshi ta kama dan noke noke ke nan kamar taga dodo ko mugu bata jimawa zata bar dakin ta ce ita zata wuce duk yadda maji tayi ta tsaya bata yarda ta tsaya idan yana nan part din.
Gwago tana son zuwa kauye don uzuri na tafiya ya taso mata zuwa gida shine taga bazata iya barin Bintu gida ita kadai ba.
Don haka tazo da kanta gurin maji tana neman arzikin Bintu ta zauna a gurin su har ta dawa daga gida.
Don babu damar ta tafu da ita a na cikin makaranta a lokacin ana karatu ne ba hutu akeyi ba.
Da yar ledae kayan ta tazo gidan aka sauketa daki daya dasu Amira da maryam.
Tunda gwago ta, tafi a takure Bintu take gidan su Amira din koda kowa yana falo Bintu tana daki ita bata fita zuwa ko ina ko kallo bata fitowa tayi a falon kamar yadda kowa keyi.
Yau da ya dawo daga wasan ball ya samu maji a kwance bata jin dadi don haka tana ganin shi tasan cewa abinci ne ya kawo shi don haka daga inda take kwance ta kwalawa Bintu kira tazo.
Mamakin jin tana kiran wani bakon suna daga ciki Umar keyi sai dai halin shi bai barin ya tambaya ko bakuwa,ce uwar tayi mai suna hakan.
Bintu tafuto tana saye da dan farin hijjab din ta a jiki don dabiar tane bata zama jiki ba hijjab ko kadan.
Mama gani inji Bintu duk da jin muryan ta da jin muryan ta da yayi ta shigo da sallama bai sa ya dago kan shi ba daga abinda yake a,wayan shi ba.
Bintu don Allah kawo wa yayan ku abincin shi kin ji,
Tau mama tace tare da juyawa zuwa dauko mai abincin dan lokaci kadan sai gata da ture ta ta dauko kayan abincin har ruwa duk a cikin ture din.
Kujeran da yake zaune akai hankalin shi a,waya ta nufa, ya dora kafan shi daya saman daya.
Ya mayar da bayan shi a makarin kujeran da yake sama zaune yana ta faman la tsan wayan shi.
Bintu ta karaso gaban shi ta dire mai turen abincin a gaban shi ta juya da,sauri zata bar falon,
Muryan shi taji kamar mai jin barci bayan ta juya yana cewa,
"Ke, yace da dan karfi abinda yasa Bintu ta,tsaya guri guda cak ke nan bata daga kafa ba kuma bata juyo ba.
Kizo ki zuba,mana zaki ajewa mutum abinci hakana kamar wata yar kauye can dalllah,
Da hanzari Bintu ta juya don bin Umurnin shi ta duka tare da jawo plate tafara zubawa a plate din dake cikin ture din.
Sai da Bintu ta shake plate din fam sannan take cewa nazuba tana shirin mikewa.
Ke Uban wa zai ci wanan abinci haka kamar jaki ko an fada maki cewa kowa irin ki dan kauye ne.
Kai Babana inji Maji wanan wani irin hali ne maka yarinya ta,dafa,ta kawo maka kuma cine kawai naka har kake kokarin kiran ta,da,sunan dabba.
Ke wuce ki shige abinki kinji Bintu kar ki tsaya,sauraren shi da zancen banzan shi.
Da hanzari Bintu ta juya zuwa cikin uwae dakin mama inda dakin su yake da,su Amira gaban ta yana faduwa irin yadda yai magana ya bata tsoro sosai.
Tun ranan bata son taji koda muryan shi don tsoro yake ba bintu din idan ta gan shi.
Da wani dare yashigo gidan sai wani lumshe idanuwan shi yake anyisa,a Bintu ma tana falon do Amira ta takura mata tafito suyi kallon wani hausa film sabon fitowa.
Bayan ya,samu guri ya zau a suka,shiga gaishe shi daya bayan day suna mashi sannu da,zuwa,
Ya zauna tare da mayar da hankali shi ga mahaifiyar su da ke zauns daga gefe saman salaya tana jan casbi ta a hannkali suka gaisa dashi daga gurin da take zaune ,
Sai dan wa lokaci ya dan nisa yanacewa Maji abinda yasa ta,dawo da hankalinya ke nan gurin dan nata don tasan magana yake son yi da ita.
Yace dama nazo maki da wani magana ne akan al,amarn da ya,shafe ni.
May kuma ya faru ne babana Maji dama ina son fada maki ne na,samu wani contarac akan zancdn ball din da nake yi wasu club suna son dauka na zuwa yi masu wasa.
Cikin sauri Maji tace ban amince ba kaji na,fada maka kada ka,fara ka,tayar da,zancen nan har wani yaji ko mahaufin ku a gidan sai nai matukar bata maka rai wallahi kaji na fada maka gaskiya.
Kallon mamaki yakewa mahaifiyar nashi don tabashi mamaki don shi a,zaton shi yai tsanmanin zatai farin ciki dajin wannan labarin tunda kullun gori take mashi akan wasan ball din da zaman banza bai zuwa shago kamar sauran yan uwan shi na, nagidan da,suke taya mahaifin su sana,a.
Shiru yayi tare da,dukar da kan shi guri guda bai daga ba har tsawon wani lokaci .
Tsam Bintu ta mike zuwa ciki don tsoro takeji naganin fushin wanan jarumin kada ya hada fushin shi dasu.
Maji amma,wanan abin fa alheri ne sosai idan har anyi nasara akai don Allah ki bari naje.
Bazaka banace na fada maka,gaskiyan magana ta ke nan har cikin raina .
Nan ma da kake a gaban mu yaya muka kare dakai balle can inda babu kowa naka.
Shiru yayi sai ya mike zuwa fita Maji tace abinci fa yace makoshi kawai yasa kai yafita daga dakin.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

A LOKACIN MU KE,,,,,,
5⃣

Ya na fita daga waje ya,ci karo da,bucket din roban da mama ta,aje a tsakar gida shuri daya yayiwa bucket din din yai sama ya maku da,bango.
Ji kake pappp karan fashewan bucket din da ya maku da bangon dakin mama Asiya ji kake tayau,
Da sauri mama Asiya tafito daga dakin ta,tana ganin irin ta,asan da Umar yai mata tafara salati tana tafa hannayen ta cikin salalami da mamaki.
Maijjidda fito fito kiga,ta,asan da,danki yai min, dan iskan yaro kawai mara mutunci, kawai bucket yana aje may ya tare maka don kawai kana haushina zakai min wanan aika aikan haka,
Bari ubanka ya,dawo yau gidan nan akwai ta don sai an biyani kudin bucket dina a gidan nan.
Haka mama Asiya taita faman masifa inda take shiga ba nan take fita ba sai yan kore da suka fito kara zugata tana hawa.
Maji dai tana daki bakin ciki da takaici ya hana ta fita waje a lokacin.
Sai dai duk abinda suke fadi a kunnuwan ta yake irin yadda suke kara aibanta mata yaro duk da ran ta ya baci amma bata da bakin magana dan kuka maija wa uwar shi jifa.
Sadauki ya jawo mata wani sabon masifa don tasan yadda mama Asiya ta fadi sai an biya ta haka zancen yake sai an biyata din.
Don haka ta mike tsam zuwa kuryan dakin kwanan ta ta dauko kudi, a take ta dauko kudi taba Amira wai ta sayo mata bucket.
Haba maji don kawai tace sai anbiya ta basai taje gurin shi shida ya fasa mata taje gurin shi mana in ta isa, ya biyata abinta.
Maji tace,ban son rashin kunya Amira ki tashi ki tafi inda na aike ki kawai.
Bintu tace mama kawo naje yanzu zan dawo sai maji tace a,a Bintu yi zaman ki bari dai Amira din ta tafi.
Mama barshi kawai ni na tafi anty Amira ta huta kawai ta duka ta karbi kudin daga hannun Maji ta saka silifas din ta dake ta kofa tafita daga dakin.
Inda Amira ke zaune Maji ta dan kalla tace kin ga ikon Allah karamar yarinya haka da kaifin hankali,
Don tafahinci baki bukatan zuwa yasa ta karbi kudin ita ta tafi, da sauri Amira ta daga kai ta kalli maji tace bance banzuwa ba maji ,
Allah dai ya kyauta Amira ina tsoron kada ke ma kizo ki zama min irin dan uwan ki nan gaba wallahi.
Haba maji don Allah kibar fadin haka mana idan ranki ya baci kiyi hakkuri don Allah ta fadi a,dan marairaice,
Allah ya kyauta ta furta a fili a cikin zuciyar ta kuma fadi take ya Allah ka shirya min yaran nan shiri irin na addinin musulunci.
