Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanisa tace ni dai gaskiya nayi niyya da kabarni kawai na sayar a samu, dan gurin rage wani hanyan kuma.
Ya fahinci bazata dauki shawaran shi tayi hakkuri da jarabbatar talaucin da suke ciki ba don haka sai ya kyale ta tayi yadda take so kawai.
Don yanzu ba matan birni ne kawai ke bijirewa girmama wa dokan mazan su ba har ma da matan kauye haka suke don yadda zamani ya juya a lokaci ne muke ciki,
Bai gida washe gari baya gida takira dillaliya sukai cinikin kayan dakin ta tazo ta kwashe akan dan kudi kalilan tabar mata su,
Ba bata lokaci ta hada kudin tana jiran dawowan maigidan ta ta fada mai ya barta taje ta dan samu abin da tai niyar saye da kudin,
Bai mussa mata ba don yasan kudin ta ne don haka ya kyale ta tayi yadda take so da abinta don yana gudun yai magana ta ga kamar yana son wani abune daga cikin kudin, nata.
Bata tsaya bayan sallah magariba ta shirya sai gidan wata dillaliya mai sayar da kayan hannu, inda tai sa,a tasamu fridge har guda uku a gidan da akasa a kasuwa nan sukai ciniki ta samu dan babban wanda bai tsufa ba sosai ta saya da kudin nata,
Suna barin gidan ta turo mai baro ya daukan mata shi zuwa gida zuciyar ta fam da farin ciki a ran ta,
Da mijin nata,ya,dawo yai mata fatan alheri da,daukaka a cikin al,amarin.
Tun daga wanan lokacin ne tafara dan sana,a da fridge din nata tana dan samun kwabon kashewa ta fannin ta ita ma,
Hakan ne ya kawo mata saukin yan damuwan yau da kullun da take ciki don tana dan samun kudin kashewa a wanan fannin nata.

****** ********* ******
Safiyane duk jama,an gari sai faman zirga zirga suke kowa harkan ga ban shi yake yi ba mai kama hannun yaro daga cikin su.
Sai faman sallama ake a gidan gwago Asmau da manyan kuloli gurin sayen masan da take soyawa tun da farar safiya.
Gwago Asmau taji dadin kasancewar Bintu da ita a yau din don ba karamin taimaka mata takeyi ba.
Komai cikin natsuwa Bintu takeyi ga tsabta sai ta wanke hannu da da kayan aiki kafinta taba shi,
Sannu sannu tafara gyara ma gwago aiyunkan ta sabanin yadda take aikin ta a baya in local way,
Bintu taba gwago shawaran cewa ta mayar da masan ta na zamani don yanzu akasarin mutane suna fama da lalurar ciwa gyambon ciki watau ulcer,
Gwago Asmau tai mamakin yadda Bintu karama da ita tasan wanan dubara gashi kuma daga kauye take zaune,
Don Bintu ta bata shawaran cewa yanzu da safe zasu dinga kai nika kuma su toya shi, a lokacin,
Gwago Asmau tace kai haba Bintu ni kada ki jawo min hasaran kudi yaya zaki ce na kai nika ranan kuma na soya masa a ranan,
Bintu tace wallahi gwago ki gwada masan ki zata samu karbuwa sosai wallahi don duk masu tsoron cin masa don tsamin shi zakiga sun fara sayen shi,
Gwago tace yaya zan yi wanan aika aikan haka Bintu na,
Bintu tace gwago zamu wanke shimkafan mu fara sai mu barta a jike cikin ruwa ta kwana da safe zamu tsamay mu hada da dan falawa dai yadda muke son shi sai mu hada da dafafan shinkafa da yis da baking powder,
Sai a kai nikan shi ayi muna kullun shi na ruwa amma kada a cika ruwa da yawa gurin nikan shi idan an dawo sai k8 dan kara gurorin dafafan shikafa da kaurin shi yadda kike bukatan shi,
Sai kawai a fara soyan shi kamar yadda ake masa a koda yaushe,
Kai yan nan akwai ki da dabara kamar wata babban mace ke a ina kika koyo wanan masan kuma,
Bintu tai murmushi har dan dimple din ta ya lutsa kadan tace nima a gurin wata makwabciyar mu dake masa a bauchi sukai zama, naga tana hakan.
Yadda Bintu ta fada hakan sukayi sai dai gwago Asmau sai Allah Allah take kada abin ya bashe su sai da taga zubin farko masa yafito da kyau hankalin ta ya kwanta,
Nan da nan masa ya kare masu washe gari masu sayen masa sai yaba dadin masan jiya sukewa gwago Asmau, suna cewa kai masan jiya ga taushi ga dadi wallahi babu tsami ko kadan, don har miyan sai da bintu ta sa aka dan zuba mai dan baking powder kadan,
Nan da nan labarin dadin masan gwago Asmau ya dan kewaye shiya, don dadin shi.

Daga gidan malam Habu aka aiko asai masan dubu da dari biyar sai aka samu akasi babu canji a gurun gwago don haka aka ba su masa kawai, sun biyo canjin .
Sai da yamma ne gwago ta ba Bintu canji ta kai gidan rayuwan Asmau bai so ba don bata son dabi,ar shiga gidajen mutane ita.
Haka yasa tun zuwan ta garin bata je gidan kowa ba, tana cikin gida gurin gwagon ta kawai sai nikan da tafita da,safe tabi almajirai, don taga yadda za,a nika masu kullun masan su.
Hijjab din ta ta saka tare da sa dan sifas din roban ta sai gidan duk da dai kwatancen gwago tabi don shiga gidan,
A hankali tai sallama daga kofan farko na shiga gidan babu kowa sai flawer a shuke daga can nesa ta hango wani saurayi a duke yana sa takalman kwallo a kafan shi da alama shigar shi ya nuna cewa gurin wasan kwallon kafa zai tafi.
lna wuni tace tare da dan duka mashi har kasa batai tsanmani ya amsa mata ba sai cewa tayi don Allah ina hanyan da zan shiga cikin gida canji na kawo na masa.
Fuska a murtuke ya nuna mata da hannun shi, ba tare da yai magana ba,
Inda ya nuna mata ta nufa a hankali sai dai tana shiga duk ta daburce don gina ne na part din mata hudu ko wace da nata daban,
Yanzu ni ina zan nufa ta fadi a ranta batare da tasan wanda zata kaiwa canji ba.
Tana shiga tai tsaye tana ta faman kwada sallama ita ka dai a tsaye shigowan wata mata gajera fara mai kiba yasa ta mayar da hankalinta ga matan,
Ina wuni take ce mata cikin ladabi matar ta,amsa a,dadare da fadin lafiya,
Bintu tace canji aka ce na kawo daga gidan hajiyan masa, kamar yadda ake kiran gwago Asmau, dashi a uguwar,
Cikin wani irin kushe fuska take cewa isa mana ki tambaya ciki tun nan ta fahinci akwai kishiya a gidan ke nan ,
Tanan tsaye sai sake, sake, take a zuciyar ta, tana niyar juyawa ta koma ne taga wata mata baka, tafito daga wani shiya dake daga can gefe tsabare da sauran shiyan ,
Hannun ta dauke da bukiti da mopa da tsiyatsiya da alamar da ga shara take futowa matar.
Itama dai cikin ladabi ta gaida matar da ta gani ta amsa mata cikin sakin fuska.
Tana cewa sannu ko kina neman wani ne ko Bintu cikin murmushi don taga fuska, tace dama canji ne akace in kawo inji Hajiyar masa,
Au daga gidan hajiyan masa kike ne, ?
Eh a nan nake tana kokari miko canjin dari biyar din dake hannun ta din,
A shigo mana daga shigowa har zaki tafi zo shigo daga ciki kinji ba mussu Bintu tabi bayan ta zuwa part din da matar ta nufa.
Suna shiga dakin taga ashe daga ciki a kwai dakuna da kuma kitchen, a cikin su.
Kujeran dake a falon gidan ta nuna mata ta zauna tare da kara gaisawa da ita,
Amira Amira matar ke kira daga falo, sai ga wata yarinya doguwa zata dan girmay ma Bintu tafito daga dayan dakin dake part din,
Tana ganin Bintu zaune sai kallon ta take da mamakin ko wacece ita, gaida yarinyar mai suna Amira Bintu tayi.
Maji gani inji Amira din tana mai kallon uwarta, don son jin mai zata ce mata.
Karbi canjin nan jeki sauran dakuna ki tambaya wa hajiyar masa take bi canji dazun da safe,
Amira ta turi baki gaba tana cewa ni wallahi in ba dole ba ban sin shiga gurin kowa a gidan nan don dai kawai da mutum ya shiga yanzu za,ace ga abinda yayi kuma.
Aiken ki fa nayi Amira kika tsaya mai da naki ba,asin son raki haka Amira taja kafa ta,wuce zuwa sauran sassan gidan,
Inda Bintu take zaune maji ta dan kalla tana fadin yi hakkuri kinji har ta dawo muji ko canjin waye,
Andan jima kadan sai ga Amira ta dawo tana konkwami tana fadin wai, maman su Hadiza tace takawo ta aje ko na baba ne amma taki bata ga kudin tana kokarin mikawa mahaifiyar ta kudin hannun ta,
Amira mai yasa baki bata ba da kika dawo da kudin nan may zanyi maki dashi a nan ,
Maji cewa fa tayi wai zata ajewa Baba ni kuma nasan ba,bashi kudin zatayi ba shiyasa nace mata tabari na tambaya sauran shiya muji in ba nasu bane,
Yadda maji take magana da yar ta acikin lumana ba daga harshe ya ba Bintu shawa sosai sai faman bin su da kallo take yi, na sha,awa.
Yadda uwa takewa yar ta magana a cikin kwantar da hankali da fahinta,
Inda Bintu take a zaune Maji ta,waiga tana fadin inaga canjin Alhajine idan ya dawo zan tambaya muji in har ba nashi bane zan sa su dawo mata da kudin.
Bintu ta mike don fita daga dakin a daidai lokacin da Umar ya shigo dakin ke nan babu ko sallama.
Sai cewa yake ni zan tafi ball kada kuma ace ban fada ba natafi , yana,wani cicin magani cikin dakewa,
Haba babana kai wai yaushe ne zaka girma zaka shigowa mutane daki babu ko sallama kana wani shan kamshi da cin magani.
Kamar wan da zai tafi gurin wani abin arziki wai ball, ball din mai zai tsinana maka a rayuwanka ne wai,
Maimakon ya tsaya yaji karshen maganan ta,sai juyawa yayi kawai ya fita daga dakin,
A hankali maji ta sauke ajiyan zuciya tana furta Allah ya shirye ka babana,
Bintu dake tsaye ta amsa da Ameen Mama sosai har cikin ran maji taji dadin Ameen din da Bintu ta amsa mata dashi.
Mama ni zan tafi sai anjima ke nan zan fada mata yadda akayi, to kin ji yar albarka ki gayar min da Hajiyar masa din kinji ,
Bintu takai kofa Maji tace may ye sunan ki ne bakuwar hajiya ?
Cikin murmushi Bintu ta amsa da Bintu nake mama Allah sarki sunan mai kyau sunan mahaifiyar maigidan nan ke nan ai.
A waje ta samu wanan mai bakin ran yana tare mashin zai hau ko kallin shi batayi ba don tsoro ma yake bata, ita,

****** ********** *****
Kida ke tashi daga cikin waya daga daki yayin da uwar ke daga gurin wanke wanke tana wanke kwanukan da suka ci abinci dashi na daren jiya,
Ganin hankalin uwar yana ga aikin da takeyi yasa Raiha mikewa a hankali zuwa gurin da ta boye kayan harkan ta a ciki ta jawo wani kwalba ta kwankwada son ranta tai wani jan iska da tsuke bakin ta a hankali.
Ta koma saman gadon da ta tashi a kai, ba bata lokaci sai barci ya dauke ta a gurin.
Uwar na shigowa daki taga yadda ta kwanta daidai da ita, a hankali uwar ta kada kan ta don takaici tana dan kiran sunan ta ,
Ke Raiha Raiha fa wai bazaki tashi ki yi abinda zakiyi bane ki kwance haka galala tun safe kamar mara lafiya.
Cikin murya irin ta mashaya Raiha tace kai haba mama please easy please easy barci nake ji fa.
Ikon Allah barci dai barci dai kamar wata malalaciya sai kin tashi ki ce wai ke yunwa yunwa kamar zaki hadiye mutane, lokaci guda.
Nan uwar ta barta ta,tafi tana mita a kanta a lokacin ta gyara kwanciyar ta da kyau taci gaba da barcin ta.
Bata farka ba sai yam lis ta farka sai bandaki tafada tana sauri don fitsari da kashin da take ji a lokaci daya.
Bayan ta dauki lokaci tafito ne daga ban dakin shine ta debi ruwa a randa ta watsa don ta dan ji jikin ta ya sake mata don nauyin da yai mata a lokacin.
Tsab ta shirya cikin wasu kananan kaya ta,dauko hijjab din ta tayafa a kan ta kamar wata ta kirki can.
Inna ni zan fita tace a gadarance uwae tace ina kuma zaki yanzu ana batun yin magariba kuma ?
Ba nisa zan tafi ba zan dan je can kasan layin mu ne na,dawo .
To ki daiyi sauri kafin mahaifinki ya dawo bai samay ki ba.
Yanzun ai zan dawo ba dadewa zanyi ba Inna, tana fita ta tare mashi sai wani uguwa da ke da yawan mutane akasarin su duk matasa ne maza da mata birjit a gurin.
Kutsawa tayi itama tashige gurin can wani dan lungu wani gaye ne ta nufa yana zaune tsakiyan su sai busa hayaki yake,
Yana saye da,riga blue mara hannu a jikin shi duk mozuqu din shi sun fito wahe sosai.
Yana ganin ta tace yar halas yanzu fa nake zancen ki a,raina nace ko kayan basu kare bane har yanzu don tun shekaran jiya baki leko mu ba nagani,
Ina tafe ai na tsaya ne har na karasa sauran wanda ya dan rage min don gudun kada na tara kwalabe a dakin namu yai yawa.
Kasan gyatumar ba sanin kai tayi ba har yanzu bat da sau nake mata koda ta rutsani nakan ce mata maganin mura ne nake sha ai,
Shegiya baby watau dai a kwana kike sakata ke nan dai ko?
Kai ma kagane ke nan ai don abin sai da kwana don ba,a,bari ai saurin sani abin.
Nawa kiia zo dashi don kin san ranan ma na biyo ki canji dai ko?
Nawa ka biyoni brosha ina dari uku ne dai kawai ko?
To dari uku ba kudi bane dasu ne ai muke karawa muna business din ga,shegun kwalawan nan kullun sai kokari suke suga,sun kama mutane don kawai su caji mutum dan canjin kashi badon a,daina harkan ba.
Ni dai kaji miko min kaya na natafi don yau ba dadewa zanyi ba ina sauri ne.
Wasu kala za,a baki akwai fa,sabbin fitowa masu aiki sosai wallahi tace cikin tsiwa bani dai wanda ka saba bani kawai na,wuce na biya shagon Samuel na kara dan kwalabe a can,
Daidai lokacin Umar yazo baiyi magana ba,sai kudin da ya miko mashi yace kaibani nabar gurin nan don ban son sa ido da yawa.
Brosha amma kasan sai ka sallameni zaka sallami wani can ko?
Umar yana daga gefe ya harde hannayen shi a kan chest din shi ya zuba masu ido yana sauraren abinda sukeyi kawai.
Sanin ko waye Umar yasa brosha fara hado mai kayan shi don yana kai wata biyu baizo gurin ba yafi aikowa a,saya mashi,
Yana kokarin miko mai canji tare da kayan shine fam cike da leda, yaji muryan Umar yana fadin ka bata da sauran canjin sai wani lokaci kuma ya juya yatafi a bin shi bai tsaya jin may zasu ce ba,
Binshi da ido Raiha tayi tana,mamaki mutum haka ga alheri ga kuna ta hango jin kai a tare da shi.
Mtwee tace tare da juyawa tace kai bani na,wuce kaji ban son bata lokaci nace ma,
Aike yau kin taka sa,a wallahi haka yake in har yazo sai yai wa wani alheri a gurin nan, sai dai kuma ba kullun ne yake zuwa ba,
Tana karba ta juya tabar gurin don zuwa chemist ta sayo sauran abubuwan ta.
Tana fitowa yana,shigewa mota ya harba yabar erea din don gudun wani ya ganshi idon sani yasa yake zuwa wanan uguwar sayen kayan mayen shi can nesa da gida.
Ko da Raiha ta isa gida lokacin har takwas da rabi na dare.
A lokacin mahaifinta har ya dawo daga kasuwa sai dai yana daki shi yana rage kayan jikin shi.
Hakane ya bata daman shigewa ciki batare da yasan dawowan ta ba gidan.
Ganin ta kawai mahaifiyar ta tayi don haka hankalinta ya kwanta don tasan da zaran mahaifinta ya ji bata gidan matsala ya faru ke nan.
Tafito daga dakin mahaifiyar ta,a,daidai lokacin da mahaifinta yake kokarin zama a,saman tabarma a kofan dakin shi tana cewa baba sannu da,dawowa kawai ta,sa kai ta shige abinta,
Ashe tana gidan ai yanzu nake batun nace wai tana ina ne banji motsin ta ba uwar tace tana ciki ai tundazun, (Uwa ke nan,)
Nan ya zauna yana cin abinci suna hira da mahaiyar Raiha cikin so da kauna a tsakanin su,

****** ********* ******
Yaro ne daga kofan gida yake kwada,sallama yana cewa abani ruwan pure water, na naira goma.
Da sauri Hanne tafito daga dakin ta tana cewa shigo ka karba kaji ta bude dan fridge din ta ta dauko mai ruwa leda biyu ta bashi ta karbi kudin zuwa dakin ta,
Ba,ajima ba wata yarinya tashigo itma ta saye haka mutane suka gane cewa tana sayar da,ruwa ana dan shigowa gida ana,saye.
Nan tai shawaran ta fara dan kayan sanyi irin zobo da kunun ayya tana hadawa dashi ko zata kara cabawa ga samu,
Kudin ta bayar aka,sato mata kayan zobo da na kunun ayya ta hada.
Ba bata lokaci aka ganeta mutane suna shigowa,saye tun dai da,zafin ranan da,ke yawa a garin don ko baiyi sanyi sosai ba ana saye hakana.
Ance rai da kwadai don haka Hanne tafara shawaran canza fridge din ta zuwa wanda yafi wanda ke gare ta girma don ta kara bun kasa sana,an ta dashi.
Da maigidan ta yadawo ta fada mai ahawaran da tayi shiru yayi don baida na fadi, don baida na fadi saboda yasan cewa shi kan shi yana amfana da wanan sana,an data samu tana dan yi yanzu.
Saboda yana tare masu gurare da dama na yau da kullun a gidan har ma,da wanda bai zata ba don yan zu a lokaci ne muke inda mata suke bada nasu gudun mawa a gida fiye ma da yadda ba, zata ba a rayuwa




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,
3⃣

MAJI ce kwance a,saman dogon kujeran dake cikin falon dakin ta, ziciyar ta a cacushe yake mata da bakin da bacin rai ga radadi da zugin da yake mata.
Bakomai ke damun zuciyar Maji ba sai irin halin rayuwan da Allah ya jarabi dan ta dashi.
Wanda a da can baya ba haka rayuwan shi take ba sai yanzu da girma ya fara shigan shi ne bakon al,amarin ya fara shigan shi haka.
Hayaniyar da take ji yana tashi daga cikin gida yasa ta sauri mikewa zaune da sauri, don ta saurara idan dai ba saudakine ya ja mata wani sabin maganan ba kuma a gidan.
Aikuwa jitayi mama tana fada tana cewa wanan yaro ya dai zama muna masifa a gidan nan yanzu.
Yaro guda ya zama alkakai acikin yan uwa wai mai saudauki ke son mayar da mutane ne haka wai, duk yaro abu ba abu ba ya kai mai duka bugu haka har na tsiya.
Sai muryan dayar kushiyarta da take biwa tana cewa ni wallahi karan shi zanyi akan takalman banza zakaiwa yaro mugun duka haka har ka fasa mai baki.
Anty watau amaryan su tace a,a kada ki karan shi kijira har shi mahaifin nashi da ya bata shi ya dawo ki fada mai muji ko muga abinda zai yi,
Basu suja batashi ba da so sun dauki son duniya sun dora akan shi yanzu ai ga abinda so ya jawo masu sun gani.
Maji dake daga daki takai zaune a hankali saman kujeran da ta tashi a kanshi tana maijin zafin maganganun su a ranta don dai ita tasan a iya yinta ba wani gatan da ta gwadawa dan ta, a baya fiye da sauran yan uwan shi.
Amma babu yadda zatayi don ance dan kuka mai jawa uwar shi jifa don da bai shiga harkan yaran su kamar yadda ta hore shi da zafin zuciyar shi akan ya rage da bai ja mata yawan magana na habaici ba ga kishiyoyin ta.
Wasu irin hawaye ne masu dumi suka fito daga idanuwan ta a hankali, a daidai lokacin Amira dake cikin daki kwance tafito falon nasu.
Ganin yanayin uwar,su yasata karasawa kusa da ita ta zauna tanavmai kura mata ido tace yaya sadauki ne ko maji.
Don Allah maji ki fita zancen su ki daina zubar mashi da hawaye malamin mu fa na islamiya yace muna ba kyau uwa tai kuka akan dan ta musan ma ma da namiji don Aljannar shi yana ga hannun ki mama don Allah ki yi hakkuri ai ya kamata ace kin saba da halin shi yanzu ki daina bata ranki a kan zancen shi hakana.
Suma ai daukan magana ne mai yakai su ga kayan shi tunda sun san bai son raini shi.
Baki maji ta bude da nufin tai magana sai kuma bacin rai ya hana ta iya furta komai sai taja bakin ta tai shiru, amma duk AmiraA yarinyace karama zancen ta ya shiga ran ta sosai don haka tai shiru kawai amma a zucuyar ta ba dadi sam wani kunci take ji sosai.
Har dare sadauki bai shigo gidan ba don yasan abinda yaiwa kanin shi yana can ana jiran shi dashi cikin gida.
Shi ko yanzu daidai yake jin shi dakowa don ya fahinci daga mahaifiyar su har su duyan ta ba mai kaunan su a gidan gaba dayan su.
Sai yamma kamar kullun malam Habu yadawo gida ko hutawa ba,a bari yayi ba aka tare shi da zancen sadauki akan yaiwa Abdul mugun duka wai don kawai yasa mashi takalman shi na kwallo yafita dashi gurin wasa.
Kai kawai malam habu ya kada yace wanan yaron wanan yaron ya kai min ko ina a rayuwana wallahi.
Daidai lokacin Maji ta shigo dakin saye da hijjab din ta mai ruwa light green.
Tana mashi sannu da dawowa amma bai karba mata ba,sai cewan da yayi Maijidda wallahi danki ya zama min masifa a rayuwana .
Kullun har zullumin dawo gida nake daga kasuwa don nasan da zaran nadawo da,wuya ba,a tareni da zancen shi wanda zai bata min rai ba.
Shiru maji tayi tana,sauraren kalamin maigidan nasu a gaban sauran kishiyoyin

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment