Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so kaman Du’a sabida tafi kowa rauni, he don’t care about kalaman da family su suke fadi akanta ana cewa itaba yar Abba bace, mayya ce, yar aljanu ce bla bla bla, all he knows is Mami da Abba suka haifeta and she’s his little sister kuma yanason kanwarshi sama da tunanin kowama.


Cikin kuka tace “Ya Hamad ni wlh inaso namutu” dasauri yacirota daga jikinshi yace “ke are you crazy? Karki kara fadin haka” bayan hannunta takai tana share fuskanta tace “Abba bayasona, Mami bata sona, Mum ma batasona, Kaka ma batasona, kaga ni kadai Abba ya tsana ayaranshi, yakorani nakoma daki dazu, kuma kaga yace yaranshi 8 yacireni daga cikin yaranshi, kullum ina kulle adakin nan kaman mayya, dama Kaka tace ni mayya ce ni aljana ce, sabida ni kadai aka haifa daban bana kama daku does that means am a witch ko aljana eh Ya Hamad? Ya Hamad bakacemin kananan ranan da aka haifeni ba kuma kace Mami ta haifeni maisa su Aneela dasu Muhammad da Mudasir kadai takeso eh? Ya Hamad babu asibitin dake chanza kalan fatan mutum ka kaini naje nakoma kalan yan gidan mu sabida Mami na da Abba su soni nima eh Ya……..” hannunshi yadaura akan lips dinta yace “ya isa haka listen to me all abubuwan nan dakikaga Abba da Mami nayi bawaidan basa sonki bane sunayine to protect you, Du’a tun kina primary school ansha ayi attempting ayi raping naki nasan lokacin kina yarinya ba lallai kituna ba, but kin tuna lokacin dakike JSS 2 abinda teacher ki da Abba ya kulle yamiki ko” runtse idanunta tayi dakarfi alamun ta tuna, hakan yasa ahankali yakai hannunshi yakama hannuwanta guda biyu yace “listen to me, Abba is only trying to protect you, Abba bai tsaneki ba” ahankali cikeda raunin murya tace “amman yana kunyan ya nunani amatsayin Babana” tai maganan tana kallon Ya Hamad kurii da manyan idanuwanta dayasa yakasama mata karya dan to some extend all abinda take fadi gaskiyane, ahankali kawai yajawota jikinshi ya rungumeta yakai hannunshi yashafa gashinta murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita sukeji yace “kin tuna abinda nake yawan fadamiki” gyadamai kai tayi ahankali ajikinshi hakan yasa yace “fada inji” murya chan kasa hawaye nabin kuncinta tace “Du’a kome kikaga yana faruwa arayuwanki Allah yasan dake, jarabawanki ne, karki kaucema Allah karki butulcemai, bake kikai kanki ba Allah ya yoki, love yourself, kiyi imani da Allah kikuma dage da addu’a watarana sai labari my beautiful little Duuudo” suka karashe maganan atare hakan yasa takara kankameshi, murmushi yayi sanan yacirota daga jikinshi, handkerchief yaciro daga aljihunshi yace “now let’s wipe those tears no more kuka okay” gyadamai kai tayi tareda murmushi yan kananun white teeth dinta suka bayyana, sharemata fuskan yayi tass sanan shima yamata murmushi yace “idan bakin nan suka tafi zan dauko miki sababbin novels din dana sayomiki kinji” gyadamai kai tasakeyi, kumatunta yaja yace “idan kika sake kuka saimun bata” dasauri tace “bazan sakeba” “kinci abincin dare?” Girgizamal kai tayi, tashi yayi yace “bari naje nakawo miki saiki bani labarin wayan nan novel din” gyadamai kai tayi yawuce yafita yana murmushi, Allah yamata brain, english novels yake sayomata dasukakai 1000+ pages cikin 2days tagama kuma tsaf zata bashi labarin novel din, abinda yataimaka mata da english ma kenan.


Bai wani dadeba yadawo dakin da bowl na hadadden pepper soup da cow head, kafinma ya iso ta tashi tsaye dasauri tace “Ya Hanad kaman pepper soup ko” bata plate din yayi yace “mayyan nama kawai” dan tana balain son nama tun tana yarinya, murmushi tayi takarba dasauri tazauna tashiga ci ya tsaya shikuma yana kallonta, she looks so happy hakan made him so happy, dan yarinya ce da dawuya kaga she’s happy saisa anytime she looks happy happiness dinta is infectious sai kawai kaji kaima ka kamu da farin ciki. Juyowa tayi takallai tana tana naman kaman wata yar baby looking so adorable ganin ita yake kallo yasa tamikamai last piece na meat din tace “zakaci” hararanta yayi yace “marowaciya sai yanzu zaki bani to banci” dan dariya tayi tace “yakuri bari naci wanan gobe saimuci tare, Ya wai yaya ake dafa nama ne”? “Har yanzu ba’a barinki ki shiga kitchen?” Gyadamai kai tayi tace “ba Kaka tahana ba” gudun karta tunakomi dan yanzun nan kuma tahau kuka tasa yace “zan sayo nama saina koyamiki a kitchen din side dina” sosai tashiga jin dadi tana tauna namanta bude kofa akayi dasauri dukansu suka waiga, Mum ce fuskarta amurtuke, wani mugun kallo tama Hamad tace “mena gayamaka? Zokabar dakin nan” tai maganan tareda nunamai kofa, tashi yayi ahankali batare dayamata gaddama ba yazo yabita gefenta yafice, shigowa dakin tayi tazo har gaban gadon Du’a data sauke kanta kasa tana rikeda bowl din pepper soup din data cinye tace “ke bazakiji da bakin jinin ki kinemi yanda zakiyi ubanki yama yarda cewa ke yarshi ce ko yadinga lissafawa dake cikin yaranshi kina nan kina nema kisama dana bakin jininki ne, sabida kinga yanda ubanku keji dashi first son dinshi ga ilimi ga kyau shine zaki biyo tanan, to ta Allah batakiba bakar mayya kawai, kijechan kiji da kanki, na tsani uwarki amman naga matsalan da haihuwanki kesata ciki wlh har tausayamata nake, wayama sani ko wani aljaninne yadura mata cikinki dan naji ance tayi aljanu datana gida da kyar namijin dare yamabarta tai aure” ahankali tashare hawayen daya zubomata sharr babu abinda ta tsana irin adinga kiranta da yar aljanu ko mayu, Mum tasake wurgamata mugun kallo tace “wawiya dakikiya kawai babu abinda tasani sai zaman daki, kannenta ma sunfita iya karatu sunfiki iya komi Babanki yamaidake gidahuma yaryar aljanu kawai” wanan karan fashewa da kuka tayi sosai takai hannunta tadaura kan fuskanta tana kuka, murya chan kasa ta yanda Baza ajiba tace “niba yar aljanu bace” da sauri Mum dake tsaye kanta tace “me kikace Du’a? Mayarmin da magana kikayi? Did you just talk back at me eh?”.



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫




✍️ M SHAKUR

Don yin magana directly da M Shakur click on this link wa.me/+2347012181461
M Shakur nada group din Matan Aure wanda idan kinason kishiga is just 1k.
hakama idan kinason advert shima M Shakur duk tanayi.




free page
EPISODE 3️⃣
Girgizamatakai tayi ahankali gwaninban tausayi alamun bada ita takeba, cikeda mugun tsana tace "haka zaki kare rayuwanki awanan dakin, agabanki yayyinki da kannenki duk zasuyi aure ke kina nan adakinnan har tsufa bazakiyi aureba saidai ko indaga dangin ubanki aljanune wasu zasuzo kuyi wup dake, mai bakin jini kawai mara kunya" tana maganan tawuce tafice daga dakin, sosai tafashe da kuka, har bakin suka tafi su Nana suka dawo dakin nan kuka take bata denaba, dayake sun saba bawai sabon abubane kukantaba saisaima babuma wanda yabita kanta saima shirin kwanciya dasuka shigayi suka gama Hawwa takashe wutan dakin, haka taci kukan nan har batasan sanda bacci yay awon gaba da itaba.


Yau Monday sabida taci kuka batai bacci dawuri ba sai wuraren 8 ta farka, koda ta tashi babu kowa adakin saidai sababbin novels datagani manya guda uku agefenta dasauri ta tashi zaune ta dauka tana dubawa, sunan Novel din farkon The Noisy Naigbour, na biyun sunanshi the killer tree, saina ukun Disastrous Love, wani kalan murmushi tayi sanan ahankali tace "thank you Ya Hamad" ajiyesu tayi tawuce bayi alwala tadauro sanan tafito tai sallan asuba tabude Al Qur'ani tana koya Haddan da Abba yabata, saida ta tabbatar ta haddace shafi daya darabi sanan ta tashi, dakinsu ta shiga gyara musu wanda yanzu zata iyacewa a rayuwa that's the only thing data iya gyaran daki shima da karfi da yaji takoyama kanta, ta gyaramusu gado sanan tawuce bayi tayi brush tayo wanka tafito ta shafamai sanan tasaka wani riga da skirt na atampa daya mata kyau tai parking gashinta da kyar sanan tadauki novel kaman barauniya tabude kofan dakinsu ahankali sanan tasakai taleko kadan ganin babu kowa yasa tafito duka, sanan tashiga sadadawa tafara tafiya ahankali zatai stairs. "Ina zaki"? kaman daga sama taji muryan Mami dasauri tajuyo, hada ido sukai da Mami data fito daga dakinta tana kallonta, saukar da kanta kasa tayi tana kara kankame novel dinta ahankali tace "Mami good morning" batare data bata amsaba tace "wuce kikoma dakinku ga Uwani nan zansa takawomiki break" gyadama Mami kai tayi ahankali sanan tajuya zata koma dakinsu bintada kallo Mami tayi harta shige sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali tawuce tasauka kasa, hada mata breakfast tayi kunun gyada da kosai, samin kanta tayi da daukan wani karamin plate tajuyemata ragowan naman da Abban su yarage sanan ta kwalama Uwani dake wanke wanke kira dasauri Uwanin tazo tray tabata tace "kaima Du'a abinci adakinsu" karba tayi tawuce sama bude kofa tayi tashiga tana kallon Du'a data bude novel tana karantawa, har gaban Du'a tazo sanan ta tsugunna ta ijiye tray din still kallon Du'a take, ahankali Du'a ta janye novel din datake karantawa daga kan fuskanta jin kaman ana kallonta hada ido sukayida Uwani, almost 2yrs Uwani na aiki a gidansu but she thinks yaune 3rd time datake ganin Uwanin hakan yasa cikin yar muryan nan nata tace "kece uhmm yama sunanki U....uuuuu...." takasa tuna sunan dasauri Uwani tawashe baki tace "Uwani sunana mai aikin gidan nan" gyadamata kai Du'a tayi sanan tasake maida fuskanta kan novel din tacigaba da karatun dan ko kadan batada surutu kusan cikin duka yaran tafi gado halin mahaifinta indai rashin surutu ne.




Sosai Uwani takasa motsi daga wajen sai wani irin kallon Du'a take dabamatasan tanayiba, bude kofa Mami tayi ahankali ganin yanda Uwani ke kallon Du'a dabamatasan tanayiba dan ita karatun novel dinta take bilhakki yasa ta dakamata tsawa. "Uwani" firgigit ta farka daga dogon tunanin datake haka itama Du'a tadan firgita jin muryan Mami hakan yasa duk suka kallo Mami, cikeda bacin rai Mami tace "kin manta kinbar aiki a kitchen ne zoki wuce kifita" dasauri ta tashi ta taho tace "yakuri Hajiya" fita tayi Mami kuma ta watsa watsama Du'a data zubama mahaifiyar nata manyan fararen idanunta harara sanan tajuya tafice, tai kasa danso take tadaura girki, kitchen ta shiga tana duba naman data saka a wuta itakuma Uwani tacigaba da wanke wanke tana tunani sai chan tajuyo ta kalli Mami da hankalin ta kekan juya naman datake dake wuta tace "Hajiya" "ya akayi Uwani"? Mami tamata tambayan batare data kalletaba, tsayarda komi Uwani tayi tace "Hajiya kunada y'a haka maisa kuke boyeta wanan yarinya taki haka aiko shugaban kasa tafi karfinshi, maisa kuke kulle ta adaki haka" tunda tafara maganan Mami takasa cigaba da juya naman datake ta tsaya chak harta gama maganan datake sanan tace "ki tsaya a huruminki Uwani inba kinaso mu sallameki mu nemo watabane" dasauri tace "yakuri Hajiya tuba nake, kawai daman abin ya tsayamin araine" juyawa Mami tayi tacigaba da aikinta bata karabi takanta ba.
*******************




Yau Friday
Sunada wata al'ada agidan ranan jumma'a kowama gidan nacin gayun Jumma'a. Su Nana tun 11 suka dawo yau sabida lectures daya kawai sukeda shi, tun safe batai wanka ba sabida Novel din Disastrous Love datake karantawa daya daukemata hankali gabaki daya, su Nana ko harsun sake wanka sunci gayu abinsu sunfice daga dakin zuwa dakin Mum dinsu. Bude kofa akayi Mami tashigo daga bakin kofan ta tsaya binta tayida kallo sanan tace "yau bazakiyi wankan bane"? Dasauri ta ijiye novel din ta kalli Mamin ta dataci gayu cikin wata hadaddiyar bubu na shadda, tashi tayi dasauri tasauka daga kan gadon daga ita sai rigan baccin data saka iya guiwa, ahankali tasaukar da kanta kasa tana wasada yatsunta tace "yanzu zanyi Mami" tana maganan dasauri tajuya zuwa bathroom dinsu tabude kofa tashiga Mami tabita da kallo harzata bude kofa tafice saikuma ta dawo cikin dakin, gaban wardrobe din dakinsu taje budewa tayi ta tsaya tana kallon side din kayan Du'a, bangaren bras dinta ta kalla danta lura kwanan nan bata saka bra at all, daukan bra din tayi ta kalla sai lokacin tagane duk su mata kadanne saisa bata sawa kuma bazata iya fadan mataba, kwasosu tayi gabaki daya tadauki wani leda tazubasu aciki sanan tawuce tafita daga dakin, dakinta tashiga ta ijiyesu agefe sanan ta kwaso mata wasu new manyan bra masu kyau guda uku sanan tafito tadawo dakin, wardrobe din taje ta ijiye bra din sanan tazakulo mata wani lace mai bala'in kyau pink and white flowers dan tasan Du'a da hauka babu abinda ta iya kowani kalan kaya tasamu saka wa take, taciro tahada mata da sabon bra da pant tadauko ta ijiye mata kan gado, sanan tamaida wardrobe din tarufe takoma dakinta, kwalli tadauko mata sabo dawani sabon turare tadawo ta ijiye mata kan gadonta daidai lokacin tafito daga wankan daureda towel a kirji, juyowa Mami tayi takalleta daga sama har kasa, sunnar da kanta tayi kasa cikeda kunyan Mami tana gyara towel din dan bai rufe mata cinya da kyau ba kuma batasan zata sami Mami adakinba data maida rigan baccin ta, juyawa Mami tayi tafice abinta, dasauri tazo kan gadonta ta zauna, kwallin da Mami ta ijiye tafara dauka tace "laaaaa yama sunanshi irin nasu Ya Nana dasuke sawa a ido" wani irin murmushi tayi ta ijiye tadau kwalin turaren tana budewa tace "laaaa nima inada turare yanzu sunanshi Zara" budewa tayi ta ijiye cikeda farin ciki, agurguje tashare jikinta sanan tashiga shafa mai sabon bra tadauka tasaka aiko yamata cip cip lace din tasaka yamugun mugun mata kyau turaren ta tadauka ta feffesa yafi feshe goma sai murmushi take sanan tadau dan kwalinta da kwallin ta tafi gaban madubi, zama tayi tadauki comb taje gashin tayi sanan tai parking gashin da kyar sanan tadau dan kwalin duk yanda taso tadaura takasa daga karshe daurin yan kauye kawai tayi dan bata iyaba amman dudda haka tai kyau sanan ta bude kwallin taciro zata saka takai idanunta looking so excited kafin tasaka tawani tsirama idanunta ihu tayi sosai tawani zarooo hakan yasa tama tundaga idanun har zuwa gefen idanun har kunnenta bakin zanen layi, sosai ta kankame idanunta tana ihu ga radadi sai kuka batasan lokacin data mikeba tana tangadi tana ihu. "wayyo idanuna wayyo idonta" Mami da haurowanta sama kenan taji ihun ta dasauri tai hanyar dakin bude kofa tayi daidai yana shirin kuma kanta da bango tana ihu dawani irin sauri Mami ta tarota tana kokarin tallabo fuskanta tace "maiya sami idon"? Rirrike Mamin tayi cikin kuka tace "Mami idona zafi kwallin nanne ya tsiremin kwayan idanun" Mami na rikeda ita ajikinta tai bathroom dinsu da ita bude tap tayi ta tare hannunta ta debo ruwa wanke mata fuskan tayi tass sanan takashe tap din tana rikeda fuskan nata tace "bude idanun naga" ahankali tabude idanun kadan, aiko idon yayi jajir, kallon Mami tayi tanadan kyafkyafta idon tace "yadena zafi Mami" Mami na rikeda ita tafito da ita daga bayin zuwa gaban madubi zaunarda ita tayi sanan tadauki wipes din Nana data gani awajen tabude taciro kwara daya sanan takama fuskanta tagoge kwallin dayamata layi har kunnenta tagoge tass, sanan ta gyara kwallin dabama tasa a ido ba saidai kasan idanun sanan tadauki kwallin, habanta takama tace "bude idanun nagani" budewa tayi sanan Mami ta zizara mata kwallin aduka idanun rirrike Mamin tayi tawani tura fuskanta kan cikin Mami tace "Mami idona wani iri daman haka yakeyi wayyooo" chak Mami ta tsaya tamanta the last time da hannunta yama taba jikin yarta saiyau, firgigit kaman wacce ta tuna wani abu sai kawai ta hankadeta daga jikinta batare data kalleta ba tace "dau dankwalinki ki daura" tawuce tafita daga dakin, bin Mamin tayi da kallo sanan tajuya ta kalli Madubi kwallin sunma idanunta wani irin hadadden kyau, murmushi tayi tadauki dankwalin tasake mai wanan local daurin yan kauyen nan sanan ta tashi hijabi tasaka tai sallan azahar ganin biyu tamayi sanan ta tashi tacire hijabi taje tagaban window dakinsu ta yaye kannenta tagani su Aneela da Amal a compound suna guje guje suna wasa duk sunci gayu suma, hakanan taji inama itace komawa tayi tazauna sanan tadauki novel dinta tabude zata fara karantawa saikuma kannenta datagani a compound suka kara fadomata arai jitayi she's damn tempted to go out, maida novel din tayi tarufe sanan tamike tsaye tana rikeda novel din tabude kofa taleko ganin babu kowa yasa da sauri tafito ta maida kofan ahankali ta rufe sanan tai stairs dagudunta har tana neman faduwa tasauka kasa nanma babu kowa, motsi dataji daga sama anbude kofa taji muryan Mum tanama Nana magana "kinduba zobon dayasa kimai hope yay sanyi"? wani irin kwasa tayi dagudu tashiga kitchen dinsu gabanta nafaduwa, gani tayi anama girki a kitchen din ga hadaddun kula na baki dataga an jera asaman kan fridge tana mamaki baki zasuyi yaune kuma, jin muryan su sun sauko kasa yasa da sauri tabude kofan kitchen dazai sadata da backyard tafita dasauri tamaida kofan tarufo dasauri daidai sun shigo kitchen din sanan tawani irin kwasa da gudu taidan mini garden din da Abban su yamusu awajen yawanci weekend Abba nazuwa garden din yazauna yasha iska, is very small a portable ga flowers sosai na daidai kudi ba irin na masu kudiba, ko kadan bata lurada mutumba sabida tana gudu tana waigan bayane jitayi kawai tai tuntube da mutum taiwani irin tumble tasaman kanshi tatsallako gabanshi zatai baya ta fadi yawani irin rikota gam gam hakan yasa dankwalin kanta yawani irin zamiye yafadi kasa, novel din datake rikeda shi yawani fadi shima, yanda gabanta ke faduwa dan tariga tasarai fadi zatayi yasa ta kankame idanunta gamgam cikeda tsoro tana wani irin nishi da bakinta dake fitowa afili.



Chak ya tsaya batare daya saki hannunta ba yake kallonta tundaga kan tattausan hannunta daya rike zuwa kyakkyawan fuskanta da yanda ta runtse idanunta cikeda tsoro tana nishi zuwa yanda jelan gashinta ke gogan kasan wajen. cikin wani irin murya yace "who are you beautiful lady"? jin muryan mutum wanda batasaniba dan duk azatonta da Abba taci karo danshi ke zama awurin nan danhar tasadakar yautamutu a hannunshi yasa tabude idanunta dasauridasauri sanan tawaresu sosai ta kalleshi hada ido tayi dawani kyakkyawan Matashi wanda akalla zaiyi mate din Ya Hamad dinsu yana sanye cikin wani farin yadi mai laushi sai zuba uban kamshi yake, kara zaro idanu tayi tana kallonshi batare datayi maganaba, murya chan kasa yace "who are you? what's your name Pretty Lady" kokarin fizge hannunta daga nashi tashigayi sanan tace "My name is Du'a" wani irin lumshe ido yayi yabude yana karabinta dawani irin mayen kallo yace "you have a very very, verrryyy beautiful name, keyar gidan nanne ko bakuwace ke" kokarin fizge hannunta take takasa sabida yanda yariketa gam gam tace "ni yar gidan nanne, nika sakenmini hannu intafi" ganin hankalin ta nakan hannunta dayaki saki yasa yace "kinaso in sakenmiki hannu"? gyadamai kai tayi batare data kalleshiba ta kalli gefe daya, yace "to answer my questions saina saken miki hannu" dasauri ta gyadamai kai tana kallon gefe dan batason hada ido dashi sabida kallon dataga yanamata ahankali yana kallonta still yace "ke kanwar su Hamad ne"? dasauri ta gyadamai kai alamun eh hakan yasa yace "amman your mum is different ko?" sake gyadamaikai tayi tace "Mami ce Mum dina" yanda take magana da muryanta kaman na yara tsabagen dadi bala'in tafiya dashi yake she talks kaman yar yarinya kuma kaman ashagwabe, ahankali yace "Yaya akayi to bansanki ba?" ahankali tace "Abba baya barina infita" yanda take maganan gabaki daya taki kallonshi sai gefe take kallo yasa yasake binta dakallo tundaga gashin kanta har zuwa kirjinta da yake hango tudun boobs dinta da kyau wowwww! dan he could have a clear sight saman sabida yanayin wuyan riganta dakuma yanda tadan rankwafo ta gabanshi, tana kallon gefe still tace "dan Allah kasakeni in tafi I don't know you, idan wajen Ya Hamad kazo kaje side dinshi Abba kadai ke zama anan" murmushi yamata ganin da gaske takasa kallonshi sai gefe taketa kallo tana magana this girl is not use to men! yay maganan aranshi sanan yace "ni wajenki nazo sonki nake" girgixa mai kai tayi dasauri tace "wlh bani bane banama fita baka sanni ba please kasakenmini hannu nakoma cikin gida ba'a san nafitoba wlh" yanda take maganan yake mugun burgeshi baisan lokacin dayace "antaba gayamiki u look beautiful whenever you talk? Is this ur natural hair"? yakai hannunshi zai taba kanta dasauri takoma baya saikuma tasaki kuka shima binta yayi tana komawa baya yana kokarin biyota zai taba mata gashin sukaji karan fadin abu dasauri dukansu suka waigo baya.



Nana ce tafito taci uban gayu sai kamshi take zubawa tadauko hadadden tray da jug din cold zobo da cups kekai dukta sakesu akasa jug din yafashe zobon nabin kasa.


💫 MY BEAUTY MY CURSE 💫


✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 4️⃣
Ganin Nana yasa takara karfin kukan tace "Ya Nana kinga wanan mutumin ko yarikeni yaki yasakeni tundazu" juyoda kanshi yayi yana kallon yanda take magana kaman zai cinyeta yace "inda nasan akwai kyakkyawan yarinya irinki agidan nan I wouldn't have wasted my expensive time on this your sister yanuna Nana" wani irin kwalalo idanu tayi sai yanzu tagane saurayin Nana ne wanda zata aura, rawa jikinta ya shigayi tana kallon Nana tana kokarin fizge hannunta daga nashi, ganin yanda ta daburce yasa yasaketa yana murmushi looking so damn happy, dawani irin gudu ta kwasa tama kasa komawa ta hanyar data biyo dazatazo kawai ta zagaya takoma ta compound tabude kofan falonsu ta shiga da gudu tai sama.




Binta yayi da kallo harsaida yadena hangota sanan ahankali yakalli dankwalinta dake wurin da novel dinta yadauka sanan yakai dan kwalin kan fuskanshi yana wani shakan kamshinta sanan ya janyesu daga kan fuskanshi yakalli Nana dake tsaye takasa kwakkwaran motsi yace "so kinada this beautiful sister baki taba gayamin anything about her ba, in fact you've never mentioned her to me ma" tattaro courage dinta tayi tasakinmai murmushi kobakomi akwai one thing data koyo daga wajen Mum dinta is kirsa, karasowa tayi kusada shi tazauna akan carpet din data shimfidamai cikeda salo irin na siyasa tace "ko Abban mu dudda yarshi ce baya acknowledging nata cikin yaranshi, bama Abba ba har uwarta Mamin ta data haifeta ma, bakaganta ba kaman mayya, Mamanta kafin tai aure tanada aljanu namijin dare, kafin acire mata aljannun akwai wanda ya aure ta so ance shine yamata cikin wanan yarinyar saisa gatanan daban, gabaki dayan danginmu ita kadaice fara, ita kadaice daban, kamanninta komi nata daban, Kakanmu ta tsaneta, she has been nothing but a bad luck duk inda tashiga saitai causing trouble saisa Abba yay grounding nata, ba boko ba islamiyya ko this our compound she's not allowed to come out, iya kanta daki, ko kitchen ba'a bari tashiga kartaje ta kashemu, I don't think ko hot water ma ta iya boiling, she has been grounded like this for years ba tun bayan JSS2" tunda take magananan yake kallonta don shi mugun dan gayu ne dan boko yaron dan gata dan masu kudi wani irin tabe baki yayi yace "you people are being sarcastic, young innocent preety girl zaku kulle haka agida sabida she's different kamanninta daban that's illiteracy, gatanan so pretty my lord, her body is so soft, ga gashi, just look at her snatch waist, ka auri wanan ai zaka more rayuwa da itane kasha miya kasha miya harka gaji" murmushin yake tayi tace "common Muhsin mubar maganan yar Aljanun nan" mikewa tsaye yayi yace "I'm being serious ni, wai kinzaci wasanake, wlh naganta inaso nafasa aurenki, bari naje nasanar da Dad, this ur beautiful sister nakeso wlh ita zan aura, gata so young daga gani batafi 20 ba" tashi tayi dasauri kirjinta na bugawa uku uku dan arayuwanta tana bala'in mahaukacin son Muhsin kaman zata haukace, yarone ga kudi ga gata ga kyau, dawani irin sauri takama hannunshi tarike tace "please Muhsin inma wasa kakemin this joke is way too expensive, bikinmu duka duka baifi 1month bafa saikace kafasa aurena kanwata kakeso daga ganinta yanzun nan don't you see what's going on abinda yasa ake cewa ita yar aljanune, minti nawa da ganinta har kaji kana sonta u are willing to risk our relationship damuka raina for years when

Please Login or Register in order to submit comment