Wannan adduan ya zama kamar waka a bakin Maji don duk abinda take adduan ta akan zurian ta dana sauran yan uwa musulmai yake.
Exactly kalar roban da ya fasawa mama Asiya Bintu ta sayo don ma saida tai yawo kusan shago uku ta samu roban.
Gap da zata shiga gidan ne a daidai side din samarin gidan dake daga wajen haraban gidan ta hango shi zaune yai zaman kamar tsuguni saman dan dakalin dake gurin.
Kamar ance ya dago kai ya hango bakuwar yarinyar da yake yawan gani dakin mahaifiyar shi yanzu tafe da buket din roba kalar dayai shuri dashi a cikin gida kuma tun kan ya karasa fita daga gidan yaji bambamin mama Asiya akan wai ya fasa mata buket wanda ba ma fashewa yayi ba.
Daga hannun buket din ne ya balle hannu daya na bucket din ya balle daga jikin roban.
Sauri take ta shige gidan sai taji muryan shi kamar daga sama yace.
"Ke,
Cak taja ta tsaya don balain tsoron shi take ji don ko yaushe fuskan shi babu rahama cikin shi, don har takanyi mamakin ace wai wanan mai siffan bugai yafito daga mace saliha kamar Maji.
Zo nan yace mata inda ta dan taka a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, har ta karasa gurin shi.
Waya aike ki sayan wanan robar ya tambaya cikin daga muryan shi.
Cikin dan in,in,niya take cewa, mamace tace na,sayo mata,
A gatsale ya tambayeta, waye mama ? Don ya tantance ko wa ya aike ta sayen robar.
Bintu tace mama ta dakin ku, kina nufin Maji ke nan, tace eh cikin daga kanta.
Miko min bucket din kice mata na karba ya,fadin cikin dakewan fuska mika mashi tayi ta juya simi simi ta shige cikin gidan yabi bayan ta da harara yana fadin munafuka kawai.
Maji tana zaune Bintu tashigo gidan tana dan kiukiu da idanuwar ta alamar damuwa a fuskan ta.
A,a Bintu ba,a samu roban bane ko kudin shine baikai ba?
Kafi Bintu tai magana Amira tace a,a ya za,ace ba,a samu irin roban ba kodai baki san inda ake sayarwa bane ?
Harara Maji ta maka wa Amira da sauri taja bakin ta tai shiru tare da kawar da kan ta don tasan har yanzu Maji a kufule take da ita ke nan.
Bintu tace na,sayo amma ya karbi bucket din a gurina.
Shi wa ya karba ?
Shi wanan yayan namu da ya,fasa roban yace na bashi roban dana sayo din .
Sadauki ke nan ko ?
Eh shi yace na bashi nace ya karba.
Mikewa Maji tayi ta saka hijjab din ta ta nufi hanyan waje fuuu a cikin fushi da hasala.
Ya na kulle kofan dakin shi zai fita ne Maji ta karaso gurin tana fadin miko min roban mara mutunci kawai.
Wani kallo ya waigo yaiwa uwar sai kuma ya,dukar da kan shi kasa ya dan fara kokarin bude kofar dakin shi daya rufe.
Yafito da bucket din yana cewa wallahi matar nan yar rainin wayo ne naso ne ki barni da ita, tun da tace yau akwai balai akan bucket din roba a gidan nan.
Fisgan roban Maji tayi daga hannun shi ta watsa mai harara tana cewa.
Duk abinda tace waja min ida baka taba kayan ta ba ai bazatai wanan fitinan ba.
Ksi tayi sadauki tunda na fahinci kwanciyar hankalina ne baka bukatan gani a duniya.
Maji ni fa ba haka nake ba ki barni kawai na wuce gurin kwallo na in huta da wanan munafukan matan.
Anki a barka anan ma da kake yaya aka kare dakai balle ka sa kafa ka tafi wata duniyan da babu mai kwabon ka a can.
Indai zaka gyara halinka ka gyara don bakai kadai bane yaro a gidan nan da kullun a ce sadauki dai sadauki.
Ta juya zuwa cikin gida kamar yadda tafito a hasale daga gidan da farko.
Maji bata shiga daki ba,saida takaiwa mama Asiya bucket din dakin ta takuma bata hakkuri akan ta yi hakkuri da halin sadauki din .
Ba kunya mama Asiya takarbi bucket din tana zuba bakar magana tana cewa wallahi da ba,a,sayo min kayana ba da yau akwai magana a gidan nan.
Da maji ta shigo lokacin Bintu da su Amira suna zaune a falon ta, Amira ce tace bai bayar bane maji ?
Kamar yaya bazai bayar ba aiko ya sha giyar wake ne bai fara shi wallahi.
Sai Amira din take cewa to Maji ina shi tsohon bucke din ai naga bai wani fashe ba fa .
Amira ki fita idona don ni ba,sa,ar ki bace, don naga kina son raina ni.
Shiru Amira tayi tare da kokarin mikewa tabar falon don gudun fadan Maji a kan ta don yanzu tana sauke mata haushin dan uwan ta a kan ta in batai hankali ba.
Inda Bintu take Maji ta kalla tana cewa Fatima kinci abinci kuwa, cikin sauke ajiyan zuciya a hankali.
A cikin natsuwa Bintu tace ina jiran su anty Amira ne muci tare dasu.
Haba Bintu kada ki biyewa wa yan nan don su cin abinci a gurin su kamar shan zuma ne sai sunga dama suke ci.
Tashi kici abinci kada gwagon ki ta dawo ta samu kin ramay kan wa yan nan mara sa kai.
Haba mama aiko suna da kai adduan ku a gare mu shine takin mu akoda yaushe cikin murmushi da kwantar da murya Bintu tai maganan ta.
Allah sarki Allah yai maki baiwa da kaifin basira karama dake Bintu amma kin san abinda ya kamata ko yaushe.
Tashi jeki ki debi abinci kici mai isar ki kin ji diyata Allah ya bar muna ku.
Bintu ta mike a hankali fon bin umurnin maji amma bafon ranta nason cin abincin ba ta shiga kitchen din su ta dan debo abinci dan kadan a cikin plate tare da ledan ruwan pure wata.
Maji tabi abincin da kallo tana cewa haba Fatima wanan dan abincin may zai maki ashe shiyasa baki kiba don baki son cin abinci sosai.
Ko har yanzun kina kewar gwagon ki ne kin ki sake jikin ki da mu.
Murmushi Bintu tayi kawai tare da cewa a kunyace a,a mama ai ban damu ba.
To dayafi maki don ko gwago ta dawo zance tabarki a nan don halaiyar ki ni dai yana min wallahi saboda yaran nan su dan kara daukan darasi a gurinki.
Don duk irin halaiyar yaran gidan nan shine diba,ar su a rayuwan su basu san halin rayuwan duniya ba.
Da,sauri Bintu ta dago kai tana kallon Maji sai kuma ta dukar da kanta tana dan juya abincin dake cikin plate a hankali ba tare da takai a bakin ta ba.
Yadda maji take jin sha,awan Bintu yasa take so da kaunar yarinyar har cikin ran ta ganin zata takura mata yasa maji ta dan mike tabar falon zuwa waje.
Bintu tana gamawa ta kwashe kayan zuwa inda suke wankewa ta wanke har ma da wanda tagani saura a gurin duk ta hada ta wanke su.
Daidai zata shigo da kayan, maji ta ganta take cewa Fatima baki hutawa duk aiki bai baki wahala ke.
Murmushi kawai tayi ta,shige da kayan ciki ta aje tana fitowa ta shiga wanka don magariba ya kawo jiki a lokacin.
Tsab Bintu tafito cikin wasu kayan da aka bata na Amira an gyara mata sun mata matukar kyau kamar don ta aka dinka kayan dama.
Maji dake zaune ta idar da sallah tana jan tasbaha takalle ta lokacin duk suna falo da yaran ta a zaune.
Duk suka bita da kallo a lokaci guda ta,zo har inda Maji take zaune tana cewa ina wuni mama.
Kai Maji dake lazumi ta kada mata tare da daga mata hannu Bintu ta mike zuwa bakin dayan kujeran ta zauna a kasa.
Maryam ta kalleta tana cewa may yasa ke baki son hawa saman kujera ne Bintu bata ce komai ba sai dan halinta watau murmushi.
Can suka fara jin dan hayaniya daga cikin gida yana tashi inda duk sukai shiru suna saurare don suji may ke faruwa ne wai.
Maji daga inda take

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment