Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan ki da adduan neman ashiryuwan daga Allah dan yanzu ke ce da matsala basu ba.
Kara jajircewa ki koma haikan gurin ubangiji tare da nemar taimako, kina bashi koda baya so ki bashi ya shanye a gaban ki ba bayan ki ba.
Insha Allahu nima zanyi kokari naga na taimaka da dan abinda zan iya gurin al,amarin.
Don kinga shi aikin shedan shiga rai ke gare shi sai mutum yai kamar zai bari sai kuma shedan ya rude ka ka koma.
Don haka yanzu ki yawaita jan shi a jiki ki kada ki biyewa maganan mutane kina nuna mai kyama ko hattara ,a,a ki jawo danki zuwa jikin ki don ki san damuwar shi.
Shigowan Bintu dauke da dan wani kwanon glass na tangaran da cibi a cikin sa yasa sukai shiru baki dayan su.
Su Amira duk suna tsa tsaye cirko cirko sai faman kuka sukeyi da tashin hankali.
Gurin da yake kwankwance sharkaf dashi ta nufa inda ta durkusa tare da dora kan shi a cinyar ta suko duk ido suka saka mata.
Amira na ganin haka ta fahinci may Bintu ke shirin yi masa don haka itama ta karaso tare da karban kwanon daga hannun Bintu.
Haka maryam itama ta guso inda suke da taimakon su ta samu ta bude mai baki da kyat suka dura mai manja da girshirin da ta hada har kusan cibi uku,
Sai ya fara wani irin tari ya bude idon shi da kyat tare da dan kara yunkurawa sai kuma bintu ta mayar da bakin shi da karfi ta rufe gam sai ko yai wani zabura tace ku danne min shi dan Allah.
Maji dake gefe tana kallon su ta kara sakewa da wani sabon kuka sosai cikin tashin hankali.
Yan mintina kadan saiko wani irin amai ya taso mai nan ya fara sharara amai kamar zai amaye kayan cikin shi a lokacin.
Amai sosai Umar yayi a lokacin sai kuma ya koma barci dan gefen su kadan.
Bintu ce ta kwashe amai don su sauran sai faman kuka suke tayi cikin tashin hankali.
Dawowa tayi falon ta zauna a cikin damuwa da tashin hankali,
Maji ce ta taso inda yake takai mai wani irin mari da duka mai gigita mutum abinda yasa shi bude idanuwan shi ke nan yana kallon ta.
Yace cikin muryan maye Maji may nayi kike duka na haka?
Uwar ka kayi dan banzan yaro mara mutunci kawai wallahi sadauki sai Allah ya,,,,
Haba mama kiyi hakkuri dan Allah kada ki furta mai mugun kalami yafi kuma nan lalace maki don Allah dai kiyi hakkuri mama takarasa cikin kuka da tashin hankali.
Mai masa tace haba hajiya watau baki dai ji abinda nake fada maki ba ke nan ko?
Wallahi idan ma yafi nan ba tsira zakiyi daga zagin duniya ba don haka ki dawo da hankalin ki guri daya kiyi nazarin magana ta.
Hannun ta ta cusa cikin aljihun shi don jin karar ledan da takeji daga cikin aljihun nashi.
Fito da ledan tayi daga aljihun nashi sai wasu kwayoyi suka zubo daga ciki da yawa haka.
Salati suka saka ita da mai masa a lokaci guda take cewa kinga abinda ya sha yafitar mai da hankali ko.
Koma ki zauna saman kujera kada ki fadi kinji hajiya akwai Allah shine zai muna maganin abin.
Ba,a san ko wacece daga cikin matan ta bugawa maigidan waya ba, sai kawai gashi yazo a sukwane gidan cikin tashin hankali shi da sauran yayyen sadauki.
Dakin maji da akace masu ya na ciki suka shiga anan suka samay shi kwance sharkaf kasa yana barci.
Nan suka samay shi da duka mai shuri na shuri mai mari yana mari saida ya farka daga barcin da yakeyi.
Suna ganin ya tashi suka jashi zuwa waje kiiii sukaci gaba da dukan shi cikin tashin hankali.
Ganin zasu halaka shine hajiyan masa ta isa gurin ta fada saman jikin shi tana tare dukan tana fadin haba Alhaji ai duka baya yi sai dai addua tunda abin yai muni ko?
Cikin takaici da bacin rai Alhajin yace mai masa bari kawai mu kashe dan banza may zanyi dashi cikin zuria ta mara mutunci kawai.
A dai yi hakkuri dan Allah abi al,amatin sannu tunda ya riga da ya aikata sai a san hanyan bi da shi kawai yafi.
Amma duka ai kara hinjira shi kawai zakuyi ba wai gyara abin ba .
Duk mutanen gidan suna tsaye tsakar gida cirko cirko sai amaryan su ce itama ta tako gurin ta kama mashi hannu zuwa part din ta duk da Alhajin yana ce mata wallahi ki barshi ya fito min gida ba dana bane wanan dan banzan yaron kawai.
Bataji ba,sai kulle kofan part din ta da tayi dashi a ciki ta,zaunar dashi nan ta shiga lalashin shi da bashi magana tana mashi nasiha.
A kan ya daina wanan muguwar akidar da ya sawa kan shi ko dan martaban iyayyen shi,
Tace ka tausayawa mahaifiyar ka Sadauki yau ka san irin halin da uwarka zata kwana aciki ai babu abi mafi muni ace yau cikin dubu nakane lalattace.
Dukar da kai UMAR yayi kasa tare da,wa i irin nadama ya,ziyarce shi a lokaci guda yake cewa mummy kuyi hakkuri insha Allahu zan daina bazan kara ba.
Tace da ka kyautawa kanka,wallahi da ka cece mahaifiyar ka daga tashin hankali da masifa.
Kuma kaje in komai ya lafa kabata hakkuri kai mata alkawarin baka sake shaye shaye har ma da mahaifinka.
Shiru sukayi ya,sadar da kan shi a kasa can takara cewa, yanzun kai ko don irin zaman da ake a,wanan gidan kowa ya tunkaho dan shi wani abu ne bai saka kai zuciya ka zama wa uwarka dan kwarai abin musali ga sauran dangi.
Maza tashi jeka kai wanka ka,tsabtace jikin ka don naji kamar sun fita daga gidan.
A lokacin su Maji suna daki hajiyan masa na kara bata hakkuri da magana mai kwantar mata da hankali, har ta dan sauko tana daukan nasihan mai masa.
Mai masa take cewa yanzu dai yana gurin kishiyar ki ta,saka shi a dakin ta ta rufe dashi nasan nasiha take mashi a can.
Wa mummy Amarya ko wa ina ganin itace dai mai daki can kusa dake karshe.
Itace maji ta fada a hankali don in ba itaba nasan indon su yayane sai dai a kashe shi ai.
Sadauki yafito daga part mummy yana tafiya cikin dan gyasawa a hankali don dukan da yasha ya taba mai kafa har da baya duk jikin shi ya farfashe sosai don dukan da yasha gurin mahaaifin shi da yayyen shi.
Wa yanda ke tsakar gida a zaune suka bishi da ido da bakar magana8 suna fadin andaiyi hasaran haihuwa wallahi.
Yadago kai ya,watsa masu harara sai dai bai tanka masu ba ya shige yafice daga gidan kawai.
Ranan Maji tayi kuka kamar ranta zaifita da,kyat mai masa ta samu tai shiru, tare da bata magana.
Gwago mai masa ta sa Maji taje taiwa Amaryan su godiya kan halarcin da ta nuna mata kan dan ta.
Maji ta shiga part din tana saye da hijjab mairuwan toka har kasa a jikin ta sai dai duk idon ta ya kumbura don kukan da ta yini yi ranan.
Da sallama a bakinta tashiga dakin inda ta dan tsaya daga kofa tana sallama daga waje.
Akai mata da iso da amsa sallaman da tayi hakan yasa ta daga labulen ta shiga daga cikin dakin.
Bayan ba,tasan dakin ta tsaru kamar na yan boko dama don komai akwai cikin dakin nata.
Amma da take ita ba ruwanta da bin dakin kishiyoyin ta,sai bata iya kaiyade abin dake cikin part din gaba daya.
A,a hajiya maijjida kece tafe yanzun fa nake son nagama da wanan dan rigiman naje gurin ki sai kuma gaki cewa karamin yaron ta da ta yaye amma ya dan tasa yagirma.
Ta kai kallonta ga yaron tace Amir kaine wai dan rigima aiko ba ruwan shi dai nagani.
Cafdi baki san komai ba ke na wanan ai fitinanne na karshe wallahi.
Yanzu fa nake zancen zuwa gurinki na kara baki hakkuri akan abinda yafaru dazun don abin ba dadi gaskiya saidai hakkuri da addua kawai Allah ya shirya muna su baki daya.
Maji tace nazo ne nai maki godiya kan irin halarcin da kikai nuna dazun din.
Nagode Allah ya saka da,alheri Allah ya kara bamu hakkurin zama da junan mu yasa wa zuria albarka.
Habba hajiya maijidda ai shi da na kowa ne danki fa da nane kamar yadda nawa suke naki.
Ke fa mutum ce mai kokari da sanin ya kamata duk irin halarcin dakike min kan nawa yaran aina sani.
Don ko dawowa sukayi ban dawo ba,daga school gurin ki ne kawai suke samun fuska a gidan nan har nadawo na,samu sunci abinci hankalin su a kwance.
Don may yau zanga naki cikin wani hali na kasa nuna bakin cikina akan hakan abin baiyi dadi ba gaskiya amma ayi hakkuri don Allah.
Hawaye ne suka zubo wa Maji daga idon ta take cewa hajiya, kubura ban san yaya zanyi da,wanan yaron ba a,rayuwa ta duk yadda ake ba yaro tarbiya nasan ina ba sadauki shi a,rayuwa amma a karshe duk ya,watsar dasu ya zabi wanan harkan na,shashan ci.
Hmm abin fa yanzu sai addua don ya fara zama ruwan dare ga matasa sai dai wanda Allah ya kare kawai shine ya tsira.
Na san zafin wanan tun a gida don ina da kani mai irin wanan rayuwan amma cikin ikon Allah yanzu ya daina ya koma normal mutum din shi kamar kowa.
Wani abinda baki sani bama shine abin fa ba mazane kawai ba harda ma mata wallahi mata ma ba,wai yara ba manyan mata hamshakai wallahi.
Ke dai kawai Allah ya gyara muna amma a lokacin muke da in kana da da namiji ko mace baka huta ba kowa da tashi irin matsalar.
Ki dai yi hakkuri kada ki sa zancen a ranki harki jawa kan ki matsala babba yazo yai maki illa a,rayuwanki.
Maji tai mata godiya inda hajiya Kubura ke cewa don Allah a dake da addua da rokon Allah kuma ki toshe kunnnen ki ga duk wani magana ko gorin da wani zai maki don ba wanda ya wuce hakan ai.
Maji takara cewa nagode Hjy Kubura nagode kwarai Allah ya saka da alheri tabar dakin tana masu sai da safe.
Ta kawo daidai tagan hjy Asiya taji tana cewa yaran ta wallahi kuyi hankalin da mashayin nan na gidan nan kunga ya fara haukacewa don haka duk wanda ya shiga tsabgan shi kun dai san ba,a shari,a da mahaukaci sai dai ace kuyi hakkuri an cuce ku.
Shigewa tayi part din ta tana jin kamar ta hade ranta yadda zancen yake mata kuna a rai.
Ikon Allah yau Sadauki dan cikina ake kirawa hauka da raina ikon Allah Allah ka taimakeni ka,shirya min wanan yaron ya Allah na rokeka.

Hajiyan masa bata zaina ba da dare ma sai gata ta dawo gidan ta kara ba Maji hakkuri inda suka kara tattaunawa akan al,amarin tai mata alkawarin shiga da fita don suga ya daina wanan harkan.
A nan tabar Bintun ta don dama ba yazo don ta,bane sai dai duk shiyan nasu ranan haka suka kwana cikin bacin rai babu maidadin rai daga cikin su.
Washe gari ma haka suka tashi sukuku duk ran su ba dadi saida safe ne Alhaji yakira su gaba dayan su ya tarasu a falon shi.
Inda ya kira sadauki da sauran yan uwan shi suka zauna don tattauna matsalar da,ya fada ciki.
Bayan gurin ya natsune maigidan yafara magana kamar haka.
Dama nataru kune nan don kowa yasan akan dalilin dana kiraku nan, batare da dogon magana ba ina son kowan ku yasani Umar gashi nan a gaba na daga yau na yafe shi daga cikin diya na.
Don ba zan zauna da dan da zai jawo min abin kunya ba a gidana, na,wuce ana nunani ga mahaifin mashayin nan can.
Kuma ka sani daga yau kada ka kara shigo min gida don kada ka bata min sauran yarana kimtsatu.
Uwargidan su tace gaskiya wanan matakin yayi daidai wallahi don gaskiya nima tun jiya nake wanan tunanen don barin shi cikin mu gamu da yawa a gida yana iya sa wani yaron yai koyi da halin shi na banza.
Mama Asiya itama ta tare zancen dacewa nima wallahi hakan yai min daidai don gaskiya barin shi a cikin mu babban hatsari ne don kada wata rana ya zo ya shawo ya kama mu da bugu.
Wani irin zafi da dacin zuciya Maji take ji shiko sadauki kan shi yana duke don kunyan mahaifiyar shima yake ji ba nasu ba don yasan shine ya jawo mata wanan sukan da ake mata mai kama da an daba mata wuka a zuciyar ta.
Assha Alhaji wanan maganan da kayi wallahi ba girman ka bane.
Ka taba ganin inda hannun mutum ya rube ya yanke ya yar dashi, don Allah ya jarabi wanan yaron da wanan lalurar shine zaka yanke wanan danyen hukuncin haka akan shi.
Wallahi baka kyauta masu ba ko kadan in kai masu haka daga shi har uwar shi.
Idan bamu jashi a jiki muka nuna mashi illan abinda yakeyi ba kyau ba, watau ya tafi ke nan yafi nan lalacewa ko?
Gidan kowa yanzu akwai matsala in hat gida babban gida ne amma kowa hakkuri yake yana boye abin shi yana jan kayan shi a jiki.
Amma ya daina shigo maka gida dakace ita uwar shi a ina zata gan shi har tasan halin da yake ciki ta tsawata ma abinta.
Da dai ka haife shi kuma jerabawa ya fado kan shi sai ayi hakkuri anema mashi shiryuwa ga Allah shine daidai.
Kai ji hajiya kubura wallahi ni ban son al,amari da munafunci uwar ahi in tana son ganin dan ta taje gidan mashaya ta,samay shi mana inda yazabi zama.
Umm,umm hajiya Asiya wallahi daji bai gama cin wuta ba ba aiwa kututure barka, kema fa uwace kamar hajiya maijidda don haka kii iya bakin ki.
Tuff tuf wallahi bakin ki ya sari danyen kashi wallahi nikan ba,a cikin kayana ba wallahi, watau baki kike min akan diyana ko ?
Ni ba baki nai maki ba gani nayi ko ita uuwar shi bataso dan ta da hakan ba, jerabawa ne dai daga Allah ya fada kan shi.
Kaidon Allah ni ya,ishe ni ban kira ku nan ba don kuzo kuna min cacan baki kiran ku nayi don ku ji shawarana.
To gaskiya Alhaji shawaran ka bai yi ba gara ka canza wani, wani irin huci Alhaji yayi yafitar da iska daga bakin shi.
Yace naji amma idan ya ganin ni wallahi ya kama kan shi inba haka ba zamu sa kafan wando daya dashi a gidan nan kaji na fada maka yaron banza yaron wofi kawai.
Tashi ka bani guri mara mutunci kawai mun sakafan wondo daya dakai a gidan nan wallahi ko.
Allah dai ya,shirya muna shi kawai za,ace amma wanan fadan ai bayi ba,wallahi tana fadin haka tamike tabar dakin cikin bacin rai, sauran suka bita da kallon ke asuwa munafuka mun san sallon kishin ki ai.
Ita ma Maji mikewa tayi tabar dakin tabarsu nan tafada dakin ta tana kukan bakin ciki da takaici.
Yau dan ta yaja mata wullakanci ga kowa agidan saboda shi anzaunar da ita ana fada mata magana son ran mutum.
Shiko Alhaji ya mutuwan son hajiya kubura badon yaso ba ya yarda da,shawaran ta don kawai kada su sami sabanine a gidan.

****** ********* ******
Tun da akai wanan case din sadauki bai kara,shigowa gidan ba yau kusan sati daya ke nan haka ranan abin da da mahaifi maji tatura maryam ta duba mata shi idan yana nan takira matashi don tana son suyi magana dashi.
Itama hajiya kubura ko yaushe tana tambaya idan yadawo ko ya shigo sai maji tace mata bai shigo ba ai.
Maryam ta samay shi a kwance dakin shi ya yi kwanciyar rigingine yana kallon saman dakin ta tsaya daga kofa tagaida,shi tafada mai sakon mahaifiyar su.
Yace taje tace gashi nan zuwa, ta dawo ta fadawa maji abinda yace mata bayan kamar minti goma sha ya,shigo gidan sai dai bai shigo ba kamar yadda ya saba ya dan tsaya daga waje kadan ya tura wani dan kannin shi ya kira mai maji dakin ta.
Yaron yashigo yana cewa yaya sadauki ne yace na kiraki yana daga waje wai.
Amira tace bazai shigo ba ke nan bari naje na shigo dashi, maji tace ai kunya marin da ne .
Amira na zuwa tace yaya Maji tace nace kashigo daga ciki mana ka tsaya nan .
Yace look Amira ki fada mata bazan shigo ba gani nan dai tazo ina jiran ta, tausayin dan uwan ta ya kamata ta juya rai a bace takoma ta fadawa uwar nasu abinda yace mata.
Maza jeki kice mashi nace bani son diban albarka shi da yai laifi ba,ai fushi dashi ba dai shine zai wa mutane zuciyan banza.
Amira na fada mai sako sai gasu a tare sun shigo gidan da ita.
Yana saye da farin shadda a jikin andanyiwa shaddan kwalliyan dan bakin kyalle a gaban rigar da fari.
Ya shigo da,sallama ya koma kaman wani kamili dashi ya ramay yai dan dogon wuya sai dan bakin da yayi.
Maji ina wuni kamar bazata amsa mashi ba tai shiru ya samu guri ya zauna a saman kujeran dakin.
Tausayin mahaifiyar shi ne ya kama shi don ita ma ta,ramay ta,fada sosai da ka kalleta kasan tana cikin rashin kwanciyar hankali sosai.
Yaya ina wuni muryan Bintu da ke mikewa zata shiga daga ciki ne ya katse mai tunanen shi a lokacin.
Lafiya kawai ya amsa mata,dashi sai kuma dan abinda ya,faru ranan yafado mai a rai din ya dan iya tuna lokacin da ta bude mai baki kan shi yana samancinyan ta ta tura mai manja a ciki.
Wani irin kunyane ya kama shi da nauyin yarinyar don yasan ta taimaka mai har sau biyu a rayuwan shi.
Maji tace kai ba,ai fushi dakai ba shine kai zakiyi da mutane ko, da kai fushi kaki shigowa may kake nufi da yin haka.
Maji ba,wai hakana bane kinji abinda baba ya fada ai shiya sa ni kuma naga gara kawai nabar shigo mashi gida kada na ja maki matsala.
Matsala kuma na yaushe sadauki akwai maysalar da kuma yafi wanan din da ka jawo min ne a cikin gidan nan.
Maji don Allah kiyi hakkuei wallahi kaddarace amma ban taba shan kwaya ba sai ranan koshi bacin raine na rashin barina nabi abokai na gurin kwallon da akayi yakaini ga hakan.
Insha Allahu bazan sake hakan ba da yardan Allah don Allah dai kiyi hakkuri maji ya fadi cikin kwantar da muryan shi.
Yanzu Baba na kana ga inin irin hanyan da ka daukar wa kanka shine daidai gareka gare mu ma.
Kaiwa kanka fada,wallahi ka dibs ka gani saboda kai aka zaunar da ni kowa na fada min irin abinda yaga dama a lokacin.
Inda ka gyara halinka duk gidan nan wa ya isa yai muna haka babu shi wallahi don ni ba ruwana da harkan kowan su.
Amma sanadiyar abinda ka aikata ji irin yadda kowa ya takamu son rashin ana fada muna abinda aka ga dama.
Maji kiyi hakkuri don Allah insha Allahu ba,zan sake ba da yardan Allah hakan ba,zai sake faruwa ba.
Nan dai taita mashi nasiha tana cewa yanzu ashe badama su Amira su yi laifi na kawo maka karan su a matsayin ka na babba a cikin su.
Ni hajiya kubura wallahi tai min komai don ta nuna min ita uwace a gareka kuma tasan ciwon kan ta ba kamar sauran iyayyen naka ba.
Don haka wallahi kaiwa kanka fada kaceci kanka kace ceni ni uwarka da yan uwanka kafitar damu daga zagi mutanen duniya.
Sun kai wani lokaci tace ya tasgi ya tafi take ce mai kuma daga yau ya tabbatar da ya dinga zuwa gida yana cin abinci bata son yana ci a waje inda batasan ko ina bane.
Yai mata godiya ya mike yabar gurin tare da kara bata hakkuri yabada baya take cewa jika don Allah kamar wani mutumin kirki can ashe mutimin kawai.
Murmushi yayi yace kiyi hakkuri maji don Allah bazan sake ba insha Allahu.
Yana fita ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa a filo Allah ka,shiyar mun da wanan yaron dama sauran yara masu halin shi na,wanan lokacin,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
8⃣

Baby yaya zamuyi ne ina son ki rakani zuwa lagos don ina da seminar da zamuyi a can, kuma dake nakeson zuwa.
Shiru Raiha tayi tana nazarin zancen shi a cikin ran ta don tasa abu mai wahala ya dauko mata.
Yaya zatayi da uyayyen ta a gida may zata fada masu ina zata ce masu zata tafi.
Muryan shi ne ya katse mata tunanen ta yana cewa naji kin yi shiru mana ko baki san rakani ne wai?
Hmm ba,wai hakana bane kasan in da hali koma ina ne zan iya raka ka amma ban san yaya zanyi da iyayyena ba may zance a gida.
Haba baby sai kace wata local can dan karya kawai zaki shirya masu mana kice zaki gurin wani dan uwan ki koda kauye ne kinga indan munje mun dawo sai na kai ki garin ko kwana daya kiyi sai ki dawo ko?
Nan ma,Raiha shiru tayi tana tunanen akan zancen shi don tasan abune mai wuya abarta zuwa wani guri ita kadai.
Gashi kuma tana son bin shi sosai a ranta don batajin yanzu zata iya rabuwa dashi ko na dan lokaci kadan ne.
Sai cewa tayi zan yi shawara don nasan abinda zan yi akan tafiyan.
Huci yayi don jin dadin yasamu yadda yake so daga gurin ta nan ya shiga yi mata abinda yasan tafi bukata daga gare shi har suka kai ga,watsewar su a hotel din da ya kaita.
Da zasu rabu ne yake jadfa mata cewa next week ne fa sunday tafiyan su kuma da jirgi zasuyi tafiyan, don haka yana son yasan idan zata tafi ya sai tickets din su shida ita.
Ba matsala tabashi amsa zansan yadda zanyi mu tafi din tare insha Allahu.
Wani shu,umin murmushi ya,sauke tare da,shafan dogon fuskan shi ya na cewa dat is my baby shiyasa nake kara,son ki.
Tun dawowan ta gida take ta faman sake sake a ranta sai kullawa take tana warwarewa ita kadai a ranta.
Can wani dabara ya fado mata a rai tai wani murmushi

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment