Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da dare ne Mummy tashigo dakin da roban dabun naman kaza da wai tasa ai mashi.
Maji ta karba tai godiya tana cewa lalai wani abu sai Baba na duk shi ke da wanan shi kadai.
Mummy dake daga tsaye takai zaune, a hankali tana fadin hjy maijidda dama naso shigowa na ganki ban samu lokaci ba.
Don Allah abinda ya faru a tsakanin mu muyi hakkuri da junan mu mu dauke shi a matsayin kaddara ne hakan.
Amma banyi maki hakan da wani manufa ba kwadayin zama da yarinyar ne kawai ya debe ni shine na kasa fito, maki ta hanyar daya dace,
Zata ci gaba da magana Maji ta katse ta da cewa haba dai ai wanan ya wuce ko shedan ne yaso ya rude mu baki dayan mu.
Amma aikomai ya wuce ko yar taki ce dai har yanzu ta kasa sakin jikin ta damu dai.
A haba Bintu ai komai ya wuce mana ki saki jikin ki da uwar ki ni na bar zance ai.
Lokacin Bintu tana daga cikin daki bata ma,san cewa hjy kubura tashigo ba a lokacin.
Sai da dare ne bayan ta idar da,sallah tafito daga ciki kamar yadda suka saba dan zama suyi hira ka fin a kwanta.
Don yanzu ba kallo saboda dan akwalan Tv su da,suke kallo ya tsaya cak yanzu ko sun kwala ma bai tashi kuma.
Haka yasa suke dan zaman hira tsakanin su wanda akasarin hiran tsakanin Amira ne da kaunarta maryam keyi.
Zaman Bintu da kamar minti uku Sadauki ya shigo dakin nasu, wanda alama ya nuna a gajiye yake a lokacin.
Gaba dayan su suka juya gare shi suna mashi sannu da dawowa.
Amma banda Bintu wace take a,tsorace don tun dawowan ta basu hadu dashi ba sai wanan lokacin.
Sadauki ya zauna a daya daga cikin kujerun falon da,duk sun tsufa sunyi taushi.
Nan Amira take cewa yaya daga gurin batun tafiyan ku kake halan naga duk ka gaji,
Da kyat ya daga kai ya bata amsa da,wallahi tin safe muna can a na abu guda sai yanzu na samu na cika komai nawa.
Nan suke ta faman yi mashi sannu da fatan samun alheri akan tafiyan shi.
Bintu taso ta share shi kada tai magana don gudun wani fitina don ta san ya tsaneta sosai a ran shi .
Amma kuma sai tai tunanen Maji bazataji dadi ba don ko banza zaman ta take a gidan.
Don haka ta dan waigo inda yake zaune tace yaya Allah ya tabbatar da alheri yasa a tafi a sa,a adawo da nasara.
Idanuwan shi dake a lumshe kamar maijin barci ya bude don tsinkayar muryanta da yayi daga sama a dakin don shi bai ko lura da ita,ba ma a dakin daya shigo sai yanzu.
Da kyat ya iya amsa mata da Ameen kawai tare da gyara kwanciyar shi da yayi.
Bintu bata kara bi ta kan shi ba ta juya masu baya tana fuskantar Maji dake can gefe daya a zaune.
Ganin yaki ya bar falon gata zaune a takure yasa ta niyar barin falon tare da mikewa tsaye.
Daidai Maji na cewa yauwa Fatima dauko mashi roban dabun da hjy kubura ta kawo mashi na tafiya.
Gurin da Maji ta nuna mata roban yana aje daga gefen daya na falon, sai ta juyo ta kalli maji din kamar zatai magana sai kuma ta nufi inda roban yake ta dauko mata shi.
Nuna mata inda yake zaune Maji tayi dakaii ta nufe shi da roban a hannun ta.
Ta isa gurin shi tana cewa, gashi yaya cikin wani murya ya dago kan shi, yana cewa may ye wanan kuma.
Daga inda Maji take zaune take ce mashi, nace maka mummy ku ce ta saka ai maka na tafiya wai.
Cikin dan tsuki yace haba Maji may zanyi da,wanan abin kuma don Allah ke kauce min dashi daga nan.
Haba Sadauki inji Uwar mata tai maka abin arziki kuma shine zaka saka mata da hakan babu ko godiya sai kawani ce wai a wuce maka dashi.
Maji ni bazan dauki komai ba sai yar jakar kaya na kawai ko shi kala daya zan tafi dashii don haka a mayar mata da kayan ta nagode.
Ke Fatima mayar inda kika dauko ki aje min kin ji wanan bai san arziki ba shi dama.
Yaya dabun kaza ce fa a ciki aiko a leda da ka saka,katafi dashii zai maka rana a can.
Ke nace bana so ko dole ne wai bazan karbi abin kowa ba watarana ai muna gori akan shi.
Maryam ma cewa tayi yaya naman kaza ce mukan kada a,mayar mata a bar muna zamuci.
Baza kuci ba ya bata amsa da cewa a mayar mata da abinta kawai don Allah please Maji.
Cikin sanyayar murya Bintu take cewa mama don Allah a mayar mata nima,ban yarda da wanan abinba wallahi.
Shiru sukayi gaba dayan su suna mamakin wace bata magana amma yau gashi tayi magana itama akan abinda bai shafe taba.
Lalai ma Bintu bakin ciki zaki muna kada muci ko may inji maryan take fadawa Bintu haka cikin zafi.
To sai munci shi in ke bazaki ci ba kinji.
Bazaku ci ba nace ya fadi a hasale ya juya gurin Bintu yana cewa ke dauka ki mayar mata kice nagode.
Ke Fatima aje roban ki zauna abinki Maji ta fadi haka cikin zafin rai.
Bintu takoma ta zauna bisa umurnin Maji din batare da ta dauki roban ba kamar yadda yace mata.
Har ya dan zauna sai ya mike tare da cewa ni zan fita sai dai da safe idan zamu wuce.
Bayan fitan shi ne Maji ta umarci maryan da ta shiga da roban daga cikin daki don kada mai tsaraban ta gani ta fahinci bai tafi dashi ba.
Mikewa Amira tayi tana fadin maryam dan tsaya,na dan diba kafi ki shiga,dashi na,tsinke miyau na.
Aa yatsine Bintu tace don Allah anty Amira kada kici abin nan don Allah dai haba mana.
Cak Amirah ta tsayar da hannunta da ta saka a cikin roban tafara diban dabun dashi.
Maji tace ke mayar da shi kin faye kwadai wallahi har yar karamar yarinya ta fiki hankalin sanin ya kamata.

****** ********* ******
Waahegari tunda farar safiya ya shigo dakin mahaifiyar shi yana saye da bakin wandon jeans na maza sai riga teashirt ja da ya saka yana rataye da yar jakar maza ta tafiya baka mai dogon igiya.
Sai ranan Bintu zata iya cewa taga alamar tausayi a fuskan shi don ya nuna damuwan rabuwa da uwar shi a fuskan shi karara.
Itako maji sai faman saka mai albarka take tare da fatan samun nasara a tafiyan.
Tana kuma kara jaddada mashi da yai wa Allah ya kula da rayuwan shi a can.
Suma su Amira har ita bintu da ke labe a gefe daya sai binshi suke da adduan samun nasaran tafiyan da zaiyi.
Maji ce takatse su da cewa katafi kai sallama dakowa na gidan nan kafiin ka wuce, shiru yadan yi na dan lokaci kamar zaiyi magana sai kuma ya juya yafita zuwa cikin gidan nasu.
Inda ya fara shiga gurin Umma, daga nan sai gurin mama Asiya duk dai kalman su daya ne shine Allah ya kai lafiya babu Allah ya,tsare yabada da,sa,a ko wani fatan alheri akan tafiyan nashi.
Daga gurin su ya nufi dakin mummy inda ya samu tana waya tana saye da uniform irin na nurses fari kal dashi.
Ganin abi ya shigo da,sallama takece wa wace suke wayan zan kiraki anjima zanyi sallama da dan kwallon gidan mu ne zaitafi yau.
Bayan tagama wayan ta juyo inda yakw tsaye dan karamin danta ya rike mai hannu yana,fadin nima yaya ka,sayo min kwalo idan kaje ina son in buga ball.
Zan sayo maka kaji Anwar yaba yaron amsa da hakana, mamakine ya kamata don ita,batai tsanmani ma har yasan sunan yaran nata ba.
Muryan mummy yaji tana cewa ashe tafiya ya tashi jiya,da dare Baba n ku, ke fada min zancen tafiyan naka ai.
Eh mummy zamu tafi ke nan tace don Allah idan an tafi ka kula,da kanka, sadauki Allah ya kai lafiya Allah bada sa,a tafada faram faram da ita.
Yace insha Allahu mummy nagode yasa kai zai fita take cewa an baka sakona ko ya dan murmusa yace eh nagode ,daga haka yafita daga dakin, yana jinta tana cewa yaranta ba zaku raka yayan ku bane, ?
Yaran suka mike suka biyo shi tare da rike mai hannu kowa da abinda yake fadin asayo mashi a can in yatafi.
Yasamu su Amira duk sun fito rakiyan shi inda ya kara shiga gurin maji sukai sallama.
Daga yan uwan shi sai yaran mummy ne suka fito rakashi a lokacin inda ya hau mashi yatafi gurin da zasu shiga motan tafiyan su zuwa lagos daga can zasu tashi.
Nan su Amira suka koma zuwa cikin gida suna ta hira akan tafiyan nashi.
Maji take cewa bari na je naiw mummy ku godiya don ban samu zuwa ba tun jiya kafin ta fita.
Har Maji takai kofa sai taji mummy tana waya don haka sai tai niyan juyowa tadawo harta gama wayan.
Abinda tajine ya bata tsoro don ji tayi mummy cikin dari take fadin yatafi kuma ya tafi da dabun can zai shiririce idan yaci ya kasa komai don yaji hadin kayan su na maye a ciki.
Wani irin shock ne ya kama,Maji a lokaci guda da,sauri ta juyo zuwa part din ta hankali a tashe tadawo dakin ta.
Jikin ta sai wani tsuma yake zuciyar ta na tafasa take wani zazzabi ya rufe ta a lokaci guda.
Ganin ciwo ya kamata yasa su Amira mata sheri wai kewan yayan su ne tafara yi tun yanzu.
Alhaji habu yana tsaye har motar su sadauki ya daga suka wuce a gaban shi ya nisa tare da,fadin Allah ya tsare a fili, ya juya zuwa kasuwa gurin harkokin shi na yau da kullun.

****** ********* ******
Nasir yai matukar mamakin yadda a lokaci guda abubuwa suke juya mashi sabanin farko da ya dauko harkan shi da kyau.
Karo biyu ke nan yana ganin zai samu nasara sai kuma abu ya jagule mashi ya kasa gane may nene matsalan nashi ne wai.
Kiris ya rage ya samu kan Nura amma kuma sai gashi abin ya juye mashi a lokaci guda komai ya,tsaya mashi ba kamar yadda ya,zata ba.
Hakan ne yas shi kara kwantar da hankalin shi don yasan duk yadda akayi akwai wanda yasan licked din shi yake mashi zagon kasa.
Sai dai duk iya tunanen shi yarasa ta inda abin ya samu matsala haka.
Don duk yadda ya,juya,da,Nura sam taki sauraren shi yanzu kamar yadda Raiha tai mashi da farko.
Ya bi duk ya,sukurkuce a lokaci guda ya rasa gane ma kan shi gaba daya.
Hakane yasa shi canza shawaran ya koma,wani guri da harkan shi tunda nan yana zargin an san aikin shi na boye.
Raiha ko duk wani movement di shi ta sani don kudin da take samu a gurin Michael yanzu bana wasa bane don haka ta saka masu bibiyan shi batare da ya sani ba.
Tsakanin ta da Nura yanzu ya zama masu babban alaka don a tare suke garalin su sun zama abokai na kut da kut.
Nura tabar gidan da take da farko ta canza wani gida inda Nasir bai sani ba.
Michael har sokoto yazo don Raiha inda ya ganta ya kuma kashe mata kudi masu yawa don akwaisu dama sosai.
Ranan da yagan ta cikin wani mota hadade sai da yai matukar mamaki kwarai yasan cewa yanzu ta wuce sanin shi ke nan.
Haka yasa shi fitar da rai zai kara samun kanta don yai matukar kwallafa ran shi da farko akan Raiha din.
Ga matsin da yake samu daga mahafiyar shi kan yayi wani aure yanzu sosai don ta saka shi gaba da zancen aure.
Ya yanke shawaran zai samu wata yarinya data kwanta,mashi a rai ya dan zarga da ita don kawai ya fita bakin mahaifiyar shi.
Amma shi sam aure bai a ranshi ya dauki aure kamar wani karin matsala ne ga,rayuwan namiji.
Don shi zaman shi haka na babu mata yana ganin crwa yafi mashi saboda baida wani nauyi a kan shi kuma da za,a saka mai ido.
Baida daman yin yadda yaso ace ga matsala kuma don mata saka ido gare su sosai ga namiji.
Shiyasa yake ganin zama da mace kamar zama da tonon asirin mutum ne.
Lokacin da yai aure a baya da farko akwai fahinta tsakanin shi da matar amma da ya fara nuna kalar shi nan matsala ya fara bulo masu tsakanin su.
Yau tace ba zai fita ba gobe kuma tace baya kwana da ita yaya ma zai kwana da ita ga mata birjit a gari bila adadin sai wacce ya zaba.
Haka sukai ta samun matsala har dai auren ya mutu kowa ya huta don tace bazata iya zama da namiji hoto ba a gida.
Hakan ne ya,bashi daman sheke ayar shi yadda ran shi ke so batare da samun wani matsala,ba kuma.
Amma yanzu ga Inna ta saka shi gaba akan wai sai ya kara wani sabon aure kuma again.
Raiha dai yanzu ta bushe fitilar ta ga yan uguwar su masu saka mata ido.
Don yanzun bata kunyar kowa kuma tafito fili tana harkokin ta babu kunya ko tsoron wani.
Da farko ana kai karanta gurin iyayyen ta amma sai mutane suka fahinci da daurin gindin iyayyen nata,take al,amarin ta haka kowa yakawo ido ya saka mata ba ruwan kowa da al,amarinta kuma.
Idon su yai matukar budewa yanzu babu ma wanda zai iya tunkaran ta duk cikin fadin shiyan su dasunan wai nasiha gareta kuma.

****** ********* ******
Maji tana kwance Bintu ta shigo dakin cikin damuwa ta dan kai wani lokaci tsaye a kanta cikin tausayawa halin da ta ganta a ciki.
Bintu tace sannu mama da kyat ta iya amsa mata sai Bintu din ke cewa mama ko a kira maki Baba ne kuje asibiti.
Murmushi ta,dan kakaro a fuskan ta tana cewa barshi kawai Fatima,dauko min dai ledan can cikin drawer akwai magani na a ciki.
Da,sauri ta fita,sai gata dauke da cup din ruwa mara,sanyi ta,dauko ledan maganin ta nuna mata wanda zata,bare mata tasha.
Yan mintina Amira,dake wanki a,waje tashigo dakin tana cewa a,a Maji jikin ne haka.
Kodai mu kira Baba ne kuje asibiti kada ciwon kuma,yafi nan.
Tace su barshi kawai tasha magani ai yanzu zata ji sauki idan bai bari ba,sai su kirashi kada yazo yai fadan ba,a fada mashi ba kamar kullun.
Ganin ta samu barci har lokacin suna tsa tsaye a kan ta yasa yaran fita daga dakin zuwa falo suka zauna suna magana akan ciwon nata.
Don sunga lafiya aka tashi da ita da safe sai gashi kuma dan wani lokaci zazzabi ya rufe ta.
Amirah tace ni dai Allah yasa ba,Maji ta saka zancen tafiyan yaya a ranta bane haka har wani abu ya samay ta can.
Zuwa wani dan lokaci Bintu ta kara lekata inda ta samu ta danji sauki harta tashi tayi sallah azahar a lokacin.
Ta juya zata fita daga dakin ganin Maji tana sallah a lokacin yasata barin dakin don taga,ta dan samu sauki,.
Fatima zoki zauna, inji Maji daga inda take zaune ta furta hakan wa Bintu.
A hankali Bintu ta juyo daga niyar da,tayi na fita daga dakin na maji.
Daga gefen maji takai katsa zata zauna sai Maji tace a,a dawo nan gefen gado ki zauna.
Nan ma yai min mama inji Bintu take fadin haka wa Maji din.
A,a ni nace aiki dawo daga nan gefena ki zauna don magana nake son muyi ni dake.
Yadda Maji ta umurce ta dayi ta mike tayi don haka sai ya kasance sun zauna gaf da gaf da junan su.
Cikin murya irin ta mai jin jiki Maji takira sunan Bintu a hankali tana cewa Fatima magana nake son muyi dake don Allah ki fada min gaskiya idan kin san wani abu cikin dan zaman da kikayi da hjy Kubura na yan kwanaki a kaina ko kan sadauki yayan ku.
Shiru Bintu tayi da,farko sai da Maji ta sake mata magana Bintu ta dan gyara zama a hankali kamar wace aka tsure, mama ban son in furta komai akan wanan matar don bazan so ace a sanadin zamana a gidan nan an samu matsala a kaina,ba.
Jinan Fatima abinda naji yau hjy kubura na fadi a,waya nasan duk yadda akayi kema kin san dan wani abu daga cikin mugun nufinta a kan mu.
Don yadda naga kin hakikance jiya akan kada kowa yaci dabun naman da,takawo aba,sadauki tsaraba.
Sai gashi yau na shiga gurin ta don nai mata godiya, amma kuma ban kai ga karasawa ba sai naji, muryan ta tana,waya.
Abinda naji ga wayan yai matukar girgiza min hankali na yau, don ban yaba zaton kishinta a kaina ya kai irin haka ba.
Na dauka kishine kawai na iya fatar baki a tsakani na da ita, na zata bata cikin wa yanda zan iya tuhuma da zasu iya min abinda zai kasara ni ko iyalina.
Amma kassh sai gashi zafin kishi yasa Kubura ta rufe idon ta tana aiwatar da mugun nufi mai muni a kaina.
Subbahanallahi mama, wallahi ko Fatima kinji abinda naji tana fadi a,waya.
Cikin sauri Bintu take cewa zata iya shi wallahi don, nima ranan na farkz a cikin dare ina jin yunwa sai na risketa tana waya nan ta fadawa Maji abinda taji kuma take cewa da fatan maji zata rufe ta kada ta nuna mata tasan manufarta gareta ,
Maji tace nagodewa Allah da,bai sa yaron nan ya tafi da,wanan naman ba don Allah kadai yasan iya mugun abinda aka, zuba acikin yin dabun don kawai yaci ya kara lalace min.
Kai wai duniya ina,zaki da mune haka,wai, kana tare da mutun tsakani da Allah ashe shi na ciki yana ciki da kai.
Yanzu kinga Fatima abinda nake so dake shine idan dare yayi ki dauki roban danbun nan ki kaishi can nesa da gida ki zuba a cikin kwata yadda wani ma ba zai iya cin shi ba kada mu cuta mashi.
Kina jina daga yau kuma ina son ki mayar da hankalinki a kan hjy kubura a gidan nan sosai don Allah Fatima amana nake son baki kan yarana kinji ki sa ido sosai akan duk wani takon ta a kan mu,,
Maji tana kawowa nan zataci gaba da magana sai ga Amirah ta shigo dakin ganin irin zaman da su kayi a tsakanin su yasa take masu kallon tuhuma.
Don ko da su Bintu bata wanan zaman haka a tsakanin su, sai gashi yau ta gan su a haka da Maji.
Maji ta kawar da tuhumanta a kansu dace wa Bintu tashi ki tafi Fatima nagode da maganin da kika bani zai kara sa naji sauki gashi kuma kin shafa min robb a baya dakai.
Haka yasa Amirah tai saurin kawar da zagin su a kanta taga kamar robb din ne ta,shafawa Maji da kuma magani.
Bintu tafita daga dakin sai Amira ta karasa tana fadin Maji ya jikin ai na zata kina barcin ne har yanzu.
Ashe har Bintu tashigo ban sani ba ta baki magani, Maji tace ai Fatima akwai kokari wallahi tazo ta samu har nayi sallah shine nace tabani magani nasha.
To yaya jikin naki tace Alhamdullahi ai na samu sauki yanzun ma zan fito falo, kun dafa abinci kuwa?
Tun dazun Bintu ta girka harda na dare tai muna a lokaci guda ai.
Amirah ta juya tafita daga dakin Maji dake zaune ta sauke ajiyan zuciya bayan fitan ta.
Sai zuciyan ta ya fam da mamakin irin sallon kishin hjy kubura na boye da ba,a gane takon ta don a fili tana nuna ba wani matsala a tsakanin su amma ashe a zuciyar ta tafi masuyi a fili sheri.
Nan dai ta bar zancen a ranta akan dai zata saka ido sosai ga yaran ta a cikin hikima duk zata hore su da gujewa sherin boye na kishiyoyin ta gaba dayan su.

****** ********* ******
Jirgin matafiya ya sauka a garin ghana wanda ke cike da matasa yan kwallo da aka zabo daga sasan nahiyar Africa mafi kusa da zasu buga wasa a tsakanin kasa shen su na zakaran gwajin dafi da za,ayi masu.
Kamar yadda Sadauki yake a gida na ba ruwan shi da kowa ko a wanan tafiyan ma haka ce ta kasan ce dashi.
Don kowa na aboki amma shi halin shi na nisanta kan shi da kowa yana nan bai shiga tsabgar kowan su sai shi kadai yake moving din shi.
Kwanan su biyu aka,fara fita dasu a gurin wasa inda wasa ya fara fafatawa a tsakanin kashen da suke da hadin gwiwa.
Yadda sallon wasan shi yake yasa tun ranan farko ya fara shiga idon mutanen dake kallo da kuma shugaban nin su na wasan.
Kafin wasa yakai karshe saida Umar ya masu ci biyu mai ban haushi kusan lokaci guda.
Haka aka,tashi daga wasan kowa na farin ciki da shi a gurin, Umar bai tsaya takan masu mashi ihu da murna.
Hudubar kakan shi da sukaje kauye ganin su don yai masu sallama akan tafiyan da zaiyi.
Dattijon yake cewa tau mai sunana ni ba komai zan fada maka,ba sai kawai nace ka rike Allah.
Kada kaje kayi sakaci da ibadan ka duk abinda zakayi ya kasance ibadan ka shine a gaba da komai na rayuwan ka.
Yin haka abokina zaka ga tarin haske mai albarka yana sauka maka ga al,amuranka ko yaushe.
Kayi kokarin kare matabar addinin ka aduk inda kake dana iyayenka wanan shine hasken da zai maka jagoran rayuwan ka.
Wanan dalilin yasa yana fitowa hudubar kakan nashi ya fado mashi a rai don haka ya dauki roban ruwan da aka aje masu nasha, guda biyu ya koma bayan motar su ya fara alwala kafin a kwashe su zuwa masaukin da aka sauke su.
Duk wanda yazo don su gaisa sai ya samu Umar yana sallah a tsanake cikin natsuwa.
Yana idarwa ya karaso inda mutane suke yafara mika masu hannu daya bayan daya.
Wanan halin da yake na rashin sakaci da ibadan shi yana burge wasu yayin da wasu can daban masu akidar wani addini suke hassada akan hakan.
Wanan matsalar ba Sadauki ba kusan yan wasan mu musulmai haka suke samun wanan hassadan daga yan hassadan addinin musulunci.
Don su a ko yaushe bukatan su suga cewa sun ja ra,ayin diyan musulmai su raja,a da addinin su shagaltar dasu

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment