Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai murmushi tana cewa Alhaji ya dawo ke nan nasan an fada mashi.
Kai wanan matar batayi ba wallahi yanzu bayan an biya ta bucket din ta kuma,shine sai ta fadawa Baba zancen.
Maryam tace ai in bata fadi yayi masifa wa maji ba hankalin ta baya kwantawa.
Mikewa Maji tayi bayan ta shafa tafita daga dakin zuwa gaida Baba da dawowa daga kasuwa.
Ta samay shi shi da mama da uwargidan su a falon shi zaune tai mashi sannu da dawowa,da yaya kasuwa.
Ta juya zata wuce sai maigidan nasu ya ce maijidda yaya akayi dan ki ya fasawa Asiya roban ta da gangan?
Shaye shayen nashi har yakawo a,cikin gida cikin iyalina kuma?
Shiru maji tayi tana maijin kunan zancen baba a ran ta sai dai cikin dakiya yau karo na,farko tun da ya fara mata cin fuska a gaban kishiyoyin ta kan dan ta tace.
Da na ko dan mu Alhaji ina bani kadai na samu yaron ba tare da kaine kuma a tare mukai mashi ladabi a cikin gidan nan gaba dayan mi daku.
Don haka sai makiyin Allah zaice ban ba sadauki ingantaccen tarbiya ba a cikin gidan nan.
Kawai dai Allah ne mai yin ikon shi akan duk wanda yaso ni kuma nasan bawai Allah yakini bane ya mayar da dan da yafito daga tsatso na haka a,rayuwa ba.
Ai bazata bari a,fadi ba don kaga har roban ta,sayo ta mayar ma Asiya da abinta wai don ta nuna ita ta haife ta.
Maji tace yaya Asiya ya kike son nayi kin face yau idan ba,a biya ki roban ki ba,akwai tsiya a gidan nan don babu mai rabaki da shrgiyar uwar shi sai Allah.
Alhaji ya juya yana cewa ke ko Asiya haka kika ce mata don maganan maji yadan sa jikin shi yin sanyi.
Ba dole ince haka ba tunda yana takamar shi dan iska ne har iskancin yakawo ga kayana tun yana dukan min yara yau kuma ya koma ga kaya na.
Idan ko haka kikace gaskiya baki kyauta ba don dai kinga maijidda ba itace ke tura shi wanan aika aikan ba.
Wai haka ma zakace Alhaji akan may zan zauna yaro kamar sadauki yana min cin fuska kala kala tsoron shi nake ji ko may da,zan kyale shi.
Yanzun dai idan har ya kara takalar wata a gidan nan don Allah na rokeku da kuyi hakkuri har lokacin da na dawo sai na dauki mataki da kaina.
Ke kuma Maijidda nasan kiyi hakane don kawar da fitinan don a zauna lafiya amma ba daidai bane ki biya Asiya roban ta don Sadauki ya fasa mata roba.
To ayi hakkuri in har ban kyauta ba amma ni bada wani manufa na biya roban ba.
Ai dan tane shi don haka ba zancen biya a tsakanin ku don dan wani yai wa,wani barna.
Mama Asiya tace wa ni sadauki ne dana Allah dai yai min katangar tsari wallahi da wanan bakar haihuwa a,rayuwana.
Ikon Allah Asiya a gabana kike wanan zancen haka ?
Ai gaskiya na fadi don bani fatan haihuwan dan majiciji a rayuwana na haife shi ya kasheni.
Allah ya kyauta inji Baba yafadi ciki kunar rai tare da mikewa yai shigewan shi daki kawai su ma mikewa sukayi suka watse daga dakin mama Asiya tana ta bakar magana.
Maji tadawo daki zuciyar ta na mata kuna ta samu su Amira suna ta hiran su Bintu tana gefe zaune a makure bata tanka masu a hiran nasu.
Suna ganin ta sun fahinci ranta a bace yake anyi ba dadi ke nan a can falon baba.
Amira tai tsuki tana fadin wallahi yaya sadauki dai yana jawo muna matsala a gidan nan.
Bintu tace sai ko mu bishi da addu,a don adfua makamin mumine ne tunda ba haka Allah ya halicce shi ba ai.
Dago kai Maji tayi ta dan tsura wa Bintu ido sai kuma ta kawar duk yadda taso ta danne hawayen ta kada su zubo saida suka zubo mata.
Hankalin yaran gaba daya ya tashi sai cewa Amira take halan mi sukace maki maji.
Bintu tace haba Anty Amira maganan manyane fa sai su kawai dai mama tayi hakkuri tabarwa Allah al,amarin shi, ian Allah mai karban adduan bayin shine idan Allah ya tashi canza shi sai kowa yai mamaki a gidan nan.
Hmmm Bintu ke nan baki san ko waye yaya sadauki ba ko a gidan nan ki barshi kawai kuyi yar nisa danisa dashi shine sauki wallahi.
A,a anty Amira insha Allahu wata rana sai kunyi mamakin shi Allah dai yasa wanan halin na iya kurciyane kawai.
Ikon Allah ke kin iya magana kamar tasbin kaka kamar wata babba van wallahi.
To Antu ai ba abinda yafi karfin ubangiji nagani don shine maitin komai a lokacin kuma da yaso wanan fa jerabawa ne akan su mama da baba sai dai muce Allah ya basu ikon cinyewa kawai.
Shiru dakin yayi suna nazarin zancen Bintu yarinya karama da babban magana kamar wata babba can.
Jin sunyi shiru Bintu tace da zamu dage ko mu iya dakin ga mu dinga aiwatar da ibada akan shi kawai ba,wai mu tsaya muna magana kamar sauran mutane ba muna kuma yin sadaka akai insha Allahu ba,dadewa zamuga saukin al,amarin da yardan Allah.
Don ni wallahi na yarda da addua takobin mumine sosai don da na roki Allah saiki ga an karba min.
Dariya,suka saka mata kai Bintu wanan cika baki haka kamar wata,shirihiya can.
Hmmm anty ke nan nifa tun ina karama Baba na ya kowaya min yin addua kin san ban tashi a gaban mahaifiyata ba.
Da sauri maji wacce sai yanzuta sa masu baki a zancen su tun shigowan ta tana hawaye tace.
Fatima ina mahaifiyar ki take Bintu tace tana can wani kauye tana aure sun rabu da Baba ance tun ana goyo na da ya auri kishiyar mamana.
Shine da aka yayeni iyayyen ta suka dawo dani gurin mahaifina wai bazasuyi wahalan banza ba .
Tayar dake shine suke gani wahalan banza Bintu tace cikin yar murya haka suke gani sai kawai ga kwallah ya zubo mata,
Bata daina magana ba don kwallan sai cewa tayi, mama nasha wuya a gurin mama hausi sosai don har tsakar gida na kwana ni kadai tun ina yarinya na.
Da kuma na girma abin ba,a cewa komai don ba irin wahalan da bata gwada min.
Amma sai gashi duk yaran ta ba wanda ya kaini don mazan su da matan su duk sun lalace mata sai nice ma nadawo tana dan jin sanyi a gurina.
Ina ganin ganin da Baba yayi aikin wahala zai kashe shine suka hada baki da,gwagona wai nazo nai mata hutun sati biyu na koma.
Sai daga baya gwago take fada min cewa wai Baba na yace na zauna gurin ta kada na koma garin mu.
Takarasa maganan cikin kuka tace ina kewan gida da yan uwana sosai da farko amma yanzu don rikon da gwago take min yasa na manta da komai gashi yanzu zama daku yakara sa hankali na ya kwanta sosai bisa ga zamana a can kauye don abubuwan da ban sani ba,a,rayuwa yanzu na,san su sosai.
Tun ina shekara sha hudu na haddace alkur,ani maigirma yanzu tulawa nake sai dai akwai banbancin karatun mu na can da naku na,nan birni sosai.
Kinga ashe na,dan san wani abu nima ga,addini ke nan don malamin mu yana gwada mu abubuwa siri sosai.
Allah sarki ashe mahaifiyar ki bata tare da mahaifinki gaskiya wasu mata akwai ha,inci a tare dasu sosai wallahi.
Shi yasa nake ta hakkuri tun farko da cin fuskan da ake min a gidan nan don yaran nan dake gabana don idan na fita na barsu cikin gidan nan wa kuke ganin zai rike min ku amma na cikin su, ina ciki ma yaya muka kare dasu balle na fita na barku.
Duk shiru sukayi suna nazarin maganan Maji don sun san gaskiya ta fadi ba mai iya rike su amma kamar yadda suke rike yaran su.
Kowan su tasan gaskiya Maji tafadi don ba mai iya rikon su amana suji dadi kamar yadda tace don haka sukaji tausayin uwar tasu ya kara shigan su sosai a gidan.

****** ********* ******
Salamu Alaikum wai ana sallama da Raiha sai mama dake duke a kitchen ta dago tana cewa kai waye da yamman nan ka ce bata nan.
Kai tsaya Raiha dake fitowa daga bandaki tace wa yaron je kace gani tafe kaji.
Raiha yanzu don baki da kunya zance zaki fita da rana haka kowa yana ganin ki kikau a kofan gida tsaye da namiji duk wanda ya wuce yai miki tir da halinki ko?
To mama kin san ko waye da,zaki kore min mai shi mama bari naje naga ko waye nadawo, kawai sai ta shiga daki ta shiga gyara fuskan ta tsab ta saka hijjab din ta sai waje.
Mama dake waje ta rike habar ta cikin mamaki sai cewa tayi ikon Allah yaran yanzu Allah ya kyauta kawai.
Raiha tana fita taga gidan su tunfitowan ta ya kura mata ido yana kare mata kallo nan yasan yarinyar tayi mashi ga komai kuma,zai more mata sosai idan yai sa,a ta yarda da bukatan shi gare ta.
Dan waige waige taks don bata ga mai neman taba a lokacin sai wani bakar mota mai tsada da ta hango, daga wajen gidan su, dan nesa kadan da gidan.
Hon din da mutumin dake cikin motar yayi yasa tagane shine mai neman ta a lokacin.
Raiha ta nufi gurin a cikin mamaki don ita duk iya sanin ta,bata da saurayin da keda koda karamar mota balle wanan dirkekiyar motan dake gaban ta.
Mutimin da tagani a motar bata taba ganin shi ba,a,rayuwan ta don haka sai tai tsanmanin ba gurin ta yazo ba.
Sai taji yace malama,Raiha ko ?
Eh nice
Bisimillah shigo daga ciki mana ko kina tsoro ne kuma.
Tai wani irin har da idanuwan ta ce tsoron may zanji kawai dai ban gane ka bane dai.
Bazaki gane ni ba,asalima baki sanni ba ni ne dai na,san ki ta hanyar gane gane na nahagonki kawai.
Shine na biyo ki har nagane gidan ku ne nan sai yau na yanke shawaran nazo gurin ki dafatan zaki fahince ni ai.
Wani kallo tai mai kamar bata yarda da,zancen shi ba sai tace mai a ina ka ganni ne ?
Sai da yai murmushi sannan yace a gurin birthday din Salim murmushi tayi don tasan anyi hakan .
To amma duk tsararun yan matan;dake gurin bai gansu bane sai ita zaizo gurin ta, sai kuma,wata zuciya tabata amsa dacewa kece kikai masa kawai a gurin.
IkonnAllah tace a fili tare da,fadin shine kabiyo ni har gida kuma ?
Yace eh mana ko nayi laifi ne tace bance ba yace to sunana Abdul amma ana kirana duwel ne don haka abokaina ke kirana dashi.
Hmm tau nagode da,har ka zabi kazo guri na,dafatan lafiya kazo har gidan mu a,kaina.
Murmushi guy din yadan yi tare da,cewa ai tunda kika ganni a gurin ki ke ma kin san alheri ne yakawoni gareni da,fatan zaki fahinci manufata a,gare ki batare da kin fassara min zance na ba.
Murmushi Raiha tamayar mashi tana cewa da fatan zan samay ka mai cika alkawari nima.
Nan suka tsaya suna dan kara fahintar da junan su kan shi tare da dan hira yana fada mata ko shi waye da inda yake aiki.
Ganin yamma tayi sosai tasan mahaifinta zai iya dawowa a lokacin yasa ta yi mashi sallama ta,shiga gida da fara,anta.
Tana shiga takasa boye farin cikin ta take cewa mama yau saura kiris ki kore min sa,a ta kin kuwa ga mutumin da yazo gurina ne.
Uwar ta mayar da hankalinta akan yar ta tana sauraren bayan nin da takd mata akan bakon ta.
Har saida mahaifinta ya shigo gidan suka bar zancen don gudun kada yaji zancen su.
Tun daga wanan ranan suka hada alaka a tsakanin su ita da Abdul din guy din da ya tafi mata da imanin ta gurin son ta.
Ba uwarta ba har mahaifin ta saida ya,san da zaman Abdul din don masifan son da Raiha take mashi.
Wasa wasa Abdul ya fara dan test din Raiha da,wasu yan abubuwan da yake son sani ko tasan da su a sabon sallon so da matasan yanzu ke ciki yanzu.
Bai samu matsala ba don ya samay ta yarinya ce yar rock sosai ba wasa don haka harkoki suka fara tafiya a tsakanin su ba bata lokaci.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

A LOKACIN MU KE,,,
6⃣

Murna sosai takeyi don ganin ta dauko sabon fridge dinta da ta dade tana gurin taga ta saye a rayuwan ta, don bunkasa sana,arta.
Ta bude fridge din yafi a kirga tana duba ciki da wajen shi don tabbatar da lafiyan shi.
Ba laifi don ta samu yadda take bukata saboda sanyi da kankara yake daga sama har kasan shi tsab.
Wanan abin yasa ta yini tana farin ciki da wanan karuwan da ta samu na ci gaban ta.
Ranan sai da ta aikawa makwabta da kankara tana fada masu idan suna son saye ta sai fridge mai kankara da ruwan sanyi, don haka su sa mata albarka a ciki.
Wasu sun yaba, wasu kuma sun kushe don haka duniya take dama wani baka hada komai dashi ba amma yana bakin ciki da karuwan ka a duniya.
Shima maigidan ta bawan Allah da ya dawo yai mata fatan alheri akan fridge din, tare da yar guntuwar nasiha akan sai tayi hakkuri da jama,a don mai saye da sayarwa sai hakkuri dama.
Sai dai kassh matsalan hauwa shine bata da hakkuri don ta sawa ranta masifan son kudi sosai.
Ta manta cewa zafin nema baya kawo samu sai in Allah yaso bawan shi da arziki yake arziki.
Ba dama mutum yazo sayen kankara ya mayar mata koda yace bai kankareba sai ta hau masifa da fada taki canzawa mutum abinda yake so.
Gashi duk samun da takeyi yanzu baisa mijin nata yakai idon shi ba ga kudin ta, don ko ba dadi sai yakawo masu dan abinda zasu dafa agidan suci.
Yana da matukar kokari gurin ganin ya kare hakkin iyalin shi sosai a rayuwan shi.
Amma daidai da rana daya idan dan wani abu ya kasa ga cefanen shi sai Hauwa tai mirsisi taki yi masu girki wai sai ya ciko ta girka masu.
Don ita bazata yarda da akidar cikawa namiji kudun cefane ba saboda itama tana da nata bukatan ai da kudin ta don yanzu ta sa rai wai fili take son saye ta yarda kaddaran itama.
Baida fushi hakan bai damun shi, dole sai ya samo ya cika mata sai ta girka masu inba haka ba su kwana da yunwa har yaranta.
Wanan kuma ba komai bane sai zugin uwarta da kullun take mata hudubar shedan akanta.
Na karta yarda da namiji don tana ganin ta ita kadai bai hana wata rana sai tagama kashe maijiki ya ce zai jajibo mata kishiya.
Halin Rashi hakuri irin na hauwa yasa mutane suka dan rage shigowa sayen kayanta yanzu sosai sun kwammace suje wani guri su saye.
Haka yasa ake barinta da kimin kankara a fridge har su narke tayi hasaran kudin ta.

****** ******* ******
Cikin mota suke a kofan gidan su Raiha yana yadda ranshi yaso da ita, a cikin rashin damuwa Raiha ta barshi yana juyata yadda yake so.
Don son shi da kalaman shi ko yaushe suna kara tasiri ne a zuciyar ta don ta yarda dashi 100%.
Daga nesa matasan dake zaune suna hira hankalin su yana gare su tun shigar Raiha motar, daya daga cikin matasan yake cewa kai yanzu dai mutane basu da tsoron Allah wallahi.
Kadiba fa yarinyar can ina lura da ita tun dazun suke zaune a motar nan har takai motar tana motsi don kanta.
Ashe bani daya nake lura da hakan ba inji dayan matashin yaba dayan amsa.
Sai dayan da sai yanzu yai magana yake cewa ai wanan yarinyar batayi ba wallahi.
Gaba daya haliyar ta baida kyau bata dauki kanta diyan tallakawa ba ko kadan takai kanta inda Allah baikaita ba ko.
Ni yanzu Raiha tafita raina tunda abokina yake fada min cewa yagan ta uguwar su gurin sayen kayan maye.
Kaifa Nasir ?
Yace wallahi ranan daya ganta a uguwar nan yake ce min a uguwar nan take ne nace mashi eh.
Shine yake cewa babba yar hannu ce sosai tana zuwa uguwar su gurin wani deler ta sayo kayan aiki masu karfi a can.
Sai wanda yafara magana yake cewa kai amma ko udan gaskiya ne wallahi dole mu saka mata ido don kada ta kawo muna matsala ga sauran yan matan shiyan nan.
Yanzu kai ya kake ganin zamuyi yace kokari zamuyi mu kamata a hannu sai mu dauki mataki daga iyayyen ta mana ko yaya kuka gani.
Hakane sauran suka bashi amsa da,sauri suna cewa wallahi in har ba,a,dauki mataki ba zata iya gurbata wasu ba,a sani ba.
To yanzu ita ina ta koyo wanan bakar akidar naga dai a uguwar nan ta tashi a gaban mu ai.
Kai yanzu sai wani ya koya wa mutum hakane abin fa masifa ne kawai sa warai ne ai.
Ni wallahi mamaki take bani yadda idon ta ya bude baki daya a lokaci guda haka.
Kaidai bari ai yanzu haka kila a makaranta ko kuma wasu sabbin kawaye ne suka koya mata wanan harkan.
Tana shiga gidan mu gurin kanne na zan shiga nai masu fada wallahi su rabu da ita tun bata lalata min kanne ba.
Kaidai kawai Allah ya,sauwaka ita kuma Allah ya shirye ta don kaga ai mahaifinta mutumin kirki ne.
Uwarta kuma bata ko magana shiru shiru mutumiyar kirki ce sosai don bakajin ance ga abinda tayi a uguwar nan na assha.
Sai wani lokaci Raiha ta bude kofar mitar ta sako kafan ta guda daga waje, daga inda matasan suke zaune suna iya hango ta daga cikin motar tana gyara rigar ta da kuma saka hijjab din ta.
Allah ya kyauta amma dole mu dauki mataki akan wanan fitsaran da ake muna da rana tsaka a uguwa.


****** ********* ******
Abin duniya ya ishi zuciyar Umar faruq ya rasa yadda zai shawo kan Maji ta yarda ta mara mai baya akan zancen tafiyan shi zuwa ghana kwallo kamar yadda yan club din su suke son yaje ya buga masu ball.
Haka yasa yafara dirkawa cikinshi kwaya kala kala har takai ya shiga hali na maye sosai.

Fatima don Allah zoki sayo min magani kafin duhu ya kara yi don yanzu dana aiki su Amira Alhaji yagan su fada zai min sosai.
Kiyai sauri ki dawo da wuri kinji Fatima kada ki dade kinji Fatima dare ya soma sosai.
Don takwas saura yanzu, ban son fitan dare ga diya mace haka koshi dole yasa zan aike ki don kaina ya matsa min da ciwo sosai wallahi.
Bintu ta dauko hijjab dinta ta,saka ta fito ta karbi kudin maji tafada mata kalar maganin da take son a,sayo mata.
Tana zuwa aka bata maganin ta juyo zuwa gida gap da zata shiga gidan ne taga mutum a kwance bakin get.
Sai faman nasari yake harta dan raba shi zata wuce don tagane wanene a kwance gurin.
Da,sauri ta dawo ta dan duka a kan shi a hankali tana fadin.
Yaya sadauki ka tashi ka,shiga daga ciki kada wani ya gan ka anan haka.
Da kyat ya bude idanuwan shi ya kalleta cikin maye ya nunata da hannu ya bude baki da kyat yana fadin, tare da nunata.
"Ke zan _ci uban,ki idan baki ban guri ba walla_hi sai ya mayar da kan shi kasa.
Innalillahi Bintu ta furta a fili ta mike tsaye kamar zata wuce sai kuma taji bazata iya ba don idan har wani ya gan shi a haka yashe a kasa cikin maye, yau bakwanciyan hankalin ga Maji dama gashi kanta tun safe take yana mata ciwo.
Komawa tayi iya karfin ta ta dago shi daga kwancen da yake ta na cewa tashi yaya ka koma dakinka don Allah.
Shegiya idan baki barni ba zan maki dukan tsiya wallahi, yafadi a cikin muryan dan maye.
Bintu bata bi ta nashi ba sai kokarin mikar dashi take shiko sai ashar yake jefa mata.
Cikin ikon Allah ta samu ta daga shi daga inda yake kwance ta kaishi daidai kafadan ta duk da yai mata nauyi amma haka ta daure ta ja shi zuwa dakin shi.
Da kyat ta lalabo key daga jikinbshi cikin wandon shi na baya ta bude dakin tana,shiga wani wari ya daki hancinta, haka ta daure ta kaishi bakin katifan shi.
Sai barci yake a kafadan ta cikin maye, tana son kifar dashi don duk tagaji saura kiris su zube tare sai ya kwararo mata amai da fitsari a lokaci guda duk ya bata mata jiki dashi.
Haka ta daure ga,warin amai yana damun ta ta kifar dashi akan katifan dakin.
Kallon hijjab din ta da ya lalace da amai da fitsari tayi tare da girgiza kanta tana Allah ya kyauta tajowo mai kofan dakin tare da dunkule hijjab dinta daya lalace da aman shi.
Gap da zata shiga gida taji karan motar Alhaji habu dake dawowa daga kasuwa, shi da sauran yaran shi dake bin shi shago.
Da,sauri ta karasa kada suga fitowan ta part din samarin gidan kuma dakin sadauki su fassara mata zance.
A can cikin gida kuma Maji hankalinta ya tashi sosai ganin Bintu ta dade sai gata saidai a hargitse take don hankalinta ya tashi.
Amira data kalleta yadda ta shigo gidan take cewa, ke lafiya kika dawo wata kala haka dake ji yadda jikin ki ya lalace.
Saida Binta ta kalli jikin ta take cewa cikin sauri faduwa nayi gurin kwata da,wata mota tabiyo gefena.
To amma ai ba kwata bane kamar amaine jikin ki tace gurin masu saida abincine gurin.
Ta mikawa Maji maganin ta,shige ciki don duk a tsawale take da aman dake jikin ta dama.
Saida tai wanka ta gyara jikinta tsab tafito falon inda suke ta zauna tana kallon shirin da ake a sokoto tv.
Maji dai bata ce masu kalla ba don kanta da yake damunta da ciwo a lokacin.
Sai da ta dauki lokaci bayan tasha magani sannan kan ya fara lafa mata

2 Comments On A LOKACIN NE
avatar
usama-6

1 year ago

Reply

Alhamdulilah

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to usama-6

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment