Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yana cewa ki fada mashi wallahi zanyi maganin shi don na lura kamar ma ya fara shaye shaye ne a rayuwan shi.
Niko bari kiji in har hasashe na ya zama
gaskiya to wallahi ba zan barshi a gidana ba ya bata min sauran yara na na kirki.
Allah ya tsare ya kare Maji ta furta a fili aidama haka kawai zaki iya cewa bayan shi baki da,wani abin fadi ai,
Bata ce komai ba,sai hadiyan bacin ran da tayi tare da juyawa tana fadin Allah ya kyauta.
Malam Habu yace ai zai zo ya samay ni zan mu hadu dashi don ba zan yarda ya,sabauta min yara ba ga banza.
Maji dai fita tayi daga dakin don tasan ko ta,tsaya,babu abin da,zataji banda bacin rai kawai.
Din haka taiwa kanta kiyamallaini tabar dakin don bazata iya jure sauraren kalaman mijin nasu ba akan ita da dan ta.
Tafiya take zancen mijin nasu gareta yana ci mata rai don zancen sadauki shi ne zance mafi muni dake hada ta,da maigidan nasu.
Duk irin kwaram din da,aka,sha a,baya baya akan kishiyoyinta da ita a baya, baya tayar mata da hankali kamar zancen sadauki da ya taso mata a yanzu,
Yanzu saboda shi tana ji tana gani duk wanda ya kwaso zancen shi akan tane zai yaba mata don halin dan ta kawai,
A kulun kalaman maigidan ta ga dan ta yanzu yana kona mata zuciyar ta da jikin ta ba ma zuciyar ta kadai ba,
Ita a,zaton ta ai wanan abin abinda ya shafe su ne baki dayan su bawai ita kadai za,a dorawa laifin ba don itace mahaifiyar shi ne kawai kowa ke ganin laifin ta ita kadai.
Abin da ya kamata su taru su nuna bacin ransu a kai su tayata bakin ciki amma sai gashi kowa ya,zamay yabarta da laifi ita daya.
Amma babu komai ta furta a,ranta tare da hade yawun bakin ciki a cikin ta, tana mai sauke ajiyan, zuciya kawai.
Bata ankara ba,sai hawaye kawai taji yana biyo mata a idon ta.
Gaskiya zancen Sadauki yana tayar mata da hankali sosai ta rasa wanda zata kai kukan ta gare shi ya tayata bata shawara a cikin gidan.
Don duk yanzu suna matukar nuna mata kyama akan zancen shi gabadayan su gidan har shi maigidan kan shi.
Shin may nayiwa Allah da yai min wanan mumunan jerabawan haka akan dan tilon da daya da Allah yabani namiji a duniya ?
Ni dai nasan harga Allah ban cuci dan kowa ba a rayuwana da wanan jerabawan yafado a kaina.
Duk da ni marainiya ce na riki maraici na ban kai kaina inda Allah bai kaini ba, ina zama a matsayina na mara galihu har a gidan aure na.
A hankali ta kara lumshe idanuwan ta tana tuno rayuwanta na baya da kuma irin kokatin ba yaran ta tarbiyan da takeyi.
Ba komai take kara tunawa ba,sai irin dafin bakin da maigidan su yake mata a,baya,
Da yakan ce maijidda duk da ba komai ke gare ki ba,a,duniya ni ina sonki a yadda kike.
Don kina da komai da nake bukata sabida ke ta daban ce acikin matana, ba zan iya jure rashin mace irin kiba .
Kallo daya in nai maki yana wanke duk kan wata matsalar rayuwana don haka nake kwadayin samun zuri,a dake don nai alfahari dasu koda bayan rayuwana ne.
Murmushi gami da hawaye ne yazo mata a lokaci guda ta furta namiji kanin ajali.

****** ********* ******
Akwana a tashi yau Bintu satin ta hudu gurin gwago Asmau a garin sokoto.
Kullun sauraren take raji gwago na mata zancen zuwa gida amma shiru kake ji ba zancen, har ranan ta gaji tai wa gwagonta zancen komawan ta gida amma sai gwago take ce mata.
Haba Bintu yanzu ke har kina sha,awan komawa gida gurin wanan bakar matan uban naki mai mugun nufi a kanki ko yaushe.
Nifa da mahaifinki mun yanke shawaran kiyi zaman ki a nan don yace hankalinshi yafi kwanciya idan kina a guri na ko kiyi ni sa dasu kadan.
Don haka ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan ba zancen komawa gida don hankalin mahaifinki ya kwanta.
Badon Bintu taso ba dole ta yarda da zancen gwago din don tasan haka zancen yake.
Kullun adduan mahaifinte ke nan akan Bintu Allah ya kawo lokacin da zaki bar gidan nan zuwa wani guri ke ma ki huta hakana wa rayuwan ki.
Tunda mahaifiyarki ta barki bata damu da damuwar ki ba ko wani hali kike bata sani ba.
Gaki yarinya natsatsiya duk halarcin da kikewa matar nan da diyan ta kina bauta masu dare da rana ba gani take ba.
Amma kiyi hakkuri da irin rayuwan da kika tsinci kanki a ciki haka Allah ya kaddara maki taki rayuwan zai kasance a gidan uban ki.
Hawayen da ya silalo mata ne ta dan sa gefen hannun ta ta share a hankali.
Duk lokacin gwagon tana kallon ta a cikin muryan kuka ta dan dago kanta a hankali tace to gwago zancen karatuna fa ?
Wanan ba matsala bane ai Bintu zan yi magana a,samo maki makaran tar jeka kadawo dake can kasan layin mu ta gwaunati sai kici gaba da zuwa ko?
A hankali Bintu ta,daga kai alaman taji ta juya jiki ba karfi zuwa cikin dakin kwanan su don ta gyara masu saboda yamma yayi kuma,su basu sharan dare saboda ance baida kyau, yana kawo tsiya a gida.
A kwana a tashi ba,wuya a,wurin Allah Bintu tafara zuwa makaranta kamar yadda gwago tai mata alkawari a baya.
Da yake Bintu yarinya ce mai hazaka baiwanta daga Allah ne, sai bata sha wani wuya ba sosai a cikin karatun ta komai tana ganewa yadda ya dace.
Yawan aiken da take mata gidan malam Habu yadan sa tasaba da Maji da yaran ta don a gurin su kawai take dan samun fuska a gidan ko su ba wani can sosai ba.
Sai dai idan Maji ta aiko sayen masa in har Bintu ce a kan tandar suyan waina sai ta cika masu kula fam tace akaiwa maman ta.
Haka yasa watarana Maji tasa su Amira su dan yi kwalemar kayan su su ba Bintu don taga tana da bukatan haka saboda rashin wadatan da basu dashi ita,da,gwagon nata.
Gwago Asmau batai sanyi a kafa ba gurin shiga gidan don taiwa maji godiya ita da yaran ta, da suka ba yar ta kyautan kaya.
Ta shiga gidan bayan sallah azahar lokacin Bintu ta dawo daga makaranta ke nan.
Tare suka shiga ita da Bintu din, inda suka samu maji zaune a falon ta kasan tias din dakin nata tana gyara wani ganye da,alamar magani take hadawa dashi.
Sallaman su yasa ta dan gyara tana mai ansa masu sallaman su da fara,a a fuskan ta.
Sun gaisa da,gwago inda tafara zabga masu godiya tana mata fatan alheri akan alherin da sukai wa yarta, Bintu.
Cikin murmushi Maji take cewa ai Bintu yarinyar kirki ce halin alherinta ne yasa sukai mata haka.
Sun dan fara hira tsakanin gwago da Maji inda gwago ke cewa wallahi nakan so shigowa mu gaisa da ke, amma kuma yanayin gidan naku ne baida dadin shigowa don kowa idan ka,shigo sai ya,dinga ma kallon munafuki.
Maji tace haba dai hajiyan masa ai ba yau muke dake ba koma sun zarge ki da hakan ai su ma mutanen arzikin su suna shigowa gidan nan amma ban damu dasu ba ni.
Gwago tace ai babu komai insha Allahu zan dan dinga shigowa idan na,samu lokaci.
Suka mike suna,wa junan su sallama nan gwago ke cewa ina Sadauki ya yashiga kwana biyu bana ganin shi dai.
Murmushi Maji tayi tana cewa yana nan baidai zamane suna batun rubuta jerabawan su na karshe ne shi yasa ba,a ganin shi yanzu.
Allah sarki inji gwago Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a Allah ya tsare muna su daga duk wani abinki dana sheri a rayuwan su.
Amin inji maji inda taji dadi sosai da addu,an mai masa da,taiwa sadauki wanda ta dade rabon da taji wani mahaluki yai mashi wanan adduan.
Har,zasu fita Maji tace su dan tsaya tazo inda tashiga daki ta dauko masu dan sabulun wanki da clean cikin irin wanda mijin su yake kawo masu duk sati don wankin tufafin su.
Gwago tana ta godiya da fatan alheri ga maji suka fito, a tsakar gidan nan suka hadu da amaryan su tana shigowa gwago na gaishe ta wani kallo ta,watsa mata na ke wacece ?
Gap da zasu fita daga get din gidan suka hadu da sadauki yadawo ko kallon arziki basu ishe shi ba sai ma gwago ke ce mai Umar sanda mazan fama andawo daga bokon ke nan ?
Ya wani sha toka fuska babu walwala ya ansa ciki ciki Maji dake tsaye daga bayan su data rako su take ce mai bakajin hajiyan masa tana gaida kai ne sadauki
Yace cikin wani murya ai na amsa mata mana ya shigewan shi part din su na,samarin gidan.
Allah ya shirya ka inji maji ta furta a fili sai gwago tai dan murmushi tace amin ke dai ai yaran yanzu sai addua kawai.
Ke dai kibi abinki da,addu,a Allah yasa halin iya kurciya ne kawai .
To Amin hajiyan masa halin wanan yaron sai shi wallahi haba bari fafin haka mana inji gwago ke zaki kara jan abinki ga jiki kina lurar dashi dasannu zai bari ai wanan kurciya ne Allah yasa takara fadi tai masu sallama ta tafi.
Bayan sun tafi maji taga yadace tabishi dakin shi suyi magana tunda Allah yasa yashigo a gaban idon ta.
Yana duke yana hada wayan tv tashigo dakin abinda yasa shi saurin dagowa ke nan daga inda yake duke.
A hankali take bin dakin dake hargitse da kallo sai warin dakin irin na,samari ke tashi daga dakin.
Cikin ya mutse fuska take ce mashi, yanzu kaiko inda kake kwana baka iya gyarawa babana ace dakin dan musulmi ne haka inda ake ibada?
Wai may ke damun kane haka babana na zaci kaine mutim na,farko da za,ayi koyi da halin shi nagari a gidan nan sai dai kasshh ban samu hakan daga gareka ba sadauki.
Naga alamar abinka ba mai yankewa bane, sai a lokacin yadago kai yadan kalli mahaifiyar tashi yana fadin may kuma nayi yanzu maji?
Yanzu fa na dawo daga makaranta tun safe da nafita gidan nan .
To babana shine baka iya,gyara muhalin ka haka dubi fa kagani ai wanan wani abin cutarwa ma yana iya shigo maka baka,sani ba.
Zan gyara ya bata ansa a takaice don yasan duk lokacin da tai amfani da kalaman babana a,gars shi maganace ta kwantar da hankali da fahinta take nufi a gare shi.
Don ba ko yaushe take amfani da kalman babana a gare shi ba tafi kiran shi da,Sadaukin da kowa a gidan yake kiran shi kamar yadda mahaifin shi yake kiran shi dashi tun yana karamin shi dashi.
Ta,dan dade a,tsaye tana kallin shi a cikin tausayawa dan nata ga,irin rayuwan shi ta bahagon halin da ya,fada ciki.
Hawaye ne ya,gangaro mata a,daidai lokacin da ya,dan dago kan shi ya kalleta don jin da yayi tayi shiru a,tsaye bata fita ba daga dakin.
Shiru yayi yana kallon ta sai ya dan dukar da kan shi gareta, tace babana ban son ganin rayuwan ka haka .
Wanan rayuwan da kake yi ba,shine irin rayuwan da na,soka dashi ba a,rayuwan ka.
Don Allah babana ka canza rayuwanka a gidan nan ka koma kamar ko wani yaro na gidan nan.
Ina son naga ka canza ka koma normal life din ka kamar kowa a gidan nan wanan halaiyar dakakeyi ba,rayuwan alheri bace a gare ka damu ma kan mu da muke naka.
Katai maki rayuwanka saudauki ka canza halinka don Allah kazamo min abin alfahari a,duniya, gama kowa dake tare damu.
Zan so ace na zamo uwa abin alfahiri ga duniya na nasamu da dan albarka a,rayuwana, kamar yadda sauran uwaye suke alfahari danasu diyan.
Zan so ka,sasauta halaiyar ka akan wanda kake a yanzu don samun natsuwar hankalina dana mahaifin ka.
A hankali maji ta fashe da kuka,wanda kuka ya sa ta kasa karasa maganan da take son ta fada mashi.
Maji ya ce cikin sanyin murya nifa ban san wani hali da nake yi ba,wanda har zaisa ki zubar da hawayenki haka akaina.
Kallon shi maji tayi a cikin mamaki don watau shi bai fahinci ma yana,da nakasu ba ke nan tare dashi.
Tace kako san har mutanen gidan nan sun fara zargin wai kana shaye shaye ne,
Ya,dago kai da,sauri ya,dan kalle ta sai kuma ya dukar da kan shi yace maji nifa wa yan nan mutanen sun fara isa ta,sun fara saka min ido har da bina da,sheri haka?
Ni dai ka gyara halinka shine bukatana a,gare ka idan ka gyara babu wanda zai dora ma,sheri ai.
Ta juya tana cewa Allah ya kyauta kaji bukatana gareka don naga yanzu guduna ma kakeyi baka son shigowa nasan lafiyan ka kamar yadda kasaba yi a baya.
Bin bayan mahaifiyar shi yayi yana mamakin mutumin da,yafara gano likin shi a gidan don haka ya zama dole ya canza takon shi tun mahaifan shi basu tabbatar da,zargin su ba akan shi.
Don yasan in hakan ya tabbata ba karamin tashin hankali mahaifiyar shi zata shiga ba har ma mahaufin shi din dake nuna yanzu babu ruwan shi da shi yanzu.

****** ******* ******
Zaune take ta tula kudi a gaban ta,sai faman kidayawa take a hankali don gudin tai kure.
Sai da ta kirga su cif tajera a,faban ta tana kallo sannan ta,sauke ajiyan zuciyar ta.
Yanzu abin da ya rage min na hada kudin fridge din nan saura dubu goma don haka bari na kara kaimi naga sun hadu na,samu kafin azumi na dauko babban fridge wanda zai isheni sana,a yadda nake so.
Tashi tayi da sauri ta mayar da kudin inda ta ciro su ta boye, don gudun kada wani ya gani yasan inda ta,aje don tasan da,zaran maigidan ta ya kyala ido yaga kudin nan sunan ta sorry don yanzu zai mata dadin baki sai ya karbe su gaba daya su huta.
Abinda bata sani ba shine shi maigidan nata sam hankalin shi bai ga,abin hannun ta ko kadan don asali ma,shi bai bukatan wanan sana,an wahalan da yaga tana saka rayuwan ta a ciki yanzu.
Don da,ace yana,da,hali da iyalin shi sunji dadin rayuwa a gurin shi.
Amma ina talauci kamar ya yanke saka ne a kan shi don kullun bida yake amma kamar ba,ayi yake sai dai Allah bai hanashi dan abinda zasuci ba agidan daidai gwargwadon hali.
Mikewa tayi ta gyara dakin har zuwa tsakar gidan su don akwaita da,tsabta ko yaushe duk da,talaucin su zaka,samu gidan su tsab tsab dashi.
Yaran tane suka fara dawowa daga islamiya inda tun a,waje tasan da zuwan su din saboda hayaniyar su da taji tun daga waje.
Sannu da gida Umma suke cewa sai faman ce masu take kun dawo sannun ku da,dawowa ,
Yar karamar yar ta,take cewa mama yau a makaranta malam yai muna alwala mungani nima zan iya yadda yai muna nagani.
Nanyaran suka shiga bata labarin yadda malamin su ya koya musu yadda ake alwala har lokacin da mahaifin su yadawo daga kasuwa suka juya gurin shi yana,alwala suna bashi labari n abinda yafaru a islamiyar su yau.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

A LOKACIN MU KE,,,
4⃣

Waya take sai ko mama dake kusa da ita bata iya jin may take fadi a,wayan , saboda matukar tausa muryan ta da tayi ga wayan.
Sai yar dariyar da tayine yasa mama dake zaune saman kujera yar tsugunno dago kai tana mata kallon mahaukaciya.
Ta dan dauki lokaci tana wayan cikin jin dadin abinda ake fada mata ga,wayan wanda babu maijin ta balle a san abinda su ke fadi.
Mikewa,tayi zuwa cikin dakin su inda ta kwanta saman dan gadon katakon dake dakin mahaifiyar nata.
Nan ta shige cikin katon hijjab ta rufe kanta sai dai hannunta na akan gaban ta zuwa kirjin ta a hankali take dan shafa,su don kada a gane may take a lokacin.
Nan taci gaba da,wayan ta na tsawon lokaci mai tsawo sannan tai wani mike barci ya dauke ta.
Haka mahaifiyar ta ta shigo dakin daga gurin girkin da take yi ta samay ta kwance tana barci,
A fili ta furta kai amma,anyi malalaciyar yarinya gurin nan yanzu barci kikayi ashe ni ina jiranki ki min shara a,tsakar gida.
Nan dai uwar dole itace ta karasa aikin ta,da kan ta inda Raiha bata farka ba sai bayan sallah azahar ko shi sai da kyat uwar ta,tayar da ita don tai sallah.
Bayan ta gama cin abinci a lokacin har uwarta na zance dora girkin dare don yamma tayi sai ga Raihanatu tafito a cikin shiga na fita da katon hijjab din ta har kasa.
Sai dai kassh da mutum zaiga mai ta sa a kasan ta da yayi tir da Allah waddai da irin shigar ta haka.
A,a Raihatu ina kuma zaki a wanan lokacin bayan yamma ya riga da yayi ko?
Mama dan wani guri ne zan tafi ba,wai dadewa zanyi ba yanzun zan dawo mama.
Tana fita bata tsaya ba sai shagon sayen kayan mayen su wand kamar kullun gurin ya zama majalissan matasa yan maye kala kala.
Duk da jami,an tsaro suna kawo masu samay akoda yaushe suna zuwa kama mata a gurin masu dabian shaye shaye.
Can ta kutsa tashige daga ciki gudun kada wani yagan ta a gurin don gudun ganin idon sani.
Brosha na ganin ta a lokacin yana mikawa Umar kayan harkan shi Umar wanda yake tsaye da bakaken kaya fuskan shi a murtuke.
Burosha yana ganin ta ya fara washe bakin shi cikin farin ciki da ganin ta yana cewa
A,a yau mutumiyar an shigo ke nan kayan aiki sun kare ke nan dai ko don ba,a ganin ku sai rana,tai zafi.
Ya dauko canji zai mikawa Umar yake ce ko yau din ma,za,a barmata canjin ne dan wancan katon ma naga kai ka biya mata.
Wani kallo Umar ya watsa wa Raiha yace cikin dakiya don Allah ka,sallamay ni don kasan ban son ina dadewa a gurin nan naku,
Raiha cikin yatsune fuska tace aikowa ma,sauri yake don ba wanda yazo don ya tsaya .
Kamar Umar ya bata amsa har ya dan bude baki da zuman yai magana sai kuma yaja bakin shi yai shiru .
Borasha ya mika mai canjin shi yai gaba bai tsaya bin ta kan raiha ba balle ya kulata ma.
Bin shi Raiha tayi da kallo tana fadin ji shi kamar wani mutumin kirki wai sauri yake bai son a gan shi.
Brosha yace to ke nan fa wanan zubulelen hijjab da kika,sa wa zai dauka ba islamiya zaki a haka ba .
Dallah gafara malam nagafa kafara saka min ido don tsokanarka ya fara yi min yawa fa.
Dan sa ido kawai ina ruwan ka da shigata wanan nayi ne kawai don batar da sau amma a ciki ai shigar manya ne nayi sai ta dan daga mashi hijjab din ta inda ya hago wani matsatsen rigar da ta,sa duk nonuwan ta sun dan bultso a gaba sai dan guntun buje na zuwa part dakd saye a kunkurun ta iya cinya kawai.
Kai brosha ya daga tare da fadin kai amma Raiha kin kai shu,uma irin wanan shigar haka sai ina?
Don dai nasan da,akwai inda kike nufi zuwa da wanan shigar haka da kika boye cikin wanan katon hijjab din naki.
Tai wani har da idanuwan ta tana cewa ashe ka gane ke nan mazan, yau casu gare mu har dare shiyasa na dauki kayan aikina don ya taimaka min a can,
Tirka sa ki ce yau akwai babban harka ke nan raiha don nasan mutanen mu zasu hadu a gurin,
Tace hakane amma ba,wai irin wa yan nan ba wanan gayu ne masu harka da kwalabe da manyan wa yan nan,
Nima hanya akai min don naje naba idona abinci ko zanyi cafka a can don kasan ala,amarin sai da kwaskwarima ciki wanan lokacin don gamu nan birjit ko ina kowa na rabon ido yasamu mai cafkan shi.
Gaskiyan ki Raiha nima nasan sai da haka al,amarin don abin ba,a cewa komai.
Aje lafiya a dawo lafiya a yo muna kamu babban giwa mu sha shagalin mu muma ga,aljihun shi.
Ta,wuce tana tafiya a cikin rangaji da layi irin nasu na mashaya da suka goge a fagen boyon kan su, don batar da kaman nin su ga mutane.

****** ********* ******
Guri ne mai kyau da,shuke, shuke ko ina bakajin komai sai sautin kidan dake tashi na turan ci na mawakan Afrika.
Tana fita daga cikin napep din da ya kawo ta ta samu dan nesa kadan ta cire hijjab din dake a jikin ta tare da dan kara gyara tufafin dake jikin ta.
A hankali take takon ta zuwa inda mutane sukai dan dazo akasarin maza da matan gurin zakace ko ba diyan gari bane.
Don irin shigar su da kuma aakin kan su sai mutum ya rantse cewa ai a wata kasar arna ya ke ba cikin garin sokoto ba ma gari shehu usman dan fodio.
Mutumin da yai gwagwalmaya akan addini a kasa da,watsa su har sauran kasashen duniya don amfanin al,umma.
Amma,yau sai gashi a,kasan shi garin shi duniya da lokaci yasa matasan kasar kwaso akidar yahudawa suna yadawa da cusa shi ga,sauran masu tasowa na baya.
Wanda ba,a sokoto ba kawai yanzu ko ina a kasashen hausaw a na samun wanan akido jin na koyan akidar wasu da,al,adun su.
Allah ka tausaya muna ka,shirya muna al,umman mu yaran mu kan,nen da ma,sauran yan uwa musulmai baki daya,
Da farkon shigan Raiha a guein ta dan sha jinin jikin ta don tana ganin abinda yafi karfin idanuwan ta.
Sai da ta hadu da,wasu kawayen ta biyu haka yadan sata sake jiki dama can sune suka gaiyato ta gurin.
Daga inda take a zaune tana bin mutanen gurin da,kallo a fakaice tana kallon irin shigar da mata da mazan gurin sukayi abin sai shukaran kawai.
Don nata shiga ai mai sauki ne bisa ga na wasu yan matan yadda suka saka dan mitsitsin abu a jikin su abin ba dadin gani
Raiha sai tarena kanta a guri don taga iyakar wayewa

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment