Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takalli Du'a tace "ke baki bamu labarin saurayinki ba" Dan zaro idanu tayi tanuna kanta tace "ni"? dasauri Mariya dake gefenta tadan bugi kafadanta tace "common on don't be shy, tell us about the lucky guy" dan murmushi tayi saikuma tadauke kai dan tambayan tabata kunya ahankali tace "ni banda saurayi ko daya wlh" wani irin bude baki sukayi suna kallonta sabida mamaki, Rahima dake gefen Mariya tace "Du'a wasa kike ko" girgixa kai tayi tace "wlh ba wasa nake ba" shiru duk sukayi yanda yarinyar nan keda kyau ace bata da saurayi basu wani karyata ta sosai ba sabida sunga ko wayama batada shi, share maganan sukayi suka shiga wata hiran har sukakai mango dazasu, nan Du'a taga yanda ake shopping ita bama tasan mezata dauka ba hakan yasa kome suka dauka itama saisun daukan mata anata cart din, tundaga kan Bra da tuni suka gwadata suka shiga zakulo mata sizes dinta zuwa pants, pads kayan makeup, duk suna tura cart dinsu kowa na diban abinda akeso TV super market din dake makale asama na aiki Channels television news inda ake program REINVENTING THE NIGERIAN YOUTH....



Suna tsaye bangaren English wears Rahima ta amshi tape tana kokarin ana waist din Du'a dan asan size din jeans dinta itama ta dauka kaman daga sama wani kyakkyawan eloquent voice yadaki dodon kunnuwan Du'a da hakanan taji kaman tasan muryan, dawani irin sauri tadaga kanta sama takalli TV, chak ta tsaya ko motsi kirki tasaka, idanunta ne suka sauka kan fuskan da kusan kullum saitaga fuskan, wanda yacetota daga rijiya, yana sanye cikin wasu classic suit dark blue, ga necktie awuyanshi, yana zaune kan wata hadaddiyar kujera yayi crossing legs dinshi in a stylish way, yadaura hannunshi biyu kan cinyanshi wrist dinshi na daure da agogon Rolex, idanunshi fari kalll wanan karan babu bakin glasses akan su, lips dinshi sunyi wani masifaffen pink kaman ya shafa janbaki pin akai, gashin kanshi dake da yawa sunyi wani kalan extraordinary coils, yana magana da english da accent dinshi na bristish, kaman acikin mafarki taji ana Du'a, Du'a, Du'a, tabatan da akayi yasa tai firgigit tafarka ta kallesu da sauri dan sai alokacin ma tasan ashe tayi nizan tunani ne, neck dinta Rahima takai hannunta ta taba tace "baki da lafiya ne? Tunanin me kike haka kin tsare TV da ido eh harmun gama siyan kaya" binsu tayida kallo ganin yanda suke kallonta kaman sun damu yasa takakalo murmushi tace "tunanin abubuwan dazan saya fa nake" murmushi dukansu suka mata, Rahima tace "mungama da wanan shop din next stop is abaya store, mutafi mubiya mufice yamma nayi" gyadamusu kai tayi tabisu zuwa wajen cashier tana kara waigowa tana satan kallon TV da Asad har lokacin ke magana, kowa kudinshi yabiya sanan aka musu parking kayan a leda sanan suka wuce suka fita still saida takara waigowa takalli TV, sanan suka fice, ranan basu suka dawo gida ba sai 8 nadare kasa bude kayan tayi salla ta lallaba tayi sai bacci tashinta grandma tayi saida ta tasa ta agaba taci abinci sanan tabarta takara komawa bacci da tagaji bata saba fita ko wahala hakaba, all abinda tasani is wanka kwanciya da cin abinci shikenan saisa tai bacci awahale.


DAN MAGANA DANI M SHAKUR CHAT ME UP BY CLICKING ON THIS LINK wa.me/+2347012181461



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

EPISODE 2️⃣2️⃣
Kaman an tsikareta wuraren 4 na asuba tafarka da kanta batare da an tadataba, TV dake bangon dakinta ta tsaya chak tana kallo kaman mai tunanin wani abu, dasauri ta yaye bargon data lulluba dashi tasauka daga kan gadon, kunna switch din bangon tayi nan TV da decoder na DSTV duk suka kunna komawa tayi tazauna kan gadon tana sosa idanunta dake cikeda bacci, tadauki remote tashiga neman channels television news, da kyar ta iya ganoshi ta saka da sauri tana gyara zama kaman akwai abinda take shiri ta kalla, ganin ba abinda take nema sukeyi ba yasa tashiga wasu channels din tana skipping amman duka bataci karo da abinda take nema ba yarda remote din tayi akan gado sanan ta tashi tashiga bayi tai duk abinda zatayi sanan tafito dadduma ta shimfida tai nafila sanan tadauki Al Qur'ani tashiga karantawa har aka tada salla hakan yasa tarufe tai salla tana idar wa tai azkar ta tashi sanan tawuce tafito ko kadan batajin dadi, gaban dakin Hajiya tayi knocking tayi sanan tabude kofan ta shiga kan dadduma taga Hajiya zaune tana lazimi, ahankali tace "ina kwana Grandma" murmushi tamata tace "Du'a jiya angaji anyi bacci dawuri, tashi ga wayanki chan na samiki a chaji ina ganinma yacika" dasauri takalli inda ake nuna mata hadadden waya ne a bango dawani irin sauri tafada Jikin Hajiya batasan meyafaru ba kawai saita saki kuka sosai tunda tazo gidan nan she has been so happy, babu mai takura mata ko matsa mata ko kyaranta, ba'a taba bata matarai ba, ba'a hanata zuwa ko'ina, she's truly happy, jin yanda take kuka yasa grandma ta kankameta itama ahankali tace "I promise you Du'a inhar inada rai adoron kasan nan u will never be sad again, wlh wanan karan ko uban waye kulleshi zanyi akanki, abinda kika going through agidan mahaifinki u will never go through that again kinji, kina tare dani anan har aurenki, I will take care of you, malamin islamiyya da boko ma na saman miki zai dinga zuwa Saturday da Sunday, u will excel kinji, forget komi dayasameki abaya kaddara ce, kyaune Allah yabaki amman hakan bazaisa ki karake rayuwanki a kulle adaki ba dan haka u will learn how to live with ur beauty kinji Du'a dina" gyadamata kai tayi ajikinta ahankali, dagota Grandma tayi takai hannunta kan fuskanta tana share mata hawaye tace "ba'a kuka agidan Hajiya, now tashi kidauki wayanki kije falo ki kwaso kayan shopping dinki ki jera komi a inda yakamata adakinki, idan aikin yamiki yawa ki kira su Razika su tayaki" gyadamata kai tayi ta tashi daga kan jikinta wayan tawuce tadauka tana kallo, iPhone mai kyau 11 pro max Grandma dinta tasai mata ga Sim din MTN aciki, fita tayi daga dakin taje falo ta kwaso kayayyakinta tadawo dakinta, ta shiga jera kayayyakin, harda bags da shoes hadaddu, masu tudu da flat, ga kayan kwalliya, saida tagama tsaf sanan tashiga bayi tayo wanka tafito, shiryawa tayi cikin hadadden abaya again kaman yanda Hajiya tafadi mai ruwan kasa, tai rolling gyalen da kanta dan jiya sauka su Rahima suka koyanata a shagon abaya sunma sai mata pins na kama gyalen tasa pin din, sanan tadauki wayanta tasa a jaka tasaka wani takalmi baki mai dan tudu kadan dayama farin kafanta kyau sosai sanan tafito, a falo taga Hajiya zaune tana shan ruwan bunu kusada ita tazauna tace "grandma bazaki je office yauba" murmushi tamata tace "nariga nai retire, idan kinga naje office ko akwai wani important meeting ne, kokuma naje supervision, tashi kiyi break direba na jiranki zai dinga kaiki yana zuwa ya daukoki kullum, banda latti koni bana tolerating late coming dan tahaka ake discipline na employees, go and eat" tashi tayi tawuce yau tayi breakfast kadan saita shiga kitchen wani karamin roba tadauko mai marfi ta zuba pepper meat aciki duk Hajiya na kallonta sanan ta taho tasa ajaka tana murmushi ganin Hajiya na kallonta, dan hararanta tayi tace "da yanda kikecin nama haka kikecin abinci danaji dadi kura kawai" dariya tayi tarataya jakan a shoulder tace "Grandma Byeeee" Bye Du'a ayi addu'a, gyadamata kai tayi tafice Hajiya na kallonta tundaga kan kafafunta kafanta badai kyau ba ya ilahi, tana ganin zatamai fara sakata sa Safa, mota ta shiga direba yajata zuwa office.



Yau tana shiga batai kauyencin datayi jiya awajen kofa ba, glass din na budewa ta shiga ciki, mutane sai kallonta suke maza da mata, saukar da kanta kasa tayi tana tafiya ahankali kafafunta na neman hardewa sabida yanda ake kallonta, dukfa sun tsayar da aikin dasuke kallonta ake, this is the first time data shiga waje kowa ya tsayarda abinda yakeyi yana kallonta, wani irin rawa jikinta yafara kafanta na hardewa daidai tazo stairs tahau kafanta yaturgude baya tayi zata fadi, jitayi antareta ta baya an daura hannaye biyu akan kafadunta murya chan kasa taji ance. "careful" dawani irin sauri tajuyo ta kalleshi, Sharif ne yana sanye cikin suit black yay wani irin kyau, hannayenshi dakekan shoulder dinta ya kalla sanan yajanye su ahankali murya chan kasa yace "sorry about that" sanan yajuya daga inda yake yakalli ma'aikatan su da ganinshi yasa kowa yafara aikin gabanshi kaman da gaske dan kwafa yayi sanan yajuya yakalleta yace "let's go kinada aiki yau" yay maganan yana gaba ahankali tabiyoshi abaya, Cafeteria dinsu yaje yakarbi cup biyu yajuyo na tea yabata sanan yarike na coffee sukai stairs yana tafiya yace "omg, at this points knees dina sun kusan cirewa kuma duk kece Du'a, mezan fadama future wife dina idan suka cire" dan murmushi kadan tayi tana binshi abaya batare datace komiba hakan yasa yajuyo yakalleta, boye murmushin tayi dan zaro idanu yayi cikeda wasa yace "did u just smile knees dina na aching" ahankali tace "sorry" juyawa yayi yacigaba da tafiya yace "zan gayama future wife dina it's one gurl called Du'a tasani nake bin stairs zuwa 5th floor fa sabida tana tsoron elevator" murmushi tasakeyi batace komiba har sukakai office dinta, shiga sukayi ta ijiye komi kan table ta tsaya agefe, juyowa yayi ya kalleta yace "me kikeyi abayana sit akan kujeran ki nabaki aikin ki natafi" gyadamai kai tayi tazo ta gabanshi tawuce tazauna kan kujeranta ahankali kaman mai tsoro, wani karamin mini pad yamika mata yace "the CEO sent this, yanaso kiyi zanensu next week idan yashigo aikinsu za'a fara, 5 design na hills, 5 na loafers, 5 different design na croc and unhooked sandals" ganin yanda take kallon pad din yasa yace "it's a whole lot of work ko, don't worry take ur time zaki iya kadan yau kiyi sauran gobe" gyadamai kai tayi ahankali hakan yasa yajuya yace "in that case bari natafi" haryakai kofa ta dago kanta ahankali tace "ummmm" juyowa yayida sauri yakalleta yace "da wani abu ne"? gizgiza mai kai tayi tace "thank you, su Rahima gave me the money, Allah amfana Ya Sharif" tunda take maganan harta gama yake kallonta, dauke kai yayi yace "you are welcome" sanan yawuce yafita daga office din.


Ranan haka tawuce zane take a E-board dinan, bakaramin burgeshi zanenta Sharif sukayi ba, kafin 4 tagama gabaki daya ma dan she's so fast da zanen tawuce ta tafi direba yadauketa.



Tana shiga gida tafito tawuce ciki, Razika da Shemau tagani zaune a falo suna kallo TV tabi da kallo ganin film suke kallo yasa tace "ina Grandma" Razika dake kallonta tace "tana sama kaman ta kwanta bata dade da shigowa ba" sama tayi ahankali tabude kofan dakin Hajiya ganinta kan gado tana bacci yasa tawuce dakinta, kaya tacire tawuce bathroom wanka tayo tafito daure da towel tayi gaban wardrobe wani simple short gown tadauka tasaka, jin anyi knocking kofar ta yasa tace "shigo" shigowa Razika tayi dauke da tray na abinci tace "abinci nahado miki nasan kin gaji" wani irin murmushi tayi Razika nada kirki karban tray tayi tace "nagode Razika" gyadamata kai tayi tawuce tafita zama tayi kan gadon ahankali rikeda tray din tana kallon sinasir dake cikin plate, ga lafiyayyen miyan taushe dayaji naman kan Rago, dago kanta tayi sai kawai tacire tray kan jikinta ta ijiye agefe tamike tsaye da sauri switch din TV ta kunna tadau remote takoma kan gado ta zauna, gama booting yayi hakan yasa ta kunna tashar Channels Television News, daidai an nuno wani daga cikin audience ya daga hannu, hoster tace "go ahead" mikewa tsaye yace "My name is Samuel Madina Chris, My question to Mr Asad Abdullahi Kitse is you see we all know you come from a wealthy home/family, so setting up a business starting a company can not be a problem for you cus ur family are buoyant enough to support you with startup capital, mu yanzu that come from not so financially strong family how can we source for start up capital dan bamu da yan uwan dazasu taimaka mana"?
Nuno Asad akayi, yau yanacikin wani hadadden suit ash color dark ash da yamai bala'in kyau, yay crossing leg as usual, looking so elegant and classic, gashin kanshi sun kanannade suna wani irin kyalli, lips dinshi sunyi pink yirrrr....... Ahankali Du'a tawani irin sauke ijiyan zuciya idanunta kur akan TV akanshi gabanta nafaduwa dum dum dum.......

Gyara zamanshi yayi yay adjusting mic din dake gabanshi wani dan karamin cute smile yasaki dako hakoranshi basu bayyana ba cikin husky melodious voice dinshi yace "I appreciate this question Mr Samuel you know why" yadanyi shiru kafin yadan ciki lebe kadan yace "sabida mutane dayawa nada wanan misconception din, suna tunanin all mutanen dasuke business are from wealthy homes, lemme tell you all something, mahaifina nada companies, yanada kudi, but kunsan 1naira na mahaifina kona family na banyi amfani dashi a business dina ba, I strive for my business with my hard earn money" wani irin tafi hall din yadauka hakan yasa yay shiru yana jiran sugama yace "akwai lots of organizations that ayanzu the youth can reach out to dan su sami kudi and establish business dinsu ko expanding business dinsu, CBN, SMEDAN, BOI, and so much more, listen business is not for the lazy ones dayay depending on his families, and is not for the ones that doesn't have the zeal to strive hard and hard and hard to achieve his goals, business is for people that doesn't believe in impossible, don't tell ur self is impossible to establish a business because my parents are poor I don't have any source of income..." wani irin tafi aka fara a hall din kowa na having goosebumps sabida yanda yake maganan yana penetrating a zukatan audience din, saida sukai dan shiru sanan yace "business na mutane ne that believe in their self, people that have vision and are ambitious, people that are vasitile and strong hearted, we'll ladies and gentlemen I think we've reached the end of today's program saikuma gobe, thank you" wani irin tafi aka fara a hall din kowa yamike tsaye anamai tafi shikuma yawuce yana tafiyan nan kaman zaki looking damn elegant, classic and sexy yawuce yafita daga hall din, tashi itama Du'a tayi ahankali tama rasa mezatayi kawai saita koma ta kwanta kan gadon ahankali tana kallon TV da har anfara another program.




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR

Free page
EPISODE 2️⃣3️⃣
Lumshe ido kawai tayi looking so somehow da bazaka tabace ga asalin yanayin datake ciki ba, ahaka bacci yay awon gaba da ita saida Hajiya tashigo ne ta tadata taje tai salla sanan ta sata agaba aka kawo mata wani abincin aka tafi danada dan bataci ba sanan tabarta ta kwanta dan akwai baccin sosai a idanunta.
******


Ahaka tai good five days a company from Monday to Friday Sharif has always been there for her, yanada kirki mara misultuwa, he's very nice and generous kaman ba boss dinta ba at all, yamaida ta kaman wata sister dinshi hakan yasa itama tadaukeshi kaman wanta Ya Hamad, itadasu Rahima kuma kaman sunsan juna tuni suka koya mata watsapp suka sakata group dinsu na yammata inda ake hiran samari da heart break ita saidai ta karanta taita mamaki, kullum 4 nayi take fitowa driver Hajiya ya dauketa tana dawowa gida zata gudu dakinta tasaka channels television news but kodaa yaushe ending din program din Asad take samu wani zubinma bata samin takalla kafin takai gida an gama barin ma ranakun da holdup yakamasu, har kasan ranta she wish zata iya ganinshi tace mai thank u for saving life dinta dan ko kadan takasa manta da fuskanshi da idanunshi dasune tagani da kyau danhar kasan zuciyanta takasa mantasu.



Yau Saturday su Rahima sunso sujata yawo Grandma tahanasu dan malamin ta zaizo, wuraren 10 malamin bayerabe yazo, Hijab tasaka har kasa tafito karatu yamata both na boko da islamiyya dan irin genius ustazan malaman nanne, karfe one suka gama yatafi, dakinta takoma ta kwanta yau kawai she's so happy koba komi tana gida zata kalli program dinan daga farko har karshe yau, salla ta tashi tayi jin ankira sanan takoma ta kwanta sai bacci, wuraren 3 Hajiya tashigo dakin tadata tayi. "ke Du'a oya tashi" bude ido tayi ahankali ganin Hajiya yasa ashagwabe ta daura kanta kan cinyarta murya chan kasa tace "Grandmaaa nagaji" smooth kumatunta Hajiya tashafa tai murmushi tace "oya tashi sonake ki shiga kitchen tareda su Razika kema kisoma iya girki, tuwon shinkafa zakuyi da miyan taushe sai farfesun kifi" ahankali tabude idanunta dahar sunyi dan ja sabida baccin datayi takalleta, tashi tayi zaune sanan tamike tsaye tace "grandma dakaina zanyi girkin ni kawai su nunamin yanda zan dinga yi" gyadamata kai Hajiya tayi tana murmushi tace "to gimbiya Du'a hakan za'ayi" wani kalan murmushi tayi cikeda murna tawuce tafita daga dakin dan tafi kowa so ta iya girki dan girki na burgeta, shiga kitchen sukayi aiko su Razika sun sha dariya dan targen tuwo bata iyaba haka suka dinga koyanata suna dariya gabaki daya ta manta da abinda takeso tayi, saida suka gama tuwon sanan ta kalli agogo dake manne abandon kitchen din, dawani irin gudu tafita daga dakin ta sama dakinta tashiga, TV kawai ta kunna dan decoder a kunne yake dama tana kan channels din, ganin angama program din yasa taji wani abu yatokare mata wuya, wata matace ta bayyana agaban TV tace "to jama'a ni karan kaina bakin cikin sanar daku nake cewa a yau ne wanan program din da gwamnatin Nigeria takawo muku sabida tallafawa Matasan kasa wanda wanan shahararen matashin nan dan kasuwan nan wato business Mr Asad Abdullahi Kitse ya gabatar muku yazo karshe, ku saurara kuji" matan tayi murmushi tace "channels television news tasami sakonni da dama kan shafukansu na sada zumunta da emails kan Mr Asad cewa mutane naso sugana dashi, toga wata sanarwa, gwamnatin Nigeria tashirya kyakkyawan liyafa wato dinner nagama wanan program din agobe karfe 4 na rana inda star dinku Mr Asad zai hallata, ana gayyatan marasa su fito duk kuzo dan Mr Asad zai sake bayarda jawabi wato speech awajen dazai taimakawa marasa wajen fara tasu sana'ar, za'ayi wanan taro ne ababban hall din transcop hotel, a huta lpy" daidai nan suka shiga talla kuma, zama tayi ahankali kan gado tai shiru, kwala mata kiran da akayi yasa ta tashi tafita daga dakin da sauri suka daura miya, suna gamawa ta debi nata tafito ta tafi dakin Grandma dinta dake waya hakan yasa tai zamanta tanacin tuwon. Gama wayan Hajiya tayi tace "iyye manyan mata anyi mana girki yau" washe baki tayi tace "grandma abincin nan dadi wlh sosai" hararanta Hajiya tayi tace "nidai tashi kikai plate dinan kitchen ki wuce kije kiyi wanka, haka akeso mace tadinga yi idan tagama aikace aikacen gida ko girki, wuce daganan sai kiyi salla" tashi tayi tadau kwanon tafito saida taje ta ijiye a kitchen sanan takoma dakin ta wanka tayi tanajin dan ciwo ciwon ciki kaman MP dinta zaizo, fitowa tayi ta tsaya gaban madubi ta kalli kanta tawani kara haske fatar jikinta na kyalli sabida man da Hajiya tasaimata mai bala'in kyau ne, tamadanyi kiba, wanan kumburin kukan da idanunta keyi a gidansu duk babu yanzu, gama shafa man tayi batabi takan kalaban kanta dake lilo ba dan batai parking nasu ba tawuce wardrobe dinta wani dogon riga tadauka na kanti mai kyau pitch color ne tasaka kawai ajiki batare datasaka bra ba sanan tasa hijabi tai salla, tana zaune kan dadduma tana biya karatun da aka mata aka kira isha'i tashi tayi tayi sanan tamike tsaye cire hijabin tayi ta ijiye kan kujera tadauki wayanta dake gaban madubi tawuce tafito, kasa ta sauka, ganin babu kowa a falo yasa tawuce dakin su Razika dake nan akasa, zaune suke su biyun suna assignment dinsu dan malamin su yabasu assignment, suna ganinta duk suna dagokai suna kallonta, murmushi tayi tace "kuma anbaku assignment" dukansu gyadamata kai sukayi, fadawa kan gadonsu tayi tace "to kugama bari nai chatting dasu Aneesa" saida suka gama sanan Razika tarufe book din ta ijiye tana kallon gashinta tace "yaushe zaki kwance kannan gashinan harya soma kwance kanshi sabida gashibki nada santsi" yatsine fuska tayi tace "ni bazan kara zuwa saloon dinan ba suncika kallon mutane wlh" dariya daga Razika har Shemau sukayi dan yanda tai maganan zaka dauka yarinyar ce harda dan turo baki She looks so cute, matsowa gaban gadon Shemau tayi tace "ai sabida kinada kyau ne saisa ake kallonki Du'a mu ana kallonmu ne Razika"? Girgizakai Razika tayi alamun a'a, yatsine fuska Du'a tayi tace "wlh ko bansan kyan nan, uhm, bari naje na kwanta" tai maganan tana tashi daga kan gadon tamike tsaye, hannunta tasa tadauki wayanta sanan ta musu murmushi ganin yanda suke kallonta tace "saida safe" "Allah tashemu lpy, Du'a gobe kezaki break" bude kofan tayi tajuyo cikeda murna tace "dagaske?" gyadamata kai Razika tayi tace " eh" fita tayi tana murna, Shemau ta kalli Razika tace "Razika daman haka takeda nono ni wlh nadauka breziya ce ke sa nononta yay girma a riga irin push up dinan sai yanzu naganta da ba breziya ajikinta" tashi Razika tayi tana gyara gadonta tace "haka takeda su harda bombom ma kaman ita tai kanta, wlh inason yarinyar sosai Shemau mugun burgeni take, dan she's so simple, batada wani ji da kanta sabida tanada kyau kaman yanda masu kyau keyi dinan kiga suna daddaukema mutane kai sabida sunga sunada kyau, Du'a ga kyau ga kamun kai ga natsuwa bakiga ko saurayi batada shi ba" Gyadamata kai Shemau tayi cikeda gamsuwa tace "hakane, Allah yabata miji kyakkyawa irinta, ni wlh daurewa kawai nake dabana tsareta da idanu dan wlh bangajiya da kallonta" murmushi Razika tayi tace "bacci nakeji".


Fitowa daga dakin Du'a tayi tana murmushi tana tattaba wayanta dan Aneesa ce kebata dariya tana kawomata karan Mariya waita sace mata zobenta, typing yakuri tayi sanan ta ijiye wayan kan dinning tawuce tana tafiyan nan ahankali takarasa gaban fridge din dake dinning din tabude dan kishi takeji sosai, wani karamin bottle water mai sanyi taciro tana kallon goran, maida kofan fridge din tayi tarufe kafin ahankali tashiga bude marfin goran sanan takafa ahankali abaki tawani lumshe ido tanasha.

"you know cold water is not good for the body" kaman daga sama taji murya kaman na Sharif akanta, dawani irin sauri tabude idanunta tareda juyowa, yana zaune kan dogon kujera shi kadai a falon yana sanye da 3quater na sojoji da farin t-shirt yana rike da system dake kan cinyanshi, dudda taga ba kallonta yakeba amman saida taji wani irin kunya dasauri ta ijiye ruwan sunnar da kanta kasa tayi amugun kunyace tace "Ya Sharif ina yini" batare daya kalleta ba still yana aikin dayakeyi ne yace "hope u good" gyadamai kai tayi ahankali tama rasa mezata ce tace "uhmm kaga Grandma dina? Tana sama bari nakira maka ita" tai maganan tana fitowa daga dinning tai stairs dasaurinta harda dan gudun ta, wani irin turgudewa tayi kafanta ya lankwashe dayasa tasaki wani irin wawan ihu. "wayyo Allah na kafata" tashi Sharif yayi daga kan kujera dasauri yawaigo daidai lokacin Grandma datagama wayan datakeyi tafito kenan taji ihun ta tazo stairs din dagudu tace "subhanallahi maiya faru? Muga kafan" Hajiya tafadi dasauri tana karban kafan da Du'a takasa ijiyewa kasa tsabagen azaba tana dan kuka mara sauti dan yamugun mata zafi, cikeda tausayinta Hajiya tace "sannu ijiye kafan nagani" gyadamata kai tayi tana kokarin ajiye kafan akasa wani irin ihu tayi saikuma tafashe da kuka sosai wanan karan mai kara tace "dazafi Grandma" cikin dan fushi Hajiya tace " kinsan wajen nan bene ne akan wani dalili zaki dinga gudu akai eh" cikin kuka sosai tana kokarin kama hannun Hajiya dake liliyamata kafan tace "zan kiraki ne naga Yaya Sharif yazo" cikin fada Hajiya tace "Sharif da tuntuni muke tare muna hiranmu har tuwo yaci,

Please Login or Register in order to submit comment