Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don ranan bata ko fita zuwa yiwa maigidan su sannu da,dawowa ba.
Wai ko yau yayan ku yadawo kuwa don banga ya shigo ba daukan abincin shi.
Amira tace, waya sanan mashi kila yana can gurin yawon banzan shi sai baba yasan bai gidan yazo yaitawa mutane masifa akai.
Bintu tace da zan shigo nagan shi zai shigo da leda da,ya,sayo doya soyayya gurin mai sayar wa nagan shi da zan wuce yana saye.
Oho ashe shiyasa banga yashigo ba ya samu abinda zaici ke nan .
Ai da yana jin yuwa da yanzu yashigo ya cinyewa mutane abincin su ko inji maryam.
In baici abinci ba nan a ina kuke son yaje yaci ne maryam, ni dai idan zai shigo yaci a nan din ai zaifi min komai dadi.
Bintu taji tausayin Maji ya kamata a zuciyar ta take cewa kai uwa uwace dai.
Da yau maji zata san halin da dan ta yake ciki tasan da yanzu suna cikin tashin hankali da balai a rayuwan su a shiyar su.
Amma dai yau Allah ya rufa wanan asirin an wuce gurin in ba,wani ikon Allah ba kuma.
Tana jin su suna hiran su amma bata saka masu baki ba sai faman tunane take a ran ta.
Shigowan baba a part din ya katse mata tunanen ta suka fara gaida shi suna mashi sannu da,dawowa.
Bintu ce tafara mikewa tashige daga ciki sai Alhaji yabi su Amira da harara dole suka mike simi simi suka shige bayan Bintu.
Yace marasa kunya kawai wai har bakuwa tafisu hankalin sanin ya kamata.
Har yanzu gwagon yarinyar nan bata dawo bane ko kuwa dai?
Bata dawo ba Maji taba shi amsa a takaice, takara da cewa ni ban ma son rabuwa da yarinyan don halinta na kirki yai min.
Hmmm ki dai ji da na kanki kafinki kara jajibowa kanki sabon matsala ya bata amsa.
Ai Fatima ba matsala bace zan ma iya cewa zaman ta ya zama min alheri don kaga yaran nan suna samu karuwa sosai a gurin ta ga ta yar karama amma akwai addini sosai a kanta.
Ta godewa Allah da,ya bata wanan baiwan har takai ga samun yabo haka na alheri Allah muma ya shirya muna yaran mu.
Ban ganki ba ne yasa nabiyo nagani ko lafiya don nasan ba halinki bane rashin zuwa yi min sannu da kasuwa.
Maji ta dan ya mutsa fuskanta tana cewa wallahi tun safe nake fama da ciwon kai yanzun ma aka sayo min magani na,dan sha shine naji yadan fada min.
Naso naje gaishe ka amma sai nai tunanen ko ka shige ne ko ai.
Ki daina shan magani haka batare da likita ya baki umurni ba idan kinji kan ya matsa maki aida kin kirani nazo mun tafi asibiti ko .
Naga ciwon kaine kawai shiyasa ban dauke shi wani babban ciwo da zani asibiti ba.
Haka dai kikace a lokacin da ya karasa takon shi inda take zaune yana kai hannun shi akan wuyan ta don taba jikin ta yaji lafiyan ta.
Kai haba Alhaji ai na samu sauki dana sha maganin nan yanzu, ki dai bar wasa da ciwo don ciwon da ka raina shike zama babba yanzu.
Allah dai ya sauwaka inji maji tafada cikin dan sauke ajiyan zuciya.
Ki dai bar tunane akan wanan yaro ki kai kukan ki ga Allah shine zai bamu mafita akan shi,insha Allahu.
Allah yada inji Maji ta fadi voice din so soft don zancen Sadauki yana tayar mata da hankalinta sosai.
Daga haka yai mata saida safe yabar part din nata cikin tausaya mata halinda take ciki yanzu kan lalurar dan ta wanda duk ta tayar da hankalin ta.

Washegari sun tashi kowa na batun fita zuwa makaran ta sai Bintu ce a gida don ita yau basu zuwa makaranta suna hutu.
Part din nasu yai shiru bakajin motsin kowa duk lokacin kowa yafita zuwa nashi tsabgan gaban shi don ci gaban rayuwan su.
Wani irin yunwa ne ya farkan dashi daga nauyayen barcin da ya yi mai tsawo bai san inda yake ba.
A hankali ya bude idon shi inda ya kurawa silin din dakin nashi ido, can yakai kallon shi ga agogon dakin a hankali yaga har tara da rabi na,safe.
Da kyat ya iya mikewa zaune ya samu har yakai tsaye don yunwan da yake ji yai mai yawa sosai a lokacin.
Wanka yashiga yana wankan ne abinda yafaru jiya da dare ya dan fara dawo mashi a,rai.
Kai aiko na,shige su tunda wanan bakuwar yarinyar ta san da wanan zancen don yanzu nasan ta fadawa Maji halin da,ta ganni a ciki daren jiya.
Aiko idan har ta fadi sai yai mata dukan da sai an kwantar da ita asibiti sai da ya shirya tsab yafito tare da kulle dakin shi ya nufi cikin gida don ya gaida Maji ya kuma karya saidai gaban shi na faduwa badon yana son cin abinci ba da bai shiga gidan ba a lokacin.
Da sallama a bakin shi ya shiga part din nasu duk da ya hadu da mama a kofa amma bai mata magana ba ya shige abinshi tabishi da harara tana fadin mara kunyan yaro kawai tabbatacce.
Maji dake zaune saman salaya tana lazumi ta karba mai sallaman shi tana cewa sai yanzu katashine babana kowa a gidan manya da yara sun kama gaban su ko.
Yace cikin dan shafan kan shi wallahi Maji barci ne ya kara daukeni bayan mun dawo daga sallah.
Ai jiya da,dare muna ta jiran kazo kaci abinci baka shigo ba har ana batun rufe gida sai Fatima ce ke fada muna cewa.
Gaban shi yai wani faduwa ras ras kafin yaji ma yarinyar tafada wa maji din.
Maji tace take ce muna ta gan ka,,, lokacin Bintu tafito daga cikin daki tana cewa Mama a canza zanin gado ne.
Wani uwar harara ya,watsa mata saida ta kasa fadin maganan da zata kara fadi.
Maji tace ashe jiya doya kaci ka kwata gata itace ke ce muna tagan ka kana,sayen doya da kwai da dare dana aike ta.
Wani wawan numfashi ya sauke tare da dan sake fuskan shi yace eh wallahi maji shi nake son ci shiyasa na saya ai.
Fatima dauko wa yayan ku abinci shi ya karya yafita shima don ban son zaman gidan nan kamar mace.
Bintu ta juya inda yake tana cewa ina kwana yaya can kasan harshen shi ya amsa mata da lafiya kalau,
Ta juya zuwa cikin kitchen ta dauko mai abin karin shi takawo mai gaban shi ta duka don ta aje mai ya faki idon Maji yana cewa kin kuru baki fadiba dana karyaki yau wallahi.
Da sauri Bintu ta mike tabar falon don kada ya kara ce mata wani abin kuma don ko yanzu ta tsorace dashi don mashayi ba abinda bai iyayi shi.
Sunaci suna hira da mahaifiyar nashi tana dan mashi hira maikama da nasiha sai cin abincin shi yake hankali a kwance abin shi.
Daidai Bintu na shigowa taji yana cewa ni dai Maji don girman Allah ki yardan min natafi wanan wasa kiyi hakkuri ki gwadani ki gani idan ban canza ba kada ki kara bari na tafi don Allah maji.
Daka ta sadauki na riga na fada maka cewa bazan yarda da zancen tafiyan ka ba,wani kasa can da babu kowa na gida a tare da kai, nan ma da kake a gaban mu yaya muka kwashe da kai?
Bintu batasan yadda akayi ba tace mama yace don girman Allah ki barshi yaje insha Allahu zakiga canji a gare shi da yardan Allah ke dai adduan ki yake nema da yardan ki.
Da har zai bude baki yace ke wayasa bakin ki zan balballaki yanzun nan, amma sai yaji maji tace .
Fatima bar shi kawai ni nasan halin abina ke yarinya ce baki gane may nake nufi da zance na yanzu amma ba zancen tafiya a guri .
Tafiyan ma fa wai na wasan kwallo haba sai kace uwar banza da batasan ciwon kan ta ba.
Maji komai zamuyi saida adduan ku don haka kamara yayi kisawa zancen albarka ki mara mashi baya yakai ga kudirin shi.
Don ba,a san mai gobe zai iya yi ba shiru maji tayi tace kai Bintu badai iya magana ba dai kam.
Shiko Umar shiru yayi yana mamakin wanan yarinyar yadda ta iya magana haka kamar wata tsohuwa can.
Fatima naji zancen ki sainai shawara ya dan dakance ni kawai nagama nazari nagani ,
Daga haka ya mike tare da cewa cikin murya ba dadi zan fita sai nadawo Allah ya tsare tace sai kadawo.
Haka fita jiki ba karfi yabar dakin sai dai yaji dadin yadda wanan yarinya ta saka baki har Maji ta dan yi taushi sosai yagani ai.
Tun lokacin da sukai wanan magana hankalin maji bai kwanta ba sai sakawa take ta walwalewa a ran ta daga karshe dai ta watsar da zancen ma kawai.
A na cikin haka gwagon Bintu ta dawo daga kawai ta zo gidan bayan ta huta don ganin Bintun ta.
Nan suka tare ta da murna sai bin Bintu take da kallon yadda gaba daya ta canza mata a fuskan ta ta kara haske da kiba, taiwani irin kyau da ita.
Nan ta shiga yi wa Maji godiya da karamcin da tai mata akan rike mata yarta yar dan uwan ta da take hannun ta.
Maji tace haba hajiyan masa ai Fatima mutun ce yarinya ce mai dadin zama da sanin ya kamata sosai.
Naji matukar dadin zama da ita a gidan nan don ta taimaka min da abubuwa da dama a gidan nan
Hakane ma yasa nace ko kin dawo bazan barta takoma gurin ki ba sai dai mu zauna nan da ita tunda danan da can guri ki ai duk dayane kuma a shiya daya muke dake.
In dai har hakan bawai zan takura maki bane gwago tai godiya da karamcin Maji tana cewa nagode Hajiya dama ba zama nadawo nayi ba don jinya nake a can na yayata da bata da lafiya.
Shine naga na barta a nan da suna sati biyu gashi har nai sati hudu a can baku da labarina, kada hankali ku ya tasbi na rashin jina da bakuyi ba na tsawon lokaci.
Ai babu komai nasan tunda najiki shiru lafiya ne ai tunda kin san inda aka barta ai.
Nan suka dan taba hira gwago tana bata labarin rashin lafiyar yar uwarta da take jinya a kauyen su.
Da zata wuce ne ta bukaci da Bintu ta rakata ta dan gyara gida don kuran da yayi na rashin mutum a cikin shi na wani dan lokaci.
Aiki sosai Bintu tayi a gidan harda girki saida tai masu don suci tanayi tana tambayan gwagon ta labarin mutanen gida.
Sai da suka natsune Bintu takw fada mata irin rayuwan kawai cin data samu a gurin Maji da kuma irin matsalar da take ciki akan dan ta da baijin magana da bukatar shi a gurin mahaifiyar shi na son tafiya wani gari buga kwallo da yake son zuwa yi.
Gwago tace kai amma ko hajiya da ta barshi don bata san ko shine mafitan ta ba arayuwa tunda har yai mata alkawarin canzawa idan ya dawo.
Gwago tana fada irin ta manya tana fadin ai gara ta barshi ya tafi don batasan abinda Allah ya shirya ba a kan yaron.
Suna ta zancen ita da gwagon ta har dai dare yayi don haka ranan a na gidan su Bintu ta kwana da,gwagon ta suna kewan junan su.
Sai washegari da yamma ta shigo gidan cikin jin kunyan Maji da yaran ta, sai faman yi matasheri sukeyi taga gwago ta gudu masu.
Maji tace yanzu Fatima haka zamuyi dake ni da nake fadin anan zaki zauna shine kina gani gwagon ki kika gudu gurin ta ko?
Ko dama bakijin dadin zama damune dai kika boye muna hakan ?
Da sauri Bintu takai kasa tana cewa ,a,a mama ba hakana bane kawai dai na tsaya ne na kara shirya mata kayan ta.
Jeki ga abinci can a kitchen ki diba kici inji Maji tana mata magana cikin kallon fuskan yarinyar.
Mama na koshi gwago tai muna gwaben ganye mun ci dazun mun koshi sosai ban jin yunwa yanzu. Sai dai anjima in Allah ya kaimu.
Daga nan ta samu guri ta zauna tana kallon maryan dake dakilar wayan ta tana dariya ita kadai.
Sun kai wani lokaci falon yana tsit kowa yana tsabgan gaban shi sai Bintu dake ta tunane kala kala cikin ranta yadda zata zauna a gidan nan dake cike da tarin matsaloli.
Fada sukaji tsakanin mama Asiya da uwargida ya kaure sai cacan baki suke a kan yaran su.
Maji bata fita ba tana zaune a falon ta har sukaci suka sude ko magana batayi ba, sai ma Amira da tace su daici kan su munafukan banza kawai kanku ake ji.
Sai lokacin Maji tai magana dacewa Amira ban son rashin kunya fa iyayyen naki kike zagi da munafukai kuma.
Kada na kara jin wanan kalamin a bakin ki ko kin manta cewa ke ma watarana uwace a wani gidan.
Shiru Amira tayi don tasan in ta kara furta,wani abu yanzu Maji zatai cikin ta da masifa sosai.
Har masu fadan suka kare cacan bakin su da tonon asiri ba,wanda yai magana a dakin daga dakin mummy Amarya ma ba tafito ba haka ma yaran ta.
Don ita dama,yar i don't care attitude ce a,gidan harkan kowa bata shiga sai in abu yakai mata karo.
Sai da yamma sosai gwago ta shigo gidan gurin Maji inda ta aika mata da abincin dare tace kada ta girka komai ta dinga bari akai mata daga nan gidan su.
Shine gwago tashigo yin godiya gurin Maji din da,wanan irin halarcin da take gwada masu haka.
Maji tace haba dai mai masa ai yiwa kaine ina laifi duk cikin shiyan nan baki aminta,da kibar yar ki a gurin kowa ba sai gurina, kika yaba da ni ai wanan ma wani mutuncine babba.
Murmushi gwago tayi tana cewa Allah dai yabar daukaka da girma Allah kuma ya kara shirya muna yaran mu.
Ameen inji Maji tare da sauke ajiyan zuciya a fili tace bari mai masa ba boyo a tsakanin nidake yanzu.
Jin haka yasa Bintu tai saurin mikewa,zuwa ciki tabar su gurin ganin ta,shige yasa maji hararan su Amira dake zaund suma din mikewa sukayi suka shige suna zunburo baki gaba.
Maji ta kara kwantar da muryan ta kasa, tana cewa hajiyan masa ina cikin matsala da,wanan yaron na,waje na.
Yayan su Amira ke nan inji gwago maji tace shifa,wallahi sai tace cikin kariyan murya mai masa yaron nan yana son kashe ni wallahi.
Maganar safe daban ta rana,daban ya zama wa kowa kaya a gidan nan balle ko banza kin san irin zaman da muke a gidan nan.
Yanzu msi masa nifa har na fara,zargin ko yana shaye shaye ne don abinda yake abin ma bana kai sake bane.
Subbahanallahi i ji gwago Allah ya tsare ya kare hajiya amma kada ki mashi mumunan zargi haka don Allah.
Koma maye dai dole ke uwa hakkuri zakiyi kikara jan danki a jikin ki kina nusar dashi hanyan alheri har ya gane.
Mai masa ni yanzu har abin yana son yafi karfina wallahi don kinga sam yaki zancen shago kamar kowa shi kuma ba,wani sana,a yaje zuwa yi ba yadda kowa keyi.
Ina gani a gidan nan ko wani da yana kawo wa uwar n shi abin arziki daga shago amma ban dani sai ma shi Alhanin ne wani lokaci yakan ji tausayina ya dan taimaka min ko shi da kwankwami da komai yake min.
Tunda kinga ba karfine gareni ba don ni banyi karatu mai zurfi kamar sauran matan gidan ba.
Amma mai mas wanan yaron duk da haka bai zama min da ba wallahi takare da sake kuka wi, wi,wi a lokaci guda.
Ba kuka zakiyi ba hajiya kamata yayi ki kara jajirce kina mashi addua da fatan alheri, kin fasan bakin uwa taki ga "yayan ta.
Mai masa wallahi inayi sai dai kawai na kara akan wanda nakeyi don banda lokacin kai na ko yaushe sai na yarana tun bai zama haka ba ma, balle yanzu da al,amarin shi yai kamari sosai cikin gida.
Yanzu ke hajiya baki fahinci ko akwai wani buri wanda yafison yayi abin ba akan kasuwan ci din.
Saida Maji ta share hawayen da ke fuskanta take cewa, mai masa waifa shi ba komai bane gurin shi sai sha shanci wai kwallo.
Kwallo yake da ra,ayin yi maigidan mu yayi fada har yagaji yanzu ya saka mashi ido yabarshi da kwallon.
To hajiya wa ya,sani ko anan alherin shi yake ga wasan kwallon.
Wasan kwallo kuma mai masa za,a samu wa i alheri a cikin sa ?
To ba haka naji ana fadi ba wai suna samu ga harkan sosai kinga sai muyi mashi addua mugani ko anan arzikin nashi yake.
Hmmm mai masa ni wanan ai abin kunyane a gareni ace wai cikin gidan nan da na yafita zakka wai bai kasuwanci sai kwallon kafa kawai.
May zai samu a cikin wasan kwallon kafa kuma banda shashanci irin na sadauki kawai.
A,a hajiya ban son ki na fadi haka fa kin daiga ki godewa Allah idan har zaiyi wasan ya jawo mai alheri da kintsuwa ai gara a arshi ya,tafi yayi abinshi kinga,zaki rage taahin hankali don kin san inda yake.
Ni kuma nai maki alkawari insha Allahu zan taimaka maki akwai gurin malamin dazan tafi maki can kauyen mu sai yai muna istihara akan matsalarshi don muga may ke damun shi ne wai.
Don kingafa gidan ku babban gidane gaki da kishiyoyi marasa imani da tsoron Allah.
Don haka abu na farko shine mu fara,sani may ye nasabar wanan matsalar tashi ne wai ?
Shin daga Allah ne ko kuwa,saka mashi hannu akayi din a danbala makishi yakoma haka.
Hmmm mai masa ba,wanda ya saka mashi hannu shashancine kawai irin na yaran yanzu .
Ya hadu da miyagun abokai sun sauya mashi tarbiyan dana bashi tun farko don rashin tausayi irin na dan yau.
Kin taba zuwa akai maki istihara akanzancen ne ko kuwa dai haka kike gani ke ?
Gaskiya ban taba zuwa ba mai masa ina dai hasashen hakan ne kawai a raina.
Hajiya yanzu duniya tai nisa wallahi kibar mutum inda kika barshi kai kana kwana,wasu na maka hansari ne,
Balle yanzu ba,a zama kan yara ko nawane gareka dole katashi masu tsaye gurin nema masu tsari da kuma addua.
Gaskiya ni mai masa ban taba yin komai akan yaran nan ba gaskiya nidai nasan ina masu addua sosai wallahi.
Hajiya wanan zamani ai ya,wuce ko gurin mutane don zamani ya lalata mutane da son kai, don A LOKACIN MUKE,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
7⃣

A gurin da suke zaune suna magana suke jin hayaniya daga cikin gida, shiru sukayi suna saurarawa.
Labulen dakin tane ya,daga ko sallama babu ya fado masu dakin duk jikin shi yai futu, futu da kasa ga wandon shi kamar yai fitsari a ciki.
Kara shigowa yayi daga cikin dakin ya fadi kasan ties din falon jagwab dashi sai kuma ya fara nasarin barci.
Innalillahi Baba na may ke faruwa ne haka, may ya samay ka, may akai maka, wa yai maka wanan abin haka.
Sai ta,sake wani irin kuka cikin wani murya mai ban tausayi da tsuma zuciyan mai sauraren ta.
Innallilahi wa,inna alaihim rajium Baba kada dai ace da gaske shaye shaye kake yi haka.
Cikin kuka take magana da tashin hankali, mai masa kin ga yaron nan yau yadda ya koma ikon Allah.
Allah kataimake ni ya Allah wanan yaron yau may zangani haka da idona.
Nashiga uku na lalace a rayuwata Sadauki may ka koma haka yaushe ne kafara wannan bakar rayuwan haka.
Takara daga murya tana cewa Baba na badai shaye shaye kakeyi ba cikin gigicewa take maganan.
MAJI bafa,,, abinda ya,samay ni just ,,,, relax ,, relax Maji,,, kawai,kawai dai ,,,, dan joy neeee,,,,,
Sai ya mayar da kan shi kasa yaci gaba,da barcin shi, nashiga uku mai masa yau dan nan ya, jawo min magana babba a cikin kishiyoyi da al,umma.
Baba da nasan wanan rayuwan zakayi a duniya da na barar da cikin ka na huta da ganin wanan bakar ranan da nagani yau a,rayuwa na.
Haba haji ki daina fadin hak don Allah yanzun dai musan abin yi kafin abin yai mashi illa haka.
Mai masa ai gara ace ya mutu da na zauna ina ganin shi a gabana haka.
Umm,umm hajiya don girman Allah ki daina fadan haka wa dan ki Ai babu abinda ya gagari Allah ko?
Kuka mai tsuma rai Maji takara sakawa cikin tashin hankali tana fadin da daya ke nan tilo namiji da Allah ya bani mai masa yau ga abinda ya zama min a duniya.
Ba u komai Allah ya shirya muna shi dashi da ma sauran diyan musulmai masu wanan halin.
Daga waje kofa tsakar gida kuma kishiyoyin maji a tsatsaye suna fadin ikon Allah yaukan mun ga abin mamaki a cikin gidan mu wanan bakar masifan ya,fado muna.
Hmmm lalau akwai magana da,sake don dole a,dauki mataki ga hakan kafin a lalata muna yaran mu.
Dayar kuma sai cewa tayi kai gurin bakar jaraba har an kwaso muna jikokin yan maye a gida yau ga abinda bakar jaraba ya jawo a gidan nan.
Ace wai cikin gidan nan yadda muke da mutunci a cikin shiya an samu dan maye irin haka.
Allah kai muna tsari da wanan bakar masifan ka kare muna yaran mu dama karshen so ke nan ga yaron da ba,a kwabo ai.
Haba dai ai wanan ba daga nan ba inji amaryan su kowa dai yabi nashi da addua amma ai ita Maji ba itace ta turashi zama haka ba kudai kowa ya iya kan sa don wanan masifan ta shafi kowan mi a gidan nan, ba ita kadai ba.
Ke don Allah ni ban son munafumcin banza ina ko ke bai bari ba indai sadauki ne a gidan nan.
Haka sukai ta cacan bakin su daga kofan dakin Maji da suke daga ciki suna jin cacan bakin su.
Mai masa kinji abinda nake fada maki ta fadi cikin kuka da tashin hankali.
Ai basu kamar Allah ba don ba wanda ya wuce jerabawan ubangi daga cikin su.
Ke dai kibi

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment